Skip to main content

BABI NA 90-99: Shiga Fada

 Babi na 90: Sa'a ko ƙaddara


"Ɗakko shi." kyaftin Bisaiya ya umarci ma'aikacin dake gefensa daya ɗakko gangar jikin wannan saurayi dake yawo akan ruwa.


Ba jimawa aka shiga da wannan saurayi cikin ɗakin duba marasa lafiya na jirgin tare da kirawo wani siririn mutun sanye da fararen kaya ya dubashi. Idan kayi duba izuwa wannan saurayi zaka ga ba wani bane illa Armad Wilbafos. 


Shi kansa kyaftin Bisaiya bai san mai yasa ya ceto shi ba, duk da kuwa yana tunanin ƴan fashi. Amma koda yaga Armad sai ya zare ido cikin mamaki tare da fara tunanin mai ya kamata yayi. 


Abin mamaki duk da Armad na numfashi amma sun kasa farkar dashi. 


"Ransa yana hannun ALLAH. Amma tashinsa zaiyi wahala." Likitan ya bayyana wa kyaftin Bisaiya bayan yayi iya yinsa ya kasa.


A kwana a tashi saida Armad yai sati ɗaya cir a sume kafin ya farka. Bayan ya buɗe ido ya fara ganin dishi-dishi kafin daga bisani ya warware ya fara jin surutan fasinjojin jirgin suna tattauna rayuwa.


Armad ya daddagira ya sakko daga kan gadon inda ya nufi bakin ƙofa. Jikinsa na nan yadda yake babu gajiya ko tsami. Yana isa ya buɗe ƙofar, hasken rana ya haske masa ido lamarinda yasa ya kare da hannunsa. Iska mai ɗumi ta daki fuskarsa lamarinda ya gano lallai ya rabida wancan sanyi da ƙanƙara na cikin kurkuku. 


"Kunga ya farka... "


"Ashe zai rayu.."


"Yana da ƙarfin ruhi..."


"Kai yaushe rabon da naga wanda yai sati a sume kuma ya rayu.."


"Ko maiya sameshi?"


Haka dai Armad ya fara tsintar maganganu fasinjojin daga nesa. Ga dukkan alamu kowa ya san da zuwansa. Armad ya gano cewa ɗakin cin abinci ya buɗe bayanda ya fuskanci cewa jama'ar na zaune a zagaye da tebura na abinci.


"Koma ka kwanta karka faɗi.." Likitan jirgin ya tallafi Armad ta gefe. Abinda bai sani ba shi ne Armad tar yake jinsa kamar ya rungumi zaki. Juyewar jikinsa izuwa walƙiya yana bashi damar shanye gajiya da ciwo cikin ƙanƙanin lokaci. 


Armad ya dubi likitan ya ce, "Ehmm... Nagode amma naji sauƙi. A ina nake?"


Likitan ya amsa da cewa, "kana cikin jirgin Fataken-dare, muna hanyar zuwa doron ƙasa ta huɗu daular Sisiya." 


Armad najin wannan jawabi yai murmushi tare da cewa, "Sa'a ko ƙaddara?"


Likitan bai gane mai Armad ya ce ba saboda haka ya tambaya, "Sa'a ko ƙaddara? Mai kake nufi?"


Armad ya amsa da cewa, "Ba komai. Kawai dai nima hanyar Sisiya nayi, ban sani ba ko zaku taimaka ku isar dani domin bani da ko sisi tare dani amma idan muka isa akwai wacca zata ranta min na biya ku."


Koda jin wannan batu sai Bisaiya ya taso a fusace, "Da kuɗinka nake buƙata da ban ceto ka ba. Kai dai kawai ka samu sauƙi kurum."


Armad na ganin Bisaiya ya gane shi ne kyaftin din wannan jirgi. Saboda haka yai shiru yana kai-komo da karamcin da Bisaiya yake nuna masa a zuciyarsa kafin ya kyaɗa kai cikin murmushi yana godiya. "Nagode."


"Zo ga abinci." Bisaiya ya kira Armad izuwa teburinsa. 


Tuwo da nama haɗe da kifi soyayye sune cike a kwanon da aka turowa Armad. Cikin annushuwa ya fara danna tuwon nan yana korawa da sanyayyar fura samfurin daular Sisiya. Kowa idonsa na kansa amma ko a jikinsa. Kan kace meye wannan tuni ya gama da kwanukan dake gabansa. 


"Bari a ƙaro ma, lallai yunwa kake ji." Bisaiya yai odar wasu kwanukan. Armad baice a'a ba, koba komai baya so mutanen wannan jirgi su fara yi masa kallon aljani wanda baya buƙatar abinci. 


Bayan ya ci ya sha sai Bisaiya ya kaishi wani ɗaki domin ya huta. "Ga ɗakinka kafin mu ƙarasa. A lissafi na nanda sati biyu zuwa uku zamu isa."


Armad yai godiya, har ya doshi ɗakin saiya waiwayo ya dubi Bisaiya yana cewa, "baza ka tambaye ni daga ina na fito ba. Baka tsoron ɓarayin ruwa ko kuma na jawo muku wata matsalar?"


Bisaiya yai murmushi, "Tuni nasan ko kai waye, Armad Wilbafos. Amma ka kwantar da hankalin ka babu wanda ya gane ka acikin fasinjoji na."


Nan take Armad yaja da baya ido a zare yana cewa, "mai kake nufi? Ya akai kasan suna na?"


Bisaiya ya kada baki ya ce, "Kada ka manta hotunan ka sun baza ko'ina. Kuma duk wanda ke karanta jarida yasan fuskarka. Saboda haka nasa likita na yaɗan kyara maka hanci da baki da ido." Yana magana ya nunawa Armad mudubi.


Abu na farko da Armad ya gani shi ne hancinsa ya loma ciki sannan ya gajarce kamar na biri. Idanunsa sun futo waje sun zama manya-manyan kamar na masu maƙoƙo. Sannan bakinsa ya ƙara faɗi kamar an yaga. Kalmar farko data zo bakimsa zagi ne amma ya fasa, "Kut... wa yasa ku mai dani haka?"


Bisaiya ya dubi Armad babu alamun wasa a fuskarsa, "Idan ban maida kai haka ba ya zanyi da fasinjoji na idan suka gano akwai Ayrid miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar acikin jirgin?"


Armad yai zumbur ya buɗe baki kamar wanda wani abu ya faɗo masa, "Idan haka ne to mai yasa kai baka miƙa ni ba? Ko kana jira ka isa gaɓa ne ka miƙa ni?"


Bisaiya ya amsa da cewa, "ba zance maka ka yarda dani ba, amma nayi maka alƙawarin baza ka samu matsala daga jirgi na ba. Shekarar mahaifina bakwai a kurkuku yanzu, saboda an saka kuɗi akansa akan abinda bai kai ya kawo ba. Kaima ina da yaƙinin ba wani abu ka aikata ba aka dora wannan kudi akanka. Kawai dai ana so a wanke gimbiya Nostaljiya ne a ɗora maka laifi saboda kai baka da galihu. Idan baka yadda dani ba zaka iya sauka a kowanne lokaci." Yana rufe baki ya juya ya bar Armad a tsaye a wajen.


***

Babi na 91: Gashin-Balbela


Kwanan Armad shida acikin wannan jirgi yana ta kai-komo da abubuwan dake ransa. Abu na farko gaskiyar mutanen cikin wannan jirgi, zai iya amince musu ko kuwa. Abu na gaba mai zaije ya tarar a daular Sisiya. Tunda Armad yake bai taɓa saka ƙafa a babban birnin ɗaya daga cikin garuruwan sarakunan Jinzidal ba, saboda haka bai masan mai zai tarar ba. Yaya yanayin garin yake? Shin wacce irin karɓa Nostaljiya zata yi masa? Abu ɗaya da yake da tabbas dashi shi ne mahaifin Nostaljiya Bihanzin mai dauwamammen sara bazaiyi murna da ganinsa ba. Ko a gamuwarsa ta farko kuma ta ƙarshe guduwa yayi dan kada su haɗu. 


Duk da Armad bai ga laifin Bihanzin wajen ƙoƙarin kare ƴarsa ba amma yana jimamin haɗuwa dashi. Musamman duba da cewa wannan shi ne karo na farko da zai gamu da Sarkin Jinzidal. 


Sannu a hankali Armad yaci gaba da gudanar da ragowar kwanakinsa acikin wannan ɗaki da Bisaiya ya bashi. Lokuta kaɗan yake fita yaga hasken rana saboda baya so wani acikin jirgin ya gane shi. A rana ta bakwai yana kwance akan gado yana tunanin yadda rayuwarsa take kasancewa sai kurum ya fara jin hayaniya daga waje. 


Da farko Armad yayi tunanin fasinjojin ne ke caca kamar yadda suka saba, amma ba jimawa ya gane cewa hayaniyar tafi ta haka.


Bayan ya ɗauki daƙiƙa ashirin yana nazarin hayaniyar saiya fuskanci ƙaraji ne kawai da ƙuwwa. Nan take Armad ya yasan faɗa ake. Kodai ƴan fashi sun kawo musu hari ko kuma faɗa ya kaure tsakanin fasinjojin jirgin. Koma dai wanne ne bai shafi Armad ba. Koda ƴan fashi ne, kowanne jirgi yana da dabarun kare kansa daga irin haka. Rufe idonsa kawai yayi, yaci gaba da nazarin yadda zaiyi ya gamu da Nostaljiya zarar ya isa daular Sisiya. 


Abu kamar wasa sai Armad yaji ihun ya fara raguwa, lamarinda yasa yayi tunanin cewa anci galaba akan ƴan fashin. Amma kuma wata zuciyar ta gaya masa cewa lokacin yayi ƙaranci ace har an gama da ƴan fashin. 


"Hmmm..." Armad yaja dogon numfashi tare da girgiza kai. Bai san mai yasa ba amma hankalinsa yaƙi kwanciya, saboda haka ya rufe idonsa ya fara laluben yanayin-izzar ma'aikatan jirgin. Nan take ya miƙe zumbur ya nufi ƙofar ɗakinsa. Yana buɗewa wani koren hayaƙi mai ratsin yalo yai masa sallama. A ƙasan hayaƙin mutane ne fululu a kwance sun sume.


Armad na ganin haka ya gane maike faruwa. Wannan hayaƙi guba ne kuma shi ne dalilin suman mutanen cikin jirgin. Koma waye ya feso wannan hayaƙi ba abokin Armad bane. 


