Skip to main content

366-369

 "Da ace na buɗe fuskata da zaiyi wuya masu gadi su bari na shigo. Ni kuwa ba tashin hankali ne ya kawo ni ba."


Tana faɗar haka ta kai hannu ta cire hijabin dake fuskarta. 


Ganin fuskarta yasa Fatima taja da baya gami da zare takobinta. Yarima mai jiran gado da kannensa guda biyu suka zare takobinsu. Sauran mutanen da suke cikin fada sun kasa koda motsawa. Watakila tsoro ne, watakila kuma mamakin ganinta ne amma dai duk cikinsu babu wanda ya motsa. Idan ka lura sosai za kaga wannan mace data buɗe fuskarta ba wata bace illa Hidaya. 


Fatima da Yarima mai jiran gado suka kewayeta suna jiran umarnin sarki su afka mata. Kafin sarki yayi magana sai ga wani mutum nan ya tako ya shigo fada. Dukkan masu gadin dake wajen babu wanda yayi ƙoƙarin tare shi. Ba wai dan basa son tare shi ba sai dan jikinsu yaƙi bin umarninsu. Haka suna ji suna gani ya wuce har wajen da Hidaya take tsaye inda ya wuce gaban sarki ya durkusa. "Ni, Taidara Wilbafos, jinin Ayubul-laisiy Al-wilbasi, nazo da aminci ina neman auren Fatima a wajenka."


Sarki ya dube shi a hasale yace, "kana tunanin al'ummar ƙauyen Nafada daka kashe zasu yarda a baka auren wata mace a daular nan bama 'ya ta ba?" 


"Mai zai hana?" Inji Taidara. "A tambaye su a ji." 


Sarki Abbas ya ɓata rai a karo na farko. "Zan iya yarda na haƙura idan mutane na suka faɗi a fagen daga. Abinda bazan yarda dashi ba shi ne ciwa al'umma ta mutunci da zaginsu bayan sun mutu"


"Ina mai rantsuwa da abin bautata dukkanin mutanenka suna raye," inji Taidara. "Ɗaya daga cikin fasahata mai suna Hisabi nayi amfani da ita akan su. Shekaru ɗari da suka wuce na samar da fasahar Wasu-wasi wadda idan na sari mutum da ita ya kan dauki lokaci kafin saran ya bayyana. Da dama sukan mutu da Wasu-wasi akan fuskarsu suna kokwanton mai ya kashe su. Shekaru sha-uku da suka wuce na ƙarawa wannan fasaha karfi sannan na canja mata suna ta koma Hisabi. A yanzu idan na sari mutum saran bazai bayyana ba har sai adadin lokacin dana kayyade masa ta cika. Amma kuma a lokacin dana yi saran a lokacin izzar mutum zata ƙafe, mutum ya daina numfashi wanda hakan zai sa a ga kamar mutum ya mutu. Amma a zahiri duk wanda na sara yana da rai har sai ranar da lokacin Hisabin sa ya cika. Zaka gansu da mamaki akan fuskokinsu suna kokwanton ko sun mutu ko su nada rai. A yanzu idan sarki ya bani dama zan iya zuwa na tashe su."


Sarki Abbas yayi shiru ya ƙura masa ido. Yayi daɗewar da a duniya babu wata fasaha da za'a ce masa an gani ya ƙaryata, amma duk da haka duk fasaha data shafi mutuwa tana sashi kokwanto. Kuma a lokuta da dama yakan jinkirta yadda da irin wannan fasahohi har sai ya gansu da  idonsa. Saboda haka nan take ya umarci sadaukai su je su haƙe kaburbura su kawo masa gawarwakin mutanen. 


Fatima tayi tsalle ta zube a gaban sarki. "Ya mai girma mai izza, ina ganin akan maganar waɗannan ƴan ta'addan bai dace muje mu haƙe yan-uwanmu, mu tona asirin makwancinsu ba. Indai da gaske yake to ya gwada akan ƴarsa mu gani tukunna sai mu yadda da maganarsa."


Sarki ya ɗan sosa goshinsa cikin tunani. Tabbas maganar Fatima haka take to amma baya tunanin wannan mutun zai amince yayi gwaji akan ƴarsa. Haka nan kuma wanda ya mutu ya riga ya mutu, ko an haƙe shi daga kabari ko ba'a haƙe shi ba, saboda haka yana ganin indai akwai yiyuwar gaskiya a zancensa to ya kamata ace an gwada. 


