Skip to main content

BABI NA 176-183: Nusi-ya

 Babi na 176 : Nusi-ya

***

Fada takai fada. Dogarai dubu na tsaye a ɓangaren dama, dubu na ɓangaren hagu. Dukkansu kansu a sunkuye yake. A can ƙarshen fadar sarauniya Nusi ce zaune kan karaga ta kishingiɗa. A gabanta akwai waziri Saiza wanda ya fito daga jinsin jan Dordor da kuma galadima Naru, mutun mai yawan doguwar haɓa da farin gashi, sai kuma sarkin Bai Rayaya a kusa dashi wanda shima ya fito daga jinsin mutane. 


Daga wajen fadar akwai dubban mutane na tsaye suna jiran hukuncin sarauniya.


Waziri ya umarci ɗaya daga cikin dogaran, "a shigo da mai ƙara na gaba."


Nan take wata mace mai gashi ruwan ɗorawa ta shigo ta zube a ƙasa tayi gaisuwa sannan ta fara bayani. "Suna na Ƙaulatu. Na kawo ƙarar Aburu mai saida nama a kasuwar Ɗandai. Ya siyi saniyata Ayird dubu takwas da ɗari uku da hamsin amma har yanzu wata uku bai bani cikon kuɗin ba."


Waziri ya kalli wani dogari ya ce, "akawo wanda ake ƙara. Yana rufe baki dogarin ya fice. Ba daɗewa ya shigo da ɗan gajeren mutun mai faɗi."


Mutumin ya zube a ƙasa ya risuna.


Waziri ya daka masa tsawa, "faɗi tsakaninka da wannan mata."


Cikin ƙinƙina ya fara bayani yana cewa, "saniyar data siyarmin sace ta akayi, wannan shi ne dalilin da yasa ban biya taba. Amma.."


Waziri ya ƙara daka masa tsawa, "ciniki ya shiga. A hannunka aka sace saniya saboda haka an baka kwana uku ka biya ta kuɗinta ko kuma ka fuskanci fushin Nusi-ya."


[Ana kiran sarautar Nusi da -ya, saboda haka maimakon ace sarauniya Nusi sai ace Nusi-ya]


Nan take dogarai suka ɗauke shi sukai waje dashi aka shigo da mai ƙara na gaba. 


Haka wannan majalisi ya ci gaba da gudana. Amma kana ganin fuskar Nusi kasan hankalinta na wani wajen. Idanuwanta sun ƙara haske sannan kamannin mulki sun bayyana a fuskarta. 


La'asar sakaliya aka kammala wannan majalisi. Karagar mulkin da Nusi-ya ke zaune akai tana da dogayen ƙafafu wanda suka miƙe gudu da gaba, yamma da arewa. Dogarai suka gabato suka kama wannan ƙafafu suka ɗauki Nusi zuwa cikin gidan sarautar.


Waziri, galadima da Sarki Bai suka bi baya kansu a durƙushe.


Bayan an ƙarasa an ajiye ta aciki ɗakin tattaunawa na sirri sai dogaran suka basu waje. Waziri ya fito da wasu takardu na sirri daga aljihunsa ya miƙa su ga Nusi-ya.


Bayan ta karanta ta dube su ta ce, "da gaske ne ranar zaɓar sarkin ikwatora na sashi na shida yazo. Dukkan alamu sun nuna cewa Baƙar-guguwa zata bayyana a sashin cikin wannan wata."


Waziri ya numfasa ya ce, "gaskiya ne, Nusi-ya. Kuma daga cikin wanda zasu taka rawa akwai sarkin sashin na yanzu Ƙaraiƙisu. Da sarkin sashi na huɗu Tambaɗisu da waziri Jilani na sashi na ɗaya. Wannan sune manyan gwaraza da zasu taka rawa amma akwai sauran sadaukai wanda suke ganin karansu yakai tsaiko daga dukkanin sashe shida na Ikwatora. Akwai ƙiyasin mutane maitan ga sunayen a wajen sarkin bai."


Waziri ya ƙara durƙusawa sannan cikin ladabi ya ce, "Mutane suna neman wannan kujerar saboda shugabanta kamar shugaban sashin ikwatora ne. A yau da Nusi-ya zata shiga wannan gasa tayi nasara ita ce zata zamo shugabar sashin ikwatora. Sannan kuma a matsayinki na sarauniya baƙar-guguwa ta riga ta zaɓeki, saboda haka koda bakiyi nasara ba guguwar baza ta ciki ba. Zaki dawo gida lafiya."


Nusi ta tari numfashinsa, "bani da ra'ayi. Babban abinda nake son ji shi ne labarin ƴan aikenmu wanda muka su nemo mana hanyar shiga kurkukun Bango."


Galadima shi aka ɗora akan wannan aiki saboda haka ya risuna ya ce, "sun kawo labari mai daɗi Nusi-ya. Sarki Ƙaraiƙisu yana da hanyar da yake bi kuma sunyi ƙoƙari sun gano wannan hanya. Amma har yanzu basu da tabbashi akan ina zata kaika idan ka shiga. A halin yanzu akwai tsaro da yawa a wajen saboda haka basu iya ƙarasawa kusa ba. Amma zarar aka fara yaƙin neman zaɓen, Baƙar-guguwa ta bayyana hankalin masu tsaron zai koma can saboda haka zasu samu damar ƙarasawa."


Nusi ta tambayeshi, "Mutanena nawa ne a wajen?"


Sarkin Bai ya amsa da cewa, "akwai sarkin yaƙi Barilu da Salsa ɗinsa. Da mai unguwa Shísu da Salsa ɗinsa. Da Inyaya [Takobin-Jini] da salsa ɗinsa."


Dukkan sashi na shida na ikwatora babu wanda yakai wannan mutun uku kwarewa a fannin izza domin kuwa babu wanda a cikinsu bai kan matsayin Sammai ba. Nusi da kanta ta umarci sarkin Bai ya zaɓi wanda suka kowa ƙarfin izza. 


Nusi ta ce, "Ana fara bikin zaɓe zamu je wajen na gani da idona."


Sarkin bai ya zare ido cikin tsoro ya ce, "Nusi-ya da kanki. Idan arnan daji suka kawo farmaki da matsala."


Yana rufe baki shima waziri ya numfasa ya ce, "nima na yadda da sarkin Bai. Akwai hatsari babba a fitarki. Musamman duba ga cewa akwai Arnan-dajin Felis wanda suke tashe. Naji ance karon-battarsu da sarkin sashe na uku baiyi daɗi ba. Hasalima ance sune sukai masa rauni wanda badan haka ba da shima zai taka rawa a zaɓen sashi na shida. Wasu suna ganin wannan arnan-daji Ƙaraiƙisu suke wa aiki amma dai jita-jita ce."


Galadima ya gyaɗa kai alamun amincewa.


Nusi ta daki tebur ta ce, "wai me kuka ɗauke ni? A halin yanzu indai ba mahaluƙin daya shiga wadin Déba ba babu wani mahaluƙi da nake tsoro. Duk wanda yake ganin cinta ya tare mana hanya."


Yanayin dagiya na furucinta da alamun kafiya a fuskarta yasa sukai shiru.


Bayan an tattauna sauran al'amuran mulki galadima ya miƙa mata sunayen mutun maitan da za suka shiga gasar zaɓen gwani da za'a gudanar a sashi na shida. Wanda zasu shiga cikin baƙar guguwa kamar yadda Nusi ta shiga. Wanda ya sami nasara acikinsu ya zama sarki.


Nusi ta karɓi sunayen sannan ta miƙe ta nufi turakarta. Kuyangi ɗari biyu suka kewaye ta. Bayan ta ƙarasa ta zarce wani sihirtaccen tafki inda tayi wanka ta canja kaya. Sannan ta dawo ɗakinta na sarauniya. Girman ɗakin yakai taku ɗari uku a kowanne ɓangare. Ƙanshi da turare kala-kala na tashi. Wani ƙaton gado ya cika rabin ɗakin. Daga jikin bango akwai hotunan mutane uku an zana su. Armad, Cokali da Iliyasis. 


Ta ƙurawa hotunan ido hawaye na zuba daga idanunta. A waje gimbiya ce amma acikin wannan ɗaki budurwa ce wadda ta rasa abin ƙaunarta da kuma ƴan'uwanta. 


