Skip to main content

297-300

 Armad da Nostaljiya na tsaye a gefen titi. Wata budurwa ƴar kimanin shekaru bakwai na tsaye a gaban su tana kallon ƙasa. Armad dai na sanye da jar riga yar-shara da baƙin wando. Tambarin Miyura na ɗamfare a goshin sa, sannan kuma, kamar kullum, idanun sa na hagu a rufe da audugar jamsiƙa. Ita kuwa Nostaljiya na sanye farar riga doguwa. Kanta babu ɗan-kwali tayadda gashin kan nata ya kwanto gadon bayanta. Duk inda ta motsa sai kaga gashin yana yalali yana haske abin sha'awa da ƙawa. Fatar jikin ta, kamar kullum, haske take bayarwa a duk sanda rana ta haska. 


Amma duk wanda ya lura sosai zai gane cewa babban abin jan hankali shi ne wannan budurwa dake gaban su Armad tana kallon ƙasa. Rigar jikin ta baƙa ce dunɗum. Fatar ta ja ce jajawur kamar gashin kanta. Idanun ta kuwa wasu iri ne, maimakon alamar baƙin ido dake tsakiyar idon kowa ita takobin ce a tsakiyar idon ta. Kai hatta idon nata samfurin takobi ne - a fiƙe yake yake kallon doron ƙasa ta farko yanai mata izgili. Wani abin mamaki shi ne duk da wannan irin baƙuwar siffa ta wannan budurwa amma kyakkyawa ce, kuma ragowar jikin ta irin na mutane ne idan kaɗauke cewa hannayen ta guda shida ne. Dukkan hannayen shida ta kafaɗa ɗaya suka fita. Lallai wannan budurwa nada ban mamaki. Ko a ina Armad da Nostaljiya suka samo ta?


Suna tsaye Armad ya nuna bishiyun dake jere a gefen titin, ya ce, "Nostee, a ganin ki da bishiyar dabino data giginya wacce taɗi daɗewa a duniya?"


Nostaljiya ta ɗanyi shiru cikin tunani kafin ta ɗago kai ta ce, "giginya mana. Ai giginya tafi daɗewa."


"Wannan son kai ne." Inji Armad. "Kawai sabida giginya mace ce shi yasa zaki ce ita, amma ai dabino yafi daɗewa. Baki ji ana cewa 'kayi shekaru kamar na dabino ba'? Ai sabida daɗewar da dabino yake yi. Wataƙila wannan dabinon da kike gani kakannin-kakannin su ne suka shuka."


Nostaljiya tayi jim kamar ta yadda, amma daga bisani ta girgiza kai. "Da gaske giginya tafi."


Armad yayi murmushi ya rabu da ita ya juyo kan budurwar dake tare dasu. "Saif-al-barzak, nuna mana hanya."


Budurwar ta gyaɗa kai ta shige gaba ba tare da cewa uffan ba. Armad da Nostaljiya suka bita a baya. 


Suna cikin tafiya a gefen titin Nostlajiya ta juyo ta dubi Armad ta ce, "Wai ina ka tura Nazara, baka cemin komai ba?"


"Nazara kwamanda ne mai zaman kan sa. Ina ganin zaifi kyau mu ringa kallon alaƙar mu dashi a matsayin haɗaka da taimakon juna saɓanin alaƙar ɗa da ubangidan sa."


Nostaljiya ta karkata kai tana tunani na ɗan lokaci kafin daga bisani ta gyaɗa kai. "Hakane. Tun farko tun ma kafin yazo wajen mu yana da shirin sa na musamman. Da ace shi wani mai girman kan ne da bai zo ba, domin kuwa yana da rundunar sa mai zaman kanta. Kuma zaka iya cewa shirin sa yama fi namu daɗewa duba ga shekarun sa da kuma alaƙar sa da Nusi."


"Hakane. Shi yasa nake tunanin shi zan haɗa da Bihanzin idan anzo faɗan ƙarshe. Akwai ƙiyayya a tsakanin su sannan kuma duk shirin sa akan Bihanzin yake. Koda bazai iya cin galaba akan sa ba zai iya riƙe mana shi zuwa sanda zamu gama da Ikenga. Sarkin-sarki ce zata zama matsala domin har yanzu ban san wanda zan haɗa da ita ba."


"Gani. Meye amfani na?"


