Skip to main content

BABI NA 209-218: Karan-batta

 Babi na 209-211

***

Banda ɓangaren ƙofar-gaskiya wadda Armad ya shiga akwai ɗaya ƙofar wadda ake kira da ƙofar-asali. Acikin ƙofar-asali anan ne dukkan ragowar masu fafatawar kamarsu Ikenga suke. A dai-dai wannan lokaci Ikenga ya ƙaraso mataki na biyar wanda daga shi sai mataki na karshe wato mataki na shida. 


A wannan mataki babu komai sai sahara iya ganinka. Wuta mai balbali wadda launinta baƙi-ƙirin ne naci akan wannan sahara. Abin da ake so a wannan mataki shi ne mutun ya kai ƙarshen wannan sahara wanda anan zai tadda matattakala wadda zata kaishi mataki na shida. Sai dai kuma kana ƙara yin gaba kana ƙara shiga cikin baƙar-wutar. Wannan baƙar-wuta ba wata bace illa wutar da Hidaya ke ƙone komai da ita. Wutar da tasa ake kiranta da Baƙar-wuta. 


Ikenga ya baza [Yanayin-izza]rsa ko'ina ya tabbatar babu kowa akan wannan mataki sai shi. Ikenga yana da fasahar [Lokaci] wadda yake iya sarrafa lokaci yadda yaga dama da ita. Sannan kuma yana da aljani mai sarrafa ruwa, walƙiya da ƙanƙara. Saboda haka yana bayyana ya kira ɗalasimai wanda suka sa akwatin ƙanƙara ya bayyana ya kewaye jikinsa sannan ya zana wani hatimi akan ƙafafunsa. 


Ya fara tafiya taku ɗai-ɗai yana tunkarar wutar. Duk sanda wutar ta daki akwatin ƙanƙarar dake kewaye dashi sai kaga tiriri ya tashi sama ya tokare da sararin samaniya. Idan akwatin ya narke sai Ikenga ya samarda wani. Haka abin ya kasance tsahon lokaci. Koda ya fara yin nisa saiya fuskanci cewa zafin wutar ƙaruwa yake sama da yadda ƙanƙararsa zata iya ɗauka. Fatarsa ta fara canja launi tana komawa baƙi da shuɗi-shuɗi. Nan take ya samarda walƙiya domin kare kansa amma tana bayyana baƙar-wutar ta kewaye ta inda walƙiyar ta kama da wuta ta ƙone ƙurmus. Kaji wuta mai kona walkiya. 


Ikenga ya daki ɗalasimin dake ɗaure a ƙafarsa wanda ya fara haske yana walwali. Take lokaci ya fara canjawa a kewayen da Ikenga yake. Wajen yayi duhu, wasu lambobi da rubutun Elburish suka fara sauka daga sama. Nan take Ikenga yayi tafiya acikin lokaci ya bayyana a ƙarshen wutar ba tare wutar ta taɓa shi ba. Sai dai kuma yana bayyana yaga kayansa sun zagwanye sun narke ƙasa. Jikinsa ya bayyana tsirara. Idan ka lura sosai za kaga akwai alamun tsufa a jikansa, wannan dalili shi ne yasa ba kowanne lokaci Ikenga yake amfani da wannan fasaha ba. 


Ya buɗe zoben dake hannunsa ya ɗakko sabbin kaya ya saka. Bayan ya kammala komai zaiyi gaba da tafiya sai yaji tamkar takubba kaifafa guda biyu sun cake shi a ƙirji. Yana waiwaya yai arba da wani saurayi ma'aboci baƙaƙen idanuwa, zaune ya tankwashe ƙafa yana kallonsa. Ga dukkan alamu wannan ma'aboci baƙaƙen idanuwa ya daɗe da zuwa wannan waje. 


Ikenga ya ja tunga ya tsaya cak suna kallon-kallo da wannan saurayi. Sunan wannan saurayi Ƙaizadussa'ayi Ururu ɗan yarima Dumaƙisu. Babu wanda yasan yadda akai Ƙaizadu yazo wannan waje, sannan kuma babu wanda yasan meye dalilin zamansa a wajen bai shiga mataki na shida ba. 


Bayan tsahon lokaci ana kallon-kallo Ikenga ya tabbatar Ƙaizadu bashi da niyyar kula shi sai ya wuce ya hau kan matattakalar da zata kaishi mataki na shida ya bar Ƙaizadu a wajen. Da haɗuwarsu da rabuwarsu ɗaƙiƙa sittin, babu wanda yacewa wani uffan.


A dai-dai wannan lokaci Hasanu na tare da Elbinuil a mataki na huɗu suna tattaunawa. 


Hasanu ya gyaɗa kai cikin tunani ya ce, "Armad ya shiga ƙofar-gaskiya kuma tuni ya fara fafatawa da ruhin-heeda, idan yayi nasara zai dawo ya wuce ta nan. Saboda haka ina ganin bamu da buƙatar ƙarasawa mataki na shida."


Elbinuil ya karkaɗa kunnensa na dama ya ce, "fasaharka ta jini-uku ce ta gano Armad ya shiga ƙofar-gaskiya? Saboda muna nan babu wata alama data nuna mana haka." 


Hasanu ya gyaɗa kai tare da cewa, "sunanta Láidan."


Elbinuil yayi murmushi ya ce, "Lalle Láidan babbar fasaha ce. To amma ace gaskiya ne a halin yanzu Armad yana can yana fafatawa da ruhin Hidaya. Babu tabbas shi zaiyi nasara saboda haka idan muka jira anan zai iya zama ɓata lokaci."


Hasanu yayi murmushi ya ce, "zaiyi nasara. Shawara ta rage ya naka; ka jira anan tare dani idan Armad yazo mu zamu fara tare shi mu kwace ruhin ko kuma ka ƙarasa gaba ka haɗu da Ƙaizadu da Ikenga."



Ɓangaren Armad



Armad na tsaye cak suna kallon-kallo da Hidaya. Yayi amfani da Miyura, yayi amfani fasahar walƙiya ta Sikai, yayi amfani da littafin-takobi amma duk da haka babu alamun nasara. Abinda kawai ya rage shi ne Negrinkinsa. 


"Kana da sauran wani abu a fannin izza?" Inji Hidaya wadda ke tsaye cikin alkyabba da farar-riga doguwa.


Armad ya ɗaga hannunsa sama ya dunƙuleshi inda wani jan hayaƙi ya fara fita daga jikin hannun. 


Lokacin amfani da Negrinki yazo.


Hayaƙin yana ɓulɓula ya kewaye Armad sannan yayi sama ya tokare da sararin samaniya. Idan ka lura sosai zaka ga a tsakiyar hayaƙin akwai dunƙulalliyar walƙiya tana ruruwa.


"[Hannun-aradu]."


Armad ya dunƙule hannunsa ya daki iska inda Negrinkinsa ta haɗu da sinadarin walƙiya ta haɗe a waje guda ta tunkari Hidaya. Hatta iskar dake wajen saida ta fara daddarewa tana tarwatsewa saboda tsananin ƙarfin harin. Kai kace Armad duniyar gaba ɗaya zai tarwatsa.


A karo na farko Hidaya ta zare ido. Ta matsa baya taku ɗaya sannan ta dunƙule hannunta ta daki iska. Hayaƙi mai ruwan ɗorawa ya ɓulɓulo daga hannunta ya nufi Armad gadan-gadan. 


Koda Negrinkin Armad da na Hidaya suka haɗu sai ƙasa ta dare gida biyu. Sama ta dare gida biyu; ɓari ɗaya ja ɓari ɗaya ruwan ɗorawa. Iska ta fara daddarewa tana ƙara tana tarwatsewa kamar gilashi. Sannu a hankali hadari ya haɗo, ruwa mai launin jini da ɗorawa ya fara sakkowa kamar da bakin kwarya. 


Daga jikin Armad ƙatoton dunƙulallen hannun jan Negrinki da walƙiya ya taso ya haɗu da dunƙulallen hannun yaluwar Negrinki daga Hidaya. Wato a taƙaice yaƙi akeyi daga nesa, kowa yana aiko da Negrinkinsa a siffar dunƙulallen hannu. Idan Negrinkin Armad ta danno sai ita ma Hidaya ta danno. Haka aka wanzu ana wannan fafatawa tsahon daƙika hamsin kafin daga bisani Negrinkin Armad ta zuƙe Negrinkin Hidaya zuwa wata duniyar.


Negrinkin Armad tayi dishi-dishi kafin daga bisani ta ɓace bat. 


Armad yaga abinda ya faru: kamar yadda Negrinkinsa ta zuƙe Negrinkin Hidaya zuwa wata duniya haka ita ma Negrinkin Hidaya ta zuƙe izzar dake cikin Negrinkinsa. A taƙaice dai Negrinkin Hidaya tana da fasahar zuƙe izza.


Idanun Armad suka zazzaro cike da mamaki, ya kurawa Hidaya ido. Mai sauraro ba lalle yasan mai hakan ke nufi ba amma Armad wanda ya karanta littafin takobi yasan cewa babu wani mahaluƙi da yake da Negrinki mai zuƙe izza. Fasahar sarrafa izza fasaha ce wadda ake gadonta acikin jinin Wilbafos kaɗai, kamar yadda ake gadar Ururu a tsakanin ƴaƴan gidan Ururu. Irin waɗannan fasahohi da ake gada a jini da kuma fasahohin Negrinki suna da banbanci. Ƙa'idar ita ce babu wata Negrinki dake da fasahar da ake gadonta. Misali babu Negrinkin da zata baka damar sarrafa fasahar izza ko kuma Ururu. Wannan ƙa'ida an gaje ta tun a farkon lokaci kuma babu wani mahaluƙi daya taɓa mallakar Negrinki mai ɗauke da fasahar gado. 


Wasu daga cikin malaman izza sun alaƙanta abin da allon Tsarin-ruhi. Wato ɗan ƙaramin allon nan dake cikin Tsarin-ruhin kowanne mutun. Ance a ɓari ɗaya na allon anan ake rubuta fasahar gado, a ɗaya ɓarin kuma anan rubuta fasahar Negrinki. Misali Armad zai samu tambarin Miyurarsa a ɓari ɗaya a ɗaya ɓarin kuma zai samu Negrinkinsa. Ance biyun basa taɓa haɗuwa. Wasu masanan suna ganin cewa idan da ma'abota izza zasu iya amfani da Negrinki su kwaikwayi fasahar gado da an daina gane su waye ƴan asalin ƙabila. 


