Dukkan masu tsaron ƙofar suka zubo musu ido. Wasu ma harda nuno su da makami, kai wasu ma zare makaman nasu sukai suka tunkaro su. Ba komai ne ya janyo haka ba illa wasu ƴan-dalilai: na ɗaya dai ana cikin halin yaƙi da fargaba; na biyu rundunar sarki Iluru bata daɗe da dawowa daga filin daga ba inda suka fafata da rundunar Ayubu; na uku kuna Armad, Nusi, Nostaljiya, Cokali, Inara da Lamarudu kawai bayyana sukai akan iska. Dole hankalin kowa ya tashi domin kuwa wajen dasu Armad suka dira har ƙura ce ta tashi, kai kace an jefa dutse a ruwa.
"Kai, ku tsaya cak a inda kuke!"
Shugaban masu tsaron ƙofar ya daka musu tsawa a yayin dashi da mutanensa suka tunkaro su da mugun nufi.
"To wai ta ina zamu fara?" Inji Cokali. Ko kaɗan bai damu da dubban mutanen dake kalon su ko kuma masu gadin dake tunkaro su ba.
"Nima dai abinda ke raina kenan." Inji Nostaljiya. "Kaga neman ƴaƴan Deniz Huhutu ba abu ne mai sauƙi ba, tunda kuwa da abu ne mai sauƙi da tuni kowa ma ya nemo su. Dan kawai munzo garin su bashi ke nuna mun same su ba. Idan ma mun same su bana tunanin zamu samu amsar da muke buƙata cikin sauƙi. Kaga yadda tarihi yake nunawa suma manyan ma'abota izza ne."
Armad ya gyaɗa kafaɗa, ya ce, "Ku bari mu shiga garin. Zamu san yadda zamu yi."
"Sarki, akwai matsala a wajen nan fa. Kalli." Lamarudu ya nuna gaban su inda masu gadin suka kewaye su riƙe da makamai.
"Bari nayi maganin su." Inji Nostaljiya. Amma kafin ta motsa Nusi ta tureta ta shiga gaban ta. "A'a, malama, keda kike da ciki ina ke ina faɗa."
Armad na gefe baice uffan ba.
"Ce miki akai mai ciki raguwa ce? Kauce kiga yadda ake yi." Nostaljiya ta ture Nusi.
Suna cikin kace-nace masu gadin suka fara turo musu da saƙo. Dunƙulen walƙiya, masu da kibbau suka nufo su. Sarki Iluru ya hana duk wani baƙo shiga garin, sannan kuma an basu dama su halaka duk baƙon da basu yadda dashi ba ko kuma wanda yaƙi bin doka.
Armad ya juyo ya fuskanci masu-gadin zai ɗau mataki, amma Inara yai zumbur cikin ladabi ya shige gaba. Ya dunƙule hannun sa ya daki iska dashi. Nan take iskar wajen ta ɗau zafi. Ƙafin hare-haren su ƙaraso walƙiya ta fara tartsatsi akan iska. Nan take hannun-aradu ya bayyana. Duk mashin ko kibiyar data tunkari hannun sai dai kaga ta narke tabi iska. Hannun aradun yayi kan masu gadin gadan-gadan. Kan kace meye wannan sauran ƴan kallo sun ranta ana kare. Su kuwa masu-gadin basu gudu ba; tsayawa sukai cikin kafiya da dagiya. Amma ina, kafiya da dagiya bata isa ta tsaya gaban babbar izza ba, kafin su ankara al'amari ya canja. Hannun aradu maɗaukaki ya murƙushe su ya ƙone su. Sannan ragowar tartsatsin walƙiyar ya ƙarasa ya tunkari ƙofar garin gadan-gadan.
Armad ya juyo kan mutanen sa ya kira babban ɗalasimi.
"Aiban'shisu!"
Mutanen Armad kawai buɗe ido sukai suka gansu a tsakiyar wata kasuwa acikin garin. Wataƙila sabida yanayi na yaƙi babu mutane da yawa a kasuwar.
