Skip to main content

323-328

 Garin Sarki Iluru - Seerish

Unguwar Daif 

Teburin mai shayi


***


Koda yake zai yi wuya a kira wajen cinikin Salmanu da teburi domin kuwa tuni wajen ya daɗe da ƙasaita ya zama shago, shago kuma ya zama wajen cin abinci. A halin yanzu akwai ƙaton ɗaki da kuma kujeru inda kwastoma suke zama suna cin abinci sannan suyi hira, musamman ma hira.


A unguwar Daif babu wani waje dake tara magidanta (maza da mata) irin wannan wajen. Zaka iya cewa duk wata gulma da ƙananun zantuka na unguwar dama na sauran gurare a faɗin duniya akan tattaunasu a wajen. 


Salman yayi ƙasa da murya cikin raɗa ya ce, "kun san asalin sunanta?" 


Wasu mutun uku dake kusa da teburin da Salmanu yake kai suka matsa kusa domin jin abinda zai ce. Suma ragowar mutun goma sha ɗin dake cikin ɗakin zubo kunne sukayi suna sauraro. 


"Mulkiyya sunanta - ƴa ce a wajen sarki ƙaraiƙisu, babban sarkin ikwatora." Inji Salmanu.


Wani daga cikin su yayi farat ya amsa da cewa, "Amma da gaske ne an saka ranar daurin auren?" 


"Eh mana," inji Salmanu, "ana gama kamfen za'a ɗaurashi a sashin ikwatora. Ai yarima Bizaya ya caɓa, naji ance kyakkyawa ce ta gasken gaske kamar gimbiya Zahra, kuma gata ƴar sarki. Gata tafa-tafe shima zai iya zama sarkin ikwatora."


A dai-dai wannan lokaci ɗaya daga  cikin masu sauraron wannan  tattaunawa daga baya ya leƙa ya tsoma baki, "wai ba ance sarki ƙaraiƙisu basamude bane, to idan ƴarsa ma basamudiyace yaya za'ai aurensu ya yiwu da yarima Bizaya wanda mutun ne?"


Nan take kowa ya zubowa wannan mai maganar idanu akai shiru tsahon dakiku ana kallon sa.


"Waye ya gaya maka sarki ƙaraiƙisu basamude ne? Ai babu sauran samudawa a wannan zamani banda sarki Iluru da shugaba Deniz Ururu." Inji Salmanu. 


Mutumin da yayi maganar ya girgiza kai, "a'a fa. Ni dai wani ya gayamin akwai samudawa a sashin ikwatora. Kuma shi ya taɓa zuwa shi yasa ma na yadda."


Salmanu ya ture kofin shayin dake gefen sa a fusace, har wani ma ace an fishi sanin gulmar gidan sarki a unguwar Daif, bazai yiwu ba. "Kwastoma, ya sunan ka?" Inji Salmanu cikin ɓacin rai.


"Suna na Cokali." 


Nan take mutanen wajen suka fara yamutse fuska. Cokali kuma? Wannan wanne irin suna ne?


To amma a lokaci guda shi Salmanu ba sunan ne ya dame shi ba. Babban abinda yafi damunsa shi ne zancen gulma. Tayaya za'ace yana mai shayi har wata gulma tazo wadda bai sani ba. 


"To bari kaji, Cokali, duk duniya babu wanda ya shiga sashin ikwatora tun bayan yaƙin duwatsu shekaru dubu da suka wuce. A sanda al'ummar sama suka haɗa hannu da ƙarfe dana ƙasa suka kashe marigayi babban sarki Deniz Huhutu. Ance ruhinsa shi ne ya shige sashin ikwatora kuma ya rufe sashin. To tun a wannan lokaci babu wanda ya ƙara shiga sashin ikwatora, ko mace ko namiji, ko babba ko yaro. Idan ma akwai samudawa to bamu san dasu ba, kuma tunda bamu san dasu ba to duk wanda ya faɗa maka ba tare da wata hujja ba to ƙarya yake."


To fa!


Cokali ya ƙara girgiza kai, "naji, to amma ba ƙarya nake ba, nasan yanzun nan sai kuce ni makaryaci ne." Ya juya dubi na kusa dashi, "Inara, da ALLAH zaka iya tuna abinda Madugu ya gaya mana akan samudawan sashin ikwatora da sarkin su mai ƙaho a tsakar ka?"


Na kusa dashin mai suna Inara ya gyaɗa kai. "Sosai ma. Bashi ne ƙaraiƙisu ba?"


Salmanu ya yamutse fuska ya matsa kusa ya fuskanci Cokali, "to ai sai ku kawo mana shi wannan Madugun da yake ikirarin ya shiga sashin ikwatora mu gani indai ba ƙarya kuke ba." Koda ya fadi wannan sai ya ɗauke kai ya rabu dasu inda yaci gaba da bayar da labaransa. 


"Wai kunsan sashi ɗari da uku ne a yankin ikwatora?" Inji Salmanu, fuskarsa cike da jinjinar ban girma, kana gani kasan ya yadda da labarin da yake bayarwa. "Maimakon sashi bakwai da ƙasashen ƙasa suke dashi sashi ɗari da uku ne a yankin ikwatora, garuruwa dubu, sarakuna dubu, deba dubu...."


Cokali ya kasa daurewa ya tari numfashinsa, "kaiii, gizo, waya gaya maka?!" 


Salmanu ya harari Cokali. Bai taɓa samun banzayen kwastomomi irin wannan mutanen ba. Ace mutun bazai tsaya tsam ya saurari labari ba saiya tanka. 


"Dama ai kun gama shan shayin ku, ku tashi ku fice." Inji Salmanu. Koda Cokali yayi jinkiri sai Salmanu ya daka masa tsawa, "ku tashi ku fice min nace."


