Garin Jékis
***
"Ku canja shiri." Inji Deba Liyurul Linbul. "Ana sane aka bani tsaron wannan gari. Kada ku taɓa tunanin sa'a ko ƙaddara zata sa kuyi nasara akaina."
Iliyasisi da Cokali sun gwada kwarewarsu. Munga yadda Cokali ya haɗa fasahar marubutan farko da aljanin sa A'Barmushe, da kuma yadda Iliyasis ya kira aljanin sa Jurnutu, amma duk a banza.
Ganin hakan yasa sarkin duba Babara ya janyo sandar sa ta tsafi. Yana niyyar shigewa gaba ya afkawa deban amma Nostaljiya ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu. Ta shige gaba kai tsaye. Babara dasu Cokali suka ja da baya suka bata fili.
Liyurul Linbul da ragowar mutanen sa uku suka zagaye ta. Kowannen su ya zare manyan makamai wanda aka sarrafa da sinadarin yeniy.
Liyuru takobi ce a hannunsa, Hussuil mashi ne, Kanduil fafalo ne, Cunduil wuƙa ce mai sheƙi. Kowannen su yai azama wajen afka mata.
Nostaljiya taja dogon numfashi a nutse, babu alamun firgici ko kaɗan a tattare da ita. Wuƙa, mashi, takobi da fafalo suna gabda cimmata amma ko kaɗan bata firgita ba.
Cikin yadda da kai ta kira fasahar ta. "Idanun Nára."
Tana rufe baki idanunta sukai haske. Baƙin tsakiyar ya koma yalo. Gashin kanta ya miƙe. Abu ne sananne kwakwalwa tana aiki da sinadarin izza na musamman wanda shi yake bawa ɗan-adam damar tunani. A duk sanda aka katse wannan sinadari kwakwalwar mutun zata daina aiki nan take. Za kuma a iya sarrafa wannan sinadari a sawa mutun duk irin tunanin da ake so ba tare da mutumin ya sani ba. Mutane ɗai-ɗai ne kaɗai ke iya sarrafa wannan sinadari - mutanen da aka haifa da baiwar abin. A wasu lokutan mutane irin su Armad da Nusi da Ikenga wanda ba'a haifa da baiwar iya sarrafa wannan sinadari ba sukan iya sarrafa tunanin ɗan adam, to amma ta hanyar ɗalasimi. Saɓanin waɗancan ƴan'baiwa wanda aka halitta da abin. Zaka iya cewa banbancin su kamar banbancin ɗan-gado da ɗan na-koya ne. Shi ɗan-gado a jininsa abin yake. Baya buƙatar wani ɗalasimi. Sannan kuma ƙarfin ikon sa akan fasahar ya banbanta matuƙa dana sauran ɗalasimai.
Idan mai karatu bai mantaba a can baya munga yadda Nostaljiya ta karanta tunanin Armad cikin ƴan daƙiƙu kaɗan ta gano duk abinda yaji acikin allon nan mai ɗauke da sirrin da zai rikita duniya. A yau ma Nostaljiya ta shirya tsaf domin yin amfani da fasahar ta wajen samo musu nasara.
Tana kiran [Idanun Nara] idanun ta suka canja, ta fara ganin sinadarin dake cikin kwakwalen wannan deba guda huɗu. Ba tare da ta ɗaga ɗan'yatsa ba ta tarwatsa wannan sinadari. Take kwakwalen su suka tsaya cak suka daina aiki. Nostaljiya tai tsalle ta fice daga tsakanin su.
Liyuru wanda ke riƙe da takobi yana shirin saran ta ya zarce ya sari Hussuil wanda ke saitin sa. Shima Hussuil ya cakawa Liyuru mashin dake hannun sa. Dukkanin su babu wanda yasan inda kansa yake. Kanduil da Cunduil a saitin juna suke, sabida haka fafalon dake hannun Kanduil ya shige ya ratsa wuyan Cunduil wanda wuƙar sa bata samu damar samun Kanduil ba.
A zahiri duk wannan abubuwan basu isa su kai su ƙas ba. To amma basa iya tunani a halin yanzu. Zaka iya cewa kamar mutun ne aka cire masa kwakwalwa, duk ƙarfin sa babu abinda zai iya. Duk girman deba ba komai bane idan babu kwakwalwa. Haka Liyuru da mutanen sa suka zube a ƙas kamar gawa, ko motsi basa iya yi. Ƴan daƙiƙu kaɗan da suka wuce suke cika baki akan sun shirya, amma a yanzu suna ƙasa basu san halin da suke ciki ba. Idanuwan su a buɗe suke suna ganin komai, to amma kwakwalwar ta daina aiki. Sai dai a juya a kwantar. Deba sun je ƙas.
Cokali abin wasan yara ya zuƙe su cikin littafin sa.
Dama idan ba'a mantaba tuni katangar garin Jekis taje ƙas, sabida haka kai tsaye wannan manzan ni suka afka cikin garin.