Bayan lokaci ta kwanta tana kallon sama. Gabda bacci zai ɗauketa taji motsin takarda acikin rigarta. Takardar da sarkin bai ya bata ta sunayen wanda zasu taka rawa a zaɓe mai zuwa.


Ta zaro takardar da niyyar tayi jifa da ita amma ƙaddara takai idonta kan suna na takwas. IKENGA O. BAYAJIDDA.


Take ta miƙe gumi na kwaranya a wuyanta. Ta kwalawa kuyangar dake bakin ƙofa kira. 


Kuyangar ta shigo ta zube a ƙas.


"Kirawo sarkin bai. Sannan a shirya siddi, zanyi tafiya zuwa sashi na shida." Nusi ta bada umarni tare da miƙewa ta saka alkyabbarta.

***

Babi na 177

***

Ɓangaren Nusi 

[Giwa] sarautace wadda ake bawa babbar kuyangar sarki ko sarauniya a sashin Ikwatora. A mafi yawancin lokaci Giwa na tare da sarauniya kuma ita ce take kula da manyan buƙatun sarauniya da kanta. Ƙananun buƙatu kuma tasa ƙananun kuyangi.


A dai-dai wannan lokaci Giwar Nusi na tafe akan iska ta nufi gidan sarkin Bai. Izzarta na bada ƙanshin Sammai. Duk inda tayi kawai gaisuwa mutane ke bayarwa. 


Ba jimawa ta iso gidan wanda yake madaidaici. An kewayeshi da katanga mai zanen takubba. Masu tsaron gidan na ganinta suka zube sukai gaisuwa.


"A kirawomin sarkin Bai. Nusi-ya na nemansa yanzu-yanzu."


Nan take shugaban masu tsaron ya rankaya amma ko taku bakwai baiyi ba sarkin Bai ya bayyana.


"Ina shirin shiga halwar izza naji yanayin-izzarki saboda haka na rankayo domin naga wanne dalili ne ya kawo Giwa gidana da wannan daren. Ko ta canja shawara ne akan soyayya..."


Kafin ya ƙarasa ta tareshi. Fuskarta nada faɗi kamar kafaɗunta. Muryarta nada kaushi kamar ta maza sannan kuma tana da manyan damatsa da kakkauran hannu. Kana ganinta kasan tayi kama da Giwar gaske. 


Ta dubi sarkin Bai ta ce, "Baiban ka taho Nusi-ya na nemanka."


Baiban shi ne sunan sarkin Bai na gaskiya. Tunda shima ta faɗi sunansa saiya faɗi nata. "Zanshika, wanne dalili ne kuwa zaisa a nemoni a wannan lokaci kodai nayi wani laifi ne?"


Zanshika wadda akafi sani da Giwa ta gyaɗa kai. "Nima ban sani ba amma dai maza ka taho."


Baiban ya ɗanyi jum kafin daga bisani ya amsa da cewa, "Muje zuwa."


Zanshika ta ce, "harka shirya? Ba lalle ka dawo da wuri ba."


"Aini kullum a shirye nake Zanshika. Ina ɗauke da jakar tsafina mai kuma nake buƙata."


Take wannan mutun biyu suka tashi sama suka nufi gidan sarauta. Kafin suje tuni Nusi ta shirya. Cikin duhun dare ta fito ta same su a bayan gida. Sarkin Bai na ganinta ya zube a ƙas ya kwashi gaisuwa. 


Bayan gidan nada duhu sosai sannan kuma a kewaye yake da bishiyun tafasa. Baiban baiyi mamakin ganin Nusi wannan waje ba domin a wajen ne ake yin duk tattaunawarda ba'a son sauran ƴan-fada su ji. Akwai sirri ajikin bishiyun tafasar dake wajen wanda ke tare yanayin-izza. Abinda ya tsorota Baiban shi ne wanne abu ne har yakai girman da za'a kawo shi nan. Nan take jikin Baiban ya fara karkarwa.


Nusi ta dubeshi ta ce, "Ikenga O. Bayajidda, maika sani akansa?"


Baiban ya risuna ya fara jawabi, "yana daga cikin masu taka rawa a zaɓen da za'a gudanar a sashi na shida amma ban san komai akansa ba. Ance dama ya daɗe yana shiri kuma shi ne shugaban arnan dajin sashin ikwatora."


Nusi tai dogon numfashi tare da gyaɗa kai ta ce, "Muje ƙofar Eycigan ina so naga wannan mutun mai suna Ikenga O. Bayajidda."


Baiban da Zanshika suka kalli juna cikin mamaki. Menene alaƙar Nusi-ya da wannan mutun? Sannan wannan babbar tafiya ce wadda ya kamata ace an haɗa runduna mai yawa an tafi da ita amma mai yasa Nusi take son su tafi su uku. 


Muryar Nusi ita ce ta katse musu tunani, "Bana so kowa yasan nayi wannan tafiya. Nabar waziri jiran gari saboda haka muyi azama."


Nan take Zanshika ta koma ɓangaren dama shi kuma Baiban ya tsaya a ɓangaren hagu suka saka Nusi a tsakiya domin kariya. Bayan sun rufe fuskokinsu suka rankaya izuwa ƙofar Eycigan dake sashin. 


Sannu a hankali suka iso. Baiban yaje wajen masu tsaron ya biya Ayrid maitan aka basu shaidar shiga. 


Ɓangaren Ikenga

Sashi na shida na Ikwatora shi ne sashi mafi girma da ƙawa. Akwai manyan gine-gine wanda suka daɗe shekara da shekaru amma suna nan kamar kullum basa tsufa.


Akwai miliyoyin mutane da Dordor suna harkokinsu na yau da kullum. Kasuwanni na ci kamar kullum saima abinda yai sama sabida shirye-shiryen zaɓe da ake. Da dama daga cikin mutanen wannan sashi suna jin daɗin mulkin saiki Ƙaraiƙisu bayan shekara sama da sittin da yayi yana mulki. Kuma da damansu suna so ya zarce. Wannan ne yasa duk inda ka shiga zaka ga zanensa ana tallata manufofinsa. 


Daga ɓangaren arewa na wannan sashi akwai garin da ake cewa Landir. Acikin wannan gari aka sauki dukkan masu adawa da mulkin Ƙaraiƙisu wanda suke ganin ya kamata a canja. Akwai sarki Tambaɗisu na sashi na huɗu da waziri Jilani na sashi na ɗaya. Da kuma sauransu. Domin mutanen sashin Ikwatora suna ganin babu waɗanda suka isa suja da sarki Ƙaraiƙisu sai waɗannan. Shi dai sarki Tambaɗisu jinsin baƙin Dordor ne mai kai tara. Tuni yakai matsayin wadin Deba kuma ana ganin babu wanda ya kaishi ƙarfin izza dukkanin sashin sai Ƙaraiƙisu. Shi kuwa waziri Jilani hatsabibi ne masanin taurari wand ake ganin shi kaɗai ne yasan sirri da asalin Baƙar-guguwa. An rawaito cewa shi ne ya fara cewa Bakar-guguwa zata bayyana a sashi na shida na ikwatora kuma mace ne zatai nasara. Kuma hakan ta faru Nusi tayi nasara.


To amma banda wannan mutun biyu akwai Ikenga wanda babu wanda yasan asalinsa ko kuma daga inda yake. Da dama kamar sarkin Bai suna ganin asalinsa arnen daji ne shi yasa ba'a sanshi ba. 


Yana zaune cikin wani hotel tare da  basamuden nan mai suna Deniz Ururu da kuma hadiminsa Nara da yaron nan mai idanun Ururu da kuma hadiminsa na biyu wanda ya samo a lokacin daya shiga duniyar ƙasashen ƙasa wato Daidara. Dukkan mutun huɗun na durƙushe a gaban Ikenga wanda shi kaɗai ne akan karaga.


Ana zaune ana tattauna yadda za'ai nasara. 


Deniz Ururu ya ce, "Baƙar-guguwa bazata zaɓe muba. Domin kunsan asalinta da kuma su waye suka halicceta. Hanya ɗaya da zamu samu nasara shi ne mu halaka ita kanta Baƙar-guguwar. Bayan nan saimu sa Deniz Iluru ya kawo mana runduna daga duniya ƙarƙashin ƙasa mu yaƙi sarakunan ikwatora. Duk wanda baiyi amanna ba mu kashe shi."


