Skip to main content

362-365

 "Daga Hidaya Wilbafos ta Farkon Lokaci. Ya kai wannan sarki, ina umartarka daka yiwa gidan Wilbafos mubaya'a ko kuma na karɓe izzata da kake amfani da ita kamar yadda na karɓe ta ƴaƴanka uku."


Sarki ya miƙe tsaye a fusace. "Marar kunyar ƙarshen zamani! A shirya doki. Da kai na zan fita nayi mata ladabi."


Fatima tazo gabansa da sauri ta durkusa. "Baba, ni ka bani dama naje na kawo maka ita a mace ko a raye."


Sarki yayi shiru yana tunani. Baya don ya tura Fatima ita ma ta faɗa komar maƙiya. Amma kuma ya yadda da karfin izzar Fatima. Yana da yaƙinin indai ba daga sama za'a sakko ba to baza a iya yin nasara akanta ba. Ya ɗora hannunsa akanta. "Ki je ki kawo min ita a raye. Ina so naji waye ya tsaya mata har da zata ja da marubucin farko."


Fatima ta miƙe ta fice. Babu ko kokwanto a ranta tasan ita ce zatai nasara. 


Acikin wancan gari kuwa Hidaya tana zaune akan gawarwakin data kawar suna hirar da mutumin da tace babanta ne. Babu wani alamun damuwa ko firgici acikin ranta. 


Da yammaci Fatima ta iso ƙofar garin. Tun kafin ta iso ta ɗauki yanayin izzar mutum biyu acikin garin. A hankali ta taka ta shiga cikin garin. Kamar yadda yarima Umaru ya bayyana mutun biyun na zaune akan gawarwakin suna hira. 


Daga inda take tana hango fuskokin mutane da dama data sani. Wasunsu sun fito ne tare da yarima mai jiran gado. Wasu kuma daga baya suka taho bayan da sarki ya bada umarnin a kawo masa kan yan ta'addan a kuma dawo da yarima. Mutane irin su Maikiro Dudu, Maikiro Tina, Lahuna Djinn, kai da dai sauransu.


Dukkaninsu ba wanda yake numfashi. Zuciyar Fatima ta fara tafarfasa, tabbas sai ta ɗauki fansar mutanen ta. Wani abu daya ƙara ƙona mata rai shi ne yarima mai jiran gado data gani yana kwance a ƙasa yana numfarfashi. Babu alamun izza a jikinsa, lamarin da yake nuna an tsinka zaren izzarsa. Ɗan uwanta bazai ƙara sarrafa izza ba. Anyi masa hukuncin da yafi kisa zafi. Tabbas babu sauran sulhu. Ko waye yayi wannan aikin sai ya fuskanci hukunci.


Ta tafi inda yake kwance ta durkusa ta ɗora hannu akan kirjinsa. Sirrin izza ya fita daga hannunta ya shiga jikinsa. Duk da cewa izzarsa bata dawo ba amma ƙarfin jikinsa ya dawo. Ya dagira ya tashi zaune ya buɗe baki zaiyi mata magana amma ta ɗora yatsa akan bakin sa. "Baka buƙatar kace komai, nasan abinda ya faru. Duk wanda ya taɓa muhibbar ka to kamar ya taɓa muhibbar sarki ne."


Da wannan ta taɓa wata jijiya a wuyansa. Kafin ta ɗauke hannu daga wuyansa yayi bacci. Ta buɗe jakar tsafinta ta cilla shi ciki sannan ta juyo ta fuskanci mutane biyun da sukai wannan aiki. Har yanzu basu daina hira ba. Bata jin yaren da suke yi amma tasan da ita suke. 


Daga inda take ta kaɗa ɗan yatsanta na dama. Wata ƴar ƙaramar wuƙa ta bayyana a hannunta. A wani salo na tsananin kwarewa ta jefe su da wuƙar. 


Hidaya da namijin sukai tsalle gefe suka kaucewa mata. Inda wuƙar ta dira yayi bindiga kamar an tashi nakiya. Fatima ta zare takobinta tayi kansu. Kafin ta ƙarasa namijin yayi tsalle gefe ya bar Hidaya wadda ta zare takobinta tayo kan Fatima. 


