Skip to main content

318-322

 "TULADAN-NAN-GALAK!!"


Nan take tambarin miyurar Armad ƙatoto ya bayyana kan iska yayi kan Ikenga.


Sauran kiris ya haɗiye Ikenga amma a lokacin aka ji babbar waƙar izza ta fara tashi daga jikin Ikenga. Kiɗa da sauti amma fa samfurin aljanu irin wanda baki bashi iya bayani, kuma kalmomi basu iya bayyanawa. 


Ikenga yayi ƙaraji, "NI ZAN ZAMA SARKI!


Armad ya kaɗa takobin sa sama, yayi kururuwa ya ce, "a mafarki ba."


A dai-dai wannan lokaci suka haɗu da juna. A ɓangaren Ikenga ƙatotuwar rana ce ta baƙin hadari ta tokare sararin sama, hakana a ɓangaren Armad ƙatotuwar rana ce ta Negrinki jajawur. Suna haɗuwa duniya ta fara girgiza. Tartsatsin wuta ya tashi sama ya rufe ko'ina. Abu kamar wasa anyi tunanin abin zai tsaya a haka amma sai aka ga wutar ta haɗiye su, sannan taci gaba da ambaliya tana faɗaɗa. 


Deniz Curu-curu shi ne ya fara ankara da wutar. Kallo ɗaya kacal ya gano cewa wutar ba gama garin wutar tsafi bace. To amma duk da haka yayi imani da ƙarfin izzar ɗalibinsa kuma shugaban sa Ikenga. Lallai yasan Ikenga bazai taɓa zuwa ƙasa ba ko ta wane hali. Yana cikin wannan tunani ne wutar ta bunƙasa ta hadiye Ikenga da Armad. 


A wannan hali na tsaka mai wuya babban sarkin ƙaraiƙisu yai fitar burtu ya shige cikin wutar suka daina ganin sa. Ganin haka suma ba jira sukai linƙaya suka afka cikin wutar domin ganewa idanunsu al'amarin dake faruwa.


Idan muka leƙa cikin wannan wuta zamu ga akwai ɓangarori uku: ɓangare na farko na Ikenga, sai kuma ɓangaren Armad da kuma ɓangaren sarki ƙaraiƙisu.


Tunda daɗewa Ikenga a shirye yake da duk wani hari da Bihanzin ko Armad zasu kawo masa. To amma a har kullum akwai harin da zaka iya cewa yafi gaban shirin mai shirin, sabida irin wannan hari shi yasa ake tafiya da kwamandu domin idan abu ya ɓaci su kawo agaji.


Bari muyi duba na tsanaki izuwa harin da Armad ya aikawa Ikenga. Munga Saif-Al-Barzak, munga Ɗorawa Abada, mun kuma ga ruhin gidan Wilbafos wanda ya fito daga goshin sa, ruhin daya halaka Uznu a shekarun baya. Bayan wannan hare-hare uku akwai wani ɗalasimi mai suna Tuladan-nan-Galak wanda Armad yayi amfani dashi ya samar da ƙatoton hoton miyurar sa akan iska ya kuma harbawa Ikenga shi. 


A ɓangaren Ikenga kuma akwai takobin Yurashira wadda za'a iya cewa babu wanda ya taɓa ganinta tana aiki a wannan zamani. Ita ce takobin daya gada daga Amraikugyu, wadda kuma ya karɓo daga hannun Bihanzin a lokacin yaƙin sarakunan jinzidal ya bashi dalasimin taswirar ƙarƙashin ƙasa. A lokaci guda kuma akwai ruhi ɗai-ɗai har guda biyar tsaye acikin hadarin dake rugugi a bayan Ikenga. Ruhi na farko shi ne ruhin Bayajidda wanda kai tsaye ya kirawo Shaibal-shísu sannan yayi taku bakwai. Take baƙin hadarin dake saitin sa ya juye izuwa farin haske ya tokare da sararin samaniya. 


Ruhin dake kusa dashi na Amraikugyu ne. Shima shuɗin haske ya fara yana gaurayuwa da baƙin hadarin. Kafin kace meye wannan ya shata layi a kusa da farin hasken dake tashi daga jikin Bayajidda. 


Daga gaban sa mace ce mai tambarin miyura wadda ta zare takobi ta nuna Armad. A kusa da ita balbalin wuta ne ke tashi daga jikin halittar nan ta wuta. Sai kuma ruhin ƙarshe na mutun wankan tarwaɗa ɗan kimanin shekaru hamsin. Wannan ruhi rabewa gida biyu yayi. Sannan kowanne acikin su ya ƙara rabewa gida biyu suka zama huɗu. Mutun huɗun suka rabe suka zama takwas, takwas suka zama sha shida, sha shida suka zama talatin da biyu. Bayan ƴan dakiku dukkan naman jikin su ya zagwanye suka zama ƙashi. Kafin kace kwabo tuni ƙasusuwa sun taru sun tokare sama kamar ana dalar gyaɗa. 