Dolen Cokali da Inara suka kaɗe rigarsu suka fice. Jim kaɗan wasu mutun biyu suka mike suka bi bayansu. Bayan ɗan lokaci wasu mutun biyun masu sanye da babbar riga da rawani suka bi bayansu. Wannan mutun huɗu na fita suka sha kwana suka haɗu da Cokali da Inara suna jiransu a wajen. Idan ka lura sosai zaka ga masu rawanin da babbar rigar mata ne: Nusi da Nostaljiya. Sai kuma namiji ɗaya mai sanye da hirami ya rufe fuskarsa wanda idan ka lura zaka ga ba wani bane illa Armad. Shi kuma na ƙarshen Lamarudu ne wanda shi dama fuskarsa a buɗe take tunda babu wanda ya sanshi. 


"Wato dai babu wani labarin yaki acikin garin nan. Kowa harkar gabansa yake." Inji Armad. Dama dai wannan fitowa ce ta zaga gari wadda suka shirya ba tare da sanin mutanen fadar Iluru ba. Yawancin mutanen garin babu zancen da suke sai zancen auren Bizaya da wannan mace mai suna Mulkiyya ƙaraiƙisu. Abin mamaki shi ne kwata-kwata babu zancen auren acikin fadar ko kaɗan. Ko a ina mutanen garin suka samo wannan labarin? 


Nostaljiya ta numfasa ta ce, "ina ganin ya kamata mu koma kafin wani ya ankara bama nan."


Lamarudu yayi ɗan tsaki. Dama dai ya gaji da zancen karairayin da mutanen garin suke ta yaɗawa akan sashin ikwatora. Ga dukkan alamu babu wanda ya taɓa zuwa ikwatora acikin su sai ƙarya. Wai sashi ɗari da uku, garuruwa dubu, sarakuna dubu da deba dubu.


Armad ya dubi Nusi. "To, Nusi, kin shirya?" 


Ta gyaɗa kai alamun eh, amma bata ce komai ba. 


Gabda zai ƙaddamar da Aiban'shisu sai Cokali ya ɗaga masa hannu. "Ɗan tsaya, Armad. Wai waye ya taɓa min Nusi?"


Nostaljiya wadda ta fuskanci abinda ke faruwa matsawa kusa tayi ta ɗora hannu kan kafaɗar Nusi ta gyaɗa mata kai. Nusi tayi murmushi. A zahiri duk dakika daya data wuce ƙara samun yaƙini take yi a ranta cewa ba Armad bane a gabanta ba. A halin yanzu kawai Nostaljiya take jira kafin ta afka masa da sara da suka.


A dai-dai wannan lokaci Armad ya matsa kusa ya kalleta da wasa ya ce, "ko baki da lafiya?"


Ta kaɗa kai. "Ina jin dai haka."


"Hmm.. to mu koma mu nemi magani." 


"Aiban'shisu!"


***


Bayan sun dawo fada kowa ya wuce ɗakinsa. Jim kaɗan da dawowarsu Armad ya tafi wajen Nusi. Yana shiga ɗakin ya tarar da Nusi a kwance kan gado tayi rigingine tana kallon sama. Duk da taji shigowarsa amma bata ɗago ta kalle shi ba. Haka ya tsaya a ƙofar tsahon dakiku kafin daga bisani ya rufe kofar.


Kai tsaye ya wuce kan gadon da take. Yana zuwa bai zame ko'ina ba sai gefen inda take kwance inda shima ya kwata. Yayi shiru yana jira yaji ko zata yi magana amma bata ce komai ba, hasalima ko motsi batai ba. Bayan ɗan lokaci ya gaji da jira ya numfasa ya ce, "wai ke saboda nace zan aure ki shi ne kike rashin lafiya?" 


A lokacin Nusi ta buɗe baki zata gaya masa ba shi ne Armad ba kuma ya dawo mata da Armad ɗin ta, to amma ta fasa. Badan komai ba saboda sun riga sun yanke shawara da Nostaljiya zata duba ƙwaƙwalwarsa to gwanda ta barta ta ƙarasa aikin ta. Watakila tana gaya masa zai ankare ya kuma hana Nostaljiya duba shi, ko kuma yayi wa tunaninsa wani abu dazai hana su gane gaskiya. 


"Ba komai. Kawai dai bani jin dadi ne." 


"Hmm.." Armad ya hura iska alamun rashin amincewa, "harma ace ma'abociyar izza kamar ki tana rashin lafiya. Juyo mu gani, idan ma gaskiya ne izzar ki zata nuna."


"Armad, bana son magana sosai yanzu, ko zaka tafi ka dawo muyi magana in anjima."


Armad najin haka yayi shiru na yan dakiku kafin ya mike ya fice daga ɗakin. Ya rufe ƙofar kenan ya juya zai tafi sai sukai arba da Nostaljiya a tsaya a bakin ƙofar dakinta tana kallonsa daga nesa.


Suna haɗa ido ta ɓata rai sannan ta juya ta shige dakinta. Ganin bata rufe ƙofa ba ya ingiza Armad yabi bayanta. 


Yana shiga ya rufe ƙofar. Kafin ma ya samu nutsuwa yaga Nostaljiya a gabansa. 


"Wai meye tsakaninka da Nusi? Kada ma ka ɓoye min wani abu indai ba so kake rai na yayi mummunan ɓaci ba. Naga yadda take kallonka, kuma kai ma naga yadda kake kallonta. Kuma tabbas wani abu ya faru a tsakaninku idan ba haka baza ta ringa ganinka tana ɓata rai ba. Sabida haka kawai ka gayamin meye yake faruwa." Inji Nostaljiya tana huci.


