Idanunsa suka zaro kamar zasu fito. "Ta kan bango kuka biyo? A'a, ƙaryane, ban yadda..."
Idanun Armad daya kalla yasa nan take ya rufe bakinsa. Baya buƙatar ƙarin bayani.
"Ku tsaya cak a inda kuke!" Inji Armad.
Suka tsaya kikam har su Armad suka zo suka wuce.
Wannan ma'aikata su aka naɗa domin hana mutane wucewa ta wannan guri. Sama da shekaru goma kenan suna wannan aiki amma ko mutun ɗaya basu taɓa gani ba. Dama duk wanda aka turo wannan waje to kamar an turo shi ya huta ne. Babu wani mai hankali dazai biyo ta kan bango domin yazo sashi na farko. Komai tsadar ƙofar Eycigan gwanda ka biya indai a sashin ikwatora ne. Kai ko a wajen ikwatora taimakon Ururu ne yasa jirage suke iya hawa kan bango suyi tafiya lafiya. Idan ba'a mantaba a lokutan ƙarshen shekara Dul'Ururu yakan janye kariyarsa. A dukkan wannan lokuta zaka ga safara bata yiwuwa akan bangon. Ance hatta dordor dake kan ruwan Dul'Ururu suke yiwa aiki. To kaga kenan a sashin ikwatora da babu Ururu babu wata kariya kenan. Duk wanda ya hau sai abinda ya gani.
Wani abu daya firgita ma'aikatan shi ne ance musu su tsaya kuma sun tsaya. Har yanzu basu san dalili ba, kuma sun kasa bijirewa umarnin.
Suna tsaye Zaikid ya karyo reshen bishiya ya saƙa jirgin ruwa. A jikin kowanne reshe ya zana ɗalasimi. Cikin ƙanƙanin lokaci jirgi ya haɗu. Kai tsaye suka ƙara hawa kan bango sukai sama. Sai a lokacin ma'aikatan suka dawo cikin hayyacinsu. Da sauri suka fara jifan su Armad da hare-hare amma tuni aikin gama ya gama. Kan kace kwabo sun ƙule acikin gajimare.
Bayan sunyi nisa, Zaikid ya daki ruwan da hannunsa. Wajen daya daka ya dare gida biyu suka shige ciki.
Ruhin bangon yayi ƙara ya tura su waje. Da sauri suma suka ware ƙarfin ikon su suka danna ciki.
Sashi na farko na ikwatora yana saitin doron ƙasa na biyu. Suna ɓullewa zasu tsinci kansu a doron ƙasa na biyu inda Dul'Ururu yake mulki.
Sannu a hankali suna tafiya har suka iso bakin gaɓa. Abu na farko da yayi musu sallama shi ne katangar ƙarfe wadda ta raba doron ƙasa na biyu dana uku. A yanzu samanta suke gani maimakon a da da suke ganin ƙasanta. Babu wanda ya taka katangar acikinsu, kai tsaye suka tashi sama sukai tafiya akan iska har suka iso dai-dai gaɓar inda doron ƙasa ya rufe ƙarfen katangar, sannan suka diro ƙasa.
A wannan lokaci su Armad sun iso wajen da suke ta ƙoƙarin zuwa.
Daga gabansu kaɗan wata runduna ce ta sadaukai aƙalla dubu. Dukkansu a zube a ƙasa basa motsi. Duk inda ka duba jini ne, da kuma takubba, da masu, da sulke a zube a ƙasa. Ga dawaki sun riga mu gidan gaskiya. Tabbas an gwabza yaƙi a gurin ƴan sa'o'i kaɗan da suka wuce domin har yanzu ƙurar yaƙin bata lafa ba.
Babban abinda yafi jan hankalin Armad shi ne wasu sadaukai uku dake zaune akan gawarwakin suna hira. Armad dasu Zaikid suka tsaya suna kallon wannan sadaukai.
Ganin su Armad, sadaukan suka taso suka nufi inda suke. Shata ya zaro garayarsa cikin shiri. Armad kuwa kawai murmushi ya fara. Ganin haka Zaikid ya tsaya bai motsa ba.
Suna ƙarasowa suka buɗe fuskokinsu. Rafiyan Nazára ne wanda aka fi sani da yarima Niyashi. Ragowar mutun biyun kuma duk babu wanda Armad bai taɓa gani ba. Akwai kwamanda Jan-doki da kwamanda Asifu Ruwan Bala'i wanda dukkansu babu wanda bai taka rawa ta musamman a yaƙin sarakunan jinzidal ba.
"Armad Wilbafos?" Inji kwamanda Asifu. "Har yanzu kana Sammai?"
Armad yayi ɗan murmushi amma bai bashi amsa ba.
Jan-doki matsowa yayi kusa da Armad ya dafa kafaɗarsa alamun jinjina.
Armad ya kalli Nazára kallo mai cike da tambaya.
"Armad, ina ka tafi wata guda?"
Kana jin muryar Nazára kasan sun nemi Armad har sun gaji.
"Fasahar Wilbafosiyan Siwod Dans ce ta aika ni wata guda gaba."
Armad ya kwashe duk abinda ya faru ya gaya masa, sannan ya nemi yaji abinda ya faru dasu Nusi da Nostaljiya.
"Labarin yana da tsayi," inji Nazára. "Amma dole muyi sauri domin saura awa shida kacal su yankewa mahaifiyarka hukunci. Sun gayyato duk wani mai biyayya ga Ururu dake doron ƙasashen ƙasa. Suna Filin-Jiri suna jira."
"Filin-Jiri?" Inji Armad.
Nazára ya gyaɗa kai. "Filin atisaye ne acikin shalkwata. Anan suke so ayi yaƙin. Watakila mu haɗu dasu Nusi a hanya ko kuma su riga mu zuwa."
Yana magana ya juya ya nufi hanyar gari. Suka rankaya suka bishi.
Akan hanyarsu Nazára ya fara bayyanawa Armad abubuwan da suka faru, da yadda akai yazo doron ƙasa ta biyu, da kuma yadda al'amura suka kasance.
"Kasan munyi dakai zanje na tono wasu mayaƙa a maƙabartar garin mu, ko?" Inji Nazára.
Armad ya gyaɗa kai. Nazára yana da shiri na dawo da martabar baba Daljari. A cewar Nazára Baba Dalja yana da wani amini wanda yake iya ɓoye mutane a kabari a zata sun mutu. Wannan amini nasa shi ne ya taimaka masa suka ɓoye wasu hamshaqan mutane a daular rafiya dama wasu dauloli. A cewar baba Dalja duk abinda Nazára yake nema wannan mutane dake cikin kabarin zasu bashi. A wancan lokaci da Armad suke magana da Nazára bai san wanene mutumin da baba Dalja ya kira da amini ba, amma a yanzu bayan tarihin da Zaikid ya bashi yasan wannan mutum ba wani bane illa babansa Taidara. Dama ance Taidara shi ne ya saka Baba Dalja a harkar kasuwancin ɗalasimai a wancan zamani.
"Muna zuwa muka tarar babu kowa a kabarin," inji Nazára. "Wani ya ɗebe su. Amma abin mamakin babu wanda yasan ɗalasimin da za'a iya tashin na cikin kabarin sai ni kaɗai. Ta yaya wani zai ɗebe su? Waye ma yasan dasu?"
"Baka tunanin wanda ya bawa baba Dalja ɗalasimin tun farko shi ne yazo ya tashe su?" Inji Armad.
Nazára yayi shiru yana tunani. "Eh to, hakan zai iya yiwuwa, mutumin daya bashi ɗalasimin zai iya dawowa ya tashe su. Amma ka manta abin ya faru ne tun a wancan zamanin. Zaiyi wuya ace wanda sukai wannan abu da baba Dalja yana raye har yanzu."
"Yana nan raye," inji Armad. A lokacin ya kwashe labarin tawagar matattu ya gayawa Nazára.
"Wai kana nufin mahaifinka Taidara shi ne ya bawa baba Dalja ɗalasimin?"
Armad ya gyaɗa kai.
"To idan kuwa haka ne akwai damuwa. Baka tunanin akwai alaƙa mai ƙarfi tsakaninsu? Ina na cikin kabarin suke yanzu? Idan Taidara ne ya tashe su to mai zaiyi dasu?"
"Wannan sune tambayoyin," inji Armad. "Amma dai yanzu gayamin mai ya faru da nusi. Ina su Nostaljiya? Yaya akai har abin ya zama haka acikin wata guda kacal da bana nan?"
***
Idan muka koma doron ƙasa ta biyu, cikin kurkukun dake shalkwatar Ururu, zamu ga tsaro ya ƙaru.
Ƙatoton ɗakin kurkuku ne wanda aka haska da fitila aci bal-bal. Daga kusurwa ɗaya ta ɗakin wata mace ce durkushe akan gwiwowinta. Hannayenta biyu a ɗaure suke da ankoki a wani yanayi irin na ukuba. An banƙarata ta baya ta yadda babu wani kwakkwaran motsi da zata iya yi.
