Skip to main content

BABI NA 34-39: Armad da Niyashi

 Babi na 34: Armad da Niyashi (1)

***

Acikin wannan filin gasa kuwa, tuni aka kammala duk wasu shirye-shirye da ake buƙata domin fafatawa tsakanin Armad da Niyashi, a wani salo na tantance tsakanin aya da tsakuwa.


A kuma ga wanne acikin su zai isa zagaye na kusa dana ƙarshe.


Dukkanin ƴan kallo, tuni suka fara murna da nishaɗin ganin mai zai faru, da kuma wa zaiyi nasara.


Kusan kowa, sama da mutun dubu ɗari zaka iya cewa idonsu akansu yake, a dai-dai wannan lokaci da alƙalin wasa ya bada umarnin a fara.


Armad na ɓarin arewa, rataye da takobinsa, Shi kuma Niyashi na tsaye a ɓarin kudu, mashinsa na maƙale acikin wani abu mai kama da aljihu da aka ɗinka masa na musamman domin ajiye mashin.


Gashi dai an busa ƙaho, kuma an basu dama su fara fafatawa, amma har zuwa tsahon daƙiƙa talatin babu wanda ya motsa acikinsu, kuma babu wanda yace uffan!


Can daga bisani Niyashi yai ajiyar zuciya a wani yanayi mai kama da tausayawa Armad, ya ce, ''naga kaima kana daga cikin ƙalilan da a zagaye na farko baka kashe kowa ba, saboda haka zan baka dama ɗaya ka fita daga cikin filin nan. Domin kuwa hakan ne kaɗai zaisa ka tsira da ranka. Na baka daƙiƙa biyar.


Bayan ya gama magana sai kawai yai shiru yana kallon Armad. Idanunsa cike da mamakin ko mai yasa Armad bazai yi amfani da wannan dama ba, ya fice daga cikin wajen.


Kasancewar a dukkanin tunaninsa shi ne, Armad bazai taɓa iya jure koda ɗaya tak daga cikin azabar hare-haren jan mashin saba.


Amma ganin Armad yai masa shiru, kuma bashi da niyyar fita daga filin, yasa ransa ya ɓaci. Nan take ya ce, "bana son masu girman kai, saboda haka kada ka zargi kowa sai kanka akan abinda zai biyo bayan girman kanka."


Yana ambata haka ya tafa hannayensa guda biyu inda ya kira sunan ɗalasimin da yake so yai amfani dashi, ''Sayanósis!!"


Koda wannan ɗalasimi ya fita daga bakin Niyashi sai ya dunƙule hannunsa na dama ya fara dukan iskar dake gabansa. A duka na uku ne wata iska mai zafin gaske tamkar wuta, ta kaɗa a dukkanin ilahirin wannan fili. Wannan iska tayi kan Armad ganga-ganga tamkar zata haɗiye shi. Ya ɗaga hannunsa ya ɗan kare fuskarsa, amma ina, wannan iska ta fara ƙoƙarin kaishi ƙas.


Wani mummunan jiri ya fara ɗibansa yana neman kaishi ƙas.


Yai taga-taga ya nufi ƙasa, amma a lokacin ne ya dage ya dasa takobinsa a ƙasa tayadda gwiwowinsa basu je ƙas ba.


Can daga nesa ya ci gaba da jin Niyashi yana bayani cikin girman kai da yadda da kai, "kamar yadda kaji, wannan ɗalasimi sunansa Sayanósis, kuma na ƙabila ta ne kaɗai a duk faɗin duniya.


"Muna amfani da faɗan hannu da akewa laƙabi da 'fiƙar zaki' wajen canja iskar da mutun ke shaƙa!


"Mu tsame kason da jiki ke buƙata, tayadda inma ka shaƙi iskar baza tayi amfani a jikinka ba.


"Ta haka idan babu iskar da jikinka ke buƙata acikin jininka, fatar jikinka zata fara canjawa izuwa koriya ko kuma baƙa, kafin daga bisani ka fara jin jiri, kafin ka suma."


Yana faɗar haka ya juya da niyyar tafiya, yana cewa, "ban san iyakacin lokacinda zaka iya jurewa ba kafin ka faɗi. Amma an riga an kammala wannan faɗan, sai dai ka tara a gaba!!!"

***

Babi na 35&36 : Armad da Niyashi (2)

***

Tsakanin kowanne mutun da aljaninsa akwai wata ƴar rata wadda bata wuce taƙi uku ba. Bayan an haifi kowanne mutun kafin ya girman baya iya ganin aljaninsa sai dai kawai wannan ɗan taƙin dake tsakani.


Acikin wannan ɗan taƙin ake ganin fasahar da aljaninka ke da ita. Yawanci ana fara gani daga shekara biyar zuwa sama. Sannan kuma bayan mutun ya girma ya mallaki hankalin kansa, sai kuma ayi ƙoƙarin haɗa shi da wannan aljani nasa a wani salo mai kama da bautarda wannan aljani. Tayadda wannan mutun zai iya sarrafa sirrin wannan aljanin. Wato dai idan aljanin mai sarrafa wuta ne, shima zai zamo yana iya sarrafa wutar.


Armad tun yana yaro ɗan shekara sha uku, ya fara iya ganin wannan ɗan taƙi dake tsakanin ruhinsa da aljaninsa. Kuma yakanga wajen acike da walƙiya da tsawa da aradu, tamkar ana maka tsawa daga sama. Yana ɗan shekara tara, kakansa da babarsa da Shugaban makarantar da yake koyon harkar Izza aciki, suka haɗa ƙarfi da ƙarfe domin haɗa shi da wannan aljani nasa. 


Akai sa'a aljanin ya amince, kuma Armad ya mallake shi. Tun daga wannan rana Armad ya fara sarrafa tsawa da walƙiya tamkar shima walƙiyar ce. Idan ka hangi Armad walƙiya tana rawa a jikinsa da hannunsa kai kace ɗan aiken mutuwa ne. Lallai mallakar ƙarfin aljanu da sarrafa fasaharsu abu ne wanda yake ƙara daraja da ƙarfi na ma'aboci Izza. Kuma abu ne wanda yake sawa sauran mutane su tsorace shi. 


