Babi na 119 & 120: Walƙiya da Walƙiya
Yarima Bizaya yayi sassanyan murmushi yana shafa farin gashinsa. "Zahr.."
Gimbiya Zahra ta ɗan yamutsa fuska. "Nace ka daina faɗamin wannan sunan. Mai yaci 'A' ɗin. Idan zaka ce Zahra ka faɗa amma ka daina Zahr!"
Ko kaɗan yarima Bizaya bai nuna ɓacin ransa ba. Ya fashe da dariya yana cewa, "To naji.. Zahr.."
"Ka ƙara faɗa ko!!" Nostaljiya ta tashi tana huci zata tafi amma yayi sauri ya miƙa hannu zai jawo ta ya zaunar da ita amma cikin hanzari Nostaljiya ta kauce.
"Bana so wani bil-adama ya taɓa ni. Na riga na gaya maka."
Maimakon Bizaya yaji haushi sai kawai ya fashe da dariya. "Idan kina faɗar haka sai kisa naji kamar ke ba Bil-adama bace. Kuma in banda abinki ina kika ga an taɓa aure a haka. Zauna mana ko.."
Nostaljiya tai jim tana tunani kafin daga bisani ta numfasa ta zauna. "Kaga kada ma ka taɓa tunanin sonka ne ya kawo wi nan. Wannan aure da ake so a haɗamu bashi da alkhairi kamar yadda baka so na, nima kuma bana sonka."
Bizaya ya katse ta cikin hanzari. "Ke dai bakya so na amma ni ina sonki. Sannan kuma kada ki manta ke ƴar uwata ce.. A yanzu haka mahaifina da mahaifinki suna fada suna tattauna yadda za'a ƙulla yarjejeniya a kuɓutar dake daga sharrin sauran sarakunan Jinzidal dake nema su halaka ki. Wannan haɗinkan na ƙabilunmu zai bamu ƙarfi sama da na dukkan sauran dauloli. Kuma auranmu yana da muhimmanci ga wannan haɗaka."
Nostaljiya ta ɓata rai. Amma hakana dole ta daure ta zauna. Sanin cewa mahaifinta na buƙatar wannan haɗinkai domin kaucewa yaƙin daka iya afkuwa shi ne yasa ta zo wannan waje bawai dan tana son Bizaya ba.
"Ina buƙatar amsarki.. Zaki aure ni? Bawai sai kina so na ba, kawai dai aure ne da za a ɗaura dan yarjejeniya tsakanin daulolin mu."
Nostaljiya tayi shiru tana tunani tsahon lokaci kafin daga bisani taja dogon numfashi gami da girgiza kai. "Ni dai gaskiya bazan iya ba!"
Bizaya najin haka ya haɗe rai tare da yamutsa gira. "Ina ga banji ki ba sosai, kika ce baza ki iya ba?"
Nostaljiya ta gyaɗa kai.
"Gimbiya Zahra, ina ganin baki fuskanci abinda ake ciki ba sosai. Idan baki yadda anyi wannan aure ba, ƙabilata baza su taimaka muku da komai ba koda kuwa yaƙi ya taso. Kinsan a bisa kundin tsarin mulki laifin da ake zarginki dashi sarkin Jinzidal guda ɗaya tak zai iya yafe shi. Sarki Rafiya bazai taɓa yafewa mahaifinki wani abu ba, hasalima shi yafi kowa son a kaure da wannan yaƙi domin ya ɗauki fansar abinda Bihanzin yayi masa.
"Sarki Maikiro Abbas na daular Maikironomada ma bazai yafe muku ba, kema kinsan mai yasa.
"Shi kuwa sarki Hanibal na daular Hán yana da buƙata. Naji ance ya turowa mahaifinki zai yadda ya yafe muku amma a maimakon fasahar dauwamammen sara. Kema kinsan mahaifinki bazai yadda da wannan ba.
"A saboda haka ina ganin mahaifina shi kaɗai ne daga cikin sarakuna biyar na Jinzidal dazai yadda ya yafe wannan laifi. Kuma a halin yanzu shi kaɗai ne abinda ya hana ɓarkewar yaƙi. Amma kuma indai ba'a amince da wannan buƙatar aure tamu ba lallai mahaifina bazai yafe wannan laifi ba domin kamar wani abin kunya da cin mutunci ne ace mun taso tun daga daular ƙarƙashin ƙasa munzo neman aure amma an hanamu. Ai wannan zai zamo abin dariya ga mu da mutanenmu a doron ƙasa. Shin kin fahimci mai nake nufi?"
Bizaya ya ƙare labarinsa da wata mummunar dariya. Yana ji cewa dole ne Nostaljiya ta amince.
Amma Nostaljiya ta numfasa cikin ɓacin ta mayar masa da martani. "Mahaifina bazai taɓai min auren dole ba, idan zaku taimake mu a matsayinmu na ƴan'uwa ku taimake mu. Idan baza ku taimake mu ba shikenan."
Tana faɗar haka ta tashi ta juya ta bar wajen. Bizaya ya bita yana huci, kafin ta farga ya finciki hannunta. Ta juyo da ɗaya hannun zata mare shi amma kawai taji hannun nata yaƙi motsi. Ƙusar-yaƙi guda ɗaya ta kafe shi akan iska.
Ran Nostaljiya yai dubu ya ɓaci, ta dube shi ta ce, "wai kana da hankali kuwa. Kasan dai a inda kake ko?"
Bizaya yai dariya har da shewa yana cewa, "ni kuwa nasan inda nake. Ina cikin daular surukaina. Kuma dan na riƙe matata ta gobe ba wani abu bane."
"Ka bari!"
"Na bari?! Saboda me zan bari bayan an riga an bani ke. Bari ma kiga, sai na ɗaura mana aure yanzu anan"
A wannan lokaci Bizaya ya ƙara matse hannun Nostaljiya da mugunta har saida ta runtsa ido. Sannan ya taka ya ƙara matsawa kusa da ita.
"Me ma ake cewa idan za'a ɗaura aure? 'Na karɓi auren Gimbiya Zahra a bisa tufatarwa da ciyarwa da ilmantarwa?' A'a ba haka bane ko? Akwai abinda na manta, ki tuna min."
Nostaljiya ta cizi harshe, ta gama yanke shawara ta cakawa Bizaya wuƙa idan ya ƙara matsowa kusa da ita amma a wannan lokaci ne wani hannu ruwan tarwaɗa ya zagayo ta gefen Bizaya ya riƙe masa hannu gagam. Bizaya ya finciki hannunsa cikin fishi da isa amma yaji ko motsi baiyi ba kamar an siminceshi a jikin bango.
A fusace Deniz ya waiwayo ya kalli mai wannan hannu inda yayi arba da Armad Wilbafos. Nan take ya tuno waye Armad a gasar data gabata ta Jinzidal da aka gabatar a garinsu.
"Kai ne.. Armi.. ko? A'a Arme.. Arma ko? Hmm.. Kai koma dai meye sunanka kaita shafa. Kuma abinda ke faruwa anan tsakanin ƴaƴan sarakuna ne saboda haka bai shafi marasa asali ba irinku."
Armad baice komai ba, kawai ƙara matse hannun Bizaya yayi cikin fushi sannan ya fincike shi daga jikin Nostaljiya ya sata a bayansa. Shi kuma ya tsaya ya fuskanci Bizaya da kakkausar murya. "Tace bata so dole ne? Ko basa koya tarbiyya a ƙarƙashin ƙasa?"
Nan take wajen ya ɗau haske a yayinda walƙiya ta fara tashi daga jikin Deniz Bizaya. Shima Armad haka amma bai juyarda dukkan jikinsa izuwa walƙiya ba dan ɓadda kama.
Tsahon lokaci haka suka tsaya suna kallon kallo tsakaninsu su biyu kafin daga bisani Deniz Bizaya yayi wata dariya ta mugunta ya ce, "wato Nostaljiya wannan baƙin kika zaɓa akan ni ɗan uwanki? Lallai kinyi kuskure mabayyani, kuma da sannu zan hana faruwar wannan haɗinkai tsakanin daulolinmu. Zaki gane kuskurenki sannu a hankali, har sai kinzo kin durƙusa kina nema na aureki koda a matsayin kwarkwara ne."
Yana magana ya juya yabar wajen, Armad ya bishi cikin fushi zai aikata shi amma Nostaljiya ta riƙe tana girgiza kai.
**
Bayan Armad ya raka Nostaljiya sashinta acikin fadar saiya wuce ɓangarensa. Ba jimawa bacci ya ɗauke shi wanda bai farka ba sai washe gari. Yana farkawa ya tadda mutanensa a kewaye dashi akan gado.
Iliyasisi ne ya fara jawabi. "Tattaunawa tsakanin sarki Bihanzin Sisiyu da sarki Deniz Iluru ta tashi baran-baran. Ance ana cikin tattaunawar ɗansa Deniz Bizaya ya shiga ya tada rigima. A halin yanzu dai kai sani muna gabda faɗawa yaƙi. Ragowar sarakunan Jinzidal huɗu sunce sai Bihanzin ya miƙa musu ƴarsa Zahra indai yana so su lafa masa idan ba haka ba kuwa zasu shiryo ɗamarar yaƙi suzo su kwace ta ta ƙarfin tsiya. Tuni suka yanke mata hukuncin kisa da horo mai tsanani."
Cokali ya ɗora da cewa, "kuma Denizawa sun tafi da dukkan dinaren da suka kawo a matsayin na gani ina so. A halin yanzu wannan daula ta Sisiya basu da abokai kuma suna tsaka da fuskantar barazanar yaƙi."