Idan kayi duba izuwa ɗaya ɓangaren ɗakin zaka ga ƙasusuwa ne zube a ƙasa a jikin ankwa. Ankwar ta daɗe, ƙasusuwan ma sun daɗe sun tsofe, har sun fara zama gari. Ko waye mai ƙasusuwan dai anan ya mutu a ɗaure cikin ankwa. Babu wanda yayi ƙoƙarin kwance shi bayan ya mutu.
Rairayin cikin ɗakin yayi duhu saboda daɗewa da kuma yawan ƙasusuwan da suka narke acikinsa. Kana matsawa kusa zaka ji yanayin shekaru. Lallai an ɗaure mutane da dama acikin wannan daki kafin zuwan wannan mata. Kuma idan ka lura zaka ga akwai wata ankwa a jikin ɗaya bangon wadda sabuwa ce. Zaka iya cewa ba'a daɗe da kwance mutun daga jikinta ba. Watakila ma anan Zaikid ya zauna.
Idan muka koma kan wannan mace zamu ga sanye take da farar riga doguwa wadda tayi baƙi sosai saboda gwagwarmaya. Kanta yana sunkuye yana kallon ƙasa, sannan jikinta baya motsi ko kaɗan ta yadda idan baka lura ba sai kace ta suma, amma indai kasan abinda ake cewa izza to kasan tana nan raye.
A dai-dai wannan lokaci Suwainah ta iso bakin ɗakin ta tsaya. A bayanta akwai ayarin sadaukai wanda suka rakota.
"Fatima Wilbafos?" Inji Suwainah, tana kallon matar.
Matar tayi shiru bata amsa ba.
"Fatima?"
Ta ƙara kwala mata kira. Koda taji bata amsa ba sai ta fashe da dariya.
"Haha... Ko kin haɗiyi zuciya ne?"
Suwainah ta ƙara kyakyacewa. Kurkukun tana ɗaukan sautin muryarta tana bashi amo.
"Ku shiga ku dakko ta."
Nan take ayarin dake bayanta suka buɗe kurkukun suka ƙarasa wajen da matar take. Tunda ƙarfen ankwar Bilak-siton ne basu da damar taɓa shi saboda haka suka saka Gatari suka datse ankokin daga jikin bangon. Maza biyu suka tsaya a ɓangaren dama, biyu suka tsaya a ɓangaren hagu. Kowannensu ya fara ƙoƙarin cuccubar wannan mace su ɗaga ta.
A lokacin ta motsa. Duk su huɗun suka jada baya cikin firgici. Na bayansu suka zare makamansu. Wani namiji mai doguwar haɓa yana karkarwa yana cewa, "kada ku bari tayi magana, zata kira babban ɗalasimi."
Kafin kace kwabo sun kewayeta da makamai. Suwainah ta tako cikin ɗakin suka buɗa mata ta tsaya a gaban matar.
"Kai! Tsoron mai kuke ji?" Ta daka musu tsawa. "Kuna cikin amincin manya masu ɗaukakar bakaken idanu." Ta juya wajen matar. "Ko ki tashi ki taho, ko kuma nasa su ɗauke ki."
A lokacin matar ta ɗago kai. Idanunta cike da kafiya irin ta mutanen Farkon Lokaci. Kallo ɗaya zaka gane Fatima ce mahaifiyar Armad, ƴa a wajen Zaikid.
Fatima ta miƙe a hankali ta tashi tsaye. Ba tare da tace komai ba ta wuce gaba. Suwainah da sauran ayarin suka bita a baya.
Akwai wani ƙaton fili da ɗakuna daga wajen ɗakin da aka kulleta. Akwai fursunoni acikin ɗakunan. Kowanne da laifinsa amma babu wanda yasan tsahon shekarun da kowa ya shafe a wannan waje. Wannan ita ce kurkuku ta uku da muka ga Ururu suna amfani da ita. Ta farko: kurkukun bango; ta biyu: gadar zare; ta uku: wannan kurkuku wadda take babbar shalkwatar Ururu ta doron ƙasa ta biyu.
A hankali Fatima ta wuce suna binta a baya. Ta hau kan matattakala wadda zata fitar dasu Filin-Jiri. Tana tafiya, sautin takunta yana amo acikin barandar. Sannu a hankali suka fara hango hasken waje.
Babu alamun tsoro ko fargaba a tattare da Fatima. Kai kace ba mutuwarta take dosa ba. Haka taci gaba da tafiya. Suna fitowa hasken rana ya haske musu ido. Waje yayi tsit duk da dubunnan mutanen dake tsaye sun jeru sahu-sahu.
Suwainah ta wuce da Fatima kan aba'in da aka tanada domin sare mata kai. Dogon gado ne na karfe. Akwai matattakala wadda tayi sama zuwa gadon da za'a zauna. Anan Suwainah ta ajiye Fatima. Hauni yana tsaye da takobinsa a bayanta, fuska a rufe, yana jira a bashi umarni ya sare mata kai.
Suwainah ta sakko ƙasa kan barandar dake gaban gadon. Akan wannan baranda daga hagu anan Han'ibal da sarki Ƙaraiƙisu suke tsaye. Daga ɗan nesa dasu kaɗan Ibraham Nil ne yake tsaye tare da Maruta Ururu. Suwainah ta wuce wajen ta tsaya a kusa dasu. Daga ɗaya ɓangaren kuma kujeru ne guda biyar wanda kwamandun Ururu suke kai. Kwamanda Yurba da kwamanda Diwani suna zaune a kujeru biyu na dama. Kwamanda Binani da kwamanda Ki'jini (mai ƙunshi a gemu) suna zaune a kujeru biyu na hagu. Kujerar tsakiya babu kowa akai.
Waje yayi tsit ana jira. Kafin wani ya tambayi wa ake jira sai ga Dul'Ururu nan ya ɓullo. Tun daga nesa zaka san yayi shirin yaƙi. Babu makami a hannunsa amma yafi makami illa da hatsari da kuma rashin kyan gani. Rigarsa baka-kirin ce mai tsayi har ƙasa. A saman kafaɗarsa ta dama tauraruwa ce ƴar karama mai haske. A saman kansa kuma inuwar taskar ruhi ce take yi masa rumfa. Ya ƙara tsayi, ya ƙara cika, ya ƙara kamala. Lokaci na farko da muka ganshi a saman tsibiri ne. Uznu Ururu yaje neman shawara. A wancan lokaci mun ganshi yana farauta. Amma fa farauta irin ta taurari da ruhin bil'adama da aljanu. Da dama sun fi saninsa da mafarauci. Yaga jiya, yaga shekaran-jiya, kuma gashi yana ganin yau. Yana ɗaya daga cikin Ashura. Shi ne wanda babban sarki Kuyurussa'ayi ya bawa ajiyar ƙasashen ƙasa. Kuma shi ne wanda yake da mafi girman muƙami a dukkan ƙasashen ƙasa. Watakila idan mutun yace mafarauci yana daga cikin na sahun farko a Ashura baiyi kuskure ba.
Ganin Dul'Ururu yasa rundunar dake jere sahu-sahu sukai shewa.
"Mafarauci!"
"Mafarauci!!"
"Mafarauci!!!"
"Ururu!"
"Ururu!!"
"Ururu!!!"
Mafarauci ya wuce kujerar dake tsakiyar su Yurba ya zauna. Maruta ya taka ya hau kan matattakala yaje inda Fatima take ya nemi waje ya zauna a gefenta ya tankwashe ƙafa.
Wato a ɗan-tsukin nan, bayan Maruta sunyi magana da Dul'Ururu, har sun canja tsarin yaƙin. Kada a manta shirinsu na farko Haruta da Maruta sune zasu zauna tare da Dul'Ururu a ɓangaren dama. Yurba dasu Diwani su zauna a ɓangaren hagu kusa da Ƙaraiƙisu dasu Han'ibal. Amma yanzu abin ya canja bayan ɓatan Haruta.
Ururu sun shirya tsam sun fito domin a gwabza. Ko yaya shirin yake a ɓangaren Nusi? Wata guda daya gabata munga yadda Nusi da Cokali da tawagarsu ta mutanen ikwatora suka je wajen marubucin sarki domin ya taimaka musu su nemo Armad. Daga baya Nusi ta yadda da sharadin da Maikiro'Abbas ya saka mata. Bamu san mai ya faru ba bayan nan. Amma a halin yanzu Nazára zai bawa Armad labarin mai ya faru.
A dai-dai wannan lokaci Suwainah ta iso bakin ɗakin ta tsaya. A bayanta akwai ayarin sadaukai wanda suka rakota.
"Fatima Wilbafos?" Inji Suwainah, tana kallon matar.
Matar tayi shiru bata amsa ba.
"Fatima?"