Takubbansu suka haɗu a tsakiya. Wata ƙara ta tashi mau ɗaukan hankali da tartsatsin wuta sukai sama. Ƙasa ta fara girgiza, sama tana juyawa. Fatima da Hidaya su kayi tsalle baya suna kallon juna. Bayan dakika biyar suka ƙara yin tsalle suka afkawa juna. A wannan lokaci takubbansu na haɗuwa ƙasa ta dare gida biyu, a ɓangaren Fatima ƙasar tartsatsi ta fara tana aman walkiya, a ɓangaren Hidaya kuwa ƙasar kamawa tayi da wata irin wuta baka-kirin. Hayakin ta baƙi, tokar ta baƙa, tana amo tana ƙara baƙi. Nan take yanayin garin ya sauya daga sanyi zuwa zafi. Sai ka rasa gane wane ɓangare ne yafi zafi. Shin ɓangaren Fatima ne wanda yake ci da walkiya, ko kuma ɓangaren Hidaya wanda yake ci da baƙar wuta? 


Kai kace masifar bata isa haka ba, kawai sai walkiyar dake bayan Fatima ta cure a waje guda tayi sama ta haɗe da sararin samaniya. A ɗaya ɓangaren baƙar wutar dake ci tayi sama ta haɗe da sararin samaniya. Matan biyu suka ɗaga takubbansu sama, walkiyar ta haɗu da takobin Fatima a yayinda wutar ta haɗu da takobin Hidaya. Suka jada baya suka kaiwa juna sara. Haɗuwar takubbansu ya sa sama ta dare gida biyu; a ɓangare ɗaya walkiya, a ɗayan ɓangaren wuta. Ko wane bangare yana ƙoƙarin cinye ɗan'uwansa. 


A wannan rana zaka iya cewa duk wanda ke rayuwa a doron ƙasa ta biyar (sashin arewa) sai da yaga abin al'ajabi. Fatima da Hidaya suka ci gaba da kaiwa juna sara ta ko'ina, tsawon awa guda ba tare da sun gajiya ba. Sama tayi jajawur tana rugugi. Da dama mutane sunyi zaton azaba ce zata sauka. 


Shi kuwa namijin dake tare da Hidaya yana gefe yana kallo babu ko alamar zai shiga faɗan. Awa guda da fara faɗan suka tabbatar amfani da aljani bazai saka suyi nasara ba. Dole suka rabu suka ja da baya suna haki. 


Fatima ta dubi Hidaya ta ce, "na gane dalilin da yasa ki kayi nasara akan yarima, amma ki sani kin zo in-taha, bazan bari ki ci gaba da yaɗa ɓarna aban ƙasa ba."


Hidaya kawai murmushi tayi ba tare da ta bata amsa ba. 


"Shaibal-shísu!"


Fatima ta kira babban ɗalasimi. Ta ja da baya tayi taku bakwai, sannan ta dawo gaba da taku bakwai. Koda kafarta ta taɓa ƙasa a taku na ƙarshe sai kayan jikinta suka ɗau haske. Tayi tafiya a cikin lokaci ta bayyana a gaban Hidaya. Kafin Hidaya ta ankare takobin Fatima ta sauka a kafaɗarta ta dama. Ƙarar saran kamar an sari dutse. Hidaya tayi ƙoƙarin zamewa ta zille amma kafin ta iya yin hakan takobin Fatima ta ratsa ƙashinta, jini ya fara zuba a ƙasa. 


Hidaya tayi tsalle baya domin ta samu sa'ida, amma kafin ta dira a ƙasa Fatima ta ƙara yin taku bakwai tayi tafiya acikin lokaci ta bayyana a gabanta. Ta kai mata sara a ɗaya kafaɗar. Hidaya ta ga tashin takobin, kuma tasan a kafaɗarta zata dira, hasalima tasan abinda zai faru idan takobin ta dira, amma duk da haka ta kasa kaucewa. Dole ta haƙura ta barwa Fatima kafaɗar ta sara, a lokaci guda ta kira nata ɗalasimin. 


"Dorawa Abada!"


Tana rufe baki taurari bakwai suka bayyana akan takobinta ta kaiwa Fatima sara. Takobin Fatima na dira kafaɗarta, tata takobin ta dira a hannun Fatima mai riƙe da takobi. 


Jini yayi feshi sama. Wawakeken rami ya bayyana a jikin kowa.


Dolensu suka ƙara ja da baya. Jini na zuba daga jikin kafadun Hidaya. Ita kuma Fatima hannunta dake riƙe da takobi yana zubar da jini. 


"Kece ta farko da kika taɓa zubar da jinin wannan jiki," inji Fatima. "Kinyi kokari wajen bawa Kanki horo." 


"Kalmomi na kika faɗa," inji Hidaya. 


Su kayi shiru suna kallon juna babu wadda tace uffan tsawon minti guda. 


"Kece Hidaya ta Farkon Lokaci?" Fatima ta tambaye ta. 


Budurwa tayi shiru kamar ba zata bata amsa ba kafin daga bisani ta gyaɗa kai alamun eh. 


"Ki na tunanin Farkon Lokaci zai baki nasara akai na? Ko kuma hakan zai baki dama kiyi abinda kike so?" Inji Fatima.