Abinda kawai Armad yake buƙata shi ne yayi duba izuwa wannan ɗan taƙi dake tsakaninsa da aljaninsa, ya kuma ɗebo walƙiyar dake wajen wadda aljanin nasa ya tara masa. Sannan ya aiwatar da fasaharsa.


Armad yakan yi amfani da walƙiyar sa wajen ƙarawa kansa gudu kamar yadda aka gani a harinsa mai suna 'WASU-WASI', ko kuma yayi amfani da ita kanta walƙiyar domin kaiwa abokin gabarsa harin Aradu.

____

Armad najin duk abinda Niyashi yake faɗa, kuma hasalima duk waɗannan bayanai ALLAH ya taimakeshi ba sababbi bane a wajensa! 


Ba dan komai ba, sai dan cewa daga cikin littattafan daya koya yana yaro akwai mai suna "jiki da Izza" na dafta Hauwas al-kamaini. Wanda babu abinda babu acikin abubuwan da ya faɗa, kai harma da ƙari. Sai dai kuma Armad ba komai yake iya tunowa ba. Amma dai cikin sa'a ya iya tuno abinda zai iya cetarsa daga cikin wannan hali da yake. 


Armad ya dage yai ƙaraji gami da buɗe idanunsa, inda yai taga ya dawo ya tsaya cak da ƙafarsa gami da kafa ido yana kallon Niyashi, wanda ya juyo cikin sauri, fuska cike da mamaki. 


"Eehhhh...." shi ne kawai abinda ya fito daga bakin Niyashi, sannan ya ƙurawa Armad ido yana kallonsa ciki da bai, kamar wanda ke ƙoƙarin karanta wani abu acikin jikin Armad. 


Can bayan wasu ƴan daƙiƙu yayi wani murmushi mai cike da mugunta, gami da cewa, "lallai yaro ba laifi! 


"Watohar zaka iya amfani da Izzar dake jikinka, kana rage yawan iskar da jikinka ke amfani da ita, tayadda duk da baka shaƙar dai-dai adadin iskar da jikin naka ke buƙata, zaka iya jurewa tsahon wani lokaci." 


Ya girgiza kai gami da cewa, "ban taɓa tunanin kamar kai zai samu irin wannan ilmi ba, wanda ko a ƙabila ta abu ne daba kowa ya sani ba. 


"Amma duk da haka ina sane cewa wannan hanyace kawai da zata ƙara maka lokaci, amma a hankali cikin awanni masu zuwa baza ka iya jurewa ba." Ya ƙara girgiza kai yana yatsine fuska. 


"Sai dai kash, bani da wannan lokaci. Saboda hakan bazan iya jiranka ba." 


Yana faɗar haka ya ja baya gami da canja tsayuwa. 


Lamarinda yasa shima Armad wanda ya riga ya dawo dai-dai, ya canja tsayuwarsa. 


Daga can gefe kuma, wannan alƙalin wasa yana kan wajen gabatarwarsa babu abinda yake sai zuzuta abinda ke faruwa tsakanin Armad da Niyashi. 


Amma yana ganin dukkaninsu sun canja tsayuwa ya saki baki gami da cewa, "ga dukkan alamu kowa acikinsu ya maida hankali, bari mu zuba ido, shin yarima Niyashi daga Infiriya ne zai samu nasara, ko kuma wannan saurayi da ba'a san ko wanene ba, mai suna Armad Djinn daga Maikironomada." 


Kafin ma ya ƙarasa rufe baki Niyashi ya nufi Armad da sassarfa. 


Idan ka lura da hannunsa na dama zaka ga cewa wani baƙin haske ne ya bayyana kuma ya keta zagaye hannun. 


Yana isa ga Armad wanda har yanzu bai motsa daga inda yake ba, ya ƙara sauri inda cikin ƙiftawar ido ya kaiwa Armad Sara da hannunsa mai zagaye da wannan baƙin haske ta gefen Armad na hagun. Yana mai kiran sunan wani ɗalasimi, "Kulo-han-Difómiti!" 


Sai dai amma a dai-dai wannan lokacin ne Armad ya ɗaga hannunsa sama, inda wani haske ya fara bayyana yana kewaye hannun. Nan take wannan hasken ya juye izuwa walƙiya mai kama da kama da Aradu. Wannan walƙiya ta rikiɗe izuwa dauƙule-dunƙule har guda uku. 


Dukkanin dunƙule ukun juyawa kawai suke akan hannun saman hannun Armad. Su na ƙaraji suna ƙuwa irin wadda kake ji yayinda ake ruwan sama. Kai kace zasu ci babu.


Armad ya cillo ɗaya daga cikin wannan dunƙulallun walƙiya uku wadda ta taho tana gunji, ta kuma daki baƙin hasken dake zagaye hannun Niyashi. Wata ƙara mai kashe kunne ta tashi. Dukkanin ƴan kallon dake wajen saida suka rufe kunnensu. Kai harda ma idanunsu, domin kuwa hasken daya tashi saida ya kashe wa kowa ido.


Ƙarfin daya tashi daga wannan walƙiya yai cilli da Niyashi gefe. Tamkar an cicciɓeshi sama an watsar. Toda yake shima ba ƙaramin ma'aboci Izza bane, tun kafin ya je ƙasa yasa jan mashinsa ya tare. Inda ya cake shi akan filin wasan, lamarinda ya bashi damar miƙewa ba tare da yaje ƙasa ba. Yai wata katantawa a wani salo na nuna kwarewa, sannan ya kuma ƙara fuskantar Armad yana mai nuna shi da mashinsa. Kai da kaga Niyashi zaka san cewa lallai duk wani wasa ya kau daga idonsa. Kuma lallai yanzu ne za'a fara fafatawar da gaske.A gefe guda kuwa shima Armad tasa takobin ya zare a hannunsa na hagu. Sannan a hannunsa na dama kuma yana riƙe da bala-balan walƙiya guda. Waɗanda suke ta kewaya hannun nasa a wani salo mai ban tsoro.


"Ehmm..." Armad yai ajiyar numfashi gami da haɗe rai, sannan yaci gaba da cewa, "bani da lokacin dazan tsaya ina wasa dakai anan. Watanni kaɗan ne suka rage min nayi abinda duk duniya ta kasa, saboda haka ina baka shawara daka haƙura, ka fitar da kanka daga wannan gasa."


