Ayubu ya fuskanci mutun-mutumi irinsa guda huɗu. Dukkansu kamar su ɗaya da Armad sak. Kai zaka iya cewa dukkansu Armad ne kawai da zuciya daban-daban.
"Butulu," inji Armad 1. "Shugaban mu shi ne ya halicce ka sannan kuma ya raya ka, amma ka butulce masa. Kai kuwa yaya kake ji a ranka?"
Armad 2 da Armad 3 da Armad 4 suka haɗa baki suka amsa da cewa, "butulu, butulu, butulu."
Maimakon yaji haushi sai Ayubu ya fashe da dariya.
"Nasan abinda kuke ji a ranku," inji Ayubu. "Kuna jin imani da soyayyar Armad. Kuna so ku faranta masa, bakwa son yin duk abinda zai ɓata masa rai. Umarninsa kamar ibada ne a wajen ku. Haha.. akwai lokacin da nake jin dai-dai irin abinda kuke ji a yanzu. A hankali idan kuka rayu zaku gane gaskiya. Hankalinku zai dawo ku fuskanci tunanin ku na yanzu ba dai-dai yake ba. Abu na farko da zaku gane shi ne Armad mutun ne kamar ku. Dan me shi zai rayu ku kuma ku mutu? Na tabbata kuna son rayuwa, ko ba haka ba?"
Armad 3 da Armad 4 suka kalli juna cikin kokwanto.
"Kada ku saurare shi," inji Armad 1. "Ku kashe shi domin kuwa barinsa zai zamo illa a wajen shugaba Armad."
Yana rufe baki ya zare takobi yayi kan Ayubu. Armad 2 ya rufa masa baya. Armad 3 da Armad 4 suka ɗanyi jim suna lissafi kafin su afka kan Ayubu.
"Wilbafosiyan Siwod Dans," inji Ayubu. Ya kawowa Armad 1 sara.
"Ɗorawa Abada," inji Armad 1. Yasa takobinsa ruwan ɗorawa ya tare.
Wuta tayi sama tana tartsatsi.
Armad 3 yayi amfani da Kaban'Zhisu ya kai Armad 2 da Armad 4 bayan Ayubu. Armad 2 ya fesa masa Negrinki da baki, a yayinda Armad 4 ya dunkule hannu ya saukar masa da Hannun Aradu.
"Kaban'shisu," inji Ayubu, a ƙoƙarinsa na ficewa daga tsakiyar mutun-mutumin. Sai dai a lokacin Armad 3 ya kira irin ɗalasimin ya kuma tare masa hanya. Dole Ayubu ya tsaya hannun aradun ya sauka a kansa. Negrinkin Armad 2 ta daki ƙafafunsa. A lokaci guda Armad 1 ya danne shi da ƙarfin nauyin takobin ɗorawa.
Wajen ya turnuke da ƙura da wuta tsahon dakiku kafin ya lafa. Mutun-mutumin Armad sun kewaye wajen suna jira ƙura ta lafa suga Ayubu.
"Idan mun mutu iska muke komawa saboda tsarin jikin mu," inji Armad 3. "Shin mai Ayubu zai koma? Jini, ko tsoka, ko kuma iska?"
Ragowar suka kalleshi cikin tunanin amsar wannan tambaya.
"Kai ina ruwanka da abinda zai koma?" Armad 1 ya daka masa tsawa. "Ka kiyaye. Babu ruwanka da duk abinda Ayubu ya faɗa idan ba so kake ka jefa kanka cikin bala'i ba."
Armad 3 ya gyaɗa kai yayi shiru.
Suna tsaye ƙura ta lafa. Ayubu ya bayyana. Hare-haren sunyi daga-daga da kayan jikinsa. A wasu guraren ma jini ne yake zuba. Yana zaune a ƙasa yana kallon sama.
"Butulu," inji Armad 1. "Dama ƙarshen butulu kenan. Ku ƙarasa shi."
Ayubu bai tsorata ba. Hasalima dogon numfashi yaja kawai yaci gaba da kallon sama. Armad 1 yasa takobi ya sare masa hannun dama. Armad 2 ya zuƙe hannun da aka sare zuwa duniyar Negrinki. Shi kuma Armad 4 ya saukar masa da hannun aradu. Kafin kace kwabo sunyi daga-daga da Ayubu.
Dole Ayubu ya kwanta ƙasa cikin jini yana numfarfashi.
"Da kai, da kai," Armad 1 ya nuna Armad 3 da Armad 4, "kuje ku tare Diwani. Kada ku bari ya fito da Ki'jinu."
"An gama," Armad 3. Ya dauki Armad 4 da Kaban'Zhisu suka ɓace.
Armad 1 da Armad 2 suka tsaya akan Ayubu wanda har yanzu yake kwance cikin jini.
"Ko Kasan yanzu Armad 3 yake tambaya yaya tsarin jikinka yake," Armad 1 ya gayawa Ayubu. "Wai ko kana da jini ko babu. Ga dukkan alamu dai kana da jini."
Armad 1 da Armad 2 suka fashe da dariya. Sunyi babban kamu.
"Hmmm." Ayubu yaja numfashi. "Dama nasan wannan jikin bashi da kwari, amma ban san rashin kwarin nasa yakai haka ba."