Sarki na cikin wannan tunani ne yaji muryar Taidara a kunnensa. "Idan sarki ya yarda zan gwada wannan fasahar akan ƴa ta Hidaya."


Cikin sauri sarki ya amince. 


Taidara yaja da baya ya zare takobi ya kai sara kan iska. Ɗiso-ɗison shuɗi ya bayyana akan takobi. Kowanne ɗiso ya juye izuwa dunkulen haske wanda suka taru a waje ɗaya suka juye izuwa siffar takobi. Takobin tayi fitar burtu taje ta sari Hidaya a kafada. Faruwar hakan keda wuya Hidaya ta zube a ƙas sumammiya. Sarki da kansa yazo ya duba ya tabbatar ba rufa-ido bane kuma da gaske bata numfashi. Sannan kuma ga mamaki da Wasu-wasi akan fuskarta kamar wadda aka canjawa kamanni. Yana tuno irin wannan kamanni akan fuskar waɗanda aka binne. A lokacin yayi imani da fasahar Wasu-wasi. Amma duk da haka Fatima bata aminta ba sai da tasa Taidara ya gwada fasahar akanta kowa ya gani. 


Daga nan a kaje maƙabarta aka fara haƙe mutanen garin da aka binne ana kawowa Taidara su yana tashinsu. Duk wanda ya ɗora hannunsa akan kafaɗarsa sai kaga mamakin dake kan fuskarsa ya kau sannan ya buɗe ido. Kai kace ba daga kabari suka fito ba. Nan take babban birnin Maikironomada ya cika da koke-koke da iface-iface. Wasu na murna, wasu na mamaki, amma dai da dama daga cikin mutane dimaucewa su kayi suna gudu suna dukan kirjinsu, suna marin fuskokinsu, suna kiran kaiconsu. Yau sun ga mai tashin matattu. Ashe dama rai zata tashi bayan ta mutu? Babu wani bayani da Taidara zaiyi ko kuma sarki Abbas wanda zai sa mutane su yarda ba tashin matattu aka yi ba. Cikin kankanin lokaci jama'a da dama sun fara ziyartar maƙabartu, suna haƙe masoyansu da suka binne, suna garzayowa dasu fada wajen Taidara. Kan kace kwabo fada ta cika da matattu da kwarangwal. Tuni aka daina zancen auren da Taidara yazo nema aka koma zancen yaya za'a tayar da matattu. 


Da sarki ya gwada ya kasa shawo kan mutane sai ya tura musu Taidara da Hidaya suje su karata, shi kuwa ya rufe fadarsa. A wannan rana duk inda Taidara da Hidaya sukai acikin birnin Maikironomada sai dai kaga mutane suna binsu riƙe da kwarangwal da matattu. Suna kuka suna roko Taidara ya tayar musu dasu. Mutane suka fara siyan ayrid suna tura sakonni zuwa makwabtan garuruwa. Daga nan labari ya bazu ko'ina a sassan duniya. Jaridar Aminiya sune na farko da suka zo birnin Maikironomada suka ga abinda yake faruwa suka kuma buga a shafin farko na jaridar. Labari mai taken 'tawagar matattu'. Abu kamar wasa sai aka daina zancen faɗan Fatima da Hidaya, duk inda ka zagaya labarin tawagar matattu akeyi. Sai da akai wata uku kafin ƙurar ta lafa. 


A ɓoye Taidara ya ringa zuwa wajen sarki Abbas neman auren Fatima. Haƙansa bai cimma ruwa ba domin kuwa Fatima ta dage bata son sa. Tun yana zuwa duk sati har ya haƙura ya koma wata-wata, kai har dai ya haƙura ya koma sai ya bushi iska zai je. Daga baya ya ɗauke ƙafa gaba ɗaya. 


Armad yana zaune yana kallon abubuwan da suke faruwa. Koda aka zo dai-dai nan sai Zaikid yasa hannu yayi gaba da bidiyon ya kai shi can wajen wani daji. 