"Baki fuskanta ba," inji Hidaya tana girgiza kai. "Farkon Lokaci ba wani abu bane da zaki damu dashi. Sunan Hidaya shi ne abinda zaki damu dashi. Domin kuwa shi ne sunan wadda zata halakaki, ta halaka duk wani wanda kika sani, kuma ta turmuza hancin wannan sarki naki mai biyayya ga Ururu."


A lokaci na farko wani duhu ya bayyana a fuskar Fatima. Bata ce komai ba amma kana gani kasan maganar da Hidaya ta faɗa tayi matukar sosa mata rai. 


Hidaya ta ɗaga hannunta sama inda wata sabuwar takobi ta bayyana a hannunta. Ta girgiza takobin sannan ta kai wa zaren izzar Fatima sara. Fatima ta zare tata takobin amma maimakon ta kare saran sai ta kai wa zaren izzar Hidaya sara. Kafin takobin kowa ta sauka sai su kayi tsalle baya suka kauce. Alamun mamaki suka bayyana a fuskar Hidaya.


"Ta yaya kike ganin zaren izza ta?" Inji Hidaya.


"Ke ta yaya kike ganin nawa?" Inji Fatima.


Su kayi shiru suna kallon juna. A lokacin ko wacce acikinsu ta fuskanci da zuri'ar Wilbafos take faɗa domin dai su kaɗai suke iya ganin zaren izza. Amma kuma hakan bai sa sun sassautawa juna ba.


Hidaya ta girgiza takobinta da niyar ta kaɗa izzar Fatima, amma Fatima ko gezau batayi ba. Izzarta tana nan daram-dam babu wani canji a tattare da ita. Ita ma Fatima ta ɗaga tata takobin ta kaiwa shekarun izzar Hidaya sara daga inda take tsaye. Hidaya tana tsaye ba tayi ƙoƙarin kare kanta ba. Ta tsaya a inda take har Fatima ta gama. Shekarun izzarta suna nan babu alamun wani tangarda a tattare dasu. Zaren izzar walwali da kyalli kawai yake, kai kace ƙara masa ƙarfi akai. 


A lokacin dukkaninsu suka tabbatar harin izza bazai aiki akan abokin fafatawarsu ba. 


Fatima ta ɗaga hannunta sama inda wani jan hayaki ya fara fita ta tsakanin ƴan'yatsun ta. Duk wanda yayi rayuwa a wannan zamani yasan wannan hayaki shi ake kira da Negrinki. Bayan minti guda iskar wajen ta koma ja. Daga cikin hayakin takobi ta samu. Fatima ta damƙi takobin ta nuna Hidaya. 


A ɗaya ɓangaren Hidaya ɗaga hannu tayi sama ta samar da Negrinkinta. Sannan ta samar da takobi daga ita. Ta nuna Fatima da takobin. 


Suka ja da baya suka ƙara afkawa juna. Koda takubbansu suka haɗu, sai takobin Hidaya ta karye gida biyu. Rabi na hannunta, rabi ya faɗi ƙasa. Idan ka auna rabin daya faɗi ƙasa da wanda yake hannunta zaka ga basu kai asalin tsayin takobin ba. Hidaya ta kula da hakan amma kafin ta gama tunani Fatima ta ƙara kawo mata sara ta sama. Dole ta yarda takobin dake hannunta tayi tsalle baya. Takobin Fatima ta dira a ƙasa. Ƙasar wajen da takobin ta taɓa ya ɓace ɓat. Wani wawakeken rami ya bayyana a wajen kamar anyi haƙa. 


A wannan lokaci Hidaya ta fuskanci yadda fasahar Fatima take aiki. Duk abinda ta taɓa ɓacewa yake yi. Kamar yadda tsakiyar takobin ta da kuma ƙasar da takobin Fatima ta taɓa suka ɓace. Abinda bata sani ba shi ne ina abinda ya ɓace yake tafiya. Shin kawai ƙonewa yake yi ko kuma wani waje ake kai shi?


Cikin sauri Hidaya ta samar da wata takobin ta tare takobin Fatima. Abin mamaki takubban na haɗuwa sai suka ɓalle gida biyu. Fatima ta tsaya tana kallon takobin ta cikin mamaki. Ta yaya za'a ce takobin ta ta ɓalle? Shin hakan na nufin Hidaya tana da irin fasahar ta?


Ita kuwa Hidaya kawai dariya ta fashe da ita. "Yau na samu sabuwar fasaha," inji Hidaya. "Negrinki na daban ce da duk irin wadda kika saba gani. Indai na taɓa Negrinki da tawa to ina kwafar fasahar dake ciki kamar yadda yanzu na kwafi fasahar ki."