Armad ya riƙe numfashinsa tare da tsayawa, tsaiwa irin ta ma'abota izza, sannan kai tsaye ya afka cikin hayaƙin. Bayan kimanin taku uku sai ya tsaya ya buɗe bakinsa ya huro iska waje. Amma maimakon iska sai feshin walƙiya ya fara ambaliya daga bakinsa. Kan kace meye wannan tuni feshin mai ɗauke da walƙiya ya kawar da wannan hayaƙi.


A wannan lokaci Armad ya gane ashe wani ƙaton jirgin ruwa ne ɓoye cikin duhu a gaban jirginsu. Girman jirgin yasa jirgin su Armad ya zama kama wani ɗan kwale-kwale. Daga inda Armad ke tsaye yana hangen sunan jirgin ansa GASHIN-BALBELA da manyan baƙi. 


Armad ya dawo da hankalinsa kan mutanen da ke cikin jirginsa. Da yawansu wannan hayaƙi yasa sun sume, amma wasu na tsattsaye. Ga dukkan alamu hayaƙin bacci kawai yake sawa kuma rayuwarsu bata cikin hatsari. Har Armad zaiyi ajiyar zuciya ya godewa ALLAH saiya hango Bisaiya kwance cikin jini riƙe da ƙirjinsa. Ƙarshen kibiya ya leƙo ta gaban ƙirjinsa. Dukkan ma'aikatan tsaron su shida na kewaye dashi suna ƙoƙarin taimakonsa. 


Armad na shirin ƙarasawa ya bada nasa agajin yaji murya daga cikin Gashin-balbela. 


"Ku bamu dukkan kayayyakin ku da makaman ku idan kuna so ku tsira da ranku."


Kyaftin ɗin jirgin shi ne yai wannan kashedin, amma a bayansa akwai ma'abota izza guda goma sha bakwai. Babu ko tantama jirgin ɓarayi ne domin ko fasinja ɗaya babu acikinsa. 


Armad ya dubi ma'aikatan jirginsa guda shida yaga dukkaninsu sun cika da tsoro, babu ko alamun kwarin gwiwa a tattare dasu. Ya juya izuwa ragowar fasinjojin da bacci bai ɗaukesu ba yaga tuni wasu daga cikinsu sun fara tattaro ragowar kayayyakinsu da niyyar miƙawa wannan ƴan fashi.


Ana haka Armad ya lura da wani jarumin saurayi tsaye akan Bisaiya riƙe da takobi, idonsa babu ko alamar tsoro. 


Cikin ƙiftawar ido Armad zai iya ƙarar da wannan ƴan fashi amma mutanen jirginsa zasu gane waye shi, wanda kuma hakan zai jawo masa matsaloli da dama a yayin tafiyarsa. Daɗin daɗawa wannan ƴan fashi basu cancanci ya kashe su ba indai ba wani suka taɓa ba, sannan kuma fasinjojin jirginsa sun yadda da sharaɗin ƴan fashin. Wasunsu tuni sun fara haɗo kayansu. Armad ya yanke shawara maimakon yaƙar wannan ƴan fashi kamata yayi ya fara ƙoƙarin ceto rayuwar kyaftin Bisaiya. Saboda haka ya nufi inda yake.


Yana isa ya fuskanci cewa wannan kibiya a kusa da zuciyar Bisaiya ta cake, lallai ana taɓa ta zai rasa ransa. Duk ƴadda akai hayaniyar farko daya ji ƴan fashin ne suka fara yi musu sallama da kibbau kafin su aiko wannan hayaƙi maisa bacci.


Kala-kalar tunane-tunane suka fara yawo a zuciyar Armad. Akwai tausayi na mutumin daya taimakeshi, akwai kuma haushi na wannan ƴan fashi. 


Ana haka Armad yaji wannan saurayi dake riƙe da takobi yayi ƙaraji ya afkawa Gashin-balbela. Wuta ce mai ruruwa tayi tsiri ta tsinin takobinsa ta daki akalar Gashin-balbela. Nan take wajen da wutar ta daka ya tsage, jirgin ya fara ƙara zai fashe. Ana cikin haka ɗaya daga cikin jaruman dake cikin Gashin-balbela ya tafa hannunsa, ya samarda wata ƙanƙara wadda ta ɗinke wajen daya tsage. 


Sadaukin ya ƙara tafa hannunsa ya samarda ƙatoton mutun-mutumin ƙanƙara wanda ya aikawa saurayin da saurin gaske. Kafin saurayin yai wani abu ƙanƙanra tayi masa akwati. Armad ya lalubi izzar wannan saurayi yaji hamsin da ɗaya ce kamar tasa a lokacin daya fita daga gida. Shi kuwa ma'aboci ƙanƙarar izzarsa shekaru ɗari da sha bakwai ce. 


"Yaro kayi ganganci. Babu wanda ya isa ya kwana da rai bayan ya taɓa min Gashin-balbela." Kyaftin ɗin jirgin Gashin-balbela ya gayawa saurayin. Kafin ya juyo ga mutumin dake gefensa. "Kawo min kansa."


Mutumin yai tsalle ya diro cikin Fataken-dare. Sannan ya zare takobi ya nufi saurayin da niyyar sare masa kai.  


A wannan lokaci ne Armad yai tsawa mai tsananin firgitarwa daga yake zaune. Abin mamaki Armad bai ɗaga muryarsa ba, amma babu wanda baiji tsawar ba har cikin ransa, musamman mutanen cikin Gashin-balbela.  


Nan take wannan sadauki daya tunkaro saurayin ya tsaya cak a inda yake, kafin gumi ya fara keto masa. A hankali ya ɗaga kansa cikin tsoro yai tsinkaye da ma'aboci wannan tsawa, lamarinda yasa ya fara karkarwa kamar wanda aka jefa tubalin ƙanƙanra acikinsa. 


Armad yakai ƙololuwar ɓacin rai, kuma tuni ya yanke shawarar nitsar da Gashin-balbela. Ya dubi wannan sadaukin dake ƙoƙarin kashe saurayin ya kirawo ɗaya daga cikin kalaman izzarsa, "Sanyin-babban-sihiri!" 


Nan take ƙanƙara ruwan toka ta haɗiye sadaukin. Armad ya nunashi da ɗanyatsansa, lamarinda yasa ƙanƙarar ta tamke shi tamau kamar zata fasa ƙasusuwansa. Kan kace meye wannan ya faɗi ƙasa sumamme. 


Armad ya dubi kyaftin ɗin Gashin-balbela ya ce, "idan kana so ka tsira da ranka, toka koma inda ka fito. Amma kayi sani cewa anan zaka bar wannan jirgin naka."


***


Babi na 92: Maikiro Inára


Armad bai jira amsar ƴan-fashin dake cikin jirgin Gashin-balbela ba ya wuce izuwa wannan saurayi ya rusa akwatin ƙanƙarar daya rufe shi. Sannan ya juya izuwa jirgin dake gabansa.


Kyaftin ɗin cikin jirgin, wanda ƴan daƙiƙu kaɗan da suka wuce shi ne ya bada umarnin a kashe wannan saurayi saboda ya taɓa masa jirgi, shi ne ya fara yin tsalle ya afka cikin ruwa. Kafin daga bisani sauran ƴan fashin su bishi. Lallai duk wanda ya rayu a wannan zamanin yasan menene sanyin-babban-sihiri, babu ko tantama akwai ratar izza mai yawan gaske tsakanin mutumin da yake iya sarrafa sanyin-babban-sihiri da wanda bai iya ba. 


Armad yai ajiyar zuciya sannan ya juya izuwa kyaftin Bisaiya, a lokacin ne ya gane cewa dukkan mutanen dake cikin jirgin kallonsa suke kamar wanda suka ga wani mala'ika. Kowa ƙoƙari yake yasan wane ne shi. Kasancewar Armad yana iya sarrafa sanyin-babban-sihiri hakan na nuna yakai aƙalla izza shekaru dubu ɗaya, wanda hakan ke nuna Armad ya futo daga ɗaya daga cikin manyan dauloli biyar na ƙasa bakwai. Domin kuwa bawai abu ne mai sauƙi ba ka samu wanda shekarun izzarsa suka kai dubu, saboda duk hanyoyin da ake iya samun izzar da takai dubu hanyoyi ne wanda zaiyi matuƙar wuya wanda baya cikin wannan dauloli ya samu.


Koda isar Armad saiya tarar Bisaiya na kakarin mutuwa, inda yana ganinsa yayi masa manana jini na fita daga bakinsa. "K....kayimin abu ɗaya badan na... isa.. ba." 


Armad ya riƙe hannunsa cikin tausayi. Bai san mai Bisaiya zaice ba amma kawai ya kyaɗa kai. 


Bisaiya ya ɗaga ɗan-yatsansa da kyar yai nuni izuwa wannan jarumin saurayi ya ce, "Ka kularmin da ɗana." 


Armad najin haka ya zare ido cikin mamaki da al'ajabi. Tun farko dai bashi da masaniyar Bisaiya nada ɗa, sannan kuma shi kansa wahalhalun kansa sun masa yawa ballanta ace ya kula da wani. To amma a halinda Bisaiya ke ciki na gabda mutuwa babu yadda za'ai yace masa a'a. Daɗin daɗawa kafin Armad ya gama tunani yaji kakarin da Bisaiya ke yi ya ƙaru, kafin daga bisani ya faɗi matacce. 


Armad na ganin Bisaiya ya mutu ya canja shawara yai tsalle ya faɗa cikin ruwa yabi wannan ƴan fashi. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya dawo dasu a ɗaure cikin igiya. Wannan saurayi na zaune a gefen Bisaiya yana hawaye. Sauran ma'aikatan cikin jirgin duk kuka suke, kana gani kasan sunji daɗin aiki da Bisaiya. Duniya budurwa wawa, yanzu kake da rai in anjima babu. Waye zai taɓa tsammanin Bisaiya wanda ke da cikakkiyar lafiya ƴan daƙiƙu da suka wuce zai faɗi matacce yanzu. 


Su kuwa sauran fasinjoji wanda ke kwance a sume sun fara farkawa, abu na farko da suke iskewa shi ne gawar Bisaiya. 


Nan take Armad yasa aka rataya igiya a wuyan dukkan ƴan-fashin goma sha bakwai. Sannan ya dubi wannan saurayi ya fara bayani. "Wanda ya kashe wani shima kasheshi za'ayi. Idan kana so ga igiya." Armad ya miƙawa saurayin igiyar dake hannunsa wadda ana janta zata ƙarasa rataye ƴan-fashin.