Ta ƙara kwala mata kira. Koda taji bata amsa ba sai ta fashe da dariya.
"Haha... Ko kin haɗiyi zuciya ne?"
Suwainah ta ƙara kyakyacewa. Kurkukun tana ɗaukan sautin muryarta tana bashi amo.
"Ku shiga ku dakko ta."
***
Nan take ayarin dake bayanta suka buɗe kurkukun suka ƙarasa wajen da matar take. Tunda ƙarfen ankwar Bilak-siton ne basu da damar taɓa shi saboda haka suka saka Gatari suka datse ankokin daga jikin bangon. Maza biyu suka tsaya a ɓangaren dama, biyu suka tsaya a ɓangaren hagu. Kowannensu ya fara ƙoƙarin cuccubar wannan mace su ɗaga ta.
A lokacin ta motsa. Duk su huɗun suka jada baya cikin firgici. Na bayansu suka zare makamansu. Wani namiji mai doguwar haɓa yana karkarwa yana cewa, "kada ku bari tayi magana, zata kira babban ɗalasimi."
Kafin kace kwabo sun kewayeta da makamai. Suwainah ta tako cikin ɗakin suka buɗa mata ta tsaya a gaban matar.
"Kai! Tsoron mai kuke ji?" Ta daka musu tsawa. "Kuna cikin amincin manya masu ɗaukakar bakaken idanu." Ta juya wajen matar. "Ko ki tashi ki taho, ko kuma nasa su ɗauke ki."
A lokacin matar ta ɗago kai. Idanunta cike da kafiya irin ta mutanen Farkon Lokaci. Kallo ɗaya zaka gane Fatima ce mahaifiyar Armad, ƴa a wajen Zaikid.
Fatima ta miƙe a hankali ta tashi tsaye. Ba tare da tace komai ba ta wuce gaba. Suwainah da sauran ayarin suka bita a baya.
Akwai wani ƙaton fili da ɗakuna daga wajen ɗakin da aka kulleta. Akwai fursunoni acikin ɗakunan. Kowanne da laifinsa amma babu wanda yasan tsahon shekarun da kowa ya shafe a wannan waje. Wannan ita ce kurkuku ta uku da muka ga Ururu suna amfani da ita. Ta farko: kurkukun bango; ta biyu: gadar zare; ta uku: wannan kurkuku wadda take babbar shalkwatar Ururu ta doron ƙasa ta biyu.
A hankali Fatima ta wuce suna binta a baya. Ta hau kan matattakala wadda zata fitar dasu Filin-Jiri. Tana tafiya, sautin takunta yana amo acikin barandar. Sannu a hankali suka fara hango hasken waje.
Babu alamun tsoro ko fargaba a tattare da Fatima. Kai kace ba mutuwarta take dosa ba. Haka taci gaba da tafiya. Suna fitowa hasken rana ya haske musu ido. Waje yayi tsit duk da dubunnan mutanen dake tsaye sun jeru sahu-sahu.
Suwainah ta wuce da Fatima kan aba'in da aka tanada domin sare mata kai. Dogon gado ne na karfe. Akwai matattakala wadda tayi sama zuwa gadon da za'a zauna. Anan Suwainah ta ajiye Fatima. Hauni yana tsaye da takobinsa a bayanta, fuska a rufe, yana jira a bashi umarni ya sare mata kai.
Suwainah ta sakko ƙasa kan barandar dake gaban gadon. Akan wannan baranda daga hagu anan Han'ibal da sarki Ƙaraiƙisu suke tsaye. Daga ɗan nesa dasu kaɗan Ibraham Nil ne yake tsaye tare da Maruta Ururu. Suwainah ta wuce wajen ta tsaya a kusa dasu. Daga ɗaya ɓangaren kuma kujeru ne guda biyar wanda kwamandun Ururu suke kai. Kwamanda Yurba da kwamanda Diwani suna zaune a kujeru biyu na dama. Kwamanda Binani da kwamanda Ki'jini (mai ƙunshi a gemu) suna zaune a kujeru biyu na hagu. Kujerar tsakiya babu kowa akai.
Waje yayi tsit ana jira. Kafin wani ya tambayi wa ake jira sai ga Dul'Ururu nan ya ɓullo. Tun daga nesa zaka san yayi shirin yaƙi. Babu makami a hannunsa amma yafi makami illa da hatsari da kuma rashin kyan gani. Rigarsa baka-kirin ce mai tsayi har ƙasa. A saman kafaɗarsa ta dama tauraruwa ce ƴar karama mai haske. A saman kansa kuma inuwar taskar ruhi ce take yi masa rumfa. Ya ƙara tsayi, ya ƙara cika, ya ƙara kamala. Lokaci na farko da muka ganshi a saman tsibiri ne. Uznu Ururu yaje neman shawara. A wancan lokaci mun ganshi yana farauta. Amma fa farauta irin ta taurari da ruhin bil'adama da aljanu. Da dama sun fi saninsa da mafarauci. Yaga jiya, yaga shekaran-jiya, kuma gashi yana ganin yau. Yana ɗaya daga cikin Ashura. Shi ne wanda babban sarki Kuyurussa'ayi ya bawa ajiyar ƙasashen ƙasa. Kuma shi ne wanda yake da mafi girman muƙami a dukkan ƙasashen ƙasa. Watakila idan mutun yace mafarauci yana daga cikin na sahun farko a Ashura baiyi kuskure ba.
Ganin Dul'Ururu yasa rundunar dake jere sahu-sahu sukai shewa.
"Mafarauci!"
"Mafarauci!!"
"Mafarauci!!!"
"Ururu!"
"Ururu!!"
"Ururu!!!"
Mafarauci ya wuce kujerar dake tsakiyar su Yurba ya zauna. Maruta ya taka ya hau kan matattakala yaje inda Fatima take ya nemi waje ya zauna a gefenta ya tankwashe ƙafa.
Wato a ɗan-tsukin nan, bayan Maruta sunyi magana da Dul'Ururu, har sun canja tsarin yaƙin. Kada a manta shirinsu na farko Haruta da Maruta sune zasu zauna tare da Dul'Ururu a ɓangaren dama. Yurba dasu Diwani su zauna a ɓangaren hagu kusa da Ƙaraiƙisu dasu Han'ibal. Amma yanzu abin ya canja bayan ɓatan Haruta.
Ururu sun shirya tsam sun fito domin a gwabza. Ko yaya shirin yake a ɓangaren Nusi? Wata guda daya gabata munga yadda Nusi da Cokali da tawagarsu ta mutanen ikwatora suka je wajen marubucin sarki domin ya taimaka musu su nemo Armad. Daga baya Nusi ta yadda da sharadin da Maikiro'Abbas ya saka mata. Bamu san mai ya faru ba bayan nan. Amma a halin yanzu Nazára zai bawa Armad labarin mai ya faru.
***
Bari mu koma wata guda kafin wannan rana...
***
A yau Armad ya ɓace da sama da kwana ashirin. Babbar gasar da za'a yi ta jinzidal a doron ƙasa ta biyu kuwa saura kwana huɗu kacal. Nusi da Maikiro'Abbas sun cin ma matsaya akan zaiyi amfani da ruhinta ya samar da fasahar da zata wanzar dashi a ban ƙasa, shi kuma zai biyawa Nusi buƙata guda ɗaya.
A dai-dai wannan lokaci Nusi tana zaune a tsohon gidansu dake garin Khan. A ɓangaren damanta Cokali ne zaune yana riƙe da ƙatuwar cinya yana asuwaki da ita. A hagunta Giwa ce tana zaune tana yi mata fifita, a gabanta kuma sarkin yaƙi Barilu ne, da mai unguwa Shísu, da Inyaya takobin jini, da kuma Sarkin Bai. Dukkansu sun zube a ƙas suna fadanci cikin biyayya da ladabi.
Cokali ya ɗan tsaya da cin naman dake hannunsa ya dubi Nusi yace, "bari dai na ƙara fuskantar abin nan. Sarki Maikiro'Abbas ya yarda zai baki runduna ki kai hari doron ƙasa ta biyu ki kwato Fatima indai zaki bashi ruhin ki yayi tsafi dashi."
Nusi ta kaɗa kafaɗa. "Haka muka yi dashi."
Da Cokali da sauran wanda ke cikin ɗakin suka zare ido cikin mamaki. Sun kasa fuskantar abinda ke faruwa.
Da sauri Cokali yayi wuri da naman ya ɗan rankwafa kusa da ita. "Kuma duk kin yarda kin amince da wannan ba tare da musu ba ko shawara?"
Nusi ta ɗora hannu a kafaɗarsa cikin tausasawa ta ce, "Cokali, babu wani ciwo da nake ji a jikina. Ni wata sabuwar lafiya ma nake ji wadda ban taɓa ji ba a rayuwata."