Fatima ta ɓata rai. Bata taɓa tunanin akwai wani mahaluki da zai iya kwafar fasahar ta ba. Amma hakan ba wani abu bane. Har yanzu tana da tsimi a ɓoye.


"Kina tunanin dan kin kwafi fasaha ta hakan zai hana ni samun nasara akan ki?" Inji Fatima.


"A'a," inji Hidaya. "Kwafar fasahar ki bazai hanaki samun nasara ba. Sai dai kash, dama tun can baki da nasara a wannan faɗan. Tun farko banyi niyar gamawa dake bane shi yasa har yanzu ki ke numfashi. Ina fatan idan naci gaba da jan faɗan watakila sarkin daya turo ki ya gaji da jira yazo da kansa. Domin dai ke ba sa'ar faɗa na bace, matsoracin can Maikiro'Abbas shi ne sa'a na."


"Indai ke haifaffiyar ƴa ce ki ƙara kiran sarki na da matsoraci," Inji Fatima tana huci.


"Haha... Matsoraci, matsoraci, matsoraci. An faɗa sarki Maikiro'Abbas matsoraci ne. Ba ke ƴar aike ba ko shi kansa babu abinda zai iya. Idan kina ganin akwai abinda zaki iya to ga fili ga mai doki."


Idanun Fatima sukai jajawur. Ta durkusa ta ɗora hannunta akan kasa. Nan take ƙasar wajen gaba ɗaya ta narke izuwa jan hayaki. Hidaya tayi sauri tayi tsalle baya dan kada ta faɗa rami. Tana dira a ƙasa Fatima ta bayyana a bayanta. Kawai sai ji tayi takobi ta sauka a bayanta ba tare da taga sanda akai saran ba. Takobin ta ratsa har cikin kashin ta. Tayi tsalle gefe amma kafin ta dira Fatima ta bayyana a dai-dai inda zata dira ta kuma ƙara kawo mata wani saran. Ta kauce amma kawai sai ji tayi takobin ta sauka akan kirjinta. Ta ƙara tsalle baya amma kafin ta dira Fatima ta riga ta zuwa. A lokacin Hidaya ta gane lallai akwai wani sihiri da yake aiki a wajen wanda yake rage mata sauri yana ƙarawa Fatima. 


Hidaya ta daka mata tsawa. "Ke ƴar aike! Wane surkulle ki kayi? Saurinki da ƙarfin takobinki bai kai wannan mataki ba. Ki faɗa min mai ki kayi, watakila na tausaya miki idan nazo hukunci."


"Garin surutunki kika faɗi abinda bazan taɓa yafe miki ba," inji Fatima. "Kin kira babana da matsoraci. Kiyi sani kin shigo duniya ta. A wannan duniyar babu wani iko da yake aiki sai nawa. Ƙarfi na bashi da iyaka, ƙarfinki ba komai bane. Lokacinki yayi; idan kina da wasiya to yanzu ne lokacin ta."


Ba tare da bawa Hidaya damar yin magana ba ta ƙara bayyana a bayanta ta kai mata sara. Takobin ta shige cikin tsokar Hidaya. Jini yayi tsartuwa sama ya feshe ko'ina. Hidaya tayi tsalle gefe tana ƙoƙarin danne jinin amma kafin ta dira Fatima ta ƙara bayyana ta kai mata sara. A haka sai da akai sama da sau goma. Hidaya ta kasa kaucewa saran Koda sau ɗaya. A kowanne lokaci sai dai taji saukar takobin a jikin ta, kai kace Fatima tasan abinda zai faru. Cikin kankanin lokaci Hidaya tayi kaca-kaca da jini. Ko ina a jikinta zuba yake. 


A lokacin da dukkan alamu suka nuna Fatima tayi nasara, a lokacin goshin Hidaya ya fara haske, tambarin miyura ya bayyana. Akwai abubuwa da dama a jikin miyurar amma abinda yafi jan hankalin Fatima shi ne wata takobi dake tsakiya tana juyawa da kuma wani hatimi daya kewaye takobin. 


Kafin Fatima tayi wani abu, hatimin ya bazu ko'ina ya rufe jikin Hidaya. Duk inda ya taɓa sai kaga ciwon wajen ya warke sannan kuma a lokaci guda sai kaga zanen hatimin ya ƙara kauri. Cikin dakika goma hatimin ya rufe ko ina a jikinta. Fatarta ta koma baƙa launin hatimin. Ta zira hannu acikin goshinta ta zaro takobin dake cikin miyurar. Da farko takobin ta haske ce kafin daga bisani ta juye ta koma ta baƙin karfe. Zanen hatimin da yake jikinta ya fita daga hannunta ya shiga jikin takobin. Takobin ta fara fitar da wani hayaki. Waƙar izza mai ɗauke da baituka mara sauti ta fara tashi daga jikin takobin. Katangar ƙarfe ta bayyana a bayan Hidaya. Aljanu sha-biyu: shida yara, shida manya suka bayyana akan katangar suna ɗauke da makamai irin na aljanu. Bakinsu a buɗe suna bin waƙar dake tashi daga jikin takobin Hidaya. A lokaci na farko tun yaƙin rukunai biyu waƙar izza ta samu sauti da ambato. 