Wato a zahiri a wannan lokaci Ikenga ya rikide ya zama majanuni abin tsoro. Daga nesa abinda zaka fara hangowa shi ne baƙin hadari yana kwaranya daga sama kamar ana ruwan azaba. Idan ka matsa kusa zaka ga wasu mutun biyar sun raba hadarin zuwa gida biyar: na farko fari, na biyu shuɗi, na uku baƙi, na huɗu ja, na biyar ruwan ƙashi.


Duk wannan bai isa ba, Ikenga zare Yurashira yayi, sannan yayi ƙaraji ya afkawa Armad. A ɗaya ɓangaren shima Armad tahowa yayi suka haɗu a tsakiya. 


Takobin Wilbafos mai ɗauke da fasahar Ɗorawa Abada ta haɗu da Yurashira. Saif-Al-Barzak ta haɗu da Amraikugyu. Ruhin Wilbafos ya haɗu da ruhin Bayajidda. Tambarin miyurar dake kan iska ya haɗu da macen dake bayan Ikenga. Baƙin hadarin Ikenga ya haɗu da kogin Negrinkin Armad. 


Iskar wajen tayi ƙara sannan kai tsaye ta fara fashewa tana tsagewa kamar ana fasa tangaran. Tsarin fasalin gaskiya da samuwar halittu ya tarwatse. Ana cikin wannan hali mutumin daya koma ƙashi ya juye izuwa basamuden mutun-mutumin ƙashi ya afkawa Armad. A lokaci guda halittar wutar ta sulale ta zagayo ta bayan Armad tana neman haike masa da mugun nufi irin na shaiɗanun Farkon Lokaci. 


Ga Ikenga a gabansa, ga zabgegen mutun-mutumin ƙashi yana kawo masa duka ta gefe, ga kuma wuta ta bayansa. Wannan ita ake cewa tsaka mai wuya.


Armad yai sauri ya zame takobinsa daga jikin takobin Ikenga sannan ya zillewa hannun mutun-mutumin ƙashin, a lokaci guda kuma cikin kwarewa ya sunkuya ya kaiwa Ikenga sara ta ƙasa. Nauyin takobinsa ya hana Ikenga kaucewa akan lokaci inda hakan ya janyo Ikenga yayi asarar ƙafafuwan sa guda biyu. 


Wawan ihu ya ƙwacewa Ikenga, "Aaarghh..." 


Armad na ganin haka yayi wani gwauron numfashi tare da ajiyar zuciya. Lallai haƙansa ya cimma ruwa domin dama sara ɗaya kacal yake nema ya aiwatar. Sauran kaɗan yayi nasara, sauran ƙiris.


Da sauri ya mirgina ƙasa ya gocewa wutar data tunkaro shi ta baya sannan ya miƙe domin ya ƙarasawa Ikenga hukunci. 


Sai dai kuma kash, a dai-dai wannan lokaci ne yaga takobin Wilbafos mai ɗauke da fasahar Ɗorawa Abada dake hannunsa ta haɗu da Yurashira. Saif-Al-Barzak ta haɗu da Amraikugyu. Ruhin Wilbafos ya haɗu da ruhin Bayajidda. Tambarin miyurarsa dake kan iska ya haɗu da macen dake bayan Ikenga. Baƙin hadarin Ikenga ya haɗu da kogin Negrinkinsa.


Iskar wajen tayi ƙara sannan kai tsaye ta fara fashewa tana tsagewa kamar ana fasa tangaran. Tsarin fasalin gaskiya da samuwar halittu ya tarwatse. Ana cikin wannan hali mutumin nan daya koma ƙashi ya juye izuwa basamuden mutun-mutumin ƙashi ya afkawa Armad. A lokaci guda halittar wutar ta sulale ta zagayo ta bayan Armad tana neman haike masa da mugun nufi irin na shaiɗanun Farkon Lokaci. 


Ga Ikenga a gabansa, ga zabgegen mutun-mutumi na ƙashi yana kawo masa duka ta gefe, ga kuma wuta ta bayansa. Wannan ita ake cewa tsaka mai wuya.


Armad ya yamutse fuska. Mai yasa yake ƙara maimaita abinda ya faru yanzu? Abu na farko daya zo kansa shi ne an taɓa tunanin sa, wato Ikenga yayi amfani da fasahar tunani. Nan take ya duba yaga tunanin sa dai-dai yake tafiya babu abinda ya taɓa shi. Daga nan sai yayi ƙoƙarin tsayar da jikinsa amma bisa mamaki ya kasa. Kai kace ba jikinsa bane. 


Bayan ɗan gajeren tunani ya gano mai ke faruwa. 