Babu wani kokwanto wannan saurayi ya miƙe ya nufi inda Armad yake ya karɓi igiyar dake hannunsa. Idanuwan wannan ƴan-fashi suka zazzaro cikin tsoro, sun san cewa rayuwarsu na gab da ƙarewa. Wasu daga cikinsu suka fara roƙon yafiya wasu kuma suna jiƙa wandonsu. Wannan saurayi ya ja igiyar ya rataye su. Da dama daga cikin fadinjojin kasa kallo sukai suka koma ciki. Amma Armad da saurayin da ma'aikatan cikin jirgin na tsaye suna kallon har ƴan-fashin suka gama harɗe-harɗensu suka mutu. Armad ya jefa gawarwakinsu cikin ruwa sannan ya bada umarnin ayiwa Bisaiya wanka. 


Bayan Armad ya tambayi ɗaya daga ma'aikatan jirgin akan al'adun ƙabilar da Bisaiya ya fito daga ciki ta fannin binne mamaci saiya fuskaci cewa ƙonawa suke sannan su jefa acikin ruwa. Armad ya tambayi saurayin idan akwai abinda yake buƙata ko kuma wani canji da yake so ayi wajen binne mahaifinsa, saurayin ya amsa da a'a. 


Sun samu dukiya mai yawa acikin jirgin Gashin-balbe wanda hakan ke nuna ba ƙananan ƴan fashi bane aciki. Daga ƙarshe suka zaɓi suci gaba da tafiya acikin jirginsu domin girmamawa ga Bisaiya.


Kwanaki uku akai ana jimami acikin jirgin Fataken-dare kafin Armad ya samu damar tara kowa ya fara yi musu bayani cikin tattausar murya mai cike da kwarjini. 


"Marigayi kyaftin Bisaiya shi ne wanda ya ceto ni daga cikin ruwa yayimin maganin ciwuka na a lokacinda bai sanni ba. A lokacin rayuwarsa ya kasance jarumi ne mara tsoro, domin kuwa baiji tsoron komai ba a lokacinda yake ceto ni. Lallai bazan taɓa mantawa da abinda yayimin ba. Kowa da lokacinsa, lokacin ɗan-uwanmu Bisaiya yayi babu wanda zai iya hanawa. Amma nayi muku alƙawari zan kare wannan jirgi daga nan har zuwa sanda zamu isa daular Sisiya." Armad ya ɗanyi shiru na ɗan lokaci kafin ya wuce izuwa ɗakinsa yana tunani akan wasiyyar da Bisaiya ya bar masa taya kular masa da ɗansa. Tsahon kwanakin nan uku bai cewa ɗan komai ba, domin bai san mai zaice ba. Bai san mai ake buƙata daga gareshi ba. 


A rana ta shida saurayin ya gabato izuwa ɗakin Armad. 


"Suna na Maikiro Inàra." Saurayin ya ce, "Asalin mu ƴan daular Maikironomada ne amma dani da mahaifina mun zaɓi zama a daular Sisiya. Idan ka yadda zan bika na koyi al'amuran izza daga gareka na ɗan lokaci kafin mu rabu."


Armad yaja dogon numfashi, sannan bayan ɗan tunani ya amince. Koyarda al'amuran abu ne mai tsada wanda sai anje manyan makarantu na manyan dauloli kafin a koya, amma idan kana da babban ma'aboci izza wanda zai koya maka ba saika je ba. Shi ma Armad kakansa shi ne ya koyar dashi. Koyawa wannan saurayi ba wani abu bane, kuma zaisa Armad ya biya bashin ceto shi da Bisaiya yayi. 


"Na amince zan koya maka al'amuran izza amma a halin yanzu ina kan hanyata ta zuwa daular Sisiya domin samawa mahaifiyata lafiya. Ban san yadda zata kaya ba, kuma abubuwa zasu iya rincaɓewa. Bazan iya gaya maka koni waye ba, amma ni mutun ne wanda keda kuɗi akansa. Bina zai zamo abu mai hatsari a gareka. Abu na ƙarshe idan zaka bini saidai ka haƙura da sana'arka ta tuƙa jirgi, domin kaga nidai ba'a ruwa nake yawo ba."


Saurayin yai murmushin takaici tare da zubewa akan gwiwowinsa yana cewa, "Nasan haƙiƙanin kokai waye, Armad Wilbafos. Kuma a kowanne lokaci zan iya dawowa sana'ar tuƙa jirgi baƴan na gama koyon al'amuran izza. Koyon al'amuran izza shi ne abinda rayuwata ke buƙata a yanzu, babu wanda na zarga da mutuwar babana sai rashin ƙarfin izza ta. Indai zaka koyamin al'amuran izza zan bika ko'ina ne a duniya."


***

Babi na 93: Samari biyu


Ragowar kwanakin da Armad yayi acikin wannan jirgi baiji daɗinsu ba sosai, domin kuwa kowa idan ya ganshi kaucewa yake tamkar yana tsoron kada ya ɓata masa. Tun yana damuwa harya daina, shi kuwa Maikiro Inára kullum a ƙofar ɗakin Armad ya dawo kwana, a cewarsa ɗalibi kullum yana tare da malaminsa. Babu yadda Armad baiyi ba amma Inára bai daina kwana anan ba. Hatta ma'aikatan jirgin duk abinda zasu yi sai sun nemi izini wajen Armad. 


A sati na huɗu suka iso daular Sisiya, ɗaya daga cikin manyan dauloli shida dake faɗin duniya a wannan zamani. Armad yayi farin ciki sosai da faruwar hakan domin koba komai ya ƙara kusantar matakin samawa mahaifiyarsa lafiya. Yana ji a ransa cewa wannan shi ne karo na ƙarshe da zai fita nemar mata lafiya domin kuwa a wannan lokaci zai samu abinda yake nema kuma bazai ƙara bari ta faɗa cikin rashin lafiya ba koda sama da ƙasa zata haɗe.


Sannu a hankali jirgin Fataken-dare ya sauka a gaɓar doron-ƙasa na huɗu sashin arewa inda anan daular sisiya take. 


Gaɓar jirgin acike take da ƴan kasuwa da kuma iyalan fasinjojin da duka zo taryar su. Cikin ƙanƙanin lokaci fasinjoji kowa yai sallama da juna sannan suka godewa Armad kafin kowa ya kama gabansa. Tuni daman Inára ya sallami dukkan ma'aikatan jirgin ya biya su haƙƙinsu, saboda baya sa ran ƙara tafiya a kowanne lokaci kusa. 


Koda kowa ya ɓace aka bar Armad da Inára sai Inara ya nemi iznin zuwa ya bada ajiyar jirgin Fataken-dare har zuwa lokacinda zai dawo kan ciniki. Armad ya amince kuma ya bayyana masa wajenda zasu haɗu bayan ya gama.


A lokacinda suka iso gaɓar rana na tsakiyar sama amma kafin Inara ya hattama komai sai da rana ta faɗi. A lokacin ya iske Armad a ɗaya daga cikin gidajen-kwana na wannan gaɓa. Armad na zaune yana tattara bayanai akan wannan daula ta sisiya. Dama abinda yazo yi kenan. Inara na bayyana Armad ya tashi suka kama hanya. 


Armad ya dubi Inara ya ce, "Da fatan ka gama komai?"


Inara ya gyaɗa kai. "Eh, na gama ya shugaba na. Na samu wanda zai ajiye min jirgin Fataken-dare har zuwa sanda zan dawo."


"To yayi kyau." Armad ya ce, "daga binciken da nayi na gano cewa wannan daula nada adadin mutane miliyan ɗari biyar zuwa ɗar shida. Wannan mutane sun rarrabu a tsakanin garuruwa ashirin da tara da babban birni guda ɗaya wanda ake kira da Jékis. 


"Kowanne ɗaya daga cikin wannan garuruwa ashirin da tara nada sarki amma dukkan wannan sarakai suna ƙarƙashin babban sarkin dake mulki a babban birnin tarayya na Jékis. Wanda ba wani bane illa Bihanzin mai dauwamammen sara. Daga nan zuwa can tafiyar wata da watanni ce, amma ina da sihirtaccen doki mai suna Ubbaru wanda zai taƙaice mana wannan tafiya."


Armad na zuwa nan a zancensa ya hanhanga ya tabbatar babu wanda ke kallo sannan ya sha kwanar wani layi mai duhu ya buɗe ƙofar zobensa ya ɗakko Ubbaru. 


Inara na cikin mamakin wannan zobe na Armad yaji muryar Armad na masa bayani. "Saboda tsananin gudun wannan doki jama'a basa ganinsa a yayinda yake tafiya. Ina ganin ba matsala muyi amfani dashi  mu isa babban birnin."


Armad da Inára suka hau dokin sannan suka ɗau hanya. Da tsakar dare suka isa babban birnin Jekis, wanda hakan ke nuna Ubbaru ya taƙaice tafiyar wata da watanni acikin awanni. Babban abinda ya bawa Inara mamaki shi ne yadda shi yake iya ganin mutane da garuruwan da suke wucewa amma mutane basa ganinsu. Kuma duk wannan azabar gudu iska bata damunsu. Lallai Ubbaru doki ne mai yawan sihiri. 


Inara ya dubi Armad ya ce, "A yanzu sun rufe ƙofa sai dai mu jira zuwa asuba."


Armad ya amince suka sami gindin wata bishiya suka fake har zuwa safiya. Abin mamaki har yanzu ƴaƴan itacen da Nostaljiya ta bar masa suna nan basu lalace ba, saboda haka Armad ya fito dasu suka ci sukai hani'an.


Da safe suka nufi ƙofar wannan babban-birni mai suna Jekis. Duk da sammakonsu saida suka tararda layin mutane a bakin ƙofar wanda a tafe suka kwana. Wani tafkeken bango ne iya ganinka ya kewaye garin. Duk wanda zai wuce saiya nuna shedar ɗan-ƙasa ta sisiya da kuma harajin ayrid hamsin ko ɗari idan baka da sheda. 


A wannan lokaci Armad ya tuno bashi da ko sisi duk da akwai naira miliyan ɗaya da rabi a kansa. Koda Inara ya fuskanci halinda Armad ke ciki saiya fito da ayrid ɗari da hamsin ya riƙe a hannunsa. Kallonsa kawai Armad yayi tare da yin murmushin godiya. 


Sannu a hankali layi ya fara raguwa, saura mutun sha uku a gabansu. A wannan lokaci ne Armad ya hango wasu samari guda biyu a gabansa. Tsakaninsa dasu mutun goma ne kawai. Ɗaya daga ciki yana da ƙiba, ɗaya kuma siriri ne kuma yana ɗauke da takobi. Dukkansu sun saka hirami sun nannaɗe fuskarsu amma Armad yana ji lallai ya sansu amma babu dama ya sauka daga layi ya isa gare su. Saboda haka saiya rufe ido ya gane yanayin-izzarsu.


