Duniyar izza nada faɗi. Tarihin ta nada tsayi. Al'ummar ta suna amfana da doguwar rayuwa, kasancewar babu mutuwa har sai izzar ka ta ƙare, indai ba kashe ka akai ba. A irin wannan duniya mai izza shi kaɗai ne mutun; saura kuma bayi ne kawai. Mai izza shi yake kawo tsare-tsare na rayuwa, kuma kowa dole yayi biyayya. Sarki Kuyuru yayi nasara akan gidan Wilbafos, kuma a yanzu tsarin sa ake bi. Zancen ana so ko ba'a so bai taso, dole ne abi abinda yace. Idan a yau wani ya taso yana ji cewa wannan tsari bai yi masa ba, to yana da dama yai shirin yaƙi ya afkawa doron ƙasa ta farko. Zarar kayi nasara to shikenan kai ma sai ka kawo naka tsarin.
A halin yanzu Armad ɗan Taidara jikan Zaikid ya taro yaƙi da doron ƙasa ta farko. A lokaci guda kuma yana yi da Ikenga da Bihanzin. Babu wanda yasan waye zaiyi nasara a wannan yaƙi, amma abu guda da kowa ya sani shi ne dole (a ƙarshen yaƙin) duniya zata canja. Duk wanda yai nasara zai kawo sabon tsari irin nasa wanda ran sa yake so. Mai ƙarfi sai ALLAH ya isa.
A garin Faideba kuwa ba'a jima ba Babara ya haɗe kan abokan gabar su ya tarwatsa su, sannan suka rankaya izuwa cikin gari.
Duk da al'ummar garin Faideba suna zaune cikin ɗar-ɗar, hakan bai hana mutane da dama harkokin su ba. Wani zai iya cewa kamar basu damu da yaƙin ba, ko kuma sun raina shi, musamman duba ga cewa har yanzu ba'a ga rundunar Hanibal ta fito ba.
Kwamandun Armad biyar (Babara, Lamarudu, Iliyasisi, Cokali da Nostaljiya) suka rankaya izuwa cikin garin bayan sun bar rundunar mutun dubu sha biyar dake tare da Lamarudu a wajen gari suna jira.
Suna tafe kan iska sun durfafi babbar fadar garin inda suke jiyo yanayin izzar abokan su. Duk inda suka wuce sai kaga mutane suna ɗaga kai suna kallon su. Amma abin a iya kallo ya tsaya, babu wanda yayi gangancin yi musu magana.
"Wai shin abin baya damun ku? Ya kamata ace akwai sojoji cike fal a garin nan. Koda ace basu san da zuwan mu ba, kawo wannan lokaci yaci ace sun ankara sun kirawo sojojin su. Amma har yanzu shiru. Anya kuwa babu lauje cikin naɗi?" Inji Nostaljiya.
Nan take duk suka amince. Daga sanda aka ce akwai rundunar abokan gaba a wajen garin ka ya kamata ace ka fito da duk sojojin ka domin tarar su. Amma ko Tagwayen-auni mutun dubu ɗaya kacal suka zo dasu. Ina ragowar sojojin yaƙin garin suke? Hanibal sarkin jinzidal ne bawai ƙaramin sarki ba, aƙalla akwai mutun dubu talatin zuwa sama a ƙasan sa.
Babara ya haɗe gira tare da gyaɗa kai. "Nima dai haka na gani. Lallai akwai rina a kaba. Amma mai kuke tunani?"
Daga inda suke suna hango fadar garin a can nesa, amma ko kaɗan ita kanta fadar babu tsaro a tare da ita.
"Ɗayan biyu." Inji Iliyasisi, "kodai sojojin Hanibal basa cikin garin nan kwata-kwata, ko kuma suna nan acikin garin nan sun ɓuya. Idan basa nan to suna ina? Idan suna nan kuma to suna ina? Mai ya hanasu fitowa su yaƙe mu?"
Nan fa aka fara kai komo da hasashe-hasashe, kowa yana faɗar albarkacin bakin sa. Suna cikin haka suka ji wata hamshaƙiyar tsawa mai razanarwa. Ƙura da guguwa mai ƙarfi tai sama ta danna su baya. Ƙasa ta fara girgiza kamar zata tsage. Wata iska mai zafi ta fara sauka daga sararin samaniya. Ba shiri suka ɗaga kai sama, inda sukai arba da ƙatoton dutse yana ci da wuta ya afko musu ganga-ganga zai murƙushe.
Su kai tsalle gefe guda cikin zafin nama. Da ace sunyi gangancin tahowa da rundunar su da tuni labari yasha banban. Domin kuwa a halin yanzu dutsen da suka kaucewa ya fafake ƙasa ya samar da wani wawakeken rami wanda faɗin sa kaɗai yakai zira'i maitan, tsayin sa kuma yakai ƙafa dubu. Kai kace wata tsohuwar rijiya ce. Hayaƙi baƙi mai kauri yana fitowa daga cikin ramin.
Ba wai su kaɗai ba, duk wani mahaluƙi dake cikin garin Faideba wannan tsawa taja hankalin sa. Tagogin gidaje sun girgiza sun kaɗo ƙura waje, ƙofofi kuwa sun ɓaɓɓalle sabida tsabagen girgiza. Idan abinda ya afku a baya bai ɗau hankalin jama'ar wannan gari ba, to a yanzu ya ɗauka.