Yana rufe baki sai hasken rana ya fara taruwa a jikinsa. Idan ya taru akan fatarsa sai ya shige ciki. A hankali sai tsoka ta fara fitowa.
Armad 1 yana ganin haka yasa takobi yayi kaca-kaca da Ayubu. Amma duk da haka hasken ranar bai daina taruwa ba. Dole ya koma baya yana kallo.
Bayan minti guda sai jikin Ayubu ya fara walwali. Wata iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa a kewayensa. Armad 1 ya kalli Armad 2 suka yamutse fuska. A wani salo na sai da rai sukai tsalle suka shiga cikin guguwar da niyar ƙarasa Ayubu, amma suna taɓa ta akai jifa dasu gefe.
Ayubu ya miƙe tsaye ya fuskance su daga cikin guguwar. Abin mamaki jikinsa gaba ɗaya warke. Babu ciwo ko ɗaya a tare dashi.
Kamar abin bai isa haka ba sai Ayubu ya fara ƙara girma. Wasu hatimai suka fara bayyana a jikinsa. Akan idon kowa a filin Ayubu ya ninka kansa girma. Hannunsa da ƙafafunsa duk suka kumbura. Idan ka kwatanta zaka ga yayi huɗun Armad a tsaye.
"Ku kalli jikina na samudawa," inji Ayubu cikin alfahari. "Ni ne na farkon ku. Kuma dole kuyi min biyayya."
Yasa hannu ya doke Armad 1. Ƙarfin dukan ya tashi iska sama. Shi kuwa Armad 1 tuni ya tsinci kansa akan iska yana lilo.
Ayubu yasa ƙafa ya take Armad 2. Ya samar da Negrinki a hannunsa na dama yabi Armad 1 sama da gudu. Yana zuwa ya ƙara dukan Armad 1 a saman kafin ya faɗo. Ƙirjin mutun-mutumin inda ya daka ya fafake. Tun daga nan mutun-mutumin bai ƙara motsi ba. A haka ya faɗo ƙasa a mace. Bayan ƴan dakiku sai jikin Armad 1 da Armad 2 ya fara komawa iska yana narkewa.
Acan nesa kuma Armad 3 da Armad 4 sunga abinda ya faru. Ba shiri suka tsaya cak a inda suke. Da farko sunyi ƙoƙarin komawa su kaiwa yan'uwansu ɗauki, amma sai suka fuskanci hakan bazai haifar musu da ɗa mai ido ba. Watakila zasu fi samun nasara akan Diwani da ayubu. Saboda haka suka juya zasu tafi. A lokacin Ayubu ya bayyana a gabansu. Har yanzu yana basamuden sa.
"Zan baku zaɓi," inji Ayubu da murya kakkaura irin ta samudu. "Kodai kuyi min mubaya'a na baku ƴanci ta hanyar raba ruhinku dana Armad, ko kuma ku bijire na kashe ku kamar yanda na kashe yan'uwanku."
Armad 3 da Armad 4 suka kalli basamuden dake gabansu sannan suka juya suka kalli Armad. Tabbas ko'ina halaka ce. Idan suka zaɓi Armad to Ayubu kashe su zaiyi. Idan kuwa suka zaɓi Ayubu to Armad kashe su zaiyi.
"Nasan mai kuke tunani," inji Ayubu. "Amma babu abinda armad zai iya akanku. Da zarar kun amince zan datse zaren izzar da yake sarrafa ku dashi. Daga nan bashi da iko akan ku. Zan baku dama ku shiga duniya kuyi abinda kuke so. Ya kuka ce?"
Mutun-mutumin suka shiga lissafi. Akwai waraka a tare da Ayubu sai dai wanda ya halicce su, wato Armad, bazai laminta ba.
"Kunga abin mai sauki ne," inji Ayubu, a ƙoƙarinsa na janyo su ɓarinsa. "Idan kuka amince akwai yiwuwar Armad ya kashe ku. Amma babu tabbas. Ni kuma idan baku amince ba, to kashe ku zanyi a take anan wajen. To kunga wannan tabbas ne babu kokwanto aciki."
Mutun-mutumin guda biyu suka shiga lissafi. Maganar haka take. Ayubu anan take zai kashe su, amma Armad babu tabbas tunda ga Ayubu ya bijire masa kuma ya tsira da ransa.
"Na amince," inji Armad 3.
"Nima na amince," inji Armad 4.
Ayubu yayi murmushin samun nasara. Da sannu zai saka duk wani mutun-mutumi da Armad ya halitta ya bijire masa.
Ya ɗaga hannu sama ya danna hatimi a ƙirjinsu. "Daga yau na ƴanta ku."
Koda Ayubu ya faɗi haka sai suka ji kamar an sauke musu nauyi. Hatimin ya shiga jikinsu ya narke. Ko kaɗan basa buƙatar suyi wa Armad biyayya yanzu. Irin ƙarfin soyayyar Armad da suke ji ya ragu. Sunfi son kansu da Armad.
"Wannan shi ne yanci," inji Ayubu.
Armad 3 da Armad 4 suka kalli juna tare da ɗaga hannayensu sama suna kallo. Kamar suna mamakin yadda abin ya kasance.
"Kuje na ƴanta ku," inji Ayubu.
Armad 3 da Armad 4 suka juya cikin murna zasu tafi.