Armad yaja ya tsaya tare da juyowa ya kalle ta. "Ke kuma?"


"Eh mana."


"Kina tunanin zan barki ki fafata da tsohuwar mayya wadda take kan Allon Izza? Macen da tafi kowacce mace ƙarfi a ƙasashen ƙasa?"


"To, Armanos, meye amfani na idan ban bada gudummawa ta ba? Idan fa muka rasa wannan yaƙi akai galaba akan mu to dani dakai duk mun halaka. Meye amfanin na zauna a gida ina jira bayan kuma akwai gudummawar da zan iya bayarwa? Kai ma kasan bazan zauna ba. Na rantse da mahaliccin ƙasa bakwai duk inda kasa ƙafa nima nan zan saka."


Armad ya buɗe baki zaiyi magana amma ya fasa. Bayan ɗan-lokaci ya numfasa ya ce, "mu tara ne. Da son samu ne kowa acikin mu ya zama ya haɗa rundunar sa tasa ta kan sa kafin yaƙin ƙarshe. To amma hakan zaiyi wuya. Ba kowa ne yake iya haɗa mutane yasa su bishi ba."


Nostaljiya tayi dariya. "Samun mutane masu baiwar sarrafa tunani nada wahala, amma zan gwada. Wataƙila idan naci sa'a na samu."


A dai-dai wannan lokaci budurwar da Armad ya kira da Saif-al-barzak ta juyo ta dube su ta ce, "anzo." Tana nuni izuwa katafaren ginin fadar garin Seerisha wanda ke tsaye gaban su.


"Munzo, Armanos."


Armad yayi murmushi tare da zira hannu a aljihu zai zaro wani abu, amma a lokacin ya tuno cewa babu komai a aljuhun nasa. Budurwar mai suna Saif-al-barzak ta cuno baki ta dubi Armad ta ce, "yana waje na fa." 


"Au, na manta." 


Yarinyar ta cire hular fulanin dake kanta. Take wani dunƙulen haske ya faɗo daga cikin hular, yana fitowa ya juye izuwa ɗan-mudubi madaidaici wanda dukkanin fuskokin sa hoto suke bayarwa (wato dai bashi da gaba). Armad ya karɓi mudubin ya saka a aljihu. Su ukun suka nufi ƙofar fadar gadan-gadan.


Suna isa masu-gadin suka juyo suka kalle su, suka ƙare musu kallo tsahon daƙiƙu kafin daga bisani su ɗauke idon su su koma kan abinda suke yi (wato caca ba).


Suna shiga suka tadda katoton soro wanda girman sa yakai zira'i dubu maitan. Armad baya ganin ƙarshen sa ko ƙaɗan. Saman soron a rufe yake da wani gilashi mai haske wanda ana iya ganin gajimare ta ciki. A kowanne ɗan taƙi ma'aikata ne tsaye da makamai cikin shirin yaƙi suna sanye da sulke sannan suna riƙe da masu dogaye a hannayen su. Armad da Nostaljiya suka wuce kan su tsaye cikin soron. Duk sanda suka gifta sai kaga ma'aikatan sun ɗago kai sun kalle su sannan su kauda kai kamar basu gan su ba. A haka har suka kai ƙarshe. 


Suna fita suka tadda wani ƙaton lambu a dama da hauni cike da bishiyu iri-iri da ƴaƴan itatuwa. Akwai wata ƴar-siririyar hanya a tsakiyar lambun wadda ta wuce ta cikin lambun har zuwa cikin fadar. Su  ukun suka bi ta wannan hanya suka isa cikin fadar. 


Abu na farko da suka tarar shi ne wani ɗan ƙaramin gari wanda yafi girman garin su Armad. Akwai manyan gine-gine guda huɗu a tsakiyar garin, akan kowanne akwai suna. Na farkon an saka Deniz Yabulu, na biyun an sa Deniz Wuyawuya, na ukun an saka Deniz Yudusu, sai kuma na ƙarshe an saka Deniz Curucuru. Kowannen su akwai mutane da matakan tsaro aciki kowa yana harkokin gaban sa. Duk wanda wani ya gansu sai kaga ya ɗauke kai kamar bai gan su ba. 


"Zuri'ar ƴaƴan Deniz Huhutu guda huɗu kenan, kowanne da nasa gidan." Inji Saif-al-barzak.