Armad ya gyaɗa kai tare da jan dogon numfashi, dama dai tuni ya riga yasan haka zata faru. "Ina ganin kubar wannan daula tun kafin yaƙi ya ritsa daku. Sunan Nusi da muka gani acan ko ita ce ko ba ita bace ya zamar mana wajibi mu binciki wannan sashi na Ikwatora domin tabbatarwa. Amma a halin yanzu bani da damar tafiya na bar daular Sisiya a haka bayan na jawo musu wannan abu. Duk wanda acikinku yayi niyyar tafiya bazan zargeshi ba ko kaɗan domin kuwa wannan yaƙi nawa ne nini kaɗai."
Armad na gama bayani ya basu lokaci suyi shawara, sannan ya tashi yai wanka, yaci abinci kafin daga bisani ya nufi cikin fada wajen Nostaljiya. Shi kam tuni ya gama yanke shawarar abinda zai aikata.
Sannu a hankali Armad ya isa cikin gidan Nostaljiya. Amma bisa mamaki babu kowa a gidan, hatta ɓangaren su yarima Kiru da yarima Hasanu babu kowa. Har Armad ya juya sai wani mai gadi ya hangoshi yai sauri ya iso gareshi ya bashi wata takarda. Armad ya buɗe takardar saiga rubutun Nostaljiya aciki.
*Kazo fada sarki yana son ganinmu!*
Armad na ganin haka yai azama ya nufi cikin fada. Lokaci-lokaci ya kirawo ɗalasimin Kaban'shìsu domin ya ƙara sauri, saboda haka kan kace meye wannan ya iso cikin fadar.
Yana zuwa ya tararda fada ta cika maƙil ana zaman fada. Karagar sarki Bihanzin na can gaba daga ɓangaren yamma, inda yake zaune cikin ƙasaita yana gudanar da al'amuran mulki.
Tsaye a gabansa dogon layi ne ta ɓangaren dama da hagu. A ɓangaren dama sarakunan dake ƙarƙashinsa ne guda talatin da ɗaya, da kuma sarkin yaƙi kwamanda Damjinu. Kowannensu yasha ɗamarar yaƙi. Kana gani kasan tuni an buga gangar yaƙi.
A ɗaya ɓangaren hagun kuwa ƴaƴan sarki ne guda uku suma tsaye kansu a sunkuye. Armad na shigowa ya rasa inda zai tsaya domin shidai ba sarki ba, kuma ba ɗan sarki ba. Sannan kuma ga dukkan alamu waɗannan rukuni guda biyu ake gayyata wannan taro.
Amma yana cikin dubi-dubi yaji muryar sarki Bihanzin a kunnensa. "Duk wanda ya auri ƴar sarki ai shima ya zama ɗan sarki, saboda haka kazo ka tsaya anan." Ya nuna masa ɓangaren hagu.
Armad ya ɗanyi jim kafin ya taka ya nufi ɓangarensu Nostaljiya. Dama dai Hasanu shi ne a farko saboda shi ne babba. Sai Kiru sannan kuma Nostaljiya. Saboda haka Armad ya tsaya a gefen Nostaljiya.
Fada tayi tsit babu wanda yake cewa komai, sai can daga bisani Bihanzin ya fara da cewa, "kamar yadda kowa ya sani ƴa ta Nostaljiya ta zaɓi Armad a matsayin wanda zata aura. Shin akwai mai jayayya, ko kuma wanda yake gani wannan abu bai kamata ba?"
Waje yai tsit babu mai cewa uffan kowa ya sunkuyar da kansa. Bayan tsahon lokaci Bihanzin yai gyaran murya yaci gaba da bayani. "To idan babu wani mai inkari nasa ranar wannan ɗaurin aure nanda kwana bakwai. Kowa acikinku yaje ya shiryawa gimbiya kyauta ta musammna kuma za'a fara shagalin bikin daga ranar ɗaurin auren harya zuwa kwana bakwai baya. Ban ɗaukewa kowa ba, ayi aike zuwa kowanne gari da ƙauye. Zuwa kowacce doron ƙasa."
Bihanzin na gama wannan jawabi ya miƙe ya fice daga fadar ba tare da yin zancen yaƙin dake gabato su ba. Tamkar bayajin tsoron duk wani abu dazai faru.
Armad ya kalli Nostaljiya, ita kuma ta sunkuyar dakai cikin kunya tana murmushi. Nan take Hasanu da Kiru suka miƙowa Armad hannu suka gaisa suna tayashi murna. Sannan sauran sarakunan dake wajen suma suka biyo layi.
A wannan rana saida Armad ya gaisa da dukkan sarakunan daular Sisiya.
Saura kwana bakwai biki! Ko za'ai wannan taro lafiya?
***
Babi na 121: BAƘAR-WUTA
Acan wani sihirtaccen ɗakin taro dake kan wani tsibiri, wasu mutane ne guda biyar ke taro domin tattauna makomar shugabanci a bisa doron ƙasashen-ƙasa guda shida.
Ɗaya daga cikin wannan mutane yana da baƙaƙen idanuwa irin na Ururu. Ragowar huɗun kuma suna sanye da kaya na sarakuna daban-daban. Kowannensu akan kujera ta alfarma. Ɗakin a rufe ruf yake babu wata hanyar haske sai wata ƙatular aci bal-bal dake ajiye a ƙuryar kudu. Hakan yasa ba'a ganin siffofin wannan mutane sosai amma duk da haka kayan jikinsu a bayyane suke.
Mutun na farko yana sanye da alkyabba ruwan ƙasa wanda hasken aci bal-bal dake ɗakin ya mai dashi ja. Yana zaune kansa yana fuskantar kewayeyyen teburin dake tsakiyar ɗakin. Wannan mutun ba wani bane illa sarkin Jinzidal Maikiro'Abbas na daular Maikironomada.
Mutun na biyu sanye yake da riga mai kama da ƴar shara sai dai daga gefenta anyi mata ado da bezar gashi launin baƙi. Wannan mutun shi ne sarkin Jinzidal Han'Ibal na daular Hán ta doron ƙasa ta uku wato asalin inda Armad ya futo kenan.
Mutun na uku sanye yake da doguwar riga har ƙasa, wacca take a ɗinke babu ko aljihu. A jikin rigar akwai alamun hadari wanda akaiwa fenti da launin ja da baƙi. Shi ne Sarki Rafiya na daular Infiriya daga doron ƙasa ta huɗu sashin arewa.
Mutun na huɗu shi ne sarki Deniz Iluru, sanye yake da yadi tafkeke wanda ya naɗe jikinsa dashi kamar harami. Deniz Iluru dai yafi kowa girma a wajen tunda daman jikinsa irin na samudawa ne. Kuma shi ne ya ke fuskantar ma'aboci Ururun dake zaune a gefen kujera. Wannan ma'aboci Ururu ba wani bane illa Uznu Ururu, ɗaya daga cikin kwamandoji biyar na Ururu dake mulki a ƙasashen ƙasa.
Maikiro'Abbas shi ne ya fara yin magana cikin kakkausan harshe. "Ko meye ya kawo Ururu wannan tattaunawa da bata shafesu ba. A iya sani na wannan abu ne daya shafi sarakunan Jinzidal kaɗai."
Uznu ya ɗanyi murmushi tare da girgiza kai. "Idan bakwa son na shiga wannan yaƙi shikenan, amma kuyi sani wannan yaro da ake cewa Armad ya aikata min babbar taɓargaza a gari na, kuma bisa kundin doka ko'a ina yake zan iya hukunta shi. Saboda haka ko ku yadda na shiga wannan yaƙi ko ba ku yadda ba rai da rayuwar wannan yaro na hannuna, kuma ko'a filin daga muka gamu dashi zan ɗauki fansa ta."
Sarakunan najin haka suka fara muzurai suna kallon juna. Tun farko dai babu wanda ya gayyaci Uznu wannan taro kuma babu wanda yasan yadda akai Uznu yasan za'ai wannan taro har yazo. Abu ne sananne cewa ba'a ga micizi tsakanin kwamandojin Ururu na ƙasashen ƙasa da kuma sarakunan Jinzidal saboda kowa ƙoƙari yake ya ƙara ƙarfi. Saboda haka wannan yaƙi tsakanin sarakunan Jinzidal kamar wata dama ce da Ururu suka samu da zasu ƙara ƙarfinsu.
Sarki Maikiro'Abbas ya ci gaba da cewa, "wannan yaro bai dame mu ba, idan zaka yanka shi ka dafa ko ka soya duk kai ta shafa. Amma dai babu ruwanka cikin yaƙin sarakunan Jinzidal. Ina ganin mun sallame ka daga wannan taro."
Sauran sarakan dake wajen suka gyaɗa kai alamun amincewa. Lallai duk da rigimar dake tsakaninsu baza su so Ururu su shiga tsakaninsu ba. Saboda haka suka amince da wannan mataki.
Uznu yayi murmushi naɗan lokaci yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya kafin daga bisani yayi tsaki ya miƙe. "Ni dai na faɗa muku. Indai nayi arba da wannan yaro ko'a filin daga ko'a gida ko'a daji to nawa ne."
Uznu ya fice daga wannan taro cikin fishi.
Kamar sarki Maikiro'Abbas zaiyi murna da wannan al'amari amma kawai saiya ɓata rai ya juyo izuwa sarki Deniz Iluru. "Kai kuma Deniz, kana tunanin duk cikinmu babu wanda yasan abubuwan da suka faru tsakanin sarki Eyriyon da ƙabilarka? Kayi sani cewa ni Maikiro'Abbas ina sane da tarihin duniya, kuma babu abinda yake ɓoyuwa a gareni. Idan ka koma gida ka gayawa Deniz Ururu ni nafi ƙarfin ya turomin wakili na tattauna dashi. Idan yana so mu gana yazo da kansa."