A nasa ɓangaren Armad yaga duk abinda ya faru. Zaka iya cewa tun daga sanda mutun-mutumin huɗu suka tare wa Diwani hanya har zuwa sanda Ayubu ya shigo duk akan idon Armad ya faru.
Wani abin mamaki shi ne akwai wasu sabbin mutun-mutumi biyu a gefen Armad wanda suma suke kallon duk abinda ke faruwa.
Fuskokin wannan mutun-mutumi a yamutse suke. Babu annuri ko kaɗan akai. Suna kallon Armad 3 da Armad 4 da wata irin tsana.
"Shugaba," inji mutun-mutumin. "Ka bamu dama mu kashe su."
Armad wanda ke tsaye akan tsibiri yana sarrafa gidan gizo-gizo ya girgiza kai. "Bana buƙatar ku. Abinda nake so shi ne ku zuba ido kuga mai zai faru da duk wanda yayi min butulci."
Mutun-mutumin suka durkusa akan gwiwowinsu.
"Tur da butulu," inji mutun-mutumin. "Babu wata sa'a ko dakika da zata zo ta samu muyi maka butulci."
Armad yayi murmushi a zuci. A hankali yake ƙara gane yadda wannan fasaha ta mutun-mutumi take aiki. Wato duk yadda zaka kai wajen ragewa mutun-mutumi ƙarfi da kayyade musu fasahar da zasu yi amfani da ita, indai zaka basu tunani to akwai yiwuwar su butulce maka. Suna daɗewa a duniya yiwuwar su butulce maka tana ƙaruwa. Ba'ayi bayanin hakan acikin fasahar Aldaima ba saboda haka Armad da kansa yake ganowa. Sai dai hakan ba abin mamaki bane tunda Armad ya canja fasahar daga yadda Aldaima ya kawo ta acikin waƙar maƙabarta.
A dai-dai wannan lokaci Armad 3 da Armad 4 kwatsam suka fara ihu. Armad ya nunawa mutun-mutumin dake gefensa inda abin yake faruwa yace, "ku kalla ku ɗauki darasi."
Ayubu ya datse zaren izzar daya haɗa Armad da Armad 3 da Armad 4. Hakan ya bawa mutun-mutumin ƴanci. Kuma yanzu basa buƙatar suyi biyayya ga Armad kamar dai yadda Ayubu baya buƙatar yayi biyayya. Sai dai jim kaɗan bayan faruwar hakan sai izza ta fara shiga jikin mutun-mutumin. Da farko sunyi zaton ƙarfi suke ƙarawa. Amma daga bisani suka fuskanci izzar da suke zuƙa tafi ƙarfinsu. Idan izzar taci gaba da shiga jikinsu zasu iya yin bindiga kamar yadda Armad yayi a ɗazu sanda suna faɗa da Ƙaraiƙisu da Diwani.
"Ayubu?" Mutun-mutumin suka juya wajen Ayubu domin neman taimako. "Ka taimaka mana."
Ayubu wanda ke gefe ya dawo jikinsa na mutane ya ƙurawa mutun-mutumin ido. Armad ya fishi dabara. Kai zaka iya cewa Armad yasan Ayubu zaiyi ƙoƙarin sawa mutun-mutumin su butulce masa. Saboda haka daya halicce su sai ya saka musu Zaren Manyan Mayu a matsayin zaren izzarsu, maimakon zaren izza wanda kowane mutum yake dashi. Da farko sanda mutun-mutumin suke tare da Armad, kafin Ayubu ya datse zaren daya haɗa su, izzar Armad ta danne Zaren Manyan Mayun dake jikin Armad 3 da Armad 4 ta kuma hana shi aiki, amma a yanzu da Armad ya raba mutun-mutumin da Armad sai Zaren ya fara aikinsa. A halin yanzu duk wata izza dake filin yaƙin kawai shiga jikinsu take yi babu ka'ida. Musamman idan suka matsa kusa da mutane sai kaga izzar mutanen ta fara fita tana shiga jikinsu. Haka idan hari ne ya gifta ta kusa dasu sai kaga sun zuƙe izzar dake cikin garin. Kafin kace kwabo sun zuƙi izzar da tafi ƙarfinsu. Jikinsu ya fara kumbura zai fashe.
Ayubu yana ganin haka ya gudu ya bar su.
Ganin haka yasa mutun-mutumin suka yanke shawarar suzo gurin Armad su nemi gafara. Da saurin Kaban'Zhisu suka zo gurin Armad suka zube a ƙasa suna neman gafara.
Sai dai hakan babban kuskure ne. Armad yana daga cikin wanda suka fi kowa izza a filin yaƙin saboda haka suna zuwa kusa dashi suka zuƙi izzar da tafi ƙarfinsu. Tsarin ruhinsu ya cika ya batse.
Armad yasa sabbin mutun-mutuminsa suka ɗauki Armad 3 da Armad 4 sukai cilli dasu kansu Yurba. Kafin su ƙarasa sun tarwatse a sama.
Yurba da Binani suka dare suka basu guri. Ɗan kaucewar da suka yi ya bawa Armad dama ya ƙara ɗaure dukkan tsibiran da mutane ke kai da zaren izzarsa tayadda zaiyi wuya Yurba ya iya ɗaga su, ballantana ya kifar dasu.