Daga nan suka wuce izuwa sashi na gaba acikin wannan fada. A wannan sashin babu komai sai filayen karɓar horo ana ta atisaye. Kowanne fili an zagaye shi da katangar gilashi tayadda ana iya hango abinda ke ciki. Har zasu wuce Saif-al-barzak ta nuna ɗaya daga cikin filayen wanda ke can baya ta ce, "ga Deniz Bizaya can acikin fili na uku." 


"To mai zamu yi masa?" Inji Nostaljiya. 


Armad ya girgiza kai. "Nostee, zanso naga wanne irin Deba ne."


Nostaljiya ta tafa hannu inda nan take suka ɓace daga inda suke suka bayyana acikin fili na uku a gaban Bizaya. 


Bizaya kwata-kwata bai lura da zuwan su ba. Gashi dai yana ganin su amma kuma ya kasa tantance su waye. Idan ka tambayi Bizaya zai gayamaka yasan su Armad ne a gaban sa to amma a lokaci guda ruhin sa da kwakwalwar sa suna gayamasa babu matsala. Suna gayamasa cewa kasancewar su Armad a wajen dai-dai ne kuma haka ya kamata. A wajen sa rashin ganin su a wajen shi ne matsalar. To fa, kaji wani sabon al'amari. Shin wannan ko wacce irin izza ce take aiki akan Bizaya?


Bizaya na nan kamar yadda aka sanshi: gajere mai faffaɗar fuska da kafaɗa. Yana da hasken fata ga kuma yawan gashin gira. Banbancin wannan Bizayan da wanda aka gani a gasar Jinzidal shi ne nutsuwa. Wato akwai nutsuwa wadda ake samu ta hanyar izza a fuskar wannan Bizayan saɓanin wancan na da. Idanun sa akwai kafiya irin wadda takai taja hankalin Armad. 


Armad ya dubi Nostaljiya cikin tsokana ya ce, "Deba manya. Shima tsohon saurayin ki fa ya shiga Deba." 


Nostaljiya ta harare shi. "Saurayi na kuma?" Take ta juya ta fice daga wajen tana huci tabar Armad da Saif-al-barzak a tsaye a gaban Bizaya.


Armad ya ƙara duban Bizaya. Wato shekaru sunja daga wancan lokacin zuwa yanzu, amma abubuwan da suka faru a tsahon wannan lokaci sun ma fi lokacin yawa. Armad yana tuno sanda suka haɗu da Bizaya a garin Sisiya a sanda Bizaya da baban sa Iluru suka zo neman auren Nostaljiya shi kuma Armad ya dawo daga neman Nusi. 


"A yanzu ma zamu iya yi masa aiki idan kana so." Inji Saif-al-barzak.


Armad ya girgiza kai. "Da sauran lokaci."


"Kullum haka kake cewa. Mu kashe su kawai. Mu kashe kowa da komai da duk wani abu mai numfashi har sai ya rage babu kowa sai mu kaɗai." Saif na magana tana lashe baki. Idan ka lura zaka fuskanci cewa harshen Saif shima samfurin takobi ne.


"Sauran ƙiris, Saif, sauran ƙiris. Ƙara haƙuri, Saif."


Saif ta ɗan haɗe gira alamun rashin jin-ɗaɗi amma daga baya ta saki fuska. 


Armad da Saif suka juya suka bi bayan Nostaljiya cikin fadar.


Ba jimawa suka bayyana a tsakiyar wannan fada. Daga inda suke suna hangen sashin sarki Iluru an kewaye shi da manyan bishiyun tsamiya (kasan tsamiya da ɗaukan sihiri), suna kuma hango sashin matar sarki Iluru da kuma sashin ɗan sa Bizaya. Suna zuwa wajen Nostaljiya ta tsaya tana dube-dube. 


"Iyakacin abinda Ulbaru ya sani kenan. Akwai yiwuwar bai taɓa shiga sashin Iluru ba." Inji Nostaljiya.


Armad ya ɗan ɓata rai kafin daga bisani ya ce, "hakan ma yayi. Katse."


Yana rufe baki duniya tayi hatsa-hatsa sannan komai ya ɗauke ɗif.