Tun kafin Armad ya rufe bakinsa wani abu yazo wuyan Niyashi ya tsaya saboda tsananin baƙin ciki dake dukan ransa. Lallai babu wanda ya taɓa gaya masa baƙaƙen maganganu irin waɗannan. A matsayinsa na ɗan sarki, jikan sarki. Sannan kuma babban abin takaicin ma shi ne, wanda ke gaya masa wannan baƙaƙen maganganu na raini Izzarsa bata fi hamsin ba. Bayan shi Niyashi yana da kusan ɗari. 


"Da sannu zaka gane kuskurenka!" Wannan shi ne kawai abinda ya fito daga bakin yarima Niyashi yayinda idanuwansa suka kaɗa sukai ja. Baƙin ciki ya cika ruhinsa, sannan kuma yaji babu abinda zaisa ya ƙara yin dariya a ban ƙasa idan bai turmuza hancin Armad a ƙas ba. Nan take yai ƙaraji da ƙuwa, tare da tafa hannayensa a wani salo na kiran ƙarfin dake cikin Izzarsa. 


Nan da nan wata ankwa mai launin ja, wadda akayi ta da zallar azurfa irin ta mutanen farko ta bayyana a saman kansa tana lilo akan iska. Wannan doguwar ankwa ta lanƙwashe izuwa ƙawanya ta kuma kewaye kan Niyashi. Idan da zaka matsa kusa ka kuma ƙirga adadin waɗannan jar azurfar data haɗa wannan ankwa, to da zaka ga cewa guda casa'in da tara ne dai-dai. Kowacce acikin wannan azurfa tana ɗauke da ƙarfin shekara ɗaya na Izza. Wato dai a taƙaice dukkan ƙarfin Niyashi na Izza yana tattare a jikin wannan azurfa. 


Yarima Niyashi ya ƙara tafa hannayensa, lamarinda ya janyo wannan ankwa ta jar azurfa ta rikiɗe izuwa mashi kwaya ɗai-ɗai har casa'in da tara. Kowanne mashi idan ka duba zaka ga irin na hannun Niyashi ne. 


Ba tare da ƙara ɓata lokaci ba, Niyashi ya tafa hannayensa a karo na uku, tare da kiran sunan ɗalasimi, "Láyukúr-mazayà!"


Ya na rufe bakinsa goma daga cikin wannan masu suka fara ci wuta, tare da afkawa kan Armad suna masu burin halaka shi. Lallai waɗannan masu guda goma masu ɗauke da ƙarfin Izzar shekaru goma zasu iya bada komai domin su zubar da jinin Armad. Duk inda suka ratsa sai kaji ƙarar iska da ƙuwa na tashi, tamkar ita kanta iskar tsoronsu take. 


Armad na ganin haka ya ƙara yin duba izuwa wannan ɗan taƙi dake tsakaninsa da aljaninsa, nan da nan ya zuƙo walƙiya guda goma. Wannan walƙiya na bayyana ta kewaye jikinsa tana haske, kafin daga bisani ta rikiɗe izuwa ƙawanyar walƙiya ɗai-ɗai har guda goma.


Armad ya kira ɗalasiminsa, "Hushúsul-baijuru." Yana rufe baki waɗannan ƙawanyu na walƙiya sukai kan wannan masu guda goma. 


Suna haɗuwa wata ƙara mai rikitarwa ta tashi sama, haɗe da wani haske mai kashe ido. Kan kace meye wannan filin fafatawar ya fara girgiza yana neman tarwatsewa. Alƙalin wasa kuwa saida ya durƙusa domin kare idanunsa daga tartsatsin wutar dake tashi. Tamkar ƴan kallo dake nesa saida firgici ya cika zuciyarsu suka fara rirriƙe kujerunsu domin tsoron kada girgiɗin da ƙasar filin wasan keyi tayi cilli dasu.


Bayan kimanin daƙiƙu goma wannan sauti mai kama da girgizar ƙasa ya lafa. Amma maimakon aga Armad da Niyashi a tsaye suna hutawa, dukkaninsu sai suka ƙara ci gaba aikawa juna hare-hare. Armad na ƙoƙarin tarwatsa Niyashi da ƙawanyar walƙiyarsa, shi kuma Niyashi yana ƙoƙarin soke Armad da Jan mashinsa. Babu abinda kake ji sai ƙara mai kama da yaƙin duniya. Kan kace meye wannan tuni anyi musayar sama da hari hamsin a tsakaninsu.


Sai dai kuma fa a wannan lokaci ne gizo ya fara saƙar. Domin kuwa kamar yadda ƙa'idar ƙasa-bakwai ta kasance tun iyaye da kakanni, iyakacin izzarka iyakacin shagalinka; idan kana da Izza hamsin to ƙawanyar walƙiya hamsin kaɗai zaka iya zuƙa daga aljaninka. Hakana idan kana da ɗari kawai ɗari zaka iya amfani dasu. Har sai ka jira kimanin awanni tukunna, bayan ƙarfin ruhinka ya dawo, wanda kuma baza ka samu hakan ba idan ana tsaka da faɗa. Wato dai a taƙaice a wannna lokaci ne adadin walƙiyar da Armad zai iya amfani da ita tazo ƙarshe. A yayinda shi kuwa Niyashi yana nan akan ganiyar ƙarfinsa.


A wannan lokaci Armad ya miƙa hannunsa domin kwance ɗaurin dake gaban goshinsa, sai dai kuma a lokacin ne kwatsam alamarin daya faru da Miyurarsa ya faɗo masa. Shaf ya manta. Tunda farko Armad yayi lissafi da cewa faɗan fito-na-fito zai kai masa, tunda zai iya amfani da tambarin Miyurar ya ƙarawa kansa ƙarfi da yawan Izza. 


To abinka da abinda tunda aka haifeka yana tare dakai, lallai koda Armad ba yaro bane ɗan shekara sha shida ba, zai iya mantawa. Kuma dole sai a hankali zai saba da rashin Miyurar. 


Nan da nan Armad yayi tsalle baya cikin firgici da tunanin maiya kamata yayi, sannan kuma ta yaya ne zai iya cin galaba akan Niyashi wanda yana da kusan ragowar masu guda arba'in a ƙasa.


