"Zaren Babbar Mutuwa!"
A dai-dai sanda Armad ya kira babban dalasimin sa, manya-manyan mutun-mutumi guda uku Iluru ya janyo daga karkashin wannan makeken ruwa a wani salo mai nuna dama can da shirin sa yazo gurin. Wasu tafka-tafkan ƙusoshin haske guda uku suka bayyana a hannun kowanne mutun-mutumi. Mutun-mutumin uku suka dunguma sukai kan Armad da mugun nufi. Baka jin komai sai ƙugin iska da rugugi da kaɗawar ruwa kai kace aljanu ne suke sauka.
A dai-dai wannan lokaci Armad ya saukar da hannun sa ƙasa inda gidan gizo-gizon ya sakko ƙasa ya rufe ko'ina baka ganin komai sai fari. Cikin ƙanƙanin lokaci zarurruka suka dunƙule guri guda a gaban Armad suka tari gaban mutun-mutumin. Abin mamaki suna haɗuwa kawai sai aka ga wannan samudawan mutun-mutumi wanda kowanne yafi zira'i dubu a tsaye sun ɓace ɓat. Babu su babu alamun su. Babu ƙusoshin babu alamun su. Idan ka lura sosai zaka ga shi kansa ruwan dake ƙasa ya ragu matuka kamar bakan gizo ya shaye.
Babu kowa sai Armad da Iluru.
A nutse Armad ya nuna Iluru da ɗan yatsa, lamarinda yasa dukkan zarurrukan da suka haɗa gidan gizo-gizon sukai kansa. Kafin ya ankara sun rufe shi sun dunƙule shi guri guda kamar buhun goro.
"Ɓace!" Armad ya daka masa tsawa. Dole Iluru yabi umarni ya bace.
Abu kamar wasa babu Iluru babu labarinsa. A ƴan dakiku da suka wuce Iluru na tsaye cikin ƙasaita da nuna isa, ga manyan mutun-mutumin dutse a bayansa suna gadinsa, sannan kuma ga ƙusoshi masu wuyar sha'ani duk a tare dashi suna kareshi. An juyo shi yana cewa Ikenga da tawagarsa duk suna bayansa, amma kuma a wannan lokaci Iluru ya zama tarihi. Babu shi babu alamun sa.
A halin yanzu zaka iya cewa babu wanda yasan inda Iluru yake sai Armad da zaren sa. Duk da haka ran Armad na nan a ɓace babu alamun murna ko murmushi duk da kuwa ya gama da Iluru.
Armad ya yunkura ya kira wani dalasimin, "Aiban'shisu!"
A ƙa'idar wannan ɗalasimin zai dauke shi ya kaishi duk inda yake so indai ya taba zuwa wajen kuma yana tuno wajen a ransa yadda zai iya ayyana shi a ransa a lokacin da yake karanta ɗalasimin. Asalin ɗalasimin ci gaban dalasimin Kaban'shisu ne, amma maimakon ya aika mutun shi kuma kewayen da mutun yake nan yake ɗauka ya musanya shi da can wani gurin na inda mutun yake son zuwa.
Ɗalasiman Armad a halin yanzu suna da yawa. Amma lallai daga cikinsu waɗanda yafi ji dasu akwai Aiban'shisu da Zaren Babbar Mutuwa. Farkon Aiban'shisu - Kaban'shisu, farkon Zaren Babbar Mutuwa - Zaren Mayu. Hasalima harin Zaren Babbar Mutuwa shi ne hari mafi girma da aka ga Armad yayi amfani dashi acikin kurkukun lokaci. Wannan yasa Armad yana da yaƙini a ransa yasan ya gama da Iluru, kamar yadda yake da yakini a ransa cewa kiran dalasimin Aiban'shisu da yayi zai kaishi har cikin fadar Iluru. Inda zai kashe kowa da komai. Dama can Iluru yana daga cikin wanda suka bada gudummawar aika Hidaya lahira. Sabida haka tun kafin wannan rana dama can hukuncin kisa ne a kansa. Wanda duk ya kashe wani shima a kashe shi.
Armad ya ɗan ƙifta ido da niyyar yana buɗewa ya ganshi acikin fadar Iluru, to amma a har kullum ba komai ka shirya zai tafi daidai ba, musamman a duniya ta izza wadda kowa yake iya bakin ƙokarin sa yaga ya cimma burin sa. Kuma yadda kake shiri kowa shima shiri yake. Maimakon Armad ya ganshi a inda yake so wato cikin fadar Iluru kawai sai ya ganshi tsaye ƙiƙam a inda yake.
"Aiban'shisu!" Ya kara kiran fasahar. Watakila da kuskure yayi bai kira dalasimin dai-dai ba. Amma dai babu abinda ya faru. Komai yana nan daidai yadda yake kuma bai motsa daga inda yake ba.