Cokali ya riƙe hannunta da hannu biyu. "Yar uwa, wannan shi ake cewa talala mai kamar sake. Kamar mutum ne ya ringa ciyar da ragon layya yana jiran ranar salla tazo ya yanka shi. Ina da tabbas so yake yi ki koshi, kiyi kitse, kiyi maiƙo, yadda ruhinki zai yi daɗi."
Nusi ta ɗan yamutsa fuska kafin ta fashe da dariya." Cokali, Cokali... Yanzu dai a bar zancen nan, aikin gama ya riga ya gama. Abinda ya kamata shi ne mu fara lissafin yadda zamu yi. Maikiro'Abbas yace zai bamu rundunar mutum dubu talatin. Shi kansa zai taka rawa a wajen kwato Fatima, manyan ƴaƴansa suma zasu taka rawa. Yanzu maganar ita ce yaya zamu yi mukai mutun dubu talatin doron ƙasa ta biyu ba tare da Ururu sun ankara ba."
Giwa ta ɗan numfasa. Har yanzu bata daina fifitar ba. Bakinta a buɗe tana so tayi magana amma kuma tana kokwanto da wasu-wasi, kamar tana tsoron yin magana ko kuma abinda zai biyo baya.
"Giwa?" inji Nusi.
Giwa ta kalli Sarkin Bai sannan ta juya a hankali ta kalli Nusi.
"Nusi-ya, wai... wanene Armad ɗin nan ne? Kece sarauniyar mu kuma dole duk abinda kike so shi zamu yi. Mun yadda da manufarki, ɗari-bisa-ɗari. Amma waye wannan Armad ɗin da kike so ki taimaka haka?"
"Armad shi ne wanda zai canja duniya," inji Nusi, kai tsaye babu wani alamun kokwanto. Kana jin muryarta kasan ta aminta da abinda take faɗa.
Giwa ta kalli Cokali tana neman ƙarin bayani. Cokali ya girgiza kai a hankali. Alaƙar dake tsakanin Armad da Nusi tafi gaban ayi bayaninta da kalmomi. Zaifi kyau kawai kayi shiru ka kalla daga nesa.
"Yaya zamu hau doron ƙasa ta biyu?" Inji Nusi. "Kowa ya kawo mana hanyoyin da yake ganin zasu yi aiki."
"Mu rarrabu mu shiga daban-daban tunda sun buɗe ƙofa," inji Cokali. "Ina ganin har a gama jinzidal baza su rufe ƙofa ba."
Sarkin Bai ya girgiza kai. "Zamu iya yin haka idan mutanen basu fi dubu ɗaya zuwa dubu biyu ba, amma dubu talatin sunyi yawa. Ban san irin tsaron dake kan hanya ba tunda ban gama wayewa da al'amuran 'duniyar-waje' ba, amma har gida nawa zamu raba mutun dubu talatin kafin su narke?"
Nusi ta gyaɗa kai. "Nima dai haka nake gani. Zai yi wuya mu shigar da mutun dubu talatin babu wanda ya kula, komai yawan yadda zamu raba su. Mai zai hana mu bi ta sashin ikwatora? Mun san hanyar da Ƙaraiƙisu yake amfani da ita wajen shige da fice a sashin ikwatora. Idan muka shiga sashin ikwatora na shida sai muyi amfani da ƙofar Eycigan mu hau sashi na farko. Daga nan sai mu shiga bango zuwa doron ƙasa ta biyu. Kunga mun shallake katangar Ururu."
Nan take suka fara gyaɗa kai alamun amincewa da wannan shiri. Cokali ne kaɗai ya girgiza kai tare da buɗe littafin marubutan farko ya nuna musu wani saƙo.
A jiki an saka:
***
Dul'Ururu da kansa ya kawo farmaki sashin ikwatora. Ban san meye dalilin zuwansu ba, amma na shiga cikin mayaƙansu na saje ina bincike. Akwai yiwuwar barazana ce kawai suke yi domin har yanzu basu kai hari ko'ina ba.
Daga Babara Bayajidda na Dogon Zango.
***
"Wannan kwana huɗu kenan da suka wuce," inji Cokali. Ya buɗe shafi na gaba ya nuna musu wani saƙon. "Wannan kuma jiya ya turo shi."
***
A yanzu na tabbatar duk furkakin da Ururu suke basu da niyar yaƙar sashin ikwatora. A kullum shugabannin tawagar da aka saka ni suna zuwa tattaunawa da alkalan sashin ikwatora bakar guguwa. Dul'Ururu da Ƙaraiƙisu suna daga cikin wanda suke jagorantar tattaunawar. Akwai yiwuwar Ururu haɗin kai suke nema daga ikwatora saɓanin yadda muke tunanin farmaki suka kawo.
***
Cokali ya ƙara buɗe shafi na gaba.
***
Alkalan sashin ikwatora sun yadda za'a buɗe shalkwatar Ururu a sashin ikwatora wadda zata ringa 'kula' da al'amarun ikwatora. Sannan sun amince ƙaraiƙisu da wasu sadaukai dubu suje doron ƙasa ta biyu suyi kwana goma. Ban san mai suke shirin yi a wannan kwana goma ba amma zan bincika.
***
"Kada ku manta lokacin da Babara ya shiga sashin ikwatora bamu da labari akan kama mahaifiyar Armad," inji Cokali. "Saboda haka bai san abinda yake faruwa ba. Musamman duba ga cewa sashin na ikwatora a killace yake. Labari ɗai-ɗai ne suke shiga. A yau da safe na bayyanawa Babara shirin da Ururu suke yi na kashe Fatima. Ga abinda ya ce."
Ya buɗe musu shafi na gaba.
***
Fatima zasu kashe?! Anya kuwa, Cokali? Ka ƙara dubawa dai. Fatima ita ce dalilin da yasa Ururu basa kawowa gidan Wilbafos farmaki duk tsahon wannan shekarun duk kuwa da sun san inda suke. Amma idan ta tabbata Fatima suke so su kashe to zan iya cewa na gane mai yasa suke haɗa mayaƙa daga kowane sashi na duniya a doron ƙasa ta biyu.
***
"Dana tambaye shi mai yake nufi da hakan sai ya gayamin ai Fatima ƴar Maikiro'Abbas ce."
Nusi ta kalli Cokali fuska a yamutse. "Zaikid ɗin fa?"
"Eh to," inji Cokali. "Nima dai haka nace. Amma Babara ya dage min wai Maikiro'Abbas shi ne asalin wanda ya haifi Fatima."
"A'a, idan haka ne to ba ƴar gidan Wilbafos bace kenan," inji Giwa. "Sai dai ta zama Maikiro'Fatima ko kuma Fatima Abbas. Kai, anya kuwa Armad zai kasa sanin asalinsa? Kuma yadda Armad yake da ƙarfin jinin Wilbafos zai yi wuya ace ba gaba da baya bane."
Nan fa aka shiga kai-komo da maganar. Ita ma Nusi bata yadda da abinda Babara ya faɗa ba. A cewar Babara dalilin da yasa Armad bai sani ba saboda sirri ne wanda mutane kaɗan ne suka sani. Shi kansa ta hanyar bugun-kasa da duba ya gano hakan.
"To idan haka ne Fatima ita ce kanwar yarima Najunanu kenan?" Inji Nusi. "Kaai, Cokali, anya kuwa?"
"Ni dai bani na faɗa ba," inji Cokali. "Ku tambayi Babara."
Sarkin yaƙi barilu ya ɗaga hannu inda ya jira Nusi ta bashi umarnin yayi magana.
"Ni ina ganin idan Fatima ƴa ce a wajen Maikiro'Abbas hakan zai bada ma'ana. Na farko dai hakan yana nuna Maikiro'Abbas zai je yayi ƙoƙarin ceto Fatima koda baki bashi ruhinki ba. Kinga zamu koma wajensa muce mun fasa. Na biyu kuma, hakan zai haska mana dalilin Ururu na gayyatar mayaƙa daga sashi-sashi na duniya, zai kuma nuna mana dalilin da yasa Ururu suka shiga sashin ikwatora domin samo mayaƙa."
Nusi ta haɗe gira cikin tunani. Abin ya fara bada ma'ana acikin ranta. Idan ka ɗauke Taidara, Maikiro'Abbas shi kaɗai ne mutumin daya kai daɗewar Dul'Ururu a doron ƙasashen ƙasa wanda zai tadawa Ururu hankali su fara neman taimako daga sashin ikwatora. Amma kuma duk da haka ta kasa gane yadda Fatima zata zama ƴarsa.
"Mai zai hana mu tambaya?" Inji Cokali. "Muje mu tambayi Maikiro'Abbas baki-da-baki. Idan gaskiya ne zai faɗa. Ba ance daga Farkon Lokaci yake ba?"
"Tabbas daga Farkon Lokaci yake," inji Nusi. "Amma mai kake nufi?"
