Rai a ɓace, Dul'Ururu ya saka hannu biyu akan sandarsa ya ture takobin Zaikid data jan doki gefe. Sannan da sauri ya juyo ya take zakunan dake riƙe da ƙafarsa ya kuma kawowa Cokali sura. Abin mamaki kafin hannunsa ya ƙaraso sai Cokali ya ɓace ɓat. Sarkin ya juyo kan sarkin Bai da Inyaya, amma kafin ya ƙaraso duk sun ɓace. Ya ƙara juyawa kan Barilu, amma kafin yayi wani abu shima ya ɓace.
"Hmm.. wannan sihirin da kuka zo dashi bazai yi aiki ba," Inji Dul'Ururu.
To a yayinda Dul'Ururu yake fama dasu Zaikid, acan gefe kuma Maikiro'Abbas ne suke kai-komo da Ƙaraiƙisu.
"Haha... Maikiro'Abbas, Maikiro'Abbas," Inji Ƙaraiƙisu. "Kada ka bani kunya mana. Na saka rai zan samu jarumi barde wanda zan kara dashi amma har yanzu banga komai ba."
Ya ƙara kawowa Maikiro'Abbas duka da ƙafa. Maikiro'Abbas bai motsa ba har ƙafar basamuden tazo ta same shi. Zaka yi tunanin saboda girman ƙafar zata yi cilli da Maikiro'Abbas, amma sarkin ko gezau baiyi ba. Yana tsaye kikam a inda yake. Ƙaraiƙisu ya dunkule hannu ya daki cikinsa. Iska ta tashi sama saboda ƙarfin dukan. Amma bayan komai ya lafa Maikiro'Abbas yana tsaye a inda yake ido a rufe.
Ganin haka ya fusata Ƙaraiƙisu. Hannu biyu ya dunkule ya fara yiwa Maikiro'Abbas luguden duka ta hannu da ƙafa. Ya daki fuska, ya daki wuya, ya daki ƙirji, ya daki ciki, sannan ya daki ƙugu. Ƙura ta turnuke saboda ƙarfin dukan.
Sai da aka shafe mintuna biyar ana abu ɗaya. Maikiro'Abbas baiyi ƙoƙarin tare dukan basamuden ba ko sau ɗaya har yayi ya gama. Bayan ƙura ta lafa aka hango Maikiro'Abbas a tsaye baya motsi.
"Ko ya mutu?" Inji wani mayakin Ururu.
"Ko kuma dai ya suma ko?" Inji wani.
"Kai, ni nafi tunanin mutuwa yayi saboda ƙarfin dukan daya sha ya wuce misali."
Haka dai aka ci gaba da tattaunawa akan Maikiro'Abbas. Shi kuwa ƙaraiƙisu kawai baya ya koma yana jira yaga mai zai faru. Shin Maikiro'Abbas zai zube ƙasa? Shin ya suman da gaske? Abu guda da yake firgitashi shi ne ko ɗigon jini bai gani ba, kuma bai ga ciwo ba. Ko dutse yayi wa wannan duka sai ya farfasa shi balle jikin mutun.
"Ƙaraiƙisu," inji Maikiro'Abbas. Jin muryar yasa Basamuden yaja da baya da sauri. "Ba kai kaɗai kake da kakkausar fata ba. Tun Farkon Lokaci akwai Sarkin-sarki da tazo da fasahar Tauri. Akwai denizawa da suke da fasahar Rana. Bambancin taka fasahar da tasu shi ne: kai taka fatar izza bata ratsa ta. Hakan sai yasa bil'adama suga kamar fasaha bata cinka. Amma a zahiri riga ce kawai ta kariya ka saka. Mai kake tunani idan muka cire wannan riga, muka kwace kariyar da kake taƙama da ita?"
Har yanzu Maikiro'Abbas bai motsa ba. Amma jin kalamansa yasa Ƙaraiƙisu ya fara jada baya. Babu zato babu tsammani, Maikiro'Abbas yayi tafiya acikin lokaci ya cafi wuyansa ya ɗaga shi sama ya buga shi da kasa. Sannan ya ƙara tashi sama ya diro kan ƙirjin basamuden da gwiwa. Mayaƙan dake gefe suna ganin gama-garin duka ne kawai, amma shi Ƙaraiƙisu yasan abin ba haka yake ba. Duk sanda Maikiro'Abbas ya dake shi sai kowacce gaba a jikinsa ta amsa. Kuma kafin ya wartsake ya ƙara jin wani dukan ya sauka. Dai-dai inda Maikiro'Abbas ya dira da ƙafarsa a ƙirjin basamuden ya tsage gida biyu. Amma idan ka lura sosai zaka ga tsagewar bata shiga ciki ba, iyakacin fata ta tsaya. Maikiro'Abbas ya lura da hakan saboda haka ya dunkule hannu ya ƙara dukan wajen. Hannunsa yana haɗuwa da fatar basamuden, wajen ya ƙarawa buɗewa.