Wato Armad ya shiga halwar izza sanda yana cikin kurkukun lokaci, kuma ya karanta duk wata fasaha da aka taɓa amfani da ita a duk wani yaƙi da yazo a tarihi. Saboda haka nan take ya gano cewa bawai tunaninsa aka taɓa ba, ba kuma jikin sa aka taɓa ba, wata fasaha ce wadda bai san taba, wata fasaha ce wadda bata da suna, wata fasaha ce wadda ba'a taɓa yin amfani da ita a duniya ba sai a wannan lokaci. 


Yana cikin tunanin yaga hannun ƙashin ya taho gadan-gadan zai dake shi. Dolensa yayi sauri ya zille ta ƙasa sannan cikin kwarewa ya kawowa Ikenga sara ta ƙasa. Nauyin takobin ya hana Ikenga kaucewa akan lokaci wanda hakan ya jawo yayi asarar ƙafafunsa guda biyu. 


Wani wawan ihu ya ƙwacewa Ikenga, "Aaarghh..." 


Da sauri ya mirgina ya gocewa wutar data tunkaro shi ta baya sannan ya miƙe domin ya ƙarasawa Ikenga hukunci. 


Sai dai kuma kash, a dai-dai wannan lokaci ne yaga takobin Wilbafos mai ɗauke da fasahar Ɗorawa Abada dake hannunsa ta haɗu da Yurashira. Saif-Al-Barzak ta haɗu da Amraikugyu. Ruhin Wilbafos ya haɗu da ruhin Bayajidda. Tambarin miyurarsa dake kan iska ya haɗu da macen dake bayan Ikenga. Baƙin hadarin Ikenga ya haɗu da kogin Negrinkinsa. 


Iskar wajen tayi ƙara sannan kai tsaye ta fara fashewa tana tsagewa kamar ana fasa tangaran. Tsarin fasalin gaskiya da samuwar halittu ya tarwatse. Ana cikin wannan hali mutumin nan daya koma ƙashi ya juye izuwa basamuden mutun-mutumi na ƙashi ya afkawa Armad. A lokaci guda halittar wutar sulalewa tayi ta zagayo ta bayan Armad tana neman haike masa da mugun nufi irin na shaiɗanun Farkon Lokaci. 


Ga Ikenga a gabansa, ga zabgegen mutun-mutumi na ƙashi yana kawo masa duka ta gefe, ga kuma wuta ta bayansa. Wannan ita ake cewa tsaka mai wuya.


Ikenga na ganin haka ya fashe da dariyar farin ciki ya cillar da takobinsa ya ɗaga hannu sama cikin murna, "Haha... Nayi nasara akan jinin Ayubul-laisiy!" Murnarsa a fili take domin tabbas yasan yayi nasara kuma babu wanda ya isa ya canja al'amarin, "ni Ikenga ni zan zama babban sarki. Lale marhaban da babban sarki! Lale marhaban, lale marhaban!!"


Koda takobin Ikenga ta taɓa ƙasa sai Armad ya ƙame ƙam ya daina motsi. 


Ikengan kuwa sai shewa yake yana kiran, "Lale marhaban, lale marhaban!"


Armad ya datse harshen sa da hakori sabida baƙin ciki. Jini ya fito ta gefen bakinsa. Wai duk abinda yayi bazai ci nasara ba kenan?! Wai mai ake so yayi ne?


"Kada kayi baƙin ciki, yanzu fa mukai nasara akan Iluru." Inji Saif-Al-Barzak.


Armad ya ƙara cizon harshe. "To waye Iluru? Ni da nake yaƙin ruhi." 


"Haka kace? Iluru sarkin jinzidal ne wanda yayi shekaru sama da dubu a raye yana shiri. Kai fa? Shekarar ka biyar kacal da farawa. Kuma duk da haka muna da sauran shiri, ka daina magana kamar an cinye mu an gama. Ka shirya?!"


Armad yayi ajiyar zuciya. Lallai ba haka yaso ba, amma babu yadda zaiyi.


"Muje zuwa."


Koda jin haka sai Saif-Al-Barzak tayi dariyar farin ciki sannan da bakin ta mai kama da takobi ta kira babban dalasimi, "Wilbafosiyan Siwod Dans!!"


Ikenga yana cikin rawa yana tsalle yana shewa yana kiran 'lale marhaban' kawai yaga Armad ya fara haske. Kafin ya ankara yaga komai ya ɗauke.


***

Ɓangaren Iliyasisi

***


Tafe yake yana sassarfa cikin tunani. Aikin sa ya kula da ƙarƙashin ƙasa inda Bihanzin yake domin kada Bihanzin yayi wani abu. Irin wannan aiki shi aka sa Babara yayi a sashin ikwatora wajen Ikenga. Zamu iya cewa wannan shi ne aiki mafi wahala da aka taɓa bawa wani kwamanda. Kuma babu wanda yasan ko zasu cika wannan aiki ko baza su cika ba.