Wannan yaron mai idanun Ururu ya girgiza kai ya ce, "A'a wannan wahala ce. Ni ina ganin mu kashe Ƙaraiƙisu da Tambaɗisu da Jilani dama dukkan wanda ya fito karawa. Idan mukai haka Bakar-guguwa bata da yadda zatai saita zaɓemu."


Kana ya kada baki ya ce, "ni ina ganin kawai mu cire kariyar dake kurkukun bango mutanenmu dake ciki su shigo. Kaga ta haka zamu janyo ruɗani mai yawa. Ana cikin ruɗani saimu cimma burinmu."


Daidara ya ce, "munzo sashin ikwatora da niyyar neman mayaƙa. Idan muka kashe musu shugabanni baza su bimu ba. Amma kuma idan bamu kashe su ba baza mu sami abinda muke nema ba. Mai zai hana mu bari su Baƙar-guguwa. Aciki saimu halaka su ba tare da kowa ya sani ba. Ta haka saimu jefi tsuntsu biyu da tsakuwa ɗaya."


Nan take muhawarada cece-kuce ta ɓarke. Kowa na ganin shawararsa ita ce. Ikenga yayi shiru ya kishingiɗa cikin mulki yana tunanin shirinsa. 


Ana cikin wannan hali sadaukin dake gadi a ƙofa ya ce, "ya shugabannina, ga wasiƙa an kawo."


Ikenga ya yamutse fuska. Wannan ya kalli wannan wannan ya kalli wannan. Da farko dai babu wanda suka sani ko ya sansu acikin ikwatora harda zai turo musu da wasiƙa. Babu wanda yasan da zuwansu. 


Ikenga ya tashi cikin sauri ya kwaci wasiƙar. Yana buɗewa yaga ansa DAGA ARMAD WILBAFOS.


***

Babi na 178-180

***



Armad Wilbafos?! 


Ikenga ya ƙara kallon sunan yana jimanta abin a ransa. Lokaci na farko daya fara ganin Armad akan wani kaɗaitaccen tsibiri ne. A lokacin akai ɗan ƙaramin yaƙi kan littafin-takobi. Ikenga baisan yadda akai Armad ya tsira ba amma sun haɗu a gasar Jinzidal inda suka fafata fafatawa mai tsanani. Har wannan rana yanan tunano fafatawarsu da Armad Wilbafos. Sun haɗu acikin kurkukun bango inda yayi masa gargaɗi akan cewa zai gamu da hatsari a shekara mai zuwa. Ya kuma nemi Armad yayi masa mubayi'a domin ya kareshi daga wannan hatsari. 


A zahiri Ikenga baisan haƙiƙanin hatsarin da zai faru da Armad amma yaga tauraruwarsa tana ɗauke da duhun mutuwa. Irin duhun da ake gani idan mutuwa ta kusanci mutun ko kuma wani na kusa dashi. Armad yaƙi yi masa mubayi'a lamarinda yasa kowa yayi nasa waje bayan baran-baran.


Abu na ƙarshe daya ji game da lamarin Armad shi ne Heeda ta bada rayuwarta wajen ceto shi. 


Bai san meye acikin wannan wasiƙarda Armad ya turo masa ba amma yana ji a ransa cewa da matsala. Cikin kasala ya koma wajen zamansa ya zauna sannan ya buɗe takardar ya karanta.


Idan kana so kaji sirrin sashin ikwatora da Baƙar-guguwa ka zo Layin Ɗan-baƙi dake lamba 453 na unguwar Ɗan-ƙaura yau da yamma. Kazo kai kaɗai.


Daga Armad Wilbafos.


Yana gama karantawa ya miƙawa hadimansa takardar suma suka karanta.


Deniz Ururu da wannan yaro mai idanun Ururu da Daidara basu san waye Armad ba. Lokaci na farko da suka fara ganinsa a filin yaƙi ne suna karawa da Uznu Ururu. Kána shi ne kaɗai yasan tsakanin Ikenga da Armad saboda haka ya kwashe labarin dukkan abinda ya faru a baya ya gaya musu.


Wannan yaro mai idanun Ururu yayi wani murmushi mai ɗauke da mugunta da ƙeta ya ce, "Armad Wilbafos? Yayi kama da ma'aboci izza. Ina buƙatar ruhinsa na saka acikin [Taskar-ruhi] na."


Kána ya dakawa masa tsawa ya ce, "B. Ururu, Armad ba wanda zaka ɗauka da wasa bane idan ba haka ba zaka iya rasa ranka."


[B. Ururu na nufin Bayajidda Ururu. Idan mai karatu bai manta ba wannan gidan Bayajidda kafin Amri sunyi auratayya da gidan Ururu. Wannan yaro mai idanun Ururu wanda Ikenga ya ɗakko daga tsibirin Sido-Ururu yana daga cikin jikokin da aka samu daga wannan auratayya. Hakan nema yasa Kána yake ce masa Bayajidda Ururu.]


B. Ururu ya haɗe gira tare da waiwayowa a fusace ya kalli Kána. "Kai tsohon Wilbafos! Kana so ka kare ɗan zuri'arka ko? Na san waye kai Kána Wilbafos kuma nasan imaninka na gidan Wilbafos. Dan ya kashe wancan tsohon banzan Uznu shi ne kake tunanin zai iya dani. Kai sani cewa gidan Wilbafos ba komai bane a idanuna. A yanzu idan sarki Ikenga ya bada dama zan kawo masa kan Armad."


Kána baiji daɗin maganar da B. Ururu yayi masa ba saboda haka ya zare takobi. Shi kuma B. Ururu ya ƙaddamarda idanuwansa suka fara haske. 


Deniz Ururu ya buɗe baki zai daka musu tsawa amma Ikenga ya ɗaga masa hannu daga kwance ya ce, "rabu dasu suyi."


Koda Kána da B. Ururu suka ji lafazinsa sai jikinsu ya ɗau karkarwa. Nan take kowa ya maida takobinsa suka koma suka zauna. 


Bayan ɗan lokaci Ikenga ya ci gaba da cewa, "zanje na gamu dashi ni kaɗai. Kafin na dawo ina so kowa acikinku ya shiga ya samo mana labari akan al'amuran Ikwatora. Kada ku kashe kowa indai bai zama wajibi ba."


Ɓangaren Nusi


Nusi da sarki Bai Baiban da Giwa Zanshika suka bayyana a ɗaya daga cikin ƙofofin Eycigan na sashin ikwatora na shida. Wajen nada ƙatuwar rumfa wanda mutane ke layi suna jira shiga wannan ƙofa. Koda fitowarsu sai mutane suka bisu da kallo musamman ganin cewa fuskokinsu a rufe suke. 


Sarkin ya saki izzarsa ta daki mutanen dake wajen lamarinda yasa duk wani mai shirin kawo musu wargi ya canja shawara. Doka ce sananniya a wannan sashi babu wanda aka yadda yayi tafiya a sama kan iska sai wanda yakai matsayin Sammai. Koda kuwa izzarka takai dubu ɗaya. Mutanen wajen na ganin su Nusi sun tashi sama sun fara iyo kan iska suka ƙara shiga taitayinsu. 


Bayan sunyi nisa da wajen sai suka nemi waje suka ɓuya. Nusi ta ɗakko wani sinadari mai kama da tuwon amala daga cikin jakar tsafinta ta miƙa musu. Suna karɓa suka manna akan fuskarsu lamarinda yasa kamanninsu suka canja. Fuskar Giwa ta sirance tayi duhu kamar tayi shekara bata ci ba. Sannan karan hancinta ya fito ya tsaya kamar na Nusi. Babu tayadda za'ai ka iya gane ta.


Shima Baiban ya koma dattijo mai ƙasumba da ɗoguwar haɓa irinta ƴan kasuwa wanda kuɗi suka zauna musu. Sunan wannan abu Lancí, ɗaya ne daga cikin maganin izza. Kamar yadda aka sani Nusi ta kware kan harkar haɗa magani tun kafin ta shigo sashin Ikwatora. Amma tunda take bata taɓa amfani da Lancí ba saboda haka bata san yadda yake aiki ba. Bayanda taga kamannin daya mayarda su Giwa nan take ita ma ta ɗakko ɗaya ta manna akan fuskarta. Wani ɗan yalon haske ya bayyana kafin daga bisani ya ɗauke sabuwar surarta ta bayyana.


Abu na farko daya afku shi ne kwacewar dariya daga bakin Giwa. 


"Tuba nake Nusi-ya."