A ɓangare guda kuwa, koda Niyashi ya gano halin da Armad ke ciki sai yayi wata dariyar mugunta. Tare da cewa, "dama na gaya maka, da sannu zaka gane kuskurenka!" Yana rufe baki ya aikawa da Armad dukkanin ragowar masun dake kewayawa a saman kansa. 


Kai daka gani kasan so yake ya tsire Armad duk a huta. Domin yana ji acikin ransa cewa lallai bazai samu kwanciyar hankali ba idan bai halaka Armad ba a wannan lokaci. Domin kuwa Armad ya gaya masa maganganun da babu wanda ya taɓa gaya masa.


Dukkanin ƴan kallo da alƙalin wasa sun riga sun gama hango Armad a lahira. Domin dai dama sunan Armad baya daga cikin waɗannan sunaye guda shida da ake ta kallo kafin a fara gasar. Sunayen da ake tunanin zasu samu nasara. Shi kuwa Niyashi yana ciki. Sai dai kuma wasu daga cikin ƴan kallon sun soma ɗan sawa Armad kyakkyawan zaton zaiyi abin kirki. Musamman yadda suka ga yana wasa da walƙiya cikin kwanciyar hankali. Amma a wannan lokaci tuni suka cire rai kuma suka ɗebewa Armad haso daga dukkan tsira.


Kai a taƙaice dai shi kansa Armad yana cikin yanayi na kokwanton ko zai rayu. Musamman sanda yaga ratar dake tsakanin ƙirjinsa da waɗannan masu sama da arba'in baifi taku ɗaya ba.

***


Babi na 37 : Motsin Littafin-Takobi


A dai-dai wannan lokaci ne da Armad Wilbafos yake cikin halin ƙaƙa ni kayi, dogayen jajayen masu sama da arba'in masu cike da Izza suna gab da tsire shi. Sannan kuma gashi dukkan Walƙiyar da aljaninsa zai iya bashi ta ƙare, a wannan lokaci na tsanani da matsi, kwatsam sai yaji wani ɗan motsi acikin aljihunsa na ciki. Kafin yayi wani tunani akan wannan motsi da yaji kawai sai yaji wani mummunan raɗaɗi mai zafin gaske a dai-dai wajen da yaji wannan motsi. Kan kace meye wannan raɗaɗin ya juye izuwa raɗaɗin garwashi. Nan take Armad yaji wajen yana soyuwa. Da kyar ya iya tunano cewa a dai-dai wannan wajen da yake jin wannan raɗaɗi wannan littafin-takobin ya ajiye a wajan. Nan take ya fara ƙoƙarin yin cilli da littafin.


Amma kafin yayi wani abu yaji wata irin Izza irin ta mutanen farko ta shiga jikinsa. Bai san lokacin da yayi wani ihu ba saboda zafin da yake damunsa. Kan kace meye wannan Armad yaga ɗan taƙin dake ɗauke da walƙiyarsa ya cika da walƙiya. Bai san daga ina wannan walƙiya take ba, abu dai guda ɗaya daya sani shi ne lallai wannan walƙiya ba irin tasa bace ta da. Domin akwai wani sirri na ƙarfin Izza aciki, wanda Armad bazai iya ganewa ba. Armad ya zuƙo wannan walƙiya daga ruhinsa inda ya fuskanci cewa walƙiyar bata da yawa sosai, kuma zata iya samar da Ƙawanyar walƙiya guda ɗaya ne kawai. Sai dai kuma a jikin wannan walƙiya akwai wasu layika jajaye guda uku suna kewayata. Kai daka gani kasan cewa wannan walƙiya ta musamman ce.


Armad bashi da lokacin tsayawa yayi tunani sosai akan abubuwan dake faruwa saboda haka kawai kai tsaye ya aikawa Niyashi da wannan ƙawanyar walƙiya. 


Dukkanin abubuwan dake faruwa sun ɗau lokaci wajen bayani amma a zahiri sun faru ne cikin abinda bai wuce daƙiƙa biyu ba.


Wata ƙara ce mai kama da girgizar ƙasa ta tashi sama, sannan kuma wani haske ya lulluɓe ko'ina babu abinda ake gani face rugugin tsagewar filin wasan da Armad da Niyashi ke kai. Kan kace meye wannan komai ya tarwatse inda bayan da abubuwa suka lafa aka ga Armad ya bayyana daga cikin wannan rugugi yana mai riƙe da takobinsa a hannun hagu cikin ƙasaita. 


Bisa mamaki shi kuwa yarima Niyashi na kwance a sume. Ko madai mai ya faru tsakanin ƙawanyar walƙiyar Armad guda ɗaya da kuma masun Niyashi sama da arba'in babu wanda ya gani. Saboda haka kowa idanunsa akan Armad suke a kafe, suna fatan ko zai yi musu bayani akan abinda ke faruwa. Amma ina, abinda basu sani ba shi ne shi kansa Armad bai san maike faruwa ba. Domin kawai abinda ya gani shi ne dukkanin waɗannan masu guda arba'in da ɗoriya ɓacewa ɓat sukai a lokacin da suka haɗu da walƙiyar nan guda ɗaya daya tura, tamkar ma basu taɓa faruwa ba. Sannna kuma walƙiyar taje ta daki Niyashi inda ta sumar dashi nan take.


Abu ɗaya da Armad ya sani shi ne wannan Littafin-Takobi dake ɓoye acikin rigarsa lallai yana da muhimmancin gaske.


Nan take aka buga ƙugen nasara, kuma aka bawa Armad nasara. Inda shi kuma Niyashi likitoci suka tafi dashi. 


Sai dai kuma wani abu ya faru a dai-dai lokacin da Armad yaji motsin wannan littafin-takobi acikin rigarsa. Wannan abu kuwa babu wanda ya sani illa mutumin da abin ya faru dashi wato Uznu Ururu. 