Acan sama Diwani ya isa wajen akwatin ƙanƙarar amma wani sadauki ya hanashi wucewa. Sadaukin yana da doguwar haɓa da ɗan saje. Diwani yaja tunga suka fuskanci juna.
"Ina zaka?" Inji sadaukin.
Maimakon Diwani ya bashi amsa sai ya fashe da dariya. Sannan ba tare da cewa komai ba ya afka kansa. Yana zuwa ya shige ta cikinsa ya wuce.
Sadaukin yayi ajiyar zuciya. Dama yasan zaiyi wuya kwamanda ya kasa gane shirinsa. Siffar sadaukin ta juye ta koma yarima Abba. Kada dai a manta tun farkon fara yaƙin kwamanda Ki'jinu ya mayar da yarima Abba hoto.
Diwani ya ƙarasa gurin gidan ƙanƙarar. Yasa al'amudinsa ya daki ƙanƙarar. Wata ƙara ta musamman ta tashi sama. Kafin ƙarar ta lafa, gidan ƙanƙarar yayi nakiya. Wuta ta rufe ko'ina.
Bayan komai ya lafa sai akwatin ƙanƙarar ya bayyana a fili. Har yanzu yana nan a sabo babu alamun zai ɗauke.
A fusace Diwani ya ƙara dukan gidan ƙanƙarar lamarinda ya samar da wata ƴar ƙaramar ƙofa. Ki'jinu ya yunkuro da sauri zai fito daga ciki amma kafin ya ƙaraso ƙanƙarar ta haɗe.
Diwani ya ƙara dukan dai-dai amma a banza.
Wani abin al'ajabi da wannan ƙanƙara shi ne bata ƙarewa kuma bata gajiya da sabunta kanta. Ki'jinu yana duka ta ciki, shi kuma Diwani yana duka ta waje, amma a banza. Shi kuwa yarima Umaru yana kwance yana kallonsu cikin nishadi.
Ganin Diwani ya kasa fito da Ki'jinu yayi matuƙar faranta wa Armad. Sai dai bai gama murna ba ƙasar da yake kai ta fara fashewa tana dagargaje wa. Daga can nesa ya hango Yurba yana kiran wasu sabbin ɗalasiman. Wato tunda bazai iya ɗaga su ya kifar ba, bari ya dagargaza ƙasar su faɗa ciki.
Armad ya kalli Najunanu sannan suka juya suka kalli Yurba. Kafin wanin su yayi magana biyu daga cikin tsibiran sun narke, mutanen dake kai suka faɗa cikin ramin dake ƙasa. Suna faɗawa duhu ya rufe su. Tun Armad yana jiyo ihun su har ya daina. Daga baya yanayin izzarsu ma ya ɓace. Sama da mutum ɗari biyar amma Armad baya jin ko alamunsu. A lokacin ya ƙara fuskantar zurfin ramin. Watakila ma rami ne da aka haɗa da sihiri.
Kamar abin bai isa haka ba, sai murfin kwanon Binani ya bisu ƙasan. Wato koda wani acikinsu zaiyi ƙoƙarin tasowa to babu hanya.
Armad ya saba ganin mutuwa, amma ya daɗe bai ga rashin imani irin na wannan rana ba. Mutanen kan tsibirin suna kuka, suna roƙon Yurba, amma a lokacin ya ɗaga hannu ya nuna tsibiri na gaba. Wani haske ya fita daga hannunsa ya daki tsibirin. A take ya zagwanye ya narke. Mutanen kai suka fara faɗawa. Wani dattijo ya riƙe matar dake kusa dashi. Ita kuma ta riƙe namijin dake gabanta. Dukkansu suna riƙe a ƙafar wata mata mai ƙarfin hali wadda ta riƙe murfin kwanon tana lilo. Suna ta wutsil-wutsil sai kawai suka ji kwanon ya fara motsi. Sun fuskanci abinda zai faru to amma basu da hanyar kubuta. Idan suka saki ƙarfen zasu faɗa, idan kuma suka ci gaba da riƙewa basu saka ba ya danne su.
Lllll
Sabbin mutun-mutumin Armad suka bayyana a ƙasansu zasu ceto su. Sai dai kafin su ƙarasa, kwanon ya danna mutanen ƙasa. Suna ihu, suna kuka, amma haka suka yi ƙasa.
Maikiro'Abbas ya kawowa Dul'Ururu duka da hannu. Maimakon Dul'Ururu yasa hannu sai yasa jakar tsafinsa ya kare domin tabbas yasan ba gama-garin duka bane. Acikin dukan akwai sirrin marubutan farko wanda idan yayi wasa zaiyi cilli dashi.
"Mutane na sunfi ƙarfin mutanen ka," inji Dul'Ururu bayan ya tare dukan. "Muna nan tare dakai babu inda zaka je kuma babu wanda zaka kaiwa ɗauki. Anan zaka shaida mutuwarsu. Dama can mune mukai maka gata muka baka sarauta. A yanzu daka bijire mana zaka fuskanci kai ba kowa bane."
Yana cikin magana ihun mayaƙan Maikiro'Abbas ya ƙara tashi. Tabbas mayaƙan suna cikin barazana kuma babu wanda zai iya taimakonsu sai shi. Hatta Armad yana kan tsibirinsa ya kasa komai.