Binciken masana da dama ya nuna ɓarin allon guda biyu a duniya daban-daban suke, sai dai kuma har izuwa wannan lokaci ba'a iya gano dalilin da yasa ɓarukan biyu basa haɗuwa ba. Armad yasan cewa bai isa Negrinkinsa ta samu fasahar izza ba ko kuma fasahar Ururu ko kuma wata fasaha wadda take ta gado. Amma kuma Negrinkinsa tana da fasaha irin tata ta musamman. 


Abin mamaki a dai-dai wannan lokaci Negrinkin Hidaya ta sarrafa izza. Nan take wani abu ya faɗo zuciyar Armad. Tambayar da masana suka daɗe suna yiwa kansu akan tayaya Hidaya take sarrafa izza? Idan mai karatu bai manta ba ba'a taɓa ganin Hidaya tayi amfani da Miyurarta ba, saboda haka dubunnan masu bincike har a jami'ar Bábila sun daɗe suna tambaya akan ta wacce hanya Hidaya take sarrafa izza. A dai-dai wannan lokaci bama Armad kaɗai ba, duk wani mai tambaya akan yadda Hidaya take sarrafa izza ya samu amsa. Hidaya tana sarrafa izza ne da Negrinkin ta. 


Sai dai kuma kamar Armad sanin hakan bai sa sun samu sauƙi a zuciyarsu ba. Babu abinda hakan yayi sai ƙara samarda wasu tambayoyin. Ya akai Hidaya take sarrafa fasahar gado ta gidan wilbafos da Negrinkinta? Hakan ba abu ne mai yiwuwa ba duk da kuwa cewa itama ƴar gidan Wilbafos ce. A ƙa'ida sai dai tayi amfani da Miyura indai tana so ta sarrafa izza.


Armad tare da sauran mutanen duniya suna cikin wannan mamaki Hidaya ta tafa hannayenta biyu ta ƙara samarda Negrinki sannan ta kira wasu ɗalasimai inda Negrinkin ta juye izuwa Baƙar-wuta.


Mamaki yakai mamaki. Wai dama Baƙar-wutar da Hidaya take amfani da ita daga Negrinkinta take samar da ita? 


Kafin Armad ya amsa wannan tambaya sai kawai Baƙar-wutar ta afko masa. A karo na farko tsoro da firgici ya cika ruhinsa. Lallai al'amarin bana wasa bane. Take wutar ta kewayeshi tana neman haike masa. Tufafin jikinsa ya narke, gashin jikinsa ya ƙone, fatarsa ta fara sauyawa. 


Yana ƙoƙarin yin amfani da Kaban'shísu ya ɓace sai kawai yaga baƙar-wutar ta bayyana a dai-dai wajenda yake niyyar bayyana. Sannan ta ƙara kewayeshi, ta matseshi a tsakiya, ta toshe masa dukkan ƙofar tuba. 


Armad ya samarda Negrinki ya kewaye jikinsa da ita tayadda duk inda wutar ta taɓa shi sai kaga wutar ta ɓace. Negrinkinsa ta zuƙe ta cikin wata duniyar. 


A hankali ya ringa ƙara yawan Negrinkin tasa yana sawa tana ƙara faɗaɗa har saida ta kusa cinye wutar.


Sai dai kuma a wannan lokacin ne baƙar-wutar da tayi ragowa ta juye izuwa Neginkin sa. Wataƙila da a iya nan abin ya tsaya da da sauƙi, amma nan take Negrinkin ta fara yin irin abinda Negrinkin Armad take yi sak. Wato tana zuƙe Negrinkin Armad zuwa wata duniyar. Babu shiri Armad ya ɓace daga inda yake ya bayyana a can nesa yana mamaki baki a buɗe. 


Akwai tambayoyi da dama amma ta farko da tazo bakinsa ita ce, "tayaya kika kwaikwayi Negrinki na?!?!"


Hidaya ta ja dogon numfashi tare da yin ajiyar zuciya ta ce, "a ganinka tayaya akai mace mai ƙarancin shekaru kama ta ta shahara a duniya. Na gagari mutanen sama dana ƙasa, na buwayi aljanu da dordor?! Ni ce wadda ake faɗa a zikirin Bábila na safiya da maraice, ni ce mai Negrinkin da yake iya kwafar duk wata fasaha a duniya. Zarar ka bari Negrinki na ta haɗu da taka to an gama, kamar ka bani fasahar ka ne. A halin yanzu duk wani mahaluƙi dana taɓa fuskantar Negrinkinsa ina da fasaharsa. Idan zaka buɗe ido ka buɗe, har yanzu ina da ragowar fasahai da yawa wanda baka gani ba. Idan kuma kana so na taƙaita maka wahala ne a yanzu sai na ɗinke ka da fasahar rana da wata."


Tana iya kwafar duk wata fasahar Negrinki?! 


Armad ya tambayi kansa a murya ƙasa-ƙasa. Lallai babu wata hatsabibiya kamar ta. Idan haka ne to babu tayadda za'ai mutun ɗaya ya iya yaƙar Hidaya yayi nasara, hanya ɗaya tak daza ayi nasara akanta shi ne ayi mata taron dangi.


Armad ya miƙe. Bashi da tsimi bashi da dabara. Duk abinda yazo dashi yayi amfani dashi amma a idon Hidaya baiyi komai ba. Lallai yana buƙatar ya canja shiri.


Armad ya cije baki ya juyar da jikinsa izuwa walƙiya sannan ya kewaye jikinsa da Negrinki. Yai ƙaraji yai kururuwa ya afkawa Hidaya. 


Hidaya tayi murmushi tare da haɗe gira, "yaro bai san wuta ba saiya taka."


Ta tsaya cak a inda take saida yazo gab da ita sannan ta daki ƙasa da ƙafarta. Take dukkan duniya ta cika da Negrinkin ta. Armad ya ga sanda Hidaya ta fara samarda Negrinkin ta amma kafin ya ankara yayi wani abu dukkan duniyar ta cika da Negrinkin ta, sannan tayi amfani da fasahar Armad ta zuƙe shi izuwa wata duniya. An cishi da yaƙi da Negrinkinsa. 


Duniyar da yake kai mutane ta hanyar amfani da Negrinkinsa shima an kaishi. 


Hidaya tayi ajiyar zuciya sannan ta tafa hannayenta inda kujera ta bayyana akan iska ta hau ta zauna cikin ƙasaita.


A ɗaya ɓangaren kuma Armad ya bayyana a wata duniya ta daban. Da kyar ya miƙe saboda ciwon da jikinsa keyi daga zuƙar da Negrinkin Hidaya tayi masa. A zahiri abin yayi kama da yanayin shiga ƙofar Eycigan amma yafi hakan ƙarfi. Armad na miƙewa yaji jiri inda ya koma ya zauna tare da yin aman jini. 


Bayan tsahon lokaci ya tashi zaune ya hanga gefe da gefe, sama da ƙasa. Akan wani ɗan ƙaramin tsibiri yake wanda ke lilo akan iska. A kusa da tsibirin akwai wasu tsibiran guda shida duk suna lilo akan iska. Daga can ƙasa kuma hayaƙi ne ke tashi sabida balbalin wuta dake ci a ƙasa. Yana bayyana yaji Miyurarsa ta fara ɗaukan zafi tamkar ana cinna mata wuta. Take idanuwansa suka zazzaro sukai jajawur. Ana cikin haka tsibirin ya fara yin ƙasa yana tunkarar wutar dake ƙasa. 


A lokacin Armad ya gane cewa duk abinda yake jehowa cikin wannan duniya nan yake zuwa. Hakan ne yasa ya tuno da Han'Diyuza wanda shi ne mutun na farko daya fara jefowa wannan duniya. 


Bayan wannan ƙananun tsibirai guda bakwai babu komai a duniyar iya ganin ka. Babu ƙofar shiga babu ƙofar fita. 


A hankali Armad ya gane cewa dalilin da yasa Miyurarsa ce kaɗai ke zafi saboda tana shanye duk wani zafin duniyar ne a maimakonsa. Ba daban haka ba da tuni ya daɗe da narkewa. Cikin kwana ɗaya da rabi mai zuwa wannan tsibiri zai ƙarasa juyawa ya tsoma shi acikin wutar dake ci a ƙasa. Saboda haka ya zamar masa wajibi ya nemo hanyar fita cikin ɗan lokaci. 


Sabida zafin da Miyurar take ɗauka Armad baya iya gane abubuwa sosai. A hankali ya ɗora hannunsa akai inda nan take hannun yayi jajawur kamar garwashi. Armad ya zube a ƙasa sumamme. Bayan wani lokaci ya farko ya ganshi cikin jini. Goshinsa na ta malalar da jini kamar wanda aka cakawa wuƙa. Tsibirin da yake kai yayi ƙasa sosai yana dab da taɓa wutar. Domin a halin yanzu kusan duk acikin hayaƙi yake. 


Yayi ƙoƙarin yin amfani da Kaban'shísu amma ya kasa. Ga dukkan alamu fasaha bata aiki a wannan duniya. 


Armad ya daddagira ya miƙe tsaye sannan ya tsaya. Yana yin taku ɗaya yaji nauyi ya danna shi ƙasa ya hanashi ɗaga ƙafa.


Wato tafiya ma babu!


Armad ya laluba cikin littafin-takobi ko zai samu wata fasaha amma babu wani labari. Haka ya kwanta a wajen yana tunanin mafita. Bayan gari ya waye yaga dutsen ya ƙara yin ƙasa. Yana hango wutar tana ci tana ambaliya. A wannan lokaci Armad ya fara ɗebe haso daga rahama. Duk wata fasaha bata aiki a wannan duniya sannan kuma gashi ko tafiya baya iya yi. Ga wuta tana neman ƙone jikinsa. Haka ya wanzu tsahon lokaci yana dabaru kala-kala amma babu labari. Ƙarfinsa ya ƙare ko motsi baya iyawa. 


Ana cikin wannan hali yaji murya tana ƙuwwa a kunnensa.


"Shin har ka haƙura?"