*** 


Armad na zaune acikin ɗakin su na otal, Nostaljiya na kishingiɗe a jikin sa ta ɗora hannu ɗaya akan wani mutun wanda ke zaune a ƙasa a sume, hannu ɗaya kuma akan Armad. Nusi, Cokali, Inara da Lamarudu na tsaye sun kewaye wannan mutun da Nostaljiya ta ɗora hannu akan sa. Idan ka lura sosai zaka fuskanci wannan mutun ba kowa bane illa sarkin ƙofa Ulbaru wanda Iluru yasa ya kamo su Armad. 


Ko mai yake faruwa a wajen nan?


*Bayanin sai mun koma baya kimanin minti talatin.*


Armad, Nusi, Nostaljiya, Inara da Lamarudu na tsaye a bakin wani shago acikin babbar kasuwar garin. Duk da halin da garin ke ciki akwai mutane acikin wannan kasuwa, kuma zaka iya cewa koda su Armad basu rufe fuskokin su da rawani ba ba lallai wani ya gane su ba. Amma sabida tsaro kowannen su ya nannaɗe fuskar sa da rawani.


Suna tsaye sai ga Cokali ya fito daga cikin shagon riƙe da takardu a hannu. Yana zuwa ya gyaɗa musu kai alamun an dace sannan suka juya suka shiga cikin kasuwar. 


Nusi da Cokali suka nufi shagon siyar da kayan abinci; Inara, Lamarudu da Nostaljiya suka nufi wajen siyar da kayan sawa; shi kuwa Armad babban shagon siyarda takobi na garin ya nufa. 


Wannan shago acike yake da takubba, masu da kibbau, kai dama wasu samfurin makaman na musamman irin su ƙososhi, fafalon yara, zarto, da dai sauran su. 


Armad ya zarce kai tsaye wajen da aka jere takubba akan wata ƙatuwar kanta. Zaka iya raba takubban gida uku: akwai takubban tarihi, akwai ƙerarrun takubban, akwai kuma takubban sihiri. Abin mamakin shi ne kowacce takobi da sunan ta. 


"Wacce kake so?" Mai shagon ya tambayi Armad. 


Armad yayi jim kafin ya ce, "wacce tafi kowacce tsada da tarihi?"


Mai shagon ya kalli Armad sama da ƙasa kafin ya nuna takobi ta farko a jerin takubban tarihi. "Wannan ita ce Saif-al-ƙisas - takobin yaƙi. Shekarar ta wajen ɗari a shagon nan amma babu wani mahaluƙi daya taɓa iya zaro ta daga cikin kufen ta." Mai shagon ya matso kusa tare da sauke murya ƙasa-ƙasa ya ce, "kakana Deniz Kansulu ya labartawa mahaifina Deniz Andululu cewa wannan takobi nada alaƙa da babban sarki Huhutu."


Armad ya haɗe gira cikin mamaki. "Sarki Huhutu?"


Mai shagon ya gyaɗa kai. "Eh mana. Kayi ƙanƙanta sosai kasan waye sarki Huhutu."


Armad ya ɗago kai ya ƙara kallon mai shagon. A ƙiyasin sa mutumin zai iya kaiwa shekaru arba'in zuwa arba'in da biyar. Yana da furfura wadda wataƙila ta wahala ce duba ga cewa shekarun sa basu kai yayi furfura haka ba. Izzar sa shekaru sittin ce kacal. 


Mutumin yaci gaba da cewa, "akwai lokacin da duk duniya tana ƙarƙashin daular denizawa kuma sarki Huhutu shi ne yake mulkar ta. Mutuwar sarki Huhutu shi ne abinda yasa martabar denizawa tayi ƙasa. Amma duk sanda magajin sa ya bayyana zamu dawo da martabar mu ta asali. To kaga idan ka sayi Saif-al-ƙisas akwai yiwuwar kai zaka zamo Magajin Huhutu. Meye yafi wannan daɗi? Ace ka tashi daga gama-garin mutun zuwa magajin mutun mafi daraja."


Armad yayi shiru yana sauraran wannan mutun. Wataƙila duk daɗin baki ne kawai irin na ƴan kasuwa, amma duk da haka akwai abinda ya ɗau hankalin Armad akan wannan takobi. "Idan na fahimta dai-dai wannan sarkin na yanzu yana da alaƙa da sarki Huhutu, idan kuwa haka ne ya za'ai ya bar takobin magabantan sa anan? A gani na kamata yayi ace ya killace ta a kusa dashi."