A dai-dai wannan lokaci Iliyasisi yana bakin dajin ramuka, dajin da ake bi ta ciki domin zuwa biranen ƙarƙashin ƙasa. A can baya lokacin gasar jinzidal munga Armad da Nusi sun shiga cikin wannan rami domin zuwa garin Seerisha na sarki Iluru inda aka gudanar da jinzidal a lokacin. Daga baya munga Ikenga ya shiga ta cikin wannan rami yaje wajen Daddara inda ya karɓo ajiyar Amraikugyu.


"Ina zaka?!" Ɗaya daga cikin masu gadin ya daka masa tsawa. 


A hankali Iliyasisi ya ɗaga kai sannan ya amsa da cewa, "garin Shadeniza." 


"Haa.." mai gadin ya wage baki, "garin Sha... shadeniza?" 


Iliyasisi ya gyaɗa kai alamun eh.


Mai gadin da abokan aikin sa suka fashe da dariya.


"Kai, yaro. Idan neman mutuwa kake to zamu iya baka ita anan ba sai kaje ko'ina ba." 


"Mutuwa?" Iliyasis ya girgiza kai, "a'a, lokacin mutuwa ta baiyi ba. Amma ina ganin alamun mutuwa a fuskokin ku. A har kullum lokacin mutun yakan yi ba tare da ya sani ba. Abin takaicin shi ne baka ganewa sai lokaci ya ƙure kana gabda ƙarasawa."


Koda jin abinda Iliyasis ya faɗa sai masu gadin suka murtuke fuska. Ɗaya daga cikin su ya fara shafa takobin sa yana matsowa kusa. Kafin Iliyasis ya ankara dukkanin su sunyi fitar burtu sun kewaye shi ta ko'ina. 


Har yanzu Iliyasis a nutse yake. "Ku talatin da biyu ne. Koda zaku tarar min ku kawomin hari ta kowanne ɓangare baza kuyi nasara ba."


Kafin ya rufe baki dunkulen walkiya ya fara sauka a kansa. Yayi tsalle sama ya kauce musu amma duk da haka saida suka same shi ta baya a kafaɗar dama. Abin mamaki sai kafaɗar ta guntule ta fadi ƙasa tare da hannun. 


Masu gadin suka gyalgyala dariyar mugunta sannan suka ci gaba da aika masa luguden walkiya. Kafin kace meye wannan jikin Iliyasis yayi daga-daga ya tarwatse. Wani abin mamaki shi ne har yanzu babu jini ko ɗiso. Ana cikin haka jikin sa ya fara juyewa izuwa fararen tsuntsaye. Tsuntsu ɗaya, tsuntsu biyu, tsuntsu uku... Kafin kace meye wannan tsuntsaye barkatai sun bayyana. Sukai fiffike suka tashi sukai kan masu gadin wanda tuni suka zare ido cikin mamakin abinda ke faruwa. 


Babu yadda suka iya dole kowa ya jada baya suka fara ƙoƙarin kare fuskokin su daga tsuntsayen. Sai can daga baya zasu fuskanci cewa hakan ba ƙaramin rashin lissafi bane domin kuwa a lokacin da tsuntsayen suka wuce zasu nemi kawunansu su rasa. Gangar jikinsu na tsaye tana neman kanta a yayinda neman bazai mata amfani ba domin kuwa an fille kan da takobi mai kaifi irin na Farkon Lokaci. 


Iliyasis ya wuce kai tsaye zuwa tantin waɗannan masu gadi ya fara laluben takardun dake ciki. Ba jimawa yana nazarin takardun ya gane cewa hatta su kansu masu gadin basu da masaniyar inda garin ƙarƙashin ƙasa na Shadeniza yake. Zaka iya cewa babu abinda ƙananan bil'adama suka sani a ƙarƙashin ƙasa banda daular denizawa ta Seerisha. To amma kwamanda Iliyasis yasan ba haka bane, yasan lallai akwai boyayyiyar daula a ƙarƙashin ƙasa wadda mutanen dake rayuwa a sama basu sani ba. Kaɗan daga cikin wannan sihirtattun dauloli na karkashin ƙasa su ne garin Shadeniza, garin su Nusi, garin da Bihanzin ya koma. To amma Iliyasis bai san inda garin Shadeniza yake ba, kuma bai san hanyar da zai bi yaje ba. Shi dai kawai aiki Armad ya bashi ba tare da ya gaya masa hanya ba, shi kuma bai tambaya ba. Watakila sabida shi kansa Armad ɗin bai san hanyar ba, watakila kuma ya sani amma saboda wani dalili bai fadawa Iliyasis ba. 


Waje Iliyasis ya samu ya zauna yana tunanin mai ya kamata yayi. Ba jimawa wata dabara ta fado masa inda ya miƙe ya nufi cikin dajin ya nemi waje ya buya. 