Armad ya dudduba sama da ƙasa, kudu da yamma, gabas da arewa amma bai ga kowa. Sai dai muryar tayi kama da wadda ya taɓa ji. Bayan ɗan tunani ya gano cewa ita ce muryar da yaji a farkon fitowarsa daga gida. Muryar da tace masa ya kula da Ururu.


A wannan lokaci tambaya ta farko da Armad ya fara yiwa muryar ita ce, "waye yake magana?"


Muryar ta ɗanyi shiru na ɗan lokaci kamar baza'a amsa ba kafin daga bisani ta ce, "NI NE ARMAD WILBAFOS!"


Armad ya miƙe cikin mamaki ya ce, "sunan mu ɗaya kake nufi?"


Muryar ta ce, "har yanzu dai baka gane ba, NI NE KAI!" Daga ƙarshe akwai alamu na kaushi acikin muryar.


"Ban gane kaine ni ba. Mai kake nufi?"


Muryar ta amsa da cewa, "ni ne ruhinka wanda ke cikin Miyurarka a ƙulle."


Armad ya cika da mamaki. "Ruhi na? Gaskene ruhi na ya taɓa rabe wa biyu sanda Miyura ta ta cire amma tun kafin Miyura ta cire nake jin muryarka. Mai ke faruwa?"


Muryar ta amsa da cewa, "ruhin ka guda biyu ne. Ko kuma nace ruhinka ɗaya ne amma an ara maka wani ruhin saboda haka ruhinka ya zama biyu. Ruhin da aka ara maka bazai iya cin galaba akan Hidaya ba domin shima a rabe yake, amma ruhinka zai iya. Zan sakar maka ZAREN IZZAR ruhinka!"


Duk duniya za'a iya cewa Armad ya daɗe bai shiga ruɗani irin wannan ba. Na farko ance masa ruhi biyu ne a jikinsa; ɗaya na aro ne, ɗaya kuma nasa ne amma yana ɗaure acikin Miyurarsa. Waye ya ara masa ruhi kuma meye dalili? Waye ya ɗaure ruhinsa acikin Miyurarsa? Menene zaren izza?


Bayan tsahon lokaci Armad ya buɗe baki zaiyi magana amma kawai sai muryar ta ce, "koda nayi maka bayani a yanzu baza ka gane ba, kuma koda zaka gane bazan yi maka bayani ba. Nayi MASA alƙawari bazan gaya maka komai ba. Ga zaren izzar ruhin ka nan. A halin yanzu kana da Zaren izza guda biyu: dana ruhin da aka ara maka da kuma na ruhinka. Tabbas baka da wani dalili da wani mahaluƙi zai ƙarayin nasara a kanka."


Koda zuwa nan a zancenta sai muryar tayi shiru. Armad yayi magana yayi magana amma shiru. Bayan ɗan lokaci sai kawai yaji Miyurarsa ta daina zafi. Idanunsa sunyi haske sannan idanunsa suka juye izuwa ruwan ƙasa. A karo na farko Armad yaga amfanin idanu ruwan ƙasa. 


Wasu fararen abubuwa dogaye masu kama da zare suka cika duniya. Komai ya kalla sune. Ana haka lokaci ya tsaya cak, sai da Armad ya kwashe dogon lokaci wanda shi kansa bai san adadinsa ba yana nazarin wannan zarurruka. Duk da farare ne kowanne zare yana da tsarinsa, da fasalinsa da kuma yanayin farinsa. Kowanne yana da tsayinsa da faɗinsa da kaurinsa. A jikin kowanne akwai suna wanda bashi da rubutu kuma bashi da yare. Shi kansa Armad bai san yadda akai ya gane akwai sunan ba. Kawai yana ji akwai shi kuma yana iya jinsa amma babu shi a rubuce, babu shi a zane. 


Lokaci yaci gaba da tafiya Armad na kwance yana nazarin wannan zarurruka. A duk sanda ya gano wani abu sai yaga ashe akwai wani abin daya fishi. Wani zaren na abubuwa masu rai ne wani na dabbobi ne, wani kuma na abubuwa marasa rai ne. Abu ɗaya da kowanne zare yake dashi shi ne izza. Kowanne zare yana da izzar sunanda ke jikinsa. A wani lokacin sai kaga wani zaren ya ɓace wani kuma ya tsaya ya daina tafiya, wani ya fashe wani ya tsinke. Kowanne zare yana bayani akan mamallakinsa. 


Armad ya miƙa hannu ya janwo ɗaya daga cikin zaren. Nan take yaji a ransa cewa a hannunsa yana riƙe da izzar wani mutun a wani waje wanda shi bai sani ba. 


A dai-dai wannan lokaci sai kawai wani tunani ya faɗo masa. Nan take ya zauna ya tankwashe ƙafa ya rufe ido ya buɗe littafin-takobi ya fara nazari. Nazari akan zaren-izza da idanun gidan wilbafos. Menene alaƙarsu da Miyura? Menene sirrin sarrafa izza? 


Bayan tsahon lokaci ya buɗe idanunsa. Hasken da yake ciki a yanzu babu shi a baya. Duniyar da da yake tunanin babu mafita yanzu yana ganin ƙofa. 




***

Babi na 212-213

***

Wata sabuwar nutsuwa ta bayyana a idanun Armad. Dukkan wani ruɗani da hayaniyar duniya ta ɓace daga gareshi. Kallon da yake yi wa duniya ya canja: abinda baya gani a da ya bayyana a gareshi. 


A hankali ya tashi ya zauna sannan ya tankwashe ƙafa ya rufe idanunsa ya shiga halwar izza. Menene zaren izza? Zare na farko da Armad ya maida hankali akansa shi ne zaren-izzarsa. Muryar dake cikin Miyurarsa ta ce yana da zaren izza guda biyu: ɗaya na sa ɗaya kuma na ruhin da aka ara masa. Har yanzu Armad bai fuskanci abinda ake nufi da ruhin aro ba, amma yana sa ran idan yayi nazari akan zaren izzarsa zai samu amsar wannan tambaya ta sa. 


Zaren izzar Armad na farko dogo ne fari mai ratsin baƙi. Yana ɗaure a jikin zuciyarsa inda ya fito ta ƙirjinsa yayi sama. Armad ya buɗe idanunsa ruwan ƙasa ya bishi da kallo sama. A can ƙololuwar sama zaren ya haɗu da wata tauraruwa mai matuƙar girma. Girman wannan tauraruwa yafi girman duniyar baki ɗaya da abinda ke cikinta. 


Bayan wannan zare akwai wani zaren kuma wanda ya tashi daga jikin Miyurarsa. Launinsa jajawur ne kamar wuta. Armad ya miƙa hannunsa ya taɓa zaren, nan take zaren ya juye izuwa siffarsa. Wanda hakan ke nuna cewa wannan zaren izzar ruhin sa ne. 


Ya juyo ga ɗaya zaren ya taɓashi, nan take zaren ya juye izuwa siffar wani saurayi kyakkyawa fari riƙe da takobi. Saurayin na kwance akan iska yana lilo. Koda Armad ya ƙura masa ido saiya buɗe ido ya kalleshi. Idanun saurayin na daban ne; maimakon kwayar baƙin-ido wasu gumaka ne guda uku a tsaye a tsakiyar kowanne ido. Wannan gumaka launin ruwan ƙasa ne amma ragowar idon fari ne fat. Akwai tambarin Miyura irin na Hidaya sak a goshinsa. Wata iska mai nauyi na tashi daga jikinsa wadda tasa Armad yaji numfashinsa ya fara ɗaukewa.


Saurayin yana da doguwar haɓa a tsaye wadda ta dace da gidan sarauta. Yana da ɗan ƙaramin siririn saje wanda ya haɗe da wani gajeren gemu a ƙasan haɓarsa wanda baifi ɗan taƙi ba. Abin mamaki hancinsa da bakinsa suna yanayi dana Hidaya matuƙa. Koda ganin haka sai saurayin yayi murmushi lamarinda yasa wushirya ta bayyana a bakinsa. Haƙoransa suka haskewa Armad ido. A siffa da kamala wannan saurayi yafi duk wata halitta da Armad ya taɓa gani harda Heeda da Bihanzin. 


Armad bai san mai yasa ba amma yana ji ajikinsa kamar ya taɓa ganin wannan saurayi. Ya buɗe baki zaiyi magana amma ya kasa cewa komai saboda tsananin girman kamalar wannan saurayi dake gabansa. Armad yana jin wani yanayi wanda ake ji idan bawa ya tsaya a gaban sarki mai iko.


Saurayin ya buɗe bakinsa mai kamala ya ce, "Armad W-fakta... Sannu da zuwa."


Armad ya buɗe baki yana mamakin yadda akai wannan saurayi yasan sunansa. 


"Kana mamakin yadda nasan sunanka?" Saurayin yayi murmushi yaci gaba da cewa, "duk da na daɗe ina bacci ai bazan manta kaba. Nasanka kuma nasan yayarka Hidaya."


Bayan doguwar ajiyar zuciya Armad ya ce, "waye kai kuma mai kake anan?"


"Oh, banyi maka bayanin kaina ba ko? Ni ne sarki ɗan sarki, ni ne izza ɗan izza, ni ne na gagari na jiya da shekaran-jiya, ni ne... Au na manta nace bazan gaya maka suna na ba. Amma dai ni ne..."


Armad ya tsaya cikin mamaki yana kallon wannan saurayi yana ziga kansa. "Ance duk wanda yace shi shi ne to kuwa ba shi bane." 


Koda yaji abinda Armad ya faɗa sai saurayin yayi murmushi ya ce, "mahaifina ya mulki duniya kuma nima na zauna akan karagar daya zauna, kaga sarki ɗan sarki kenan. Jikina daga izza aka halicceshi kamar na mahaifina maimakon naka da aka halitta da walƙiya, kaga ni ne izza ɗan izza. A jiya na gagari Bihanzin da Sarkin-sarki da Ƙaraiƙisu, a shekaran-jiya kuma na gagari Dumaƙisu da Hidaya da Haruta da Maruta. Acikin magana ta meye ba daidai ba, abinda kawai na manta ban faɗa ba shi ne yaƙi na da Kuyurussa'ayi."


Armad ya cika da mamakin yadda wannan saurayi ya saki jiki dashi yake ta bashi labari. "Maiya faru a yaƙin ka da Kuyurussa'ayi?"