Bayan wannan samari sun wuce layi ya iso kan su Armad. Masu gadi ashirin ne a bakin ƙofar. Rabi riƙe da makamai rabi kuma suna ƙirga kuɗi. Dukkansu sanye da kaya yalaye masu ratsin baƙi a hannunsu. 


Inara ya miƙa kuɗin dake hannunsa tare da katinsa na ɗan ƙasa yana cewa, "ga nawa ayrid hamsin, gana malami na ayrid ɗari domin bashi da shedar ɗan ƙasa."


Mai gadin yayi wa Armad wani kallo mai tsayi kamar wanda ke kallon mai laifin kisa. Sannan daga bisani ya ce, "daga wacce daula kake?"


Armad ya amsa da cewa, "daular Hán ta doron ƙasa na uku."


Mai gadin ya ƙara matsawa kusa kamar wanda ke kokwanton kamannin Armad. A jikinsa yana ji cewa lallai Armad mai laifi ne. Nan take ya buɗe wani ƙaton littafi a gefensa mai ɗauke da hotunan mutane masu laifi wanda aka sa kuɗi akansu. 


Duk da Armad yasan kamanninsa a canje suke sai da zuciyarsa ta buga da yaga mutumin ya buɗo shafin da hotonsa ke ciki. 


Mai gadin ya tsaya tare da ƙara tambayar Armad, "Yama kace sunanka?"


Armad ya amsa da cewa, "Han Djinn."


Mai gadin yaja dogon numfashi tare da buɗe baki zai ƙara wata maganar amma sai Inara ya zira hannu a aljihu ya miƙa masa ƙarin Ayrid ɗari. Lamarinda yasa yai murmushi tare da buɗe musu ƙofa.


Cikin sauri Armad yabi bayan wannan samari biyu daya hanga a gabansa. Suna shiga kuwa manyan gine-ginen birnin sukai musa sallama. Amma duk da haka ya iya jiyo yanayin-izzar wannan samari guda biyu a ɗan gaba da inda suke. Nan take ya umarci Inára daya jirashi anan, sannan yayi amfani sabuwar fasaharsa ta Kaban'shisu ya ɓace daga inda yake ya bayyana a bayan wannan samari biyu. 


Yana bayyana ya kalli samarin sama da ƙasa. Nan take sai farin ciki ya cika zuciyar sa. Cikin dariya da annushuwa ya kira sunansu. "Iliyasis... Cokali... Ina Nusi?"


Iliƴasis ya juyo cikin zafin nama ya ɗora takobinsa a wuyan Armad yana cewa, "Waye kai? Kuma a ina ka sanmu? Idan baka bani amsa ba yanzu zan tsinke maka kai."  

***

Babi na 94: Tsumin-izza


Wata biyu kafin fitar Armad daga kurkuku.


A can daular Infiriya, babban birnin Rafiya inda sarki Rafiyan Kaltume ke mulki, Cokali da Iliyasis ne suka shigo domin neman bayanin ƴar'uwarsu Nusi a wajen yarima Niyashi. 


Tafiya suke cikin yadda dakai da rashin tsoro suna tunkarar babbar fadar ƙasar inda sarki Rafiyan Kaltume ke mulki. Idan mai karatu bai manta ba yarima Niyashi shi ne wanda baya tsufa. Kuma shi ne wanda ya taimaki Nusi dasu Cokali tun suna ƴan shekara shida. Saboda haka ba abin mamaki bane da Iliyasis da Cokali suka yanke shawarar su fara neman Nusi daga wajensa. Koda bai san inda take ba zai iya taimaka musu da kwatance. 


Iliyasis ya tsayar da wani saurayi mai jan gashi dogo ya tambaye shi, "da ALLAH mu baƙin yarima Niyashi ne. Ko kasan inda zamu iya samunsa?"


Koda jin tambayar sai saurayin ya haɗe rai cikin fushi ya ce, "yarima Niyashi? Amma banda ku baƙi ne saina sare muku kai. Faɗar sunan yarima mai jiran gado gatsal babban laifi ne idan baku sani ba."


Iliyasis najin haka yai murmushi tare da sanyaya murya yana cewa, "afuwa. kamar yadda ka faɗa mu baƙi ne. Amma maiya kamata mu ce masa?"


Saurayin yai shiru yana hucewa kafin daga bisani ya amsa da cewa, "shi dai wanda kuke nema shi ne alfaharin mutanen wannan daula. Kuma muna girmama shi da sunan 'Nazára' wanda hakan ke nufin mai ceto. Sannan kuma kamar yadda ake yiwa ƴaƴan babbar masarautar wannan daular shima ana saka masa kalmar 'Rafiyan' a farkon sunansa. Saboda haka daga yau ku riƙe sunansa 'Rafiyan Nazára' ɗan sarki Rafiyan Kaltume."  Koda saurayin yazo nan a zancensa sai yai shiru yana kallon su Iliyasis domin ya tabbarar sun fahimce shi kafin daga bisani ya ci gaba da cewa, "Idan kuka miƙe wannan hanya tsahon tafiyar wuni ɗaya zaku tarar da ɗakin bauta na sarki Rafiya wanda ke daura da fada. Anan zaku tadda shi yana karɓar Tsumin-Izza."


Saurayin na gama magana yayi nasa waje ba tare da sanin ko sun fahimce shi ba. Cokali yana niyyar finciko shi Iliƴasis ya ɗaga hannu. 


Haka suka ji gaba da tafiya suna tambayar sunan Rafiyan Nazára har saida rana ta faɗi. A lokacin da suka iso wani ƙaton shinge kewaye da sadaukai ma'aibota izza aƙalla dubu. Dukkaninsu sun durƙusa ƙasa sanye da fararen kaya tamkar suna bauta. A can tsakiyarsu wani saurayi ne zaune yake kallon sama. Abin mamaki ƙanƙarar Sanyin-babban-sihiri ce ke zuba a dai-dai kewayen wannan saurayi. Ba jimawa Iliƴasis ya gane saurayin ba wani bane illa Yarima Niyashi. Duk yadda akai wani babban sihirn ake haɗawa. 


Cikin zafin nama suka je suka samo fararen kaya tare da matsawa kusa da ɗaya daga cikin sadaukan dake wajen domin samo bayanai. 


Sunan abinda ke faruwa dai Tsumin-izza, kuma yawanci ana yiwa duk  wani yarima mai jiran gado na kowacce daula domin su sami izza maɗaukakiya. Mutun zai zauna ya karɓi shekarun izza daga asusun izza na daularsu. Wato shekarun izza da kowacce daula ke tarawa ta hanyar fasahar kwangila. Ƙa'idar shi ne duk kwana ɗaya mutun zai karɓi shekarun izza dubu ɗaya, kuma mutun zai ci gaba da karɓa har zuwa sanda ƙarfinsa zai ƙare. Sai dai a ƙa'idar ba ci ba sha har a gama. 


A wannan rana kwanan Yarima Niyashi bakwai yana zaune yana karɓar wannan tsumi daga asusun izza na daularsa.


A kwana a tashi saida yarima Niyashi ya kwashe kwanaki tara acikin wannan yanayi. Lamarinda ya bashi izza shekara ɗai-ɗai har dubu tara. Hatta manƴan sadaukai uku da ake ji dasu a dukkan faɗin daular izzarsu bata wuce shekaru dubu shida ba. Amma ga yarima Niyashi wanda dama yana da sirrin rashin tsufa a jininsa ya samu shekaru dubu tara. Lallai a wannan rana an ƙara haifar wani babban ma'aboci izzar wanda ya kamata a saka sunansa acikin manyan gobe.


Saida akai ƙasaitaccen biki tare da gayyato kowanne sarki daga cikin sarakuna talatin da ɗaya dake daular Infiriya domin a taya yarima Niyashi da sarki Rafiyan Kaltume murna. 


Bayan komai ya lafa Iliyasis da Cokali suka samu damar ganin Niyashi. Labarin ɓatan Nusi bai masa daɗi ba kwata-kwata amma daga ƙarshe shawarar daya basu kawai shi ne su nemi Armad. Duk inda take zai sani. 


Sunyi mamakin yadda Niyashi ya riƙe sunan Armad to amma bawai sakawa Armad kuɗi da akai bane kaɗai yasa kowa ya sanshi ba. Babban abin shi ne yadda gimbiya Nostaljiya wadda ake ganin tafi duk wata yarinya kyau a duniya take kareshi a gaban kotu. Zuwa wannan lokaci kowa ya san cewa Nostaljiya ita ce ta ceci Armad a wajen cinikin bayi daya gabata, amma saboda matsayin baban ta a idon duniya ake so a rufe a ɗorawa Armad laifi. Abin mamakin shi ne har yanzu Nostaljiya taƙi bada shedar Armad shi ne mai laifi.


Niyashi ya dubi su Iliyasis ya ce, "sarki Bihanzin baya son yaƙi ya ɓarke tsakaninsa da sauran sarakunan Jinzidal saboda haka yau kwana uku kenan ya bada auren Nostaljiya ga yarima mai jiran gado na daular Denizawa wato Deniz Bizáya. Nan bada jimawa ba za'a saka ranar bikin. Ina tunanin duk inda Armad yake zai bayyana a daular Sisiya kafin wannan biki. Indai kuna so ku gamu dashi can zaku tafi."


Koda jin haka sai Iliyasis ya kalli Cokali cikin jimami. Indai har da gaske ne maganar auren Nostaljiya da Deniz Bizaya lallai akwai yiwuwar Armad yaje daular Sisiya. To amma akwai matsaloli da dama da zasu iya afkuwa. 


Bayan sun ƙara ƴan kwanaki a daular Infiriya ƙarƙashin kulawar yarima Niyashi sai sukai azama suka nufi daular Sisiya. A lokocin da suka fito labarin auren bai baza duniya ba domin kuwa suma a bakin Niyashi suka ji, amma kafin su isa babban birnin Sisiya wato Jekis labari ya baza ko'ina. Kowa yasan gimbiya Zahra wadda akafi sani da Nostaljiya Nára zata auri yarima mai jiran gado na daular Denizawa wato Deniz Bizáya. A wani mataki na hana afkuwar yaƙin da zaiyi asarar miliyoyin rayuka.


To ta haka Iliyasis da Cokali suka iso daular Sisiya, kuma gashi ƙaddara tasa suna shigowa sun haɗu da Armad kafin su isa cikin gari.   


***


Babi na 95: Hankakan-mutuwa 


Tun kafin Iliyasis ya janye takobinsa Cokali yai tsalle ya rungume Armad cikin murna. Saida Armad yai da gaske sannan ya kwaci kansa.


Cokali ne ya fara magana. "Armad! Ashe da gaske nan zaka taho. Amma mai yasa kake tambayarmu ina Nusi bayan tare muka barku? Kar dai kace kaima bakwa tare."