Acikin rigar wannan ma'aboci Ururu wani ɗan ƙaramin allon tsafi yayi girgiza tare da fitarda wani baƙin haske kalar Idanun ubangidansa wato Uznu Ururu. Nan take wani ɗan murmushi na farin ciki ya bayyana akan fuskar Uznu Ururu. Domin yasan abinda yake nema ya samu. Wannan allon tsafi ba wani abu bane illa abinda yake amfani dashi wajen neman littafin-takobi. Matsafansa a ƙasa ta farko sun labarta masa cewa indai littafin takobin ya bayyana to wannan allo zai sanar dashi. Yanzu kuma gashi abinda ya daɗe yana nema sama da shekaru dubu ɗaya da ɗari biyar ya samu. Nan da nan ya juyo da hankalinsa gaba ɗaya kan Armad tunda daman abinda ya kawo shi wannan waje kenan.

____


A can bayan fili kuwa Armad ne ya isa wajensu Nusi, "Ahhhhh..." Nusi tayi ajiyar zuciya tare da riƙe Armad tana cewa, "hankali na har ya tashi, ga dukkan alamu bama saina damu dakai ba! Kai wataƙila dama ban rakoka ba ko!" Nusi ce a gefe da sauran mutanen da suka rako su daga garin Khan, suke ta yabawa Armad saboda jarumtar daya nuna a karawarsa da yarima Niyashi. 


"Hmmmm....kayi ƙarfi da yawa acikin ɗan ƙanƙanin lokaci, ina alfahari da kai!" Inji Nusi, acikin zuciyarta babu abinda take tunani sai wannan walƙiya ta ƙarshe da taga Armad yayi amfani da ita. Lallai tasan akwai wani abu a ƙasa. Amma dai kawai tayi shiru a lokacin domin bata so ta faɗi wani abu dazai ɗaukewa Armad hankali daga faɗan gaba daya rage masa.


"Yaya Armad, da ALLAH zan zamo ɗalibinka, ko na samu na ɗan koyi abu ɗaya ko biyu!" wani daga cikin ƴan rakiyar dake tare dasu Armad ya fara kamun ƙafa. 


"Nima haka....Nima haka...." 


Toh haka dai bayan kammala faɗa tsakanin Armad da Niyashi, ire-iren waɗannan maganganu suke ta kewayawa a tsakanin dukkanin mutanen dake wajen. 


Ana cikin wannan hayaniya kuwa tuni alƙalin wasa Gali, ya fito da wasu ganyayyaki na musamman guda huɗu. 


Dukkaninsu jajaye ne, inda yana fitowa dasu kaf ilahirin wajen yai tsit. 


Kasancewar kowa yasan waɗannan ganyayyaki bana komai bane illa na fitarda tsakani na wasannin gaba, wato dai dawa-dawa za'a kara. 


Kowa abinda ke ransa shi ne, wanne faɗa ne zaifi ƙayatarwa. Shin tsakanin Armad da Ikenga ne ko kuma tsakanin Bizaya da Han-Amuru wanda mutane da dama a wajen suke bayansa. 


Domin wani abin mamaki shi ne, idan ka cire Bizaya, zaka ga babu kusan wanda waɗannan ƴan kallo ke goyar baya kamarsa, duk da kuwa masu goyon bayan Armad sun ɗan ƙaru bayanda yaci nasara akan Niyashi. 


Alƙali Gali ya ɗauko alƙalami, wanda a jikinsa aka rubuta Deniziyya Kuronikil, ya miƙa hannu yabi kan dukkanin waɗannan ganyayyaki huɗu ya rubuta sunan ɗaya daga cikin mutun huɗun nan da suka fito. 


Sannan yana gamawa ya haɗesu waje ɗaya, kuma a gaban idon filin nan wanda tuni yayi tsit an zuba ido, alƙali Gali ya jefa waɗannan ganyayyaki huɗu sama. 


Nan take suka luluƙa sama kimanin taku huɗu, sannan suka fara sakkowa. 


Idon kowa akai, kawai so ake aga waɗanne guda biyu ne zasu fara dira ƙasa, wanda hakan shi zai nuna waɗanne ne zasu haɗu da juna. 


Wato dai a taƙaice, ganye biyun da suka riga zuwa ƙas, sunan dake kai, sune zasu kara da juna, kuma su zasu fara. 


Sannan kuma ragowar biyu da suka rage a sama su biyo baya. 


Wannan ita ce hanyarda suke bi a wannan gasa wajen zaɓar waɗanda zasu kara da juna. 


Kuma hanyace da kowa yake ganin tayi, saboda waɗannan ganyayyaki an tsinko sune daga bishiya ta musamman wanda kowa ya santa. 


Bishiya ce wadda babban abinda kowa ya sani akanta shi ne, tun daga sanda ta fara ganye har ƙarshen rayuwarta, a kodayaushe ganyayyakin ta iri ɗaya ne sak. Sunan wannan bishiya Safá, su kuma ganyayyakinta ana kiransu da Safáha.


Har zuwa sanda waɗannan ganyayyaki huɗu suka zo kusan tsakiya a tare suke tafiya, amma a wannan lokaci ne iska ta kaɗa, inda biyu daga cikin ganyen suka wuce sauran. 


Kuma kan kace meye wannan tuni sun kusa isa ƙasa. 


Suna dira suna ɗaya ya bayyana kuma sunan Han-Amuru ne a jiki. 


Ɗayan kuma a juye yake. 


To dama a dai-dai lokacin da Gali zai jefa waɗannan ganyayyaki waɗansu mutane sanye da fararen kaya su biyu, sun matso gefe sun tsaya. 


Dukkansu fuskokinsu a rufe suke, kuma su na tsaye cak kamar baza su taɓa motsawa ba. 


Amma a dai-dai lokacin da waɗannan ganyayyaki biyu suka dira a ƙas, waɗannan mutun biyu suka ɓace daga inda suke tsaye suka kuma bayyana a a dai-dai kan waɗannan ganyayyaki inda suka ɗauke su cikin sauri, tun kafin ragowar biyun su sauka. 


A gaban idon kowa kuma suka buɗe ɗayan, inda kowa yayi arba da sunan Armad Djinn akai. 


Nan take wajen ya ruɗe da shewa, kowa yana tattauna yadda rabon ya kasance, da dama dai yai musu, amma kaɗan daga ciki ba haka suka so ba. 


Armad na tsaye a kusa da Nusi tana ja masa kunne akan ya kula sosai da HanAmuru, kuma kada ganin cewa daga kan doron ƙasa ɗaya suke yasa yayi wasa, kawai sai yaji alamun ana kallonsa ta baya, inda na take ya juya ɓangaren. 