Saurayin ya fashe da dariya. "Guduwa nayi. Amma bani kaɗai na gudu ba, harda yayarka Hidaya." Ya ƙara fashewa da dariya mai cike da kewa da tuna da. "Nina fara guduwa amma ita ce ta kawo shawarar a gudu. Bazan gaya maka yadda akai muka gudu ba. Haha..."


Armad yai kasaƙe yana saurare domin ya kasa gane ina labarin ya dosa. Hasali dai bai san waye wannan saurayi ba, amma dai koma meye lalle shi ne ya ara masa ruhin jikinsa. Kuma ga dukkan alamu wannan saurayi yasan Hidaya sosai da sosai.


Saurayin yaci gaba da cewa, "Kash, nace bazan gaya maka yadda akai muka gudu ba."


Armad yai ajiyar zuciya ya ce, "ba saika gayamin ba amma ka gayamin kokai waye? Ya akai kasan Heeda? Mai yasa ka aramin ruhinka? Kuma meye alaƙarka dani?"


Saurayin ya amsa da cewa, "duk wannan tambayoyin baza ka sami amsar ko ɗaya ba. Babban abinda ya kamata ka maida hankali akai shi ne mutun miliyan nawa ne suke rayuwa a matsayin bayi a yanzu haka? A wanne ƙasashe suke? Yaya zakai ka kaɓutar dasu? Wanne shiri kake dashi? Hidaya ta sallama ranta saboda kai, dole ka cika burinta na kawar da cinikin bayi a doron ƙasa."


Armad ya fahimci abinda wannan saurayi yake faɗa. Yasan kuma bazai taɓa bashi amsar tambayoyinsa ba a wannan lokaci. Saboda haka saiya canja tsarin tambayoyinsa. "Idan har kai da Hidaya duk kun kasa da Kuyurussa'ayi tayaya kuke ganin zan iya?"


Saurayin ya tashi zaune ya dafa kan Armad ya ce, "duk wani ilmi na yadda ake sarrafa izza da idanuwan gidan Wilbafos yana cikin littafin-takobi. Zai haska maka yadda zaka sarrafa idanuwanka da Miyurarka. Babban dalilin da yasa abin yake maka wahala a baya shi ne kana amfani da ruhi na ne maimakon naka. Kada ka manta ba kai kaɗai na bawa ruhi na ba."


Armad yai zumbur ya miƙe tsaye cikin mamaki, "bani kaɗai ka bawa ruhinka ba? Yawo kake kana rabawa mutane ruhinka? To wai saboda me? Kuma tayaya?"


Saurayin yayi shiru yana kallon Armad tsahon lokaci kafin daga bisani ya ce, "nayi alƙawarin zan amsa maka dukkan tambayoyinka bayan ka hana cinikin bayi a doron ƙasa. Abu ɗaya dazan bayyana maka a yanzu shi ne Ururu sune suka ƙirƙiro cinikin bayi amma akwai wanda baza su taɓa yadda a daina cinikin bayi ba. Waɗannan mutane sune suka fi kowa amfana da harkar cinikin bayi domin tanan suke samun dukiya da kayan haɗa ɗalasimai da kuma yaƙutun izza. A duk shekara akwai dubunnan mutane da ake yin safararsu daga ƙasashen ƙasa zuwa doron ƙasa na farko. Wannan mutane siyar dasu ake a matsayin bayi, Ururu suna bada yaƙutun izza da ɗalasimai da sauran kayayyaki a maimakonsu. Koda Ururu zasu janye matakansu masu kula da rukunin Jinzidal baza a daina cinikin bayi ba.


"Mai yasa kaga mutane irinsu yaron nan Daljari sun shahara wajen cinikin ɗalasimai. Ko a ƴan-watannin baya Daljari yakai bayi dubu ɗari biyu da hamsin doron ƙasa na farko ya karɓo yaƙutun izza. Nan bada daɗewa ba shima zai fara haɗa fasahar kwangila. Kaga makarantar Babila da sashin ikwatora da hatsabibiyar matar nan sarkin-sarki da Banzir Shishirui ai tuntuni suke cinikin bayi."


Jin wannan bayani sai yasa Armad ya sandare a wajen da yake. Kusan duk abubuwan da wannan saurayi yake faɗa bai sansu ba. Hasalima basu bada wata ma'ana ba. 


Armad ya tambaya a nutse, "Kace ƴan watannin baya Daljari ya kai bayi doron ƙasa na farko?"


Saurayin ya gyaɗa kai, "eh mana, ka tambayi Hidaya. Da nabi shawararta da tuni mun tare musu hanya. Amma sannu a hankali lokaci zaiyi da za muyi maganinsa."


Armad ya tari numfashinsa ya ce, "Sarki Daljari ai yafi shekara da mutuwa, ko wani Daljarin kake nufi?"


Saurayin ya ce, "sarki kuma? Yaushe ya zama sarki?"


"Sarkin Jinzidal mana. Kafin ya mutu ɗaya ne daga cikin sarakuna biyar na Jinzidal." Inji Armad.


"Menene kuma sarkin Jinzidal?"


Armad ya ware ido cikin mamaki, "baka san sarakunan Jinzidal ba? A wacce duniyar kake rayuwa?"


Maimakon saurayin ya bashi amsa sai yayi masa wata tambayar, "a wacce shekara muke yanzu?"


Armad ya amsa da cewa, "Shekarar 1860 bayan Amri." 


Nan take saurayin ya ƙifta ido tare da jan dogon numfashi. A lokacin wata fahimta ta bayyana a idonsa wadda da babu ita, ya buɗe baki a nutse ya ce, "kasan duk sanda akai amfani da fasahar raba ruhi ta [Zungetsu] ruhin da aka cire yana shiga baccin dole. Lalle nasha bacci, tun shekara ta goma sha biyu bayan Amri nake hutawa. Bani labarin abubuwan da suka faru bayan bananan."


Nan take Armad ya kada baki ya ce, "indai kana so kasan wani abu to saika amsamin tambayoyi na."


Nan take wannan saurayi yayi murmushi tare da girgiza kai, "kada ka damu a hankali zaka samu amsar tambayoyinka amma ba yanzu ba. Ina Hidaya?"


Armad ya haɗe rai yana tunanin amsar data kamata ya bashi amma daga ƙarshe ya fasa. Ya kwashe duk abinda ya faru da Hidaya da kuma dalilin zuwansa Babila ya gayawa wannan saurayi. Kafin ya gama yaga kwalla tana kwarara daga idanun saurayin. "Ta mutu... Ta mutu.... " 


Yana mamakin cewar Hidaya ta mutu. 


Armad yayi masa shiru ya bashi damar nutsuwa kafin daga bisani ya miƙe tsaye. "Koma waye kai kuma koma meye niyyarka ina godiya da aron ruhinka daka bani. A yanzu ina so na fita daga wannan duniyar na ƙarasa abinda na fara."


Armad ya fuskanci cewa hirarsu da wannan saurayi baza ta ƙare ba kuma yana da abinyi. Har ya juya sai saurayin ya riƙe masa hannu yana cewa, "zan bar maka ruhina kaci gaba da amfani dashi, zan koma bacci har zuwa sanda ragowar sassan ruhi na zasu dawo. Ni kaina a yanzu ban san inda ragowar sassan suke ba kuma bansan dalilin da yasa na raba su ba, kuma bansan dalilin da yasa na ara maka ruhina ba. Abubuwan da nake iya tunawa basu da yawa, wannan shi ne haƙiƙanin dalilin da yasa bazan ce maka komai ba. Amma nayi alƙawarin duk sanda ragowar sassan ruhi na suka dawo zan gaya maka amsar tambayoyinka. Zaren-izzar ruhinka da idanunka sun farka, sannna kuma kana da littafin-takobi dazai nuna maka hanya. Ka fita waje ka nunawa duniya mai ake nufi da zuri'ar Wilbafos."


Armad ya gyaɗa kai. Har ya juya zai tafi saiya juyo ya ce, "mene ne yaƙutun izza?"


Saurayin ya haɗe gira cikin mamaki. Bayan ɗan lokaci ya amsa da cewa, "idan ka fita ka tambayi wani ɗalibin a Babila."


Armad ya gyaɗa kai tare da tashi sama. Ya tsaya a kan iska. Jikinsa da ruhinsa da zuciyarsa duk sun banbanta dana da. Duk wani motsinsa a lissafe yake yana karanta tafiyar izza. 


Acikin miliyoyin zaren-izzar da yake gani akan idonsa anan ya lalubo na Hidaya, sannan ta ƙarfin tsiya ya kamashi ya riƙe. Haka na faruwa iska ta dare gida inda ƙofa ta bayyana. Armad ya taka ya shige.


Jim kaɗan ya bayyana a ƙofar-gaskiya. Hidaya na zaune akan kujera taga futowarsa. Amma kafin ta motsa ya daki Miyurarsa inda dukkan takubba uku dake ciki suka fito fili suka haɗe a matsayin takobi ɗaya. Doguwar takobi jajawur mai baki biyu. Armad ya kaiwa zaren izzar sara da niyyar rabashi biyu. Duk wani zare daya shiga gaban takobin sai dai kaga ya ɓace ɓat. Yana zuwa ya daki zaren-izzar Hidaya inda wata ƙara mai tsananin razanarwa ta tashi. Tartsatsin wuta da hayaƙi sukai sama. 


A gefe guda kuma Hidaya ta faɗo daga kan kujerarta. Tana taɓa ƙasa tayi aman jini baƙi-irin. Ta ɗaga ido ta kalli Armad cikin mamaki da ɗimuwa. 


Yaro ya girma!

***

Babi na 214-215

***

Hidaya ta miƙe a hankali ta tsaya tana kallon Armad cikin mamaki. Wannan ne lokaci na farko da wani mahaluƙi ya taɓa lalubo zaren izzarta domin kuwa ta kware wajen ɓoye zaren izzarta ga barin abokan gaba. Idan abokin gaba bai gani ba babu yadda za'ai ya iya cutar dakai saboda haka Hidaya ta ɓata lokaci matuƙa wajen koyar dabarun ɓoye zaren izzarta da yi masa Hijabi. 


To amma a har kullum Hidaya mutun ce mai taka-tsantsan da shirin kota kwana, saboda haka duk da ta ɓoye izzarta bata barta haka. Akwai ɗalasimai na sirri wanda take amfani dasu wajen ƙarawa zaren izzarta kariya da tsaro. 