Watakila sa'a ce, watakila kuma ƙaddara ce, washe gari da asuba wata tawaga ta iso dajin. Mutun huɗu ne kacal: ɗaya mace, uku maza. Mazan a shirye suke cikin kayan yaƙi amma macen babu kaya a jikinta. Koda yake da dama baza su yadda da Iliyasis kan cewa babu kaya a jikin ta ba, da dama zasu fi aminta da ace akwai kaya a jikin ta amma fa kayan na haske ne. Tun daga inda yake yana ganin hasken dake tashi daga jikin wannan mace kai kace rana ce acikin duhun dare. Ba jimawa ya gano wannan mace tayi matukar kama da matar da Armad ya kwatanta musu mai suna Sarkin-sarki wadda take tare da Bihanzin.


Mazan uku suka duba wajen gefe da gefe kafin su raɗawa macen wani abu. Macen ta gyada kai sannan ta fara tafa hannu tana kiran sunayen fararen aljanu da bakake. 


(Ƙarin bayani: ance idan mutun ya zage ka koda baka jin yaren kana iya gane an zage ka, koda kuwa daga nesa inda baka ji aka zage ka. To shi kiran sunan aljanu kamar zagi yake, kowa yana gane shi komai nisa, saboda haka ba abin mamaki bane dan Iliyasis wanda ke can nesa baya jin abinda suke cewa ya gane Sarkin-sarki kiran sunan aljanu take.)


Bayan macen mai kama da Sarkin-sarki ta kammala kiran sunan aljanun sai kurum ta afka cikin ɗaya daga cikin ramukan. Suma mazan guda uku suka bi bayanta. 


Iliyasis yayi murmushi ya mike daga maboyar sa ya fito ya nufi ramin da Sarkin-sarki ta faɗa. Zaka yi tunanin zai ji tsoro ko kuma ya firgita da ganin Sarkin-sarki, to amma ko kaɗan hakan bata faru ba. A wajen Iliyasis kawai Sarkin-sarki wata hanya ce da zata kaishi ga garin ƙarƙashin ƙasa na Shadeniza inda zai gamu da Bihanzin. Abu guda ɗaya daya tsaya masa a rai shi ne mai ya kawo Sarkin-sarki wajen ita da aka ce tana can tana yaƙi da Deniz Curu-curu da kuma B. Ururu akan boyayyiyar daula? Koda yake shima Armad da yana nan da zai tambayi kansa yaya akai yaga Deniz Curu-curu da B. Ururu tare da Ikenga bayan ance suna yaƙar Sarkin-sarki? 


Babu wani tsoro yana ƙarasawa yayi bakin ramin da yaga sun shiga - rami mai lamba ta 309. Kai tsaye ya danna ciki. 


Watakila mai karatu ya manta amma wannan ramuka kayan tsafi ne. Har yanzu bamu san yadda aka gina su ba, kuma bamu san waye ya gina su ba, to amma tsafin dake jikin su baya tsufa. Al'amari ne na babbar izza. Duk wanda yayi gangancin shiga wannan rami ba tare da goron gayyata ba to ƙarshen sa halaka. Wannan goron gayyata yakan zo ta hanyar dutsen izza wanda mutanen daular denizawa suke bawa mutane idan zasu ƙasar su, ya kan iya zuwa ta wasu sihirtattun hanyoyin wanda bamu sani ba. Koma dai yaya ake ciki zaka iya cewa Iliyasis ya aikata ganganci wajen shiga ramin duk kuwa da cewa an taɓa ganin Ikenga ya shiga kuma ya fito a raye, saɓanin yadda magabata suke tunanin duk wanda ya shiga ya shiga kenan: kodai ya ɓata a rasa shi, ko kuma ya leƙa barzahu, gidan da izza bata aiki.


Abu na farko da Iliyasis ya fuskanta bayan shigar sa shi ne rashin iska mai kyau. Gurbatacciyar iska mai wari da zafi da tururi. Lallai tun anan za'a rufe babin mutun idan karamin mai izza ne. Bayan wannan akwai matsi da rashin sukuni acikin ramin. Faɗin sa baifi zira'i biyu ba, sabida haka dole kai da gangar jiki su bugu su fashe, watakila jini ya haɗu da ƙwaƙwalwa a suma. Abu na uku akwai wani sihiri wanda yake hana amfani da yanayin izza, ta haka babu wata hanya da zaka iya sanin ina zaka faɗa, sai dai kurum kayi ta tafiya acikin duhu har ka isa. Banda wannan akwai tsananin fargaba da faduwar gaba da baƙin ciki da kuma rashin tabbas wanda mutumin dake fadawa zai fuskanta. Lallai wannan ramuka sun cika da sihiri madaukaki.