Ganin hakan yasa Armad tunanin wataƙila ɗalasimin ne ya samu matsala sabida haka ya kira wani ɗalasimin domin ya gwada.
"Kaban'Zishu!" Abu kamar wasa shima baiyi ba.
"Kaban'Zishu!"
"Kaban'Zishu!"
"Kaban'Zishu!"
Amma ina, babu komai. Kamar ma ba ɗalasimin yake kira ba.
A wannan lokaci Armad ya gano akwai matsala. Tabbas akwai wani abu ba dai-dai ba a wannan guri.
Kamar an amsa tambayarsa kawai sai yaga tekun tana lankwashewa tana malkwadewa. Wataƙila kalmar da Armad yayi amfani da ita ba daidai bace to amma ya rasa kalmar dazai saka wadda zata fi dacewa. Abu guda daya sani shi ne yaga gangar ruwan tana curewa waje guda, ɓangaren kudu ya taso kamar wata tabarma yana hadewa da bangaren arewa. Shima barin yamma ya taso ya malkwado yana nadewa zai haɗe da bangaren gabas. Kaikace katifa ko kuma tabarma ake nadewa. Abu kamar wasa suka fara saka Armad a tsakiya. Babbar katangar nan mara iyaka daya baro a can baya ita ma ta taso akan iska ta fara nufoshi. Sabida girman almarar abin saida Armad ya runtse idon sa ya muttsika shi yana ƙoƙarin tabbatar wa da kansa ko gaskiya yake gani. Domin abin ya wuce hankali.
To amma kamar abin bai isa haka ba sai busasshiyar kasar nan daya wuce a baya da dajin nan na farko suka fara tasowa akan iska suna nufo Armad. Nan take Armad ya gano cewa zamansa anan ba abu ne mai yiwuwa ba. Yai fitar burtu ya yanki hanya. Koda babu fasahar Kaban'shisu da sauran fasahohinsa na sauri ai shi kansa yana da sauri sama da na sauran ma'abota izza duba ga rantsattsen jikin izza da yake dashi.
Armad ya cilla hannu sama inda nan take zaren izza ya tashi yai sararin samaniya. Kafin kace meye wannan zaren ya taba gajimare. Yana tabawa ya manne a jiki ya makale. Armad yabi zaren ya shilla sama domin gujewa haukan dake faruwa a kasan sa. Kasancewar kalmar hauka ita ce kaɗai kalmar data dace da abinda yake gani a wannan lokaci. Yana da kyau mutun ya gane girman ƙasar da take kasan wajen da kuma shi kansa ruwan. Dajin farkon kaɗai yafi garin jekis girma sau uku. Busasshiyar ƙasar tafi dajin girma, shi kuma ruwan yafi su girma duk da kuwa har yanzu Armad bai ga ƙarshen ruwan ba. To ace duk wannan abubuwa sun hade guri guda suna nadewa kamar tabarma ai dole kace hauka ko mafarki.
To kamar duk wannan bai isa haka ba, kawai sai kwatsam Armad yaji wata yar kara a kunnen sa na hagu. Dauke kan da zaiyi kafin ya ankara komai dake duniyar ya dauke dif. Da ruwan da babbar katangar da busasshiyar kasar da dajin duk sun bace babu komai sai hayaki. Kallon farko da zakai wa wajen zai tuno maka da duniyar aljanu inda Armad yaje neman K'Narbig. Idan mai karatu bai mantaba wannan duniya basu da ƙasa. Wajenda ya kamata ace ƙasa ce babu komai sai gajimare da hayaki. To kamar haka wannan waje ya koma.
Ana cikin haka kwatsam sai Armad yaji jikinsa ya fara karkarwa yana rawar dari. Kafin kace meye wannan jikin sa ya fara ci da wuta. Ya ɗauki lokaci kafin a gane ba wuta bace Negrinkin Armad ce take fita daga jikinsa ta lullube shi tasa ake ganin kamar wuta ce. Ana haka aka jiyo ƙara kamar ana fasa nakiya acikin jikin Armad. Sannan kuma daga cikin Negrinkin aka hango Iluru ya sullubo ya fito ya fado kasa. Rigarsa tayi daga-daga kamar an fizgoshi daga bakin kura. Yana haki yai tsalle can gefe guda nesa da Armad.
Armad ya kalleshi cikin mamaki da al'ajabi. A karon farko tun bayan haduwar su fuskar Armad ta sauya: nutsuwar da da take kai ta ɓace an maye gurbin ta da Wasu-wasi. A halin yanzu akwai kokwanto. Armad yasan tabbas murkushe Sarkin Jinzidal abu ne mai wahala. To amma duk da haka fita daga cikin duniyar Negrinkinsa ba abu ne mai sauki ba. Hasalima sanin hakan ne yasa ya tura Iluru ciki.