Nusi ta daka mata tsawa tai shiru sannan ta waiwayo kan Baiban ta ce, "kaima kayi dariyarka idan zakai."


Baiban ya kasa daurewa ya fashe da dariya amm ba kamar Zanshika ba baiyi ƙoƙarin bada haƙuri. Nusi sarauniya wadda ta iya mulki kuma tasan yadda zata tafiyarda wanda ke ƙarƙashinta. Yasan cewa baza ta hukuntasu akan wannan ɗan abinba. 


Lancí dai baiyiwa Nusi adalci ba. Hancinta ya koma wafcece kamar na botorami. Idanuwanta sun ƙanƙance sun koma loko. Ga wani tayanin-muni ya fito mata ƙatoto. Idan da iya wannan ne ma da da sauƙi to amma gashinta yayi furfura ya ƙanƙance ta tsofe. Ba makawa saita canja formular da akeyin Lancí tana komawa gida.


Suka rankaya izuwa wani hotel mai suna Kaza-fara. Dukkansu sukai rijista da sunayen ƙarya. Da yammaci liƙis Nusi ta tura Baiban ya nemo mata labari akan Ikenga. Bayan awa bakwai ya dawo da sunan hotel da ɗakin da Ikenga ya sauka.


"Giwa, rubuta wasiƙa kice daga Armad Wilbafos."


##


Akwai lokutanda idan Nusi zatai wani abu suke bata shawara akan bai kamataba ko kuma ya kamata amma wannan ba irin wannan lokuta bane. Sun san akwai shirin da Nusi take saboda haka nan take suka rubuta wasiƙar aka turawa Ikenga.


"Da yamma zanje na sameshi ni kaɗai." 


Zanshika najin haka ta zare ido a firgice ta ce, "Nusi-ya, Ikenga mutun ne mai hatsari. Idan sa gaske abinda ake faɗa cewa shi ne shugaban arnan daji bai kamata kije ke kaɗai ba."


Sarkin Bai ya gyaɗa kai alamun amincewa. 


Nusi ta ce, "Ikenga ba shi ne shugaban arnan daji ba. Nasan haƙiƙanin waye shi kuma shi me dalilin da yasa zanje ni kaɗai. Abinda nake so kuyimin ku kula da sauran muƙarrabansa a yayinda muke tattaunawa."


Baiban ya kalli Zanshika sukai ajiyar zuciya amma sun san babj yadda za'ai su canja mata ra'ayi saboda haka sukai shiru. 


Rana tsaka Nusi ta shirya ta nufi layin Ɗan-baƙi dake lamba 453 na unguwar Ɗan-ƙaura wajenda ta ce zasu haɗu da Ikenga. Sai yamma zasu haɗu amma akwai shirye-shirye da zatai a wurin domin taryarsa saboda haka ta fito da wuri.


Da yammaci Ikenga yasa doguwar ƴar shara ya fito daga hotel ɗin da suka sauka ya nufi layin Ɗan-baƙi.


Gabda zai isa sai yaji cikinsa ya murɗa. Ya duba gabas yamma kudu sa arewa yaga babu wata mafaka dazai raɓe saboda haka ya lissafa lokaci yaga akwai ragowar rabin sa'a kafin lokacin haɗuwarsu da Armad Wilbafos saboda haka ya nufi daji. 


Ya tashi sama ya fara tafiya cikin tsananin sauri. Cikin ƙanƙanin lokaci ya iso bayan gari inda ya nufi daji gadan-gadan. Akwai manyan bishiyu na kuka wanda suka tokare da sama saboda girma. A bayansu zai fake ya biya buƙatarsa kafin ya dawo. Ya nufi ɗaya daga cikin bishiyun wadda tafi masa sirri. Gabda zai ƙarasa sai tsigar jikinsa ta tashi. Nan take ya tsaya ya ƙaddamarda idanuwansa na Bayajidda wanda suka fara haske ruwan kore. 


Kibbau bakwai suka taso daga kowacce ƙurya suka nufoshi da mugun nufi suna neman tsireshi. Ikenga ya kira Ruwa ya jiƙa kibban sannan ya daskarar da ruwan izuwa ƙanƙara. Sannan ya saukarda Walƙiya ya mai dasu toka.


[Idan ba'a mantaba aljanin Ikenga yana iya sarrafa ruwan sama da ƙanƙara da walƙiya]


A dai-dai lokaci Nusi na kan wani reshe dake gudu maso gabashin inda Ikenga yake. Tana zaune kwatsam taga reshen yana daddarewa yana rududdugewa. Cikin daƙiƙa ɗaya bishiyar gaba ki ɗaya ta tarwatse rassanta sukai zubo kan Nusi wadda ke cikin faɗowa ƙasa. A dai-dai wajenda zata diro wasu masu da kibbau sama da dubu suka feso kanta suna nufin tsire ta. Nusi ta ɗakko wata kwalba daga cikin jakar tsafinta mai cike da magani. Tana fasa kwalbar wani hayaƙi ruwan kwalba ya feso ya cika wajen. Duk abinda hasken ya taɓa sai kaga ya narke ya zama hayaƙi. Ta haka Nusi ta diro ƙasa lafiya.


Tana dira ta nuna ƙasar dake kewaye da Ikenga. Haka na faruwa sai ƙasar da Ikenga ke kai ta fara girgiɗi, nan take ta dare gida biyu Ikenga ya faɗa ciki sannan ta rufeshi. 


A dai-dai lokacinda ƙasar ta binne Ikenga a lokacin wani mashi ya bayyana akan iska a bayan Nusi zai cake ta. Nusi ta ɓace daga inda take ta bayyana a can gefe. Ɗan wannan dama da Ikenga ya samu da ita yayi amfani ya fito da kansa daga cikin ƙasar data binneshi. Dashi da Nusi suka tsaya suna kallon-kallo. Kowa na jinjina ƙarfin fasahar ɗan'uwansa. 


Zakai tunanin Ikenga zai ɓata rai amma kawai ya fashe da dariya. Bayan daƙiƙa bakwai ya tsaya da dariyar inda hoton Nusi dake gabansa ya ɓace. Mashin daya harbawa Nusi shima ya ɓace. Bishiyar data rududduge ta jefo Nusi ƙas ta dawo yadda take da. Duk abinda ya faru a lokacin ƴar gajeriyar fafatawar da sukai ya ɓace tamkar bai taɓa faruwa ba. 


Ikenga ya numfasa ya ce, "har ace kinyi amfani da fasahar sarrafa tunani kinsa naji cikina ya kaɗa sannan kika saka nazo wannan daji ba tare da na sani ba lallai kin cika hatsabibiya. Mai zai hana ki fito fili muyi magana. Dama ina nemanki, Nusi Kil-zanki."


Nusi ta sakko daga reshen bishiyar data ɓuya akai. Tayi ƙoƙarin shiga tunanin Ikenga domin taga ko yasan wani abu kan lamarin Armad da kuma yadda akai ya shigo sashin Ikwatora amma abin yaci tura. Daga baya tayi ƙoƙarin jawoshi wannan daji ta hanyar saka masa tunanin yaji cikinsa ya lalace. Ta sami damar yin hakan amma kuma gabda zata cimma burinta Ikenga ya gano abinda ke faruwa. 


Haka na faruwa shima Ikenga ya shiga tunaninta ta hanyar saka mata hoton bishiyar da take kai yana rushewa. Ita kuma Nusi ta saka masa tunanin ƙasar da yake kai t dare gida biyu ta binneshi. Kafin haka ta faru Ikenga ya saka mata tunanin cewa akwai mashi a bayanta yana nufin kasheta. Dukkansu babu wanda yayi nasara. Shidai harin tunani haka yake. Inda ka karyashi to komai zai ɓace ya koma gan-gan. Amma idan ka bari ya cika to abinda ya faru a tunanin zai zamar maka gaske. 


Sai dai kuma duk wannan ba shi ne abinda yafi damunta ba. Babban abin shi ne ya akai yasan sunanta Nusi Kil-zanki. Ita kanta bata san ƴar ƙabilar Kil-zanki bace saida ta shiga cikin Baƙar-guguwa. Kaf rayuwarta ta gama tafiya akan cewa ita ƴar ƙabilar Djinn ce. A lokacin data shiga cikin baƙar guguwa a lokacin gaskiya ta bayyana a gareta. Har yau bata san taƙamaiman maike faruwa ba kuma bata san meye dalilin da yasa ta zama Kil-zanki ba maimakon Djinn. Hasalima tun daga wannan ranar har yau bata taɓa bayyyanawa wani wannan sirri ba domin kuwa bata da cikakkiyar masaniyar mai hakan ke nufi. Abinda kawai ta sani shi ne Kil-zanki tsohuwar ƙabila ce wadda sukai wa ƙabilar Wilbafos laifi kafin Amri wanda haka yasa aka halakasu.