Armad ya dube ta ya ɗan yamutse fuska, sannan kai tsaye ya ce, "cewa nayi zan aure ta."


Nostaljiya ta wage baki ta zare ido, "me kace?"


"Yadda kika ji. Nace mata zan aure ta shi ne duk take wannan abubuwan."


Nan take wasu tunane-tunane suka fara yawo a ƙwaƙwalwar Nostaljiya. Na farko dai tasan Nusi tana son Armad, so na hakika. Kuma tabbas Nusi zata yi murna idan Armad ya ce yana sonta zai aure ta. Hasalima babu wani dalili da zai sa Nusi taƙi amincewa domin babu sarkin da baya iya auren mace biyu ko uku ko huɗu. Watakila wannan ita ce kaɗai damarta ta auren Armad to amma kuma duk da haka Nusi tana ganin ba Armad bane. Sabida haka dole ne akwai wani dalili da yasa Nusi tayi wannan ikirarin duk kuwa da cewa har yanzu Nostaljiya bata ga wani baƙon abu a tattare da Armad ba. 


Nan take Nostaljiya ta yanke shawarar shiga tunanin Armad domin ta duba halin da ake ciki. Shin Nusi gaskiya ta faɗa ko kuma shaci-fadi ne kawai?


Nostaljiya ta haɗe rai tayi kucin-kucin da fuska. "Nusin zaka aura? Kuma sabida rashin kyautawa ko gayamin bakai ba? Wannan ai cin amana ne. To wallahi ban yadda ba." 


Tana magana tana huci, bata ma saurari amsa ba ta wuce ƙofar ɗakin zata fita. 


"Bada yawuna ba. Indai zaka aureta to sai dai ka sakeni."


Armad yayi ajiyar zuciya. Dama yasan za'ai haka shi yasa bai gayamata ba. 


Yayi sauri ya riƙo ta. "Tsaya-tsaya, ai duk abin bai kai haka ba. Yanzu mai kike so ayi?"


"Kafi kowa sanin mai nake so. Idan banda wulakanci to ka bari na haihu mana tukunna. Kuma kawai sai ka fara wani lissafin ƙara aure bayan kana cikin wannan hali. Ka bari a gama yaƙin ruhi ka kuma gama da Kuyurussa'ayi. Daga baya ko ɗari kake so sai ka aura."


Armad yayi shiru yana kallonta. Itama Nostaljiya ƙugu ta kama tana kallonsa ido cikin ido, babu abinda ke tashi daga jikinta sai kumfar kishi. 


Daga ƙarshe Armad ya buɗe baki ya ce, "to na fasa. Ita ma Nusin dama bata so." 


Nostaljiya ta cuno baki, "au, ka fasa ne sabida bata so, bawai dan saboda ni bana so ba?"


"A'a, ba haka bane. Tsaya kiji..."


"Ba wani nan. Kawai..."


Armad ya ɗora hannunsa akan leɓenta ya rufe mata baki. Maimakon ta saduda sai kawai takai masa cizo a hannu. Ai kuwa ALLAH ya bata sa'a ta damƙi tsokar hannunsa ta gatsa.


"Aaarghh..." Armad yayi ihu. "Kika cije Ni?"


"An ciza ɗin. Bakai bane kaje kace kana son wata macen banda ni? Akwai abinda bani dashi." 


Armad ya girgiza kai kamar yayi kuka saboda ya rasa yadda zaiyi da kansa.


"Ko zaka rama?" Inji ta.


Armad yayi murmushin yaƙe. Maimakon ya rama kawai sai ya janyota jikinsa ya rungume ta. A dai-dai wannan lokaci da Nostaljiya taji Armad ya saki jikinsa sai tayi sauri ta cilla fasaharta ta gogi saman tunanin sa. Amma nan take ta janye domin har yanzu yana cikin hayyacinsa kuma tana matsawa zai ji ta. A takaice dai ƙananun mu'amaloli na aure baza suyi aiki ba. 


Nostaljiya ta rufe idonta ta ƙara kwantawa a jikinsa. Ƙanshin jikinsa da yadda yake motsa jikinsa a nata duk iri ɗaya ne sak dana Armad. Kai hatta yadda ya ɗora hannunsa a jikinta da yadda yake kallonta duk irin na Armad ne. 


Ta tsaya cak tana jira taga mai zaiyi. Shi kuwa Armad kawai sai ya tsaya yana kallonta tsahon dakiku. Bayan ɗan lokaci tayi murmushi ta jashi kan gadon ɗakin. Wato shi kansa wannan samfurin Armad ne. A har kullum idan Armad yazo wajenta ita ce da kanta take jansa kan gadonta idan har tana son ayi mu'amala ta aure kenan. Armad yana da wani irin hali na rashin kulawa da irin wannan abubuwa. Yakan daɗe suna tare amma hankalinsa yana wani wajen, bawai dan baya sonta ba, a'a, sabida kawai abubuwa sunyi masa yawa a kansa. Duk waɗannan halaye dama wasunsu Nostaljiya take son gwadawa domin ta ganewa idanunta dawa take tare. Lallai kamar yadda Nusi ta faɗa wannan ita ce kaɗai hanyar da zasu tabbatar waye shi.


Idan ma Ayubu kwafin Armad ne, kowannensu tunaninsa daban. Kuma babu abinda Ayubu ya sani game da abubuwan dake cikin kwakwalwar Armad sai wanda Armad ɗin ya gaya masa. Kuma duk duniya babu wanda yasan yadda Armad da Nostaljiya suke mu'amalarsu ta aure sai su biyun kacal. Daɗin daɗawa idan muka duba cewa har yanzu bamu yi tsinkaye da mai ƙarfin fasahar tunani kamar Nostaljiya Nára ba a dukkan fadin duniyar kasa bakwai, sannan kuma shima Armad babu wanda zai iya shiga tunaninsa ta sauki. Sabida haka zaiyi wuya ace wani ya shiga tunaninsu yaga yadda suke mu'amalarsu ba tare da sun sani ba. Idan wannan mutumin dake gabanta ba Armad bane, to tayaya yasan wannan sirrika?