Duk da Armad ya samu damar saran izzarta amma bai iya tsinka zaren ba. Tayi aman jini mai kauri saboda ƙarfin saran amma duk da haka tana nan a tsaye bata je ƙas ba. Idanunta suna kafe akan Armad tana nazari. 


Akwai wani sirri acikin idonsa wanda hatta a nata idanun babu. Banda haka kuma Miyurarsa ita ma ta banbanta, maimakon ace cire takubban da yayi ya rage mata ƙarfi sai kara mata yayi; kai kace dama can takubban ne suke matse ta. Wasu lambobi da yaren Elburish suna kewaya tambarin Miyurar suna haske. Shi kuma mutun-mutumin dake tsakiyar miyurar ya yarda al'amudinsa ya miƙa hannayensa biyu gaba kamar yana riƙe da abu amma kuma bata iya ganin komai aciki. 


Nan take ta goge bakinta ta miƙe ta fara kirawo ɗalasimai manya da ƙanana, na jiya dana shekaran jiya. Wani ƙaton hatimi ya bayyana a tafin hannunta inda ta dunƙule hannun ta kawo wa Armad duka dashi. Hatimin yai fitar burtu yai kan Armad zai haɗiye shi. A lokacin wannan mutun-mutumi ya motsa babban ɗan'yatsansa na hagu sai kawai dukkan izzar dake jikin hatimin ta ɓace ɓat. Inda shima hatimin ya narke ya bi iska. 


Amma maimakon Hidaya taji haushi sai kawai ta fashe da dariya domin ta gano abinda take so. Dama wancan hari na bincike ne, tana so ta tabbatar da abinda take tunani. 


"Haha... wato kamar yadda aka halicci Al'yaya kaima haka mutun-mutumin Miyurarka yake. Abinda ban gane ba shi ne alaƙar Al'yayan daka samar a ƙofar garin Khan da kuma wannan mutun-mutumi. Wanne ya samarda wani? Ko kuma kowanne zaman kansa yake?"


Armad najin haka ya haɗe gira domin kwata-kwata bai gane abinda take nufi ba. Kafin ya tambaya taci gaba da bayani. 


"Nasan baka sani ba amma amfanin Al'yayan dake ƙofar garin Maikironomada shi ne kare zaren izzar duk wanda ke cikin ƙasar. A tafin hannayensu suna riƙe da kowanne zare suna bashi kariya. Da farko da naga mutun-mutumin miyurarka ya yadda al'amudinsa ya ware hannu ban gane mai yake faruwa ba amma yanzu na gane. Mutun-mutuminka yana riƙe da zaren izzar mutane. Abinda ban sani ba shi ne waɗanne mutanen? Ni dai tabbas ina ciki domin badan haka ba da baza ka iya lalubo zaren izza ta ba. Bayan ni akwai wasu dubban mutane wanda mutun-mutuminka ke riƙe da zaren izzarsu amma bana iya ganin yawansu ballantana nasan ko su waye. Lalle Miyurarka ta banbanta, wannan zai baka damar rinjaye akan abokan gabarka koda sunfi ƙarfinka indai kana da zaren izzarsu. Amma kayi sani cewa ni ma na banbanta."


Hidaya na zuwa nan a zancenta idonta na dama ya cika da haske kafin daga bisani ya juye izuwa hoton rana. Na hagu kuma ya juye izuwa hoton wata. 


Fasahar rana da wata!


Armad yai tsalle baya ya dire tare da nunata da takobinsa. Ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya sannan ya kira duk wata fasaha ta kare kai domin tunkarar wannan hari. 


Koda bayyanar idanuwan Hidaya guda biyu sai rana da wata sukai duhu, dukkan wani haske ya kau ga barin duniya. Babu kowa sai ita, sarauniyar izza a jiya da shekaran-jiya. Kada mai karatu ya manta idanunta na dama kaɗai shi ne ya tarwatsa Hajarul-ururu da ankokin dake sawa al'ummar ƙasashen-ƙasa takunkumi. Na hagun kuma shi ne ya tsare yarima Dumaƙisu ya hanashi motsi tsahon lokaci. 


A halin yanzu Armad ya gama shiri domin tunkarar wannan idanu guda biyu a lokaci guda. Duk da ƙarfin fasahar baza takai kamar sanda Hidaya tana raye ba amma duk da haka akwai tsoro aciki. Dukkan wani gashi a jikin Armad yana gaya masa ya gudu, yana gaya masa mutuwa. Armad shi ma yaji a jikinsa cewa koda ya ninka haka karfi bazai iya ɗaukar wannan fasaha ba a lokaci guda. Amma ba'a san maza da gudu ba. 


Hidaya tayi murmushi ta ce, "ALLAH ya jiƙan ka."


Tana rufe baki ta saki fasahar dukkan idanuwan guda biyu a lokaci guda. Hoton rana da na wata suka bayyana akan iska suka tunkaro Armad gadan-gadan. A lokaci na farko gumi ya fara keto masa. Idan ya mutu ya riga ya mutu kuma babu wanda zai dawo dashi. Kuma babban tashin hankalin shi ne bai san wata hanya da zai iya tseratar da kansa daga mutuwa ba a dai-dai wannan lokaci.


Yana tsaye watan da ranar suka iso. Ya kai musu sara da takobinsa ta izza amma suna haɗuwa sai kawai takobin ta narke, sannan hannunsa ma ya narke kamar kitse. Watan da ranar suka wuce suka daki ƙirjinsa lamarinda yasa yai ƙara mai razanarwa wadda har a waje sai da aka jita. Nan take walƙiyar ta ɓace jikinsa ya dawo dai-dai, sannan ya fara daddarewa yana ɓantarewa kamar biskit. Yana ji yana gani jikinsa ya tarwatse ya zube a ƙas kamar wake. Zafi da ƙuna da raɗaɗi suka cika ruhinsa amma babu damar yin kuka.


Tabbas a wannan lokaci yana jin mutuwa tana gab da ɗaukansa amma abin mamakin duk da haka bai cire rai ga rayuwa ba. Yana jin alamun rai a jikinsa. 


Hidaya tayi ajiyar zuciya. An riga an rufe babin Armad. A wannan lokaci a wajenta Armad ba wani bane illa wani baƙo mai burin sace ruhinta yayi amfani dashi. 


Duk duniya tayi tsit tayi shiru kowa ya rasa abinda zaice. Wasu suna ganin kamar wani abu zai iya faruwa amma da dama sun san cewa an gama. Sai dai kuma wani badai Armad ba.


Ana cikin haka wani abu wanda da Armad da Hidaya basu da masaniya akai ya faru. 


Jikin Armad da ruhinsa daya tarwatse ya fara rabewa gida biyu; ɓarin dama dana hagu. Dukkan wanda yayi ɓarin hagu baƙi ne, na dama kuma fari ne. Bayan ya gama rabewa sai baƙin ya ƙara narkewa ya nutse acikin ƙasa. Shi kuma farin ya fara juyawa yana haɗe jikinsa. Bayan ɗan lokaci ya koma izuwa walƙiya, sannan ya koma sinadarin Yeniy, kafin daga bisani ya koma zaren-izza illa.


Wannan zaren izza ya haɗe jikinsa a hankali ya koma ɗan ƙaramin mutun wanda baifi jariri ba. Ana haka sai jaririn ya fara girma, ƙafafuwansa da hannayensa suka ƙara tsayi suka koma na manya. Sannan kansa da wuyansa da gangar jikin suma suka koma na manya. Har yanzu babu fata a jikinsa ballantan a gane waye saboda haka duniya tayi tsit tana kallo. Hatta ruhin Hidaya dashi kansa Armad ɗin da abin ke faruwa a kansa basu da masaniya.


Bayan ɗan lokaci wannan halitta ta juye izuwa siffar Armad Wilbafos. Sai dai wannan Armad ɗin na daban ne, jikinsa na izza ne da walƙiya. A duk sanda ka kalli fatarsa zaka ga wani haske yana tashi mai razanarwa da firgici, yaro bai isa ya kusanto ba.


A hankali ya miƙe ya tsaya, ya fara kallon duniya. A da idan yana kallon zaren izza akwai dishi-dishi da duhu, kuma baya iya ganin sunan mai zaren amma yanzu komai ya bayyana a fili tar-tar. Babu wani abu da yake ɓoye masa. Hasalima yana kallon mutun-mutumin dake cikin miyurarsa kuma yana ganin zarurrukan izzar dake riƙe a hannunsa. Wato zaka iya cewa bawai a riƙe yake da zarurrukan ba, kawai dai kamar shafa su yake kuma sabida kusancin dake tsakaninsu zai iya damƙar kowanne a duk sanda yayi niyya. 


Yawan zarurrukan suna da yawa matuƙa tayadda lissafa su bazai taɓa yiwuwa. Idan aka tambayi Armad da wannan yawan zaren da yawan mutanen duniya wanne yafi bai sani ba. 


Bayan ya gama nazarin zaren ya juyo izuwa kan Hidaya. Suna haɗa ido wani abu ya kaɗa acikin zuciyarta. Lalle ta gane wannan mutun dake tsaye a gabanta, wannan mutun ba baƙo bane kuma ba mai son sace ta bane. Wannan mutumin ƙaninta ne ciki ɗaya, Armad.


Nan take kafin da Hidaya tasa akan ruhinta kafin ta mutu ya ɓalle. Dukkan wani sirri data ɓoye ta ajiye acikin ruhinta saboda wannan rana ya bayyana. Ita ce ta saka wani sirri acikin fasahar rana da wata wanda zai narka jikin Armad ya cire duk wani ɗan-adantaka a jikinsa, ya mayar da jikinsa ainihin yadda yake wato jikin izza da walƙiya. Kuma ita ce tasa idanunta su gane wannan jiki na Armad idan ya bayyana. Sannan kuma bayan ta gane shi tunaninta da kwakwalwarta su dawo. 


Haka kuwa komai ya faru. Tasan dole Armad zaizo neman ruhinta ko ba daɗe ko ba jima. Idan yazo kuma zasu fafata har zuwa sanda zatai amfani da wannan fasaha. Idan haka ta faru zata tsarkake Armad da fasahar rana da wata sannan ta bishi. 


