"Ni, Maikiro'Abbas, na bawa Taidara Wilbafos auren 'yata Fatima Bayajidda akan sadaki kamar haka: na farko, littafin takobi; na biyu, izza shekaru dubu tamanin da uku."
"Ni, Alu mai sango, na karɓawa ɗana Taidara Wilbafos auren Fatima Bayajidda a bisa sadaki kamar yadda aka faɗa."
Mutanen da suke cikin ɗakin sukai shewa sannan aka fara kade-kade da raye-raye. Idan ka dubi dakin taron za kaga wajene makeke amma ko ina cike yake da mutane sanye da kaya na sarauta. Kowa ka gani kasan ya isa domin dai a wannan rana babu wani saƙo da loko wanda sarki Maikiro'Abbas bai tura goron gayyata ba.
Sai da akai kwana uku cir ana biki sannan jama'a suka fara watsewa. Bayan an kammala aka kai amarya dakin mijinta.
A dai-dai lokacin da amarya take tare da mijinta, a dai-dai lokacin yarima mai jiran gado yabi Hidaya cikin wani lambu dake fadar. Tana zaune tayi shiru tana kallon kifaye suna iyo, ƙafa ɗaya kan ɗaya. Idan iska ta kaɗa sai kaga gashin kanta yana tashi sama, fatarta tana ƙara haske da kyau, kamaninta na 'ya mace suna kara bayyana musamman saboda yar-karamar rigar dake jikinta.
Har yarima yazo ya tsaya a bayanta bata kula ba, idan kuwa ta kula to bata nuna ba. Har sai da ya ajiye fulawar dake hannunsa a gefenta sannan ta ɗago kai ta kalle shi.
"Yarima?"
"Gimbiya."
Hidaya ta karkata kai ta harareshi. "Yaushe na zama gimbiya? Tsokanar ta motsa kenan. Wai ma na tambaye ka, yaya sunanka na gaskiya? Babu wanda yake faɗar sunan sai dai kowa yace yarima mai jiran gado, to ni dai yau sai naji sunanka na gaskiya."
Yarima yayi murmushi. "Indai kin yarda ke gimbiyace to zan faɗa miki sunana na gaskiya."
Hidaya ta girgiza kai. "A'a, bafa zan yarda ba. Kawai ka ƙaƙaba min wata gimbiya bayan ko tabarmar fada ban gada ba, kai dai ka faɗa min sunanka na gaskiya indai kana so mu zama abokai."
Koda jin wannan kalami nata sai fuskar yarima tayi haske ya fara murmushi, da sauri ya zagayo ya zauna akan kujera kusa da ita. Yana zama ya ɗauki fulawar daya ajiye a gefe ya miƙa mata, tasa hannu ta karɓa tana murmushi.
"Sunana Najunanu, amma dai da dama da suka san sunan suna kirana da Najan. Sunan baban mahaifina ne Maikiro'Abbas shi yasa mutanen garin nan basa faɗa, kamar wata girmamawace da ake yiwa sarkin tunda dai ba wanda zai ji daɗi a ringa kiran sunan mahaifinsa kai tsaye."
Hidaya ta ɗanyi shiru tana tauna sunan a bakinta. "Mai zai hana na ringa ce maka Nanu? Kaga babu wanda zai gane sunanka nake faɗa sannan kuma 'Nanu' da daɗi."
"A'a fa, Gimbiya, babu wani Nanu, sai kace wani mai nanannen hanci. Idan zaki ce Najunanu ki faɗa, idan ba zaki faɗa ba kice Najunan, idan kuma ba zaki fadi hakan ba to kawai kice yarima mai jiran gado amma babu wani Nanu."
"To kuwa kaima ka daina cewa Gimbiya indai baka son na ringa ce maka Nanu."
Yarima ya ɗanyi shiru kafin ya gyada kai. "To naji, na daina cewa gimbiya amma kada ki ƙara cewa Nanu."
Hidaya ta fashe da dariya. "Har ka saki wuƙar da wuri haka, kai da zaka ci gaba da ja har sai na gaji na haƙura. To bari kaji, bazan daina cewa Nanu ba, ehe."
Yarima ya ciji haƙora amma kuma kana ganin fuskarsa kasan bawai haushi yake ji ba, idan ma yaji haushin to bai wuce irin haushin nan na masoya ba.