A wannan dajin mutum baya iya banbance safiya da maraice, ko kuma rana da dare, saboda rana bata isowa cikin dajin. Wasu manya-manyan bishiyun kuka ne suka rufe dajin baki daya. Fala-falan ganyayyakinsu yafi na duk wata bishiya da Armad ya taɓa gani a rayuwarsa girma. Sun haɗe junansu sun tare hasken rana ta yarda ƙananun bishiyoyi na ƙasa basa samun koda ɗison haske. Hakan yasa bishiyoyi irin su darbejiya, mangwaro da tsamiya basa girma. Zakaga bishiyar tsamiya kamar tafasa saboda rashin hasken rana. Yawancin ƙasar dajin a cike take da danshi da kuma sanyi mai ratsa ƙashi. Ƙananun dabbobi kuwa irin su miciji da kunami da kwadi wanda basa buƙatar hasken rana sunyi girma na gaban misali. 


Wani koran kwado ƙatoto mai idanuwa uku shi ne ya fara yiwa Armad sallama. Yana laɓe a bayan wata bishiya yana hangen wasu mutane guda biyu da aka ɗaure a saman bishiyar. Watakila burin wannan kwado ya cinye mutanen. Bakinsa a buɗe yake ya kuma saitashi dai-dai mutanen. Idan ka dubi mutanen zaka iya cewa burin wannan kwaɗo ya kusa cika domin igiyar da aka daure kafafunsu da ita ta kusa tsinkewa. Sun galabaita matuƙa, ruwan jikinsu ya bushe, leɓensu sun tsatstsage, da kyar suke buɗe idanuwansu. Duk da haka Armad ya gane namijin, macen ce dai bai gane ba. Namijin ba kowa bane illa farfesa Zaikid wanda ke zaune a gefensa yana nuna masa faifan bidiyon. Ga dukkan alamu a wannan lokaci Zaikid ya jigata domin duk kwanjinsa babu shi, ƙasusuwa sun bayyana sosai a jikinsa.


Daga can ƙasa wasu mutane ne suke harkokinsu na yau da kullum. Ko kaɗan basu damu da su Zaikid ba. Sun kafa tantuna acikin dajin suna rayuwarsu kai kace acikin gari ne. Yara suna ta kai-komo suna odi-odi. Daga can ƙasan wani tanti wasu manyan mutane ne zaune a kewaye da wani teburi suna tattaunawa. Wani lokacin sai kaga sunyi shiru sun juya sun kalli inda su Zaikid suke ɗaure, ko kuma kaga sun kalli inda wasu ƙarti suke kokawa. Saboda hayaniyar mutane da kyar Armad yake jin abinda wannan mutanen suke cewa. Zaikid yayi amfani da 'yantsunsa guda biyu ya buɗe faifan bidiyon yadda Armad zai ga mutanen dake zaune a kewaye da teburin sosai. 


Mata ne guda biyu da maza guda biyar. Akwai wani farin namijin a gaban teburin yana zaune yana sauraran matan da mazan suna tattaunawa. Tunda Armad yake bai taɓa ganin farin mutum kamarsa ba. Yafi Nostalgia fari, kuma yafi sarkin-sarki haske, kai kace kasancewarsa a wajen ya ƙarawa wajen haske. 


Ɗaya daga cikin matan wadda ke kusa dashi ta buɗe baki tace, "ba fa zasu gaya mana inda yarinyar da suka haifa take ba komai azabar da muka yi musu. Ni ina ganin mu kashe ɗaya daga cikinsu mu ɗaure kansa a akwati mu tura shi daular Maikironomada. Ina da tabbas ɗaya daga cikin matan nan da suke faɗa ita ce wadda suka haifa. Duk su biyun suna amfani da izza, kuma yanayin yadda suke sarrafa zaren izza ya wuce ace koya su kai, dole 'ya'yan gado ne. Tabbas 'ya'yan Wilbafos kuma ina kyautata zaton Fatima ita ce wadda suka haifa tunda dama munsan ba ƴar wajen Abbas bace. Kaga babu abinda zai hanata zuwa ɗaukan fansa idan taga mun kashe iyayenta. Tana zuwa sai mu kamata."


Ɗaya daga cikin mazan dake wajen ya amsa da cewa, "tayaya kika tabbatar Fatima suka haifa? Duk su biyun munga suna amfani da izza wanda hakan yake nuna duk 'ya'yan Wilbafos ne, daga ina dayar take? Yaya zamu yi idan ta tabbata ba Fatima bace, Hidaya ce?"