Murmushi kawai tayi Armad yasan cewa Hidayansa ta dawo. Ya tafi da gudu zai rungumeta amma yana zuwa yaji jikinsa ya kama iska kamar babu kowa a wajen. Ya juyo cikin mamaki, a lokacin ya gane abinda ke faruwa. 


Kowanne ruhi ana bashi jiki a yayinda za'a fara wannan gasa amma daga lokacinda aka ci galaba akan wannan ruhi aka kamashi jikin zai ɓace ya koma ruhi kawai. Shi kuma ruhi bashi da jiki sannan kuma babu wanda yake ganinsa sai maishi. Misali a halin babu wanda yake ganin Hidaya banda Armad. 


Hidaya ta ce, "akwai labari amma mu gama da nan tukunna mu keɓance. A halin yanzu akwai mutane dubu tara da ɗoriya suna jiranka a ƙofar asali. Mu fara takansu."


Armad ya dube ta cikin mamaki ya ce, "kema zaki taka rawa ne?"


Hidaya ta girgiza kai, "a'a mana, ko ina jaririya ai nafi ƙarfin faɗa da ƴan'tsaki. Kai dai kawai muje na ga kamun ludayinka. Idan naga kana buƙatar taimako nasa baki."


Armad ya fashe da dariya, "taimako? Kada ki damu."


A hankali Armad ya juyo ya fito daga ƙofar gaskiya. Yana fitowa yai arba da Tankel, mutuminda ya ƙara masa kuɗin shiga. Koda suka haɗa ido sai Tankel ya fara karkarwa, ba shiri ya zube a ƙas, "kai mun rai, Izza." ya ce. 


Armad bai damu da mai mutumin yake cewa ba kuma bai ma ishe shi kallo ba, sabida haka ya wuce kai tsaye zuwa ƙofar-asali. Akan hanyarsa dubban ƴan kallon dake wajen wanda kafatalinsu ɗaliban dake wannan makaranta ne suka zuba masa ido. Wasu suna masa kallon tsoro wasu kuma sunai masa kallon wanda ba mutun ba. Tun bayan ruhin deban da Bihanzin ya ci galaba akai ya samo hankakan mutuwa ba'a taɓa samun wanda ya shiga ƙofar-gaskiya ya fito ba. Ko wanne irin hankaka Armad zai samo?


Ɗaya daga cikin malaman Babila mai suna Shaihu Kyandir ya bayyana a gaban Armad. A idanunsa akwai jinjina da yadda a yayinda yake kallon Armad. 


"Shugaban makarantar Babila, babban Shaihu, ya ce a gaya maka indai ka ɗaga ƙafa baka kashe ɗaliban Babila dake cikin wannan gasa ba to zaiyi maka tarɓa ta musamman idan ka kammala wannan gasa. Kuma zaku ɗaura alaƙa ta musamman wadda zata taimaki juna."


Armad yayi jim yana tunanin amsar dazai bayar inda Hidaya ta ce, "ka amince, akwai manyan ma'abota izza a wannan makaranta wanda baza kaso ku sa ƙafar wando ɗaya ba. Amma ka tambayeshi ɗalibai kaɗai ko, domin akwai wanda zamu kashe."


Armad ya dubi shaihu Kyandir ya ce, "amma ɗalibai kaɗai ko? Duk wanda ba ɗalibi bane babu ruwanku?"


Kyandir ya gyaɗa kai, "eh... wannan haka yake."


Armad ya ce, "na karɓa." Sannan ya wuce ya buɗe ƙofar-asali ya shiga."


Yana shiga yayi arba da wani fili fetal. A bayan filin akwai ƙaton daji da manyan bishiyu wanda da yawansu an sassaresu. A can gaban filin kuma akwai wani makeken kogi iya ganinka yayi sama ya tokare da samaniya. A saman kogin akwai jiragen ruwa maƙire da mutane. Abinda ake so shi ne ka je ƙarshen wannan kogi koma ta wacce hanya ce. Da dama daga cikin wanda suke wannan mataki sun yanke shawarar haɗa ƙarfi da ƙarfe domin samun nasara. Hakan ne yasa suka shiga daji suka yanko bishiyu suka gina jirage sannan suka shiga ciki. 


Armad ya tashi sama ba tare da ɓata lokaci ba ya nufi kan ruwan. Yana isa ya gane cewa ashe iska ce mai ƙarfin gaske take yawo akan ruwan tana hana mutane yin gaba ko baya. Sannan kuma ga muggan namun ruwa suna kawo farmaki. Yana ganin haka ya kira ɗalasimi.


"[Kaban'shisu]"


Bai tashi bayyana a ko'ina ba sai a gaɓa. Ya juyo baya ya hango dubban mutane, wasu sun kusa ƙarasowa wasu kuma suna can baya. Amma wanda ke wajen suna ganinsa suka afka masa domin tun daga sanda ya mallaki ruhin Heeda aka sanar da duk wanda ke cikin gasar abinda ke faruwa sannan kuma aka basu kamanninsa. 


Koda ganin haka sai Armad yai ajiyar zuciya ya gyaɗa kai tare da cewa, "ku tsaya a inda kuke idan kuna so kuga gobe."


Amma ƙaddara ko jinsa basu yi ba. Hakan ya fusata shi ya daki ƙasa ya kira babban ɗalasimi.


"[Sanyin-babban-sihiri]"


Nan take wata iska mai ɗauke da ƙanƙara ta tashi sama tai kansu. Duk wanda iskar ta taɓa sai kaga ya koma ƙanƙara. Hatta kogin sai da ya daskare. Jiragen ruwansu suka daskare sannan suma suka daskare. Cikin daƙiƙa guda komai ya koma ƙanƙara. Babu kowa sai Armad sai izzarsa. 


Hidaya tayi tsaki ta ce, "bari nayi bacci dan bazan iya ganin wannan baƙin cikin ba, harma ana iya kawo wa sarkin izza hari! Abin takaici wasu ƴan tsaki ne ma, ya zama dole na ɗau mataki akan wannan da zarar na tashi daga bacci."




***

Babi na 216-218

***

Cikin ruwan sanyi Armad ya wuce izuwa mataki na biyu. Sai dai saɓanin yadda yayi tunani a wannan mataki babu kowa. Ya waiga dama da hauni babu kowa, gabas da yamma sama da ƙasa babu kowa. Shi kansa filin ya banbanta da na baya domin kuwa ko'ina a cike yake da wasu irin baƙaƙen zarurruka suna bada baƙin haske mai walwali.


Armad ya dubi Hidaya yaga idanunta a rufe suke tana bacci saboda haka yaci gaba da duddubawa. Bayan ɗan lokaci saiya hangi wani saƙo fari-fari ruwan ƙasa. Nan take ya rankaya a guje yai wajen. Yana isa ya tadda ashe ƙasa ce a wajen.


Ya miƙa hannu ya ɗebi ƙasar amma kafin ya miƙe ƙasar ta juye izuwa baƙaƙen zaren. Shima wajen ya juye izuwa baƙi. Armad ya yamutse fuska cikin mamaki. Ya miƙa [Yanayin izza]rsa sama amma baiji komai ba. Ko'ina babu komai tamkar babu kowa a duniyar. 


Yana tsaye kawai yaji tsigar jikinsa ta tashi, yana waiwayowa yaga kyallin tsinin takobi ya dososhi, tsakaninsa da ita kamu uku. Nan take ya juye izuwa walƙiya. Takobin ta soke shi a allon kafaɗa kuma abin mamaki sai kawai yaji saran ya shigeshi duk da kuwa kafaɗarsa tana walƙiya. Ya duba babu jini amma duk da haka yana jin saran a jikinsa kai kace ruhinsa aka sara. Girman takobin yakai zira'i maitan amma bata da faɗi sosai. Ana haka sai takobin ta ɓace ɓat ko sama ko ƙasa.


Akwai abubuwa da dama da suka shige masa duhu: na farko tayadda akai saran ya shigeshi; na biyu tayadda akai baiji tahowar takobin ba ta [Yanayin izza]rsa; na uku waye ya aiko takobin kuma daga ina; na huɗu mai yasa takobin ta ɓace.


Yana cikin wannan tunani ne yaga ƙasar da yake kai ta luma ciki ta kalmashe kanta tana neman haɗiye shi. Yai tsalle ya kira fasaha:


"[Tafiyar Taurari]"


Nan take ya tsaya cak akan iska tare da zare takobinsa. 


Ana haka sai duniyar ta juye izuwa wannan baƙaƙen zarurruka masu kauri da tsayi. Kowanne zare yana da tsini kamar mashi, suka haɗe kansu suka yi kansa. Sannan ta samansa kuma takobin ta ƙara bayyana. 


Armad yai murmushi ya daki iska da ƙafarsa inda wata guguwa ta tashi ta watsa zarurrukan sannan ta tura takobin baya. Ya ɗaga hannunsa sama inda jar Negrinki ta bayyana ta juye izuwa siffar takobi. Yayi amfani da takobin ya kai sara gabas. Nan take iska ta dare gida biyu, duk abinda ke wajen ya shige cikin duniyar Negrinkin Armad. Lamarinda ya samarda wata ƙofa izuwa duniyar.


"[Kaban Shísu]"


Ya kira ɗalasimi ya shige cikin ƙofar. Da takobin da zarurrukan suka bi bayansa. 


Yana bayyana acikin duniyar Negrinkinsa takobin da zarurrukan suka biyo shi, amma nan take wutar dake ƙasa tai ambaliya ta haɗiye su. 


Har zuwa wannan lokaci Armad bai gane abinda ke faruwa ba amma maganar ita ce bashi da buƙatar sanin abinda ke faruwa. Akwai wani mahaluƙi acikin gasar da yake amfani da wata ɓoyayyiyar fasaha yana kawo masa hari, bashi da buƙatar sanin ko waye kuma bashi da buƙatar sanin dalili ko kuma ba'asi, abinda kawai ya sani shi ne hukunci ya tabbata akan wannan mahaluƙi ko waye shi. 


Armad ya miƙa hannunsa ya kamo zaren izzar ya fito daga cikin duniyar. Bai bayyana a ko'ina ba sai a mataki na huɗu wanda hakan ke nuna cewa ma'abocin zaren izzar daya kamo yana kan wannan mataki. Ko mai ya faru da mataki na biyu dana uku? Ko ina sadaukan da suke kai?