Bari muyi duba kadan zuwa duniyar Negrinki. Wato dai ita wannan duniya wani shinge ne na musamman wanda yazo da fasahar Negrinkin Armad. Lokaci na farko da muka fara ganinsa bayan Armad ya farkar da Negrinkin sa a ƙarshen littafi na biyu munga yadda Negrinkin take bulbula daga cikin tsokarsa. Zaka iya cewa kamar jinin Armad ne yake juyewa izuwa ita: ta zama Armad, Armad kuma ya zama ita.
Munga yadda Armad ya jefa Han'diyuza ciki amma Sarkin-sarki ta zaro shi ta wata sihirtacciyar hanya da ba'a bayyana ba har yanzu. Kuma munga yadda Armad ya wulla mutane da dama irin su Hasanu da Elbinuil Randuil da Kaizadu ciki a gasar ruhin deba. Kai daga baya ma munga yadda Armad ya haɗa Negrinkin sa da zaren izza ya samar da Zaren Babbar Mutuwa - zaren da yake zuke izza kuma ya zuke jikin mutun. A baya-bayannan munga yadda Armad ya buɗe yar taga zuwa cikin wannan duniya ta Negrinki inda ya aika hare-haren da aka turo musu a ƴar gajeriyar fafatawar da sukai dasu Dul'ururu.
A takaice zamu iya cewa Armad yana iya shiga cikin wannan duniya kuma yana iya tura komai ciki, mutun ko hari ko aljan ko dordor. Ta hakan Armad zai iya guduwa cikinta ya buya idan harka batai daɗi ba, kuma zai iya jan abokin gabansa ciki ya hallaka. A iyakacin jerin fasahohin Armad babu mai yawan amfanin ta. Eh, wasu zasu iya cewa zaren izza yafi ta, to amma a zahiri zaren izza baikai faɗin duniyar Negrinki ba, a ganin Armad fa kenan. Amma a halin yanzu gashi Armad ya jefa Iluru ciki kuma Iluru ya fito duk da a jigace ya fito amma dai ya fito. Ko tayaya aka haihu a ragaya?
"Haha... Na tabbatar mamaki kake. Yaya za'ace na fito daga cikin wannan hatsabibiyar duniya ta Negrinki?" Iluru yayi ajiyar zuciya sannan ya miƙe ya tsaya dai-dai tare da takaita nishin da yake yi. "Duniya mai girma da fadi cike da wuta da narkakkun duwatsu sannan kuma babu hanyar fita? Lallai fasahar ka fasaha ce mai hatsari, nima na yadda, Ikenga ma ya yadda. To amma kai sani babu wata fasaha wadda bata da rauni da nakasu. Tun lokacin gasar ruhin deba muke nazari akan fasahar ka da yadda zamu cimmata, ba tun yau muke nazari akanka ba, Armad. Shin kana tunanin zan tare ka ba tare da shiri ba?"
Maimakon bashi amsa Armad kawai zare takobi yayi ya afka masa. Kafin ya karasa taurari bakwai sun bayyana kan tsinin yaluwar takobin. Nan take nauyi ya dira akan Iluru ya danna shi ƙasa kan gwiwowin sa akan ruwan. Armad ya saukar masa da babban sara mai ɗauke da yaluwar walkiya.
Kasusuwan kafar Iluru sukai ƙara suka fashe sannan kashin gwiwar ya fice fit kamar an sare. Haka ma kasusuwan cinyarsa dana kugunsa. Kafin kace meye wannan kasusuwan kirjin sa sun hade dana bayansa sun murkushe zuciyar sa da kayan cikin sa a tsakiya. Jini yai feshin ya zuba kan ruwan.
"Zancen banza." Armad yayi tsaki ya kade takobin sa.
Har ya juya zai tafi yaji motsi a bayansa. Yana waiwayawa yaga jikin Iluru daya tarwatse yanzu-yanzu akan ruwan yana tasowa kamar ana tsamo naman salla daga tafasasshen mai. Kasusuwan da suka rududduge suka fara warwarewa suna hadewa suna zama jiki. Tsoka da jijiya suka ware suka koma mazauninsu. Cikin abinda bai wuce kace uffan ba komai na jikin Iluru ya koma daidai kamar babu abinda ya faru. Iluru ya dawo sabo.
"Ban taɓa tunanin ƙarfinka zai sa nayi amfani da kololuwar fasaha ta ba. Wai shin ka taba tunanin mai yasa duk al'ummar denizawa babu basamude daga ni sai shugaba Deniz Curu-curu? Idan baka taba tunani ba to zan gaya maka. Sirrin gangar jikin da kake nemarwa Hidaya dashi aka tsumamu. Bari na nuna maka abinda zan halaka ka dashi." Iluru ya ciji yatsansa jini ya fito sannan ya shafa jinin a goshinsa. Take goshin ya fara haske sannan wata miyura ta bayyana akan goshin.