"Kin cancanta kiga miyura maɗaukakiya," Inji Hidaya. "Amma kiyi sani duk wanda yaga wannan miyura bazai wayi gari ya bada labari ba. Wannan alƙawari ne tsakanina da mahalicci izza."


"Ko mai zaki ce yau sai kin ziyarci lahira," Inji Fatima. "Babu ruwana da alƙawarinki da mahalicci izza. Laifinki kin kira babana da matsoraci, hukuncinki kisa."


Hidaya tayi murmushi sannan cikin murya ƙasa-ƙasa tace, "yarinya bata san wuta ba sai ta taka."


Fatima ta ɓace daga inda take ta bayyana a gaban Hidaya ta kai mata sara. Hannun Hidaya da takobinta suka ɓace daga inda suke suka bayyana a dai-dai wajen daya kamata ace sun bayyana domin kare takobin Fatima. 


Takubban biyu na haɗuwa ƙasar da suke kai ta rududduge ta zagwanye sannan ta ɓace. Fatima da Hidaya suka tsaya akan iska suna kallon juna. A lokacin suka fuskanci cewa lallai ƙarfinsu yazo ɗaya, idan kuwa suka ci gaba da faɗan to akwai yiyuwar duk su biyun su halaka. Amma abin ka da taurin kai irin na mutanen Farkon Lokaci. Ko kaɗan basu tsaya ba, ƙara azama su kayi suka afkawa juna da sara. 


A wannan lokaci ƙarfin saran sama yayi ya wuce doron ƙasa na hudu, ya wuce doron ƙasa na uku, bai sauka a ko'ina ba sai a doron ƙasa ta biyu. Yana sauka ƙasa ta fara girgiza tana darewa. Jami'an kula da girgizar ƙasa suka bayyana a wajen suka fara aiki.


Awa guda suka ɗauka suna aiki kafin su shawo kan girgizar ƙasar. Har sun fara yiwa juna murna, amma a lokacin wata girgizar ƙasar ta sauka a tsakiyar gari. Suka garzaya suka tafi. Sun fara aiki kenan sai aka bayyana musu ga wata girgizar ƙasar can a fadar sarki. Dole rabu gida biyu. Wasu suka ci gaba da aiki anan, wasu kuma suka tafi fada. Sai dai kafin su ƙarasa ire-iren girgizar ƙasar sama da goma sun faru a sassa daban-daban na faɗin ƙasar. Dole aka tsaya aka fara tunanin mai yake faruwa. Ba jimawa manyan masana suka gano dalilin girgizar ƙasar inda suka alakanta shi da faɗan wasu manyan ma'abota izza a doron ƙasa ta biyar. 


Jama'ar gari suka dunguma suka kai kuka ga sarki bisa doron ƙasa ta biyu - Dul'Ururu. Shi kuma ya kira ƴan majalisarsa taron gaggawa. Taron da ya haɗa da Uznu Ururu, Haruta Ururu, Maruta Ururu, da kuma kwamanda Yurba Ururu. 


Da yammacin ranar alhamis sarki Dul'Ururu ya naɗa wakilai suka sakko ƙasa zuwa doron ƙasa ta biyar fadar sarki Maikiro'Abbas. Sanda suka iso an kammala zaman fada amma shugaban tafiyar, kwamanda Uznu Ururu, yasa akai masa iso da sarki. Bayan sarki ya fito kwamanda ya bayyana masa damuwar al'ummar sama akan abinda yake faruwa. 


"Ka bayyana damuwar ku, amma baka bayyana abinda kake so ayi ba," Inji sarki Maikiro'Abbas.


"Sarki Abbas," Inji Uznu. "So muke yi kayi maganin matsalar dake faruwa ba tare da ka jawo mana girgiza ƙasa ba. Yanzu mai kake tunanin zai faru idan girgizar ƙasar dake faruwa a doron ƙasa ta biyu ta zarce sama zuwa doron ƙasa ta farko? Da mu da kai duk zamu iya fuskantar hukuncin babban sarki Kuyurussa'ayi. Saboda haka ya zama wajibi akanka damu ka ɗauki matakin daya dace kafin hakan ta faru."