Ɗaya namijin ya bude baki yace, "naji ance Hidaya 'ya ce a wajen mutumin da suke tare, Fatima kuma mun riga munsan ƴar riƙo ce a wajen Maikiro'Abbas. Saboda haka ina ganin Fatima ita ce wadda muke nema."


"Amma bamu da tabbas Hidayan abinda ta faɗa gaskiya ne," Inji ɗaya macen dake wajen. "Zata iya yiwuwa ba baban ta bane."


Nan take aka fara kace-nace akan waccece yarinyar da Zaikid ya haifa. Kowa acikinsu yana kawo hujjoji akan wanda yake ganin ita ce. Wasu suna ganin Fatima ce tunda ita ce 'yar riƙo, wasu kuma suna ganin Hidaya ce tunda basu san asalinta. A wannan zamani zaka iya cewa duk wani ɗan gidan Wilbafos sun san dashi kuma sun san a ina yake, kuma zaka iya cewa wannan shi ne karo na farko da sukai karo da ɗan Wilbafos da basu san asalinsa ba.


Bayan yar-gajeriyar tattaunawa farin mutumin ya yanke shawarar ayi kuri'a. Wanda suke ganin a kashe Zaikid ko kuma macen a tura da kansu daular Maikironomada suka rubuta a takarda suka bayar, wanda kuma suke ganin babu buƙatar yin hakan tunda dai babu tabbas Fatima ita ce yar da Zaikid ya haifa suma suka rubuta a takarda suka bayar. Wanda suke ganin kisan bashi da amfani suna bada hujjar cewa idan Fatima ba ita ce yarinyar ba to sunyi a banza kenan kuma sun rasa makamin da suke dashi. Dama dai lissafin wannan mutane shi ne suyi amfani dasu Zaikid su janyo yarinyar da suka haifa sannan su haɗasu su kashe.


Aka lissafa kuri'a a gaban kowa. Ana gamawa farin mutumin ya tashi ya nufi inda su Zaikid suke ɗaure ya kwanto matar yasa aka kawo masa takobi. Saboda galabaita ko motsi bata yi sosai. Haka yasa kanta ta fuskanci gabas sannan ya ɗaga takobin sama.


Zaikid ya fara kuka yana magiya. "Ni ka kashe ni a maimakon ta. Duk abinda ya faru laifi na ne. Idan kana tunanin anyi wani laifi to ai Ni ne nayi, ita meye laifinta aciki bayan aurenta aka yi? Ni da na aureta ni zaka kashe. Ni ne na sirka jinin Wilbafos, ba ita ba."


Farin mutumin bai nuna yaji abinda Zaikid yake faɗa ba. A nasa ɓangaren kawai karatun yanka ya fara. "Ni, Umuk-li Wilbafos, a bisa tsarin kundun Wilbafos babi na huɗu, sakin layi na biyu, na yankewa Kulsum Bayajidda hukuncin kisa saboda karya darajar gidan Wilbafos da tayi. Ina fatan hakan ya zamo izina akan mu da ƴaƴanmu a gaba."


Ya ɗaga takobin ya sauketa a wuyan matar. 


Zaikid ya ɗauke kai, kwalla ta ciko idonsa. Har yanzu bayan tsahon shekaru yana ɗauke da baƙin cikin abinda ya faru. Ko ba'a faɗa ba Armad yasan wannan mace da aka kashe ita ce matarsa Kulsum. Kuma ita ce babar Fatima. Dama ya gaya masa iyalan Wilbafos basa goyon bayan auren amma bai san abin yayi tsanani haka ba.


"Bayan Umuk-li ya kashe Kulsum sai yasa kan acikin akwati ya tura daular maikironomada," inji Zaikid. "Fatansa Fatima tazo da kanta ɗaukar fansa ita ma ya kashe ta, sannan nima ya kashe ni. A cewarsa hakan shi kaɗai ne zai tsarkake jinin wilbafos da muka lalata."


Ana tsaka da zaman fada ɗan-aike ya shigo da akwati a hannu. Ya jira akan layi har lokacin shigarsa yayi. Wasu daga cikin na kan layin sun fara kallon akwatin suna so su ga meye aciki kasancewar ba kullum ake ganin akwatin baƙin ƙarfe a fili ba. Sa'ar da wannan ɗan-aike yaci jini baya ɗisa daga akwatin domin kuwa da tuni jama'a sun ɗago shi.