Yana juyawa yai arba da idanun Han'Amuru, wanda kallonsu kaɗai zai iya sawa kaji tamkar an jefa ka acikin wuta, saboda wutar da take ci aciki. In ba'a manta ba aljanin Han Amuru na wuta ne.


Kana gani kasan kallo ne mai cike da so da marmarin yaƙi, haɗe kuma da turawa Armad saƙon cewa a shirye yake.


Shima Armad baiyi ƙasa a gwiwa ba, wajen mayar masa da irin wannan kallon dake gaya masa shima a shiryen yake. 

***

Babi na 38 : Badalar wuta 


"Zo kaji!" Nusi ta ja Armad da sauri suka bar cikin mutane izuwa wani ɗan shinge dake wajen filin-wasan. "Wannan yaron mai suna Han Amuru na sanshi a shekarun baya da suka wuce a lokacin da mukai ƙoƙarin shiga garin ƙarƙashin ƙasa na Shadniza dana labarta maka a baya. Lallai yana da hatsarin-gaske sama dana gobarar daji, dole ka kiyaye."


"Ehmmm......" Armad ya kyaɗa kai tare da ajiyar zuciya. "Kada ki damu kanki sosai, ni nasan zanyi nasara domin sama da ƙasa zata haɗu bazan mutu ba saina tabbatar mahaifiyata ta samu lafiya. Akwai fasahar Wasu-wasi da nake da ita wanda har yanzu banyi amfani da ita ba. Akwai ɗalasimin Kaban'shisu shima." Armad yana magana cikin taushi musamman ganin yanayin tausayi da so acikin idanun Nusi.


"Da gaske fa...... Ki dena damuwa da yawa." Armad ya matsa kusa da Nusi tare da ƙara jaddada mata abinda ke zuciyarsa bayanda yaga alamun rashin amincewa a idonta. 


Nusi ta girgiza kai, "Ban san mai yasa ba amma jikina yana bani kamar akwai wani hatsari dake tafe. Lallai hankali na bazai kwanta ba sai naga mun bar wajen nan lafiya." 


Nusi ta matsa kusa da Armad domin kare shi daga wasu mutane dake wucewa wanda suka fara nuna Armad suna cewa, "shi ne Armad Djinn, shi ne yai nasara ɗazu akan yarima Niyashi."


Nusi ta ƙara jan Armad suka bi bayan wasu shaguna dake kewaye da filin domin ɓuya daga idanun jama'a.


"Ungo wannan Layar." Nusi ta fito da wata Farar-Laya ɗaure da wani zare mai launin roɗi-roɗi daga cikin rigarta ta kuma miƙawa Armad. "Nasan kasan amfanin ta."


Idanun Armad suka cika da mamaki, shin wai abinda yake gani dai-dai ne ko kuma mafarki yake. Domin kuwa idan dai Layar da yake tunani ce to lallai ya tsinci dami a kala. "N......nusi... Ya akai kika samu Farar-Laya....."


"Sh...sh.... ka daina faɗa da ƙarfi mana kosai kasa wasu sunji." Nusi tayi sauri ta rufe masa baki. Sannan taci gaba da bayani bayan ya karɓi Layar. Ga dukkan alamu wannan Laya aba ce ta musamman. To ko meye amfaninta.


"Zaka iya amfani da wannan Farar-Laya amma ka sani ba mai ƙarfi bace, saboda haka sau ɗaya kacal za'a iya amfani da ita. Ungo wannan safar kasa a hannunka, domin kaima baza ka iya taɓa ta ba." Ta ƙara miƙa masa wata ƴar safa ruwan ƙasa. Har a wannan lokaci daya miƙa hannu ya karɓi safar idanunsa cike suke da mamaki. Domin yana da cikakkiyar masaniyar cewa ba ƙaramin abu mai wahala bane ga mutun ya mallaki wannan Farar-laya ba koda kuwa mara ƙarfi. Nan danan ya ƙara sanin cewa lallai akwai manyan ma'abota da suka tsayawa Nusi. Musamman daya tuno labarin data gaya masa na cewa suna da ƙungiya mai ƙarfin gaske da suke ƙoƙarin buɗe garin ƙarƙashin ƙasa na Shadeniza.


A dai-dai lokacin da yazo nan a tunaninsa ne suka jiyo ƙarar ƙararrawa alamun lokaci yayi daza aci gaba da fafatawa. Nan da nan suka rankayo izuwa cikin filin.


Lokaci kaɗan bayan kaɗawar ƙararrawar aka buga ƙugen yaƙi, inda Armad da Han'amuru suka fito filin daga, babu abinda kake ji sai shewar ƴan kallo wasu suna goyon bayan Armad wasu Hanamuru, amma kana gani zaka san na Hanamuru sunfi yawa.


Gabda zai hau kan filin dagar Armad ya ƙara shafa aljihunsa domin jin halin da Littafin-takobi yake ciki. Shi kansa baisan dalilin da yasa bai gayawa Nusi labarin wannan littafi ba duk da kuwa yasan ya kamata ya gaya mata. 


Sai dai abu guda ɗaya da yake ta sukar Armad a rai shi ne, baisan dalilin da yasa Littafin-takobin ya taimake shi a yayin faɗansa da Yarima Niyashi ba. Saboda haka bashi da tabbas zai ƙara samun irin wannan taimako daga wannan littafi, kuma lallai bai kamata ya ta'allaƙa dashi ba. Saboda haka ma baya son ya gaya mata hankalinta ya ƙara tashi. Kuma tunda ma'aboci aljanin wuta Han Amuru ya fishi girman Izza lallai yana da buƙata ya fito da wata hanya da zai samu nasara cikin gaggawa.


Saboda haka ya fara tunanin mafita, 'Ina da Saran takobi mai suna Wasu-wasi, sannan kuma ina da adadin ƙawanyar walƙiya guda hamsin da ɗaya. Mafi muhimmanci kuma ga Farar-laya dana samu daga Nusi.' Armad ya ci gaba da tunane-tunanen hanyar dazai samu nasara ba tare da neman taimako daga littafin ba. Saboda shima yana ji a jikinsa cewa akwai wani sharri  maɗaukaki a tattare da wannan Littafi.