Maikiro'Abbas yana gama jawabi ya miƙe ya nufi ƙofa. Ragowar sarakunan suka bishi da kallo. Dama dai an san Maikiro'Abbas da zafin zuciya amma abin nasa kullum gaba yake yi.
Yana fita ya banke ƙofar. Sarki Rafiya ya kalli ragowar sarakunan biyu dake cikin wajen ya numfasa ya ce, "dama munyi tunanin haka, saboda koba komai Maikiro'Abbas baya son fafatawa da Bihanzin. Wataƙila abinda abinda tarihi yazo dashi gaskiya ne, tsoronsa suke ji. Amma mudai da muke nan mun riga mun yanke shawara sai munga bayan Bihanzin, dama can shi kaɗai ne wanda yake hana mu rawar gaban hantsi. Wannan abu da ƴarsa ta aikata kawai dama ce muka samu wadda muka daɗe muna neman. Kamar mai neman kuka da aka jefa da kashin awaki. Komin ƙarfin takobin Bihanzin ya zaiyi da ƙarfin rundunar sarakuna uku na Jinzidal."
Sarki Deniz da sarki Han'Ibal suka gyaɗa kai alamun amincewa. Tun kwanaki bakwai da suka gabata suka gama fitarda taswirar yaƙi da yadda zasu ɓullowa daula Sisiya su ruguza ta har ƙas. Sarki Han'Ibal ya shimfiɗa ƙatuwar takardar dake hannunsa wadda ke ɗauke da jadawalin yaƙin.
Ya dube su sannan yayi nuni da wasu manyan tubala biyu a jikin taswirar yana cewa, "wannan sune wajaje biyu da zamu shiga daular Sisiya. Zamu yaƙe su ta dama da hauni tayadda zamu raba musu hankali su rasa ina zasu tare. Sannan kuma zamu tanadi manyan mayaƙa wanda suka fi kowa ƙarfi kamar guda goma wanda zasu shiga ƙasar a asirce domin su cimma ƴar tasa Zahra. Amma kafin a fara komai ya zama wajibi mu tura ƴan leƙen asiri su gano mana halin da ake ciki a garin. Da yawan mayaƙan su da sirrikansu da kuma shirye-shiryensu."
Sarki Deniz yayi gyaran murya tare da cewa, "Han'Ibal, wannan bayani naka ya bada ma'ana to amma runduna biyu kenan kake zance, mu kuma nan muna da runduna uku, ina ɗaya rundunar zata yi?"
Hán'Ibal yayi murmushi tare da cewa, "eh.. kayi gaskiya. Wannan tsari da rundunarka data Rafiya sune zasu ƙaddamar dashi. Ni kuma zan ɗebi runduna ta nayi gabas."
Deniz ya haɗe rai. "Gasas kuma?"
A wannan lokaci sarki Rafiya shi ne ya bashi amsa cikin nutsuwa. "Eh, gabas. Wataƙila ka taɓa jin labarin wadda ake kira da BAƘAR-WUTA?"
Sarki Deniz ya gyaɗa kai cikin tunani. "Baƙar-wuta? Ba ita ce Hidaya Wilbafos ba? Menene haɗinta da wannan yaƙin?"
Sarki Rafiya ya gyaɗa kai. "Eh, ita ce. Kasan a doron ƙasa ta uku aka haifeta, kuma sarki Han'ibal yayi bincike ya gano ita ce yayar wannan saurayi mai suna Armad wanda shi ne maƙasudin haddasa wannan yaƙi. Sanin halin zuri'ar gidan Wilbafos yasa munsan cewa lallai baza ta zauna mu hallaka ƙaninta tana gani ba. Saboda haka dole mu tanadeta, idan ba haka ba kuwa ita kaɗai zata iya jawo matsala acikin wannan yaƙi. Saboda haka sarki Hanibal yayi bincike ya gano inda take, kuma dashi da manyan sadaukansa zasu tare ta daga can su hana ta isa wajen yaƙin. A yayinda mu kuma zamu turmuza kan Bihanzin da mabiyansa."
Sarki Deniz ya gyaɗa kai cikin amincewa, yasan cewa lallai wannan shiri yayi. "To amma yaushe za'a fara wannan yaƙi?"
Sarki Rafiya ya amsa da cewa, "Sarki Han'Ibal shizai fara fita neman Baƙar-wuta, a yayinda runduna ta da taka zamu aiwatarda duk wasu shirye-shirye mu zamo cikin shiri har sai sanda Han'Ibal ya tabbatar mana ya cimma Baƙar-wuta. A sannan zamu fara aiki."
Sarki Deniz ya ƙara gyaɗa kai. "To amma naji cewa akwai tsohuwar gaba tsakanin Han'Ibal da Baƙar-wuta, ina tsoron kada ya manta da cewa aikinsa kawai ya tare ta bawai ya tsaya wani abu ba..."
Nan take sarki Han'Ibal ya fara huci. "Deniz, ba ruwanka da alaƙa ta da ita. Kai dai kawai kayi naka aikin."
***
Babi na 122: Ranaku Huɗu
Nostaljiya na zaune kan kujerar girma a fadar sarki Bihanzin. A gefenta Armad ne zaune, dukkansu sun sha kayan sarauta jajaye wanda akaiwa ado da alharini tun daga sama har ƙasa. Babu kowa sai kuyangi kyawawa dake ta hidima.
Bayan ɗan lokaci sai mai tsaron ƙofar ya bada sanarwa. "Sarakuna sun jeru a layi suna neman iso su shigo."
Nostaljiya ta kalli Armad alamun neman izininsa. Armad ya bada umarni. "Na farko ya shigo."
Nan take aka buɗe ƙofa sarki na farko akan layi ya shigo. A hannunsa riƙe yake da wata ƴar jaka fara. Ya taka har saida yakai kimanin taku takwas kusada Nostaljiya sannan ya tsaya ya ajiye jakar dake hannunsa. Wani ƙaton farin dutse mulmulalle ya bayyana aciki. Sarkin ya ɗakko dutsen dakyar yana cewa, "Ni sarki Fatahu Sisiyu na bawa gimbiya kyautar wannan dutse wanda aka gada a dangi na sama da shekaru dubu da hamsin da suka wuce. Ni kaina bansan iyakacin amfanin wannan dutse ba amma a littafin da kakana ya bari ya ce ana iya amfani da wannan dutse wannan haɗa fasahar Kwangila tsakanin mutun da aljan. Na baki wannan dutse a matsayin kyauta."
Nan take kuyangi suka ƙaraso suka zo suka ɗauke kyautar sukai gefe da ita. Sarki Fatahu yayi godiya sannan ya fice aka kirawo sarki na gaba.
"Ni ne sarki Ɗamaru Sisiyu daga garin Kalmir. Na bawa gimbiya Ayrid miliyan goma da dinare dubu ɗari."
"Ni sarki Na'isu na garin Bawa na bawa gimbiya sulken Ƙaruna!"
"Ni sarki Shiftu na garin Dalru na bawa gimbiya kyautar ingarman dawakai dubu goma da sulken yaƙi dubu goma."
Haka dai aka wuni a wannan rana ana ta layi ana shigo da kyaututtuka. Tun Armad yana mamakin yawan kayan har ya daina. Kan kace meye wannan fada ta cika maƙil da kaya. A wannan rana Armad da Nostaljiya basu bar fada ba sai yamma liƙis.
Suna tafiya akan farfajiyar fada Armad zai raka Nostaljiya sashinta suna hira irin ta masoya.
"Mai yasa naga kamar baka farin ciki?"
Armad yai sauri ya fito daga kogin tunanin daya faɗa ya ce, "a'a haba, ni kuwa nake farin ciki. Kawai dai..."
Nostaljiya ta juyo ta kalleshi da sauri. "Kawai dai me?"
"Kawai dai.. kinsan saboda wannan auren yaƙi yake neman ɓarkewa, kinga kuwa dole nayi tunani. Kina ganin akwai wata hanya da za'a iya yin wannan aure kuma a lokaci guda a kare asarar rayuka da wannan yaƙi zai jawo?"
Nostaljiya tayi murmushi tare da girgiza kai. "Na daɗe dayin wannan tunani, ni da kaina na samu mahaifina akan hakan. Kasan mai ya cemin?"
Armad ya girgiza kai.
Nostaljiya ta amsa da cewa. "Akwai tsohuwar gaba tsakanin mahaifina da sarki Rafiya. Sannan shi kuma sarki Hán'Ibal ya daɗe yana so ya mallaki fasahar Dauwamammen-Sara daga mahaifina. Su biyun nan koda babu wannan aure sun daɗe neman hanyar da zasu afka mana da yaƙi. Saboda haka mahaifina ya gayamin mu kalli wannan yaƙi a matsayin wata dambarwa da za'a gwada kwanji tsakanin sarakunan Jinzidal. Mahaifina yana so ya nuna musu cewa yana nan da ƙarfinsa kamar kullum. Wannan shi ne dalilin da yasa kaga cewa mahaifina yaƙi yadda a ɗaga wannan aure domin ya nunawa abokan gaba sa idonsu babu abinda zai hana. Idan sun isa suzo su hana. Kaga kenan hanya ɗaya da za mu taimaka shi ne muga anyi wannan biki lafiya an gama lafiya. Sannan kuma idan yaƙi ya zo mu tsaya mu kare daular mu da sarkin mu da mutanenmu."
Armad yaja dogon numfashi yana nazarin wannan magana data gaya masa. Lallai babu shakka abubuwan haka suke, wannan yaƙi ne kawai da za'ai na fidda gwani tsakanin sarakunan Jinzidal. Amma duk da haka dole ne Armad ya tabbatar nasara ta faɗo gare su koba komai wannan zai zamo wani ɗan'ba a shirinsa na tarwatsa ita kanta Jinzidal ɗin.