Sannu a hankali layi yazo kansa. Ya isa gaban sarki ya zube a ƙasa yayi gaisuwa. Bayan ya kammala sarki ya bashi dama yayi magana.


"Shugabana, Umuk-li, shi ne ya turo ni," inji ɗan-aiken. Ya miƙawa hadimin sarki akwatin domin a bawa sarki. 


Hadimin ya daka masa tsawa. "Buɗe mu gani meye aciki?"


Babu musu ɗan-aiken yasa hannu ya buɗe akwatin. Ganin kan mutum aciki yasa mutanen dake wajen suka jada baya. Wasu makamai suka zare. Hatta sarki sai da ya miƙe daga kan karagarsa. Su Fatima da ƴaƴan sarki suka zo gaban ɗan-aiken.


Kafin kace kwabo fadawa sun durkusar da ɗan-aiken a ƙasa kan gwiwowinsa. 


Ba tare da kallon cikin akwatin ba Fatima ta ɗora takobinta a wuyansa. "Yi bayanin kanka."


"Shugabana, Umuk-li, shi ne ya ce na kawo muku wannan akwati. Ya ce idan nazo na haɗa muku da wannan." Ya miƙa hannu zai zaro abu a aljihunsa amma yarima mai jiran gado ya doke hannun gefe. Yarima yana ganin mutumin zai iya ɗakko makami ko kuma wata guba daga aljihun. Saboda haka yarima da kansa ya zira hannu a aljihun ya zaro takardar ya miƙawa hadimin sarki mai karatu.


Hadimin ya karanta takardar:


***

Daga ni Umuk-li Wilbafos, magajin Wilbafos na farko a ban ƙasa tun bayan shudewar daular Wilbafos. Wannan kai na wata mace ne mai suna Kulsum Bayajidda. Ta yaudari ɗaya daga cikin ƴaƴan gidana ta karya jinina. Hakan ya saɓa da kundun tsarin mulkin Wilbafos. Bani da yadda zanyi face na yanke mata hukunci. 


Dalilin da yasa na turo maka kan shi ne ina so kayi izna da abinda ya faru da ita ka bani ƴar data haifa wato Fatima. A matsayinka na sarki abinda ya kamata ka fara tunani shi ne mutanenka - lafiyarsu da jin dadinsu. Tabbas idan baka bani Fatima ba...

***


Mai karatun yayi shiru yana kallon sarki kamar wanda yake jimamin karanta ragowar abinda ke cikin wasikar. Ga Fatima a gefe tana kallonsa.


Kafin sarki yayi magana Fatima ta daka masa tsawa. "Kaci gaba da karantawa mana." Jikinta har ɓari yake.


Bafaden ya kalli sarki wanda ya gyaɗa masa kai alamun yaci gaba. Murya na rawa yaci gaba da karantawa.


***

Tabbas idan baka bani Fatima ba, to ni da kai na zan dirar maka nayi maka hukunci irin wanda ya dace dakai. Ina yi maka wasiyya da kada ka shiga rigimar da ba taka ba. 


Daga ni jikan Aldaima - Umuk-li Wilbafos, Magajin Wilbafos na farko, jinin Eyriyon na Farkon Lokaci.

***


Fada tayi tsit babu mai cewa uffan kamar mutuwa ta gifta. Bayan tsahon lokaci Fatima ta durkusa ta ɗakko kan dake cikin akwatin. Koda sukai ido biyu dashi sai kowacce jijiya ta jikinta ta fara ɓari. Hawayen baƙin ciki mai zafi ya fara zuba daga idanunta. Ta san babarta sarai domin kuwa ba wannan ne karo na farko da suka gamu ba. A lokuta da dama Zaikid da Kulsum suna kawo mata ziyara a ɓoye ba tare da kowa ya sani. Idan ranar haihuwarta ta zagayo suna zuwa su kawo mata kyauta kala-kala tun tana yarinya kuma har yanzu basu daina ba. Lokaci na ƙarshe data gansu shi ne sanda ta cika shekara sha-tara. Jiya-jiyan nan take tunanin ina suka shiga kwana biyu bata gan su ba. Tayi tunanin zasu zo suyi mata magana akan faɗanta da Hidaya amma bata gan su ba. Har sarki Abbas ta tambaya akan hakan wanda yace zai tura a nemo mata su. Yanzu gashi an kawo mata kan mahaifiyarta a akwati.