Nusi ta canja fuska kamar bata gane abinda ya ce ba. "Wacece Nusi Kil-zanki?"


##


Ikenga yai shiru yana kallon Nusi sama da ƙasa kamar wanda yaga dinare. Har yanzu sabbin kamanin Nusi na Lancí basu canja ba.


Bayan ɗan lokaci ya buɗe baki ya ce, "zaki iya canja kama da murya da yanayin-izza. Amma a gaban idanuna duk wannan bashi da amfani. Indai inason naga abu zan ganshi. Tun a shekarar 1853BA lokacinda na ganki a gasar Jinzidal na gane wacece ke. Amma ban taɓa tunanin kina sashin ikwatora ba da tuni na kawo miki ziyara."


Nusi taci gaba da yi masa kallon bata gane mai yake faɗa ba. Shima Ikenga yasan yana buƙatar babban bayani indai yana so ya janyo Nusi ɓangarensa saboda haka ya ci gaba da jawabi.


"Baƙar-guguwa ita ce sirrin sashin ikwatora kuma ita ce dalilin da yasa hatta Ururu basu da iko kan wannan sashi. Ita kaɗai ce abu ɗaya tak da zai iya yaƙar Kuyurussa'ayi. Nazo wannan sashi naku domin na bautarda Baƙar-guguwa a shirye-shiryena na mulkar duniya. Dani dake Nusi bamu da banbanci da yawa. 


"A ƙarni na farko ƙabilun Wilbafos da Ururu da Shishirui su kaɗai suke da mulki, dukkanmu bayinsu ne wanda bamu da ta cewa. Sunfi kowa ƙarfi sunfi kowa iko. Idan kaji wata taƙaddama a tsakaninsu ne amma mu babu wanda yake ta tamu. Saida akai shekaru sama da dubu goma sannan wannan ƙabilu uku suka gano muna da amfani ta dalilin rashin haihuwa da sukeyi. Idan akai aure tsakanin Wilbafos da Wilbafos, Shishirui da Shishirui ko kuma Ururu da Ururu akanyi sama da shekaru ashirin ba'a haihu ba. Kuma mafi yawan abinda suke iya haifa shi ne ɗa ɗaya. 


"Saboda haka suka gano idan aka ci gaba da tafiya a haka ƙarewa zasu yi cikin ƴan shekaru. Wannan shi ne dalilin da yasa Aldaima ya auri Nára da Kil-zanki duk da ƴan majalisarsa basu amince ba. Wannan kuma shi ne dalilin da yasa Ururu suka auri Bayajidda da Uzzus. Wannan shi ne dalilin da yasa Shishirui suka auri ƴan ƙabilar Djinn. Djinn, Nára, Bayajidda, Uzzus, da Kil-zanki duk ƙananun ƙabilu ne. Amfaninmu a wajensu shi ne kawai mu haifar musu ƴaƴa.


"Amma haƙarsu bai cimma ruwa ba. Dukkan wannan auratayya sai ta ringa zuwa da matsala. Ƴan ƙabilar Shishirui da Djinn sai suka ringa haifo matattun yara. Duk wanda suka haifa koda yazo da rai ba jimawa saiya mutu. Aure tsakanin ƴan ƙabilar Ururu da Uzzus sai ya ringa haifo jini mara ƙarfi. Duk yaran sai kaga basu kai ƙarfin ƴan asalin ƙabilar Ururu ba. Ta haka sai ƙarfin ikon ƴan ƙabiƙar ya fara raguwa saboda haka suka tsayarda auratayya tsakaninsu da Uzzus. Suma ƴan ƙabilar Wilbafos basu samu yadda suke so ba domin sun ringa haihuwar ƴaƴa masu baƙaƙen idanu kamar na Ururu manyan abokan adawarsu.


"Aure biyu ne kacal sukai nasara. Aure tsakanin Bayajidda da Ururu da kuma tsakanin ƙabilar Wilbafos da Kil-zanki. Kai abin bama anan ya tsaya ba, ƴaƴanda aka haifa ta wannan hanya sai suka zo suka fi ƴan asalin ƙabilun Wilbafos da Ururu ƙarfin izza. Amma saboda tsana da girman kai na wannan ƙabilu sai suka zauna sukai shawara cewa wannan hatsari ne ga makomarsu. Suna ganin idan suka barmu wataran zamu kwace mulki daga hannunsu. Tun daga wannan rana ake kashe ƴan ƙabilun mu dani dake. Ƴan ƙabilar Wilbafos su suka kashe kowa naki. Acikin wannan gari na ƙarƙashin ƙasa wanda aka rufe tsahon shekaru ba komai bane illa gawarwakin mutanenki da nawa. Kinsan duk abinda na faɗa haka yake domin kin shiga Baƙar-guguwa. 


"Nida ƙabilar Wilbafos da Ururu sai kisa. Da zan karɓi wata ƴar ƙabilar Wilbafos dana karɓi Heeda a lokacin data taimakeni na wuce garuruwan masu bautar Rana da Wata wato Ƙayyiduba. Ƴan shekarun baya na taɓa yiwa Armad Wilbafos abokinki tayi amma maganata bata kai zuci ba. Addinina bai yadda da kashe mutun ba dalili ba, kinga tunda na bashi dama yayi mubayi'a yaƙi ina da dalilin halakashi a duk sanda muka ƙara haɗuwa. Kiyimin mubayi'a Nusi Kil-zanki. Dani dake ƙaddara ta daɗe da haɗamu tun a ƙarni na farko. Idan kikai mubayi'a zan aureki na maida ke sarauniyar sabuwar daulata dazan kafa. Armad babu abinda zai baki banda baƙin ciki da tsoro, ni ne zan mulki duniya..."


Nusi ta ɗaga masa hannu ta dakatar dashi. "Ikenga Bayajidda. Ban san yadda akai kasan wannan labarai ba duk da baka shiga cikin Baƙar-guguwa ba, amma ina mai tabbbatar maka da cewa ni Nusi ni zan dafawa Armad Wilbafos ya zama sarki koda kuwa zan rasa raina. Domin na yadda dashi."


Ikenga ya haɗe rai yana kallonta cikin mamaki. Bayan ɗan lokaci ya ce, "ni zan zama sarkin Ikwatora kuma ni zan bautarda Baƙar-guguwa. Armad na can cikin kurkukun bango, ƴar'uwarsa Hidaya ta daɗe da riɓewa a kabari. Kina tunanin zai iya ja dani? Ki canja tunani ki daina yi kamar jaririya. Dama nake baki saboda abinda ƙabilarsa suka aikatawa ƙabilarki. Amma..."


Nusi ta daka masa tsawa. "Na gaya maka, Armad ɗan'uwana ne, ruhina ne. Idan ka taɓa shi ni ka taɓa. Indai kana son sashi na shida na ikwatora su baka haɗinkai babu ruwanka dashi."


Koda jin haka sai fuskar Ikenga tai baƙi. Dukkan wani annuri ya ɗauke. Wasu sarakuna shida na haske suka bayyana a bayansa. Abin mamaki ɗaya daga cikin sarakuna bakwan dake bayan Ikenga siffar Amraikugyu ce dashi.


Ikenga ya dubi Nusi ya ce, "Na daina barin ragowar yaƙi, duk wanda baiyi mubayi'a ba mutuwarsa tazo." 


Yana rufe baki ya zare takobinsa sannan ya kira [Shaibal-shísu].


Nusi ta daki jakar tsafinta ta fiddo da wani tafkeken tanderu na dafa magani. Tanderun na bayyana ƙanshin magani ya cika wajen. Nusi ta zaro muciyar tsafi daga cikin jakar tsafinta ta fara daka magani, amma fa na yaƙi.


Samaniya tai duhu sannan hadari ya haɗo. Karawar manyan ma'abota izza a sashin ikwatora. 