Abin mamaki har sanda suka bayyana a kasuwar harin Inara na hannun-aradu bai ƙarasa kan katangar garin ba. Suna bayyana suka ji ƙara da rugugi, hannun-aradun ya daki ƙofar garin, kai kace ƙatuwar gudumar ƙarfe ce ta daki dutse.
Hankalin kowa a kasuwar ya juya kan ƙofar garin. Gashi dai Seerish babban birni ne, amma ƙarar babu wajen da bata kai ba. Kowa ka gani a kasuwar tunani yake hari aka kawo musu. Ba jimawa mutane suka fara gudun neman tsira.
"To, Armad, da kasan da wannan ka bari muka sha wahala a banza." Inji Cokali.
Armad yayi murmushi tare da buɗe baki zai bashi amsa amma Nostaljiya ta riga shi. "Laifin Nusi ne." Inji Nostaljiya. "Da Nusi bata yimin katsalandan ba da niyya ta na goge tunanin masu-gadin, tayadda baza ma su san munzo ba."
Nusi ta juyo a fusace. "Ki saurara. Wane irin laifi na? Ana ƙoƙarin kare abinda ke cikin ki amma bakya gani."
"Me kika ce?"
Armad ya shiga tsakani ya tsaya. "Ku bari mu fara samun waje daga baya saiku ci gaba."
Daga inda suke Armad yana hangen wani ɗan wajen cin abinci a ƙasan wani ɗan otal. Ba tare da neman shawarar su ba Armad yai wuf ya cilla su cikin otal ɗin, ɗaki mai lamba ta ashirin da uku.
A wajen da suka bari babu komai sai ɓarin gado da wata rabin katifa. Idan ka lura sosai zaka ga gadon da katifar kamar an sa wuƙa an yanke su daga jikin asalin su. Ragowar mutanen dake cikin kasuwar basu kula ba, musamman sabida hargitsi da hayaniya da kuma gudun neman tsira da kowa ke yi.
Acikin otal ɗin, a ɗaki mai lamba ta ashirin da uku, Armad ne tsaye tare da Nusi, Nostaljiya, Iliyasis, Cokali, Inara da Lamarudu, a gaban su wani rabin gado ne, kwata-kwata ba'a san inda ɗaya rabin yake ba. Ga wata katifa a kan gadon wadda ita ma ba'a da masaniya kan inda rabin ta.
Inara ne ya fara leƙawa ta taga ya hango rabin gadon da rabin katifar akan titi inda suka baro. Mutanen kasuwar ko kaɗan basu da masaniya kan daga ina wannan rabin gado da katifa suka fito ba. Wataƙila bayan kwanaki idan an matsa da bincike a gano daga inda rabin gadon da katifar suka fito.
"Gaskiya, Armad, idan za'ai irin wannan shillin a ringa gayamana." Inji Nusi tana haki.
"To, Nusi, zanyi amfani da Aiban'shisu na kawo mu nan." Inji Armad.
"Kafin kayi zaka gayamana!"
Armad ya fashe da dariya ganin yadda fuskarta tayi.
Nusi ta wuce banɗaki tana ƙoƙarin amai. Har Armad ya buɗe baki zaice 'abin har yakai haka' amma wata zuciyar tace ya fasa ya rufe bakin sa.
Nostaljiya kuwa waje ta samu a gefen yankakken gadon ta zauna tana yiwa Nusi gwalo.
Inara, Lamarudu da Cokali abin yafi ƙarfin su - kamar abin nan ne da ake cewa faɗan manya ba'a shiga - sabida haka suka fice daga ɗakin suka fara tasu tattaunawar a tsakanin su.
"ArmaNos, kasan mai yake bani mamaki? Ko ni da nake ɗauke da ɗa banji komai ba amma Nusi ta rikice."
Armad ya girgiza mata kai alamun ta daina tsokanar Nusi amma kamar ziga ta yake yi.
"Wataƙila ma amai zata kwara a banɗaki. Hmm... Matsalar raunanan mata kenan. Kuma in anyi magana tace ba'a kyauta mata ba."