Iliyasis ya buɗa hannayen sa yayi ƙoƙarin riƙe bangon domin rage gudun da yake. Ance rashin sani yafi dare duhu. Yana taɓawa yaji kamar ya taɓa narkakken dutse. Zafi irin wanda izza bata korewa ya shiga jikinsa yasa ya fara rawar ɗari. To amma abinka da wanda ya kai matakin kwamanda, nan take ya murje ya buɗe idon sa, sannan ya saita jikinsa a tsakiyar ramin aka ci gaba da tafiya. 


Zurfin wajen ya wuce duk yadda bil'adama zai iya tunani. Amma a haka Iliyasis yaci gaba da faɗawa ƙasa yana kaucewa duwatsu da ramuka da ɓanɓorai a yayin tafiyar. Babban abinda kowa ya kamata ya gane shi ne ƙasan ramin ba'a sumulmule yake ba, saɓanin saman. Amma duk da haka ko a jikin Iliyasis, tafiya kawai yake cikin umarni.


Sa'o'i suka wuce ana abu guda amma babu alamar zaiga ƙarshen ramin. Bayan tsahon zamani, bayan Iliyasis ya fara ɗebe haso, sai kwatsam ya fara hango haske a ƙasansa. 


Ya miƙa hannu kan takobin sa sannan ya ƙaddamar da izzarsa domin shirin kota-kwana. 


Koda yazo wajen hasken sai ya fuskanci ƙarshen ramin ne. Nan take murna ta kama shi ya fara tunanin mai zai tarar a ƙasan. Sai dai kuma kafin ya gama tunanin anyi jifa dashi waje da ƙarfin tsiya. A wannan lokaci Iliyasis (dama duk wani wanda ya shiga cikin wannan ramuka sukan yi ƙoƙarin tare wannan izza take jifa da mutane to amma abin yafi karfin su), dole haka kowa yake haƙura a cillo shi waje. Kana fitowa zaka tsinci kanka a tsakiyar gajimare. 


Kamar yadda Iliyasis yana fitowa ya ganshi acikin gajimare yana iyo. Kafin ya ankara ya fara fadowa ƙasa. Babu abin riƙewa haka dole ya haƙura yaci gaba da fadowa ƙasa tsahon rabin sa'a kafin ya fara hango ƙasa. 


Iliyasis ya wage idanunsa yana mamakin irin ƙasar da yake hange. Babu tsiro ko guda ɗaya a kanta, kuma babu gida gaba babu gida baya, sannan kuma fara ce fat kamar farar ƙasa.


Yana dira ƙura ta tashi ta turnuke ko'ina. Bayan komai ya lafa Iliyasis ya tsinci kansa tsaye a fili fetal shi kaɗai babu wata halitta. Ya duba gabas da yamma, kudu da arewa amma babu wani alamun gida ko kuma rayuwa. Bai san a inda ya tsinci kansa ba ballantana yasan inda zashi. Yayi tunanin idan ya bayyana zai ga hanyar dasu Sarkin-sarki suka yi ya bisu amma babu labari. Bayan ɗan gajeren tunani Iliyasis ya yanki hanya ya fara tafiya. Saida ya shafe kwanaki yana abu ɗaya. Idan ya gaji da taku saiya juye izuwa tsuntsu yayi tayi, baji ba gani. Kwanaki shida da fara tafiya ya fara hango wata katanga ta farin ƙarfe a can nesa. Nan take farin ciki ya cika zuciyarsa. Burinsa kurum ya samu muƙulwar ruwa yasa a bakinsa. Yau sama da sati kenan babu abinda ya shiga bakinsa: ba abinci ba abin sha. 


Yaci gaba da tafiya a hankali har ya iso bakin garin. Saboda yunwa ko kaɗan bai damu da zai iya gamuwa da wani sharri ba. Indai zai samu ruwa to koma meye daga baya ne. Sabida yunwa Iliyasis bai kula cewa katangar garin ta ƙarfe bace, dan kuwa babu wani gari da yake gina katangar karfe a duniyar mutane a wannan zamani, ko kaɗan bai kula cewa a kan hanyar shiga akwai takubba da masu da kibbau zube a ƙasa ba. Shi dai ya samu ruwa ya sha. 


Yana isowa yaje bakin ƙofar ya kwankwasa. Ya fara a hankali amma daga ya fara da ƙarfi da ƙarfi. Kam kace kwabo ya kwankwasa har sau biyar a jere. Koda ya tabbatar baza a buɗe ba sai ya fara tura ƙofar yana ƙoƙarin budewa. 


Yana cikin wannan hali ne yaji an daka masa tsawa, "KAI!" 


Sai dai kuma tsawar ba daga cikin garin ta taso ba, daga waje take bayan sa. Firgigit ya juyo amma abin mamakin shi ne wajen ba kowa sai shi kaɗai amma kuma yana jin magana. 


"Waye?"


Kamar ana bashi amsar tambayarsa sai wajen dake gabansa ya fara juyawa yan haɗewa kafin daga bisani wasu mutane huɗu su bayyana. Wannan mutane ba wasu bane illa... Sarkin-sarki da mutane uku dake tare da ita, wanda Iliyasis ya gani sun shigo ramin ya biyo su. 