Nusi, Nazara, kai harma da Inara duk kowa ya hallara. Su Nostaljiya suna gefe. Kowa idon sa akan ramin an nutsu (ƙololuwar nutsuwa) ana jira aga mai zai fito daga ciki.
Suwainah guda shida wanda suka fafata da Inara, Hannibal da kansa duk sun bayyana a wajen. Akwai wani mutun mai ɗan siririn saje da fiƙaƙƙen gemu tsaye a can gefe yana murmushi. Idanun sa farare ne fat: babu baƙin ido aciki kuma babu wani launi sai fari. Wannan mutun idan sukai arba da gama-garin mutun zai ce makaho ne wanda ya rasa ganin sa. To amma manyan ma'abota izza suna gani sun san wannan idanu su ake kira da Sidal'Ururu.
Saɓanin kusan duk wani mutun dake wajen, hankalin Suwainah na kan wannan mutumi tana hararar sa. Shi kuwa yayi funfuris yaƙi kallon ta, yana ta kallon ramin abinsa yana murmushi.
Hanibal yana tsaye a gefe, fuskar sa wasai babu alamun ɓacin rai, haushi, tsoro, ko baƙin ciki. Akwai yiwuwar Hanibal ya san meye acikin wannan ramin.
Nosltajiya dasu Babara sukai tsalle suka koma ɓangaren su Nusi. A halin yanzu zaka iya cewa kwamandu takwas na rundunar Armad sun hallara.
Bayan wucewar ɗan lokaci sai aka fara jiyo motsi daga cikin ramin. Wata sabuwar ƙurar tayo ambaliya ta fito. Dutsen da suka gani da farko ya taso sama a hankali ya fito daga cikin ramin. Akan dutsen akwai wani dattijo mai yawan farin gemu.
Duk acikin kwamandun Armad takwas babu wanda yasan wannan dattijo banda Babara, Nazara da Nostaljiya. Da Nazara da Nostaljiya sun taɓa ganin sa ne a yayin ziyara da iyayen su suka kai doron ƙasa ta biyu. Shi kuwa Babara yasan wannan mutun farin sani. Sunan sa Dul'Ururu, wanda akafi sani da mafarauci.
Dul'Ururu ya dubi Suwainah ya yamutse fuska. "Na fuskanci maganar su Dumaƙisu gaskiya ce; kan ki yana rawa. Tunda tsohon nan Ibraham Nil ya ɗora miki Miyura shikenan kike wuce gona da iri." Ya juya ya kalli mutumin mai farin ido irin na makafi ya ce, "Kai kuma Ibraham Nil idan ita bata da hankali kai bai kamata ace ka biye mata ba." Dul'Ururu yai tsaki tare da ɗora hannu a goshi.
"Tsoho fa kace?! Kai, Dul'Ururu, har wani kace min tsoho, shekara nawa na baka. Kut..." Inji Ibraham Nil.
Suwainah ta share Ibraham Nil ta dubi Dul'Ururu a hasale ta ce, "Wai Kawu dan ALLAH me nayi? Babu wanda na kashe har yanzu, wasa kawai nake yi dasu."
"Amma kin san ba ƙwari ne dasu ba, garin wasa zaki iya kashe su baki sani ba." Inji Ibraham Nil cikin zaulaya.
Dul'Ururu ya harare shi. "Yi min shiru, Ibraham. Kai ma ba kwari ne dakai ba."
"Ah.. wariyar 'launin ido' kuma za'a nuna min? Bari na barka da ita to."
"Dama dai yafi. Kaje kaci gaba da aikin ka yafi maka shiga abinda ba'a saka ba." Inji Dul'Ururu kafin ya juyo kan su Nostaljiya ya fara bayani. "Mazauna ƙasashen ƙasa, inai muku sallama irin taku. Kuyi haƙuri da abinda ƴaƴana na suka aikata muku. A addinin mu bama yaƙar kowa idan ana kamfen. Shi saƙo idan yazo dole ka bawa bayi dama suyi tunani kafin su yanke shawara. A sani na basu gaya muku saƙon ba, ballantana su nemi amsar ku, hakane?" Yai shiru na ɗan lokaci yana jiran amsa kafin ya gaji ya ɗora, "to kuwa idan hakane sunyi kuskure, kuyi haƙuri. Saƙon shi ne kamar haka: rukunin Jinzidal da Amri suna nan daran-dam. Zamu yi kanfen saƙo-da-loko na ƙasashen ƙasa cikin wata uku masu zuwa har sai mun tabbatar kalmar gaskiya taje wajen kowa. Daga nan zamu ɗauki wata biyu domin bincikar dukkanin sarakuna ɗari da bakwai dake mulki a ƙasashen ƙasa. Bayan nan zamu fara hukunci: wanda ya karɓi gaskiya ya tsira, wanda kuma ya bijire ya halaka. Nostaljiya ƴar gidan Nara, faɗi ra'ayin ki naji, zaki karɓi gaskiya, ko kuwa zaki bijire?"
Comments
Post a Comment