Armad baida lokacin amsa wannan tambayoyi, abinda ke gabansa shi ne fuskantar mutumin dake gabansa wato Hasanu Sisiyu. Ɗaya daga cikin mutane na farko da suka fara haɗuwa da Armad bayan futowarsa daga gida. Yayan Nostaljiya da Kiru, ɗan gidan sarki Bihanzin mai dauwamammen sara. Yana tsaye daga nesa yana jiran Armad, a jikinsa akwai dogayen kaya baƙaƙe wanda akaiwa kwalliya da gashin-bakin shaiɗanu. Daga gefen kafaɗarsa ta hagu ana hangen mariƙin takobi ya tashi alamun takobin na ɗaure a bayansa. 


Daga gefen Hasanu akwai wani saurayi fari dogo, ya ɗan ɗara Hasanu tsayi da kamala. Yana da kaifafan idanu da dogayen kunnuwa. Wannan saurayi ba kowa bane illa Elbinuil Randuil ƙanin sarkin-sarki. Koda suka haɗa ido da Armad sai tsigar jikinsa ta tashi. 


Kowanne acikin wannan samari biyu da suke niyyar afkawa Armad manyan gobe ne a daularsu. Zaka iya cewa babu wani matashi dake rayuwa a daular Sisiya ta Bihanzin wanda yakai Hasanu ƙarfin izza, kamar yadda babu wanda yakai Elbinuil a daular Elbis. 


"Armad, tsahon lokaci, ina ƙanwata?" Hasanu ya tambaya cikin tsokana.


"Nasan mun yaudareka a fannoni da dama amma wadda tafi sosa min rai ita ce ta ɓangaren Nostaljiya. Kai a tunaninka ka kai matsayin da zamu baka auran jinin Shishirui? Nostaljiya ba jininmu ba ce, wata mara asali ce kawai akan hanya muka tsinto ta domin biyan buƙatar mu. Saboda haka kada ka zarge mu dan mun yadda ita. Nasan baka sani ba amma sabida hasken fuska da take dashi kafin mu tsinto ta sana'ar farantawa maza rai take a gidan magajiya. Idan baka gane ba sana'ar karuwanci kenan, kuma..."


Kafin ya rufe baki kawai kyallin Armad ya gani a gefensa. Armad ya miƙa hannu ya daki ƙirjinsa inda ƙirjin ya loma ciki, sannan yasa farce ya fasa ƙirjin ya finciko zuciyar Hasanu daga ciki. Jini yayi feshi, zuciyar ta ƙara bugawa sau uku kafin daga bisani ta tsaya cak. Kafin Elbinuil ya motsa Armad ya kawo masa sara da takobin Negrinki. Takobin ta sara wuyan Elbinuil ta shige kamar kitse. Take shima Elbinuil ya faɗi ƙasa matacce. 


Armad ya kalli gawarwakinsu ya ce, "Duk wanda ya faɗi kalma ɗaya tak ta ɓatanci ga ahlin gida na hukuncinsa kisa."


Sai dai kuma bai gama rufe bakinsa ba yaga duniyar daya sani a da tayi farfari kafin daga bisani tayi hazo-hazo ta ɓace. Abu na gaba daya gani shi ne Hasanu da Elbinuil suna tsaye a ɗan nesa dashi suna musu.


"Na gaya maka idan ka bari aka ƙara kashe ka bazan dawo dakai ba." Inji Elbinuil.


Hasanu ya ja dogon numfashi ya ce, "bansan yana da sauri haka ba amma na gane shi yanzu zamu gama dashi. Kayi ta dama zanyi ta hagu."


Elbinuil ya haɗe rai ya ce, "a'a, barni dashi kawai nizan kaishi lahira. Ka huta."


Hasanu ya girgiza kai, "bawai nace baza ka iya kaishi lahira kai kaɗai ba, saboda ka adana ƙarfinka, kaga akwai Ƙaizadu da Ikenga a sama suna jira."


Haka suka ci gaba da musu tsahon daƙiƙu, Hasanu yana nuna falalar suyi a tare shi kuma Elbinuil yana so yayi shi kaɗai. Armad kuma na gefe yana nazarin abinda ke faruwa. Tabbas ya kashe su ba mafarki yake ba, amma Elbinuil yayi amfani da wata sihirtacciyar fasaha ya dawo dasu. Armad ya ɗan lazamci fasahar: maimakon fasahar Ikenga da take dawo da lokaci baya wannan fasahar bata amfani da lokaci, abubuwan da suka faru take canjawa. Misali kashe su da Armad yayi shi ne ya canza amma lokaci yana nan. To amma abinda bai sani ba shi ne tayaya fasahar take aiki? Menene makasar ta? 


Sai dai kuma kash, Armad ɗin yanzu baya buƙatar amsar wannan tambayoyi. 


Ya buɗe baki a nutse ya ce, "wataƙila ban faɗa da ƙarfi ba, bari na maimaita. Hasanu ka yankewa kanka hukuncin kisa kuma nine zan aiwatar dashi, idan kana da sauran bankwana ka faɗa amma babu tabbas zan isar. Kai kuma mara suna mai dogon kunne ban san kaba amma idan kana so hukuncin ya shafe ka ka shigo ciki."


Hasanu ya kalli Elbinuil suka fashe da dariyar mugunta. Lalle Armad bai san halin da yake ciki ba, suna buƙatar su yi masa nuni. 


Elbinuil ya ɓace daga inda yake ya bayyana a bayan Armad ya kirawo fasaha, "[Kan-Kada-Mai-Kwari]" 


Ta gaba kuma Hasanu ya ɗaga hannayensa biyu inda wata guguwa mai ɗauke da jar iska ta tashi ta turnuƙe sama. Daga cikin guguwar sai mutane suka fara bayyana. Ɗaya bayan ɗaya saida mutane sama da dubu shida suka bayyana. Wannan mutane ba wasu bane illa ɗaliban Babila dake cikin wannan gasa. Sune a mataki na biyu dana uku amma Hasanu yayi amfani da wata sihirtacciyar fasaha ya kawo su wannan waje. Abin mamakin shi ne kowanne mutun idanunsa a juye suke. Kowannensu yana zare da takobi yana fitarda aniyar kashe Armad kamar wanda aka aiko.


Armad ya tsaya cak a inda yake bai motsa ba. Ta gabansa mutun sama da dubu shida kowanne yana zare da takobi. Ta bayansa kuma Elbinuil ne da fasahar Kan-kada. 


Elbinuil ya daki ƙashin bayan Armad da kansa inda yaji kamar ya daki dutsen dala. Kansa ya fara hayaƙi kafin daga bisani yayi jajawur amma jikin Armad ko kwarzane. Dole Elbinuil ya jada baya. Mutun dubu shida da ɗoriya suka afkawa Armad da sara da suka har saida takubbansu suka dakushe suka kakkarye amma Armad bai motsa ba. Hasalima bai juyarda jikinsa izuwa walƙiya ba. Yana tsaye kamar gunki. 


Elbinuil yaga Kan-kada bazai yi ba saboda haka ya canja fasaha. "[Kan-Gwanki-Mai-Rangwangwan]."


Kansa ya ƙara girma ya zama kamar wani ɗan ƙaramin tsauni. Sannan ya juya kala yayi baƙi-ƙirin kamar al'amudin bakin ƙarfe. Yayi kan Armad da kware amma duk da haka Armad bai motsa ba, yana tsaye ƙiƙam kamar mataccen dutse. 


Elbinuil ya ƙara dukan bayansa amma Armad baiyi ko gezau ba. Elbinuil ya ƙara jada baya ya kawo kware amma ina, ko kwarzane. Koda ganin haka sai ya ƙara canza fasaha. Ya zare wata takobi mai roɗi-roɗi ruwan barkono ya yiwo kan Armad da mugun nufi. 


Sai a wannan lokaci Armad ya juyo ya kalleshi. Tsakaninsu zira'i biyu, Armad ya zare takobinsa ya rufe ta da Negrinkinsa sannan ya daki ƙasa da ƙafarsa ta hagu. Abin mamaki dukkan ƙasar wajen sai ta juye izuwa Negrinki ta yi kan Elbinuil. Koda ganin haka sai Elbinuil yayi ƙoƙarin yin tsalle sama amma abin mamaki sai ya tarar da Negrinkin Armad tayi masa lema ta sama. Ta gaba kuma ga Armad ya kawo sara. Hanya ɗaya data rage wadda zai iya guduwa itace baya saboda haka ya juya zai gudu domin yaga abinda Negrinkin Armad take yi. 


Sai dai kuma yana juyawa yaga walƙiya ta rufe ko'ina. Idan aka baka zaɓi tsakanin ka shiga walƙiya ko Negrinki babu shakka walƙiya zaka zaɓa saboda haka Elbinuil ya shige cikin walƙiyar da niyyar ya ɓulle ta baya. 


Armad yayi murmushi domin a nutse ya shirya komai. Acikin walƙiyar ya ɓoye Negrinkinsa. Jira kawai yake Elbinuil ya shiga ya haɗiye shi. 


Aikuwa haka akai, Elbinuil yana shiga walƙiyar ta ɓace Negrinki ta haɗiye shi, bai zame ko'ina ba sai ɗaya duniyar. 


Dama shirin Armad kenan, idan ya ɓatarda Elbinuil kaga babu mai dawo da Hasanu idan ya kashe shi. Saboda haka ya juyo kan ƴan-kuci ku-bamun sadaukan da suke ta kawo masa hari. 


"[Sanyin Babban Sihiri]" 


Take dukkansu suka ƙame cikin ƙanƙara. Babu kowa daga Armad sai Hasanu.


Sai dai kuma abin mamaki duk da haka Hasanu ko gezau baiyi. Yana tsaye yana kallon Armad. 


Bayan ƴan daƙiƙu na kallon kallo Armad ya dubi Hasanu ya ce, "na riga na rubuta sunanka a wanda zasu isa lahira yau, koda duniya zata haɗu akan su kare ka sai ka isa lahira. Hukuncin zagin ahlina kisa."