Sannu a hankali sukai shiru naɗan lokaci kafin su ƙarasa ƙofar gidan Nostaljiya. Armad ya buɗe mata ƙofa a irin zubi na sarauniyoyi sannan ya bata hanya ta wuce kafin yabi bayanta.
"Wai kika ce daga RANAR-KYAUTA sai RANAR-KEWAYE ko?"
Nostaljiya ta ɗan haɗe rai cikin shagaɓa ta ce, "wai dan ALLAH sau nawa zan gaya maka tsarin al'adar biki a garin nan? Yau fa ita ce Ranar-kyauta, ranar da kowanne sarki zai bamu kyautarsa. Sannan abinda zai biyo baya shi ne ɗaurin aure a RANAR-AURE. Washe-garin Ranar-aure ita ce Ranar-kewaye. Ranar da ango zai ɗauki amaryarsa a baya ko'a wuya ya kewaya gari da ita jama'ar gari su saka musu albarka. Daga nan sai RANAR-TARIYA, amma tunda kaga ban cika shekara sha takwas ba babu tariya. Ka riƙe wannan ranaku guda huɗu dan bazan ƙara maimaita maka ba. Ranar-kyauta. Ranar-aure. Ranar-Kewaye. Ranar-tariya."
Armad yaja dogon numfashi cikin murmushi ya ce, "ai bazan ƙara mantawa ba."
Suna shiga gidan Armad ya kara buɗe mata ƙofar farfajiyar tsakar gidan kafin daga baya ya jada baya ya tsaya. Nostaljiya ta kalleshi kallo mai cike da tambaya. Inda ya bata amsa da cewa, "ina da uzuri.. amma zan dawo da daddare."
Tun ma kafin ta bashi amsa Armad ya fice da gudu yana dariya.
Nostaljiya kawai kallonsa tayi tana murmushi. Tuni tasan inda zashi. Sama da kwanaki huɗu kenan yana irin haka inda daga baya ta bincika ta gano duk sanda yabar wajenta wajen horo yake tafiya.
***
Armad na futowa ya nufi ɗakinsa kai tsaye. Babu lokacin ɓatawa saboda haka yayi amfani da ɗalasimin Kaban'shìsu. Yana bayyana a ɗaki ya nufi kan wasu manya-manyan littattafai wanda bai daɗe da arosu daga ɗakin-karatu ba. Wannan littafai dai Armad yana amfani dasu ne wajen gano yadda zai iya amfani da fasahar Kwangila. Tunda dai wannan fasaha ba'a taɓa samun mutun ya aiwatar da ita ba, a har kullum aljani shi ne wanda yake bada Kwangila ga ubangidansa. Amma Armad bashi da aljani tun bayan da Uznu Ururu ya kashe nasa, amma saboda fasaharsa ta sarki Eyriyon, Itacen-aljanu ya nuna masa zai iya ɗaukar siffar aljanu ya aiwatarda wannna fasaha.
Ta wannan fasaha Armad zai haɗa rundunarsa tasa ta kansa. To amma akwai jan aiki a gabansa domin duk yawan littattafan nan babu wanda yayi magana akan abinda yake so.
***
Babi na 123&124: Kwangilar Armad
WATA BIYU BAYAN RANAR KYAUTA
Nostaljiya ce tafe cikin ƙasaitaccen keken doki ana tuƙata. Abin mamaki wannan keken doki wajen gari yayi. A kewaye dashi akwai bayi sama da dubu suna bashi tsaro. Sannan ga kuyangi guda bakwai zaune a baya suna kula da lafiyar gimbiya.
Suna tafe a hankali har suka iso cikin wasu duwatsu, inda Nostaljiya ta tako ta fito daga cikin keken. Wannan kuyangi suka kewayeta tare da shimfiɗa shimfiɗu na alfarma domin ta taka. Su kuma ragowar kuyangin suka bi bayanta, suma bayin suka rankaya suka bi bayansu.
Acikin wannan duwatsu akwai wani kogo wanda ba'a ganin komai acikinsa sai duhu. A tsakiyar wannan kogo akwai wani jarumi zaune yana jan ɗalasimai zaune a gaban wani farin dutse mulmulalle.
Lokaci-lokaci walƙiya na tashi daga jikin wannan saurayi tana haska farar rigar dake jikinsa.
Abin mamaki Nostaljiya wajen wannan kogo ta taho gadan-gadan. Tana isowa tararda Inára a ƙofar kogon a tsaye yana gadi. Batai masa magana ba, kawai tasa aka kafa tanti a gaban wannan kogo ta zauna sannan aka fara addu'o'i.
Wannan saurayi idonsa na rufe amma duk da haka yanajin yanayin-izzar su Nostaljiya a wajen wannan kogo. Kaɗan yaɗan buɗe idonsa tare da yin ɗan ƙaramin murmushi kafin daga bisani ya ƙara rufe idon ya koma cikin halwarsa irinta ma'abota izza.
***
Bayan sati ɗaya
***
Nostaljiya na zaune a gaban wannan kogo idonta na kafe a bakin wannan kogo. Bayi na hidima.
Yau wata biyu da sati ɗaya kenan babu wani abinci daya shiga cikin wannan kogo, sannan kuma wannan saurayi bai fito ba, ballantana ya shiga da wani abu.
***
Bayan sati ɗaya
***
Wani mako ya ƙara wucewa wannan saurayi bai fito ba amma Nostaljiya bata bar bakin wannan kogo ba.
A wannan rana wani abin mamaki ya faru. Kimanin ƙarfe sha biyu na rana sai rana ta fara zazzaɓi. Kan kace meye wannan rana ta shige cikin gajimare ta ɓace. Gari yai duhu dunɗum. Wannan duhu ba wannan daji kaɗai ya shafa ba, dukkan duniya ko'ina haka abin yake.
Bayi sun fara hayaniya suna tunanin ko hari aka kawo musu, amma Nostaljiya ta daka musu tsawa kowa ya nutsu.
Ana haka kwatsam rana ta fara ɗagowa amma ta yamma. Wannan sabuwar rana data fito launin ta ja ne jajawur saɓanin launin fari da aka saba gani.
Nan take duniya ta ruɗe domin kuwa wannan kalar rana ba baƙuwa bace. Kowa ya san mai take nufi. Zarar aka ga jar rana ta fito ta yamma to alamu ne na wani bajimin ma'aboci izza ya samarda fasaha mafi girma a duniya wato fasahar KWANGILA.
Sannu a hankali wannan rana taci gaba da tasowa har saida tazo tsakiyar sama. Sannan ta saito saitin wannan kogo da wannan jarumi ke ciki.
A haka ta tsaya tsahon ƴan sa'o'i kafin daga bisani ta ɗauke gari ya ƙara yin duhu. Duniya tayi dunɗum.
Acikin wannan duhu, acan wani sashin duniya dake kusa da tsibirin SIDO-URURU wasu mutun uku ne ke tafe sun nufi wannan tsibiri. Idan ka lura zaka ga cewa ɗaya daga cikinsu Ikenga O Bayajidda ne, ɗaya kuma ba wani bane illa babban hadiminsa Kána. Na ƙarshe shi ne sabon hadiminsa daya samo a duniyar ƙarƙashin ƙasa. Suna tafe suna tattauna al'amuran izza da kuma abinda zasu aikata a wannan tsibiri wanda ƴaƴan Ururu ne kaɗai ke shiga.
Kána ya ɗaga kai sama ya kalli abinda ke faruwa kafin ya dubi Ikenga ya ce, "Jar-rana? Naji ance tana nuni da bayyanar fasahar Kwangila. Haka ne?"
Ikenga najin haka ya fashe da dariya har saida takobinsa ta YURA-SHÍRA wadda ya karɓa a wajen Bihanzin ta ɗaga sama. "Kaima Kána kana da ban dariya. Fasahar Kwangila? Haka dai mutane gama-gari suke cewa. Amma wannan kwata-kwata ba fasahar Kwangila yake nunawa ba. Bari kawai, da sannu zan baka bayanin mutun na farko daya fara amfani da wannan rana."
Kána yai murmushi ya ce, "ya shugaba na ka taɓa gayamin labarinsa ai. Ba shi ne sarki Eyriyon ba?"
Ikenga ya ɗanyi jim kafin daga bisani ya ce, "Eh hakane. Amma kasan cewa wannan jar-rana da kake gani ba wata aba bace illa idanunsa na hagu. Bari dai kawai, da sannu zan baka labarin yadda Eyriyon ya cire idonsa na hagu ya haɗa shi da ruhin littafin-takobi. Bari mu shiga wannan tsibiri mu kashe Ururu sannan mu samu ganima. Idan munyi sa'a mu samu ruhin magajin wilbafos wanda ke yawo akan wannan tsibiri a halin yanzu."
***
Akan tsibirin Sido-Ururu kuwa yara ne ke zaune suna koyar al'amuran Ururu. Ana cikin haka gari yai duhu. Nan take aka fara addu'o'i ana neman tsarin daga zuri'ar maƙiya. Limamin dake koyarda wannan yara ya fara raba addu'a.
"Maƙiya Ururu, Maƙiya zaman lafiya, masu idon rana da wata, muna neman tsarin Ashura daga gareku."
Nan take suma yaran suka amsa cike da ƙuwwa.
Ruhin Armad na zaune kusa da Suwainah Ururu. Babu wanda ke ganinsa sai ita. Yana ɗaga ido yana kallon wannan jar-rana yayi murmushi. Yasan lallai lokacin dazai haɗu da ubangidansa yana gab da isowa.