To kada dai a manta duk abinda ke faruwa yana faruwa ne akan idon gidajen jaridu. Babbar jaridar Aminiya sun tanadi manyan ayrid guda goma masu nuna faifan bidiyo suna ɗaukan fafatawar suna yaɗawa a duniya. Saboda haka zaka iya cewa babu wani birni a ƙasashen ƙasa wanda bai san abinda yake faruwa ba.
Idan muka leƙa daular maikironomada, babban birnin ƙasar, zamu hangi dubban mutane daga sassa daban-daban na ƙasar sun jeru a gaban fadar Maikiro'Abbas suna nazarin wannan yaƙi. A halin yanzu filin yayi tsit ana jimami. Kowa ka kalla fuska a yamutse yana kokwanton samun nasara.
"Umma, Abba yana cikin farare, ko?" Wani yaro riƙe a hannun babarsa ya tambayi mahaifiyar tasa.
Babar bata ji mai yace ba saboda zulumin da take ciki. Zaka iya cewa babu abinda ke ranta sai ƙoƙarin gano inda mijinta yake a filin yaƙin.
"Umma?" Yaron ya ƙara kwala mata kira.
"Meye ne wai, Ɗan Tala? Meye?" Ta daka masa tsawa.
Yaron ya firgita jin sautin mahaifiyarsa.
"Ba komai, umma, ba komai."
Ganin yaron ya tsorata sai kuma jikinta yayi sanyi. Ta durkusa a gabansa ta ɗora hannu a kafaɗarsa.
"Ɗan Tala, babanka yana filin yaƙi kuma yana cikin farare, kayi masa addu'a, kaji? Ka daina surutu, kayi ta addu'a a zuci har sai mun samu nasara, kaji?"
Da sauri yaron ya gyaɗa kai sannan ya fara addu'a a zuci. Kwalla tazo idon matar. Yanzu idan Talle ya mutu haka zata raini Ɗan Tala ita kaɗai? Yaya zata yi idan mijinta yana cikin mutanen da Yurba ya jefa rami yanzu?
Tana cikin jimami taji an ɗora hannu a kafaɗarta. Ta waiwayo suka haɗa ido da sarkin gida Santali a bayanta yana murmushi. Santali dai shi sarki ya bari jiran gari kafin ya dawo. Kuma tunda aka fara yaƙin shi ne yake kula da jama'ar da suka zo kallo wajen yana kwantar musu da hankali.
"Yaya sunanki?" inji Santali.
"Talatu," inji matar.
Santali yayi murmushi. "Talatu, kada ki damu. Nasara tana wajen mai gaskiya."
Talatu tayi murmushi mai ɗaci tare da gyaɗa kai. A zuci tasan ba kullum mai gaskiya yake samun nasara ba amma duk da haka ta yaba da ƙoƙarin Santali na ya kwantar mata da hankali.
"Yaro," inji Santali, ya riƙe ɗan nata. "Kai ma kada damu. Kaci gaba da addu'a kamar yadda babar ka ta gaya maka, kaji? Kana zaune babanka zai dawo ya same ka."
Santali ya miƙe ya wuce gaba ya samu wani saurayi dake kuka.
"Ɗan saurayi, ka daina kuka, idan abokan gaba suka gani sai suyi maka dariya. Kuma wai kukan mai kake bayan mune da nasara?"
Da kyar saurayin ya tsaya da shessheka ya gyaɗa kai yana share majina.
Haka dai Santali yaci gaba da bin mutane yana basu haƙuri. A ganinsa hakan ya zama dole domin dai a bawa mutane kwarin gwiwa kada su karaya tun yanzu. Ko babu komai yana da yaƙinin Maikiro'Abbas shi ne da nasara.
To kamar yadda ake kallon wannan yaƙin a daular Maikironomada haka ake kallonsa a sauran sassan duniya inda suke da gidan jarida. Duk inda ka duba zaka samu suna yaɗa wannan yaƙi dake gudana a doron ƙasa ta biyu.
A can wani ƙauye wani babban mutun ne zaune a teburin mai shayi. Akwai mutane da dama kamarsa suna shan shayi a wajen. Duk da babu faifan bidiyon yaƙin a gurin amma kuma zancen yaƙin ake yi.
"Ni dai, Nasuru, naga gangancin Maikiro'Abbas," inji wani kwastoma. "Har wani ya hau sama yaƙi da mutanen sama? To yanzu gashi nan ai ya fara gani. Naji ance Yurba ya ɗaga su ya kifar kamar wasa."
Wannan babban mutum yana zaune yana shan shayi baice komai ba.
"Hmmm." Na kusa dashi yaja numfashi. "Gaskiya dai. Akwai Ki'jinu fa. Ga Binani da Diwani da shi kansa Dul'Ururu. Ka ajiye Maruta da sarakunan jinzidal biyu dake wajen ma, yaya Maikiro'Abbas zaiyi dasu?"
"Gaskiya dai anfi ƙarfinsu. Babu yadda za'ai wani mahaluki yaci galaba akan Ururu. A duniya dai dama mutane kala biyu ne kurum: da mutanen sama da mutanen ƙasa. Na sama suke da iko, na ƙasa kuma sai kallo."