Mutumin yayi murmushi. "Tunani mai kyau, yaro. Amma ka manta tarihi yazo cewa sarki Huhutu ya rabar da duk abinda ya mallaka kafin ya mutu? Kuma ya haramtawa zuri'ar sa kwace wannan abubuwa daya rabar kafin mutuwar sa?"


Armad ya haɗe gira cikin mamaki. Bai san wannan tarihin ba. Da sauri ya miƙa hannu ya damƙi takobin mai suna Saif-al-ƙisas domin ganewa idon sa irin izzar dake cikin ta. 


Mai shagon yai sauri zai tsayar dashi amma ina, kafin ya ƙifta ido Armad ya isa ga takobin, saurin ba ɗaya ba. 


"Kada ka taɓa ta da garaje tana ƙuna kamar wuta. Kuma kamar yadda na gayamaka baza ka iya zare ta daga cikin kufenta ba, domin kuwa acikin shekarun nan ɗari babu wanda ya iya yin hakan....."


Tun kafin ya rufe baki Armad ya damƙi mariƙin Saif-al-ƙisas sannan cikin kwanciyar hankali ya zare ta. 


Jan ƙarfe ne, siriri, kaifi biyu. Tsayin ta yakai zira'i bakwai, faɗi zira'i ɗaya. Akwai zanen hatimi a fuska ɗaya da kuma wani rubutu guda ɗaya a ɗaya fuskar wanda aka rubuta da wani yare da hatta Armad bai sani ba. 


Kafin Armad ya ankara takobin ta fara haske. Hoton rana ya bayyana akan tsinin takobin. Abu kamar wasa ranar ta fara girma, kamu ɗaya, kamu biyu, kamu uku, kamu uku....


Kafin Armad ya ankara ranar takai zira'i goma. Takobin tai fitar burtu ta fizge daga hannun sa, sannan a wani salo mai ban al'ajabi ta juyo ta kawo masa sara. 


Armad na tsaye bai motsa ba har saida takobin tazo dai-dai saitin wuyan sa sannan ya miƙa hannu ya damƙi jan ƙarfen takobin hankali kwance kamar wanda ya riƙe alƙalami, sannan ya ƙara damƙar mariƙin da ɗayan hannun ya yarfe ta ƙasa ya maida ita cikin kufen ta kamar wanda yake yiwa yaro ladabi. 


Duk abinda ya faru ya ɗau lokaci wajen bayani amma a zahiri bai wuce rabin daƙiƙa ba, musamman duba ga irin saurin da Armad ya isa ga takobin. 


Armad ya jujjuya takobin a hannun sa na ƴan mintuna sannan ya miƙa ta ga mai-shagon wanda ke tsaye baki buɗe ya kasa cewa komai.


Armad yayi murmushi sannan ya juya nufi hanyar fita. Har yakai bakin ƙofa ya juyo ya dubi mai-shagon ya ce, "bil-adaman da suka kai waadin Deba suna yin aure uku a rayuwar su: aure na farko suna aurar mace bil-adama; na biyu suna aurar aljana; na uku suna aurar takobi. Na riga na auri takobi babbar takobi dana gwada wannan takobin taka." Yana rufe baki bai tsaya jiran amsa ba ya juya ya fice. Shi kuwa mai-shagon na tsaye ya ƙame ƙam baya ko motsi. Lallai yau ya samu labarin bayarwa zuwa shekaru masu zuwa. Matsalar kawai baiga fuskar Armad ba. A nasa hasashen Armad muridin aljani ne ko kuma wani tsohon rauhani abin girmamawa a tsakanin shaiɗanu.


Armad na fitowa ya tarar dasu Nusi da Nostaljiya suna jiran sa a ƙofar shagon. Take ya ɗebe su ya mayar dasu inda suka fito. Buɗe ido kawai sukai suka gan su a ɗakin su na otal.


Nusi ta harari Armad. "Armad! Na gayamaka ka ringa sanar damu kafin kayi wannan abin." Tana rufe baki ta zarce izuwa banɗaki tana huci.


"Au, na manta." 


Suka fashe da dariya. 


"Tana ƙarama bata da tsoro." Inji Cokali. 


"Girma ne yazo mata." Inji Nostaljiya.


***


Bayan sun ɗan huta daga gajiyar kasuwa aka dawo kan teburin tattaunawa. Cokali ya kawo musu taswirar garin da kuma ta kewayen fadar garin domin suga ta ina zasu ɓullowa sato sarki Iluru. 