"Yaya sunan ka?" Sarkin-sarki ta tambaye shi. 


A lokaci na farko a rayuwarsa yayi arba da macen da tafi Nostaljiya kyau (a ganinsa), amma maimakon yaji taushi a ransa wani sabon firgici ne ya saukar masa. 


Tuni Iliyasis ya riga ya gama yanke shawarar mai zaice a irin wannan yanayi. Dole ya ɓoye sunansa da asalinsa domin ɗan leken asiri ne shi. Sunan ƙarya zaiyi amfani dashi ya ce musu shi matafiyi ne yan'uwansa suka cuce shi suka kwace masa kuɗi, sannan suka jefa shi cikin ramin badan yana so ba. To amma duk wannan lissafin yana yin ido biyu da Sarkin-sarki babbar fasahar Kamalar-ruhi tayi aiki a kansa. 


Maimakon ƙaryar daya shirya zaiyi sai ya amsa da cewa, "suna na Iliyasis." 


Iliyasis? Ta yamutse fuska.


"Mai yasa kake bin mu?"


"Shugaba Armad ne ya turo ni nayi masa leken asiri a ƙarƙashin ƙasa daular Bihanzin."


Ana yi masa tambaya yana amsawa cikin ladabi.


"Meye alaƙar ka dashi wannan shugaba Armad ɗin?"


"Shugaba na ne."


Sarkin-sarki najin haka ta ɗanyi shiru na ɗan lokaci kafin ta gyadawa na kusa da ita kai. Nan take suka shige gaba suka zagaye Iliyasis. Iliyasis ya miƙa hannu zai kai musu hari amma suna haɗa ido da Sarkin-sarki ya fasa. Ikon ta shi ne kaɗai iko a wajen. 


Nan take suka ɗaure Iliyasis suka ajiye shi a gefe suka juya suka fuskanci katangar ƙarfen. 


Abin mamaki kawai sai Sarkin-sarki ta ware hannu, ta jada baya ta taho a guje ta daki ƙofar da dukkan ƙarfin ta. Ƙasa tayi girgiza kamar zata tsaye amma ƙofar na nan daram-dam bata buɗe ba. 


"Tsk.." Sarkin-sarki taja dogon tsaki. "Wai mai ya faru? Yaya za'ai ace daga fitar mu zuwa yanzu har garin ya ƙara rufewa."


"Ranki ya dade."


"Ranki ya dade."


"Kai... Ku rufemin baki da 'ranki ya dade' 'ranki ya dade' ɗin nan, dama rai na dole zai daɗe. Abinda nake so shi ne amsa. Uban mai ya faru? Mun lissafa sanda ƙofar zata ƙara rufewa kuma aƙalla akwai sauran wata guda, to tayaya za'ace har ta rufe?"


Tana gama magana ta ƙara dukan ƙofar da ƙarfin gaske. 


"Ni ina ganin Alu Mai Sango yana da saka hannu aciki." Inji ɗaya daga cikin mazan. 


"Tsk.. to, Madaruil'ylud, ka taɓa ganin abinda ya faru a ƙarƙashin ƙasa wanda ba saka hannun Alu? Ai tun wuri na gayawa Bihanzin mu kashe shi kafin ya zamar mana matsala amma yaƙi. Yanzu gashi nan." Sarkin-sarki taja dogon kunnenta tana bata rai tare da muzurai irin na kyawawa. Can daga bisani ta juya wajen namijin dake tsaye a bayan Iliyasis ta ce, "Ubu'ylud, kasan tsiyar da zamu yiwa Alu Mai Sango?"


Namijin mai suna Ubu'ylud ya girgiza kai, "a'a, sarauniya."


Sarkin-sarki tayi murmushi. Tabbas duk da halin da Iliyasis yake ciki yaga wajen ya ƙara haske sabida murmushin. "Kuzo mu tafi." 


Mazan suka gyaɗa kai suka fara shirin tafiya. A lokacin Ubu'ylud ya dube ta ya ce, "ya zamu yi da wannan yaron?"


"Daure ka ɗakko shi, zaiyi amfani." Inji Sarkin-sarki.


Har sun ɗauki Iliyasis suna niyar tafiya sai suka ji ƙara daga sama. Suna daga kai sukai arba da wani abu yana gudu yana doso wajen da suke. Kafin suyi wani abu abin ya dira a bakin garin ya daki ƙofar shiga garin. Ƙasa tayi girgiza sannan ta dare gida biyu amma ƙofar garin bata motsa ba ko kaɗan. 


Bayan ƙura ta lafa, a inda abin ya faɗo wani mutum ne saurayi, fari, dogo, mai faffadar kafada, wanda bazai wuce kimanin shekaru ashirin da uku zuwa da huɗu ba. Abin mamakin shi ne duk wajen babu wanda bai san wannan saurayi ba. 