Dogon nishi Armad yayi, tare da komawa gefe ya nemi waje ya zauna ya rufe idon sa. A ransa yana cewa sha'anin mata sai su.
Armad na zaune, yaji yo hayaniyar su Cokali a bayan ɗaki suna magana ƙasa-ƙasa. Hakan yaja hankalin sa ya tashi ya leƙa ta taga domin ganin mai yake faruwa.
A bayan ɗakin akwai ɗan-ƙaramin lambu cike da fulawowi da fure kala-kala, wasu farare, wasu koraye, wasu ruwan ɗorawa. Iska na kaɗawa tana bada yanayin sanyin yammaci. Armad na leƙawa ƙanshin fure ya daki hancin sa. A dai-dai tsakiyar wannan lambu Lamarudu ne tsaye zare da takobi. Inara na tsaye jikin sa ya juye izuwa walƙiya, shi kuwa Cokali littafi ne a hannun sa yana rubutu.
Kalmar farko da Armad ya fara ji ita ce: "biyu da ɗaya."
Lamarudu ya ɗaga takobin sa ya sari kafaɗar Inara. Takobin ta shige ta wannan ɓari ta fice ta ɗayan ɓarin ba tare da Inara yaji komai ba.
"Uku da ɗaya." Inji Cokali. A lokaci guda kuma yana rubutawa acikin littafin sa.
Armad ya tsaya ya ƙura musu ido cikin mamaki, hankalin su na kan abinda suke yi (koma meye), sabida haka babu wanda ya kula da zuwan Armad.
Bayan ɗan lokaci yana kallon su sai ya juya ya koma cikin ɗakin wajen Nostaljiya. Armad ya zauna a kusa da ita ya gishinkiɗa a jikin ta yana kallon ta yana murmushi.
"Nostee Fara, kyakkyawa, doguwa, mai dogon hanci da ɗan-ƙaramin baki."
Nostaljiya ta fashe da murmushin farin ciki. "Ba haka ake cewa ba." Sannan ta juya sautin ta ya koma waƙa ta fara rera masa waƙe.
"Armad, kyakkyawa, ɗan-fari, mai hanci, dogo, siririn sarki."
"Armad, kyakkyawa, ɗan-fari, mai hanci, dogo, siririn sarki."
"Armad, kyakkyawa, ɗan-fari, mai hanci, dogo, siririn sarki."
Armad bai san sanda dariya ta kwace masa ba ya rungume matar sa. Idan son samu ne su zauna a haka tsahon shekaru, to amma akwai yaƙi na tunkaro su.
Armad ya ɗago kai a hankali ya kalleta sannan ya ɗora hannun sa akan cikin ta. "Ya akai kika san namiji ne?"
Nostaljiya ta gyaɗa kafaɗa, ta ce, "Na gayamaka namiji ne. Ina ji a jiki na."
Armad ya ɗanyi shiru kamar zai tanka amma daga bisani ya fasa.
"Sai mu saka masa sunan abban ki."
Nostaljiya ta haɗe rai. "Abba na kuma?"
"Eh mana. Ko bakya so?"
Nostaljiya ta turo baki. "Armanos zamu saka masa."
Armad yai zumbur ya miƙe ya dube ta baki hangame ya ce, "Armanos kuma? Haba, Nostee, wane irin Armanos sai kace a tatsuniyar gizo da ƙoƙi."
Nostaljiya ta fashe da dariya. Amma har cikin ranta Armanos take niyyar saka masa, kawai dai tasan Armad bazai yadda ba.
A haka wannan masoya suka wanzu suna tattaunawa tsahon awa biyu kafin Nusi ta shigo ɗakin da kwanukan abinci a hannun ta. Tana zuwa ta ajiye su a gaban Armad tana hararar Nostaljiya ta gefen ido. Amma ko a jikin Nostaljiya, hasalima Nusi na ajiye kwanukan tayi sauri ta kai hannu zata buɗe. Nusi tayi wuf ta janye kwanukan.
"Ki saurara, cewa akai ke na kawo wa?" Inji Nusi.