Da farko dai ta kasa amincewa da abinda idanunta suke gani. To amma a hankali hoton yaci gaba da shiga kanta. Tabbas wadda ta kawo ta duniya ce. Gatanan a mace tana gani, kowa yana gani. 


Fushi da kiyayya suka danne zuciyarta. A take a wajen kanta yayi tsawa ta zube a ƙasa sumammiya. Kafin ta iya ƙasa yarima mai jiran gado yayi sauri ya tare ta. 


Fadawa suka kora mutane waje, fada ta tashi. Shi kuwa ɗan-aiken a wajen yarima Umaru ya jashi wajen fadar yayi masa hukunci.


Acikin fada kuwa an kewaye Fatima ana yi mata fifita. Da kyar ta farfaɗo. Tana buɗe ido taga mutane akanta. Da farko bata gane mai yake faruwa ba amma a hankali abin ya dawo mata. Tabbas an kashe mahaifiyarta kuma zata ɗauki fansa. Akwai lokacin da zata zauna tayi kuka amma yanzu lokaci ne na ɗaukar fansa. Baza ta bari jinin mahaifiyarta ya bushe ba tare da tabi mata hakkinta ba.


Tana miƙewa ta lalubi takobinta sannan tayi ƙofar fita daga fadar. Su yarima sukai ƙoƙarin tare mata hanya su hanata fita. 


Shi kansa sarki bai goyi bayan hakan ba. 


"Ko waye wannan Umuk-li ɗin yana da hatsari," inji sarki Abbas. "Kamata yayi a jira ayi bincike kafin a shigeshi. Mai yake so? Daga ina yake? Ta yaya ya samu nasara akan Zaikid da Kulsum? Idan muka samu amsoshin wannan tambaya sai mu kama shi da hujja."


Fatima ta juyo idanu cike da kwalla. Murya tana rawa ta ce, "bazan iya jira ba, Baba, kayi haƙuri."


Sarki yayi ajiyar zuciya. "To ki bani awa guda kacal na haɗaki da salsa ku tafi tare."


"Idan naci gaba da jira zuciyata zata iya bugawa. Zanyi gaba, su biyoni daga baya." Inji Fatima.


Sarki Maikiro'Abbas ya miƙe. "Bana so ki fita ke kaɗai, Fatima." 


"Ni zan rakata idan sarki ya amince," inji wata murya daga can gefe. Mai maganar ba wata bace illa Hidaya. Jama'a sunyi mamakin ganinta da kuma jin abinda tace, amma Fatima kawai gyaɗa kai tayi ta fice. Hidaya tabi bayanta. 


Sarki ba'a son ransa ya barsu suka fita ba, amma a wannan lokaci babu mai tare Fatima. Da ita da Hidaya suka nufi dajin da Umuk-li ya bayyana za'a same shi acikin wasikarsa. Basu cewa juna komai ba haka suka isa har dajin. Ita fatima bata tambayi dalilin da yasa Hidaya zata rakata ba, ita kuma Hidaya bata tambayi Fatima alaƙarta da wadda aka kashe ba. 


Suna isowa Hidaya ta saka wuta ta ƙone bishiyun kukar da suka rufe dajin. Dajin ya fito fili. Umuk-li da tawagarsa suka bayyana. 


Babu neman ba'asi Fatima ta zare takobi ta afka musu. Hidaya ta take mata baya. 


Umuk-li kawai gefe ya koma ya turo mutanensa aka fara fafatawa.


"Kwana biyu akai ana faɗa," inji Zaikid. "Ina ɗaure a saman bishiya ina kallo bani da damar taimakonsu. A kwana na uku Fatima da Hidaya sukai nasara akan kwamandun Umuk-li. Dole ya shigo da kansa. To amma a lokacin labari yasha banban. An ce tunda akai daular Wilbafos ba'a taɓa samun mai ƙarfin dantsen Umuk-li ba. A wannan lokaci waƙar maƙabarta tana hannunsa. Cikin ƴan mintuna yaci galaba akan Fatima da Hidaya kamar yadda yayi nasara akai na da Kulsum. Yasa aka ɗaure masa su a kusa dani. Abinda kawai ya rage masa shi ne ya tambaya yaji wacece acikinsu wadda na haifa."