"Ah, ƴar-uwa, kin manta yadda dabi'ar mutanen Farkon Lokaci take?" Inji Cokali. "Ƙarya ta saɓa da halayensu. Duk wani ma'aboci izza da muka karanta a littafan Farkon Lokaci baya ƙarya. Ƙarya ta saɓa da dabi'arsu."
Nusi ta gyaɗa kai a hankali. Hakane, tabbas mutanen Farkon Lokaci basa ƙarya. Nan take suka yanke shawarar suje su tambayi Maikiro'Abbas. Idan Fatima ƴarsa ce ta cikinsa to kaga alhakin karɓota a kansa yake ba akan Armad ba.
Har Nusi ta miƙe sai ta kalli lokaci. Tuni sha-daya na dare tayi. Dole ta koma ta zauna.
Ana wayar gari ta garzaya fada. A wannan lokaci dukkansu suka tafi babu wanda aka bari. Suna zuwa akai musu iso. Maikiro'Abbas da kansa yace duk sanda suke son ganinsa su zo saboda haka babu wanda ya tare su.
Yarima Najunanu, da yarima Umaru, da yarima Abba suna tsaye a hagun sarki. A daman sarki babu kowa. Yana daga abin mamakin wannan fada babu wanda yake tsayawa a daman sarki. Wasu sunce wajen na aljanun sarki ne. Wasu kuwa suna ganin wani sulkulle sarki yayi a wajen ta yadda duk wanda ya tsaya anan sai ya mutu. Nusi bata yadda da duk wannan canfin ba. Abinda ta sani shi ne kawai sarki bai ga damar ajiye wani a wajen ba.
"Nusi-ya," inji Maikiro'Abbas. A lokaci na farko Nusi ta risuna. Sarkin yayi kamar bai gani ba yaci gaba da magana. "Naji ance haka ake kiranki a sashin ikwatora."
"Ina gaisuwa babban sarki na Farkon Lokaci," inji Nusi cikin girmamawa. Tunda ya girmamata to ya wajaba itama ta girmama shi. "Amma zanso na faɗawa sarki kalmace wadda mabiya suke faɗa. Bai kamatu ga babban sarki kamar ka ya faɗa ba. Zai zamo kamar kaskanci a gare ka. Ni kuma zai iya saka ni girman kai. Ni ɗin kuma ba kowa bace illa hadima a wajen sarki Armad na gidan Wilbafos."
Sarki yayi dariya tare da miƙewa daga kan kujerarsa ya taka wajen da Nusi take.
"Hmm. Armad, Armad, kullum dai maganarki Armad. To, naji, yanzu meye ya kawo ki da sanyin safiyar nan? Kada kice min kin fara jin canji a jikinki." Yayi shiru yana nazarin fuskarta kafin ya haɗe gira. "Idan kina kokwanton bazan cika alkawari na ba to ki daina. Tuni na zaɓi mutun dubu talatin mafi ƙarfin izza a runduna ta zan baki. Ita ce buƙatar ki, ko?"
Nusi ta gyaɗa kai a hankali. "Ita ce buƙatar dana gaya maka a baya, amma yanzu ina so na canja."
Maikiro'Abbas ya ƙara hade rai.
"Kina so ki canja?"
"Eh, nayi bincike na gano sunanta Maikiro'Fatima ba fatima Wilbafos ba. Kai ne mahaifinta kuma kai ya cancanci ka taimake ta. Ni yanzu buƙatata ka kashe Bihanzin. Ance kai kaɗai ne mutumin da zaka iya yin hakan. Ko Bihanzin ko Ikenga, duk wanda ka kashe yayi."
Fuskar Maikiro'Abbas tayi baƙi. Ruwan zafi ya fara ɗisa daga idanunsa.
"Kina nufin zaki saɓa min alƙawari?"
"A'a, babu zancen saɓa alƙawari, amma bazan yadda ka kashe ni dan na taimaka maka ka ceto ƴar daka haifa ba. Ka gayamin ni-da-kai kace Fatima ba ƴar ka bace. Ni kuma zan amince."
Shiru sarkin yayi yana kallonta. Bayan ɗan lokaci ya juya ya koma kan karagarsa ya zauna.
Nusi tasan ta samo bakin zaren. Maganar Cokali gaskiya ce. Mutanen Farkon Lokaci basa ƙarya. Kamar yadda Maikiro'Abbas bazai iya cewa Fatima ba ƴarsa bace tunda shi ne ya haife ta. Wato da a haka yake so yayi mata wayo ya kwace ruhinta kuma ta taimake shi ya karɓo ƴarsa. Hmm.
"Fatima ba ƴata bace," inji Maikiro'Abbas.
A hankali Nusi ta ɗago kai. "Ba ƴarka bace? An ce min ƴarka ce, tayaya zaka ce ba ƴarka bace?"
Maikiro'Abbas ya kada kafaɗa. "Na gaya miki ba ƴata bace amma idan baki yarda ba zaki iya tambaya. Ko kuma kije laburare ki duba. Amma kiyi sani munyi alƙawari dake: zaki bani ruhinki ni kuma zan karɓo miki Fatima mahaifiyar ɗan'uwanki Armad. Amma bazan zarge ki ba idan kika ce kin fasa, ba kuma zan zamo mai cuta a gare ki ba. Zan baki ruhinki, ni kuma na riƙe runduna ta."
Nusi tayi tsam tana kallon sa. Tun farko dai Abbas bai yi zancen Fatima ba, kuma baice zai je ya ceto ta ba. Ita ce ta nemi ya je ya ceto ta a matsayin buƙatar ta idan yana son ruhinta. Idan da yarsa ce da tabbas shi ne zai zamo a sahun gaba wajen zuwa ya karbo ta. Kuma a duk zamanta a daular Maikironomada bata taɓa ji ance Maikiro'Abbas yana da 'ya Fatima ba. Hakan zaiyi wuya domin a muƙaminta babu wani ahalin sarki Abbas da bata sani ba. Daɗin-daɗawa idan Fatima 'yar Maikiro'Abbas ce to babu yadda za'ai Ururu su bayyana zasu kasheta saboda dalilai guda biyu. Na farko, har yanzu dai Maikiro'Abbas sarkin Jinzidal ne wanda hakan ke nuna yana ƙarƙashin kariyar Ururu. Na biyu, sarki Abbas ba mutum ne wanda Ururu zasu takala cikin sauki ba. Abbas Sarkin Jinzidal ne amma ba kamar ragowar sarakunan jinzidal ba. Shi ne na farko da aka yiwa muƙamin sarkin jinzidal wanda hakan yasa wasu da dama suke ganin saboda shi aka kirkiro muƙamin. A tarihinsa yayi faɗa da Ururu kuma basu ci nasara akansa ba. Zai yi wuya a halin da Ururu suke ciki a yanzu na rugujewar sarakunan jinzidal su kuma takali Maikiro'Abbas da faɗa. Hakan yasa Nusi take ganin akwai ayar tambaya acikin ikirarin Babara na cewa Fatima yar Maikiro'Abbas ce.
"A bani kwana uku nayi bincike," Inji Nusi. "Nanda kwana uku zan dawo na fadi shawara ta."
A lokacin sarki ya bata dama taje tayi duk binciken data ke so. Yarima Umaru wanda shi ne yarima mai jiran gado ya raka su ƙofar gari suka kama hanya.
Daga wannan rana Nusi ta fara bi laburare, laburare tana bincike akan asalin Fatima. Bayan kwana biyu tana abu guda ba tare da ta samu komai ba sai ta tafi gidan jaridar aminiya. Akan samu duk wani babban labari acikin jarida.
"Malam, sannu da aiki. Jaridar shekara nawa kuke ajiyewa?"
Ma'aikacin da take tambaya ya ɗanyi tunani kaɗan kafin ya amsa da cewa, "muna da jarida har ta shekara goma." Muryarsa cike take da alfahari. Yana ji babu wata jarida da suke iya ajiya kamar su.
"Shekara goma kacal?" Inji Nusi. Lamarin da yasa mutumin ya sace lokaci guda. "Ina neman aƙalla jaridar data shekara ɗari zuwa dubu. Kana ganin babu yadda za'ai na samu?"
"Shekara ɗari?" Ma'aikacin ya ɗanyi murmushi. "Amma dai da wasa kike ko? A duk faɗin duniyar nan wa yake da jaridar shekara ɗari? Ai bari kiji, ko a doron ƙasa ta farko baza ki samu jaridar shekara ɗari ba. Idan ajiya tayi yawa takardun kansu lalacewa suke"
"Idan bazan samu jaridar ba to ka hadani da wanda yafi kowa daɗewa a wannan ma'aikatar, zan biya ko nawa yake so idan dai zai bani labarin da nake so."
Nusi ta zura hannu cikin jakar tsafinta ta zaro Ayrid dubu goma ta ɗora akan teburin. Ko da mutumin yayi ido biyu da kuɗin sai jikinsa ya fara rawa. Nan take ya ɗauki su Nusi suka shiga ciki. Bai zame ko'ina ba sai wajen wani dattijo. Nusi ta tambayi mutumin labari akan daular Maikironomada.