Amma kafin a fara suka ga Armad ya ɗaga kai sama ya nuna tagar dake saitin sa da ɗan-yatsa.


"Mene ne kuma?" Inji Cokali.


"Mutun ɗari biyu da goma." Inji Armad.


"Mutun ɗari biyu da goma?" 


"Eh, ina jin mu suke nema. Ya kamata muje mu gaisa." Inji Armad.


Nostaljiya tayi farat ta tare Armad wanda ke ƙoƙarin miƙewa. "A'a fa, Armanos, indai ba so kake kowa yasan munzo ba ka kyale su."


Nusi ta gyaɗa kai. "Nostaljiya bata fiya faɗar gaskiya ba amma dai yanzu na yadda da ita. Armad ka rabu dasu kawai. Ba lallai su gano inda muke ba ma."


Cokali, Inara da Lamarudu suka gyaɗa kai alamun amincewa. Armad ya rabu dasu ya koma ya zauna aka ci gaba da tattaunawa. 


*Bayan awa guda*


Suna zaune kwatsam sai suka ji ana buga ƙofa. 


*Kwan*kwan.*kwan.*


Nan take suka fara kallon-kallo. Kowa na ƙoƙarin gano mai yake faruwa. 


Armad ne ya fara yin magana. "Su ne."


"Su wa kenan?"


"Wanda suke neman mu mana. Mutun ɗari biyu da goman dana gaya muku ɗazu."


Nan take ɗakin yai tsit kowa ya zare ido yana kallon Armad baki buɗe. 


"Cokali, ayi musu aiki. Ka bar mutun ɗaya a raye."


Cokali ya miƙe kai tsaye ya nufi bakin ƙofa. Yana buɗe ƙofar ya tarar da mutun biyu cikin koren sulke suna ƙoƙarin buɗe ƙofar. Ganin sa yasa suka jada baya cikin tsoro (kwata-kwata basu yi tsammanin ganin Cokali ba), amma abinka da tsoffin ma'abota izza, kan kace meye wannan sun dawo hayyacin su sun fara ƙoƙarin danne Cokali dan kada yayi ihu ya fallasa su. 


A nasa ɓangaren Cokali littafin marubutan farko ya buɗe ya fara rubutu.


*

Fari, ƙafa huɗu da rabi, ƙwalƙwal.

*

Wankan tarwaɗa, ƙafa uku, bille uku a ɓarin hagu.

*


Koda kammala rubutun sai waɗannan mutun biyu suka ga jikin su ya fara narkewa izuwa dunƙulen haske. Babu jini babu zafi amma komai nasu ya zagwanye izuwa haske. Suka buɗe baki zasu yi ihu amma babu abinda ya fito daga bakin sai iska, domin kuwa tuni sun zama haske. Hasken ya tashi ya shige littafin Cokali. Hotunan waɗannan mutane ya bayyana akan shafi na arba'in da huɗu na wannan littafi.


Ganin haka ba shiri ragowar mutun ɗari biyu da takwas ɗin dake ɓoye suka fito suka afkawa Cokali. 


Abin mamaki kawai sai Cokali ya juya a guje ya koma cikin ɗakin ya ƙullo ƙofa. 


Yana isa gaban Armad ya zube yana haki. Bayan ya nutsu ya nunawa Armad hotunan mutanen biyu daya halaka sannan ya ɗora da cewa, "amma waɗancan sunyi min yawa, Armad, littafi na ma ya kusa cika." 


Nusi ta fashe da dariya. "Mai hali baya canja halin sa, wai kai Cokali yaushe zaka zama jarumi ne?"


Cokali ya yamutse fuska. "Nusi, karfa ki manta ni na fara afkawa waɗancan deba huɗu da muka tarar a garin Jekis. Akwai jarumtar data wuce wannan?"


"Cokali yayi ƙoƙari." Inji Armad. "Fasahar sa tafi amfani wajen yaƙin ɗaya-da-ɗaya. A yaƙi irin wannan Inara zai fi taka rawa."


Ai kuwa kafin Armad ya rufe baki, Inara ya fice daga ɗakin ya isa wajen mutanen dake waje. 


Yana zuwa ya dunƙule hannu ya daki iska.


"Hannun-aradu!"