Nan take wannan tambayoyi suka jefa Armad cikin tunani. Ga dukkan alamu  bama saiya tambaya ba, suma su Cokali basu san inda Nusi take ba. To amma abin mamakin shi ne yadda su Cokali suka san zaizo daular Sisiya.


Armad ya dube su ya ce, "kuma nemanta kuke yi kenan? Rabo na da ita tun shekarar data wuce a gasar cinikin bayi ta Jinzidal. Amma yaya akai kuka san zanzo nan?"


Nan take jikinsu Iliyasis yai sanyi. Suna tunanin samun Nusi a wajen Armad amma shima bai san inda take ba. Kuma yanzu dole sai sun bayyanawa Armad tsakaninsu da yarima Niyashi da kuma yadda akai suka gano zaizo wannan gari. 


Iliyasis ya dubi Armad ya ce, "Mu ƙarasa mu samu mafaka kafin muyi magana."


Armad ya kyaɗa kai sannan dashi da Maikiro Inara suka bi bayan su Cokali izuwa cikin gari.


Suna tafe suna kalle-kallen wannan ƙasaitaccen birni na Jekis wanda ke ɗauke da manya-manyan gine-gine masu samfuri kala-kala. Amma Cokali baiyi shiru ba, saida ya taɓo labarin faɗan Armad da yarima Niyashi da kuma yadda Armad yai nasara, domin labarin tuni ya baza ko'ina. Armad dai baice komai ba murmushi kawai yake.


Ba jimawa suka iso harabar wani ƙaton gidan-kwana a farfajiyar wata kasuwa. Har yanzu dai Armad bashi da ko sisi saboda haka Inara ne ya biya masa kuɗin ɗaki kafin daga bisani duk su huɗun su hallara a ɗaki ɗaya domin tattauna matsalolinsu. 


Iliyasis yayiwa Armad inkiya daya tura Inara waje dan su tattauna cikin sirri amma nan take Inara ya buɗe baki ya dubi Iliyasis ya ce, "indai daga daular Maikironomada kuke kunsan ɗalibi baya barin gefen malaminsa a kowanne lokaci har sai sanda malamin ya yaye shi. Saboda haka ina cikin wannan ɗaki, amma nayi muku alƙawarin duk abinda zaku faɗa baza ajishi a bakina ba koda bayan raina."


Cokali ya kalli Iliyasis tsahon ƴan daƙiƙu kafin su kyaɗa kai alamun amincewa. 


Iliyasis ne ya kwashe dukkan tarihin dake tsakaninsu da yarima Niyashi ya gayawa Armad sannan kuma ya gaya masa yadda suka san zaizo wannan gari da kuma labarin auren Nostaljiya. 


Armad yai shiru yana tunani tsahon lokaci. Dukkan abubuwan dake afkuwa harda yaƙin dake neman ɓarkewa tsakanin sarakunan Jinzidal ta dalilinsa ne. Amma babban abinda yafi damunsa shi ne zancen wannan aure da kuma ɓatan ƴar uwarsa Nusi. 


Wani irin ɓacin rai mai zafi wanda Armad bai taɓa jin irinsa ba ya taso masa a ƙirji a lokacin daya hango Nostaljiya a ɗakin yarima Deniz Bizaya. Tun bayan sanda Nostaljiya ta bayyana masa tana sonsa Armad bai taɓa tsayawa yayi wani dogon tunani akan maganar ba, kuma ko a jikinsa. Amma a halin yanzu da yaji zatai aure hankalinsa yayi mummunan tashi. Da farko yayi tunanin saboda baya so ayi mata auren dole ne amma ba jimawa ya gano cewa lallai shima akwai ƙaunar Nostaljiya acikin ransa. 


Cokali ya dubi Armad cikin al'ajabi ya ce, "idanun ka sunyi ja ja wur. Da gaske kana son ta."


Armad yai shiru baice komai ba. 


Iliyasis ya dubi Armad ya ce, "Idan zaka bi shawara ta ka haƙura. Wannan auren shi kaɗai ne zai kare afkuwar yaƙi da asarar miliyoyin rayuka. Idan ka hana wannan aure lallai yaƙi saiya afku. Ina ganin kawai kazo mu juya ba tare da kun haɗu da ita ba."


Armad ya ja dogon numfashi sannan ya ce, "idan da ɗaurin auren ne ya kawo ni da nabi shawararka, amma nemawa mahaifiyata lafiya ne ya kawo ni wannan daula. Kuma lallai sai naga Nostaljiya na nemi taimakon ta. Zarar mahaifiyata ta samu lafiya sai mu tafi."


A wannan lokaci Armad ya kwashe duk abinda ya faru dashi bayan rabuwarsa dasu Iliƴasis ya gaya musu. Sannan ya nemi iznin su jirashi ya je yaga Nostaljiya kafin ya fito su bazama neman Nusi tare. 


Daga ƙarshe Armad ya dubi Inara ya ce, "kaima ka jirani anan naje na dawo."


Nan take Inara ya sunkui da kai cikin alhini yana cewa, "ya shugabana kayi haƙuri amma lallai bazan iya barin gefenka ba har izuwa lokacin da zaka sallame ni a matsayin ɗalibi."


Dama Armad yayi tunanin Inara zaice haka saboda haka kawai murmushi ya kyaɗa kai. 


Da safe bayan sun karya Armad da Inara suka nufi hanyar fadar birnin Jekis da niyyar ganin gimbiya Nostaljiya Nára. 


Ba jimawa suka tsinci kansu a wata siririyar hanya da zata kaisu izuwa fadar. Armad ya dubi Inara ya ce, "ka farkar da fasaharka?"


Inara ya girgiza kai. "A'a."


Armad yai murmushi tare da cewa, "nayi tunanin haka tunda daman baka da yawan shekarun izza. Amma ba matsala ba ce. Kamar yadda ka sani zaka iya kwarewa akan harkar fasahar aljanu, ko kuma akan takobi ko kuma akan ɗalasimai. Naga kana iya amfani da takobi da kuma fasahar aljanin wuta. Kai sani cewa wannan bazai isa ba. Indai kana so ka kware akan harkar izza saika haɗa da ɗalasimai sannan kuma daga baya bayan ka farkar da fasaharka sai ka zaɓi hanya guda ɗaya. Ina da malami mai suna Babara wanda ya kware akan harkar ɗalasimai. Zarar muka gamu dashi zansa ya farkar da fasaharka, amma kafin lokacin zan fara da koya maka dabarun amfani da takobi da kuma fasahar aljanu. 


"Kaga dai amfani da aljanu yana buƙatar shekarun izza. Kuma iyakacin yawan shekarun izzarka iyakacin ƙarfin fasahar da zaka iya amfani da ita. Da shekarun izza hamsin da ɗaya da kake dasu baza ka iya wuce mataki na farko ba daga cikin matakai shida na amfani da aljanu. Kuma indai...."


Armad na cikin bayani yaji wani yanayin-izza mai tsananin ƙarfi da buwaya ya tunkaro shi ta baya. Tunda Armad yake bai taɓa jin irin wannan yanayin izza ba. Idan a misali zai iya kwatanta girman yanayin-izzar duk daya taɓa ji a matsayin kofin ruwa ɗaya to wannan izzar takai girman tekun maliya. 


Bawai kuma girman izzar ne yasa Armad ya fara gumi ba, tsananin zafi da muni da azabar dake cikin izzar ne yasa Armad yaji tamkar ruhinsa zai fashe. 


Kafin Armad yai wani motsi Inara ya faɗi ƙasa sumamme. Yana juyawa bayansa wani ƙatoton hankaka baƙi-ƙirin mai ido kwaya ɗaya tak ya kawo masa wafta. Armad ya manta da cewa zai iya juyewa izuwa walƙiya ya baje a ƙasa wannan hankaka ya wuce.


Kafin ya miƙe hankakan yayiwo kwana. Cikin sauri Armad ya kirawo Hannun-Aradu ya fuskanci wannan hankaka. To amma bisa mamaki sai hankakan ya tsaya cak yana kallon Armad sama da ƙasa tsahon lokaci kafin daga bisani ya juya ya ɓace. 


Abu na farko daya fara zuwa ran Armad shi ne wani labari da mahaifiyarsa ta taɓa bashi akan wata ƙabila wadda aka manta da sunansu. Wannan ƙabila sune asalin tsafin Sanyin-Babban-Sihiri. Dukkan tsafinsu suna yinsa da baƙin aljanin-hankaka wanda ake kira da HANKAKAN-MUTUWA. Acewar wannan labari hatta sarki Eyriyon Wilbafos da sarki Kuyurussa'ayi Ururu baza su iya sawa wannan hankaka ya durƙusa musu ba. Shi yasa suka haɗa ƙarfi da ƙarfe suka halaka wannan ƙabila. Kuma tun daga wannan rana babu wanda ya ƙara ganin Hankakan-mutuwa a doron ƙasa. Amma indai Armad ba mafarki yake ba lallai yau yaga hankakan-mutuwa da idonsa.     


***

Babi na 96: Shiga fada


Koda Armad yaga wannan baƙin hankaka na neman ɓace masa saiya buɗe ƙofar zobensa na sihiri ya cilla Inara aciki. Sannan yayi amfani da fasahar Kaban'shísu ya ɓace daga inda yake tare da bayyana acan nesa dai-dai ƙasan inda hankakan ke tafiya a sama. 


Hankakan na ganin haka ya sha kwana tare da ƙara azama wajen iyo akan iska yana ƙoƙarin gujewa Armad. Amma murmushi kawai Armad yayi tare da barin hankakan yayi nisa kafin ya ƙara yin amfani da ɗalasimin Kaban'shísu ya bayyana a ƙasansa. Sannu a hankali Armad yana bin wannan baƙin hankaka sai kawai ganinsa yayi a kusa da fadar sarki Bihanzin mai dauwamammen sara. Abin mamaki sai wannan hankaka ya ƙara shan kwana yabi jikin katangar wannan fada ya nufi yamma.


Armad nada ragowar ɗalasimai biyu kacal saboda haka ya fara tunanin hanyar da zaibi ya kama wannan hankaka idan bai tsaya ba. Yana cikin tunani ya hangi hankakan ya tsaya a ƙarshen katangar ta ɓangaren yamma. Har wani waiwayo wa yake yana kallon Armad tamkar yana jiransa. 


A fusace Armad ya yanke shawarar yadda zaiyi ya kama wannan hankaka. Ya buɗe baki ya kira ɗalasimin Kaban'shìsu amma a wannan lokaci saiya canja maimakon ya bayyana a ƙasa saiya bayyana akan katangar wannan fadar dai-dai gefen wannan hankaka. Yana bayyana ya miƙa hannu ya damƙe jelar hankakan tare da finciko shi da niyyar jefashi cikin zobensa na sihiri.