"Wai shin sarki Abbas yana da 'ya mai suna Fatima?"
"Ehmmm..." Dattijon yaja dogon numfashi cikin tunanin. "Bani da masaniya akan wannan batu, amma tabbas akwai wani labari da kakan mahaifin babata na uku ya taɓa bani akan wani mutum mai suna Taidara da tawagar mattatu. Ance da Taidara da zuri'arsa sunyi yaƙi mai tsanani da Maikiro'Abbas a wancan zamani, yaƙin daya jawo mattatu suka ringa tashi daga kabari har aka sawa yaƙin suna yaƙin tawagar mattatu. To kinga kuwa idan Fatima ita ce matar Taidara kuma tare suka yaƙi Maikiro'Abbas kinga babu yadda za ai ace 'yar Maikiro'Abbas ce kenan."
"Yaƙin... tawagar matattu? A wace shekara aka yi wannan yaƙin?" Inji Nusi.
"Eh... to, daga dai abinda na sani yaƙin ya faru ne tsakanin shekarar ɗari biyar zuwa ɗari bakwai bayan amri."
Akwai dalilin da yasa Nusi tayi masa wannan tambayar. Yawanci komai gaskiyar labari idan ya daɗe mutane suna canja shi. Iyakacin dadewar labari, iyakacin yadda za'a canja shi. Haka dabi'ar mutane take. Idan yaƙin tawagar mattatu ya faru ne shekaru dubu da suka wuce kaga kenan akwai yiyuwar abubuwa da dama an canja su. Akwai yiwuwar anyi ƙari da ragi a sassa daban-daban na labarin.
Nusi taja dogon numfashi sannan tayi wa dattijon godiya kafin su juya su tafi. Duk da haka bata haƙura ba sai da ta kwashe kwana uku cir tana bincike akan alaƙar Fatima da Maikiro'Abbas, da kuma alaƙar gidan Wilbafos da gidan Maikironomada. A ƙarshe ta yanke hukunci Fatima ba 'yar Maikiro'Abbas bace sai dai kuma akwai alaƙa. Alaƙa wadda ta kasa ganewa saboda duk abubuwan sun ɓace acikin tarihi.
Abu ɗaya data sani shi ne alaƙar bata da ƙarfin da zai sa Maikiro'Abbas yayi faɗa da Ururu. Da alaƙar ta kai haka da Maikiro'Abbas yana gani bazai bari a kashe Hidaya ba tunda zata zama yar Fatima kuma jikarsa. Saboda haka Nusi ta yanke shawara zata iya sadaukar da rayuwarta akan Armad. Kuma babban wanda take da shi da zai iya taimakonta a yanzu shi ne Maikiro'Abbas. Farashin ba matsala bane indai za'a samu biyan buƙata.
Washe gari da safe ta dawo fada.
"Na amince zan baka ruhi na, amma bayan mun kwato Fatima da Zaikid ina so ka nemo Armad."
"Buƙata ɗaya mu kayi dake," Inji Maikiro'Abbas. "Yanzu kin kawo biyu. Armad ɗin kike so a nemo ko kuma iyayensa?"
"Duk biyun," inji Nusi. "Idan ba haka ba kuwa bazan amince na bada ruhina ba."
"Zaki saɓanin alƙawari kenan?"
"Ba zancen saɓa alƙawari bane, mai martaba, zancen matsayin abinda zan bayar ne wanda farashinsa bazai misaltu ba."
Su kayi shiru suna kallon juna. Babu wanda yasan meye a zuciyar sarkin amma Nusi addu'a take yi ya amince da buƙatar ta. Mai zata cewa Armad idan ya dawo ya tarar an kashe mahaifiyarsa ba tayi komai akai ba saboda tsoron mutuwa?
"Ki je, zan neme ki a kwana uku. Idan kika ji shiru ban amince da buƙatar ki ba."
Nusi ta juya ta fice daga fadar. A garin Khan suka nemi waje suka jira.
"Kin yi shawara mai kyau," inji Cokali.
Nusi ta kalle shi ta gefen ido amma bata ce komai ba. Tana da cikakkiyar masaniyar Cokali da mutanenta basa goyon bayan hukuncin data yanke na bayar da ruhinta. Sunyi shiru ne kawai saboda babu yadda zasu yi.
A rana ta uku sukai baƙo. A lokacin da aka kwankwasa ƙofa sunyi tunanin ɗan-aiken sarkin Abbas ne, amma bayan an buɗe ƙofar sai suka yi arba da saurayi mai gashi dogo, jajawur abin sha'awa.
Cikin sauri Nusi ta miƙe. "Nazára?"
Nazára yayi murmushi. A tare dashi akwai kwamanda Jan-doki da kwamanda Asifu Ruwan Bala'i.
"Hmm.. nasan indai nazo nan zan same ku," inji Nazára.
Nusi ta yamutse fuska. Shin kai tsaye ya taho garin Khan ko kuma yaje wasu wuraren nemansu?
"Ka koma daular denizawa ne?" Nusi ta tambaye shi. A lokacin da zasu rabu, Nazára yace idan ya gama abinda yake zai same su a ƙarƙashin ƙasa, daular denizawa. Saboda haka bata ga dalilin da zaisa yayi tunanin zai same su a garin Khan ba indai ba yaje daular denizawa bai gansu ba. Ko kuma ya samu su Nostaljiya sun gaya masa abinda ya faru shi ne ya taho nemansu.
"Na je." Ya gyaɗa kai.
Nusi tana jin haka tayi farat tace, "duk abinda Nostaljiya ta gaya maka karya ne. Kada su yaudare ka, Armad ɗin daka gani a tare dasu ba Armad bane - Ayubu ne. Ina da hujja."
Cikin sauri ta lissafa masa hujjoji wanda take ganin Armad ɗin da Nazára ya gani ba shi ne na gaskiya ba.
Nazára ya jira ta gama sannan ya tambaye ta, "wai wane Armad kike zance ne? Nifa ban ga kowa ba. Babu Armad, babu Nostaljiya, babu ke, babu kowa. Sai da nayi kwana uku a daular denizawa ina nema. Har zaren izzar da Armad ya bani saboda irin haka nayi amfani dashi amma babu labarin ku."
Nazára yayi shiru yana kallon fuskar Nusi.
"Menene?"
"Er... baka ga su Nostaljiya ba? Suna fadar sarki Iluru." Ta tambaye shi.
"Fadar sarki Iluru kuma?" Inji Nazára. "Ni ai bamu yi daku zaku je fada ba. Kunce zaku shiga daular ku nemo fasahar karfafa jiki domin Hidaya. Amma bamu yi zancen fada ba."
Nusi tayi shiru tana lissafi. Basu gayawa Nazára zasu shiga fada ba. Su ma kansu basu san zasu shiga ba. Zaka iya cewa komai ya faru ne saboda sun gamu da abubuwan da basu yi tunani ba. Amma koda sun bar fada suna otal.
"Ka duba otal-otal ɗin garin baka gansu ba? Akwai wani otal kusa da kasuwar garin anan muka barsu."
Nazára ya girgiza kai. Babu wanda ya gani duk kuwa da lokacin da ya duba. Nan fa aka shiga kai-komo da maganar ana tunani. Ina su Nostaljiya suka yi?
"Amma idan kina tunanin Armad ɗin da kika bari tare dasu Ayubu ne to akwai matsala kenan," inji Nazára. "Watakila sun kashe su ko kuma sun ɗaure su a kurkuku."
Nusi tayi shiru tana tunani. A yanzu ta ƙara samun yaƙini akan abinda tayi. Tabbas ba Armad bane. Amma ina su Nostaljiya sukai to?
"Yanzu meye abin yi?" Inji Nazára.
"Babu wani abu banda mu jira mu gani," inji Cokali. "Duk wani kwamanda dole zaiyi ƙoƙarin zuwa doron ƙasa ta biyu domin karɓo Fatima. Zamu haɗu a can."
Maganar Cokali haka take. Idan suka ce zasu fara neman Nostaljiya daga ina zasu fara? Neman Armad ma ya ishe su. Sannan kuma akwai yiwuwar su haɗu a doron ƙasa ta biyu idan sunje karɓo Fatima. Yanzu komai ya ta'allaka da hukuncin da Maikiro'Abbas ya yanke. Saura kwana biyu kacal a fara jinzidal saboda haka gobe ita ce ranar daya kamata su tafi indai suna so su isa akan lokaci.
"Amma mai ya kawo ku nan?" Inji kwamanda jan doki. "Zanyi tunanin zaku fita neman Armad tunda kince wancan Armad ɗin bana gaskiya bane. Mai kuke yi a daular Maikironomada?"
