Armad ya girgiza kai, ya ce, "Ki ajiye Maruta da Haruta a gefe, babban hatsabibin shi ne Dul'Ururu, banda fasahar sa ta sarrafa zamani yana da iko akan baƙaƙen dordor dake rayuwa kan Bango. Yana da ido akan taurari dake yawo a samaniya."
Cikin tantin yai tsit. Kowa yana lissafa al'amarin. Wato yaƙi ne ta fuska uku. Duk wanda ya juya baya shikenan an gama dashi sai dai ya tara a lahira. Kuma Armad yafi kowa damuwa tunda bayan Ikenga da Bihanzin akwai Dul'Ururu a gaban sa.
Idanun Armad suka dawo kan taswirar, ya ɗakko dutse ya ɗora akan doron ƙasa ta biyu. "Idan muna so muyi nasara to dole mu afka wa Dul'Ururu kafin ya ankare; kafin ya gama kamfen ya tattaro kan rundunar sa. A lokaci guda kuma muna buƙatar saka ido akan Ikenga da Bihanzin domin musan mai suke aikatawa, kada wani daga cikin su ya zagayo ta baya ya afka mana da zarar mun juya baya. Waye acikin ku zai je ƙarƙashin ƙasa ya saka mana ido akan Bihanzin? Waye zaije sashin ikwatora ya saka mana ido akan Ikenga, sannan waye zai tsaya ya kular mana da taurari? Aljanu ba abin dogaro bane ballantana mu laru dasu."
"Ni!"
"Ni!"
Mutun uku acikin tantin (Inara, Lamarudu da Babara) suka amsa a tare. Kowannen su ƙoƙari yake ya amsa umarnin Armad.
Ga dukkan alamu Armad ya gama yanke shawara acikin ran sa, domin kuwa babu ko ɓata lokaci ya zaɓi wanda yake so suyi wannan aiki. "Iliyasis, kai zaka je garin ƙarƙashin ƙasa na Shadeniz domin sa ido akan Bihanzin. Idan ka samu dama ka assasa rigimar dake tsakanin Bihanzin da ƴan asalin garin wanda aka ƙulle musu gari, amma kada ka nuna kan ka har sai ranar yaƙin ƙarshe. Babara, kai zaka kula da sashin Ikwatora. Kai ma idan ka samu dama ka haɗa rigima. Kada kabar Ikenga ya nutsu har ya samu damar kawo mana hari."
Da Lamarudu da Inara kowa yana tunanin shi za'a tura ya sa ido akan Dul'Ururu da taurarin sa, amma kawai sai aka ga Armad ya juya ya kalli Ayubu. "Ayubu, kai zaka je doron ƙasa ta biyu. Aikin ka ne ka kula da duk abinda suke yi kuma ka sanar dani. Dole ka maida hankali sosai kan tafiyar taurari, domin a kowanne lokaci Dul'Ururu zai iya canja aniya, yayi wani abin da bamu zata ba."
Ayubu ya turo baki amma bai ce komai ba. Su kuwa Babara da Iliyasis miƙewa sukai cikin ladabi suka saɓi makaman su.
"Mu haɗu a yaƙin ƙarshe, ƴar'uwa." Inji Iliyasisi. Ya dubi Nusi yayi mata murmushi sannan ya fice.
Babara kawai gyaɗawa Armad kai yayi, sannan ya daki ƙasa da sandar sa ya ɓace.
Sauran Ayubu, wanda a halin yanzu idanun kowa na kan sa.
"To, nima nayi nan." Inji Ayubu. Ya fice daga tantin ya ɓace.
Ya rage saura Armad, Nusi, Nostaljiya, Cokali, Inara, Nazara da Lamarudu.
Armad ya juya ya dubi Nazara, ya ce, "saura kai. Yaya shirin yake tafiya?"
Nazara ya gyaɗa kai. "Komai yana tafiya dai-dai. Kusan lokaci yayi ma da zan fara haɗa kan su."
Armad yayi murmushi. "Yayi dai-dai. Kai ma kaje ka fara aiki. Mu haɗu a sa'ar ƙarshe."
Nazára ya miƙe tsaye ya nufi ƙofa. Har ya kusa ficewa ya juyo ya dubi Nusi ya ce, "Nusi, akwai abinda kike da buƙata kiji kafin mu rabu."
Nusi tayi shiru tana kallon sa. Gashi dai sunfi shekaru sha-biyar da sanin juna, amma a kullum Nazara ƙara bata mamaki yake. Gashi ita ce kusan mafi kusanci dashi a halin yanzu tun bayan mutuwar kakan sa, to amma kuma babu abinda ta sani a kan sa. Bayan ɗan gajeren tunani Nusi ta miƙe ta bishi suka fice waje.
Armad ya dubi sauran mutanen dake cikin tantin, ya fara bayani, "Deniz Huhutu shi ne wanda ya ƙirƙiro fasahar da muke nema wadda zata taimaka wajen dawo da Hidaya. To amma shi kan sa Huhutun yana lahira. Zaɓin mu guda ɗaya kacal shi ne mu nemi ƴaƴan sa, nasan tabbas ya bar musu fasahar."