"Kinga, kayan miji na mata ne, ki ajiye mana kawai idan zaki ajiye, dama yunwa nake ji." Inji Nostaljiya.
Armad na gefe kawai dogon numfashi yaja. Indai Nusi da Nostaljiya suka haɗu tofa sai yayi ciwon kai. Suna farawa Armad ya ɗauki kwano ɗaya ya fice dashi wajen su Cokali wanda har yanzu wasan suke.
"Sha uku da bakwai." Inji Cokali.
Armad ya dube su ya ce, "wanda zaici abinci yazo."
Ko kallon sa basu yi. Hankalin su nakan abinda suke yi.
Armad ya juya da kwanukan sa ya nemi waje ya zauna. Birabusko ne da miyar taushe, sai naman busasshiyar kada da kitsen aljanin-rago a gefe.
Armad dai yana cin abinci ne kawai sabida ɗanɗano bawai dan buƙata ba. Tun yana yaro (sanda ya samu fasahar Sikai) ya daina buƙatar abinci. Idan kaga yaci abinci to kawai danɗano ne ko kuma ganin ido.
A wannan rana Armad kawai ɗora hannun sa yayi akan abinci. Wani farin haske ya fita daga hannun sa ya shiga cikin kwanon. Koda abinci ya haɗu da hasken sai kawai abincin ya narke ya koma ƙawanyar walƙiya. Sannan ya shige cikin hannun sa.
Da wannan Armad ya kammala cin abincin. Ya tashi zai koma ɗaki ya kwanta amma yana tunowa da Nusi da Nostaljiya sai ya canja shawara ya dawo ya samu waje acikin lambun ya kwanta. Take bacci ya ɗauke shi.
Zaka iya cewa shi kansa wannan wani abu ne kawai daya zamarwa Armad al'ada, amma a zahiri baya ɓuƙatar bacci kamar yadda baya buƙatar ci da sha. A halin yanzu Armad mutun ne amma ba kamar sauran mutane ba.
A wannan guri Armad ya kwana. Cikin dare Nostaljiya tazo ta kwanta a gefen sa suka kwana tare. Gari na wayewa kowa ya bayyana kan teburin tattaunawa.
Armad ne ya buɗe taro.
"Nawa da nawa kuka tashi jiya?"
Cokali najin haka yai farat ya amshe kamar daman jira yake Armad ya tambaye shi. "Inara ne yayi nasara da maki uku. Wasan shaɗi: Lamarudu ya yanki Inara sau talatin da uku, shi kuma Inara ya shanye saran sau talatin da shida."
Inara da Lamarudu aka kalli juna akai murmushi, ga dukkan alamu wasan yai musu daɗi.
"To ai ratar ba yawa. Nan gaba dani za'ai." Inji Armad.
Lamarudu ya sunkui da kai baice komai ba. A ransa yana cewa wane ganganci ne zai sa yayi shaɗi da Armad.
"Ƴaƴan Deniz Huhutu guda uku muke nema wato Deniz Wuyawuya, Deniz Yudusu da kuma Deniz Curucuru. Curucuru yana tare da Ikenga sabida haka mun riga mun san inda yake. Deniz Wuyawuya da Deniz Yudusu muke nema. Dole ɗaya acikin su yasan inda fasahar da muke nema take.
"Nostee ta bani tabbacin cewa duk wanda muka kawo mata zata shiga cikin kwakwalwar sa ta ga meye aciki, kamar yadda ta taɓa shiga kwakwalwata taga maganar Amraikugyu." Armad na zuwa nan ya ɗanyi shiru tare da yiwa Nostaljiya hararar wasa. Nostaljiya ta haɗe rai gami da turo baki da kafaɗa. A ranta tana cewa 'wai dole kullum Armanos sai ya taso da wannan zancen'.
"Eh, dole mana na taso dashi." Inji Armad. Amma babu wanda yaji maganar sai Nostaljiya. Wato dai ta cikin kwakwalwarta yayi mata magana.
Nostaljiya ta ƙara haɗe gira tana hararar sa.