"Ni fa daman ina neman ka," inji Hidaya. Ta juyo ta fuskanceshi. "Ina son na baka haƙuri akan abinda nayi maka. Dana san haka kake da kirki da ban cutar dakai ba, kai ko ɗan-yatsa da bazan ɗaga maka ba. A matsayin biyan bashi zan baka shekarun izza dubu, sannan zan biya maka buƙata guda ɗaya indai zan iya."
Wani daɗi da farin ciki ya mamaye yarima amma bai bari ya bayyana akan fuskarsa ba. Maimakon haka sai ya zumburo baki. "Kinga nace ki daina zancen faɗan nan, dan kawai kinci sa'a kin samu nasara sau ɗaya kacal shi ne kike tunanin ke wata kwararriya ce? To ai zamu ƙara gwadawa a ga wane zaiyi nasara."
Hidaya ta ɗaga hannu cikin saranda. "A'a, ba sai an maimata ba, Ni na yarda kafi ƙarfina. Amma dai ka gayamin, ka haƙura?"
A wannan lokaci duk wanda yasan Hidaya a fagen fama bazai ce ita ce ba domin kuwa ta saki fuska tana ta dariya.
"To na haƙura amma kada ki sake tada zancen, kinji?"
"Naji kuma nagode."
Da wannan suka ci gaba da hira ta yau da gobe suna tattauna al'amuran da suka faru na biki. Sai can dare Hidaya ta miƙe domin ta koma makwancinta. Yarima yayi ta maza ya tsayar da ita. Cikin cizon harshe, ya durkusa akan gwiwarsa guda ɗaya.
"Hidaya Wilbafos, zaki aure ni?"
Lokaci ɗaya fuskar Hidaya ta canja. Bawai alamun baƙin ciki bane ko kuma haushi ba, a'a, damuwa ce. Ta buɗe baki za tayi magana amma kalmomin suka maƙale a maƙogoronta.
"Ba sai kin bani amsa yanzu ba," inji yarima. "Ki yi tunani, zan iya jira tsahon lokaci, kawai dai kada kice a'a. Kinga yanzu kin bani kyauta ta shekaru dubu saboda haka zan iya jira. Duk abinda za kiyi kije kiyi a hankali ki dawo ki same ni. Ni dai kawai kada kice a'a."
Hidaya tayi shiru, wani gumi ya fara tsattsafo mata. Yarima ba shida laifi, duk wata mace za tayi farin ciki idan ta samu cikakken namiji kamarsa. Ga shi yarima, ga shi ma'abocin izza, ga shi jinin marubin farko. Tabbas da aurene a gabanta zata iya ce masa ta amince amma kuma a halin da take ciki a yanzu aure shine abu na ƙarshe a rayuwarta data ke tunani. Kuma banda wannan ba akwai wanda take so, ko kuma tace akwai wanda ta taɓa so. Amma kuma duk da haka tana jin nauyin yarima, tana kuma jin daɗin zama dashi da hira dashi, tabbas ba zata so ta rasa abokantakarsa ba duk kuwa da ba zata iya sonsa ba. Cikin sauri zuciyarta ta fara lissafin amsar da zata bashi wadda ba zata sosa masa rai ba, wadda kuma ba zata saka masa rai akan abinda tasan bazai samu ba.
Har yanzu dai yarima yana durkushe akan gwiwar sa. Daga inda take tsaye tana ganin wuyan rigarsa ya jike sharkaf da gumi. Tabbas ta san yana sonta, kuma ƙarya take tace bata taɓa ganin wasu alamu ba a shekarun da su kayi tare, amma tayi tunanin so ne gajere wanda zai zo ya tafi, sai dai kuma abin ba haka yake ba. Yarima ya mato kuma tana gani a idonsa.
Ta ja dogon numfashi tare da runtse ido tace, "kasan daga ina muka zo dani da babana? Kada ka manta kawai ganinmu kukai rana tsaka baku san daga ina muke ba, baku san wace irin rayuwa mukai kafin muzo nan ba, baka ganin kayi hanzari a fara so na?"
Wani murmushi mai ɗaci yazo gefen fuskar yarima ya tsaya. Da kyar ya dafa ya miƙe ya matsa kusa da ita, ya miƙa hannu ya riƙe hannunta na dama.
"Babu ruwana, ko mutum nawa kika kashe, ko jinin mutane kike sha, ko mayyace ke, ko sihiri ki keyi, kai ko shaiɗan ne ya haife ki, kai ko a wuta aka haife ki, ni naji na gani ina sonki, kuma zan rayu dake, zan mutu dake. Abinda kawai nake so shi ne ki amince min."