Suna dira acikin filin, Han Amuru ya ƙara ja da baya, ya kuma ƙara nisan dake tsakaninsa da Armad inda cikin sauri ya tafa hannayensa biyu gami da cewa, "Badalar wuta!!"


Yana faɗar haka, wata wuta ta bayyana a gefensa. Wadda tana bayyana ta fara ƙara yawa tana zagaye shi, kan kace meye wannan tuni wannan Badalar wuta ta rufe Han Amuru har zuwa kafaɗaunsa, inda ta tsaya.


Amma kuma tana tsayawa sai wata irinta ta fara kewaye ta inda ita ma tayi ta ringa ƙaruwa har takai tsayin kamar wancan.


Tana gamawa wata ta fara... haka-haka har saida aka samu ƙawanyar wuta zagaye shida a kewaye da Han Amuru. Wannan badaloli su na gunji suna fitar da baƙin hayaƙi da tiriri suna kare Han Amuru tamkar sarki acikin bangon Badalar garinsa. Lallai ko kakai ƙanƙantar kiyashi baka isa ka cimma Han Amuru ba a yadda yake.


Han Amuru ya miƙa hannunsa gaba, inda ya nuna Armad, wanda ke tsaye har a lokacin bai motsa ba.


Yana nuna Armad, cikin ƙiftawar ido da bismilla, biyar daga cikin waɗannan ƙawanyar badala ta wuta, suka ɓace daga inda suke, suna ƙara bayyana sui gasu zagaye da Armad.


Haka na faruwa Hanamuru ya kyalla ido ya hango Armad a tsakiyar wutannan, kowa na gani yai wata wawar dariya gami da cewa, "Armad....Djinn ko? Naga faɗanka da Niyashi kuma ina mai tabbatar maka da cewa lallai sai nayi nasara akanka. Ni zan ƙone ka ƙurmus acikin Badala ta ta wuta! Kai sani cewa ni idan ina filin daga babu ruwana da yaro ko babba, duk hukunci ɗaya nake musu. Saboda haka kada ma kayi tunanin cewa dan kana da Izza ƴar ƙarama wadda bata fi rabin tawa ba zan ɗaga maka ƙafa."


Gunji da tiriri da wannan wutar ke bayarwa tuni ya fara ƙoƙarin haɗiye Armad. Armad ya ɗaga ido yaga shekarun Izza ɗai-ɗai har goma sha bakwai ajikin kowacce ɗaya daga cikin wannan badalar wuta guda biyar dake neman haɗiye shi. Lallai yasan indai ya bari ɗaya daga cikinsu ta taɓa shi to fa lallai ƙarshensa yazo.


Nan take ya zira wannan safa da Nusi ta bashi sannan ya tuno da ɗaya daga cikin ɗalasiman daya koya a wajen kakansa wato 'Kaban'shisu'. Ba shiri Armad yayi amfani da ƙarfin Izza na kimanin shekara goma ya tayarda wannan ɗalasimi. Lamarinda ya bashi damar kuɓucewa wannan badalar wuta abar ruruwa. Inda ta daki wajen da Armad ya bari kuma nan take ta maida shi toka. Armad ya bayyana acan gefe yana mai duba izuwa wannan waje daya bari tare da tuno cewa da bai bar wajen ba, toda tuni ya zama toka shima. 


Sai dai yana cikin tunani ne wata badalar ta ƙara yiwowa kansa da niyar haɗiye. Amma ina, Armad ya ƙara kuɓucewa. Lamarinda ya bawa Han Amuru haushi yai wani ƙaraji tare da saka badalolin wutar guda shida su haɗe izuwa babbar badala guda ɗaya. Wadda nan take ita kuma ta kewaye dukkan filin dagar inda tasa Armad da shi Niyashi a tsakiya. Sannan kuma ta fara matsewa tana haɗewa izuwa tsakiya. Wato dai a taƙaice Armad bashi da wajen guduwa indai ba tashi sama zaiyi ba. Wataƙila da yana da Miyurarsa, da zai iya tashi saman kamar yadda yayi a faɗansa damai tsaron hanya Han Diyuza, amma yanzu babu. Gashi a tsakiyar wutar badala tare da ma'aboci aljanin wuta wanda babu alamun imani a tattare dashi ko kaɗan. 

***

Babi na 39 : Farar-laya


Duk taƙi ɗaya da wannan wuta ta ƙara kusantar Armad sai yaji raɗaɗinta ya ƙaru. Tamkar ana soya naman jikinsa. Lallai bada ban jarumin gaske bane da tuni ya kwalla ƙara. 


Amma duk da wannan hali daya ke ciki wani abu ɗaya ya ɗauke masa hankali. Wannan abu kuwa shi ne kasancewar wancan badala ta wuta data nemi halaka shi, ya sha dakyar ta hanyar ɓacewa daga inda yake, ya kamata ace shekarun Izzar dake jikinta sun ragu daga sha bakwai zuwa ƙasa. Amma bisa mamaki tana nan dai-dai a yadda take;    ɗauke da shekaru goma sha bakwai na Izza. Lallai Armad yasan akwai matsala idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka. Domin kuwa idan Izzar mutun bata raguwa idan yayi amfani da ita, to tayaya Armad zai iya cin galaba akansa. 


Hayaƙi da turiri ya fara neman sawa hankalin Armad ya gushe, amma Armad yasan cewa lallai indai ya bari ya suma a wajen to ƙarshensa yazo. Saboda haka ya cije ya daure ya tsaya da ƙafafunsa, ya kuma fuskanci inda Amuru yake tsaya yana kallonsa cikin isa da ƙasaita. 


A dai-dai wannan lokaci ne Armad ya yanke shawarar mai zaiyi. Nan take ya zira hannunsa mai safar cikin aljihunsa. Inda ya janyo wannan Farar-laya da Nusi ta bashi. Sannan kuma a lokaci guda yayi duba izuwa ruhinsa, inda ya janyo ƙawanyar walƙiya na ƙarfin Izzarsa daya rage na shekaru arba'in. 