***
Acan doron ƙasa ta huɗu acikin wannan daji, a bakin wannan kogo, saurayin dake cikin kogon ne ya fito. Kallo ɗaya rak zakai masa kasan shi ne Armad Wilbafos. Sai dai abin mamaki maimakon ruwan ƙasa, idonsa na hagu ya juye izuwa siffar rana launin ja. Koda ya bayyana sai dukkan mutanen dake wajen suka ƙura masa ido suna kallon wannan ido.
Nostaljiƴa tayi sauri ta ƙarasa kusa dashi ta rufe masa fuska da mayafinta. Sannan suka shiga cikin keken dokin suka rankaya izuwa garin Jekis na daular Sisiya.
Akan hanyarsu Armad yayi magana a lokaci na farko tun bayanda ya shiga halwa wata biyu da suka gabata. "Mata ta."
Nostaljiya ta ɗanyi murmushi tana cewa, "an ɗaura ne?"
Armad ya fashe da murmushi. "Ai wani satin ne. Idan kika rufe ido tsahon lokaci sai dai kawai kiji an ɗaura baki sani ba."
Haka dai suka ci gaba da zancensu na soyayya har tsahon sa'a ɗaya kafin Nostaljiya ta sako zancen halwar da Armad ya shiga.
"Arbil, da fatan ka samu abinda ka shiga nema?"
Armad najin haka ya fara murmushi mai sanyi irin wanda ya daɗe baiyi ba. Bawai tambayar bace ta sashi wannan murmushi ba, a'a sunan da Nostaljiya ta gaya masa. Kalmar 'ARBIL' dai daga yaren Aldurish take, kuma tana nufi 'miji'. Duk irin ƙaunar da Nostaljiya take nuna masa wannan ne karo na farko data taɓa kiransa da wannan suna.
"Kaga ban naso ka ringa yimin irin wannan kallo sai naji.."
Armad ya ɗora hannunsa na dama akan idonsa na hagu lamarinda yasa idon ya koma dai-dai sannan ya matsa kusa da fuskarta yana dariya. "Sai kiji me?? Faɗi!"
"Shikenan.. Nina fasa faɗa."
"Ai kuwa zanyi wani abu yanzun nan indai baki faɗa ba. Zan irga uku."
Nostaljiya ta zare ido cikin kunya tana murmushi. "A'a to zan faɗa karkai komai. Amma saika gayamin maiya faru acikin kogon dakai wata biyu."
Armad ya ɗora hannu a fuska irin yana dogon tunanin nan kafin daga bisani ya ce, "Ehh.. to, na yadda. Zan gaya miki mai ya faru.
Armad yai tagumi sannan cikin kalar tausayi ya ce, "Ban samo komai ba!"
Nostaljiya najin haka ta fara ƙifta ido cikin ruɗani kafin daga bisani ta ce, "kaga banason irin haka, ka gayamin gaskiya." Abin mamaki sai kawai hawaye suka fara zuba daga idonta ba tare ta sani ba.
Armad na ganin haka ya rikice ya fara bayani ba tare da ya sani ba. "Na ƙaddamar da fasahar Kwangila kuma na zaɓi ruhinki a matsayin wakili na."
Kafin tace wani abu Armad yasa hannunsa a goshinta, wani haske ya fito daga cikin idonsa na hagu ya shige idonta na hagu. Nan take Nostaljiya taji wani sanyi kamar ansa idon acikin ƙanƙara. Sai kuma idon ya fara haske irin na Armad. Bayan ɗan lokaci ya dawo dai-dai. Haka na faruwa wani sabon ilmi ya bayyana a kwakwalwar Nostaljiya. Ilmin sarrafa fasahar walƙiya babban mataki na shida.
"Kiyi haƙuri ban nemi shawararki ba. Amma an bani zaɓi na zaɓi mutun ɗaya wanda zai iya yin amfani da fasahar Kwangila ta kuma na riga na zaɓe ki."
Nostaljiya tayi jim ta shiga dogon tunani. Ruhin Armad yana da banbanci dana sauran mutane. Tunda fasahar Kwangila ana yinta ne tsakanin mutun da aljan kuma da mutun ɗin da aljanin duk zasu iya raba walƙiyar tsakanin aljanu da bil-adama. To kaga idan Armad ya zama a matsayin aljani ba abin mamaki bane idan ya zaɓi mutun ɗaya wanda shima zai iya yin amfani da fasahar kwangilarsa.
"Ina fata zan zamo wadda zakai alfahari da ita."
Tunda Nostaljiya ta faɗi wannan magana ta ɓoye fuskarta a ƙasa tana tunani bata ce komai ba har suka iso fada. Tun Armad yana tsokanarta harya gaji bacci ya kwashe shi.
Bayan sun iso fada su Cokali da Iliyasis ne suka fara tararsu. Amma saboda Armad na bacci sai Inara ne ya kwashe duk abinda ya faru ya gaya musu a yayinda aka wuce da Armad gidan Nostaljiya.
Da kyar Armad ya tashi yaci abinci yai wanka sannan ya koma bacci. Yana komawa Nostaljiya ta fice ta nufo sashin da su Inára suke.
Tana shigowa suka miƙe cikin girmamawa. Amma ta ɗaga musu hannu su zauna. Sannan ta fara bayani da cewa, "Nasan kun riga kunsan aƙidar Armad ta kawarda cinikin bayi a doron ƙasa kuma a matsayinku na abokansa ina fatan kuna tare dashi."
Dukkaninsu suka gƴaɗa kai. A zahiri dukkansu basa ra'ayin cinikin bayin kawai dai dan babu yadda zasu yi ne.
"Ina so mu haɗa masa runduna ta mutun ɗari wanda suke da irin ra'ayinsa. Wanda zasu karɓeshi a matsayin shugaba kuma zasu iya mutuwa akansa. Nasan mutun bakwai masu irin wannan aƙida dake cikin wannan gari amma ragowar sai dai ku nemo su."
***
Acan daular ƙarƙashin ƙasa ta sarki Deniz Iluru wani babban taro aka kira domin tattaunawa akan Armad Wilbafos. Abin mamaki, babu wanda yasan yadda akai wannan labari ya kai gare su cikin wannan ƙanƙanin lokaci. Amma tuni sarkin ya tara dukkan mayaƙansa da ɗansa guda ɗaya Deniz Bizaya suke tattauna yadda za'ai su hallaka Armad Wilbafos.
Babban kwamanda Deniz Kalhari ya buɗe taro da cewa, "a duk faɗin duniya mu muke bada fasahar walƙiya, lallai idan labari ya bazu a doron ƙasa wani yaro yana bada wannan fasaha kamar an watsa mana ƙasa a ido ne. Ya zama dole mu gaggauta halaka wannan yaro kafin wani yaji labari."
***
Babi na 125: Raba fasahar Kwangila
Iliyasis da Cokali da Îñara na tsaye a ƙofar wani kogo suna jira. Dukkaninsu suna riƙe da makamansu cikin shirin kota-kwana.
Sannu a hankali suka fara jin taku na fitowa daga cikin kogon. Nan take suka ƙara riƙe makamansu. Iliyasis da Inara suka zare takubbansu, Cokali kuma ya buɗe littafin Marubutan farko.
Suna cikin haka saiga wani wada mai dogon gemu ya fito ɗauke da gatari a kafaɗarsa.
Suna ganinsa sukai ajiyar zuciya sannan cikin murmushi suka mayarda makamansu. Iliyasis ne ya shige gaba ya fara magana. "Barka da izza, Duhuwa. Ni suna na Iliyasis, wannan Cokali, wannan Inara. Gimbiya Zahra ce ta turo mu."
Wannan wada najin haka ya ƙura musu yana nazarinsu. Can ya numfasa ya ce, "Idan ita ta turo ku, mai kuke da makamai?"
Iliyasis ya juya yai nuni da wasu manyan tsaunika dake can nesa ya ce, "da farko wancan tsaunikan muka je bamu gane kwatancen ba. Arnan daji sukai mana ca dakyar muka sha. Shi yasa ka ganmu acikin shiri. Amma ga wannan shedar tace indai muka nuna maka ita zaka gane." Iliyasis ya miƙawa wadan mai suna Duhuwa ƴar takarda mai ɗauke da tambari.
Yana ganin tambarin yai murmushi ya ce, "mai ke tafe daku? Gimbiya bata daɗe da yi mana aike ba.. Lokacin sake yi baiyi ba."
Iliyasis yai gyaran murya ya amsa da cewa, "Tace mu gaya maka tana nemanka."
Duhuwa ya haɗe gira cikin mamaki domin hakan bai taɓa faruwa ba. "Kun tabbata?"
Iliyasis ya gyaɗa kai. "Ga wajen da tace zaku haku."
Iliyasis ya bashi wata takardar mai ɗauke da bayanai. Sannan daga bisani suka juya suka nufi waje na gaba.
**
Yau kwanan Armad uku yana bacci tun bayan dawowarsa daga wancan daji daya ƙaddamar da fasahar Kwangilarsa. Tun dai a ranar farko Nostaljiya ta gayawa su Iliyasis yadda zasuyi su haɗawa Armad runduna tasa ta musamman wadda zasu yi amfani da fasahar Kwangilarsa. Kuma tunda ita ma kanta Nostaljiya zata iya raba wannan fasaha a maimakon Armad suna so su gama komai kafin Armad ya tashi.
Waɗannan mutane dai dasu Iliyasis suke tattarowa sune waɗanda Nostaljiya take gani sun dace su zamo rundunar Armad.
Sannu a hankali saida su Iliyaisis sukai kwana bakwai suna abu ɗaya. A duk tsahon wannan lokaci Armad bacci kawai yake. A rana ta bakwai su Iliyasis suka dawo suka zarce izuwa sashin Nostaljiya inda suka tarar da ita tana tsaye tana jiransu.