***

Babi na 181-183

***

Ikenga ya ce a ransa, *Yaro bai san wuta ba saiya taka...*


Ga dukkan alamu Ikenga da gaske yake domin kuwa maimakon yayi amfani da ƙaramar fasaha saiya kawai ya zaro takobin maɗaukakiyar takobin nan ta Amraikugyu wato Yura-shíra. Ya kawo mata sara da ƙarfin gasken lamarinda yasa imiska mai kama da guguwa ta tashi. Duk inda takobin ta ratsa sai kaga ya dare gida biyu. Ciyayin dake ƙasa suka ringa tashi sama. 


Tun a lokacin gasar Jinzidal Ikenga ya saba da sarrafa lokaci saboda haka mallakar takobin Yura-shira da yayi babu abinda yayi sai ƙara masa ƙarfi. Dukkan abinda takobin ta taɓa sai kaga ya tsofe tamkar yayi shakara dubu a lokacin. 


Nusi ta saka tanderun maganinta ta kare saran amma bisa mamaki sai kawai tanderun ta tsofe a lokaci guda. Nan take fari-farin tsufa ya bayyana a jikin tanderun wanda a hankali ya juye izuwa tsufa ya fara marmashewa. Kai kace wannan tanderu ya shekara dubu a raye. 


Idanuwan Nusi suka cika da mamaki. Wannan tanderu abu ne wanda ake gadarsa a gidan sarauta na sashi na shida. Anyi masa tsimi da shirye-shirye kala-kala wanda hatta wanda yakai matsayin Deba bai isa ya tarwatsashi a hari ɗaya ba. A lokacin data haɗu da Ikenga shekarun baya ko matakin Sammai bai kai ba. Babu yadda za'ai ace cikin ƴan shekaru yakai matakin Deba ko kuma ma yafi sai dai idan dama can ɓoye ƙarfinsa yake.


Babu lokacin tsayawa ana tunanin saboda haka Nusi ta daki ƙasa da ƙafafunta. Ta kirawo ɗalasimai mafi girma da take dasu sannan ta jada baya. Take ƙasa ta fara darewa wasu matattu suka fara fitowa daga cikin kabari. 


Nusi ta numfasa ta ce, "Ko kasan dukkan duniya kabari ce? Idan zamani ya shuɗe wani ya zo maƙabartun al'ummar zamanin na farko sai su koma gidaje, gidajensu kuma su koma maƙabartu. Idan lokaci ya ƙara shuɗewa sai al'amarin ya ƙara juyawa, babu wata ƙasa ko wani gida wanda ba'a taɓa binne rai aciki ba. Bayajidda kana da fasahar lokaci saboda haka kafi kowa sanin mai nake nufi. Zan nuna maka [Rawar Kil-zanki]."


Ikenga ya haɗe rai tare da ƙara kawo sara. Ɓarangwal na mutane da dordor suka fara tsattsafowa daga cikin ƙasa. Kan kace meye wannan sama da ɓarangwal dubu sun kewaye Ikenga. Duk saransa guda ɗaya saiya maida ɓarangwal ɗari toka amma kuma kafin ya ƙara kai wani saran wasu sun bayyana. 


Nusi ta riga tasan Ikenga yakai wani mataki a fannin izza wanda yaƙarsa baza ta haifar da ɗa mai ido ba amma kuma akwai abinda take so ta gano wanda dole saita ganoshi kafin ta gudu. 


Ta tafa hannayenta tare da Koran wani ɗalasimi a zuci lamarinda yasa ƙirjinta ya fara haske kafin daga bisani wani ɗan ƙaramin allo ya fito daga cikin ƙirjinta. Wannan allo ba wani bane illa allon ruhin Nusi wanda ke cikin Tsarin-ruhinta. Kafin Ikenga ya ankare ta daki fuskar allon lamarinda yasa wani haske mai ɗiso-ɗison baƙi ya bayyana yai kan Ikenga gadan-gadan. 


A karo na farko fuskar Ikenga ta canja, alamun kokwanto da tsoro suka bayyana a idanunsa. Kafin hasken ya taɓashi ya zana wani hatimi akan iska. Hatimin na bayyana hoton Amraikugyu dake bayan Ikenga ya haɗe da jikinsa. A lokacin Ikenga ya dawo da lokaci baya zuwa kafin Nusi ta fito da fito da allon tsafinta. Sai dai kuma kash da Nusi da ɓarangwal ɗinta duk sun ɓace babu su babu alamunsu. 


Ikenga ya cizi harshe sannan ya juya ya ɓace a ransa yana cewa, "meye idan kin sani, ba jimawa zan nunawa duniya wannan sirri kowa ya sani."


Acan wani waje kimanin tafiyar shekaru uku daga inda aka gama fafatawa tsakanin Ikenga da Nusi Nusi ce ta bayyana tana haki, gumi na keto mata daga ko'ina. Wannan haki da gumi da take yi bawai na gajiya bane ba na gano waye haƙiƙanin Ikenga da tayi ne. Kwakwalwarta ta kasa ɗaukan abun. Idan bata nemi waje ta zauna ba lallai kanta zai iya yin tsawa. A duk faɗin duniya mutun ɗaya ne tak ke iya sarrafa lokaci yadda yaga dama. Wannan mutun kowa yasan shi ɗan ƙabilar Bayajidda ne. Mene ne alaƙar wannan mutun da Ikenga? Shin Ikenga shi ne wannan mutun? To amma ya za'ai haka ta kasance? Abin bai kama da mai yiwuwa ba domin kuwa zamaninsu ba ɗaya bane. 


Nan take Nusi ta yanke shawara dole ne Armad yaji wannan labari cikin gaggawa. Tana tsaye Giwa da Baiban suka ƙaraso. Sannan ba tare da ɓata lokaci ba suka rankaya izuwa wajenda su Inyaya takobin-jini suke.


Idan mai karatu Bai mantaba da Inyaya takobin-jini da sarkin yaki Barilu da mai unguwa Shísu su ne mutun uku da aka saka akan nemo hanyar ficewa daga sashin ikwatora. Kowannensu na tafe da Salsa ɗinsa. A tsahon shekarun da sukai su na aiki sun gano hanyar ficewa amma akwai cikas guda biyu. 


Cikas na farko shi ne akwai sadaukan babban sarki Ƙaraiƙisu su na gadin wajen. Barilu da Shísu da Inyaya zasu iya kawar dasu amma kuma babu wanda yake son tsokano fushin sarki Ƙaraiƙisu. Hasalima tuni sarki Ƙaraiƙisu ya haramta zuwa wannan waje ga kowa. 


Cikas na biyu shi ne sarki Ƙaraiƙisu shi ne kaɗai mutuminda ya taɓa yin amfani da wannnan hanya saboda haka babu wanda yasan taƙamaiman ina wannan hanya zata kai mutun. 


Wannan dalilai guda biyu su ne suka sa su Inyaya zaman bincike tsahon shekaru. 


Cikin sa'a biyu Nusi da Giwa da sarkin Bai suka iso wajenda sukai zasu haɗu dasu Inyaya. 


Inyaya mutun ne baƙi kakkaura mai manyan damatsa. Yana sanye da zilaika fara wadda aka tsaga daga ƙasa domin watayawa. Akwai sabuwar guduma ɗaure a bayansa na sheƙi. 


Shi kuma sarkin yaƙi Barilu yana da yawan furfura da gemu amma girarsa siririya ce kamar takobi. Hancinsa ɗan ɗugul ne kamar taguwa. Idan ka haɗa da kaifafan idanuwansa ruwan ƙasa sai kaga yana da siffa mai firgitarwa matuƙa. 


Mutun na ƙarshe shi ne mai unguwa Shisu shi kaɗai mai kamanni marasa jan hankali. Rigarsa fara ce doguwa wadda akaiwa kwalliya da gashin raƙumi. 


Dukkanin wannan mutun uku suna da wasu mutun ukun a bayansu wato Salsa ɗinsu. Sannan kuma dukkaninsu babu wanda bai kai muƙamin Sammai ba. 


Suna ganin Nusi suka zube sukai gaisuwa. "Ranki ya daɗe Nusi-ya, izza naki sarauta taki!!"


Nusi ta gyaɗa kai, "ina ne wajen?"


Sarkin yaƙi Shísu ya amsa da cewa, "tafiyar kwana biyu yamma. Akwai sadaukai ma'bota izza ɗari uku da saba'in na gadi a wajen. Mutun goma daga cikinsu sunkai matakin Sammai ragowar ɗuk Jemai ne da Ƙassai."