"Ƴaƴan sa kuma? Yana da ƴaƴa ne?" Cokali ya tambaya cikin mamaki.
"Yana da ƴaƴa huɗu." Inji Armad. "Babban su shi ne Deniz YÁbulu, wanda shi ne ya haifi Deniz Iluru, sarkin Jinzidal na yanzu. Mai bin sa shi ne Deniz Yúdusu, sai kuma mai bin sa Deniz WÚyawuya, sai ƙaramin su Deniz CÚrucuru, wanda shi ake cewa Deniz Ururu - wannan basamuden da yanzu yake tare da Ikenga. Tabbas ɗaya daga cikin waɗannan yana da wannan fasaha. Kuma mutun uku daga cikin su duk suna nan da rai, a yadda rijistar Ururu ta nuna. Deniz YÁbulu, baban Deniz Iluru shi kaɗai ne ya mutu. Abinda kawai muke buƙata shi ne mu sami ɗaya daga cikin su mu tambaye shi."
"Armad, bana jin tambaya kaɗai zata sa su bamu." Inji Nostaljiya.
Armad yayi murmushi. "Dama ai bata lallami zamu tambaya ba. Zamu fara da sarkin Jinizdal Deniz Iluru, duk da shi jika ne amma zata iya yiwuwa ya gada. Amma kafin mu tare shi ina so aƙalla mu fara gano inda Deniz Yúdusu da Deniz WÚyawuya suke. Bana so su fuskanci abinda muke so muyi su ƙara ɓuya, idan Iluru bai sani ba kunga dole mu neme su koma a ina suke."
"To amma, Armad, idan Deniz CÚrucuru shi ne Deniz Ururu wanda ke tare da Ikenga, kaga akwai yiwuwar tuni Ikenga yana da wannan sirri." Inji Nusi.
"To ai ko yana dashi bashi da Hidaya. Dan yana da sirrin amma bashi da Hidayar dazai dawo da ita kinga a banza."
Nusi tayi murmushin fahimta.
Bayan ɗan lokaci suka tattare yanasu-yanasu suka fara shirin tafiya.
Armad ya dube su bayan ya kammala haɗe taswirar dake gaban sa, ya ce, "Kun shirya?"
Nusi, Nostaljiya, Cokali, Inara da Lamarudu suka haɗa baki a tare suka ce, "mun shirya a kowanne lokaci zaka iya...."
Kafin su ƙarasa jimlar Armad ya kira sabuwar fasaha.
"AIBAN'SHISU!"
Kawai sai gani sukai duniyar ta ɗauke. Suna buɗe ido suka gan su a ƙofar wani gari. Mutane da yawa na ta shige da fice. Babu wani kokwanto akan cewa wannan babban gari ne. Wataƙila ma ɗaya ne daga cikin manyan garuruwan sarakunan jinzidal, duba ga irin ƙatuwar katanga da makekiyar ƙofar shigar da aka gina.
To amma tambayar ita ce wanne gari ne wannan?
Dukkanin su kowa ya juyo kan Armad. Babu shakka wannan aikin sa ne. Kafin su fara tambaya Armad yayi musu bayani a nutse. "A halin da ake ciki ba muda lokacin ɓatawa muyi tafiya daga sama zuwa daular denizawa dake ƙarƙashin ƙasa. Sabida haka kawai na yanki ƙasa a bakin garin Seerish na Deniz Iluru na maye gurbin ta da ƙasar da tantin mu ke kai." Armad ya ɗanyi shiru yana kallon su, ko kaɗan bai fuskanci kallon da suke masa ba. "Wai meye ne? Baku gane bayanin bane?"
Sukai shiru.
"Meye wai?" Armad ya ƙara tambaya.
Nusi ta buɗe baki zatai magana amma ta kasa cewa komai. "....."
A taƙaice dai Cokali ne kaɗai ya iya buɗe baki ya gayawa Armad dalilin da yasa suke kallon sa kamar sunga aljani.
"Aiban'shisu? Ka.... Ka... yanki ƙasa anan ka maye gurbin ta da ƙasar da muke kai a dajin can?!"
"Eh mana." Inji Armad yana mai gyaɗa kai. Kwata-kwata bai ga abin mamaki aciki ba.
"Haakane." Inji Cokali. Abin ya wuce ya ƙara cewa komai.
Armad ya gyaɗa kafaɗa, ya ce, "Bayan Kaban'shisu da Kaban'zishu, Aiban'shisu ita ce a layi. Akwai Aiban'ZIshu a gaban ta."
Gyaɗa kai kawai sukai, domin kuwa basu da ta cewa. Shirin na manya ne.
Sai dai kuma tuni hankalin masu tsaron ƙofar dake bakin garin ya dawo kan su. Kowannen su da makami. Wasu mashi, wasu takubba, wasu kibbau.
Ga dukkan shirin Armad na kada ya bari Iluru yasan da zuwan su ya ɓaci.
Comments
Post a Comment