"Wajen sarki Abbas tazo neman taimako, ko?" Inji Nazára. Yana ganin abinda Nusi tazo yi kenan tunda dukkaninsu suna tunanin akwai wata babbar alaƙa tsakanin Armad da sarkin saboda abubuwan da suka faru a baya. "Ko ba haka bane, Nusi?"
"Hakane." Nusi ta gyaɗa kai. "Amma babu tabbas abinda muke nema zamu samu. Gobe ita ce rana ta ƙarshe da muka bashi."
Daga nan ta kwashe duk abubuwan da suka faru tsakaninta da sarki Abbas tun daga sanda suka zo garin har zuwa yau ta gayawa Nazára.
Nazára ya duba agogonsa ya ce, "muna da ragowar kwana guda da awa huɗu kenan."
Nusi ta duba nata agogon sannan ta gyaɗa kai. Ba jimawa zasu san mai suke ciki.
Tuni kai ya ɗauki zafi babu wanda ya kawowa Nazára ruwa ko kuma ya tambaye shi ya hanya. Zama sukai suka saka ƙofa a gaba suna jumurin sauraro. Duk wata dakika data gilma tsammani suke ko zasu ji sallama. A haka aka kwana aka tashi.
"Bana tunanin Maikiro'Abbas zai zo," Inji Nazára. "Musamman duba ga cewa shi Ururu suka naɗa ya jagoranci jinzidal ɗin da za'ai."
Nusi tana sane da wannan. Amma hakan bai saka ta cire rai ba. Tun da aka fara jinzidal a kowace shekara sarakunan ƙasa ne da alhakin jagorantar ta. Kamar jinzidal ɗin da muka gani a baya wadda sarki Iluru ya jagoranta. A wannan karan Ururu sun fitar da sanarwar Maikiro'Abbas shi ne zai jagorata. To amma duk da haka kowa yasan wannan tsari a baki ne kawai. Ururu suna nada sarakunan jinzidal ne kawai saboda mutanen ƙasa su ga anayi dasu. Kamar yadda suke buƙatar Maikiro'Abbas yaje ya zauna ya gabatar da taron amma a zahiri sune zasu jagoranci duk abubuwan da zasu faru. Ta yaya Dul'Ururu zai bar wani yayi wani abu a doron ƙasa ta biyu bayan yana wajen?
"Bari dai mu gani," inji Nusi.
A haka suka ci gaba da jira. Bayan wata awa ukun, Nusi ta miƙe. Ba tare da tace komai ba ta shiga ta fara haɗa kayan tafiya.
Nusi, Nazára, cokali, da tawagarsu suka ɗaura sirdi suka fice daga daular maikironomada. Tafe suke sunyi shiru suna tunani.
"Yanzu meye shirin?" Inji Cokali.
"Abin yi muje kwato Fatima," inji Nusi.
Cokali yayi ajiyar zuciya ya ƙara kallon tawagar. "Iyakacin mu na nan?"
"Eh, Cokali, iyakacin mu na nan," inji Nusi.
Nazára ya fashe da dariya. "Cokali, tsoro kake ji ne?"
"Tsoro halak ne," inji Cokali. "A ina kuke tunanin zamu iya faɗa da doron ƙasa ta biyu?"
"Zaka iya komawa ka zauna a gida," inji Nazára. "Idan mun karbo ta zamu yi maka bayanin yadda akai."
Cokali ya harare shi.
A haka dai suka ci gaba da tafiya har suka iso ƙofar Eycigan. Akwai mutane da dama dake bin layi wanda suke son zuwa kallon gasar jinzidal da za'a fara gobe a doron ƙasa ta biyu. Suka jira layi yazo kansu sannan suka rankaya izuwa doron ƙasa ta biyu.
***
Ranar talata aka saka domin gudanar da gasar jinzidal ta wannan shekara. Gasar data biyo bayan kamfen ɗin da Ururu suka gabatar a watan. A yayin kamfen ɗin Ururu sun tabbatar dukkan wasu sarakuna, ƙananu ko manya, dake rayuwa a doron ƙasashen ƙasa sunyi biyayya ga ikon Ururu.
A filin gasar idan ka duba zaka ga sarakuna tamanin da bakwai a jere akan kujeru sun bi layi. Kowa da kalar kayansa wanda suke bayani akan ƙasar daya fito. Daga saman su akwai manyan baƙi daga doron ƙasa ta farko wanda suka haɗa da waziri Tadiyraini da Ibraham Nil da Suwainah. Ga kuma sarakunan jinzidal guda biyu: Iluru da Han'ibal. A saman su akwai kwamandu biyar na rundunar Ururu wanda suka haɗa da Dul'Ururu da Yurba da kuma samudawan nan uku salsan Dul'Ururu.
Fili ya cika yayi makil.
Kowacce ƙasa ta turo wanda zasu wakilce ta. Babu wanda ya tambayi ina Maikiro'Abbas ko kuma dalilin da yasa bai zo ba. A maimakonsa sarki Han'ibal ya haye kujerarsa.
"Girma ya tabbata ga babban sarki Kuyurussa'ayi," inji Han'ibal. "Munji daɗin yadda kamfen ya gudana lafiya ba tare da wata tangarda ba. A matsayina na sarkin jinzidal, ina farin cikin bayyanawa duniya dukkan sarakunan dake ƙarƙashina sunyi mubaya'a ga ikon Ururu. Haka sarakunan dake ƙarƙashin sarki Iluru. Ina so nayi amfani da wannan dama na sanar da cewa sarakuna sha-huɗu dake ƙarƙashin sarki Maikiro'Abbas babu wanda yayi wa Ururu mubaya'a a yayin kamfen. Garuruwan Bihanzin da Baba Dalja duk sun miƙa wuya. A halin yanzu yare ɗaya muke yi wanda shi ne Yaren Ururu."
Bayan wannan gabatarwar aka buga ganga aka fara fafatawa. Filaye guda shida kamar yadda aka saba gani. Kowanne cike yake da mayaƙa daga sassa daban-daban na faɗin duniya. A kowanne fili mutun ɗaya ne zaiyi nasara wanda zai samar da mutun shida gaba ɗaya. Sannan acikinsu a zaɓi mutun huɗu su fafata a zagaye na gaba.
A filin farko wani basamude ne wanda duk wanda ya taɓa ziyartar sashin ikwatora yasan shi. Ana kiransa da babban sarki Ƙaraiƙisu. Kai kace faɗa yake da ƴan-tsaki, ya nutsu yana saka ƙafa yana tarwatsa dukkan mutanen dake kan filin. Kafin kace kwabo babu kowa sai shi. Shi ne mutum na farko da yayi nasara.
A fili na biyu wani yaro ne mai ɗauke da guma-guman wuta a kafaɗa. Shima fuskarsa ba boyayyiya bace domin ya taka rawa a gasar jinzidal data gabata a karkashin kasa. Sunansa Han'Amuru. A wani yanayi na fushi ya daki ƙasa da ƙafarsa. Nan take dukkan filin ya kama da wata muguwar wuta abar balbali da hayaki. Ko ka gudu ko kuma ka ƙone. Kafin kace kwabo yayi nasara.
A fili na uku wata mace ce wadda ta ɓoye fuska. A saman kanta turmi ne na daka. A gabanta kuma bishiya ce take nade mutanen dake gabanta. Duk sanda wannan bishiya ta nade mutum sai kaga ta zuƙe izzarsa ta ƙara girma. Kafin kace kwabo wannan mace tayi nasara.
A fili na huɗu Rafiyan Nazára ne yake sharafinsa. Ya saki yashi ya rufe filin baki ɗaya. Acikin yashin akwai nikakken ƙarfe wanda yake da danko kamar mayan ƙarfe. Kafin abokan karawarsa su ankare ya haɗe makamansu guri guda ya ɗaure. Sannan yasa yashi ya watsasu wajen filin kamar kayan wanki.
A fili na biyar dana shida har yanzu fafatawa ake yi. Akwai wata mace mai amfani da takobi a fili na biyar. Duk inda tayi sai dai kaga kawuna suna zuba. Maza goma sun tarar mata amma a banza. Duk sanda ta ɗaga takobi sai dai kaga sun zube ƙasa. Abin mamaki wannan mace ƴar ƙabilar Yeren ce. Wuyanta yafi dantsen ƙato tsayi, ya kuma lankwashe daga ƙasa a wani samfuri na awarwaro. Daga ƙasa kuma wasu ƴan'yatsu ne ƙananu wanda akai wa kwalliya zobbai suka fita ta gefen wuyan.
A fili na shida abin a hargitse yake. Babu wani fitacce. Kowa ƙoƙari yake ya kashe na kusa dashi. Ƙura ta cika ko'ina. Lokaci-lokaci zaka hango walkiya ko wuta suna tashi amma har yanzu babu alamun nasara.
Kamar yanda tsarin gasar jinzidal yake wanda suka fara kammala faɗan zagaye na farko sune sukai nasara.