Nusi ta ɗanyi shiru kaɗan tana tunani kafin daga bisani ta gyaɗa kai, "muje zuwa."

##


Nan take dukkaninsu suka tashi kan iska suka nufi yamma. Washe gari suka da safiya suka fara hangen tantuna da sadaukai suna rangadi. Bayan sun ƙara matsawa suka sakko ƙasa-ƙasa amma duk da haka basu rage tafiya ba. Ba jimawa suka iso gabda tantinan. 


Nan take shugaban masi rangadin yai musu tsawa. "Ku tsaya a inda kuke ku faɗi me ya kawoku?"


Nusi ta tsaya sannan ta zaro kati daga cikin rigarta ta nuna musu, "ni ce Nusi-ya sarauniya daga sashi na shida. Nazo ne akan umarnin sarki Ƙaraiƙísu."


Koda jin haka sai sukai ƙasa da makamansu. Shugaban masu rangadin ya ƙaraso yayi gaisuwa sannan ya jasu izuwa tantinsa."


Nusi dashi su kaɗai ne suka shiga tantin su kuma ragowar suka jira a waje. Dama abinda Nusi kawai take jira kenan. Suna keɓewa ta shiga tunaninsa ta saƙa masa ƙarya da gaskiya. 


A ƙofar tantin muƙarraban Nusi da masu tsaron wajen na tsaye suna kallon juna. Ɗaya daga cikinsu ya dubi sarkin Bai ya ce, "ban taɓa zuwa sashi na shida ba naji ance akwai sanyi da yawa. Abinci yana araha sannan akwai zaman lafiya da gaske ne?"


Sarkin Bai yai murmushi sannan ya gyaɗa ya ce, "duk wannan aikin Nusi-ya ne. Idan shugaba yana da adalci talaka bazai kwana da yunwa ba."


Sadaukin da yayi tambayar yai shiru yana tunani kafin daga bisani ya ce, "amma kuma naji ance tun daga sanda ta hau mulki ƙarfin yaƙinku yake raguwa. Ance tana bawa abinci muhimmanci sama da takobi. Haka ne?"


Sarkin Bai yai ajiyar zuciya ya ce, "kada ka ringa yadda da duk abinda kaji."


Suna cikin wannan tattaunawa sai Nusi da shugaban nasu suka fito daga cikin tantin suka nufi katangar ruwan dake gabansa wato Bango. Sarkin Bai da ragowar suka bi bayansu.


Suna isowa shugaban masu tsaron ya zaro Ayrid mai mataki na goma ya ɗora akan Bangon. Wani haske ya tashi ya kewaye wajen sannan wajen ya juye izuwa ƙofar Eycigan. 


Ya nuna ƙofar ya ce, "wannan ita ce ƙofar Nusi-ya."


Ragowar masu rangadin suka zare ido suna mamakin mai yasa shugaban nasu ke buɗe ƙofar sirrin wadda sarki Ƙaraiƙisu kaɗai ake buɗewa. Amma sun halinsa saboda haka babu wanda ya furta.


Nusi ta dube shi ta gyada kai sannan ba tare da ɓata lokaci ba ta danna kai su Giwa suka bi bayanta. 


Ganinsu yai dishi-dishi sannan suka ɓace. Babu wanda yasan adadin lokacin da ya wuce kafin ganinsu ya dawo su gansu acikin ƙanƙara a wata duniya ta daban. 


Duniyar Ikwatora.


Armad na zaune idanuwansa a rufe. Kowa najinsa yana ambato sunayen wasu mutane kamar wanda ke wuridi.


"BIHANZIN! DUMAƘISU! DENIZ ILURU! DUL'URURU! MAIKIRO'ABBAS! HAN'IBAL!"


"BIHANZIN! DUMAƘISU! DENIZ ILURU! DUL'URURU! MAIKIRO'ABBAS! HAN'IBAL!"


"BIHANZIN! DUMAƘISU! DENIZ ILURU! DUL'URURU! MAIKIRO'ABBAS! HAN'IBAL!"


Haka Armad ya wanzu yana kiran wannan sunaye tsahon kwana arba'in.


A gabansa akwai Iliyasis, Cokali, Inara, da sauran ma'abota kwangilarsa mutun goma da Babara da Lamarudu Wilbafos. A bayansu akwai runduna ta mutun dubu biyu na tsaye suna kallon Armad idanuwa cike da biyayya da tsoro. A can gefe baya Nostaljiya na tsaye tana kuka. Tana jin kunyar kusantar Armad domin tana ji duk abinda ya sameshi ita ce sila.


Cokali ya dubi Iliyasis a tsorace ya ce, "mai yasa yake ambaton sunayensu??!!"


Iliyasis yayi murmushi ya ce, "sunayen wanda zai kashe ne."


Sarakunan Jinzidal! Ga yariman ƙasa ta farko. Ga sarkin ƙasa ta biyu. Ga Bihanzin mai fasahar Jini-uku da dauwamammen sara. Tsoron dake fuskar Cokali ya ƙaru matuƙa. A taƙaice yaƙin duniya Armad zai taro musu. 


Har yanzu jan Negrinki bai daina ɓulɓula daga jikin Armad ba. An rasa wanda zai ƙarasa kusa dashi. Armad na zaune yana makoki bai buɗe ido ba. Ko a ina mutun yake cikin kurkukun bango zai hangi jan Negrinkin dake tashi daga jikin Armad wanda ya haɗe da sararin samaniya. 


Saboda haka Nusi da muƙarrabanta na bayyana suka hangi wannan jan Negrinki dake tashi suka rankaya sukai wajen. Idan da ƙananun ma'abota izza ne da sun tsaya tsoron wani abu amma a yadda suke a shirye indai ba ma'aboci Deba ne zai bayyana ba babu wanda ya isa ya sha gabansu. 


Ba jimawa suka iso wajen wannan Negrinki. Suka hangi mutanen dake gaban Armad. Take Nusi taji ƙanshin jikin Armad. Idanuwanta suka cika da kwalla. 


Ba tare jiran wani abu ba ta rankaya. Sarkin ya zare ido ya ce, "Nusi-ya ya kamata mu shirya yadda zamu yi koda wani zai taso. Kuma babu san a ina muke ba bamu san su waye waɗannan mutane ba...."


Amma ina Nusi bata saurare shi ba. Kafin su ankare ta isa tsakiyar mutanen. Sadaukan dubu suka zare kwari da baka da takubba. Nostaljiya dasu Cokali suka ɗaga kai sama suna kallon Nusi cikin al'ajabi. Nostaljiya bata san wace ce Nusi ba domin basu taɓa haɗuwa amma take Iliyasis da Cokali suka cika da murna.


Cokali yai tsalle sama ya nufi inda Nusi take yana hawaye. Amma yana isa ya gano Nusi bata ma ganshi ba. Idanunta na kan Armad tana hawaye. Jikinta na rawa ta isa kan dutsen da Armad yake. Saboda zafin Negrinkin dake fita hatta dutsen da Armad ke kai ya koma jajawur. Nusi ko a jikinta ta ƙarasa ta rungume Armad. 


Bayan tsahon lokaci ta ɗago ta riƙe fuskarsa. "Ar...mad... "


Sai a wannan lokaci ta gane Armad bai san inda kansa yake ba. Take ta fuskanci abinda ke faruwa. 


Ta zana wasu ɗalasimai a tafin hannunta sannan ta ɗora hannunta a kan Armad ta shiha cikin tunaninsa domin ta dawo sa Armad cikin hayyacinsa. 


Abu na farko data gani yasa jikinta ya sanƙame.


Armad ne tsaye yana fuskantar RUHIN ƘADDARA da RUHIN MUTUWA da RUHIN LOKACI suna maida yawu. 


Armad ya dubi ruhin lokaci ya ce, "kaima baza ka dawo da Hidaya ba ko? To wallahi fansata har daku. Sarautar da kuka daɗe kuna taƙama da ita zan kwace ta."


Ruhin mutuwa ya tuncire da dariya ya ce, "ina jiranka Wilbafos, ka kai matakin izzar da zaka ci wannan alwashi saika dawo."


Ruhin mutuwa ya juya zai amma ƙofar dayya shigo yaga ta rufe. Ya juyo cikin mamaki da tsoro ya dubi Armad.


Armad ya ɗaya hannunsa sama inda takobi ta bayyana ya dubi ruhin mutuwa ya ce, "waye ya ce zaka iya tafiya duk sanda kaga dama?"