Iliyasis ya ce, "Mun samu mutun shida. Sauran, wasu bamu same suba wasu kuma sunce baza su samu damar zuwa ba."
Nostaljiya tayi jim tana saurarensu. Mutun goma ta tura su nemo amma shida sun samu. Koba komai sun haura rabi.
Yanzu abinda ya rage a kawo wannan mutun shida suyi rantsuwa zasu sadaukar da rayuwarsu ga tafiyar Armad sannan a basu Kwangila.
Haka dai shirye-shirye suka ci gaba da tafiya tsakanin Nostaljiya da su Iliyasis ba tare da Armad ya sani. Aka bawa wannan mutun shida Kwangila sannan Iliyasis ya jagoranci basu horo a ɓoye.
Yau ya rage saura kwana ɗaya kacal ranar ɗaurin auren Armad da Nostaljiya, tuni gari ya ɗauki harama ya cika da manyan baƙi daga kowacce nahiya ta daular Sisiya. Babu abinda kake ji sai kiɗe-kiɗe da raye-raye irin na zamani.
Ana cikin wannan hali amma Armad kwance yake akan gadon Nostaljiya yana sharar bacci baima san anayi ba. Duk da jikin Armad ba irin na saura bane amma yana buƙatar hutu.
Yana buɗe ido yayi arba da kyakkyawar fuskar Nostaljiya tana walwali a gabansa.
Zumbur ya miƙe yana tamabaya. "Wacce rana yau?"
Nostaljiya tayi shiru tana raba ido cikin shagwaɓa. "Yau biyu ga watan shida shekarar 1856."
"A'a.. ki bari! Ɗaya ga wata ne fa RANAR-AURE. Wai kwana na nawa ina bacci nema?"
"Da gaske nake."
Nan take Armad ya miƙe ya ɓace ya bayyana a gaban wasu kuyangi dake ƙofar gidan, kafin Nostaljiya ta fito ya tambayesu wacce rana. Inda suka bayyana masa yau talatin ga watan biyar wato ranar jajuberin ɗaurin aurensu kenan.
Armad ya ƙara ɓacewa ya dawo cikin ɗakin yana dariya yana cewa, "ai na zata na makara lokaci ya wuce."
Nan fa Armad yai wanka ya shirya sannan ya fito ƙasaitaccen falon Nostaljiya domin cin abinci.
Tuni an gama shirya komai. Inda Armad ya farma abinci kamar ba gobe. Ita kuwa kawai kallonsa take tana nishaɗi.
Bayan yaci ya ƙoshi sai suka hau hira. Armad ne ya fara magana. "Kinga naso na fara raba fasahar Kwangilarmu kafin ɗaurin aure amma bacci ya hana."
Nostaljiya dama dai tuni sukai shawara cewa baza su gayawa Armad ba, kuma baza su taso masa da duk wani abu daya shafi harkar horo ba sai bayan biki. Shima ya kamata a barshi ya huta.
Saboda haka ta kada baki tace, "ai kaima ya kamata ka huta. Kuma ka sani daga yau har zuwa nanda mako ɗaya bana son naji zancen horo ko wata fasaha. Duk lokacin ka nawa ne. Waya sani ko zamu ƙara samun lokaci irin haka a wannan rayuwar!"
Armad yai zumbur ya ce, "Mai kike nufi da baza mu ƙara samun dama irinta ba? Kamar wasu wanda zasu mutu."
Nostaljiya tayi ajiyar zuciya. Ita kanta bata san mai yasa ta faɗi haka ba. "To kayi haƙuri ba haka nake nufi ba."
"A'a nifa ba haushi naji ba. Kawai dai... Shikenan ma."
A wannan rana haka Armad da Nostaljiya suka sha hira tun daga safe har rana ta faɗi.
Dare nayi, yan'mata wanda suka kware a harkar kwalliya suka zo suka tafi da Nostaljiya gidan kwalliya. Shi kuwa Armad ya dawo ga abokansa su Iliyasis suka ci gaba da hira. Duk magana sai sun tsokani Armad akan cewa ya zama ango.
***
Babi na 126: Ranar-kewaye
Ɗaurin aure a al'adar wannan gari da miji da mata basa zuwa. Wanda suke ɗaurawa waliyan ango ne dana amarya. Sannan kuma ana yinsa ne da asuba. Gari na waye wa RANAR-KEWAYE tayi. Duk abokan ango da amarya, yan'uwa da abokan arziki sai su jeru a hanyar da ango da amarya zasu wuce domin saka musu albarka.
Haka ma abin ya faru a wannan rana. Asubar fari sarki Bihanzin wanda shi ne waliyin Armad da kuma wani dattijo wanda ya kasance kakan Nostaljiya ta wajen uwa yazo domin ya zamo mata waliyi. Sai kuma shedu wanda suka haɗa dasu Iliyasis da Cokali da Inara da kuma dukkan sarakunan daular Sisiya.
Wannan dattijo, waliyin Nostaljiya, mai suna Hilsu ya fara da cewa, "Ni waliyin amarya na bada auren ƴata Nostaljiya a bisa sadakin shekarun Izza dubu goma."
Sarki Bihanzin ya amsa cikin murmushi. "Ni Bihanzin na karɓarwa ɗana Armad auren ƴarka Nostaljiya a bisa sadaki shekarun izza dubu goma."
Bihanzin ya gabatar da aljaninsa wanda ya kawo shekarun Izza ɗai-ɗai har dubu goma ya miƙawa dattijo Hilsu. Daga nan aure ya ƙullu tsakanin gimbiya Nostaljiya da Armad Wilbafos.
Gari na wayewa jama'a suka jeru a layi tun daga fada har ya zuwa ƙarshen garin Jekis. Badan komai ba saboda yau ne Ranar-kewaye. Ranar da ango yake goya amaryarsa su zagaye gari, ƴan'uwa da abokan arziki suna saka musu albarka.
Acikin fada kuwa masu kwalliya ne suke ta fama da Armad. Sun matsa sai sun yi masa kwalliya shi kuma ya ce baya so. A taƙaice saida aka saka zaratan mata suka riƙe shi harda Nostaljiya sannan ya tsaya akai masa kwalliya irin wadda ta dace da jarumi irinsa. Ita kuwa Nostaljiya tuni komai ya gama haɗuwa.
A jikinta wata ƴar riga ce wadda idan kayi mata kallon farko sai kace fara ce, amma kana ƙara matsawa kusa sai kaga ta koma ruwa hoda. Idan rana ta haska ta saita koma ja. Idan hasken farin wata ya dira akanta saita koma shuɗi. Lallai banda kyau da ado, wannan riga ita kaɗai ce tak irin ta a duk faɗin duniya. Koda masu sarauta a doron ƙasa ta farko idan suka kalli Nostaljiya a wannan hali sai sun zub da yawu. Kowa yasan Nostaljiya takan saka rigar tsafi a jikinta domin boye hasken da ALLAH yayi mata, to amma a wannan rana babu wata riga da Nostaljiya tasa aciki domin ɓoye wannan haske. Rana ce da za'a firgita duniya da kyau.
Haske da walwali mai ƙaƴatarwa ne ke tashi tamkar ba'a duniya ake ba. Hatta Armad saida ya fara tunanin ba ita ce wadda ya sani ba domin kuwa ta canja ta zama tamkar ƴar sarkin fararen aljanun duniya. Surarta kaɗai da ɗumbun ƙasaitar kyanta yasa ilahirin garin Jekis a ranar ya ƙara kyau. Ƙanshi kuwa ba'a magana. Armad yakan ce jikin Nostaljiya a haka ma ƙanshi yake amma ayau saida aka saka turare samfuri dubu bakwai akan wannan ƙanshi.
Gashinta kuwa ta warware shi ya kwanta a gadon bayanta yana walwali tamkar walkiya na haskawa.
Lallai yau za'a shiɗe da ganin sura mafi ɗaukaka a duniya.
Armad sanye yake da riga fara mai ɗauke da adon na bezar baƙin zakin-aljanu. Armad bai canja ba sosai yana nan a yadda aka sanshi. Amma idanunsa cike suke da murna da farin ciki suna ta kallon Nostaljiya ba ƙiftawa. Wandon jikin Armad kalar rigarsa ne saidai bezar dake jikinsa tafi yawa. Sannan kuma ga hula ruwan toka akansa.
Sannu a hankali ya riƙe hannun gimbiya suka nufo bakin ƙofa kuyangi dubu suna biye dasu. Suna isa ya durƙusa ƙasa yana jiran Nostaljiya. Kamar dai yadda aka labarta a al'adar wannan ƙasa dole ango ya ɗauki amaryarsa a baya ya zagaya gari jama'a su saka albarka. Saboda haka gimbiya ma ba'a sauke mata ba.
Rigar dake jikin Nostaljiya da kaɗan ta wuce gwiwa saboda ta bata damar hawa bayan Armad cikin sauƙi. Sannan kuma ga dogon wando irin na sarauniyoyi daya rufe mata ƙafafu. Abinda kawai ya rage shi ne ta ɗare bayan Armad a fara shagalin zaga gari. Amma abin mamaki sai kunya ta cika Nostaljiya ta kasa hawa.
Shi Armad tunda ba al'adarsu bace shi ya kamata ma yafi ta jin kunya amma tuni kunyar Armad ta ƙare akan Nostaljiya. Indai har haka al'adarsu take, kuma idan ba'ai ba abin zai jawowa Nostaljiya magana tofa lallai a shirye yake.