Bayan ɗan lokaci a tsaye sai ta jashi kan gado. Daga nan mu'amala ta gudana kamar yadda Armad da Nostaljiya suka saba a sha'anin auren su. A ɗan tsakanin Nostaljiya ta samu dama ta shiga tunaninsa a lokacin da hankalinsa gushe. 


*** 


Washegari da safe Nusi ce ta fara hallara a ƙofar ɗakinta sanye da kayan yaƙi. Muzurai kawai take tana huci kamar tsohuwar zakanya. 


Tana zaune Inara da Lamarudu da Cokali suka zo wajen. Kowa yaga kayan da tasa sai yayi turis. 


Riga ce ƙarama mara faɗi da wando na saƙi wanda ya kai mata har idon sahu. Sai kuma kambun tsafi a kanta, da kuma tukunyar magani a saman kambun. Riga da wandon kaɗai da tasa ya isa ya nuna faɗa ta fito, to amma idan ka haɗa da muzuran da take da kambun tsafin, da kuma tukunyar maganin sai kaga lallai yau ba sauki. 


Nusi bata ce musu komai ba kawai Muzurai take. Cokali ne yayi ta maza ya matsa kusa da ita ya tambaye ta cikin murya kasa-kasa, "meye matsalar ne?"


Cikin murya mai karfi yadda kowa zai ji ta ce, "yau ne fa alƙawarin kwana biyun da Iluru yayi mana zai cika. Idan bai zo ba to lallai yaudare ce, kuma ya kamata mu fice daga wannan daula cikin hanzari kafin wankin hula ya kaimu dare."


Cokali, Inara da Lamarudu suka gyaɗa kai alamun amincewa. Suma sun yadda da haka, to amma duk da haka basu san meye yasa take ta muzurai ba.


Ba jimawa Armad ya buɗe kofar ɗakin Nostaljiya ya fito. Ita ma Nostaljiya tana kwance a kafaɗarsa ta dama suna tafiya ɗai-ɗai kamar sabbin masoya. Kallo ɗaya tak Nusi ta yiwa Nostaljiya taga amsar ta. Ko kaɗan bata buƙatar ta tambayi Nostaljiya amsar sakamakon data samu na duba ƙwaƙwalwar Armad domin tasan amsar da zata bata. 


Suna ƙarasowa suka zubawa Nusi ido.


"Ikon ALLAH sai kallo." Inji Armad. "Nusi lafiya?"


"Lafiyar ce haka. Idan soyayya tasa kun manta to ni zan tuno muku - nan acikin gidan makiya muke. Idan zaku farka ku farka tun kafin lokaci ya ƙure mana. Dole akwai wata matsala a wajen nan. Kwatsam Iluru ya kawo zancen sace mahaifiyarka, sannan kuma kwatsam ya gudu yau kwana biyu babu shi babu alamarsa, bayan cewa awa uku yace zai yi. Sai dai kuyi haƙuri da soyayyar amma dole yau kowa zai tattara kayansa mu bar gidan nan, ko Iluru ya dawo ko bai dawo ba." Tana bayani tana huci.


Nostaljiya ta dubeta ta ce, "wai yaushe kika zama Armad ne? Domin ni dai a iyakacin sani na Armad ne shugaban tafiyar nan kuma shi yake bada umarni. Idan yace zama za'ai to zama za'ai. Hakama idan yace tafiya za'ai." Ta juya wajen su Inara, "ko yaya kuka ce?" 


Sun buɗe baki zasu bada Armad ya taresu ta hanyar ɗaga musu hannu. "Akwai abinda Nusi ta gano tunda kuka ga ta tashi hankalin ta. Kuma na aminta da shawararta, indai har Iluru bai dawo yau ba to lallai zaman mu yazo karshe anan. Kuma.."


"A'a, Armad," Nusi ta katse shi, "ba fa yau-in-anjima nake nufi ba, yau-yanzu-yanzu nake nufi."


Armad ya yamutse fuska. "Nusi..."


"Yanzu-yanzu." Inji Nusi tana nuna ƙasa alamun jaddadawa. 


Waje yayi tsit akai jim ana kallon Armad da Nusi aka yaya zata ƙarke.


Armad yayi ajiyar zuciya ya ce, "Nusi, kada fa ki manta akwai abinda muka zo nema nan, kuma idan bamu samu ba ya zama zuwan banza mukai. Sabida haka ina ganin indai zamu samu, gwanda mu..." 


Yana cikin magana aka katse shi, sai dai a wannan lokaci ba Nusi bace, wani ihu ne mai haɗe da hayaniya daya taso daga cikin fadar. 


Nan take suka kalli juna, sannan suka mike a tare sukai cikin fadar. 


Suna shiga suka hango jama'ar sarki sun taru ana ta magana kasa-kasa. Matan sarki sai rangama kuka da ihu suke. Banda mutanen fada da matan sarki akwai manyan mayaƙa barkatai mataki-mataki a wajen. Kai tsaye Armad da mukarrabansa suka wuce cikin dakin da aka kewaye. 


"Kai, ina zaku?" Mayaƙan suka shiga gabansu. Armad ya ɗaga hannu zai ƙaddamar musu amma a lokacin ƙofar ɗakin ta buɗe. Bizaya ya leko ya gyaɗawa mayaƙan kai suka bar su Armad suka wuce. 