##

Armad ya ɓace saga inda yake ya bayyana a saman ruhin mutuwa sannan ya tsarge shi gida biyu. 


"IZZA GADO NA CE, IDAN BAZA KA DAWO DA HIDAYA BA KA GAMA AMFANI DA IZZA."


Armad ya juyo kan ruhin lokaci dana ƙaddara ya ce, "a yanzu bazan iya kashe ku ba amma kun gama amfani da fasahar izza daga yau. KUYI TAIMAKEKENIYA A TSAKANINKU DANA FARKONKU DANA ƘARSHENKU AKAN KU KASHENI KUGA KO ZAKU SAMU NASARA. Idan kun koma ku gaya musu ina nan tafe."


Ruhin mutuwa da lokaci da ƙaddara suka cije baki amma babu abinda zasu iya yi. Suka ɓace suka koma wajen iyayen gidansu suna jiran ranar da zasu rama abinda Armad yayi musu. 


A dai-dai wannan lokaci Armad ya juyo zai fice daga cikin tsarin-ruhinsa amma ya ga babu ƙofar fita. Shima ya ƙulle kansa. Sai dai yayi kwana arba'in yana neman ƙofar sannan ya ga ruhin Nusi ya bayyana. 


"Ar...mad...."


"Nu....si...."


Nusi ta jawo ruhin Armad ta fito dashi daga cikin wajen.


A lokacin Armad ya buɗe idanunsa yaga Nusi da Ilyasis da Babara da Lamarudu da Nostaljiya dama sauran mutane da dama wanda bai taɓa ganinsu ba. 


Take duk abubuwan da suka faru a yaƙin sarakunan Jinzidal ya fara dawo masa. 


Armad ya jawo hatsaniya a lokacin cinikin bayi shekarun da yawa da suka gabata. Lamarinda yasa aka saka masa kuɗin Ayrid miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar. Ita ma Nostaljiya data shigar masa aka kira ta kotu. Duk abubuwan da suka biyo baya har suka kai ga yaƙin sarakunan Jinzidal da mutuwar Hidaya da sarki Daljari. 


Nan take kan Armad ya fara sarawa yana neman fashewa. Duk abubuwan suka cika masa kai sukai ambaliya suna neman haɗiye masa tunani. 


Nusi ta girgiza shi tana ƙoƙarin farfaɗo dashi. "Armad... Armad.... Kana ji na?"


Ina Armad yai tsalle ya faɗo ƙasa yana ƙaraji. Ya riƙe kai ya nufi wani ƙaton dutse ya buga kansa. Take dutsen ya tarwatse kan Armad ya fara jini. Ko a jikin Armad ya ƙara buga kansa a ƙasa yana ƙaraji. Kawai so yake ya farfaɗo daga mafarkin da yake. Domin lallai bazai yiwu ace yayarsa Hidaya ta mutu ba, dole mafarki ne.


Babara ya taso yana ƙoƙarin riƙe Armad amma Nusi ta ɗaga masa hannu.


Iliysis ya zo kunnen Nusi ya raɗa mata, "idan Armad ya rasa tunaninsa a yanzu hankalinsa zai dusashe har abada. Duk yadda za kiyi ki dawo dashi cikin hankalinsa."


Ana haka Armad ya ɓace daga inda yake ta nufi daji. Nusi ta bishi. Duk bishiyar daya tarar a hanya sai kawai ya bangaje ta ya wuce. Ya kasa sarrafa jikinsa ya koma walƙiya babƴ abinda yake tunawa sai fuskar Hidaya a lokacin da mashi ya cake ta. Da murmushin dake kan fuskarta a lokacin da suka rabu. Da idanunta a lokacin da take dariya. Da lokacin da take goyashi ta tashi sama dashi.


Nusi ta tsaya a gefensa saida ya kwana ya wayi gari yana buge-buge sannan ta riƙe shi. "Ya isa haka... Ya isa haka... Ya isa haka..."


Armad bai jita ba ya fizge zai nufi daji amma fincikoshi ta dawo dashi jikinta. "Ya isa haka nace... Ya isa haka." Tana magana hawaye na kwaranya daga idanuwanta.


"Laifina ne da ban kare ka ba, laifina ne dana tafi ikwatora na rabi dakai. Idan akwai wanda zaka ji haushi ni ce. Idan akwai wanda zaka huce haushinka akansa ni ce. Hidaya bata nan amma ni ina nan... Kuma ba zan taɓa rabuwa dakai... Ko a wuta ko a aljanna."


Armad ya ɗanyi shi ru kaɗan kamar ya dawo cikin hayyacinsa amma kawai ya ƙara fizgewa yaje ya haɗu da wata bishiyar kuka kansa ya ƙara darewa. 


Ganin jinin dake zuba daga kan Armad yasa zuciyarta tai tsawa. Hanya ɗaya ta rage. Tayi ƙoƙarin kada tayi amfani da ita amma babu yadda za'ai. 


Ta ɗora hannunta akan Armad lamarinda yasa ta shiga tunaninsa ta buɗe masa tunaninta ya gani. 


Armad ya tsinci kansa acikin tunanin Nusi. Ya ga shekarun da sukai basu haɗu ba. A kullum Nusi takan fito fada ayi harkokin mulki ta koma gida tayi wanka ta koma turakarta taci gaba da tunaninsa. Da safe kafin ta fita ta kanyi wuturin sunan Armad. Da yammaci takan kira sunansa ƙafa ɗari kafin taci abinci. Da daddare idan zata kwanta tana lazimin sunan Armad har tayi bacci. Ɗakinta babu komai sai hotunan Armad. Dukkanin zuciyarta babu komai sai Armad. 


Watarana Nusi na zaune a turakarta Giwa ta kawo mata wani mutun mai barkwanci domin ya sata dariya. Wannan mutun yayi duk abinda zaiyi amma ya kasa saida ya fara labarun gidan Wilbafos sannan ya kama hankalin Nusi. Tana da mulki tana da sarauta, komai ta samu a duniya amma kawai shi take tunani. Tana da ƴan'uwa, Iliyasisi da Cokali, wanda ta  taso dasu amma duk da sunyi shekaru da dama basu haɗu ba bata sha'awar ganinsu kamarshi.


Armad yasan akwai amana tsakaninsu da Nusi amma bai taɓa tunanin abin yakai matsayin ƙauna ba sai a wannan lokaci daya shiga cikin tunaninta. Ƙololuwar ƙauna irin wadda bata da iyaka.


Nan take zuciyar Armad ta fara nutsuwa. Nusi tai murmushi amma ta kasa cewa komai. A zahiri baza ta iya gayawa Armad abinda ke zuciyarta ba tunda ya ɗauketa matsayin ƴar'uwa amma tunda shi ya gani da kansa da sauƙi. Hakan bai rage kunyar da take ciki ba. 


Shima Armad ya kasa cews komai. Bayan tsahon ya lokaci ya dawi hayyacinsa yaga irin duwatsu da bishiyu daya tarwata da kansa. Ya taɓa fuskarsa yaga jini. Ya tuno Hidaya lamarinda yasa yaja dogon numfashi. 


Ya buɗe baki a hankali ya ce, "Ina zuwa..." Sannan ya juya ya nufi bayan wani dutse.


Nusi tai shiru tana kallonsa kamar ta bari ya tafi amma zuciyarta ta kasa daurewa tai firgigit ta riƙeshi.


"Ina zaka? Koma ina zaka je tare zamu. Duk salon na sakeka ka ƙara tafiya na nemeka na rasa sai bayan shekaru ne. Daga yau har izuwa ranar dazan ja numfashina na ƙarshe bazan ɗauke idanuna daga kanka ba. Ina kallonka komai daɗewa komai tsahon zamani... Na zama Salsan ka daga wannan rana. Kana da ja?"


Armad yai kasaƙe yana kallonta ta riƙe masa kafaɗa da hannu ɗaya sannan ta kama ƙugu da ɗayan.


A lokaci na farko tun sanda aka fara yaƙin sarakunan Jinzidal murmushi yazo fuskarsa. Zuciyarsa tayi sanyi. 


"Ko banɗaki zanje?!"


Nusi ta kalleshi idanu cike da mamaki ta ce, "banɗaki? Ko'ina ne!! Ehe!!!"


Armad yai murmushi ya ce, "muje to."

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...