Hasanu yai murmushi ya ce, "kasan yadda akai nasan ka shiga ƙofar gaskiya tun kafin kowa ya sani? Kasan yadda akai na ɗebo wannan ƴan-tsakin daga mataki na biyu dana uku na dawo dasu ƙarƙashin iko na kuma sa suka yaƙe ka? Kasan yadda akai na kawo maka hari da babbar takobi da ZAREN LÁIDAN tun kana mataki na biyu? Idan baka sani ba to ka sani, fasahar [Láidan] kenan. Zamo na farko daga cikin wanda zasu fara ganin wannan fasaha a fili. Zamo na farko da zaka isa lahira ta hanyar wannan fasaha. Ta dalilinka za'a nunawa duniya wannan fasahar."


Hasanu ya buɗe ƴan'yatsunsa goma inda wasu baƙaƙen zarurruka suka bayyana a tsinin kowanne. Zaren guda goma sukai fitar burtu sukai kan Armad. Idan ka lura sosai wannan zarurruka irin wanda Armad ya fuskanta ne a mataki na biyu.


Koda ganin haka sai Armad yai tsalle ya kauce tare da zare takobinsa. Sai dai kuma abinda Armad bai sani ba dama can zaren ba nasa ba, harin ba nasa ba ne. Yana matsawa zaren ya sauka akan ruhin Hidaya wanda ke gishin-giɗe akan iska yana bacci. Haka na faruwa Hidaya ta buɗe ido, akwai mamaki da wasu-wasi da kokwanto a idanunta. Shima Armad haka. Yana mamakin yadda akai Hasanu yake ganin Hidaya da kuma yadda akai ya jona mata wannan baƙaƙen zarurruka.


Hidaya batai wata-wata ba ta zare takobi ta kawowa Armad sara tare da saukar masa da fasahar rana da wata. Cikin tsananin mamaki da al'ajabi Armad yayi ƙoƙarin zillewa amma a lokacin yaji wani hannu ma'aboci izza ya shiga cikin duniyar Negrinkinsa yana neman kuɓutar da Elbunuil.


Bai san hannun waye ba kuma bai san daga ina yake ba amma ya rufe ido yakai wa hannun sara a lokaci guda kuma yayi amfani da hannunsa na dama yayi ƙoƙarin kare saran Hidaya. Takobin Hidaya ta ratsa cikin takobinsa ta shige kafaɗarsa. Tsananin zafi da juwa ya ɗebeshi yayi taga-taga zai faɗi, jini yayi feshi sama.


A ɓangare guda kuma ba Armad ne kaɗai yake zubar da jini ba, shima hannun daya shigo duniyar Negrinkinsa yaji jiki. Jini ne kawai yake feshi daga wajen da Armad ya sara. Dole hannun ya haƙura ya koma inda ya fito ya bar Elbinuil. 


Shi kuma Armad ya cije baki ya dunƙule hannunsa ya saukarwa da Hidaya [Hannun-Aradu]. A tsakiyar walƙiyar akwai Negrinki Armad ya ɓoye. Hidaya ta gani amma Hasanu bai kula ba saboda haka kafin ya ankare yayi wani abu Negrinkin ta cinye Hidaya ta zuƙe ta cikin duniyar Armad. 


Armad ya ɗaga kai ya dubi Hasanu a hasale ya ce, "shikenan fasahar Láidan ɗin ko kuma akwai wani abu?"


Babban lissafin Hasanu yayi amfani da ruhin Hidaya ya yi galaba akan Armad amma haƙarsa bai cimma ruwa ba. Armad ya ɓoye Hidaya ya kuma ɓoye Elbinuil. 


Hasanu yayi murmushi tare da ƙara fito da wasu zarurrukan wanda sukai kan Armad. Abin mamaki ƙasar da Armad yake kai ita ma sai ta juye izuwa baƙaƙen zarurruka marasa iyaka. Kafin ya ankare sun cimmasa sun kanannaɗe ƙafafunsa da jikinsa. 


Nan da nan Hasanu ya fara dariya yana shewa. "Kazo hannu, yaro..."


Sai dai kuma bai gama magana ba ya rufe bakinsa. Domin kuwa ya gano cewa zarurrukansa basu kama jikin Armad ba. 


Armad ya ɗago kai a hankali ya ce, "kasan abinda ake cewa JIKIN IZZA?"


Hasanu yaji abinda Armad ya ce amma babban abinda yafi damunsa shi ne ƙullin daya gani cikin idanun Armad. Akwai kafiya da ƙololuwar dagiya da jajircewa acikin kallon Armad. Kallo ne wanda shi kaɗai zai iya tarwatsa abokan gaba. Armad ya fara taku ɗai-ɗai yana nufo Hasanu. 


Hasanu ya cije baki. A zahiri har yanzu bai gama kwarewa kan fasahar [Láidan] ba saboda rashin kwarewarsa ya kasa kama Armad da zarensa. Wato kamar mai kamun kifi ne, iya kwarewar ka idan ka zira koma iya yawan kifin da zaka kama. Wani kifin yai maka girma sai dai kallo. 


Amma duk da haka shima Hasanu jarumi ne acikin jarumai kuma bai saduda ba. Ya buɗe baki ya fara kirawo manyan ɗalasimai ya samarda wasu mutun-mutumi guda uku na jar iska a gefensa. Suka yi kan Armad da sara da suka. 


Armad bai motsa ba, ya tsaya cak suka sara suka soka amma ko gezau baiyi ba. Ko kwarzane sun kasa yi masa. Jikinsa bai koma walƙiya ba amma sabida sirrin izza dake ciki ya zama kamar wani dutsen wuta wanda baya ji baya gani. 


Bayan tsahon lokaci Hasanu ya kira wani ɗalasimin inda hankakan mutuwa ya bayyana a saman kansa. A jikin wannan hankaka akwai asalin izza da buwaya na gidan Shishirui. Anan ne Bihanzin ya ajiye sirrikansa da dukkan wani shiri, a gari banza ba'a futo da wannan hankaka sai ta ɓaci. Koda bayyanar hankakan sai wajen yayi duhu, masifu da ƙunci na korarren tsafi suka fara sauka. Armad ya zare ido domin yana ji a jikinsa akwai sharruka a jikin wannan hankaka wanda hatta jikinsa na izza bazai iya ɗauka ba. 


Amma shima Armad ba yau ya fara shiri ba. Yana ganin haka ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya, sannan ya rufe kansa da zaren izza da Negrinki. 


Hankakan yayi kansa gadan-gadan da mugun nufi. Kafin ya ƙaraso dukkan fuka-fukansa da gashin jikinsa suka cire sukai kan Armad. Kowanne gashi ya juye izuwa mashi mai cike da dafi.


"[Hannun Aradu]"


Armad ya dunƙule hannunsa ya kai duka inda dunƙulalliyar walƙiya wadda aka ƙarawa ƙarfi da Negrinki ta tashi ta yi kan wannan masu dake neman soke shi. 


Suna haɗuwa wata ƙara mai firgitarwa ta tashi sama. Ƙasar dake tsakaninsu ta dare gida biyu, iska ta daddare, feshin wuta yai sama. Dukkan wanda suke kallon wannan fafatawa a waje saida suka rufe fuskarsu cikin tsoro. 


Bayan komai ya lafa hankakan mutuwa shi kaɗai ne ya rage a sama. Yayi kan Armad gadan-gadan da wani irin sauri mai kama dana taurariya mai wutsiya. Kafin Armad ya ankara hankakan yasa baki ya caki ƙirjinsa, ya huda walƙiyar sannan ya shige ta cikin Negrinkin ya caki ƙashinsa.


Nan take izzar Armad ta fara rawa kamar zata tarwatse. Jini ya fara ɓulɓula daga wajen. Amma maimakon hakan ya ɗagawa Armad hankali sai kawai yayi murmushi tare da miƙa hannu ya taɓa Miyurarsa. Nan take izzarsa ta dawo ta daidaita. Ya miƙa hannu ya lalubi zaren izzarsa ya ƙƙɗara saita shi ya haɗe shi. Bayan ya gimtsa ya fara laluben zaren izzar Hasanu zai tsinka amma bai gani ba saboda haka ya fara taku ɗai-ɗai ya nufi Hasanu. 


Hasanu ya dubeshi cikin mamaki da ɗimuwa. Bai taɓa tunanin akwai wanda zai gagari hankakan mutuwa ba. Nan take tsoron Armad ya shiga ransa. Yana cikin wannan hali ne yaga takobin Armad ta yi kansa tana ɗauke da ƙarfin izza mai girma. 


A wannan lokaci Hasanu ya gane cewa lallai rayuwarsa tana cikin hatsari idan bai gudu ba. Domin kuwa idan ya bari ya ƙara mutuwa to fa babu wanda zai dawo dashi. 


Ya juya zai gudu amma Armad ya kai masa duka da ƙafa ya shataleshi ya faɗi ƙas. Ya bishi da takobi ya cake hannunsa a ƙasa. Hasanu yai ƙara mai cike da razani. Armad ya daki bakinsa inda gaba ɗaya haƙoran suka fice, bakinsa ya cika da jini. Ga dukkan alamu kafin Hasanu yaje lahira sai yaci duka. 


Abinka da taurin kai, bakinsa cike da jini amma ya ƙi yin shiru. "Kada ka kashe ni, mahaifiyata tafi gaban tunaninka."


Armad yai banza da ransa yaci gaba da dukan bakinsa. "Wace ce mahaifiyarka? Ko mahaifinka Bihanzin bai isa ba."


***

A dai-dai wannan lokaci da Armad yake dukan bakin Hasanu wani abin al'ajabi ne yake faruwa a waje. Wata mata mai farar fuska da dogayen kunnuwa ta bayyana acikin makarantar Bábila. Dukkan kayan jikinta na haske ne, idanunta farare ne mafiya kyawu, hancinta mafi tsari da fasali da kyawu, laɓɓanta mafi kyawun tsari da saiti. Idan tana tafiya ba'a ganin motsin ƙafafunta. Tana dira dukkan Bábila ta cika da haske. Kowa ya cika da burin ƙare mata kallo. Sai dai kuma kash, duk wanda ya waiwayo ya kalleta sai kaga idanunsa sun rufe ya makance. Daka ganta ka gama kallo. 


Nan take koke-koke da iface-iface suka fara tashi. 


Ana cikin haka dukkan malaman dake Bábila suka bayyana akan iska suka nufo inda take. Dukkansu idan ka kula akwai alamu na tsoro da firgici a tattare dasu, lalle suna tsoron wannan mace.


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...