Ɗaki ne madaidaici mai ɗauke da gadon sarauta da shimfidu na alfarma. Babu kowa aciki daga Bizaya sai wani mutum kwance kan gadon. Kallo ɗaya kacal zaka gane mutumin dake kwancen ba wani bane illa sarki Iluru.


Bizaya ya ƙarasa ya zauna a kusa da mahaifinsa sannan ya juyo ya dube su ya ce, "a sume muka ɗakko shi a gaɓar garin Eliya. Bamu san hakikanin mai ya faru ba amma kwatsam muka ga ƙusar ruhinsa dake ajiye anan fadar ta fara duhu, hasken ta yana ɓacewa kamar an kashe fitila. Koda ganin haka sai muka bazama nema. Tun shekaran jiya muke nema sai yanzu muka dawo, shi yasa kwana biyu baku ganni ba."


Armad ya haɗe gira amma kafin yayi magana Nusi tayi tsalle ta dira a bakin gadon tana huci. Kai tsaye ta wuce wajen Iluru domin tayi masa aiki dan taga rainin wayon ya fara yawa. Bizaya ya shiga gabanta. Kai tsaye Nusi ta kai masa damƙa da hannunta na hagu. Nan take wani baƙin hayaki yai fitar burtu daga hannunta ya tunkare shi. Bizaya yai tsalle gefe ya kauce ya bata hanya.


"Wai meye haka ne, Nusi?" Nostaljiya ta daka mata tsawa, "mai kike so kiyi ne?"


Nusi tayi mata banza ta wuce kan gadon. Sauran kiris ta ƙarasa Cokali yayi tsalle ya dira a gabanta. "Tsaya-tsaya, yar'uwa, yimin bayani mai yake faruwa? Kin san dai taɓa Iluru acikin fadarsa ba abu ne da zai haifar da ɗa mai ido ba."


"Cokali, ka matsa baya babu ruwanka acikin abin nan." Ta ture shi gefe da ɗayan hannunta. 


Saura ɗan'taƙi Nusi ta isa gaban Iluru ta miƙa hannu ta janyo tukunyar tsafin dake saman kanta. Sannan ta fara dakan magani, amma fa na tsafi. Abin mamakin shi ne babu komai acikin tukunyar a lokacin data fara dakan amma tana farawa cikin ƴan dakiku sai hayaki ya fara tashi haɗe da ƙanshin magani. Kai tsaye tayi tsalle ta afka kan Iluru wanda ke kwance a sume. 


Tana gab da aika Iluru lahira wasu mutun huɗu suka bayyana a tsakanin ta dashi. Ɗaya daga cikin su ba wani bane illa Deniz kalhari, babban hadimin sarki Iluru. Su kuwa mutun ukun duk baƙi ne, kuma ba wasu bane illa salsan Iluru. 


Ba tare da tambaya ba suka zare makamansu suka afka mata. Biyu daga cikin su takubba suke amfani da su. Kalhari kuma fafalo ne. Sai kuma na ƙarshen yana ɗauke da ƙusar yaƙi ta mairakana. Biyun farko suka zagaya ta bayanta suka kawo mata hari ta inda bata gani. Shi kuma Kalhari da ɗayan suka afka mata ta gefe da gefe. 


"Kaaii!" Armad ya daka musu tsawa, "ko ku tsaya ko ku fuskanci hukunci."


Nan take suka ɗan tsaya suna kallon juna. Bayan ƴan dakiku suka yanke shawarar su gama da Nusi domin lallai ba zasu lamunci cin mutunci har gida ba. Shi kuwa Armad miƙa hannu yayi kan iska. Haka na faruwa kawai sai aka ga sun tsaya cak suna dube-dube cikin al'ajabi da mamaki. 


"Ina izza ta?"


"Ina izza ta?"


Wannan kawai shi ne abinda yake fita daga bakin su. Domin sun nemi izzar su sun rasa. 


Armad ko kula su baiyi ba ya wuce wajen Nusi ya kwace tukunyar dake hannunta sannan ya tasa keyarta suka fice. Amma fa duk da haka Nusi huci kawai take. Su Nostaljiya suka bi bayansu. Kai tsaye Armad yai cilli dasu can wajen fadar cikin otal ɗin da suka fara zama. 


A halin yanzu kowa yana tsaye ana kallon-kallo. Nusi tana ta kai-komo a ɗakin, su kuma suna kallonta. Zaka iya cewa babu wanda yasan dalilin da yasa Nusi take ta huci kamar zata ci babu, watakila sai Nostaljiya. Kuma a wannan lokaci dole ne suma sauran ayi musu bayani domin abinda ta aikata kwata-kwata baya cikin abinda suka tsara zasu yi. Yanzu gashi tasa dole sai da suka fito daga cikin fadar. 


"Wai meye ne?" Inji Cokali.


"Kiyi mana bayanin mai yake faruwa." Inji Nostaljiya.


Inara da Lamarudu tunda har yanzu suna matuƙar ganin girman Nusi basu ce komai ba, amma kana ganin idon su kasan suna matuƙar son jin dalilin da yasa Nusi tayi abinda tayi. Kasancewar ita Nusin ba mai rigima bace. A wasu lokutan ma ita ce take hanawa ayi kisa ko kuma a tada hatsaniya, to amma yau ita ce kan gaba wajen aikata haka. Kaga dole kowa yayi tambaya.