A wannan lokaci wannan babban mutum ya ɗago kai ya ajiye kofin dake hannunsa. Fuskarsa tana da kwarjini matuƙa. Babu saje amma yana da gashin baki baƙi da ɗan gajeren gemu. A idanunsa akwai sani da kwarewa da kuma daɗewa anayi. Idan ka lura zaka ga mutumin ba wani bane illa Taidara Wilbafos, mahaifin Armad Wilbafos.
"Babu tabbas a wannan yaƙi," inji Taidara. Muryarsa akwai kaushi aciki wanda hakan zai saka kayi tunanin ransa a ɓace yake. Sai dai idan ka kalli fuskarsa zaka ga murmushi yake yi wanda hakan zai sa ka gane muryarsa ce a haka bawai ransa ne a ɓace ba. "Kowane ɓangare suna da shirinsu dai-dai gwargwado. Idan ka tambaye ni kowa zai iya yin nasara."
Jama'ar dake wajen suka juya a tare suka kalleshi. Ta yaya zaice haka? Ido ba mudu ba ai yasan ƙima.
"Hahah..." Ragowar masu shan shayin suka fashe da dariya. "Malan Wulba, malan Wulba, wannan hasashe naka yau bazai zama gaskiya ba. Tabbas nasara a bayyane take. Tuni mun riga mun san wanda zaiyi nasara."
Taidara, wanda ƴan ƙauyen suka fi sani da malam Wulba, bai tanka musu ba. Kawai murmushi yayi ya kalli sama.
A can filin yaƙi kuma anci gaba da fafatawa tsakanin Maikiro'Abbas da Dul'Ururu, a ƙoƙarin mai bakaken idon ya hana Maikiro'Abbas kaiwa su Yurba hari.
"Dul'Ururu," Maikiro'Abbas ya ɗaga murya. "Bani da lokacin ka."
Yana rufe baki, kalmomi huɗu na ƙarshe daya faɗa suka ɗamfaru akan iska sannan suka juye izuwa hatimi. Hatimin ya zama ɗalasimi. Ɗalasimin ya afka cikin ramin da mutanen suke faɗawa.
Dul'Ururu ya haɗe rai yana kallon Maikiro'Abbas. A lokacin rugugin ruwa ya taso daga cikin ramin. Wasu daga cikin mayaƙan Maikiro'Abbas dake nesa sun zata wani harin Yurba ya aiko domin har sun fara ihu suna kuka, amma na kusa sun san abin ba haka yake ba, harin na Maikiro'Abbas ne.
"Maikiro'Abbas?" Dul'Ururu yayi ƙaraji a fusace yana hararar Maikiro'Abbas.
"Dul'Ururu," inji Maikiro'Abbas. "Da sannu zan karɓi ƴa ta."
Tuni Armad ya gane abinda Maikiro'Abbas yayi, kuma idan ka tambaye shi to hakan shi ne abinda suke buƙata a lokacin domin takawa Yurba birki.
Rugugin ruwan ya fara ƙaruwa. Idan ka nutsu zaka ji kamar ruwan sama yake yi.
Yurba da Binani suka kalli juna. Hatta Diwani dake nesa juyowa yayi yana kallon ikon ALLAH.
Akan idon kowa ruwan kogi ya taso sama ya cika tafkeken ramin da mutane suke faɗawa ciki duk kuwa da girmansa.
Yurba ya haɗe tafin hannunsa guri guda. A take dukkan tsibiran, harda wanda su Armad ke kai, suka fashe. Mutanen Maikiro'Abbas suka faɗa ƙasa suna ƙasa suna ihu. Amma ba jimawa suka ji su acikin ruwa sun faɗa tunjim. Yurba yayi tunani zasu nutse saboda kasar dake zuba kansu amma kurum sai yaga ruwan yana tura su gefe a hankali. Kafin kace kwabo duk yawan mutanen sun koma ɓarin da Maikiro'Abbas yake.
Armad da mutanensa suka hau ɗiban mutane daga cikin ruwan suna kai su inda Maikiro'Abbas yake wanda kuma a halin yanzu shi kaɗai ne yake da sauran ƙasa.
"Mun tsira. ALLAH ya taimake mu, sarki ya kawo mana agaji," inji wata mata sanye da kayan yaƙi.
Wani saurayi ya riƙo Armad bayan ya ajiye shi. "Mungode," inji saurayin yana nishi. Tabbas kana gani kasan yayi tsammanin ya halaka.
Armad ya gyaɗa masa kai kafin ya juya ya tafi. A ransa yana tunanin dalilin da yasa ƙasar da Maikiro'Abbas yake kai bata rududduge ba kamar yadda wadda suke kai tayi. Wai ko akwai wani mataki na izza da Maikiro'Abbas yake kai wanda yake hana hari aiki a kansa?
A gefe kuma Rabi ce ta fuskanci Shata da sarkin Bai da Cokali da Giwa da Asifu da jan doki da Shísu da Inyaya da Barilu. Wanda suka fi samun rauni sune Shata da sarkin Bai. Shata ya zubar da jini da yawa ta inda Iluru ya huda shi da ƙusar mairakana wanda saboda haka fatarsa ta koma fara fat. Ko motsi baya yi balle ya miƙe. Shi kuma Sarkin Bai a ƙone yake ƙurmus. Duk inda ka sani a jikinsa ya ƙone. Tun yana ihu har muryarsa ta dashe babu abinda yake kwalla.