Maikiro'Abbas yayi shiru yana kallon kwamanda. Bayan ɗan lokaci ya buɗe baki yace, "Na yarda da abinda kace to amma tuni na tura wadda nafi yadda da ita kuma ina da yaƙinin  za tayi nasara. Amma tunda hakan bai samar da sakamakon da kuke so ba, mai zai hana a matsayin ka na babban kwamanda a rundunar Ururu kaje da kanka ka takawa abin birki?"


Kwamanda Uznu Ururu ya yamutse fuska, babu abinda ya tsana irin bil'adam su ringa bashi umarni a matsayin sa na jinin Ururu, to amma wannan wata dama ce daya samu wadda zai kashe Fatima domin ta daɗe tana ci masa tuwo a kwarya. 


"Babu matsala," Inji Uznu. "Daman ba komai ne yasa bana so na shiga da kaina ba sai dan mun riga mun sa hannu akan yarjejeniyar kai ne shugaban doron ƙasa ta uku zuwa ta bakwai. Muna ganin bai kamatu ga mutanen sama su sakko su shiga al'amuran ƙasa ba. Amma tunda kai da kanka ka amince mu shiga to ai kaga baza kai kuka da sakamakon daka samu ba."


Kwamandan ya juya ya fice daga fadar tare da mutum ukun da suka rako shi. Daga nan basu zame ko'ina ba sai wajen da Fatima suke fafatawa da Hidaya. A lokacin da suka isa babu wani gini guda daya rage acikin garin. Komai ya dagargaje ya rushe ya zama fili. Daga nesa idan ka hango wurin baza kace an taɓa yin wani gari ba a wurin ba. Abinda yafi jan hankalin kwamanda shi ne wani namiji dake zaune kusa da wajen da ake fafatawar. Ƙara da rugugin da tartsatsin wutar dake tashi baya damunsa. Yana zaune ya nutsu yana nazarin duk wani motsi da matan biyu keyi. Uznu ya ƙarasa wajen da ake faɗan. Yana matsawa ƙarfin faɗan yana dukansa. Har ya tadda wani rami wanda daga shi babu komai. Ƙasar wurin ta rududduge. Matan biyu suna tsaye akan iska suna kaiwa juna hari. 


Ya ɗan nemi wuri ya tsaya yana jira a kalleshi. Bayan minti biyu babu  wanda ya nuna yasan da zuwansa sai ransa ya fara ɓaci. Dole idan manya suka zo wuri yara su girmama su. Haka shi ma namijin dake zaune bai nuna yasan da zuwansa ba. Yana huci ya ɗaga murya ya daka musu tsawa. "Ku tsaya cak da wannan shashancin da kuke ko kuma ku fuskanci hukunci."


Zaka iya cewa da tsawar daya daka musu da maganar tasa duk dai-dai suke da babu domin kuwa har yanzu babu wanda ya nuna yasan da zuwansa. Girman kai irin na Ururu ya motsa. Babu abinda masu bakaken idanu suka tsana irin ka nuna basu isa ba. Wane na ƙasa su ja da izzar na sama? 


Uznu Ururu ya zare takobinsa ruwan toka ya tashi akan iska yayi kansu. Dai-dai lokacin daya isa, Fatima da Hidaya sun ja da baya zasu afkawa juna, yana zuwa ya shiga tsakaninsu ya nuna Hidaya da takobi. "Watakila ke kina jin magana. Ina umartarki 

da ki jefar da takobinki, kiyi biyayya ga bakaken idanuwa. Idan kuma ba haka ba zanyi miki hukunci dai-dai dana abokiyar karawarki."


A maganarsa bai bawa Fatima dama ba, kana ji kasan akwai wata kullalliya a tsakaninsu.


Hidaya bata bashi amsa ba, kai bata ma nuna tasan yana wajen ba. Tayi kan Fatima da sara ba tare da lura akwai mutum a gaban ta ba. A ɗaya ɓangaren ita ma Fatima azama tayi wajen kawo mata hari ba tare da kula cewa akwai mutum a gaban ta ba. Koda Uznu yaga haka sai ransa yayi matuƙar ɓaci. Ya samar da wata takobin a hannunsa na hagu ya nuna Fatima da ita. Suna zuwa dai-dai wajen da yake tsaye ya kaiwa Hidaya sara da takobin dake hannunsa na dama, sannan ya kaiwa Fatima sara da ɗaya takobin dake hannunsa na hagu. Yayi amfani da fasahar saɓani yaga abinda zasu aikata sannan kuma yayi maganinsa. 