"Ku rabu da ita da wannan tambayoyin. Ni nasan duk abinda yar'uwata zata yi da dalili, kuma ko bata gayamana a yanzu ba zata gaya mana nan gaba." Inji Armad, "abinda ya kamata ku tambaya shi ne: a yanzu wane mataki zamu ɗauka tunda Iluru ya dawo a sume kuma bamu san sanda zai farka ba, sannan kuma gashi yanzu sun zama abokan gabar mu. Wanne mataki zamu ɗauka?" Armad ya mike daga gefen gadon ya taka wajen da Nusi ke tsaye. Yana zuwa ya miƙa hannu zai dafa kafaɗar ta, amma cikin tsananin zafin nama ta kauce sannan ta taɗe shi yayi taga-taga zai fadi. Kafin ya ankare tasa kambun dake saman kanta ta ture shi zuwa ƙasa. Kai tsaye ta hau ruwan cikinsa ta fara naushin fuskarsa da hannu biyu.


Nostaljiya, Cokali, Inara da Lamarudu suka rankaya domin su raba. Zaka iya cewa abin ya wuce hankali. A halin yanzu dukkansu sun tabbatar akwai wani taɓin hankali a ƙwaƙwalwar Nusi. 


Gab da zasu isa kanta ta juya ta hararesu, ta ce, "ku tsaya nayi muku bayani. Wannan mutumin ba Armad bane. Ayubu ne ya haɗa baki da Iluru suka sace Armad sannan suke neman yaudarar mu." Ta juyo wajen Armad wanda ke kwance ƙasa tana huci ta ce, "kai, Ayubu, ka gayamana ina Armad yake tun muna shaida juna."


Ba shiri suka tsaya cak baki a buɗe suna kallon ikon ALLAH. Lallai idan ka ɗauke Nostaljiya babu wanda acikinsu ko a mafarki ya taɓa tunanin jin wannan magana daga Nusi. Yaya za'ayi ace wai an sace Armad basu sani ba kamar wata yar'tsana? Kuma wai Ayubu wanda mutun-mutumin Armad ne wai dashi aka haɗa baki. Suka kalli Armad wanda ke ƙasa a kwance fuska luhu-luhu, sannan suka kalli Nusi wadda ke ruwa cikin sa hannu a dunkule tana huci. 


A wannan lokaci kowa kasa magana yayi. Can bayan ɗan lokaci, Nostaljiya ta shige gaba ta tsaya a gaban Nusi. "To ɗaga shi sai muyi magana a nutse."


Nusi tayi farat a fusace ta ce, "wallahi bazan ɗaga shi ba."


Nostaljiya ta yamutse fuska ta ce, "to idan kika fasa masa wani abu aciki fa?"


Nusi tayi shiru tana muzurai.


Bayan ɗan lokaci suna kallon-kallo Nostaljiya ta tabbatar Nusi baza ta ɗagashi ba sai ta juyo ta fara yiwa su Cokali bayani domin su zama alkalai su yanke shawara. 


"Kwana uku da suka wuce Nusi ta same ni ta gayamin wai an sace Armad, wai kuma wannan da muke tare dashi Ayubu ne ba Armad ba. Ta nemi dana duba tunaninsa domin na tabbatar. Duk da nasan maganar bata da tushe banyi musu ba. Dole nabi yadda tace na duba tunaninsa, kuma na tabbatar Armad ne ba Ayubu ba. Amma duk da haka Nusi taƙi yadda. Gashi yanzu ta jiƙa mana aiki da denizawa, ta kuma ɓata mana shiri. Sannan kuma uwa-uba ta karya darajar sarautar Wilbafos. Ku duba kuga yadda ta hau ruwan cikinsa, yanzu idan kika fasa masa wani abu a ciki fa?"


Kafin kowa ya bada amsa Armad ya fashe da dariya. "Haha... wai dama abinda yake faruwa kenan?" Ya dubi Nusi ya ce, "wai ke tunani kike yi an sace ni? Hahaha... Lallai kin iya ban dariya. Hahaha..."


Nan take kowa a wajen ya fashe da dariya. Lallai abin dariya ne ace wai an sace Armad. Kamar fa ace an sace Bihanzin ko Ikenga ne. 


Bayan ɗan lokaci jikin nusi yayi sanyi. Dole ta ɗaga ruwan cikin Armad ta koma gefe ta tsaya. Armad har yanzu yana kwance a ƙasa yana kallon ta. 


Can bayan ƴan dakiku kamar komai ya lafa sai Nusi ta ƙara zabura tayi wajen Cokali ta cafi wuyansa. "Cokali, kasan ni, kuma kasan ni ba makaryaciya bace. Lallai kasan na saba faɗar gaskiya tun muna yara." Ta juya ta nuna Armad wanda ke kwance a ƙasa ta ce, "yanzu idan nace maka wannan ba Armad bane mai yasa baza ka yadda ba?"


Cokali yayi shiru yana jimamin maganar. Ya kalli Armad, sannan ya kalle ta. Tabbas Nusi ta aminta cewa mutumin da suke tare dashi ba Armad bane. To amma kuma babu wata hujja. Dama ace tayi masa maganar tun farko daya bata shawara sunbi abin a hankali, to amma a halin yanzu komai ya wargatse. Zaka iya cewa idan ma ba Armad ɗin bane to yanzu bazai taɓa bari a gano shi ba. Gashi kuma ta wargatsa alaƙarsu da denizawa. 


"Nusi, abinda ya kamata..."


Nusi tayi farat ta katse shi. "Kaga, Cokali, kawai ka bani amsa bana son wani dogon jawabi. Ka yadda wannan Armad ne ko kuma baka yadda ba."


A zahiri da baɗini Cokali bai yadda ba, kuma fuskarsa ta nuna hakan. To amma akwai abinda ake kira da yan'uwantaka. A tsarin Cokali, ko ba'a kan dai-dai ɗan'uwansa yake ba dole ne ya shigar masa. Sabida haka ya ɓata rai ya nuna Armad. "Ƙarya kake Armad ɗin ƙarya. Kai ba Armad ɗin da muka sani ba bane."