Zaikid ya tura bidiyon gaba dai-dai wajen da Umuk-li yake tambayar su Hidaya su faɗa masa wacece ƴar Zaikid.


"Ku fadamin gaskiya," inji Umuk-li. "Wacce acikinku wannan tsohon ya haifa?" 


"Ni ce."


"Ni ce."


Fatima da Hidaya suka amsa a tare. 


Umuk-li yayi murmushi. Ya ƙara tambaya suka ƙara bashi irin amsar farko. Kawai sai ya koma gefe ya zauna suka ci gaba da hira. Fatima da Hidaya suna sakale a saman bishiya kusa da Zaikid, kansu yana lilo a ƙasa. 


Sai da sukai kwana uku a haka. A kowacce rana Umuk-li zai tambaya amma zasu bashi amsa irin wadda suka fara bashi. Daga ƙarshe ya gaji ya yanke shawarar ya kashe su kawai duk su biyun ya huta.


Yasa aka kwanto masa Fatima aka kawo ta gabansa. Ƙarti suka ɗora ta akan itacen da aka kashe babarta, wuyanta yana taɓa jinin daya bushe na mahaifiyarta. Tana ganin gashin mahaifiyarta a ƙasa wanda Umuk-li ya yanke a yayin kashe ta. 


Fatima tayi karaji takai masa wafta. Amma abin mamaki sai taji zaren izzarta ya maƙale yaƙi motsawa. 


"Ni ne magajin Wilbafos," inji Umuk-li. "Sai na yadda za'ai amfani da izza. Ki yi haƙuri ta tafi cikin lumana. Nasan zuwanki duniya ba laifinki bane, laifin iyayenki ne. Amma hakan bazai canja al'amarin ba, samuwarki ta sirka mana jini, ƙarfinmu ya ragu. Abinda zan iya a baya, yanzu bazan iya ba."


Da wannan Umuk-li ya ɗaga takobinsa sama zai sarewa Fatima kai. Sai da ya rage tsakanin takobin da wuyan Fatima bai fi dan taƙi ba. A lokacin takobin ta tsaya cak akan iska. Umuk-li yayi ƙoƙarin dannata amma ya kasa motsa ta. A kusa dashi babu kowa amma takobin ta ɗauki sanyi kamar ana saka mata ƙanƙara. Yayi tunanin sanyin babban sihiri ne saboda haka yayi ƙoƙarin datse izzar duk wani mutum dake wurin, amma hakan bai sa takobinsa ta motsa ba. Dole ya haƙura da sarewa Fatima kai ya saki takobin ya koma da baya. 


Fatima ta ture mutanen dake riƙe da ita ta garzaya wajen da Zaikid yake ta kwantoshi. Sannan ta kwanto Hidaya. Dukkansu suka koma gefe. Zaka iya cewa Fatima ita kaɗai ta gane abinda ke faruwa domin kuwa ba wannan ne karo na farko da tayi arba da wannan fasahar ba. 


Umuk-li baiyi ƙoƙarin hana su tafiya ba domin a lokacin ya fuskanci akwai wata babbar halitta a gurin wadda baya gani. 


Fatima da Hidaya suka riƙe Zaikid wanda ko tsayawa baya iya yi sosai, amma basu yi ƙoƙarin guduwa ba. 


Mutanen Umuk-li suka zare makamansu suka tsaya a bayansa cikin shiri. Yaran cikinsu suka koma cikin tanti suka ɓuya. 


A ɗaya ɓangaren kuma sarki Maikiro'Abbas ne ya bayyana a kusa da Fatima. Abu na farko daya ɗauki hankalin Umuk-li shi ne baya jin yanayin izzar sarki Abbas. Bai san ta ina ya fito ba wanda hakan yake nuna zai iya yi masa illa ba tare da ya sani. 


"Kana nufin kace baka amfani da izza," inji Umuk-li.


Sarki Abbas yaja ɗan numfashi. Yayi daɗewar da a duniya babu wata tambaya da bai taɓa ji ba, har ya gaji da bada amsa. 


"Kayi girman kai, magajin Wilbafos, kuma dole ka karɓi hukunci dai-dai da abinda ka aikata." 