Wasu daga cikin kuyangin dake wajen suka matsa kusa da Nostaljiya da niyyar su ɗora ta a bayan Armad amma sai suka ga ashe hawaye take. Nan take ransu yai dubu ya tashi. Hawayen da Nostaljiya take yana gabda ɓata musu kwalliyar da suka kwana suna yi. Nan take suka fara gyare-gyare da goge-goge suna roƙon Nostaljiya data bari.
Kai a taƙaice dai saida Armad ya gaji ya sure ta ya ɗora ta a bayansa sannan kafin wani ya ankara ya buɗe ƙofa ya futo waje. Hasken rana ya haske musu ido sannan ihu da shewar mutane ya biyo baya. Ba shiri Nostaljiya ta haɗiye hawayenta suka fara tafiya.
Wanda suka fara tararwa sarki Bihanzin ne da Hasanu da Kiru. Wanda kowanne acikinsu na riƙe da filawa ruwan hoda. Armad ya tsaya a gabansu ya risuna sannan suka cilla filawar dake hannunsu a gabansu Armad. Armad ya miƙa hannu ya cafe filawar ya miƙawa Nostaljiya ta riƙe. Sannan suka ci gaba da tafiya akan siririyar hanyar da mutane suka tanadar musu. Kowa da kowa burinsa ya cillo filawa Armad ya cafe amma abin yayi yawa, Armad kawai murmushi yake yana daga musu hannu cikin murna. Ita kuwa Nostaljiya ta ɓoye kanta a bayan Armad tana jin kunya. Lokaci-lokaci zaiji hawayenta na taɓa shi.
Armad na tafe a hankali ya iso wajensu Cokali. Dole ya tsaya suka cillo masa filawarsu ya cafe ya miƙawa Nostaljiya. Cokali ya dage saida ya ƙara bada wata filawar maimakon ɗaya da kowa yake bayarwa.
Sannu a hankali Armad yai awa guda yana ratsa cikin wannan gari. Jama'a babu abinda suke sai shewa da murna da kiɗe-kiɗe suna raha suna jefe filawa domin taya su Armad murna. Lallai Armad da farko yayi tunani wannan al'ada shirme ce kuma kawai yace zaiyi ne saboda Nostaljiya amma baisan sanda ya fara jin daɗin taba. Sannu a hankali dashi da Nostaljiya suka saki jiki suka fara magana da juna a gaban mutane.
Wasu suna risunawa, wasu suna durƙusawa, wasu suna kuka. Duk wanda yaga maɗaukakiyar sura da kyawu na Nostaljiya akwai abinda yake yi domin nuna miƙa wuya. Haka dai biki yaci gaba da gudana a wannan rana da ake kira da Ranar-kewaye.
***
Acan wani sashi na duniya kuwa sarki Deniz Iluru ne da muƙarrabansa suke ci gaba da tattaunawa akan yadda zasu cimma Armad. Ana cikin wannan taro sai kwatsam Uznu Ururu ya bayyana. Kallo ya koma kansa.
Komai ya kawo shi wannan taro da ba'a gayyace shi ba?
***
Babi na 127: Hajarul-Ururu
Uznu Ururu na bayyana yayi amfani da wata sihirtacciyar fasaha ya aikawa da sarki Deniz Iluru saƙo ta zuciya ta yadda su biyun ne kaɗai suka ji wannan saƙo. Abin mamaki sai sarki Deniz ya sallami dukkan jaruman dake cikin wajen, ciki kuwa hadda ɗansa Deniz Bizaya. Inda suka ƙulle ƙofa suka fara tattaunawa akan hanyar daza a ɓullowa wannan yaƙi dake gabatowa.
Bayan awa biyu da rabi Uznu ya fito daga cikin ɗakin yana murmushi. Ya dubi sarkin yaƙi Kalhari sannan ya dubi Deniz Bizaya yayi murnushi ya ɓace. Bizaya da Kalhari suka dubi juna cikin mamaki babu wanda acikinsu yasan mai aka tattauna tsakanin sarki Iluru da Uznu Ururu.
***
Acan bakin Tsibiri-SidoUruru Ikenga ne tsaye dashi da muƙarrabansa. A gefensa na dama sadauki Kána, a gefensa na hagu jarumi Daidar ne.
Ko tsoro ɗaya tak babu a tattare dasu, suna tsaye idanunsu kafe akan tsibirin kamar suna jiran wani.
Haka awanni suka ci gaba da wucewa Ikenga na tsaye yana duban wannan tsibiri daga nesa. Idan ka dubi tsiburin daga nesa zaga ga a kewaye yake da doguwar katanga wadda takai zira'i ɗari da arba'in. Kaurinta yakai zira'i goma. Sannan anyi mata fenti da launin ja. Daga cikin katangar zaka iya hangen dogayen bishiyun dabino wanda a zahiri a tsakiyar tsibirin suke ba'a jikin katangar ba.
Sannu a hankali rana ta faɗi duhu ya fara yi. Ana tafe dare yayi gari ya waye. Gabannin alfijir ya keto wani gagarumin sauti mai kama da tashin bom ya taso daga tsakiyar wannan tsibiri. Wata ƙara mai rikitarwa ta biyo baya sannan ƙura ta turnuƙe sararin samaniya.
Ba jimawa ƙara da ihun mutane ya fara tashi daga cikin tsibirin. Ƙura na lafawa saiga wannan doguwar katanga ta faɗi ƙas. Tun daga inda Ikenga ke tsaye zaka iya hangen yara da manya na gudun neman tsira.
Ana haka wata ƙarar a jere har guda bakwai ta ƙara tashi abubuwa suka ƙara rikicewa.
Ikenga, Daidar, da Kana na tsaye ko motsi basu yi ba.
Akan wannan tsibiri kuwa tuni wanda ke kula da yaran ya buɗe ƙofar Eycigan yana bawa yaran daman tserewa zuwa doron ƙasa na farko kafin a gano maike faruwa.
Ruhin Armad na maƙale a jikin Suwainah suka danna cikin wannan ƙofa tare da sauran yara masu koyon al'amuran Ururu.
Suna shiga ƙofar ruhin Armad yaji hajijiya ta ɗauke mai ƙunshe da amai. Ba jimawa suka bayyana akan wani ƙatoton dutse. Da dama daga cikin yaran faɗuwa ƙasa sukai suna amai saboda ƙarfin hajijiyar wannan ƙofa. Ga dukkan alamu an ƙarawa wannan ƙofar sauri fiye da ƙima. A taƙaice ma Suwainah ce kaɗai a tsaye. Idanunta cike da kafiya da ƙarfin iko na Ururu. Wata bakwai da suka wuce ruhin Armad ya taimaka mata ta farkarda ruhinta na Ururu. A duk cikin yaran ita kaɗai ce ta kai wannan mataki. Ita ma kuma taimakon izza ta samu daga ruhin Armad.
Acikin ƴan watannin da suka wuce ruhin Armad da Suwainah sun shaƙu sosai sama da yadda ya kamata. Suna kula da juna kuma hatta Suwainah tana kareshi bata bari wani abu ya faru dashi. Wata biyar da suka wuce aka zo bincike daga fadar sarki Ururu domin ganin abinda ke faruwa a game da yaran. Saboda ƙarfin izzar wanda aka turo sauran ƙiris su gano ruhin Armad amma Suwainah ta taimake shi ta ɓoye shi acikin idanuwanta na Ururu.
Yanzu gashi amincinsu yakai har zata ɗauke shi zuwa doron ƙasar Ururu, doron ƙasa ka farko. Inda babu wani biladama daya ke zuwa inba Ururu ba.
Ruhin Armad na maƙale a bayan Suwainah ita kuma ta riƙe hannun ƙanwarta wadda keta amai.
Ana cikin haka sai kwatsam sama ta fara rugugi. Armad na ɗaga kai ya hango wani farin dutse yana sakkowa wanda girmansa ya rufe komai da komai. Babu rana babu wata. Komai ya rufe.
Wannan dutse shi ake kira da Hajarul-Ururu kuma shi ne abinda ya raba tsakanin doron ƙasa ta farko da ƙasashen ƙasa. Babu wanda yasan sirrin wannan dutse. Abu biyu kaɗai da aka sani akansa shi ne babu wani mahaluƙi daya taɓa gilmashi inba da iznin Ururu ba, sannan kuma tun sanda aka halicci ƙasa bakwai shima wannan dutsen yake.
Cikin ƙanƙanin lokaci Hajarul-Ururu ya sakko dai-dai taron wannan yara dake tsaye suna ɗaga kai suna kallonsa.
Anan wata ƴar ƙaramar ƙofa ta buɗe a tsakiyar dutsen. Babu abinda ake gani acikin ƙofar sai manyan idanuwa baƙaƙe guda biyu.
Nan take baƙin hasken dake cikin idanuwan ya bi takan taron mutanen dake wajen a wani salo na caje su. Hasken yaje ya dawo sannan ya ɗauke. Bayan ƴan daƙiƙu sai siffar wani mutun ta bayyana acikin ƙofar. Idan ka duba sosai zaka fuskanci baƙaƙen idanuwan nan biyu nasa ne.
Ba tare da ya ce uffan ba, basamuden mutumin ma'aboci Ururu ya buɗe ƙofa yaran suka fara shigewa. Sannu a hankali sama da rabi suka wuce aka zo kan Armad da Suwainah.
Suwainah ta nufi ƙafar gadan-gadan kamar sauran yaran amma bisa mamaki tana zuwa dab da ƙofar saita tsaya cak. Ta juya ta dubi mai tsaron ƙofar, idanuwansu biyu na Ururu suka haɗu, a dai-dai wannan lokaci Suwainah ta aikawa da mai tsaron ƙofar saƙo ta cikin bakaƙen idanuwanta ba tare da faɗar wata kalma ba.