Armad da lissafi ya turo Nostaljiya wannan gari. Ya gano cewa Nostaljiya ita ce wacca take da fasaha mafi dacewa ta yaƙi masu zaren Laidan. Tunda shi zaren aikin sa ya haɗa jiki bayan ya rududduge, sannan kuma ya tashi matacce, to amma bashi da iko akan kwakwalwa, sabida haka Nostaljiya ita ce dai-dai dasu.
Kamar yadda aka sani garin Jekis gari ne wanda suke mutunta al'adun iyayen su da kakannin su. Zaka iya ganin hakan tun daga yanayin gine-ginen su wanda basa canjawa. Ginin ƙasa mara bene wanda akaiwa fenti da jar'ƙasa. Kowanne gida yana zaune da gindin sa sabida faɗin ƙasa da ALLAH ya bawa garin. Yawancin gidajen an gina sune a kewaye da babbar fadar garin inda aka ɗaura auren Armad da Nostaljiya. Daga can nesa ƙuryar kudu zaka iya hangen babbar kasuwar garin.
Fadar garin tana nan da fenti ta ruwan ƙasa. Ba'a hango cikin fadar daga waje sabida ko'ina a rufe yake da manyan bishiyu da shukoki na alfarma. A tsakanin fadar da gidajen mutanen garin akwai wasu gine-gine wanda sun fi duk ragowar tsayi. Wannan gidaje na ƴan majalisar sarki ne.
Zaka iya cewa duk mutanen garin tuni sun san abinda ke faruwa. Kusan kowa ya fito waje yana kallon fafatawar, sabida haka sun ga yadda su Nostaljiya sukai nasara. Koda shigar su garin sai aka fara guje-guje. Yawancin mata da ƙananun yara da tsoffi gidajen su suka koma suka turo ƙofa, wasu kuma ƴan tsirari wajen gari sukai da gudu. Amma mafi yawansu makamai suka ɗakko irin su bilugari da muciya da sandan rake da katako suka fito domin su yaƙe su. Hukumar tsaron garin ta baƙin kaya data farin kaya wanda suke aiki a babbar rundunar Bihanzin sune akan gaba. Duk sun tsaya sun kewaye fada. Ko zasu mutu baza su bar wani ya taɓa kayan sarki ba.
Idan ka hangesu daga nesa abin zai baka mamaki. Su kansu ma'aikatan tsaron bai fi Cokali ya bushe su ba, ballantana mutanen gari gama-gari yaku-bayi. Kowa aciki yana riƙe da makamai na wasan yara wanda ko kaɗan babu izza a tattare dasu. Kai kace wannan mutane basu san ba'a shiga faɗan manyan ma'abota izza ba.
Nostaljiya tai ajiyar zuciya. Dama can ta faɗa zasu samu wannan matsalar. Domin duk halin yaudara irin na Bihanzin baya barin mutanen sa da yunwa. Da ɗan daular Sisiya ya kwana da yunwa gwanda a rasa abinci a fada. Nostaljiya tasan wannan. Lokaci-lokaci Bihanzin da kansa ya kanyi shigar bazata ya sa kayan talakawa ya rufe fuskarsa ya ringa zagayawa cikin gari domin ganin mai talakawan sa suke ciki. Albashin ma'aikatansa babu jinkiri. Zaka iya cewa babu mai zagin Bihanzin a faɗin garin Jekis dama daular Sisiya baki ɗaya, koda kuwa a ɓoye.
Nostaljiya ta ƙara yin ajiyar zuciya ta shige gaba gaban ta na faɗuwa. Bata tsoron yaƙi amma tana tsoron boren talakawa. Kaji masu yi dan ALLAH.
Duk garin babu wanda bai san fuskar ta ba. Da dama suna yi mata kallon butulu wadda ta bijirewa uban ta sabida miji. Dalilin hakan kuwa shi ne basu san zahirin abinda ya faru ba. Kuma Bihanzin ta ƙarƙashin ƙasa yayi amfani da ƙarfin kujerar sa wajen yaɗa jita-jita da ƙarairayi akan dalilan da suka saka Nostaljiya ta guje su. Haɗi da soyayyar da mutanen garin suke wa Bihanzin tasa ko kaɗan babu wanda yake wa Nostaljiya kallon ƴa ta gari.
"Suna na Nostaljiya Nara, na zo muku da tausayi cikin lumana da aminci. Abinda kawai muke so shi ne mu hana cinikin bayi. Da Bihanzin da sauran sarakunan Jinzidal basa so ku zama ƴantattu, domin kada..."
Nan take mutan garin suka farai mata ihu suna jifan ta da ledar ruwa.
"Wo wo wo.. Bama yi. Ku koma inda kuka fito."
"Kaji wulaƙanci, sunan babanta take faɗa gatsal."
"Mayaudariya."
"Munafika."
"Sai kinga ƙarshen ki."
"Idan cinikin bayin kuke yaƙa da gaske ku hau sama mana doron ƙasa ta farko. Ko dan kuna tsoron su shi ne zaku zo nan ku hanamu zaman lafiya. To sarki Bihanzin yafi ƙarfin aniyar ku."
Nan take hawaye ya kwace wa Nostaljiya.
Comments
Post a Comment