Daga nesa idan ka hango Armad abin zai baka mamaki; zaka ga yaro saurayi wankan-tarwaɗa sanye cikin fararen kaya. A kewaye dashi akwai ƙawanya ta walƙiya ɗai-ɗai ɗai-ɗai har guda arba'in da ɗoriya su na kewaya shi. Lallai da dama daga cikin ƴan kallon baza su taɓa mantawa da wannan yaro mai suna Armad. 


Cikin sauri ya tunkari Han Amuru yana sassarfa. Sai dai kuma wannan badala dake ta kusanto su tamkar ta gane mai Armad yake niyyar yi, saboda haka tayi kansa cikin tsananin sauri. Lamarinda yasa ta cimmasa cikin ƙiftawar ido da bismilla.


Tana zuwa ta daki wannan ƙawanyar walƙiya data kewaye Armad. Inda wata ƙara mai ruɗarwa ta tashi. Nan take faɗa ya kaure tsakanin wannan badalar wuta da kuma ƙawanyar walƙiyar Armad. Wuta tana ƙoƙarin haɗiye walƙiya, walƙiya kuma tana ƙoƙarin ƙona wuta. Lallai wannan faɗa ne na musamman, wanda dukkanin ƴan kallo hankalin ya koma kai. Sai dai kuma abinda basu sani ba shi ne a bayan wannan walƙiya Armad ne keta aman jini yana tafiya da kyar, saboda duk sanda wannan wuta ta daki walƙiyarsa sai yaji rauni a jikinsa. Badan komai ba saboda banbancin Izzar dake tsakaninsu. Lallai akwai banbanci maɗaukaki tsakanin mai Izza ɗari da mai hamsin. Wanda idan banda ƙarfin ruhi da dagiya irin ta Armad da tuni yaje ƙas.


Armad ya ci gaba da tafiya yana aman jini, burinsa kawai ya isa ga Amuru. Koda yaje dab dashi sai Amuru yayi masa wani kallo mai cike da mamaki tare da cewa, "kana ta sauri ka iso gareni, shin kana tunanin dan kazo nan zaka iya yin wani abu ne? Bari dai na nuna maka banbancin ƙarfin Izzar dake tsakanin mu."


Nan take Amuru ya dunƙule hannunsa, lamarinda yasa nan take dukkan wutar dake wajen ta cure izuwa tafkeken dunƙule guda ɗaya kewaye a hannunsa. 


Kafin Armad ya farga tuni Han Amuru ya kawo masa duka da wannan hannu nasa mai haɗe da wuta. 


Ko kokwanto babu Armad yasan indai ya bari wannan hannu ya taɓa shi, tofa lalle ko tokarsa baza a gani ba. Saboda haka nan take ya haɗe dukkan sauran ragowar shekarun Izzarsa izuwa wata ƴar ƙawanya ta walƙiya. Wadda yasa ta kewaye wannan Farar-laya dake hannunsa, sannan ya cillawa Amuru ita. 


Saboda yadda layar take kewaye da walƙiya, Amuru baiga layar ba, saboda haka yai tsaki tare da cewa, "shin kana tunani ƴar wannan walƙiyar daka cillo zata iyai min wani abu ne? Ka farka in ma mafarki kake, domin kuwa......"


Han Amuru ya haɗiye ragowar kalominsa tare da rufe bakinsa yayinda wannan Laya ta taɓa jikinsa. Sannan kuma kafin ya ankara zaren dake jikinta ya rataye a wuyansa.


Cikin abinda bai wuce ƙiftawar ido ba dukkan wutar dake kewaye da Amuru ta ɗauke tamkar ba'a taɓa yinta ba. Wani zafi mai haɗe da kasala ya cika jikinsa, inda hatta ƙafarsa yaji baza ta iya ɗaukansa ba. Ya nufi ƙasa gadan-gadan tamkar wanda aka zarewa rai.


A dai-dai wannan lokaci da kowa ke mamakin abinda ke faruwa aka jiyo muryar alƙalin wasa wato Ghalee, "F.....farar-laya! Lallai babu kokwanto acikin abinda ke faruwa. Wannan yaro mai suna Armad Djinn yayi amfani da Farar-laya ya ɗaure aljanin Han Amuru. Kowa yasan ƙarfin wannan Laya da akewa laƙabi da Farar-laya wajen ɗaure dukkan wani aljani da kuma hana ma'abota su amfani da duk wata fasaha da suke da ita. Amma babban abin mamakin shi ne a ina wannan yaro ya samo wannan laya? Ta yaya ɗan ƙaramin yaro zai mallaki Farar-laya." 


Haka dai Ghalee ya ci gaba da bayyana alajabinsa a fili ƙarara da yadda akai Armad ya mallaiki Farar-laya. Domin dai ko ba'a faɗa ba ansan ya riga yaci nasara akan Amuru, wanda tuni ya faɗi ƙasa ko motsi baya iya yi. Domin bawai kaɗai ɗaure aljanu wannan Farar-laya take yiba, hatta ma'aboci aljanin sai yaji muguwar kasalar da bazai iya komai ba.


Babu daɗewa abinda ya faru ya girgiza kowa a wajen, kuma tuni mahangar da dama daga cikin ƴan kallon akan Armad ta canja nan take.


Kusan sama da kaso arba'in sun fara yi masa kyakkyawan zato.


Likitoci suka garzayo cikin filin-dagar suka ɗauki Armad, domin abin mamaki shi ne, Armad shi ne yayi nasara amma kuma shi yake ta aman jini. Saboda ko ciwo ɗaya babu a jikin Han Amuru in banda kasancewar dai ko tashi bazai iya yi ba saboda aikin wannan Farar-laya. Inda dai ALLAH ya taimaki Armad shi ne akwai wata fafatawar kafin ayi wasan ƙarshe. Saboda haka yana da lokacin da zai huta ya ɗan farfaɗo.


Ba daɗewa aka buga wani ƙugen yaƙin, dake sanarda cewa lokaci yayi da za'a fafata tsakanin Deniz Bizaya ɗan sarki Deniz Iluru mai masaukin baƙi, da kuma Ikenga O. Bayajidda wanda shi ne sanadiyyar rabewar ruhin Armad gida biyu da kuma ɓacewar Miyurar sa! 


A can gefe ɗaya kuma Armad ya fito matakin ƙarshe na wannan gasa!

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...