Nusi ta ɗanyi murmushi tana ji a ranta lallai abokan tafiyarta sun fara fahimtar gaskiya suma. Kai tsaye ta wuce wajen Inara. 


"Inara, ka yadda wannan Armad ɗin ƙarya ne ko kuma ka aminta na gaskiya ne?"


Inara ya kalli Armad, ya kalli Nostaljiya, sannan ya kalleta. Bayan doguwar ajiyar zuciya ya ce, "Nusi, wannan Armad ne a iyakacin ilmi na, kuma mubaya'ata tana gare shi."


Nusi ta wuce gaba wajen Lamarudu. "Lamad, ina mai rantse maka da kololuwar rantsuwata wannan ba Armad bane. Ka haɗa kai dani mu murkushe shi ya fito mana da Armad ɗin gaskiyar."


Lamarudu ya girgiza kai. "A gaskiya ni ina da babban dalili da zai sa nayi imani da Armad. Indai ba gani nayi ya bayyana a fili cewa bashi bane to lallai ina tare dashi, ko a duniya ko a kiyama."


Nusi tayi shiru tana kallon ƙasa. Bayan ƴan dakiku ta juya a fusace ta nufi hanyar fita daga dakin. Cokali ya bi bayanta. 


Sai a wannan lokaci Armad ya tashi zaune ya dubi Nusi amma bai ce komai ba. Ita ma Nostaljiya kawai binta tayi da kallo. Su kuwa Inara da Lamarudu sunkui da kai ƙasa sukai suna jimami. Babu wanda acikin su ya taɓa tunanin abubuwan zasu kacame haka da wuri.


***


Awa ɗaya bayan wannan al'amari, a can wani ɗan sihirtaccen fili dake bayan gari, Nusi da Cokali ne suka bayyana. Tun daga nesa kana iya hango ramuka irin na sihiri wanda ke ɗaukar mutane daga ƙarƙashin ƙasa su kai su sama, ko kuma su ɗakko mutane daga sama su kawo su ƙarƙashin ƙasa. Kai tsaye su Nusi suka wuce wajen masu siyar da dutsen izzar da ake amfani dashi wajen fita. 


Cokali ya tambayesu, "nawa kuɗin fita?" 


"Ayrid ɗari da hamsin." Inji ma'aikatan.


Ba musu suka biya. Daga nan aka haɗasu da wani ya kaisu wajen rami na 76 - wanda shi ne ramin daya kamata su shiga. Sai dai kuma suna gab da shiga su Armad da Nostaljiya da Inara da Lamarudu suka zo.


Armad ya shige gaba da sauri ya fara roƙon Nusi data zauna kada ta tafi. "Kece fa yayata wadda muka haɗu tun shekarar dana fito daga gida. Kina yiwa ALLAH ki tsaya mu tattauna. Wai meye yayi zafi ne?"


Nostaljiya ta ɗora da cewa, "nima nasan bamu yi miki adalci ba sosai tunda bamu tsaya mun barki kinyi bayanin kanki ba, to amma duk wannan bai isa yasa ki guje mu ba."


"Yaya Nusi..."


"Yaya Nusi..."


Nusi ta ɗaga kai ta kallesu tsahon lokaci. Ganin kwalla a idanun Armad tasa jikinta ya fara yin sanyi, to amma ba jimawa ta girgije ta ware. Sannan ba tare da ɓata lokaci ba ta faɗa cikin ramin. Cokali yabi bayanta.


***


Ɓangaren Sarkin-sarki da Ikenga


***


Idanun Ikenga na kan Sarkin-sarki. Baki a taɓe ya dube ta ya ce, "SARKIN-SARKI?!"


Sarkin-sarki ta yamutse fuska da baki da gira. "IKENGA, UBAN ME KAKE YI ANAN?!" 


Ikenga ya fara muzurai yana harare-harare. Bayan ɗan lokaci ya dubi Sarkin-sarki ya ce, "nima dai abinda nake son naji kenan. Uban me nake yi anan? Uban me ya faru nazo nan?"


Iliyasis yayi murmushi, zaka iya cewa duk wajen babu wanda zai iya bayanin halin da ake ciki sai shi kaɗai domin ya san fasahar ubangidansa.  


A lokaci guda kuma wata dariyar mugunta ce ta gilma ta gefen bakin Sarkin-sarki. "Hehe.. yau rana tace. Ga yaron Armad, ga Ikenga Bayajidda har ƙofar gida na." Ta juya wajen mazan dake tare da ita, ta ce, "Madaruil'ylud, Ubuil'ylud, Har-n'ylud, ku kama shi. Idan yaƙi tsayawa ku kashe."


Kafin ta rufe baki mazan sun ɓace daga inda suke sun dirar wa Ikenga. Zaiyi wahala a iya bayyana irin saurin da wannan halittu keda shi. To amma bawai iyakacin saurin bane, wata irin takobi ce ta baƙin haske ta bayyana a hannunsu. Sabida kankantar ta zaka iya cewa wuka ce to amma kuma takobi ce. Kafin Ikenga ya ankare sun saka shi a tsakiya, kowa acikin su yana kawo masa suka ta ɓangare guda. Iska ta fara bada amo da ƙugi.


Wato da iyakacin nan abin ya tsaya da da sauki. To amma kafin Ikenga ya ankare inuwar wa'adin deba ta bayyana a saman kowanne ɗaya daga cikin ukun. Nan take wajen yayi duhu kamar magariba aka fara kaɗa gangar izza, sauti na tashi. Zaka iya cewa acikin deba yan kaɗan ne suke shiga wa'adin deba, to amma acikin wa'adin deba wanda suke iya samarda inuwar wa'adin deba basu fi cikin cokali ba. Tabbas wannan mutun uku maɗaukaka ne ko acikin deban Farkon Lokaci.


