Skip to main content

288

 A hankali Dul'Ururu ya juyo ya kalli wanda ya riƙe masa hannu, inda yayi arba da saurayi dogo, wankan tarwaɗa mai tambarin miyura a goshin sa. Idanun saurayin na dama a rufe suke da jan kyalle wanda ya rufe idon ruf, tayadda duk iyakacin sa-idon mutun bazai ga komai ba. Daga saman jan kyallen zaka hangi wani dogon tabo (alamun yankan wuƙa ko takobi) wanda ya warke da daɗewa amma duk da haka ana iya ƙiyasta zurfin sa, wataƙila sabida ingancin makamin daya aiwatar dashi. 


Idan ka juyo kan idanun saurayin na hagu zaka ga suna ɗauke da hoton miyurar dake goshin sa. Wato kamar kace an matse miyurar dake goshin an rage mata girma an saka ta acikin idon ta maye gurbin baƙin dake tsakiyar idon. Wato ganin wannan ido kaɗai firgici ne matuƙa, to amma abin tambayar anan shi ne: idan har wannan saurayi ya iya bayyana idon sa na hagu ba tare da damuwa ba to kuwa mai zai saka ya rufe idon sa na dama? Wataƙila masifar dake cikin idanun na dama sunfi na hagu, wataƙila kuma kawai ganin dama yayi.


To tunda bamu da amsar wannan tambaya bari mu koma kan gashin kan wannan saurayi. Gashi ne jajawur kamar wuta. An gyara shi, an wanke shi, an killata shi. Tun daga nesa zaka hango kyallin sa. Idan rana ta haska sai kaga kamar wuta ake hurawa akan sa. 


Dul'Ururu shi ne mutun na farko daya fara gane wannan saurayi. "Hmm... ARMAD WILBAFOS - dama kai muke jira." Inji Dul'Ururu.


Armad yayi ɗan murmushi, ya ce, "da ka turo tuntuni ai da tuni nazo."


Dul'Ururu ya taɓe baki jin izgilin da Armad yayi masa. Maimakon ya maida martani da baki kawai sai ya nuna Armad da ɗan'yatsan sa ƙarami na dama, nan take wani dunƙulen baƙin haske ya tattaru a tsinin ɗan'yatsan yai fitar burtu kan Armad. Koda ganin haka sai Armad ya fidda hannun sa na hagu (tunda na daman har yanzu yana riƙe da Dul'Ururu) ya daki iskar gaban sa, sannan ya daki ta bayan sa. Dai-dai wajen da ya daka wata ƴar taga kamu biyu da rabi ta bayyana; ɗaya a gaban sa, ɗaya a bayan sa. Jikin tagar na Negrinki ne zuryan, sannan ba'a hango komai aciki sai duhu mara iyaka. 


Harin da Dul'Ururu ya aiko masa ya shige ta cikin tagar dake gaban sa sannan ya ɓulle ta tagar dake bayan sa. Ibraham Nil yayi rashin sa'a shi ne a saitin bayan Armad. Ai kuwa kafin ya ankare harin yai gaba dashi. Idan da anan abin ya tsaya to da sauƙi, amma kafin Ibraham Nil ya ankara hasken ya juye izuwa jerin taurari ɗari. Taurarin sukai kan Ibraham Nil suka daki ƙirjin sa suka tarwatse. Duk faɗin garin Faideba babu inda ba'a ji ƙarar wannan hari ba. Ƙura ta turnuƙe tayi sama. Ƙasa ta tsattsage, kai kace haƙa akayi. 


Har yanzu Armad na riƙe da hannun Dul'Ururu, shi kuma Dul'Ururu yaƙi sauka daga kan ruwan cikin Inara. Zaka iya cewa Dul'Ururu bai damu da abinda yayi wa Ibraham Nil ba; wataƙila bai damu da abokin tafiyar tasa ba, ko kuma ya yadda da ƙwarin sa. To amma da dama zasu yadda cewa ko tsumin tauri irin na sarkin-sarki mutun ya sha harin Dul'Ururu zai iya kai shi ƙas.