"Sarki Ƙaraiƙisu daga sashin ikwatora shi ne yayi nasara a rukunin A. Ya gama a dakika sha-tara," inji mai sanarwar.
"Han'Amuru daga doron ƙasa ta uku shi ne yayi nasara a rukunin B. Ya gama a dakika ashirin-da-ɗaya.
"Nusi Wilbafos daga..." Mai gabatarwar ya ƙame a inda yake tsaye. Ya tabbatar bai ga sunan Wilbafos ba sai yanzu. Ya daga kai ya ƙara kallon macen wadda tayi nasara a rukunin C sannan ya ƙara kallon sunan. A yanzu ta cire hijabinta, fuskarta ta fito fili. "Nusi Wilbafos...?" Ya tambaya yana tsoron kada kuskuren rubutu aka samu. Nusi ta gyaɗa masa kai da bashi tabbacin dai-dai ya faɗa.
"Nusi 'Wil-ba-fos' daga garin Kanyu ita ce tayi nasara a rukunin C. Ta gama a dakika sha-biyu."
Nan take aka fara kace-nace. Yan-kallo nayi, manyan baƙi nayi. Tun daga nesa zaka hango sarakunan da aka tara suna tambayar juna. Lokaci ya tsawaita rabon da aji wannan suna a ban ƙasa. Har waye yake da tsaurin idon ya hawo har doron ƙasa ta biyu yayi ikirarin shi Wilbafos ne?
Mai sanarwar yayi sauri ya wuce zuwa suna na gaba.
"Rafiyan Nazára, ɗan marigayi sarkin jinzidal Daljari shi ne yayi nasara a rukunin D. Ya gama a dakika ashirin-da-takwas.
"Kasulà Ye daga ƙabilar Yeren ta doron ƙasa ta biyu ita tayi nasara a rukunin E. Ta gama a minti sha-biyar.
"Har yanzu ana ci gaba da fafatawa a rukunin F."
Haka dai aka ci gaba. Sai da aka kwashe awa guda ana fafatawa sannan aka kammala faɗan rukunin F.
"Ina farin cikin bayyana muku cewa sarki Ƙaraiƙisu, Han'Amuru, Rafiyan Nazára, Kasula, Neirun daga garin Salbut na ƴan'tattun garuruwa (wanda yayi nasara a rukunin F kuma a halin yanzu yake gadon asibiti), da Nusi sune suka samu nasara a zagaye na farko. Yanzu zamu cilla ganye sama domin fitar da wanda zasu fafata a zagaye na kusa dana karshe."
Ma'aikata suka matso kusa aka cilla ganye sama. Idanun kowa akan sunayen dake kai. Kowa naso yaga waye zai kara da wa.
"Nusi da Rafiyan Nazára sune zagaye na farko," inji mai gabatarwar bayan ganyayyakin sun sauka ƙasa. "Sai Ƙaraiƙisu da Han'Amuru. Kasulà da Neirun zasu samu kyautar ayrid mai mataki na goma saboda nasarar da suka samu a zagaye na farko amma kuma basu samu damar zuwa zagaye na gaba ba."
Nan take aka gyara fili. Zaka iya cewa duk wanda ke filin so yake yaga an kashe Nusi badan komai ba saboda sunanta. Tuni ƴan-kallo suka fara kiran sunan Nazára suna zuga shi.
Nusi tana tsaye suna kallon juna da Nazára. Jama'a suna jira a fara faɗa ko sa ga yadda za'a fille kan Nusi.
"Sai kayi ɗan sarki!"
"ALLAH ya jikan baba Dalja."
"Sai kayi! Sai kayi!! Sai kayi!!!"
Nusi tayi kamar bata ji su ba. Ɗora hannu tayi akan ƙasa. A take bishiya ta bayyana a ƙasan Nazára ta jayayya da ya rufe shi. Nazára ya samar da yashi yayi ƙoƙarin yage bishiyar amma ya 'kasa'. Tun yana wutsil-wutsil har ya daina motsi. Aka kirawo ma'aikata suka ɗauke shi suka fitar dashi waje. A haka Nusi tazo zagaye na ƙarshe a gasar jinzidal.
"Fasaha tayi!" Inji yan-kallon.
"Fasha ce, fasha ce."
Haka suka wanzu suna ihu tsahon mintuna babu wanda ya yanka musu. Zaka iya cewa har zuwa wannan lokaci babu wanda yasan yadda akai Nusi tayi nasara. Wasu suce Nazára ɗaga mata ƙafa yayi, wasu kuma suce ƙarfinta ne ya bata.
A haka aka buga kugen yaƙi. Ƙaraiƙisu da Han'Amuru suka fito filin daga. Tsawon lokaci suna kallon juna babu wanda ya motsa. Idan ka hange su daga nesa sai kace bajimin sa ne da kuma ɗan tayi. Ƙaraiƙisu ya yiwa Han'Amuru nisa a girman jiki ta yadda hatta ƙawanyar wutar dake ci a bayan Han'Amuru bata ƙara masa kwarjini ba. Amma kuma duk da haka babu alamun tsoro a tattare dashi. Ya fara bin gefen filin yana taku dai-dai idon sa akan Ƙaraiƙisu.
"Ka nuna min ƙarfin mutanen ikwatora," Inji Han'Amuru. "Naji ance fatarku ta fi tamu tauri, amma abinda ban sani ba shi ne: tana ƙonewa ko bata ƙonewa?" Yana magana yana zagaya Ƙaraiƙisu. Shi kuwa ƙaraiƙisu bai ce masa komai ba. Bai ma motsa ba ballantana ayi tunanin zaiyi wani abu. Yana tsaye kikam yana kallon gabansa, fuskarsa babu alamun farin ciki ko baƙin ciki a tattare da ita ta yadda zaiyi wuya ka gane abinda ke cikin ransa.
"Wato shi yasa wuta take burgeni," Inji Han'Amuru. "Koda mutun kurma ne idan ya jita zaiyi magana, kamar yadda koda mutum bebe ne idan ya jita zai bude baki."
Har yanzu Ƙaraiƙisu bai ce uffan ba. Han'Amuru ya dawo gabansa ya tsaya. Ganin cewa sai ya ɗaga kai yake ganin fuskar Ƙaraiƙisu ya ɓata masa rai. Mai zai hana ya durkusar dashi akan gwiwowinsa ta yarda zai kalli cikin idonsa yayi masa magana?
A lokacin ya nuna ƙafafun Ƙaraiƙisu da dan-yatsa. Wata koriyar wuta ta fara fita daga ɗan yatsansa tana tunkarar ƙaraiƙisu. Basamuden bai motsa ba. Wutar ta nannade ƙafafunsa har saida ta kai cinyarsa. Han'Amuru ya dunkule hannunsa a wani salo na bada umarni. Kamar wutar tana jinsa sai ta fara matsewa tana ƙara damƙar Ƙaraiƙisu. Kayan jikin sa suka fara marmashe wa suna komawa toka. Duk wajan data gilma sai kaga kayan sun marmashe sun koma toka. Han'Amuru ya fara dariya yana murna.
"Lallai ni ne zanyi nasara a wannan gasa ta jinzidal domin kuwa na shirya mata tsahon zamani."
Yana ƙara dunkule hannunsa wutar tana ƙara matse ƙaraiƙisu. Babu wani kokwanto akan nasararsa. Tuni acikin ransa ya fara lissafa irin ɗaukakar da zai samu a doron ƙasa ta uku dama dukkan ƙasashen ƙasa. Babu wani saurayi da za'a ci gaba da zance sai shi. Daman yasan a wancan lokacin sa'a ce babu amma da shi ne zai yi nasara.
Sai dai kuma kash, yana cikin wannan tunani ne ƙaraiƙisu yasa hannu ya yarfe wutar dake jikinsa. Gashi dai kayan jikinsa sun ƙone babu komai a jikinsa sai dan-bante, amma kuma fatarsa tana nan sabuwa fil babu ko kwarzane a jikin ta. Han'Amuru ya yamutse fuska yana kallon jikin ƙaraiƙisu. Bayan ɗan lokaci yayi murmushi.
"Kayi ƙoƙari daka gagari wutata Jukisa, amma kayi sani wannan ko kaɗan bazai hanani yin nasara akanka ba."
Han'Amuru ya daga hannayensa guda biyu sama. Nan take ƙawanyar wuta guda goma ta bayyana a saman hannunsa. Ko wacce ƙawanya ta rabe gida biyu sannan ko wacce ta ƙara rabewa gida biyu. Kowacce ƙawanya ta sakko ƙasa-ƙasa suka zagaye jikinsa. A wani salo mai ban al'ajabi wannan kawanyoyi suka fara juyawa suna zagaya shi. Idan ka lissafa za kaga ƙawanya ɗai-ɗai guda arba'in wanda kowacce tafi girman kan jariri. Suka ci gaba da dawafi a jikin Han'Amuru.
Comments
Post a Comment