To amma bisa mamaki sai Armad yaji tamkar ya finciki dutsen uhudu. Ko motsi wannan baƙin hankaka baiyi ba. Hasalima kaɗa jelarsa kawai yake ba tare da ya waiwayo ya kalli Armad ba. 


A fusace Armad ya sanya ƙarfin shekarun izza dubu a hannunsa ya finciko hankakan dashi. Amma bisa mamaki ko motsi baƙin hankakan baiyiba. Armad ya haɗe gira yana tunanin maiya kamata yayi domin dai bazai iya amfani da hannun-aradu ba a wannan hali. Koba komai duk wanda yaji ƙarar saukar aradu wajen zai taho yaga ganshi, wanda hakan zai tona masa asiri.


Armad na cikin tunani yaji jelar hankakan dake hannunsa ta motsa ta fincike shi. Kafin yayi wani abu hankakan ya jashi ƙasa daga saman wannan katanga sun faɗa cikin babban gidan sarautar daular Sisiya. 


Saida suka kwashe daƙiƙu suna faɗawa sannan suka isa ƙas, badan Armad yayi sauri ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya ba da tuni ya karairaye. Kafin ya miƙe hankakan ya tashi ya gudu. Armad ya tsaya yana nazarin wannan katanga. Kaurinta yakai ƙafa goma, kuma dukkaninta da duwatsu aka sarrafa ta. A tsaye kuwa takai zira'i casa'in. Lallai koda kuɗi ɓarawo bazaiyi ƙoƙarin haura wannan katanga ba. 


Yana cikin haka yaji motsin tafiya daga nesa haɗe da maganganu wanda sukai kama dana masu tsaron fadar. Nan take ya rufe ido domin jin yanayin izzarsu da kuma adadinsu da kuma ta inda suke tahowa. Amma bisa mamaki abu na farko da Armad ya fara ji wata sanyayyar izza ce mai ni'ima da faranta rai daga can gefensa ɓangaren arewa. 


Ya waiwaya ɓangaren tare da buɗe ido. To amma wajen cike da yake da bishiyun goba dana inubi wanda sukai masa duhuwa tayadda baza'a iya ganin wanda ke ciki ba daga nesa. 


Amma bisa mamaki Armad ya gane waye aciki. Murmushi kawai yayi tare da nufar wannan waje kai tsaye. Ƙanshi ne ya fara yi masa sallama, ƙanshin da yasha banban dana turare. Wannan ƙanshi mutun ɗaya ne kacal yake da irinsa a duk faɗin duniya. 


Armad ya tsaya kimanin taku uku kafin ya ƙarasa. Nan fa zuciyarsa ta fara bugawa kamar zata fasa ƙirjinsa. Bashi da cikakkiyar masaniyar maike faruwa amma yaji gumi na ƙoƙarin kwace masa. 


Sanyayyar murya wadda Armad ƴasanta sarai ita ce tayi masa sallama. "Mai yasa ka tsaya?" 


Armad ya fashe da murmushi ba tare da yasan dalili ba, ya amsa da cewa, "Mai yasa kike tsaye a duhu?"


Muryar ta amsa masa da cewa, "ka bani kunya daka kasa kama hankaka guda ɗaya tak."


Armad ya fashe da dariya yana cewa, "dama ke kika turoshi. Nasan zaki aikata. Amma meye alaƙar ƙabilarku da Hankakan-mutuwa?"


Muryar taja dogon numfashi tare da yin ƴar ƙaramar dariya sannan ta fito daga cikin duhun. Kyakkyawar sura wadda babu kamarta ce ta bayyana. Wato gimbiya Zahra wadda aka fi sani da Nostaljiya Nára. 


"Baka yarda zoben dana baka ba kenan."


Armad ya kalli zoben dake hannunsa sannan ya ɗago kai ya dube ta ya ce, "kona mutu dashi za'a binne ni."


Nostaljiya na sanye da doguwar riga mai kwalliya da bezar gashin farin aku. Jikinta kamar lokaci na ƙarshe da Armad ya ganta acikin wancan kogo haske kawai yake yana bada ƙawa da armashi. Gashinta na kwance har gadon bayanta babu abinda yake sai sheƙi da ƙanshi. Babu kalmar da tafi dacewa da wannan gashi illa mudubi domin tsaf zakai kwalliya kana kallon kanka acikinsa.


Armad ya buɗe baki zaiyi magana sai yaji masu gadin fadar sun matso kusa saboda haka ya fara lisaafin neman wajen ɓuya.


Koda Nostaljiya ta fuskanci haka saita jashi izuwa cikin duhuwar wannan bishiyu. Da farko Armad yayi tunanin ɓuya zasu yi har sai ma'aikatan sun wuce amma sai kawai yaga sun wuce izuwa wata siriyar hanya wadda ta ɓulle izuwa wani shinge mai kama da lambu. Baki a buɗe Armad yaci gaba da kallon ikon ALLAH a yayinda Nostaljiya take jansa izuwa tsakiyar wannan fada. 


Abin mamaki ko mutun ɗaya basu gani ba a hanyarsu. Amma idan akai duba da cewa wannan fada gidan Nostaljiya ce kuma anan ta taso to ba abin mamaki bane. 


Ba daɗewa Armad ya tsinci kansa a wani kewayayyan sashi mai dogayen ɗakuna wanda aka gina bangwayensu da gilasai da yaƙutu. Dukkan wajajenda suka wuce babu wanda yakai wannan waje kyau da armashi. Hatta ƙasar wajen da lu'u-lu'u aka shimfiɗe ta. Nostaljiƴa taja Armad ɗaya daga cikin manyan ɗakunan dake kewaye da wajen. 


Suna shiga Armad ya tsinci kansa akan wani farin gilas da ruwa garai-garai yana gudana a ƙasansa. Kifaye masu haske kyawawa suna ta wasa acikin ruwa. Daga can gefe kuma wani ƙasaitaccen ƙaton gado ne wanda zai iya ɗaukan mutun aƙalla hamsin. Armad yai duba izuwa manyan gilasan da suka kewaye ɗakin inda ya hango wani ƙasaitaccen lambu a bayan ɗakin. Wata iska mai armashi na ƙarawa yanayin ni'ima. Nan take Armad ya tabbatarwa kansa bai taɓa tsintar kansa a waje mai kyawu da armashi irin wannan ba a rayuwarsa ta duniya.


***

Babi na 97: Sammaci 


Nostaljiya ce fara magana. "Ka jira ni anan ina zuwa." Sannan ta fice cikin sauri, tun yana hangen jar doguwar rigar data saka har ya daina. Ajiyar zuciya kawai yayi sannan ya faɗa kan wannan hamshaƙin gado wanda tunda yake bai taɓa yin arba da kamarsa ba a tsahon rayuwarsa. 


Abu kamar wasa jikinsa na dira akai ya nutse cikin laushi ai kuwa sai bacci ya ɗauke Armad. Yayi ta sharar bacci tsahon lokaci har saida rana ta faɗi. A lokacinda yaji muryar Nostaljiya na tashinsa. Da kyar ya buɗe ido yana gani hazo-hazo har dai ya wartsake. 


Bayan Nostaljiya Armad ya kula cewa akwai wasu kuyangi guda bakwai duk sanye da kaya ruwan kasa iri ɗaya sunyi sahu suna ta shigo da kayan ci da sha. Ƙanshi ne kawai yake tashi a ɗakin. 


"Ka tashi kayi wanka kaci abinci. Mahaifina yana so zaiyi magana dakai." 


Da akwai ragowar bacci a idon Armad amma koda yaji abinda Nostaljiya tace saiya miƙe zumbur gami da fara gumi. Ko sirikinka yawon bola yake akace zaku gaisa dashi sai kaji zufa ballantana ɗaya daga cikin mafi girman sarakuna a duniya. 


Cikin sauri Armad ya tambaye ta. "Da gaske kike koda wasa?"


Nostaljiya ta fashe da ƴar ƙaramar dariya wadda ta dace da karfin ikonta. Bangon ɗakin na ɗaukan sautin kyakkyawar muryar ta. Nan take Armad yaji tamkar sarewa ake kaɗa masa. Lamarinda yasa ya faɗa cikin tunani ya manta da cewa shugaba mai dauwamammen sara yana jiransa.


"Ka tashi yana jiranka?"


Koda Armad yaga ga dukkan alamu da gaske take saiya miƙe cikin damuwa ya ce, "lafiya dai ko?"


Nostaljiya ta haɗe rai cike da shagwaɓa. "Nima ban sani ba."


Armad yai ajiyar zuciya a karo na uku sannan ya fara tunanin mai Bihanzin zai ce masa. Lallai da matsala. 


"A ina zanyi wankan? Kuma ni gaskiya..." 


Nostaljiya tayi wa Armad wani kallo mai cike da tsokana tana cewa, "Kai gaskiya me? Ga ƙoramar wanka can ta musamman nasa an haɗa maka." Tayi nuni izuwa wani ƙasaitaccen tafki mai ɗauke da filawowi a samansa. Wani tiriri ne mai alamun ni'ima ke tashi daga saman ruwan. Kana gani kasan an shirya shi ne domin wankan manya ƴaƴan sarauta.


Armad ya juya ya nufi ƙofa yana ta zulumi. Har ya kusa kaiwa ƙofar sai yaji muryarta. "Idan ka fita kasan ta ina zaka zagaya?"


Armad ya juyo fuska a murtuke yana cewa, "to kizo ki rakani mana."


Nostaljiya na ganin yadda yake magana ta ƙara fashewa da dariya tana cewa, "kaci gaba da ɓata rai saina kirawo maka yaya Kiru da yaya Hasanu yanzu-yanzu."


Armad ya buɗe baki zaiyi magana amma ya kasa ganin Nostaljiya ta taho tana rangwaɗa irin ta ƴaƴan sarakunan farko. Kwata-kwata ya manta dasu Kiru da Hasanu. Amma a wannan lokaci ya tuno da fafatawarsu da Kiru shekaru da dama da suka wuce a sanda ya fara fitowa nemawa mahaifiyarsa lafiya.


Can bayan Nostaljiya ta fara jan hannusa izuwa waje ya samu ya tattaro kwarin gwiwarsa ya ce, "Kiru da Hasanu? Da fatan suna nan lafiya? Na daɗe bamu haɗu ba."


Nostaljiya ta amsa da cewa, "ba wani nan. Da yaushe rabon da ka tambayesu? Kai dai kawai tsoron yaya Kiru kake ji. Dan kasan yanzu ya ƙara kwarewa matuƙa a fannin takobi."