Suna haɗuwa jini yayi tsartuwa sama, jinin da Uznu yana da yaƙinin cewa na Fatima da Hidaya ne, sai dai kuma bai san dalilin da yasa da yake jin zafi a kafaɗunsa ba. Yana dubawa yaga munanan sara a kowacce kafaɗa, jini yana zuba. A lokacin ya tabbatar da cewa rufa-ido su kayi masa domin babu yadda za ai ace shi aka sara. Ya ga abinda zai faru kuma yayi maganinsa, dan mai yasa za'a ce jinin sa shi ne ya zuba? Ga dukkan alamu Fatima da Hidaya basu da lokacin bashi amsa domin a tare suka sa ƙafa suka doke shi gefe. Ya wuntsila ya faɗi a can gefe. Mutum ukun da suka rako shi suka tafi da gudu suna kiran 'kwamanda kwamanda'. 


A ɗaya ɓangaren kuwa faɗa sabo ya dawo tsakanin Fatima da Hidaya. Suka wanzu suna kaiwa juna hari tsawon kwana uku. Koda doron ƙasa ta biyu suka ga girgizar ƙasa bata tsaya ba dole suka ƙara yin aike. Ɗan aiken daya zo yaga halin da Uznu yake ciki bai shiga ba, sai ya koma doron ƙasa ta biyu ya bawa sarki labari. Sarki Dul'Ururu ya taso da kansa yazo ya samu Maikiro'Abbas. Su biyun suka rankayo izuwa filin yakin. Abin mamaki da suka zo suka ga abinda yake faruwa ba suyi gangancin shiga kamar yadda Uznu yayi ba, sai suka koma gefe suna kallo. 


Bayan zuwan wannan sarakuna guda biyu da kwana uku sai wasu baƙin suka ƙara bayyana wanda suka haɗa da Haruta da Maruta da kuma waziri Tadiyraini wanda yazo daga doron ƙasa ta farko. Acikin ƴan kwanakin abinda yake faruwa tuni ya isa zuwa doron ƙasa ta farko wanda hakan ya tilastawa wazirin sakkowa. Amma abin bai tsaya anan ba, kwanaki kaɗan bayan zuwan waziri sai wani ayari yazo daga jami'ar Babila. Sannan wani ayarin yazo daga doron ƙasa ta huɗu. Cikin kankanin lokaci yan-kallo sun taru. Kowa yana ganewa idonsa irin fafatawar da aka daɗe ba'a gani ba. 


Bayan kimanin kwanaki goma yan-kallo suka fuskanci cewa babu wanda zaiyi nasara a wannan faɗan domin dai ƙarfi yazo ɗaya. Amma kuma hakan bai hana faɗan daɗin kallo ba. Idan ta ƴan-kallo ne to aci gaba da faɗan har gaban abada, amma hakan ya saɓa da tunanin Fatima da Hidaya. Kwana na goma sha uku da fara fafatawar aka rabu. Ba tare da sun cewa juna komai ba Fatima tabi Maikiro'Abbas suka koma daular Maikironomada. Ita kuma Hidaya tabi mutumin data kira babanta suka nufi daji. Da masu bakaken idanuwan da shehunnan Babila, dama duk wani mai faɗa aji da yazo kallo babu wanda yayi ƙoƙarin hana su tafiya.


A wannan rana labari ya bazu ko'ina a sassan duniya. Duk inda ka shiga babu sunan wanda ake ambata sai sunan Fatima da Hidaya. Tun ana faɗar gaskiya akan abinda ya faru har aka fara yin ƙari. Wannan ya ƙara wannan ya ƙara, wancan ya ƙara wancan, har aka juya labarin gaba ɗaya ya zama wani iri. Saboda baƙar wutar da take tashi a duk lokacin da Hidaya ta ɗaga takobinta sai al'ummar ƙasa bakwai suka koma kiranta da baƙar wuta. Ita kuwa Fatima da suka rasa sunan da zasu saka mata sai suka koma ce mata AM - Allon-rantsuwar  Maikironomada. 


Har ƙura ta fara lafawa ashe Fatima da Hidaya basu haƙura ba. Da asubahin ranar litinin sha hudu ga wata, Fatima ta fita daga Maikironomada ba tare da sanin sarki ba ta tafi titin Bayajidda inda take jin ƙanshin izzar Hidaya. Tana zuwa ta tarar da ita tare da babanta. Ba tare da neman ba'asi ba suka afkawa juna. Faɗa ya dawo sabo. Ka kace kwabo sun ƙara tara yan-kallo. A wannan karon ma haka sukai kwana goma kafin su rabu.  Sannan suka ƙara haɗuwa a doron ƙasa ta bakwai sashin arewa, garin Jiha. Kai tun suna daɗewa kafin su haɗu sai da takai suna haɗuwa akai-akai. Ya zamanto duk ranar juma'a sai sun haɗu sun fafata. A hankali abin ya zamar musu jiki ta yadda idan ma basu yi ba basa jin dadi. Kowacce acikinsu babu abinda take so illa taci nasara akan yar'uwarta. 