A lokacin Hidaya ta tabbatar yarima ya ma wuce inda take tunani. Irin son nan ne wanda yake taruwa a zuciyar mutum a hankali, a hankali har ya taru da yawa yayi wa mutum illa ta yarda zaka ga mutum ya kasa gane fari da baƙi, ya kuma kasa banbance gaskiya da ƙarya.
Tana cikin wannan tunani taji muryarsa a kunnenta."Kin amince?"
Kalmar 'kin amince' ta ringa kewayawa acikin zuciyarta tsahon lokaci har sai da taji yarima ya matsa hannunta sannan ta farfado.
"Zaka iya jira na shekara dubu?"
Yarima ya buɗe baki da sauri zai bata amsa amma ta katse shi. "Kafin ka bada amsa kayi tunani domin zaka iya wuce shekara dubu kana jira. Amma dai indai zaka iya jira har naje na gama duk abubuwan dana saka a gaba komai daɗewa na dawo to zan aure ka. Kawai dai ina so ka sani akwai wanda na taɓa so a duniyar dana baro, amma kuma yanzu yayi nisa ga bari na."
Ba tare da ya sani ba ya saki hannunta da sauri. Jin cewa akwai wanda ta taɓa so ya shige shi yadda baya tsammani, jikinsa yana rawa ya tambayeta, "akwai yiyuwar zai iya dawowa nan gaba?"
Hidaya ta yamutse fuska. Wato yarima bai ma damu ya tambayeta ko har yanzu tana sonsa ba, shi dai kawai burinsa ya tabbatar bazai dawo ba, ko tana sonsa ko bata sonsa shi dai yana sonta. Lallai akwai soyayya ta gaskiya acikin zuciyar yarima.
"Bazai dawo ba. Na rabu da shi rabuwa ta din-din-din."
Lokaci ɗaya fuskar yarima ta canja daga damuwa zuwa farin ciki. Ba tare da kamun kai ba yayi tsalle zai rungumeta, Hidaya ta matsa gefe da sauri. Sha'anin ƙabilarta yana da bambamci da garin maikironomada. Misali a wannan gari babu matsala saurayi ya rungumi budurwa, abinda basa yi a daular Wilbafos har sai bayan aure.
Armad da Zaikid suna zaune suna kallon abinda ke faruwa. Zaikid yaja dogon numfashi ya juyo ya kalli Armad yace, "tun daga wannan rana yarima Najunanu yake jira. Shekara bayan shekara, a duk shekara ya kan yiwa yayarka Hidaya sabuwar waka wadda zai raira tsahon shekara guda kafin wata shekarar ta zagayo ya samar da wata sabuwar waƙar ta bege." Zaikid ya juya ya nuna shata wanda ke kwance a gefe yana sauraransu. "Yarima ya sha ziyartar shata yasa ya rerawa Hidaya waka akan kuɗi mai tsadar gaske. Waƙoƙin da hatta aljanu sukan ɗauka su ringa rerawa matansu da ababen begensu.
"A sau da dama idan ka ziyarci babban birnin Maikironomada da daddare, ka samu dama ka matsa kusa da fada zaka juyo muryar yarima yana rera baitukan yabo, yana yabon siffofin Hidaya. Wani lokacin kuma ya yabi takobinta, wani lokacin ya yabi jarumtarta, kai a wasu lokutan ma ya kan shafe wata guda yana yabon gashin kanta. Shekara bayan shekara yarima yaci gaba da yabo babu gajiyawa.
"Wasu shekaru da suka wuce sarki Abbas ya nemi dole yarima yayi aure domin a samu magaji. Yarima ya dage Hidaya yake jira. Babu wata ƴar sarki da ba'a kai masa ba amma yaƙi. A dalilin haka sarki ya cire shi daga muƙaminsa na yarima mai jiran gado ya naɗa kaninsa yarima Umaru wanda tuni yayi aure ya haifi ƴaƴa uku. A yau idan Abbas ya mutu to yarima Umaru shi ne zai zama sarki.
"Ganin haka yasa zuciyar Hidaya tayi sanyi, tausayi ya kamata. Akwai lokuta da dama da tayi tunanin dawowa ta auri Najunanu. Tabbas da abin ta mutu a ranta. A kullum tana ganin ita ce sanadiyyar tarwatsewar al'amuransa. Kafin yaƙin sarakunan jinzidal Hidaya ta kai ziyara ta ƙarshe maikironomada. Zuwa tayi ta ganshi amma kuma ta kasa zuwa wajensa saboda kunya. Sai roƙon Abbas tayi da kada ya gaya masa tazo.