Ganin haka Ƙaraiƙisu ya fara ƙoƙarin ture Maikiro'Abbas daga kansa amma a banza. Maikiro'Abbas yasa ƙafa ya take hannunsa guda ɗaya, sannan yasa sandarsa ya take ɗaya hannun. A lokaci guda yaci gaba dayi masa luguden duka a ƙirji.
Cikin ƴan dakiku fatar ƙirjin Ƙaraiƙisu ta tsattsage. Abin mamaki kana hango wata sabuwar fatar a ƙasan fatar data tsattsage wadda tafi ta saman baƙi.
Maikiro'Abbas ya sauka daga ƙirjin Ƙaraiƙisu ya tsaya a gefe yana kallonsa. Ganin haka Ƙaraiƙisu ya fara jada baya zai gudu. Maikiro'Abbas ya ɗan durkusa ya miƙa hannu ya damƙi wuyansa ya ɗaga shi ya nunawa sama. Ƙanƙara fara tas ta fara fita daga cikin ƴan'yatsun Maikiro'Abbas tana shiga ƙirjin Ƙaraiƙisu. Abin mamaki duk ƙanƙarar data taɓa fatar wajen wadda ta tsattsage sai kaga ta narke. Amma kuma a lokaci guda wata ƙanƙarar tana shiga ciki ta tsakankanin fatar data tsage ta isa wajen fatar dake cikin. A hankali ƙirjin Ƙaraiƙisu ya fara yin fari yana daskarewa.
Ƙaraiƙisu ya fara tarin jini yana wutsil-wutsil yana ƙoƙarin ƙwacewa.
"Kaine...*tari* na farko daka.. *tari* fara gano sirrin nan. Tabbas saina halaka ka... *Tari.*
Basamuden yana magana yana tari. Wani abin mamaki, gashi rai a hannun ALLAH amma kuma cika baki yake yana cewa sai ya halaka Maikiro'Abbas. Sarkin bai damu ba. Yaci gaba da danna ƙanƙara cikin ƙirjinsa.
A hankali gaba ɗayan ƙirjin yayi fari far ya daskare. Basamuden ya daina motsi. Maikiro'Abbas yayi cilli dashi gefe guda sannan ya goge hannunsa a jikin sandarsa.
Ganin yadda ƙarshen Ƙaraiƙisu ya kasance, mayaƙan Ururu dake kusa suka fara jada baya. Dukkansu sunga faɗan Armad da Ƙaraiƙisu. Sun kuma ga yadda izza ko fasaha bata aiki akan basamuden. Da damansu suna ganin basamuden yaci dubu sai ceto; babu abinda zai iya kaishi ƙasa. Amma kuma gashi Maikiro'Abbas ya gama dashi cikin ɗan lokaci ƙanƙani.
"Ya... ya... kashe shi..." Inji wani mayakin Ururu cikin kinkina.
"Ya kashe mutanen ikwatora!"
To a yayinda suke jimami, Maikiro'Abbas kan Dul'Ururu yayi yana sassarfa. Daga inda yake yana hango abokinsa Zaikid da sauran mayaƙa suna fafatawa da Dul'Ururu. Yana buƙatar ya kai musu agaji.
Sai dai baije ko'ina ba kwamanda Yurba ya dira a gabansa.
"Kashe shi ka samu babban rabo," inji Maruta wanda ke nesa amma kuma hankalinsa yana kan Maikiro'Abbas.
Yurba yaji abinda Maruta ya faɗa amma ko kaɗan bai damu da babban rabon ba. Abinda kawai yake so shi ne ya cimma burinsa: cin nasara akan Maikiro'Abbas - mutumin daya gagari Ururu tun a wancan zamani.
Maikiro'Abbas yaja tunga suka fuskanci juna da Yurba.
Daga gefe kuma jan hayakin daya ɗauki hankalin mutane ya lafa. A ƙasansa Burjan ne tsaye yana kallon wata farar mace tana kaɗe ƙurar dake rigarta. Bayan ta kammala kaɗe duk ƙurar dake jikinta sai ta fara ware ƴan yatsunta saboda tuni sukai tsami saboda dauri.