Armad na niyyar cewa shima ya ƙara ƙarfin takobinsa Nostaljiya ta fara jansa da gudu suna sassarfa. Duk kwanar da suka sha sai sun haɗu da kuyangi suna hidima, kuma duk wanda duka gansu sai sun zube a ƙasa suna gaisuwa. Nostaljiya ko a jikinta, Armad kuma tun yana amsawa harya gaji. Ga dukkan alamu zuwansa shi ne yasa aka kawo wannan kuyangi da yawa haka domin sanda yazo babu kowa a wajen. 


Suna cikin tafiya Armad yai ciki da wata tukunyar filawa garin ya kauce mata. Nan take ya fara jan hannun Nostaljiya yana cewa, "ki daina gudu. Wai wajen wankan nan tashi zaiyi ne? Kinga ban san hanya ba ina yi muku ɓarna."


Amma Armad na magana Nostaljiya kawai ƙara jansa take tana dariya. "Komai ka fasa zan biya kar ka damu." 


Tun yana zuƙewa har ya saki jiki suka ringa zagayawa suna gudu acikin fadar nan suna shewa kamar wasu yara ƴan shekara goma. Bayan kimanin rabin sa'a suka iso wajen. Arnad ya waiwaya ya hango ɗakin da suka fito daga ciki sannan yaga hanyar da suka biyo, nan take ya gane cewa Nostaljiya na sane ta ringa zagaye dasu ba gaira ba dalili. 


Kamar ta gane mai yake tunani ta ce, "Eh mana. Ina sane na kewaya damu kaga yanzu kasan hanya baza ka ɓata ba. Kayi sauri ka shiga kai wanka tun kafin abba ya turo a ɗaukeka a tafi dakai."


Armad najin wannan kalma ya fara azamar cire kaya zai faɗa cikin ruwan, amma a lokacin ya tuna tana wajen ya juya ya kalleta. "Anan zaki tsaya?"


Nostaljiya ta haɗe rai. "Ko baka faɗa ba tafiya zanyi. Kawai dai kada ka nutse ka mutu ka barni."


Armad ya fashe da dariya a karo na farko yana cewa, "kamar wata ke. Ɗan wannan ruwan ne zai kashe ni, mutuwa ta sai anyi shiri."


"Nidai kayi sauri idan ba haka ba zan dawo na fito dakai." Nostaljiya ta juya ta fice.


Armad ya jira yana murmushi har saida ta ɓace sannan ya ƙarasa cire kayansa ya afka cikin tafkin ya fara iyo. Ruwan ya kasance mai ɗumi dai-dai wanka. Sannan yana bada wani ƙanshi mai inganci. Filawowin kai kuwa na bada wani sinadari mai kama da sabulu wanda nan take ya wanke jikin Armad tas. Idan ta shawarar Armad ne kada ya futo daga cikin wannan daddaɗan ruwa har sai ya nutsu amma sarki na jiransa.


Ba shiri ya fito ya maida rigarsa. Akan hanyarsa ta dawowa ya fara tunanin wanne kaya zaisa yaje dasu. Tambayoyi sama da ɗari suna ta yawo akansa akan menene dalilin da yasa Bihanzin ke nemansa. Kowanne dalili ya tuna sai yaji zuciyarsa ta buga. A lissafin Armad wannan ba wani abu bane illa sammaci. 


Cikin ƙanƙanin lokaci ya dawo ƙofar ɗakin daya kwanta aciki ɗazu. Yana shiga yai arba da Nostaljiya zaune tana jiransa zagaye da abinci.


"Na baka minti goma ka shirya. Idan ka dawo kaci abincin."


Armad ya zare ido cikin sauri yana cewa, "Yunwa nake ji fa."


Nostaljiya ta canja fuska sannan ta fara magana cikin shagawaɓa. "Yana jiranka fa."


Armad bai san sanda ya sanya kaya cikin ƴan daƙiƙu ba ya bita suka nufi nufi cikin fadar. Ranar da zaiyi arba da mai dauwamammen sara tazo.


***

Babi na 98: Armad da Bihanzin


Haka Armad da Nostaljiya suka yita keta cikin wannan fada suna wuce manyan gine-gine masu fasali daban-daban. Nostaljiya na ƙoƙarin yiwa Armad hira amma hankalinsa baya wajen harta gaji tayi shiru. Bayan wani ɗan lokaci suka iso harabar wani ƙaton ɗakin taro da aka kewaye da mutun-mutumin mutane kala-kala.


Nostaljiya ta nuna ƙofar ɗakin tana cewa, "shiga ka jira aciki ina zuwa." 


Armad ya nufi ƙofar ɗakin ita kuma ta kewaya tabi hanyar da tabi ta bayan ɗakin. 


Ɗakin nada madaidaicin girma amma abubuwan dake cikinsa basu da yawa. Wani ƙaton teburi ne kewaye da kujeru a tsakiyar ɗakin. Ga dukkan alamu wannan ɗaki kullum acikin kula yake domin ko ƙura ɗaya babu. Komai kyalli kawai yake, shi kansa teburin na gilashi ne. Armad ya ja kujera ɗaya ya zauna yana jiran shigowar mai dauwamammen sara.


Ba jimawa saiga Hasanu Sisiyu, yayan Noltaljiya, ya shigo. Fuskarsa babu murna kuma babu ɓacin rai. Ya dubi Armad ya ce, "kwana da yawa. Da fatan kana lafiya."


Muryar Hasanu na nan ɗauke da ƙarfi da girma irin na sarakuna. Fuskarsa ta ƙara cika da kamala, kana ganinsa kasan ba'a zaune yake ba.


Armad ya amsa da cewa, "ina nan lafiya. Da fatan na same ku lafiya?"


Hasanu ya nemi waje ya zauna sannan ya dubi Armad ya ce, "bari na baka shawara a matsayi na na abokinka. Kada kayiwa mahaifinmu ƙarya domin duk abinda zaka faɗa zai san gaskiya kake faɗa ko ƙarya."


Armad yai murmushi. "Ai dama bana shirin yin ƙarya."


Hasanu ya girgiza kai kafin daga bisani yai murmushi sannan su koma hirar takobi. Hasanu yayi ta yiwa Armad tambayoyi akan fasahar takobinsa shima Armad yana masa har dai suka ji an buɗe ƙofar ɗakin. Wani babban mutun sanye da doguwar riga ƴar shara ya shigo cikin ɗakin. Nostaljiya na tafe a bayansa. Yana shigowa Hasanu ya miƙe tsaye tare da durƙusawa, shima Armad ya miƙe ya bashi girmansa.


Mutumin na tafiya kamar ba tafiya yake ba, ƙafafunsa na motsawa cikin isa da iko irinta sarakunan aljanu. Idanunsa tsaye suke kan Armad yana nazarinsa. A tsaye zaka iya cewa wannan mutun ragowar samudawa ne domin aƙalla yakai zira'i ashirin. Wanda hakan ya ninka tsayin Armad sau wajen takwas. 


Yana shigowa ya nufi kujerar da aka tanada domin sa wacce ke gaba da dukkan sauran kujerun.


Yana zama Hasanu da Nostaljiya suka fice suka barshi da Armad. Wannan mutun dai ba wani bane illa Bihanzin mai dauwamammen sara, ɗaya daga cikin sarakuna biyar na Jinzidal. Mutuminda akai ittifaƙi takobinsa tafi kowacce takobi ƙarfi a duniya. 


A wannan lokaci Armad ya nutsu tare da tsayawa yayi wa Bihanzin kallo na tsanaki. Bihanzin dai ya kasance mutun ne wanda kana kallonsa zaka san yayi matuƙar daɗewa a duniya. Idan kana kallonsa zaka ga tamkar shekarun ƙarni-ƙarni ne ke wucewa ta ruhinsa. Idanunsa a kafe suke kuma suna bada wani haske mai ɗauke da firgici da saka jimami. Fuskarsa nada tsayi da faɗi kamar dukkan jikinsa, sannan kuma cike take da farin gemu. Gashin kansa ma fari ne dogo mai tsayin gaske wanda har bayansa yake taɓawa. Hatta shi kansa gashin girar Bihanzin a lanƙwashe yake zubin takobinsa.


Rigar dake jikinsa doguwar ƴar shara ce wadda ta bashi damar saƙale takobinsa a sauƙaƙe. Armad na ganin takobin nan yaji hankalinsa ya ɗugunzuma, tsigar jikinsa na tashi. Yanayin-izzar dake kewaye da takobin iri ɗaya ne sak dana Hankakan-mutuwan da Armad ya gani. Nan take Armad ya miƙa hannunsa kan takobinsa ba tare da ya sani ba. Tuni Armad ya manta da inda yake, babu abinda yake tunawa sai labarin da mahaifiyarsa ta gaya masa akan waccan ƙabila wadda aka manta da sunanta. Ƙabilar da tarihi ya nuna cewa saida ƙabilar Wilbafos da ƙabilar Ururu suka haɗa hannu da ƙarfe sannan suka ga bayanta. 


"Kada ka damu da takobi na. Ita wannan takobin tawa babu wanda take yadda dashi idanba ƴaƴa na ba." Muryar Bihanzin ce ta farfaɗo da Armad daga tunanin daya shiga. Amma duk da haka bai ɗauke idonsa daga kan takobin ba.


Takobin dai bata da faɗi da yawa amma tafi tsayin zira'i uku. Lallai ba daban Bihanzi basamude bane da bazai iya ɗaukanta ba. Abin mamakin shi ne takobin har wani huci take tana kallon Armad tamkar tana jin mai ake cewa. 


Koda Bihanzin yaga Armad bai daina kallon takobin ba sai yaja rigarsa ya rufe ta yana cewa, "sunan wannan takobi tawa Bankái. Indai ka biya ta Bankái haka zatai ta tsokanarka har sai ta jaka izuwa faɗa."


Mamaki ya ƙara rufe Armad yadda yaji Bihanzin yana maganar takobinsa yana bata suna kamar wata mai rai. Nan take Armad ya tuna yadda yayarsa Hidaya take yiwa takobinta magana. A sau da dama Armad yana yaro yakanyi tunanin ko Hidaya tsokanarsa kawai take amma takan ce masa takobin ta tana da ruhi nata na kanta kuma tana ji idan akai mata magana. 


Armad yai murmushi na girmamawa sannan ya ce, "barka da warhaka. Ina fatan ban ɓata maka ƙa'idarka ba dana shigo fadarka ba tare da izini ba."