Wannan miyura sabon samfuri ce wadda ba'a taba gani ba. Saɓanin ta Armad mai mutun-mutumi ita hoton rana ne a tsakiya, sannan kuma babu takobi kawai sai rubuce-rubuce sun zagaye ranar.
Bayyanar miyura keda wuya wasu zane-zanen layi-layi masu ɗauke da hatimi suka kewaye jikin Iluru kamar an daure shi da igiya. Murmushi ne akan fuskar Iluru kai kace har yanzu basu fara fadan ba kawai gabatarwa ake yi.
"Duk wata ƙabila data rayu a Farkon Lokaci suna alfahari da miyurar su, kuma suna amfani da fasahar dake cikin ta. Wai mai yasa mutanen Dogon Zauren dana Rawar Sani suka daina amfani da miyura? Nasan baka sani ba, bari na gaya maka. Asirin da akaiwa ƙabila ta shi ne yasa aka karya tafarkin miyura. A da can yadda ake so a zama Sammai ko Jemai haka ake so a zama Otaki. A tsarin izza na yanzu Kassai ne matakin farko, sai Jemai, sai Sammai sai kuma Deba. A da can kuwa matakan izza sune Otaki Kasa, sai Otaki Jemage, sai Otaki Sama, sai kuma Otaki Deba. Da miyura ake amfani a hau wannan matakai ba kamar yanzu ba da ake amfani da izza da kuma aljanu.
"Miyura ta tafi taka asali da dadewa a duniya. Idan kana ji da izza to ni kuma inada rana."
Take jikin Iluru ya fara girma yana murmurdewa. Dantse yana ƙara kauri da hauhawa. Kasusuwan Iluru suka ƙara girma suka fashe suka ƙara tsayi. Kafin kiftawar ido da bismilla ya ninka tsayinsa da kaurinsa. Kai kace wani sabon basamude ne ya bayyana. A wannan lokaci Iluru ya kai girman Deniz Curu-curu dake tare da Ikenga.
Idan ka haɗa wannan sabuwar siffa da kuma layi-layin hatimin dake kewaye da jikin Iluru sai kaga abin ya zama wani abin firgici. Amma kamar abin bai isa haka ba, katsam sai aka hangi wata ƙatuwar rana ta bayyana a sararin sama. A hankali a hankali ranar ta girmama ta faɗaɗa ta rufe sararin sama baka ganin komai sai ita sai Iluru. Kai babu ko tantama a wannan lokaci Iluru yayi kama da bajimin shaidani na Farkon Lokaci.
Amma Armad na gefe idanunsa a kafe babu ko alamun tsoro ko tashin hankali a tattare dashi, kai kace ya riga yayi nasara a yakin. Zaka iya cewa kaɗai ganin siffar Iluru a wannan lokaci zai iya tarwatsa zukatan abokan gaba, amma ko gezau Armad baiyi ba. Yana tsaye rike da takobin sa yana jira Iluru ya kammala abinda yake yi.
Iluru ya nuna kansa da hannu. "Wannan itace asalin siffa ta. Lokaci yayi, Armad."
Da farko Armad baiyi niyyar magana ba kwata-kwata amma daga baya ya kasa daurewa ya dubi Iluru ya ce, "lokacin me kenan?"
"Hahaha... Harma tambaya kake, lokacin mutuwar ka mana. Kana tunanin a yadda nake a haka zaka iya yin nasara akaina? Ka daina mafarki."
Wato duk wanda ya hango wannan jarumai biyu daga nesa yasan indai siffa tana bada nasara to anfi ƙarfin Armad. Kallo daya kacal zakai kace bajimi ne da ɗan tsaki, kuma Armad shi ne ɗan tsakin badan komai ba sai dan kankantar sa akan basamuden dake gabansa.
Amma duk da haka babu fargaba, tsoro ko bakin ciki a fuskar Armad. Kasan idan shiri yayi shiri sai kaga yaro a gaban Sarkin Jinzidal amma baya ko ɗar.
Armad ya daga takobin sa ya ƙara afkawa Iluru. Harya karasa Iluru bai motsa ba. Armad yasa takobinsa ta ɗorawa ya sari kasangalalin ƙafar Iluru tunda yayi masa tsayi ya sari wani wajen ba nan ba. Wata kara tayi sama kamar an sari bakin karfe, kura ta turnuke.
Can bayan abubuwa sun lafa Armad ya bayyana rike da takobin sa, kaifin ta yana kan sangalalin kafar Iluru. Ya kamata ace kodai nauyi ya murkushe kasusuwan Iluru ko kuma kaifi ya shige shi amma bisa mamaki ko kwarzane babu a jikin sa. Armad ya kurawa wajen daya sara ido amma babu wani rauni ko alamun sa.