"A haka yarima yaci gaba da jira har Hidaya ta mutu bai samu ya cika burinsa na aurenta ba. Zan iya cewa a duk faɗin duniya babu wanda ya kai shi takaicin mutuwar Hidaya, harda kai kanka, domin soyayyar Hidaya da take cikin zuciyar yarima ta haura matakin bil'adama, har a tsakanin fararen aljanu ana zancenta. Har yanzu yarima yana nan da rai yana bege."
Armad yayi shiru yana tunani. Basu taɓa zancen da Hidaya ba. Wato yanzu yake gane Hidaya rumbun sirri ce. ALLAH ne kaɗai yasan ragowar abubuwan data ɓoye bata gaya masa ba.
"Shin ko kasan kana da wata yayar bayan Hidaya?" Inji Zaikid.
Armad ya haɗe gira. Kamar yaya? Tunda yake bai taɓa jin wannan zance ba. Hidaya bata taɓa faɗa ba, haka Zaikid da Fatima, duk babu wanda ya taɓa maganar. Sai dai kuma dama su ba gwanayen gaya masa abu bane.
"Ina da wata yayar fa kace?" Inji Armad.
Zaikid ya gyaɗa kai. "Eh kana da ita. Bari na nuna maka."
Ya saka hannu yayi gaba da hoton bidiyon zuwa gaba. A wannan rana Fatima ta fara naƙuda.
Taidara yana ta kai-komo a bakin dakin haihuwar. Kamar wanda kunama ta ciza ya kasa zaune ya kasa tsaye. Can dai ya kasa daurewa ya matsa kusa da ƙofar ya kwankwasa.
Kwan-kwan-kwan.
Tsohuwar mai karɓar haihuwar ta leƙo ta taga. "Ya akai?"
"Ehmm... ta haihu?" Inji Taidara.
Matar ta galla masa harara. "Wai kai baza ka bari muyi aikinmu ba? Ka dame mu, gashi yarinyar taka babba ce, kanta yaƙi fitowa amma kai ka hanamu sakat."
Taidara ya durkusa a ƙasa da sauri. "Yi haƙuri, yi haƙuri. Yi maza ki koma ki ci gaba da aiki, kinji?"
Matar taja dogon numfashi sannan ta koma ciki ta rufe tagar. Za kayi mamaki idan aka ce maka Taidara ya ƙara kwankwasa musu bayan minti ɗaya kacal, amma haka akai. Kai har sai da suka fusata suka daina buɗe masa. Yayi bugun har ya gaji. Daga ƙarshe ya fawwalawa ALLAH al'amuransa ya koma gefe ya zauna. Kwana guda cir Fatima tayi tana naƙuda kafin ta haihu.
Taidara yana zaune a bakin ƙofar yana zana hatiman sulkulle, wanda a cewarsa zasu ragewa Fatima radadin haihuwar, yaji an buɗe ƙofa. 'Masifaffiyar' tsohuwar wadda ya ƙuduri niyyar duk abinda ya samu matarsa ita zai kama ta leƙo da yarinya santaleliya a hannu.
Jiki na rawa ya miƙe ya karɓi yarinyar. Tana taɓa jikinsa ta fara kuka irin na jarirai. Taidara yayi sauri ya miƙa mata ita.
"Bana son naji ƴata tana kuka, yi maza ki saka ta daina kuka."
"Kai kukan lafiya ne," inji matar.
"Ko?"
Taidara ya rungume ƴarsa yaci gaba da yi mata wasa domin tayi shiru. Can bayan ƴan-dakiku ya tuno da babar yarinyar. Kai tsaye ya danna cikin ɗakin. Matan dake aiki suka tare shi.
"Kai, waye yace ka shigo?"
"Eye.." Taidara ya wangale baki. "Naga kun gama."
"Bamu gama ba, ka koma waje."
A lokacin suka haɗa ido da Fatima yaga tana murmushi. Yasan aikinta ne wannan. Amma haka ya haƙura ya koma.
Sai bayan awa guda suka bashi dama ya shiga ya gana da Fatima.
Abin alfaharin da uwar da yarinyar duk lafiyarsu kalau.
Akai suna cikin farin ciki aka sakawa yarinya suna Abijan.