Bihanzin yai gyara murya haɗe da girgiza kai, lamarinda yasa muryar tayi kama da ana goga busasshen ƙashi a jikin bango. Dama dai muryar Bihanzin kaushi ne da ita, amma gyaran muryar da yayi shi ne yasa abin ya ƙara fitowa fili. A wannan lokaci Armad yayi ƙoƙarin jin yanayin-izzar Bihanzin amma bisa mamaki baiji komai ba sai wani sanyi mai ratsa ƙashi wanda ya banbanta da sanyin-babban-sihiri kuma ya banbanta da sanyin hunturu ko na ƙanƙara. Wannan sanyin da Armad yake ji yafi dana tsohon kabari. Nan take Armad ya daina ƙoƙarin jin yanayin-izzar Bihanzin amma duk da haka saida yaji ya fara rawar ɗari. 


Muryar Bihanzin ce ta ƙara farfaɗo dashi. "Kada ka damu, Magajin Wilbafos, tunda har ka shigo ba tare an kama ka ba ai gayyato ka akai." 


Armad ya zare ido cikin mamakin wannan magana, domin hakan na nuna Bihanzin na sane da shigowarsa. Nan take Armad ya buɗe baki zai tambayi Bihanzin amma sai Bihanzin ya riga shi magana.


"Nakan ji yanayin-izzar abokan gaba tsahon tafiyar shekara guda tun ina ɗan shekara bakwai. A lokacin da na cika shekara takwas ina iya banbance mutane na gane ko su waye ta hanyar yanayin-izzarsu koda nisansu da inda nake yakai tafiyar shekara guda. Kaga bazai zama abin mamaki ba dan naji shigowar ka daula ta a lokacin da ka sauka daga jirgin Fataken-dare."


Armad ya zare ido cikin tsananin al'ajabin ƙarfin izzar wannan halitta dake gabansa. Lallai ba'a zama sarkin Jinzidal a banza. Koda yake dama wannan shi ne karo na farko da Armad yai arba da ɗaya daga cikinsu. 


Idan dai har Bihanzin zaiji yanayin-izzar mutun kimanin nisan tafiyar shekara guda kuma ya gane waye, lallai babu wanda ya isa ya shigo wannan daula ba tare da saninsa ba. Kuma lallai ba abin mamaki bane dan Bihanzin yasan Armad shi ne Magajin Wilbafos. 


Kai tsaye Armad ya bugi ƙirji ya tambayi Bihanzin. "Mai kake buƙata daga gareni daka bari na shigo?"


***

Babi na 99: Cikakken Mutun


"Hmm... " Bihanzin yaja dogon numfashi sannan yaci gaba da bayani. "Wilbafos kai kake neman wani abu a waje na ba ni nake nema a wajenka ba. Zaka sauƙaƙa mana wannan tattaunawa idan ka gayamin hakikanin mai ya kawo ka daula ta."


Armad ya sunkui dakai yana tuno asalin abinda ya kawoshi wannan daula. Koma meye a bayan samarwa mahaifiyarsa lafiya yake kuma lallai abinda kawai ya kawo shi kenan. "Nazo neman shekarun izza domin yiwa mahaifiyata wadda take fama da cutar izza magani." 


Bihanzin ya danyi shiru kafin daga bisani ya ce, "Naji labarin cewa abinda ya fito dakai daga gida kenan shekaru uku da suka wuce. Indai wannan ne kaɗai buƙatarka to babu matsala, a yanzu zan warkarda mahaifiyarka. Koba komai bai wuce biyan bashi ba, domin har yanzu bamu biyaka fassarar dakai mana ba a waccan shekara."


Armad ya zare ido tare da miƙewa tsaye cikin murna yana cewa, "da gaske kake? Lallai idan ka samarwa mahaifyata lafiya bani da yadda zanyi na iya sakamaka. Nagode." 


Bihanzin ya ɗaga hannu yana dakatar da Armad alamun bai gama magana ba. "Nasan akwai soyayya tsakanin ka da ƴata Nostaljiya, kuma bazan ce maka ka haƙura ba indai kana sonta, amma akwai abu guda ɗaya da nake so ka sani." Koda Bihanzin yazo nan a zancensa sai ya dubi Armad a nutse domin ya tabbatar yana tare dashi sannan yaci gaba. 


"Shi CIKAKKEN MUTUN shi ne wanda yake ɗaukan alhakin abu idan yasan shi ya jawo shi. Nostaljiya ta ɗau alhakin abinda ta aikata a wajen cinikin bayi kuma taƙi yadda a ɗora maka laifi. Idan za'a wanke ta a idon duniya to sai dai ta yadda ta auri Deniz Bizaya wanda a zahiri ba shi take so ba. To amma idan bata aure shi ba, hukumar Jinzidal zata yanke mata hukunci. Hatta ni kaina a matsayi na na babanta bazan iya kare ta daga sauran sarakunan Jinzidal ba, kuma idan na hana ayi mata hukunci, yaƙi ne zai afku. Idan kace kana sonta, shin zaka iya zama cikakken mutun ka ɗauki alhakin komai a kafaɗunka ka kare ta, kuma ka shiga yaƙi saboda ita? Idan dai har zaka iya wannan to ka cancanci ƴata, amma idan baza ka iya ba to ka manta kawai. Biyo ni." Bihanzin ya miƙe ya nufi ɗaya daga cikin ƙofofin dake kewaye da wannan ɗaki, Armad na biye dashi. 


Bihanzin na tunkarar ƙofar ta buɗe, Armad ya tsinci kansa a wani ƙaton fili mai yawan rairayi. Abin mamaki iskar dake kaɗawa acikin wajen ta banbanta data cikin dakin daya baro, tamkar wata duniya ta daban suka shiga. Take saboda sanyi Armad ya tuna da cewa yana da kayan sanyi a ajiye acikin zobensa. Amma kafin ya fito dasu sai kwatsam yaji yanayin ya fara canjawa, rairayin ya fara ɗaukan zafi kamar ana kunna masa wuta. Kafin kace meye wannan gumi ya fara gudu a fuskar Armad. Suka ci gaba da tafiya Bihanzin bai ce masa komai shi kuma bai tambaya ba. Amma abu kamar wasa taku bakwai bayan an fara zafin kawai sai ruwa ya ɓarke kamar da bakin kwarya.


Armad ya tsaya ido a zare yana mamaki. Lallai akwai abin al'ajabi a tattare da wannan waje. Kuma tashin hankalin shi ne bai san inda Bihanzin yake ƙoƙarin kaishi ba. Yana cikin tunane-tunane yaji murya Bihanzin, "A cikin wannan waje duk bayan minti ɗaya yanayi yake canjawa. Kaga maimakon zafi da sanyi da damina da rani kowanne yazo a shekara sau ɗaya, kowannensu a wannan waje yana zuwa a kowacce rana sau dubu uku da ɗari shida. Acikin wannan waje nake ajiye wani kaso daga cikin shekarun izza ta na kwangila ta. Ban san shekara nawa mahaifiyarka take buƙata ba amma nayi maka alƙawarin bata shekarun izza dubu goma zuwa ashrin. Fito da ita ka ajiye ta anan."


Bihanzin ya nunawa Armad tsakiyar yashi inda ruwa ya ɗan taru. Da farko Armad ya fara mamakin yadda akai Bihanzin yasan mahaifiyarsa na cikin zoben dake hannunsa amma kuma ya tuna komai ma zai iya faruwa indai ana maganar sarki Bihanzin sabida haka babu wani abin mamaki. Nan take Armad ya futo da mahaifiyarsa sanye cikin fararen kaya kamar tana bacci. Amma yaƙi yadda ya ajiƴe ta a ƙasa har saida Bihanzin ya tafa hannunsa wani gado ya bayyana.


Bayan wasu ɗalasimai da Bihanzin ya kira a zuci sai kawai wani ƙatoton shaiɗanin aljani ya bayyana. A tsakiyar kan aljanin akwai ƙahunhuna guda bakwai, sannan yana sanye da wata baƙar hula da aka sarrafa da fatar aljanu zalla. Abin mamaki ɗauke a kafaɗun wannan aljani hankakan mutuwa ne baƙaƙe har guda biyu. Yana bayyana ya faɗi yai gaisuwa ga Bihanzin yana cewa, "Ya shugaba na. Mai kake buƙata?"


Bihanzin ya amsa da cewa, "mahaifiyar wannan yaro na fama da cutar izza, ina so ka bata shekarun izza daga ɗaya zuwa dubu ashirin. Iyakacin yadda zai ishe ta ta warke."


Aljanin ya ware samudawan hannayensa guda biyu yana cewa, "An gama ya shugabana."


Nan take wani jan haske mai ɗaukar ido ya fara taruwa a hannayen wannan aljani kafin daga bisani ya karkatar da hasken izuwa gare ta. Hasken na taɓa ta jikinta ta fara girgiza kamar mai farfaɗiya. Armad yai wuf zai riƙe ta amma Bihanzin ya riƙe shi yana cewa, "Kada ka damu, shekarun Izza ne ke shiga jikinta."


Haka Armad ya haƙura yana kallon mahaifyarsa wannan jan hasken na shiga jikinta tsahon lokaci. Saida akai sa'a guda acikin wannan hali sannan hasken ya ɗauke, aljanin ya dubi Bihanzin ya ce, "An gama ya shugaba na. Na bata shekarun izza dubu goma sha huɗu da dari biyu da sha uku, kuma a lissafi na zata farka nan da wata tara."


Cikin sauri Armad ya durƙusa a gefenta yana share mata gumi. Yana cikin haka kawai sai yaga a karo na farko acikin shekaru uku mahaifiyarsa tayi motsi. Cikin murna yai ihu yana niyyar yin tsalle yai shewa kawai sai yaga ta buɗe ido. Ta kalli Armad, Armad ya kalleta. Nan take hawaye ya fara zuba daga idanunsa. Ta buɗe baki zatai magana amma kafin tayi magana saita ƙara komawa ta suma. Amma duk da haka murnar Armad bata ragu ba. 


Yana cikin haka yaji muryar Bihanzin a kunnensa. "idan ka daɗe da yawa acikin wannan waje komawa duniyar daka fito zaiyi maka wahala."


Armad najin haka ya maida mahaifyarsa cikin zoben sannan cikin murna da annushuwa irin wadda ba'a taɓa ganinsa aciki ba ya biyo bayan Bihanzin suka nufo waje.


Koda suka dawo cikin wannan ɗaki sai suka tarar da Nostaljiya na tsaye tana jiransu. Tana ganin murnar dake fuskar Armad ta fashe da murmushi, lallai tasan an samu abinda ake nema. Koda Bihanzin yaga haka saiya dubi Armad ya ce, "Ni zan barku anan. Ka tuna da abinda na gaya maka. Ka zama CIKAKKEN MUTUN."

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...