Hannayen Rabi suka fara haske. Ta ɗora hannu ɗaya akan sarkin Bai, ɗaya kuma akan Shata. Hasken dake jikin hannun ya shiga jikinsu. Akan idon kowa sai ƙunar dake jikin sarkin Bai ta saɓe sannan sabuwar fata ta fito. Shi kuwa Shata duk ciwon dake jikinsa rufe wa yayi kamar dama babu shi.
"Ku basu minti biyar zuwa goma," inji Rabi. "Duk kansu zasu tashi. Kuyi haƙuri iyakacin abinda zan iya yi kenan a yanayi na."
"Mun gode," inji Giwa, ta zube a ƙasa. "Mun gode sosai. Kinyi mana magani, kinyi wa ƴan'uwan mu."
Rabi ta kalle ta a nutse. Bayan ɗan lokaci ta gyaɗa kai ta juya ta tafi ba tare da tace musu komai. Suka bi ta da kallo.
Cokali ya ɗaga wandonsa sama dai-dai cinyarsa ta hagu inda ya samu karaya bayan Yurba yayi jifa dasu. A halin yanzu ya warke ko alamun ciwo babu. Hasalima ji yake yi kamar yafi da lafiya. Babu karaya, babu alamun ta.
"Wacece wannan mace mai ban al'ajabi?" Inji Cokali yana kallon cinyarsa.
Dukkansu suka ci gaba da kallon Rabi har ta ɓace acikin jama'a.
Ganin ya ceto mutanensa sai Maikiro'Abbas ya samar da mashin ƙanƙara a hannu ya kaiwa Dul'Ururu suka dashi. Dul'Ururu yayi tsalle sama ya kauce. A saman ya kalli Yurba, ya kalli Binani da Diwani, ya kuma kalli ramin da suka samar wanda a yanzu ya zama wani ɗan ƙaramin kogi. A take Dul'Ururu ya tabbatar harin da suka kawo bazai yi aiki ba saboda haka bai bari ya dira ƙasa ba ya ɓace. Yurba da Binani da Diwani suka bi bayansa suka ɓace.
A can baya kusa da kujerunsu suka bayyana. Kowa ya nemi waje ya zauna. Sun so su ƙarar da kowa a harin da suka kai amma hakan bai samu ba.
Ganin manyan sun dawo gida sai mayaƙan Ururu suka fara ja da baya suna komawa gida. Acan sama ɓangaren hagu Suwainah ta wartsake daga aikin da Armad yayi mata. Tana tsaye a kusa da Ibraham Nil. Han'ibal da Ayubu da Iluru duk sun dawo gida. Zaka iya cewa Ƙaraiƙisu ne kawai baya wajen. Tundai sanda basamuden ya haɗu da Saif-Al-Barzak suka yi wani gurin. Watakila suna can a dokar daji suna ƙoƙarin kashe juna, ko kuma auren juna.
Dubban mayaƙan Ururu suka ƙara jeruwa akan layi suna jiran umarni.
A ɗaya ɓangaren kuma Armad ya haɗu dasu Cokali da ragowar mutanen ikwatora a inda Rabi tayi musu magani. Kai tsaye ya ɗauke su ya kawo su wajen Nusi.
To a yayinda kowane ɓangare ya koma gida, har ma wasu suke ganin an samu hutun rabin lokaci, a lokacin Maikiro'Abbas ya jefa mashin ƙanƙarar dake hannunsa cikin kogin ruwan dake gabansa.
Mashin yana sauka ruwan yayi ambaliya kamar an jefa dutsen dala aciki. Yayi kan Ururu zai cinye su. A ƙoƙarin nuna jarumta mayaƙan Ururu suka tsaya inda suke basu motsa ba. A nasu ganin mai ruwa zaiyi musu?
Sai dai ance rashin sani yafi dare duhu. Ruwan yana rufe su ya ƙanƙare. Babu wanda yasan ta yaya amma ruwan ya koma ƙanƙara cikin abinda bai wuce dakika uku ba. Ƙanƙara ta rufe sama da mayaƙan Ururu dubu biyar a lokaci guda. Kana ganinsu ta cikin ƙanƙarar amma babu damar fitar dasu. Zaka ga wasu iyakacin ƙafa ƙanƙarar ta riƙe musu wanda hakan ya basu damar ihu suna neman ɗauki saboda zafin da suke ji a ƙafar su.
Kyaftin Tangile ya taso a fusace ya ɗaga takobinsa ya sari ƙanƙarar da niyyar fasa ta ya fito da ƴan uwansa. Takobin ta sari ƙanƙarar inda tartsatsin wuta yayi sama. Ƙarfen takobin ya ɓalle gida biyu amma ƙanƙarar ko gwarzane bata yi ba. Tangile ya jada baya a tsorace. Bai taɓa ko jin labarin ƙanƙara mai taurin wannan ba. Shin hakan yana nufin duk mutanen dake ciki sun mutu kenan?
Yayi kururuwa yayi ƙaraji. Ga abokinsa nan kyaftin Ilu yana gani aciki ya zama ƙanƙara. Tabbas bazai bari ya mutu ba tare da yayi komai akai ba.
Kyaftin ɗin ya dunkule hannu ya daki ƙanƙarar. Hannunsa yana haɗuwa da ƙanƙarar ya bada ƙara ya ɓalle gida biyu. Kyaftin Tangile ya faɗi ƙasa yana mataguguwa.