Nusi na ganin haka ta gane mai ke faruwa. "Gaskiya ba kyau. Kuna cikin mutane kuna mana raɗa. To dole ma gulma ta ake yi."
"Eh, Armad ne yace kin takura masa." Inji Nostaljiya. Daman neman ƙiris take yi.
Nusi ta juyo zata fara bambamin bala'i amma Armad yai sauri ya katse zancen ta hanyar ɗaga musu hannu.
"Muna so kowa ya bamu shawara kan yadda yake ganin zamu ɓullowa abinda muka saka a gaba."
Suna jin haka dole suka mayarda wuƙaƙen su jaka.
"Mu shiga gari mu tambaya." Inji Inara.
"Muyi amfani da zaren izza ko yanayin-izza mu nemo su." Inji Cokali.
Armad ya girgiza kai. "Tambaya baza ta kaimu ko'ina ba, Inara, bana jin akwai wani gama-garin bil-adama ko aljan da yasan inda wannan mutane suke. Idan ka haɗa kuɗin dake kan su dana mahaifin su yafi kuɗin dake kan Tarifil-fakta yawa. Kuma bana jin yanayin-izzar su ko kaɗan. Amma hakan bashi yake nuna basa wannan gari ba. Akwai matuƙar yiwuwar suna ɓoye yanayin izzar su ne da wata irin fasaha wadda tafi ta ƴan ƙabilar Elbinuil. Ku kawo wata shawarar."
Nusi ta numfasa ta ce, "Mai zai hana mu saci rijistar Ururu muyi amfani da ita? Naji ance tana iya nemo mutun koda ya mutu, kuma koda yakai nisan tafiyar shekara guda daga inda rijistar take."
Armad ya gyaɗa kafaɗa ya ce, "Nusi-ya, ko ni daba kowan-kowa ba ina iya jiyo ƙanshin izzar mutun tsahon nisan tafiyar shekara goma akan ingarman doki. Kuma ina jin yanayin izzar mutun koda yakai shekara guda sa mutuwa."
"Ehhh.." Inara ya hangame baki. Baisan sanda ya zame daga kan kujerar sa ya faɗi ƙasa ba.
"KANAJIN YANAYIN IZZAR MATATTU KODA SUNYI SHEKARA GUDA DA MUTUWA? KUMA KANA JIN YANAYIN IZZAR MUTUN KODA YAKAI NISAN SHEKARA GOMA AKAN INGARMAN DOKI?!" Inji Nusi baki wangale.
"Eh mana. Meye?" Inji Armad. Kwata-kwata bai ga dalilin da yasa suke mamaki ba. Wannan ai ba wani abu bane a babin K'Narbig.
"Ka haura Bihanzin da rata mabayyaniya. Wataƙila ma kana tsarar Kuyurussa'ayi." Inji Nostaljiya.
Armad ya girgiza kai. "Da saura na."
"Da sauran ka? Wai kai nawa ce izzar ka ne?" Inji Nusi. "Ka fara bani tsoro, Armad. Layin daka ɗakko zaka iya sace duk wani ma'aboci izza a ban ƙasa ka zuƙe masa izza ka ƙarawa kan ka ba tare da kowa ya sani ba."
"Ah..." Armad ya buɗe baki cikin mamaki kafin ya fashe da dariya. "Ai kuwa haka za'ai, Nusi." Ya miƙe cikin murna ya riƙe hannun Nusi yana jinjina mata. "Abinda zamu yi kenan. Ban taɓa sanin ke kwaruwa bace sai yau. Wannan ita ce shawara mai kyau. Dole ma haka za'ai."
Nusi ta zare ido tana kallon sa, kwata-kwata bata gane mai Armad yake nufi ba. Wai mai tace ne har yake murna.
Bayan ɗan lokaci Armad ya fuskanci babu wanda ya fuskance shi sabida haka yayi musu bayani. "Sace Deniz Iluru zamu yi mu kawo wa Nostaljiya ta duba tunanin sa. Dole ma shi zai san inda ƙannen uban sa suke."