Abin mamakin shi ne ƙurar tana lafawa aka hango Ibraham Nil a tsaye yana riƙe da wata budurwa a gaban sa. Budurwar ta samu sassaɓawar kamanni (musamman a ƙirjin ta wanda yake a fafake da kuma hannun ta na hagu wanda ya gutsure) amma duk da haka idan ka kalli fuskar ta zaka gane ba wata bace illa Suwainah. Bata motsi ko kaɗan, kuma ko makaho idan ya shafa yasan ta mutu. A lokacin data mutu idanun ta suna kan Ibraham Nil tana hararar sa. 


Bayan ɗan lokaci ana kallon-kallo tsakanin Armad da Dul'Ururu, sai Dul'Ururu yayi ajiyar zuciya ya ɗaga Inara. Ganin ya ɗaga Inara shima Armad ya sake shi. 


Nusi ta gabato ta ɗauki Inara domin duba ciwukan sa. Ko ba komai ita ce likitan tafiyar. 


A ɓangare guda kuma yaƙi ya dawo sabo. Kwamandun Armad na bayan sa kamar yadda su Haruta da Maruta da Hanibal suka hau bayan Dul'Ururu.


Ana wannan hali ne aka jiyo muryar Ibraham Nil yana masifa. "Wai kai Dul'Ururu meye matsalar ka? Ka ringa saita hare-haren ka a dai-dai. Yanzu gashi kayi mana asara."


Dul'Ururu ya juya ya kalli Ibraham Nil, ya ce, "kana da sauran biyar ai, kuma zaka iya haɗa wata idan kana so."


Ibraham Nil ya cije baki, ga dukkan alamu kalaman Dul'Ururu basu yi masa daɗi ba. "Kasan tsadar haɗa kowacce acikin su? Kullum Tadiyraini surutu yake min akan ina ɗebe lalitar masarauta, bai san wahalar da ake sha ba. Yanzu gashi ka..."


"To naji, ka rubuta a suna na zan biya." Inji Dul'Ururu. 


Hanibal ya dubi Ibraham Nil yana murmushi, ya ce, "amma dai kasan naga abinda kayi, ko? Da kaga dama da zaka iya kaucewa harin. Dama dai kana so ka ɗebi wani abu a asusun Dul'Ururu."


Ibraham Nil ya riƙe bakin sa da hannu yana yiwa Hanibal inkiya da yayi shiru. 


A ɗaya ɓangaren Nostaljiya tana riƙe da hannun Armad tana yi masa murmushi. 


"Wai sai da ka rufe idon nan?" Inji Nostaljiya.


Armad ya fashe da dariya, yana tuno tattaaunawar da sukai da ita akan idon. "Ido na lafiya lau yake. Ba wata matsala." 


Babara ya leƙo ta gefe yayi wa Armad kwalo, ya ce, "haha.. na gaya maka idan ka makance ba wadda zata kula ka."


Iliyasis ya gabato gaban Armad yana gyaɗa kai cikin jinjina. "Wata nawa kenan rabon da muga juna? Wata uku kacal amma har ka kai wannan mataki? Jinjina a gare ka." 


"Ah, Iliyasisisisisisisisisi," Armad ya janyo Iliyasis kusa dashi yana murmushi. "Iliyasisisisisisisisisi, wata takwas kenan fa. Mugayen aljanun can ƙasa suka ƙara danna ni har sai da muka je ƙasa ta goma. Tafiyar lokaci acan yana da banbanci da wannan duniya; kamar a Non-toch-teka."


Iliyasis ya gyaɗa kai. "Na gane, to amma na meye duk sanda zaka kira suna nan sai ka ƙara 'sisisisi'?"


Kafin Armad ya bada amsa Cokali ya diro. "Ah... Iliyasisisisisisisisisisisisi... Haha.... Gaskiya Armad ka iya saka suna. Mai zai hana mu mayar dashi Iliy...?"


"Rufe mana baki, Cokali." Iliyasis ya kai masa sura. 