Ganin haka mayaƙan Maikiro'Abbas sukai ihu. Tabbas nasara ta dawo musu. Indai suna da Maikiro'Abbas to basu da tsoron komai.
Armad ya dubi hanya ya ga cewa an samu ci gaba. A da kafin Maikiro'Abbas ya samar da ƙanƙarar, rami ya raba su da Ururu. Wanda hakan yake nuna duk wanda izzarsa bata kai dubu ba bazai iya tashi sama ya tsallake ba. Amma yanzu akwai ƙanƙara mai taurin gaske ta cike ramin. Zasu iya hawa takai sukai hari. Daɗin daɗawa Maikiro'Abbas ya haɗiye dubunnan mayaƙan Ururu acikin ƙanƙara. Hakan ya tsorata ragowar mayaƙan Ururu da ƙanƙarar bata taɓa ba yasa sun fara ja da baya. Tabbas yanzu ne lokacin daya kamata su afka musu su kwaci Fatima. Tambaya guda data rage ita ce: waye zai karya kafin?
Armad ya kalli Zaikid da Shata wanda suke kusa dashi. A kusa da Nazára kuma akwai Asifu da jan doki. A kusa da Nusi akwai Cokali, Giwa, sarkin Bai, Shísu, Inyaya da Barilu. Misali Armad ya kama Dul'Ururu, Zaikid ya riƙe Yurba, Nazára ya riƙe Binani, Nusi ta riƙe Diwani. Ta haka sun gama da ɓarin dama. Sai kuma ɓarin hagu inda Suwainah da Ibraham Nil da Han'ibal da Ayubu da Iluru suke. Su biyar ne wanda hakan yake nuna dole Asifu, jan doki, Cokali, sarkin Bai, Shísu, Inyaya, Barilu, Najunanu, da Shata su san yadda zasu yi dasu. Bawai sai sunci galaba akansu ba, a'a, kawai su riƙe su tsahon sanda za'a karya kafin.
"Ruwa shi ne maganin wuta," inji Armad. Ya juya inda Najunanu yake. "Kana iya samar da ruwa kamar yarima Abba?"
"Zan iya," inji yariman. "Amma bana tunanin ruwan da zan samar zai iya kashe wutar sarki Han'ibal. Zan iya rage mata ƙarfi tabbas, amma ba lalle ya kashe ta ba. Ba a banza ya zama sarkin jinzidal ba."
"Kada ka damu ka rage mata ƙarfin, hakan ma yayi," inji Armad. Sannan ya juya wajen Cokali. "Cokali, idan an ragewa wutar ƙarfi zaka iya 'rubuta' ta?"
"Zan iya," inji Cokali, ya doki ƙirji cikin alwashi.
"To shikenan," inji Armad. "Najunanu da Cokali ku tari Han'ibal. Ƙarfinsa yana wutar da yake samarwa. Idan kuka hanashi samar da wutar bazai iya komai ba."
Armad ya juya wajen Asifu da jan doki. "Ku kuma ku tare Iluru."
"A'a," inji jan doki. "Ni ina ganin ka haɗa ni da mutun-mutumin ka Ayubu."
Armad da mutanen dake gurin suka kalli jan doki cikin mamaki. Shin kwamandan yana ganin zai iya ja da Ayubu ne duk da yadda yaga faɗan Ayubu ya kasance da mutun-mutumin Armad guda huɗu? Ko kuma yana jin tsoron faɗa da sarkin jinzidal ne saboda haka yana ganin Ayubu zaifi sauki?
"Zan bukaci ka haɗa ni da mutun-mutumin dazai hana Ayubu zuƙe min izza da kuma wanda zai hana shi jana cikin duniyar Negrinki," inji jan doki. Ya lura da irin kallon da kowa yake masa saboda haka ya ƙara da cewa. "Kada ku damu, bazan kashe shi ba."
Armad ya ɗan jinjina abin a ransa amma daga ƙarshe ya amince. Ko babu komai jan doki shi yasan ƙarfinsa da fasaharsa. Tunda yace zai ja da Ayubu to ya kamata a rabu dashi ya gwada. Armad ya bashi mutun-mutumi ɗaya sannan ya ƙara masa da cewa, "idan ka samu dama ka kashe shi."
Ganin haka sai Asifu ya dubi Armad ya ce, "dani da Shísu zamu riƙe Iluru. Idan na fuskanta Shísu yana iya sarrafa makami ya ƙara masa gudu ko ya rage, ko kuma ya canja masa hanya, ko?"
Shísu ya gyaɗa kai a hankali. Yana iya ture makamin ƙarfe daga jikinsa kowane iri ne, amma idan makami bana ƙarfe bane to akwai matsala. Sannan batun ƙarawa makami gudu kuma wannan wani abu ne daban.
"Yauwa," inji Asifu. "Kaga ina da takobi, ina da saurin dazan iya saran Iluru, amma kuma bani da ƙarfin dazan iya ratsa fatarsa, musamman idan ya koma basamude. Abinda nake so kayi min shi ne ka ƙarawa takobi na ƙarfi. Idan na sari Iluru ka danna takobin da karfin tsiya ƙasa ta shiga fatarsa ta dole. Zaka iya?"
Comments
Post a Comment