"Kaaaaiii, sace sarkin jinzidal kake so muyi?!"
"A haba, Armad, wannan ba dabara bace. Daga nan kawai kace mu afka musu da yaƙi mana."
"Sarki Armad, sace sarkin jinzidal abu ne mai wahala. Karfa ka manta sarkin jinzidal shi ne mafi girman izza a gaba ɗayan wannan ƙasa, kuma shi ne wanda yafi kowa tsaro."
Armad yai shiru yana jin su kafin daga bisani ya miƙe tsaye. "Na yanke shawara. Sace Iluru ita ce hanya mafi sauƙi da zamu nemi ragowar ƴaƴan Deniz Huhutu. Kowa acikin ku ya shirya. Yau da daddare zamu fita sace sarkin Jinzidal."
"Kai, wai da gaske kake? To idan mun sato shi a ina zamu saka shi? Anya kuwa, Armanos?"
Armad ya gyaɗa kai. Yau rana ce ta sace sarkin Jinzidal.
***
A dai-dai wannan lokaci da Armad ya yanke shawara su sato Iluru, acikin fadar sarki Iluru wani abin mamaki ne yake faruwa.
Ana zaune ana zaman fada. Kowa ka gani cikin sulke yake da takobi rataye a kafaɗa cikin shirin yaƙi. Sarki Iluru na zaune kan karagar sa. Deniz Bizaya na tsaye a ɓarin daman karagar. Sadauki Deniz Kalhari na tsaye a ɓarin hagu. Sai kuma salsa (mutun uku) dake tsaye a bayan karagar fuskokin su a rufe.
Akwai manyan kwamandun denizawa goma a ɓangaren dama, da kuma manyan hakimai goma a ɓangaren hagu. Duk sun jeru a layi cikin shirin kota-kwana. Kowannen su ya nutsu yana sauraren rahoto daga Sarkin Ƙofa - mutumin dake kula da gadin ƙofar garin.
"Hannun walƙiya ne wanda girman sa bazai misaltu ba. Duk abinda hannun ya taɓa sai ya narka, kai kace baƙar wuta ce. Masu gadi talatin da huɗu ne suka rasu a sakamakon arba da walƙiyar. Shi wanda yayi harin shi ne shugaban su, amma banda shi akwai mata biyu da maza uku. Nasan amma baza sukai ƙarfin sa ba." Inji Sarkin Ƙofa.
"Deniz Ulbaru?" Iluru ya kira sunan Sarkin Ƙofar, wanda ya ɗago kai a firgice ya kalli sarkin.
"Na'am, Mai-Rana."
"Ina iyayen ka suke?"
Ulbaru najin haka ya zare ido, jikin sa ya fara rawa. "Sun mutu, rankai daɗe."
"Haka ne, sun mutu. Sun mutu tun kana ɗan shekara shida a duniya. Ni ne na raine ka, na raya ka, na tufatar dakai, sannan nayi maka aure, na baka aikin yi. Kana gayamin zaka butulce min ne a ranar da nake buƙatar ka?"
Iluru na rufe baki Ulbaru ya zube a ƙas yana kuka. "Rai na fansa gare ka, Mai-Rana da Zafin-Rana."
"Kana da awa shida ka nemo wanda suka shigo min gari." Da wannan Iluru ya sallami Ulbaru. Sannan ya juyo kan kwamandun sa da hakiman sa ya bada umarnin ƙarshe. "A fara shirin yaƙin ƙarshe."
"An gama, Mai-Rana da Zafin-Rana." Take kwamandun da hakiman suka ɓace. Ya rage saura Iluru, salsa ɗin sa, ɗan sa Bizaya da kuma na hannun daman sa Kalhari.