Ɗaya daga cikinsu ya samarda ƙatoton narkakken dutsen wuta a ɗayan hannunsa marar wuƙar. Ɗayan kuma ƙatotuwar kawanyar walkiya ya samar. Ɗayan kuma al'amudi ne na wuta. Dukkan ukun suka saka Ikenga a tsakiya. Kai kace shikenan bala'in ya tsaya haka, to amma a lokacin suka haɗa baki suka kirawo wani sabon ɗalasimi, "ZAREN LAIDAN!"


Take sama tayi duhu, wasu bakaken zarurruka suka bayyana suka cika sararin sama. Sannan suka fara haɗewa da juna suna yin saƙa suna fitar da gidan gizo-gizo. Kafin kifta ido da bismilla sun haɗe ko'ina. Kallon farko zaka ce irin gidan gizo-gizon zaren izzar Armad ne, sai dai kawai banbancin shi wannan zaren baƙi ne. 


Ba tare da jira ba zaren ya sakko ƙasa ya rufe Ikenga. Duk wannan abubuwa sun afku ne kafin harin da deban nan guda uku suka kaiwa Ikenga ya ƙarasa. Lallai Ikenga na tsaka mai wuya. 


To amma ga dukkan alamu duk da haka hankalin abokan gabar Ikenga bai kwanta ba. Ana cikin haka kawai aka jiyo murya daga cikin garin Shadeniza, "DAUWAMAMMEN SARA!!"


Tabbas muryar Bihanzin ce. Kuma yana rufe baki zabgegen baƙin saran takobi mai ɗauke da hankakan mutuwa ya yiwo sama ya fito daga cikin garin ya tunkaro Ikenga. 


Sarkin-sarki tayi murmushi. Tunda oga yasa hannu ai ita ma dole ta ce wani abu. Nan take ta miƙa kyakkyawan hannunta gaba ta kira ɗalasimi, "ASALIN SANYIN BABBAN SIHIRI!"


Tana rufe baki ƙanƙara tayi tafiya acikin lokaci ta ƙanƙare aniyar Ikenga sannan ta fara cin jikinsa. Watakila a yanzu zaka iya cewa abokan gabar Ikenga sun samu yaƙinin kashe shi, domin kuwa jada baya sukai suka zuba masa ido suga ya zaiyi da hare-haren da suka aika masa. 


Sai dai kuma kash, ba kullum abubuwa suke tafiya kamar yadda aka tsara suba. Ana cikin haka wani mutun ya bayyana akan iska. Yana haye bisa farin alfadari dokin gabas mai fuka-fuki. Yana bayyana ya ɗaga sandarsa ya daki iska da ita. Nan take kura ta turnuke sama. 


Bayan kimanin dakika ashirin komai ya lafa. Deban nan guda uku dake niyyar halaka Ikenga sun koma gefen Sarkin-sarki sun saka ta a tsakiya cikin kariya. Ikenga na can gefe yana haki. Ita kuma Sarkin-sarki idon ta na kan wannan mutun daya bayyana akan alfadari. 


Wannan mutun dai dattijo ne amma murdadden zubinsa yasa yana kama da samari ƴan ashirin talatin. Baƙi ne mai duhun fata kamar Armad. Yana da idanu ruwan ƙasa. A hannunsa na dama akwai wani madaidaicin littafi an saka Alkur'ani-mai-girma a jiki. A hannunsa na hagu kuma sandar tsafi ce wadda yayi amfani da ita yanzu. Idan mai karatu zai tuna a can baya lokacin da za'a siyar da Armad a matsayin bawa mun taɓa ganin wannan mutun bayan Armad ya farkar da idanunsa na Wilbafos.


Sarkin-sarki ta dubeshi ido a zare baki a wangale ta ce, "ALU MAI SANGO?!" 


Alu mai sango ya kalleta yayi murmushi. "Sarkin-sarki. Ina Bihanzin?"


"Uban me kake yi anan?"


Alu najin haka ya ɓata rai. "Bangane ba, bani da damar yawo ne ko kuwa? Idan kina so ki karya alƙawarin da mukayi ne to."


Sarkin-sarki ta cije baki tana huci. 


Alu ya nuna Ikenga. "Ikenga, idan ka yadda zaka yimin aiki to tabbas zan cece ka daga hannun Sarkin-sarki. Idan kuma baka yadda ba shikenan."


Sarkin-sarki tayi tsalle ta tashi sama kan iska ta nufi wajen da Alu yake. "Karyar ka tasha ƙarya, Alu. Kana tunanin zan barka kawai ka ɗauke min abin farauta ta shikenan."


Maimakon Alu ya bata amsa kawai sai ya tafa hannunsa. Nan take wasu mahaya guda ɗari suka bayyana, kowanne akan giwa. "Dama a shirye nazo." Inji Alu.


Sarkin-sarki ta yamutse fuska ta kalli mutanen dake haye kan giwayen kafin ta juya ta kalli ƙofar garin Shadeniza wadda ke kulle, sannan ta kalli Alu amma ta kasa cewa komai.


Koda Alu yaga haka sai ya ƙara juyawa wajen Ikenga. "Ikenga, kana da dakika ashirin ka yanke shawara."


Ikenga baice komai ba kawai murmushi yayi sannan ya kira ɗalasimi na gaba, "SHAIBAL-SHÍSU; ƘARNI NA BIYU!"


Babu wanda yasan ya akai sai kawai gani akai Yurashira ta sauka akan wuyan Sarkin-sarki da wuyan Alu mai Sango. Wato idan amsa suke nema ga tanan ya basu. Gani ya kori ji. 


Abu na ƙarshe da Iliyasis ya gani shi ne feshin jini. A zahiri bai san jinin waye ba, amma dai tabbas yaga jini yayi sama.


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...