Nazara kawai gyaɗawa Armad kai yayi ya ɗaga masa ɗan'yatsa alamun jinjina. Lamarudu, wanda ke kusa dashi, hararar sa yayi, a ganin sa ya kamata Nazara ya matso kusa ya kwashi gaisuwa. A wani salo na nunawa kowa yadda akeyi ya gabato gaban Armad ya zube a ƙas yayi gaisuwa. 


"Na gaya maka ka daina durƙusa wa. Babu wani bil'adama da ya isa ka durƙusa masa." Inji Armad. 


Lamarudu ya kalli Armad ya haɗe gira yana mamakin abinda Armad ya faɗa. "To amma, shugaba Armad, ai bana ji har yanzu kana sahun bil'adama. A wajen kyawu ka ɗara manyan fararen aljanun farko, a wajen izza kafi Eyriyon, a wajen nutsuwa da lissafi kafi Aldaima, a wajen fushi kafi baƙin shaiɗan, a wajen fasaha kafi Hidaya..."


"Kai...... Dan ALLAH kayi shiru haka."  Armad ya toshe kunnen sa da hannu biyu. Kullum haka yake fama da Lamarudu. Ko a lokacin suna cikin halwa sai da Lamarudu ya dage akan sai ya rubuta littafi akan 'ikon' Armad. 


Acan gefe Nusi ta gama yiwa Inara magani amma ya kasa gabatowa gaban Armad. Kuka kawai yake. Tsahon lokaci bai ce komai ba. Ya kasa haɗa ido da Armad. A har kullum shi da ya kamata ace shi yake kare iyalan Armad amma shi ake karewa. A ransa yana ji cewa bashi da wani amfani.


Nusi ta riƙe hannun sa taja shi gaban Armad. "Armad ga Inara, shi kaɗai ne ya tari abokan gaba kai tsaye dan ya kare mu." Inji Nusi.


Armad ya rugo ya rungume Inara. "Inara, kasan me...." Armad ya ɗanyi shiru yana nazarin fuskar Inara kafin ya fashe da dariya yana nuna kumburarriyar fuskar. "Ku duba ku ga fuskar Inara, irin haka fuskar Nostaljiya take yi idan ta tashi daga bacci."


Koda jin haka sai kowa ya fashe da dariya. Nan take Inara ya daina kuka ya goge hawayen sa. 


Armad ya dubi Nusi, ita ma Nusi ta dube shi. Kafin ya ce wani abu Nusi ta gabato ta riƙe masa hannu. Acikin idanun Nusi babu wani kokwanto akan ƙaunar da take yiwa Armad. Tuni ta daina ɓoye komai.


Sai dai kuma kash, Dul'Ururu bashi da niyyar barin Nusi ta gana da Armad. "Armad, ga naka saƙon." Inji Dul'Ururu. Ya ɗaga Rijistar dake hannun sa ya nunawa Armad shafi na huɗu.


*

Armad Wilbafos


Martaba: haifaffen 'ɗa', jinin tawaye; zuri'ar marigayi Aldaima.


Laifi: 1) Cin mutuncin sarakunan jinzidal. 2) Kawo cikas ga cinikin bayi 3) Rashin girmama manya. 3) Horar da maƙiyan manya a fannin izza. 4) Alaƙa da Hidaya (Baƙar Wuta) 5) Kawo cikas ga rukunin Jinzidal 6) Mallakar Littafin-takobi 7) Kashe Uznu Ururu 8) Keta alfarmar Kurkukun Bango 9) Haɗa kai da baƙaƙen aljanu.10) Karbar Ruhin Tarifil-fakta/haɗa kai da Tarifil-fakta. 

NB: wannan kaɗan ne daga cikin laifukan ka.


Wannan laifuka sun ɓata maka suna da yawa.


Suna: -982

*


Dul'Ururu yaja dogon numfashi gami da shafa gemun sa, ya fuskanci Armad ya ce, "Armad, ka aikata laifuka da dama kamar yadda na lissafa, amma lokacin Kamfen lokacin yafiya ne. Faɗi ra'ayin ka naji, zaka karɓi gaskiya ka goyi bayan manya, ko kuwa zaka bijire ka faɗa cikin ɓatattu kafirai?" 


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...