Iluru ya buɗe baki zaiyi magana sai kwatsam fadar tayi duhu, wani irin sanyi mai kama da sanyin-babban-sihiri ya sauka ya cika fadar. Nan take Bizaya, Kalhari da salsa suka zube a ƙas sumammu. Bayan ƴan daƙiƙu duhun ya ɗauke haske ya dawo. Kalhari, Bizaya da Salsa na zube a ƙas sumammu basa ko motsi. Wasu mutane sanye da baƙar riga doguwa na tsaye a gaban Iluru. Fuskokin wannan mutane a rufe suke da baƙin haske. Bayyanar wannan mutane tasa wata babbar izza ta cika fadar, iskar dake zagawa tayi nauyi tayadda ko numfashi bazai yiwu ba. Alama ce da umarni cewa duk wani Sammai ya kauce domin kuwa bazai iya ba.
Duk abinnan dake faruwa Iluru na zaune kan karagar sa bai motsa ba yana kallon wannan mutun tara.
Ɗaya daga cikin mutanen tara ya dubi Iluru a hankali ya ce, "kasan mai ya kawo mu?" Muryar sa tana bada wani irin amo mai ban aljabi kamar ana jan guga a ƙasan ruwa, kai kace iska baza ta iya ɗaukan sautin muryar ba.
"Idan baku faɗa ba ya za'ayi na sani." Inji Iluru. Har yanzu bai motsa daga inda yake ba.
Mutanen tara sukai shiru naɗan lokaci kafin daga bisani wanda yayi magana da fari ya ƙara yin magana. "Kashedi muka zo."
Iluru ya yamutse fuska kamar yana mamakin abinda mutumin yace. "Nifa sarkin jinzidal ne mai bin doka. Duk umarnin da kuka bayar ina biyayya akai. Mai kuma kuke so nayi? Kada ku nemi ku ƙalamin sharri kan abinda ban aikata ba."
"Ba wasa ne ya kawo mu ba." Wani daban daga cikin mutun taran ya dakawa Iluru tsawa. "Mun san ka, kasan mu. Marmaza ka bar abinda kake shirin yi. Idan kabi umarni zamu baka Fatima Wilbafos ko kuma Zaikid Wilbafos. Idan kuma ka kafirce, zamu ɗaga kuɗin dake kan ka, sannan mu bayyanawa duniya sunan ka."
Iluru ya gyara zaman sa akan karagar sa ya dube su ya ce, "da gaske ne kun kama su?"
Mutun taran suka haɗa baki suka daka masa tsawa. "Kaaaiiii!!" Wata babbar izza ta daki Iluru. Take naman jikin sa ya zagwanye ya narke yabi iska. Amma duk da haka murmushi Iluru yake.
"Shiga taitayin ka, umarni ake baka."
Iluru ya girgiza kai. "Haba, kuma kunsan komai daren daɗewa bazan ci gaba da zama a ƙarƙashin ƙasa ba. Tsahon lokaci kun katange ni, tsahon lokaci kun hanani taka ƙasa, tsahon lokaci kun hana RANA haskawa. Idan kuna so na janye shiri na sai dai ku kawo min ruhin Dul'Ururu."
"Ɗul'Ururu?" Mutun taran suka tambaye shi da sauti iri ɗaya.
"Eh. Ko shi ko Taidara ko Maikiro Abbas ko Ikenga. Indai aka kawo min kan ɗaya daga cikin waɗannan zan haƙura na janye makamai na. Amma mai zanyi da wata Fatima ko wani Zaikid wanda basa cikin mutun ashirin da huɗu dake kan Allo Izza."
"Idan muka baka ruhin mutun ɗaya daga kan allon zaka janye?"
Zuwa wannan lokaci tuni tsokar Iluru ta haɗe da juna ya dawo sabo. Har yanzu yana zaune kan karagar sa bai motsa ba. Ya ɗanyi shiru kamar yana tunani kafin daga bisani ya girgiza kai. "Kai, nifa indai ba wannan mutun huɗun kuka kawo ba to babu yadda a tsakanin mu."
"To shikenan. Kayi sani cewa Idanunmu na nan yana yawo akan ka. Zaka yi dana-sanin ƙin karɓar tayin da mukai maka."
Daga nan mutanen tara suka ɓace ɓat. Kai kace dama can basu zo ba. Bizaya, Iluru, da salsa suka fara shure-shure suna ƙoƙarin farkawa.
Comments
Post a Comment