Dunƙulen hannun walƙiya ya bayyana akan iska ya daki abokan gabar su. Wutar walƙiya tayi sama tana ruruwa. Sai da ta shafe mintuna uku tana balbali kafin ta lafa. Bayan komai ya lafa babu wani ragowar mai numfashi sai mutun ɗaya - sarkin ƙofa Ulbaru.


Inara ya dawo cikin ɗakin riƙe da Ulbaru a sume. Ragowar mutun ɗari biyu da ɗoriya dake tare da Ulbaru sun daɗe a lahira. 


Inara ya gabato ya ajiye Ulbaru a gaban Armad sannan ya nemi waje ya zauna. Jikin Ulbaru babu abinda yake sai warin ƙuna da ƙonannen gashin jikin sa da walƙiyar ta narka.


Nostaljiya ta balbale Inara da faɗa. "Wai ku meye matsalar ku? Naji bakwa tsoron kowa to amma ya kamata komai ayi shi cikin hankali da lumana ba tare kun jawo kowa yasan munzo ba. Wannan rugugin aradun ai kowa yasan munzo." 


Nusi ta ɗora da cewa, "kuma fa ba kowa zaku ringa kashewa ba. Akwai wanda basu cancanci kisa ba."


Inara da Cokali suka kalli juna sannan suka juya suka kalli Armad suna jira suji mai zai ce. 


Bayan kimanin daƙiƙa goma Armad ya numfasa ya ce, "duk wanda ya ɗaga makami zai kashe mu na halatta jinin sa. Amma idan mutun bai ɗau makami ba kada a cutar dashi. Kamar yadda idan ka kashe mutumin da ya ɗau makami ya hauro gidan ka to ka kashe banza, to muma mun kashe banza indai ka ɗau makami kazo yaƙar mu. Amma ya kamata duk fasahar da za'ai amfani da ita ayi da ƙarama kamar irin su Hannun-aradu. Bana so su farga munzo garin kafin mu gano inda ƴaƴan Huhutu suke."


Maimakon amsar Armad ta kwantar musu da hankali juyowa sukai suka kalleshi a fusace. Wai meye nufin Armad ne? Yana nufin Hannun-aradu ƙaramar fasaha ce? To wace fasahar yake sawa a layin manya kenan?


Kafin su fara damun sa da tambaya ya dubi Nostaljiya ya ce, "nuna min fasahar ki akan sa." Ya nuna Ulbaru wanda ke kwance ƙasa a sume.


Cikin farin ciki Nostaljiya ta ɗora hannunta ɗaya kan Ulbaru sannan ta ɗora ɗayan kan Armad. 


"Ka shirya?"


Armad ya gyaɗa kai alamun ya shirya. Take duniya tayi hatsa-hatsa sannan komai ya ɗauke ɗif. Armad na buɗe ido ya ganshi a gefen titi tare da Nostaljiya da Saif-al-Barzak suna tsaye jikin wasu bishiyun dabino dana giginya. 


"Nostee, kin ƙara kwarewa sama da yadda na gani a duniyar aljanu. Kalli garin yadda ya fito sosai kamar na gaske."


"Ai baka ga komai ba, Armanos. Kaga dai na farko ina iya karanta tunanin Ulbaru da ilmin sa na wannan gari - duk wani titi, saƙo da loko daya sani nima zan sani. Da wannan ilmi nayi amfani na haɗa wannan garin da kake gani. Zan iya ɗakko duk wani abu dake cikin kwakwalwar sa na saka. Kamar yadda zaka gani na haɗa fadar garin kamar yadda Ulbaru ya santa. Kaga ta haka zamu ga duk wani sirri dake cikin fadar tayadda idan muka tashi shiga baza mu sha wahala ba domin kuwa mun san hanya."


"Eh to, kinyi ƙoƙari amma duk da haka dai baza ki shiga yaƙin nan ba. Kada ki manta kina ɗauke da juna-biyu."


"Armanos, ko juna-huɗu ne dani sai na shiga yaƙin nan. Ƙafarka-ƙafata."


Armad ya yamutse fuska amma baice komai ba. 


Da haka Armad, Nostaljiya da Saif-al-barzak suka rankaya cikin garin zuwa fadar sarki Iluru acikin shirin su na leken asiri. 


Wannan shi ne abinda ya faru. 


Idan muka dawo wannan lokaci kuwa, Armad da muƙarraban sa sun ɗan leƙa cikin fadar Iluru kuma sunga fasalin ta. Abinda ya rage shi ne a fara aiki.


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...