"Haha... Ka gwada iyakacin yadda zaka iya amma kai sani cewa wanda suka fika sunyi sun gaji. Wannan jikin shi ne jiki mafi tauri da kwari a ban kasa. Hatta Sarkin-sarki dashi tayi amfani ta samar da fasahar Tauri." Iluru na rufe baki ya kara kyakyacewa da dariyar mugunta. Duniya tayi masa dadi domin kuwa ya riga yasan yayi nasara akan Armad.
"Zaren Babbar Mutuwa!"
Take gidan gizo-gizo ya bayyana sannan zarurruka suka bayyana suka hadiye Iluru yana cikin dariya. Izzar Iluru ta ɓace sannan siffarsa ma ta ɓace.
A wannan karon Armad na tsaye yana jira domin yasan Iluru zai fito.
Ai kuwa ba'ai dakika goma ba sai ga Iluru ya fito. Amma saɓanin dazu yanzu jikinsa a haɗe yake babu ko kwarzane kamar ma babu abinda ya afku.
"Hahaha... Armad kenan. Baka ji amma na gayamaka mun gano sirrin Negrinkin ka. Idan zaka canja wata dabarar ka canja. Kuma kai sani ina da rumbun izza na fasahata ta kwangila. Ko sau nawa zaka zuke min izza zan dawo da abata. Wannan shi ne amfanin zama sarkin Jinzidal. Wato tun anan anfi ƙarfinka. Baka da fasahar da zaka iya ratsa fatata, kuma ko ka kaini cikin duniyar ka fitowa ta abu ne mai sauki, daɗin dadawa zukemin izza bashi da amfani domin inada rumbun da zamu iya shekara anan baka zuke ba. Baka taɓa faɗa da Sarkin Jinzidal ba amma mu din na daban ne. Ba'a tarar mu fada sai kana da fasahar kwangila."
"Ita zara ai bata barin dami, sarkin Jinzidal. Mu gwada tsakanin zaren izza ta da abinda ka tara na izza." Inji Armad. Yana rufe baki yai tsalle baya ya tafa hannayen sa.
"Zaren Manyan Mayu!"
Take gidan gizo-gizo ya ƙara bayyana ya hadiye Iluru. Amma a wannan lokaci izzar sa kawai aka zuke aka bar jikinsa. To amma kafin zaren ya ɓace izzar Iluru ta dawo. Wato ya kamata mai karatu ya fahimci cewa koda kana da izza a ajiye acikin tsarin ruhin ka zukar wannan izza zuwa cikin jikin ka ta zama taka wadda zaka iya amfani da ita wajen kai hari abu ne da yake buƙatar lokaci da kwarewa. Munga a baya yadda Armad ya ɗauki lokaci kafin ya zuke shekarun izza dubu ɗaya daya samu a ƙarshen gasar cinikin bayi. Munga yadda kwamandun Armad suka sha wahala acikin kurkukun lokaci a sanda Armad yayi ƙoƙarin basu shekarun izza ya tura su deba. Abubuwa irin su amai, gudawa, ciwon kai, farfaɗiya da zubar jini ta hanci duk sun faru. A baya munga yadda shi kansa Armad duk da yana da miyura da take da alaka da izza idan ya zuki izzar ya ƙara yawan tasa bata zama a jikinsa ficewa take ta ɓace daga zarar ya gama, badan komai ba sabida wahalar haɗe izza da jiki. To amma a daidai wannan lokaci izzar da Armad yake zukewa Iluru takai dubu goma a duk sanda yayi amfani da zaren izza, to amma a take Iluru yake dawo da abarsa ta hanyar debo shekarun izza daga rumbun sa na kwangila ba tare da wata wahala. Wanda hakan ke nuna ya saba yin hakan kuma ya kware. Ba wani abun mamaki bane idan akace ba wannan ne karo na farko ba da Iluru yake fafatawa da zuri'ar wilbafos ba. Watakila dama ya sansu kuma ya shiryi abinda zaiyi a yayin faɗa dasu.
Armad ko kadan bai gajiya ba.
"Zaren Manyan Mayu!"
"Zaren Manyan Mayu!"
"Zaren Manyan Mayu!"
Yana zukewa Iluru izza shi kuma Iluru yana dawo da ita. Armad bai damu ba, yasan cewa a juri zuwa rafi wataran za'a sha ruwa ko ba'a so. Kuma indai anci gaba da hakan tofa lallai zai ƙarar da izzar Iluru komai daren dadewa. Alamari ne kawai na lokaci.
Sai dai kuma wani abu da Armad ya fahimta shi ne Iluru haka yake so aci gaba da jan wannan fada tunda baya so Armad ya koma wajen su Nusi. Idan son samun Iluru ne ya tsayar da Armad a wajen har tsawon ranaku suna abu ɗaya kaga a wannan lokaci Ayubu ya gama shirya masa tsiya. Nan take Armad ya yanke shawara jan faɗa ba nasa bane. Lokaci yayi da zaiyi azama ya koma wajen iyalin sa.