Bayan haihuwar Abijan Taidara ya bayyanawa sarki yana so ya ɗauki matarsa su tafi doron ƙasa ta uku. Akwai wani kauye mai suna Kanyu. Anan yake so ya raini ƴarsa.
Da kyar sarki ya amince da hakan domin baya son rabuwa da Fatima. Yace zai haɗa musu tawaga a raka su amma Taidara ya dage babu buƙatar hakan.
Taidara, Fatima, Zaikid da Hidaya, da Abijan suka koma doron ƙasa ta uku. Wani abin daɗi kafin su ƙarasa sarki Abbas ya saka masu fasahar turbaya sun gina musu gidan da zasu zauna.
A lokacin babu wani sarki bisa doron ƙasa ta uku, babu Han'ibal. Zaka iya cewa duk Maikiro'Abbas shi ne yake mulki. Sai dai kuma saboda girman ƙasashen yasa baya iya sanin dukkan abinda yake faruwa a ko'ina. Irin wannan ƙananun ƙauyukan bai ma san dasu ba.
Su Fatima suka tare a sabon gidansu suka ci gaba da rayuwa cikin farin ciki. Zaka iya cewa abubuwa basu fara canjawa ba sai da akai shekara bakwai. Abijan ta fara bayyanar da wasu fasahai wanda suka sha banban da tunani.
Duk inda ta shiga sai kaga wajen ya canja launi. Haka kuma duk abinda ya kusanceta sai kaga ya canja. Watarana tana shigowa falo ta tarar da iyayenta suna ta ƙoƙarin share yana. Tana ɗora hannu akan bangon ɗakin gaba ɗayan yanar ta ɓace.
Tuni suka fuskanci Abijan tana da irin shigen fasahar Fatima. Sai dai kuma kash, yadda Taidara ya ɗauki abin ba haka Fatima ta ɗauka ba.
A nata ɓangaren Fatima bata ɗauki abin da ƙarfi ba, amma Taidara rikicewa yayi lokaci guda. Zaka iya cewa tunda yayiwa Abijan wasu gwaje-gwaje shikenan ya ajiye duk wani abu da yake yi ya koma koya mata fasaha. Babu rana, babu dare, kullum horo yake bata. Tun abin yana burge Fatima har ya fara bata tsoro. Kullum tambayar da take masa shi ne: saurin mai yake? Ya bi Abijan a hankali tunda yarinya ce. Sai dai kuma Abijan bata damu ba. Kullum ƙara azama take yi. Bayan awannin da suke yi da Taidara sai ta koma ta fara bin Hidaya tana ƙara koyon wasu abubuwan.
Zaikid bai taɓa nuna damuwarsa ba domin baya zama sosai a gidan. Yawancin lokuta zaka ganshi a kasuwa yana siyar da kayan izza, ko kuma a gona yana taya ƴan-kauyen noma.
Haka dai Fatima ta bawa kanta haƙuri tana ganin ba wani abu bane. Dole zasu yi su gaji.
Har Abijan ta cika shekaru sha-shida Taidara bai rage komai ba.
Watarana da daddare yazowa Fatima da wani labari.
"Ina son na ɗauke Abijan na tafi da ita," ya ce.
Fatima ta yamutse fuska. "Ban gane kana so ka ɗauke Abijan ka tafi da ita ba?"
"Kada ki damu, ta amince da kanta ba tursasata nayi ba," inji Taidara.
Fatima ta tashi zaune, fuska a yamutse. "Wai tsaya, ina zaku je kuma kwana nawa zaku yi?"
"Wajaje da dama, bani da masaniya akan kwana bawa zamu yi. Watakila ba lalle mu dawo a wannan zamani ba."
"A haba, ka daina wannan zancen," inji Fatima. "Ƴar tawa guda ɗaya kacal zaka shiga yawon duniya da ita? Bazai yiwu ba."
Ta tashi ta fice daga ɗakin. A lokacin ta kirawo Maikiro'Abbas da zaikid suka jawa Taidara kunne akan kada ya sake ya ɗauki Abijan. A cewarsu duk abinda yake shiryawa bai dace ya saka ƙaramar yarinya ba. Taidara yayi iyakacin ƙoƙarinsa a bashi dama yayi bayanin kansa amma Fatima ta dage bata son jin komai. A cewarta duk abinda zai faɗa ɓata mata rai zaiyi.