Can mayaƙan Maikironomada sun hango wannan mace. A tare suka haɗa baki sukai shewa cikin farin cikin samun nasara.
"Fatima!"
"Fatima!!"
"Fatima!!!"
"Barka da dawowa," inji Burjan, ya ɗan risuna kaɗan.
Fatima tayi murmushi sannan kai tsaye ta wuce wajen da Armad yake kwance a sume. Akwai ciwuka da dama a jikin Armad, amma babban abinda ya hanashi farkawa shi ne rashin izza. Idan ta bashi izza, Rabi zata ƙarasa ragowar.
Cikin sauri tayi ɗan lissafi ta gano adadin izzar da Armad zai buƙata da kuma lokacin da zata ɗauka tana bashi. Aƙalla zai ɗauki minti goma. Ta kalli Burjan sannan ta juya ta kalli Binani da Diwani da Ki'jinu wanda ke tsaye a gabansu suna shirin afka musu. Taga harin da kwamandun uku sukai amfani dashi ɗazu kuma tabbas tasan Burjan shi kaɗai bazai iya ba. Idan ta barshi dasu tsahon minti goma to zasu iya halaka shi, koda kuwa su Rabi sun taimaka masa. Mai ya kamata tayi?
A lokacin wani tunani yazo mata rai: shin wai ma tana so ta warkar da Armad a filin yaƙin? Tasan tabbas tana warkar dashi zai ƙara shiga yaƙin ya ƙara samun wani raunin. Watakila ma ciwon dazai samu yafi na yanzu. Watakila a kashe shi. Komai zai iya faruwa. Kuma tabbas bata so ta rasa ɗanta. Tayi shiru tana tunani.
A lokacin kuma taga yadda mayaƙanau suke mutuwa. Dukkansu sunzo cetonta ne ba tare da sun santa ba. Suna da iyali da ƴaƴa, amma hakan bai hana su amsa umarnin sarki ba. Sannan kuma har yanzu yaƙin ake yi ba'a gama ba, wasu da dama zasu ƙara mutuwa. Idan ta tashi Armad zai ceci da dama daga cikinsu su koma wajen iyalinsu da rai da lafiya. Tabbas akwai son kai da son zuciya idan ta hana Armad shiga faɗan a wannan lokaci. Domin da idonta taga irin ƙarfin izzar Armad. Tasan cewa a filin mutane kaɗan ne zasu iya bada gudummawar dazai bayar musamman saboda irin faɗin fasahohinsa.
Fatima taja dogon numfashi ta danna hannunta akan ƙirjin Armad. Izzarta ta fara shiga jikinsa. Bayan ta tabbatar ta haɗa zaren izzarta da nasa sai ta miƙe ta juya wajen su Diwani.
"Waye yake son uwarsa ta haifi wani acikin ku?" Inji Fatima.
Nan take aka fara kallon-kallo a tsakanin kwamandun ana ƙoƙarin gano waye zai fara shiga.
A gefe kuma faɗa ya fara ɗaukar armashi tsakanin Maikiro'Abbas da Yurba.
"Ni zan karya alkadarin ka," inji Yurba.
Garin Sarki Iluru - Seerish Unguwar Daif Teburin mai shayi *** Koda yake zai yi wuya a kira wajen cinikin Salmanu da teburi domin kuwa tuni wajen ya daɗe da ƙasaita ya zama shago, shago kuma ya zama wajen cin abinci. A halin yanzu akwai ƙaton ɗaki da kuma kujeru inda kwastoma suke zama suna cin abinci sannan suyi hira, musamman ma hira. A unguwar Daif babu wani waje dake tara magidanta (maza da mata) irin wannan wajen. Zaka iya cewa duk wata gulma da ƙananun zantuka na unguwar dama na sauran gurare a faɗin duniya akan tattaunasu a wajen. Salman yayi ƙasa da murya cikin raɗa ya ce, "kun san asalin sunanta?" Wasu mutun uku dake kusa da teburin da Salmanu yake kai suka matsa kusa domin jin abinda zai ce. Suma ragowar mutun goma sha ɗin dake cikin ɗakin zubo kunne sukayi suna sauraro. "Mulkiyya sunanta - ƴa ce a wajen sarki ƙaraiƙisu, babban sarkin ikwatora." Inji Salmanu. Wani daga cikin su yayi farat ya amsa da cewa, "Amma da gaske ne an saka ranar daurin au...
Waw gaskia ne Muna godia Sosai
ReplyDeleteMuna godiya dr
ReplyDelete