To amma wani hanzari ba gudu ba, Zaren Manyan Mayu baiyi ba, zaren Babbar Mutuwa baiyi ba, takobin ɗorawa ta Hidaya batai ba. Tabbas Armad yasan fasahar Wasu-wasi ko Hisabi suma baza suyi ba tunda matsalar a wajen taurin jikin Iluru ne bawai saurin ba, Wasu-wasi da Hisabi kuma sauri suke karawa. Dukkanin wannan fasahohi na Armad manya ne wanda yake ji dasu tsahon lokaci, to amma idan baza suyi ba dole ne ya fito da sabon shiri tunda dai ba'a banza ake ce masa K'Narbig ba.
Nan take Armad ya girgiza takobin sa inda wasu sabbin taurari uku suka bayyana ƙari akan bakwan farkon.
"Ɗorawar Abada!" Inji Armad.
A wannan karon bawai nauyi ne ya karu ba, kawai wani bakin haske ne ya bayyana a kaifin takobin. Iluru na ganin haka ya tafa hannayen sa. Ƙusoshin mairakana guda goma suka bayyana suka hade da juna izuwa babbar ƙusa guda ɗaya. Iluru ya damki wuyan ƙusar kamar wanda ya riƙi takobi sannan ba tare da bata lokaci ba ya afkawa Armad. Shima Armad afka masa yayi. Ga takobin ɗorawa, ga kuma ƙusar haske. Haduwa kawai sukai amma saida sama ta fara girgiza tana rugugi. Cikin kwarewa Armad ya sullube ta ƙasa ya kaiwa Iluru sara ta ƙasansa, shima Iluru amfani yayi da damar ya kaiwa Armad suka ta sama da basamudiyar ƙusa.
Abin mamaki duk su biyun zasu iya kaucewa amma kuma kaucewar bazata basu damar samun abokin karawarsu ba, sabida haka suka gwammace su sari juna kawai a wuce wajen. Mai ƙarfi ya rayu, mara ƙarfi ya motsa lahira.
Takobin Armad ta sari gefen cinyar Iluru inda ta yanka ta shige ciki har zuwa ƙashi, jini yayi feshi.
A gefe guda kuma ƙusar Iluru akan kafadar Armad ta sauka. Kafadar tayi bindiga amma kuma take ta juye izuwa walkiya ta dawo daidai.
Wani abin mamaki shi ne duk da kafadar Armad ta dawo walkiya amma akwai dabbare-dabbaren tabo akai wanda tuni ya kamata ace ya kone. Armad ya juye izuwa mutum, amma duk da haka taɓon yana nan. Kuma irin taɓon nan ne mai dankon bala'i. Kan kace meye wannan ya makalewa Armad hannu da kafada ya hanashi motsi.
Cinyar Iluru feshin jini take amma dariya yake ganin hannun Armad baya motsawa. "Nayi nasara akanka Armad. Nini kaɗai ma na isheka. Ƙusa ta ta mairakana wadda ni na kirkiro fasahar da kaina bawai ta haske bace ba kuma walkiya bace, saɓanin yadda kuke tunani. Taɓo na dafa da walkiya har saida ya narke sannan na hadashi da wata walkiyar na dama. Duk ƙusar daka gani walkiya ce da tabo da walkiya. Kuma taɓon irin na musamman ne saboda irin ku. Yanzu ya hanaka motsi amma kaɗan ka gani. Daga sanda ya shiga cikin tsokar ka magana ta kare. Wai kana tunanin har ka kai matsayin da zaka iya cin galaba akan sarkin jinzidal? Ka sauya lissafi yaro."
Armad ya nuna cinyar Iluru wadda har yanzu take zubar jini ya ce, "akace bakwa jin ciwo? Wai rana tana hana a ratsa fatar ku. Amma gashi kana ta zuba, mai ya faru?"
Iluru yayi jim tare da ƙurawa wajen ido. Akwai wani baƙin haske ya kewaye ciwon wanda kuma shi ne ya hana ciwon warkewa. Zaka iya cewa kamar wani nauyi ne na musamman wanda yake wara ciwon wanda kuma ya hana tsoka da kashin hadewa.
Iluru ya harari Armad. "Wannan ai satar fasaha ce, yaya akai ka samo dauwamammen sara?"
"Satar fasaha? Kasan mai kake cewa kuwa?"
"Kaga, Wilbafos, ko mai zaka faɗa kuma koma wane suna zaka sakawa wannan fasaha ba 'Dorawar Abada' ba, ni nasan wannan dauwamammen sara ne. Kuma tabbas sai na rubuta wasika na turawa Bihanzin. Baza mu yadda da satar fasaha ba."