Umuk-li najin haka ya ɓata rai. "Ƙarya kake, ƙaramin jini. Ni ne magajin Wilbafos; izza tawa ce."


Umuk-li ya zare takobinsa ya kawowa Maikiro'Abbas sara. Kafin ya ƙaraso Taidara ya bayyana a tsakaninsu ya tare shi. Ganin Taidara yasa Umuk-li ya jada baya domin yaji ƙanshin izzar gidan Wilbafos a jikinsa. 


Maikiro'Abbas shi ne ya fara magana. "Kai kuma mai ya kawo ka? Kada kace girman kan ka yakai kana ganin zaka iya taimakamin?" Sarkin yaja dogon numfashi ya girgiza kai. "Na rasa meye yake damun mutane irin ku, daga kun ɗan gaji jini mai kyau sai ku ɗauki girman kai kuma ganin kun buwaya kun gagara."


Taidara ya durkusa a gaban Maikiro'Abbas. "Ya kai wannan sarki mai adalci, ba haka nake nufi ba. Ko kokwanto bana yi akan tabbas kafi ƙarfin wannan bawa mai suna Umuk-li. Abinda kawai nake so shi ne a bani dama a matsayin ɗan gidan Wilbafos nayi masa hukunci da kai na. Hakan ya zamo kamar wani biyan bashi akan abinda na aikata a garin Nafada."


Sarki Maikiro'Abbas yayi murmushi. Kana ganinsa kasan bai ɗauki faɗan da muhimmanci ba. 


"Ga ka ga shi," inji sarkin. Ya kuma koma gefe ya bawa Taidara dama suka ware ta da Umuk-li.


Zaikid yayi gaba da faɗan zuwa dai-dai wajen da Taidara yayi nasara. A lokacin Taidara ya kwace littafin takobi daga hannun Umuk-li. Fatima da hannunta ta binne Umuk-li da kwamandunsa. Yaran kuma sarki Abbas yasa aka ɗauke su akan tafi dasu daular maikironomada aka saka su a makarantu. 


"Zaka iya cewa daga wannan rana rigimar gidan Wilbafos tazo ƙarshe," inji Zaikid. "Daga nan Taidara da Fatima suka fara magana. Hidaya da Fatima kuma suka daina faɗa. Abokina Maikiro'Abbas shi ne ya haɗa kansu. Bai ce su auri juna ba, bai kuma ce kada suyi ba, haka rayuwa taci gaba da tafiya tsahon shekaru uku. Har takai Taidara da Hidaya sun zamo kamar haifaffun ƴaƴan maikironomada. Fatima tana ƴar shekara ashirin da huɗu ta amince zata auri Taidara. Hidaya tafi kowa murna da wannan hukunci. Aka raba goron gayyata ƙasa-ƙasa."


Zaikid ya tura masa hoton bidiyon zuwa ranar bikin domin yaga yadda abubuwa suka kasance.

Comments

Most Popular

456

Aiban'zhisu Babban karni!  ************* Tunda Armad ya riga yazo nan to fa bazai koma ba sai ya ɗauki mahaifiyarsa.  "Aiban'Zhisu, babban ƙarni!" Ɗalasimin yana barin bakinsa, jikinsa ya ɗau hasken walkiya. Tun daga kai har ƙafa babu inda baya tartsatsin walkiya. A lokaci guda walkiyar ta fara juyawa tana zagaya jikinsa tana yin sama. A ɗan ƙanƙanin lokaci ta dunkule tayi sama ta fasa ta cikin gajimare ta fice ta ƙara lulukawa sama. Ta wuce Hajarul Ururu ta shiga doron ƙasa na farko tayi sama ta haɗe da gajimare. A lokaci guda da walkiyar take yin sama, wata walkiyar ce ta fita daga jikin Armad tayi ƙasa ta fasa doron ƙasa ta uku data huɗu data biyar data shida data bakwai ta shige ƙarƙashin ƙasa. Sannan kafin wani yayi wani abu sai walkiyar ta fashe zuwa ƙawanyar walkiya dubu a sama doron ƙasa ta farko, sannan wata ƙawanyar dubu a ƙasa doron ƙasa ta bakwai. Kowacce ƙawanya acikin dubun ta rabe zuwa ƙawanya ba adadi suka fantsama suka shiga duniya. Cikin rabin dakika...