A wannan shekara babu wani mahaluki da yake rayuwa akan doron ƙasa bakwai wanda bai ji labarin wannan fafatawar ba. Wata rana kwatsam Fatima ta nemi Hidaya ta rasa. Ta daina jin yanayin izzar ta kwata-kwata. Tun tana jira har ta fara bi gari-gari tana dubawa amma a banza. Daga baya ta fara biyan matafiya da fatake da masu tukin jirgin ruwa domin su nemo mata ita. Tasa aka zana hotunan Hidaya aka raba su ko'ina a faɗin ƙasa bakwai. Da taimakon sarki Maikiro'Abbas ta saka kuɗin ayrid dubu dari biyar kyauta ga dukkan wanda ya nemo mata Hidaya ko kuma ya bada labarin yadda za'a nemo ta. Haƙanta bai cimma ruwa ba har tsawon shekara biyu. Daga baya dole Fatima ta haƙura ta koma harkokin ta. Amma a kullum tana ƙara fiƙe takobinta da ƙarfin fasahohinta domin shirin kota-kwana. 


Lokaci yaci gaba da tafiya a hankali. A yau ma zaman fada aka fito kamar kullum. Fatima tana tsaye a hannun daman sarki, ƴaƴansa guda uku suna tsaye a ɓangaren hagu. A kullum idan mutum ya kawo ƙara fada, Fatima da ƴaƴan sarki uku sukan canki abinda ya kawo shi. Wani lokacin sukan saka kuɗi akan wanda yayi nasara. Zaka iyacewa tun suna yara suke haka kuma har yanzu basu daina ba. 


Ana gab da tashi daga zaman fada wata budurwa ta shigo cikin fadar. Fuskarta a rufe da audugar Jamsika. Mai gabatar da masu ƙarar ya tambayi wannan budurwa mai ya kawo ta. 


Kafin tayi magana yarima mai jiran gado ya buɗe littafin dake hannunsa ya rubuta; ƙarar mijinta ta kawo. 


Yarima Umaru ya bude nasa littafin ya rubuta: ƙarar maƙotanta ta kawo. 


Yarima Abba, wanda shi ne ƙaraminsu, ya rubuta: karar ɗanta ta kawo. 


Fatima wadda ke gefe ta buɗe nata littafin ta rubuta; to ba ƙara ta kawo ba, godewa sarki tazo yi a bisa adalcinsa.


Bayan kowa ya faɗi abinda yake tunani ya kawo wannan mata sai suka zuba ido suna sauraren suji mai zata faɗa.


Matar ta buɗe baki tace, "ya mai girma babban sarki, ya mai girma marubucin farko, ya mai girma na Farkon Lokaci, nazo nemarwa babana auren ƴar ka Fatima."


Fada tayi shiru tsawon dakiku. Babu mai cewa uffan kawai sai kallon-kallo ake. Zaka iya cewa babu wanda yafi kowa kaɗuwa da maganar da matar ta faɗa sama da Fatima. Amma bata nuna a fuska ba. Shi kuwa yarima mai jiran gado da yarima Umaru kawai dariya suka yi. 


Dogarin da yake kula da masu ƙarar ya dakawa matar kara. "Ke yar-talakawa! Karya kike, aiko ki akai, baki isa ki haɗa jini da marubucin farko ba."


Kafin ya rufe baki masu fushi da fushin wani sunyo kan macen da niyyar su cuccubeta su fitar da ita. Babu wanda ya hana su domin kowa ya aminta maganar data faɗa rashin kunya ce. Sai da suka zo kusa sai sarki ya ɗaga musu hannu suka dakata.


"Mai yasa kike tunanin mahaifinki ya cancanci na bashi auren ƴa ta guda ɗaya kacal?"


Matar ta gyada kafada. "Ba lallai ya cancantaba, amma kuma zai iya biyan duk wani sadaki da za'a ɗora masa." 


Maikiro'Abbas ya ɗan haɗa rai kafin yayi murmushi. Tabbas ya gane wadda take magana domin audugar Jamsika bata aiki a kansa. Sai dai kuma har yanzu Fatima da ƴaƴansa basu gane wacece ba. Shin wane ganganci ne ya kawo ta gabansa harma take neman auren yarsa? 


"Amma kinsan ba'a zuwa gaba na da rufin fuska ko?" Inji sarki. "Ina so naji rashin kunya ce tasa kika rufe fuskarki ko kuma rashin sani?"

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...