"Haha..." Armad ya fashe da dariya, "sarakunan Jinzidal kuna da wuyar sha'ani. Izzar ku bata da adadi, kowa acikin ku yana da tsohon shiri da dogon tarihi da kuma manufa. Bakwa zuwa ƙasa ta sauki. To amma wannan abubuwa sune suka sa ake kiran ku da 'wanda suka fi kowa karfi a doron kasashen kasa'. Sai dai kuma kash, yadda kuke a shirye, muma da shiri muka nazo."
Tafa hannu kawai Armad yayi ya kira sabon dalasimi. Take walkiyar dake jikinsa ta juye izuwa jajawur, sannan ta ƙara juyewa izuwa baka-kirin. Kafin kace meye wannan taɓon daya hana shi motsi ya ƙone ƙurmus yabi iska.
Armad yayi mamakin jin yadda ƙusar Iluru take domin kuwa bai taɓa tunanin taɓo Iluru yake narkawa ya haɗa ta ba. To amma duk wannan bai dami Armad ba. Tunda dai zai iya jiwa Iluru ciwo da fasahar Ɗorawar Abada ai an gama.
Armad da Iluru suka ƙara jada baya suka afkawa juna. Armad ya kai masa sara shi kuma ya kawo masa suka da ƙusa a kirji. Abin mamaki kawai sai aka ga wata taga ta bayyana a kirjin Armad daidai inda ƙusar zata soka. Ai kuwa tana zuwa ta shige cikin tagar. Idan ka duba cikin tagar zaka hangi narkakkun duwatsu da wuta tana balbali. Duk wanda ya taɓa ziyartar duniyar Negrinkin Armad cikin sauki zai gane ita ce.
Idanun Iluru suka zaro cike da mamaki. A wannan lokaci ya fuskanci cewa wato Armad kawai kyale shi yayi a baya daya samu dama ya taba jikinsa.
A lokaci guda kuma takobin Armad ta sari gwiwar Iluru jini yayi feshi. Biyu kenan.
Yaki ya dawo sabo suka kara rincabewa da kaiwa juna munanan hare-hare kowa yana kokarin daukan ran dan uwansa. Cikin abinda bai wuce dakika bakwai ba sun aikawa da juna sara ashirin-ashirin. Armad na nan garau amma Iluru kawai zubar jini yake. Sai dai duk da haka babu alamun jigata a tattare dashi. Jinin da yake zubarwa yana da yawa, to amma idan ka dubi cewa basamude ne zaka ga cewa jinin baifi cikin cokali ba a wajensa.
Sukai tsalle baya suna kallo juna cikin nishi. Lallai idan aka ci gaba da faɗan nan a haka to zasu iya shekara babu wanda yaje ƙasa. Iluru bai damu ba, amma Armad yana da buƙatar ya koma gida wajen iyalansu kafin a aikata masa ta'asa.
Iluru ya dube shi cikin gatsali ya ce, "zaren izza baiyi ba, takobin Hidaya batai ba, Negrinki batai ba, meye ya rage maka?"
Maimakon Armad ya bashi amsa murmushi kawai yayi. Ba tare da bata lokaci ba ya ɗora hannun sa na dama akan rufaffe idon sa na hagu. A zuci ya kirawo wasu dalasimai sannan ya jada baya ya gyara tsaiwar sa.
Shima Iluru gyara tsayuwar sa yayi yana jira yaga mai Armad zaiyi amma a lokacin ne yaga Armad ya mayarda takobin sa cikin kufenta sannan ya maida ita cikin gidanta inda ya dakko ta.
"Haha..." Iluru ya kyakyace da dariya, "ka hakura ne tun ba'a je ko'ina ba? Kasan har yanzu akwai fasahar da ban nuna maka...."
Yana cikin magana kalmomin suka maƙale masa a maƙogaro saboda motsi da yaji a bayansa. Yayi ƙoƙarin ya waiwaya yaga waye a bayansa domin a iya saninsa daga shi sai Armad a wajen to amma jikinsa yaƙi bin umarnin sa. Dole ya tsaya cak a inda yake yana ƙoƙarin gano mai yake faruwa, mai yasa jikinsa yaƙi motsawa.
Armad baice komai ba suka ci gaba da kallon juna. Armad yasan abinda ke faruwa sarai domin aikinsa ne, shi kuwa Iluru Wasu-wasi kawai yake.
Ana cikin wannan hali wani mahaukacin sara ya bayyana a kirjin Iluru tun daga kafadarsa ta dama har zuwa kugunsa. Jini ya fara ambaliya kamar an sako teku. Abin mamaki babu wanda yaga sanda akai saran, kuma babu wanda yaga mutumin da yayi saran. Kai hatta takobin da tayi saran ba'a gani ba. Ga kuma ƙarin al'ajabi kayan cikin Iluru sun fara zagwanyowa suna zubowa daga cikin sa suna dalalowa ƙasa.