Hidaya bata ce komai ba. Zai yi wuya ka gane abinda take tunani. Abu guda data faɗawa Fatima shi ne fasahar Abijan tayi kama da fasahar babban sarki Kuyurussa'ayi. Hakan yasa Fatima ta tsorata sosai. Ta fara tunanin cewa wani babban abu Taidara yake kullawa.
Bacci ya fara kujewa Fatima. Kullum idonta yana kan Abijan. Kada ta rufe ido Taidara ya sace ta ya tafi da ita.
Amma hakan bata faru ba. Taidara yaci gaba da harkokin gabansa. Horon da yake bawa Abijan ya dawo gida domin kada yayi nisa da ita Fatima tayi tunanin zai gudu da ita.
Har dai Fatima ta sakko suka shirya da Taidara. Komai ya koma dai-dai. Watarana da safe Taidara ya tashi Fatima da wuri ya jata gonar daya fara yin shuka.
Armad yana ganin iyayensa cikin farin ciki da juna suna noma da irin fatanyar da. Bai san lokacin da kwalla ta fara zubo masa ba.
"Albishirin ka?" Inji Fatima.
"Goro."
"Fari ko ja?"
"Fari da ja."
Fatima ta rufe fuska cikin kunya.
"Menene? Ki faɗa min, kinga kin saka jinina ya fara hawa."
Fatima ta buɗe baki cikin kunya ta ce, "zamu samu wani yaron."
Tana faɗa ta wuce da gudu ta koma gida. Taidara yayi shiru yana kallonta har ta kule. Maimakon ya bita ya nuna farin cikinsa sai ya juya ya nufi gabas. Sai bayan kwana uku ya dawo. Ai kuwa Fatima ta dira masa masifa sabuwa. Da kyar ta sakko. Kai har sai da Maikiro'Abbas yazo ya sasanta. Ai dan me zai tafi bai zo yayi mata magana ba? Idan baya farin ciki da samun wani yaron ne to yayi magana.
Daga baya dai komai ya koma dai-dai. Sai dai kuma zaka iya cewa ba'a taɓa raba gidan Wilbafos da hatsaniya. Saura wata guda Fatima ta haihu, watarana da safe suna cin abinci, Abijan ta fara huci. Ga shi ita ba mai magana bace sosai saboda haka nan take hankalin kowa ya tashi.
"Ni fa wannan rayuwar bazan iya ta ba?" Inji Abijan. "Iyayenmu sun mulki doron ƙasa ta farko amma mu mun maƙale a wani ƙauye muna rayuwa. Wai bari na tambaye ku, meye shirin ku? Na tabbata bakwa nufin ku mutu anan, hakane?"
Kowa ya kasa haɗiye abincin dake bakinsa. Kallonta kawai suke yi. Taidara da Hidaya ne kaɗai basu nuna alamun kaɗuwa ba.
"Nima dai haka na gani," inji Taidara. "Ya kamata mu fara shiri."
Fatima ta harareshi. "Kaji ko? Dama nace kai kake koyawa ƴata irin wannan abubuwan. To mai zamu yi? Kana so mu mutu ne? Kakanmu Eyriyon ya kasa, kai mai kake tunanin zaka iya?"
"Mun san dalilin da yasa Eyriyon baiyi nasara ba," inji Hidaya. "Fasahar duniya ce. Kuma yanzu Abijan tana da wannan fasaha. Za'a iya samun banbanci da wancan lokaci."
Fatima ta juyo wajen da Hidaya take zaune. "Har dake? Yau kuma shigar masa zaki yi? Keda nake ganin kina da hankali!"
"A'a, ba shigar masa zanyi ba, mama, kawai dai ina ganin ya kamata mu fara shiri koda iyakacin mu huɗun nan ne. Ururu baza su taɓa barin mu haka kawai ba. A kullum suna shirya mana sharri, mai zai hana mu shirya musu irin namu sharrin? Ko babu komai zamu zama cikin shiri idan sun kawo farmaki."
Fatima ta juya wajen Zaikid. "Dattijo, kai ka yadda da wannan maganar banzan?"
Zaikid ya kaɗa kafaɗa. "Mai zai hana? Shiri ai bazai zamo illa ba?"
Fatima ta tashi ta fice daga falon. Ita zaman lafiya take so. Rayuwar faɗa da yaƙi bata dace da mace mai haihuwa ba. Da ace irin wannan rayuwar take so da babu yadda za'ai tayi aure har ma ta haifi ɗa. Kuma dole baza ta bari ayi wani tashin hankali da zai kashe mata ƴaƴanta ba.
Comments
Post a Comment