"IKENGA?!"


Idanun Ikenga na kan Sarkin-sarki. Baki a taɓe ya dube ta ya ce, "SARKIN-SARKI?!"


Sarkin-sarki ta yamutse fuska da baki da gira. "IKENGA, UBAN ME KAKE YI ANAN?!" 


Ikenga ya fara muzurai yana harare-harare. Bayan ɗan lokaci ya dubi Sarkin-sarki ya ce, "nima dai abinda nake son naji kenan. Uban me nake yi anan? Uban me ya faru nazo nan?"


Iliyasis yayi murmushi, zaka iya cewa duk wajen babu wanda zai iya bayanin halin da ake ciki sai shi kaɗai domin ya san fasahar ubangidan sa. 


Domin jin bayanin yadda Ikenga yazo wajen watakila sai dai mu tambayi Wilbafosiyan Siwod Dans. 


Amma idan muka ajiye dalilin daya kawo Ikenga wajen zamu ga cewa wata dariyar mugunta ce ta gilma ta gefen bakin Sarkin-sarki. "Hehe.. yau rana tace. Ga yaron Armad, ga Ikenga Bayajidda har ƙofar gida na." Ta juya wajen mazan uku dake tare da ita, ta ce, "Salsa, ku kama su. Idan sun ƙi tsayawa ku kashe."


***


A dai-dai lokacin da Sarkin-sarki take ƙoƙarin damƙe Ikenga, a can filin yaƙi inda aka fafata tsakanin Armad da Ikenga kwamandun Ikenga ne suke baza ido suna dube-dube dama da hauni ko zasu ga Ikenga. Ko kaɗan ɓatan Armad bai dame su ba (hasalima yayi musu daɗi, duk da sun so ace sune suka kashe shi da hannunsu, amma a hakan ma suna tunanin ya mutu), babbar matsalarsu ɓatan Ikenga. Zaka iya cewa kamar ƙasa ce ace shugaban ƙasar ya ɓata. Kaga babu abinda za'a gayawa ƴan-kasa hankali ya kwanta. To haka ɓatan Ikenga yake a sashin ikwatora domin Ikenga mutun ne wanda bai daɗe da shiga sashin ba amma yafi ƙaraiƙisu suna.


Kána ya dubi basamuden mai bakaken idanu. "Deniz Curu-curu, wai mai ya faru ne?!"


Curu-curu ya girgiza kai da ƙarfi, "na gaya muku ban sani ba. Wai mai kuke so na gaya muku? Kada wanda ya ƙara tambaya ta."


Daddara ya ɗora hannunsa akan wajenda Ikenga ya ɓace ya rufe ido ya kira ƴan dalasiman sa na surkulle tsahon dakiku kafin ya buɗe ido ya ce, "Ikenga yana raye amma baya kusa. Armad kuma ya mutu."


"To dama ai dole ya mutu. Ikenga ne fa. Ko kana mamakin mutuwarsa?" Inji Kána.


Daddara ya girgiza kai, "a'a, ba tantamar mutuwarsa nake ba, kuma ba tantamar izzar Ikenga nake yi ba, amma akwai mamaki ace Armad ya mutu tunda shi ya jira fasahar data ɓatar dasu. Kaga a hankalce mutun baya kiran abinda zai halaka shi."


Sukai shiru suna tunani na ɗan lokaci kafin ƙaraiƙisu ya nuna yamma ya ce, "can ɓangaren akai cilli da Ikenga. Ban ga meye yayi cilli dashi ba amma ba mutun bane. Shi kuma Armad kawai ɓacewa yayi banga wajen da yayi ba."


Kána ya harari ƙaraiƙisu. "Kai amma ƙaraiƙisu sai a barka, kaida kaga wajenda Ikenga yayi amma ka bari muke ta hasashe. Muje mu duba. Curu-curu, kafi kowa sanin hanya shige gaba."


Curu-curu ya shige gaba. Har sun juya zasu tafi amma ƙaraiƙisu ya tsayar dasu. "Ku tsaya."


Kowa ya juyo ya kalleshi suna jiran mai zai faɗa.


"Akwai abu biyu da kuke buƙata ku sani: na farko, a rashin Ikenga ni ne shugaban ku; na biyu, sunan fasahar da Armad yayi amfani da ita ya ɓatar da Ikenga Wilbafosiyan Siwod Dans."


Suka haɗe gira suka harari ƙaraiƙisu a fusace. Uban wa zai bashi shugabanci? Idan ma akwai wanda yafi cancanta ai Kána ne.


***


To fa, ana wata ga wata. 


Ina Armad? 


Ya zata ƙarke tsakanin Ikenga da Sarkin-sarki?


Ga kuma ƙaraiƙisu yana neman mulki?


Mu haɗu a karo na gaba.



Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...