A wannan lokaci idan da Iluru ya samu dama ya waiwaya zai samu damar ganin wanda ya aikata masa wannan ta'asa. Wata budurwa ce take maida takobin ta cikin kufenta a bayan Iluru. Idan ka lura sosai zaka ga tsarin surar takobin shi ne siffar idanuwan wannan budurwa.
"Suna na Saif-Al-Barzak, ka tuna shi idan ka isa lahira zaiyi maka amfani." Inji budurwar a yayin da take ƙarasa maida takobin ta.
A daidai wannan lokaci idanun Armad na hagu wanda da a rufe yake haske yake yana walkiya kamar rana ta haska dinare.
Zubewa Iluru yayi akan gwiwowin sa. Ciwon dake kirjin sa wanda a halin yanzu kayan ciki suke zubowa ta ciki ya fara yin tsatsa kamar wani tsohon langa-langa. Kafin kace meye wannan jikin Iluru wanda yake alfahari dashi ya fara motsewa yana yamushewa. Iluru ya kasa tsaiwa kan iska inda ya sulluba ya faɗa ƙasa cikin gajimaren dake ƙasa.
An kammala faɗa. Iluru yaje kas.
Sai dai kuma shima Armad yaji jiki a yayin wannan fafatawa, domin kuwa a dai-dai wannan lokaci budurwa data yi wannan aiki juyewa tayi ta koma iska sannan ta shige cikin rufaffe idon sa. Haka na faru ya fadi ƙasa yana nishi. Lallai kana gani kasan amfani da Saif-Al-Barzak yana shan izza da yawa kuma zaka iya cewa har yanzu Armad bai kware da wannan sabuwar fasaha tasa ba. Hasalima har yanzu bamu san wacce irin fasaha bace. To ma wai wacce irin takobi ce take ɗaukar siffar yar budurwa? Kaima kasan al'amari ne na manyan ma'abota izza masu kama da aljanu farko.
To koma dai meye an gama da Iluru. Kawai lokaci Armad yake bukata ya ɗan huta ya dawo da ƙarfin sa kafin ya rankaya ya koma fada ya aikata Ayubu, kololuwar aikatawa domin kuwa shi kaɗai yasan irin abinda ya ƙudure zaiyi masa idan ya cafke shi.
Ana cikin haka Armad ya fuskanci zaman sa anan bata lokaci ne sabida haka ya miƙe zai lallaba a haka a yadda yake ya tafi fadar Iluru. To amma juyawarsa keda yaga wani saurayi tsaye kikam a bayansa.
Wannan saurayi ba Iluru bane, amma Armad ya sanshi farin sani.
"Suna na Ikenga O. Bayajidda." Inji saurayin da wata irin nutsattsiyar murya.
Armad ya yamutse fuska. "Nasan waye kai, mai kake yi anan kai kadai? Idan na kashe ka anan abin bazai bawa yan kallo nishadi ba."
Ikenga ya ɗan karkata kai kamar yana ƙoƙarin fuskantar abinda Armad yake faɗa kafin daga bisani ya kada kafada, ya ce, "bani kaɗai bane, Armad Wilbafos." Yana rufe baki ya zare takobin sa. Yadda kasan zare takobin wata inkiya ce ko kuma wani kulumboton tsafi yana zare ta mutun biyar suka bayyana a bayansa. Biyu samudawa, daya yaro wanda bazai haura shekara goma ba, biyu tsoffi. "Amma bawai saboda kai nake yawo da kwamanduna ba, sabida Bihanzin nake yawo dasu. Dukkanin mu nan munga fafatawar ka da Iluru, kuma mun yanke shawara karfin ka bai wuce karfin sarkin jinzidal ba, duk kuwa da horon daka samu a kurkukun lokaci. Wannan tawagar ina yawo da ita ne sabida Bihanzin wanda a zahiri zai iya kashe ni, bawai kai ba wanda har yanzu kana matakin sarakunan jinzidal."
Armad yayi duba izuwa ruhin sa inda takobinsa take ya ce, "Saif-Al-Barzak, wancan fasaha zamu yi amfani da ita."
Saif-Al-Barzak tayi gyaran murya. "Ka tabbata? Kada fa ka bude ido kaga shekara biyu ta wuce baka san ya akai ba." Inji ta. Kana jin muryar ta kasan akwai kokwanto.
"Aika shi lahira nake niyyar yi bawai ji masa ciwo ba." Inji Armad.
Kada da a manta wannan tattaunawa daga Armad sai takobin sa su kaɗai suke ji.
"TULADAN-NAN-GALAK!!"
Armad ya kirawo babban ɗalasimi.
Ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa! Ana dara ga dare yayi. Shi yaya Armad zaiyi da wannan babbar tawaga?
Comments
Post a Comment