Ruhin Armad na kishingiɗe a bayan Suwainah cikin kwanciyar hankali yasan babu wanda zai ganshi indai ba Suwainah ba. Kwatsam sai yaji hannu a wuyansa. Lallai yasan hannun kuma yasan na Suwainah ne to amma mai yasa ta damƙe masa wuya. Ba haka take tashinsa ba. Yawanci idan ta kira sunansa ma kaɗai zai farka.
Kafin ruhin Armad yai wani abu tuni Suwainah ta fincike shi ta damƙa a hannun mai tsaron ƙofar tana cewa. "Ni Suwainah Ururu na kamo Magajin Wilbafos yana ƙoƙarin zuwa doron ƙasa na farko."
Mai gadin ya damƙi Armad da ƙarfin gaske. Yana taɓa shi ruhin na Armad ya bayyana ya fito fili. Cikin kwarewa mai gadin ya ɗaure Armad da igiyar izza ya cilla acikin akwatin izza ya rufe.
Babu komai a idon Suwainah illa tsana da kafiya irin ta ƴaƴan Ururu. Kai tsaye ta shige tana tafiya a hankali cikin ƙasaita. Shi kansa mai gadin saida ya jinjina mata.
Acan bakin wannan tsibiri kuwa inda su Ikenga ke tsaye wasu mutane ne guda biyu suka nufo su. Ɗaya yana da Ururu ɗaya kuma babu. Suna zuwa suka gaisheda Ikenga cikin girmamawa sannan mara Ururun ya bada bayani. "Na gama komai ya shugaba na. Lokaci yayi da zaka canja duniya."
Ikenga yayi murmushi yana duban yaron mai ɗauke da Ururu wanda baifi shekara sha shida ba. "Ya sunanka?"
Yaron ya amsa cikin murna. "Bayajidda Ururu."
Ikenga ya matsa kusa ya shafa kansa cikin murna sannan su biyar ɗin suka rankaya suka tafi.
***
Babi na 128: Rundunar farko
A yayinda ma'abociyar Ururu Suwainah ta yaudari ruhin Armad tasa aka kamashi, acikin garin Jekis na daular Sisiya kuwa biki ake ta tafkawa babu kama hannun yaro. Ranar-Kewaye kenan. Kusan duk babban layin dake kan hanya Armad yabi yana ɗauke da Nostaljiya a bayansa. Sannu a hankali suka zo bakin kasuwa inda suka tarar da wani gagarumin taron yana jiransu.
Kowa dariya yake yana farin ciki ana wullo musu filawowi. Tuni Armad ya gaji babu abinda yake sai gyaɗa kai yana murmushi. Ita kuwa Nostaljiya ko'a jikinta. Murmushi kawai take tana tsokanar Armad lokaci-lokaci.
Suna tsakiyar kasuwar wani mutun yai tsalle ya faɗo tsakiyar fili inda Armad yake. Kafin kowa yai wani abu tuni mutumin ya rungume Armad yana kuka. Nan take matakan tsaro haɗe da sarkin kasuwar suka nufo wajen suka ɓamɓareshi daga jikin Armad dakyar. Nan take wasu suka fara ihu suna cewa aikoshi akai, ana ƙoƙarin fara dukansa Armad ya ɗaga hannu.
"Ku tsaya. Waye kai? Kuma mai ya kawo ka nan?"
Mutumin ya ɗago kai ya dubi Armad cikin idanu masu cike da kwalla ya ce, "wallahi tun daga ranar da naga mutun-mutuminka na Al-yaya a bakin garin Khán nake bibiyarka kawai dan na ganka. Kuma ni mutumin ƙasar ne, tun daga can na yo safara domin nazo na ganka. Ko a yanzu aka kashe ni na cimma buri na."
Armad ya ɗanyi shiru yana kallon idanun mutumin kafin daga bisani ya ja dogon numfashi yayi murmushi. Sannan ya ɗauki filawa ɗaya daga cikin filawowin dake tare dashi ya miƙawa mutumin.
Wannan mutun har shiɗewa yayi saboda murna.
Har Armad ya juya zai tafi ya waiwayo ya ce, "Ya sunanka?"
Mutumin ya risuna ya ce, "Sunana Maikiro Zarru."
Armad ya gyaɗa masa kai alamun godiya sannan ya juya ya tafi. Tun daga lokacin matakan tsaro suka kewaye Armad da Nostaljiya kuma sarki Bihanzin najin abinda ya faru ya bada umarni a kammala zagayen.
Armad da Nostaljiya suka isa sabon gidansu da aka gina musu acikin fada. Sannan ragowar mutane suka ci gaba da biki.
Dare yayi tsaka kuma babu kowa a halin yanzu daga Armad sai Nostaljiya.
Armad ya dube ta ya ce, "aka ce Ranar-Tariya sai an cika shekara sha takwas? Kuma kince min ke shekararki sha bakwai."
Nostaljiya ta ɗago kai cikin kunya zata bashi amsa amma ta kasa. Sai da kyar ta ce, "ai indai aka ɗaura aure ango da amarya suna komawa gida ɗaya amma dole gidan ya zamo na dangin matar. Ita kuma Ranar-tariya rana ce da amarya take komawa gidan mijinta ko kuma danginsa."
*Hmm...*
Armad yaja numfashi yana nazarin wannan al'ada. ALLAH ɗaya gari banban.
"Tun ina yaro ina da wani buri ban sani ba ko zai yiwu."
Nostaljiya tayi mamakin jin haka. Wanne buri ne wannan?
Armad yai sauri ya ce, "Ki daina haɗe gira burin ba wani babba bane. Kawai ina so ranar dana tare da amarya ta tayimin rawa sosai har sai nayi bacci. Ban sani ba ko zan samu cika wannan buri."
Bisa mamaki sai Nostaljiya ta ɗago kai ta dubi Armad. "Kana so?"
Armad ya gyaɗa kai da ƙarfin tsiya kamar kan zai cire.
Nostaljiya ta miƙe daga kan gadon da take zaune ta tsaya a gaban Armad. Sannan ta ajiye mayafin data rufe jikinta ta kuma kwance ɗankwalin dake kanta ta yar aƙas.
Nan take Nostaljiya ta fara rawa. Ta ɗaga hannayenta biyu sama sannan ta fara juya jiki tana rausayawa kamar babu ƙashi a jikinta. Armad ya fara ganin abin mamaki, tunda yake bai taɓa ganin wani abu mai ƙayatarwa irin wannan ba. Irin rangaji da kwarewa wajen salo na rawa, lallai al'amarin Nostaljiya ya girmama kuma ba'a a fannin kyau kaɗai ya tsaya ba.
Sannu a hankali Armad ya fara jin sautin waƙa na tashi. Ya dubi bakin Nostaljiya yaga baya motsi. Yana niyyar tambaya sai ta bashi amsa. "Nima ban sani ba. Amma tarihi ya nuna idan matan ƙabilar Nára suna rawa hatta fararen aljanu sukan sakko suyi kallo. Sannan kuma idan abin ya ƙayatar dasu sukan rera waƙa."
Armad ya fara dube-dube ko zaiga alamun mai waƙar amma babu kowa. Hasalima sautin na tashi ne daga ko'ina a sararin ɗakin babu wani waje da zaka ce yafi bada sauti.
Armad yai ajiyar zuciya ya ci gaba da kallon ikon ALLAH. Lallai anyi halitta mai yawan kyawun sura a wajen nan. Koda ace Nostaljiya ita ce ta zana kanta to lallai tayi zari. Armad bai san sanda ya fara yabon surorin Nostaljiya ba a fili yana mata kirari.
A haka suka gabatarda wannan dare a matsayin ango da amarya a karo na farko a faɗin rayuwarsu. Suna shewa suna dariya da farin ciki.
***
A dai-dai wannan lokaci da ake gudanar da soyayya tsakanin Armad da Nostaljiya a gaɓar daular ƙasar Sisiya runduna ce ta mahaya dubu sha bakwai ke tsaye suna jiran umarni. Dukkaninsu sun jeru sahu-sahu suna tsaye cak akan doki basa ko motsi. Hatta ƙarfin iskar dake kaɗawa da ruwan dake ambaliya daga kogin dake bayansu baisa sun motsa ba.
Dukkansu sanye suke da baƙaƙen kaya masu ratsin fari daga kafaɗa. Sannan a hannayensu akwai manyan makamai kala-kala. Kansu kuwa rufe yake da hulunan kwano masu haɗe da rigar sulke.
Bayan tsahon lokaci wanda zaiyi wahalar ƙididdiguwa sai ga Uznu Ururu ya bayyana a gaban wannan runduna. Yana bayyana dukkan rundunar suka sunkuya sukai gaisuwa.
Uznu ya tafa hannayensa sannan ya kira wasu ɗalasimai irin na ma'abota Ururu. Yana gama kiran ɗalasiman sai ƙasar da rundunar ke kai ta fara narkewa rundunar na nutsewa ciki kamar taɓo. Amma duk da haka rundunar basu motsa ba. Har saida ta kawo musu iya ka sannan suka nutse amma duk da haka ba suyi ko gezau ba.
Bayan sun nutse shima Uznu ya ɓace.
Bayan tsahon lokacin wanda lissafa shi zaiyi wuya sai Uznu dashi da wannan runduna suka fara ɓullowa daga cikin ƙasa a bayan katangar babban birnin Jekis na sarki Bihanzin inda ake bikin Armad Wilbafos. Kan kace meye wannan rundunar ta bayyana akan dawakai suna jiran umarni. Babu wata ƙasa ko ƙura ko wani datti a jikinsu. Tamkar ba daga cikin ƙasa suka fito ba.
Ko meye shirin Uznu Ururu?
Comments
Post a Comment