Skip to main content

BABI NA 277: Inara da Ururu

 Ƙatotuwar ƙawanyar wuta mai faɗin zira'i sha biyar ta taso daga cikin garin Faideba ta dira akan Lamarudu tare da dubunnan mayaƙan dake tare dashi suna ƙokarin hawa cikin garin. Garin Faideba a saman tsauni yake, sabida haka shiga cikinsa matsala ne, musamman duba ga cewa akwai wasu mutun biyu masu kama da juna dake jagorantar mutun dubu wajen jifan su da hare-hare. Duk da cewa Nazara ya samarda gadar bishiyu wadda ta tashi daga ƙasan tsaunin zuwa cikin garin hakan bai rage wahalar da su Lamarudu suke fuskanta ba wajen shiga garin. 


Kafin ƙawanyar wutar ta dira suka dare suka bata waje. Mutun bakwai suka zame suka faɗa ƙasa a garin kaucewa. Wasu kuma basu da sauri sosai, lamarin da yasa wutar ta ƙone su ƙurmus kafin su matsa. Wasu kuma garin kaucewa suka gwaru da ƴan'uwan su suka faɗi ƙasa, al'amarin da yasa suma basu samu damar kaucewa wutar ba. Kafin su gama farfaɗowa daga halin da suke ciki, wata ƙatotuwar ƙawanyar wutar ta ƙara tasowa daga sama. Idan ka ɗaga kai zaka hangi sadaukai biyu masu kama da juna wanda idan mai karatu zai tuna su ake kira da Tagwayen-Auni (wanda suka taka rawar gani a yaƙin sarakunan Jinzidal a shekarun baya), suna jahorantar sahu-sahu na sadaukai a bayan su. A nutse suke sosai. Kana gani kasan sun shirya kuma sun san hannun juna. Su Lamarudu suma a shirye suke, to amma matsalar ita ce rundunar basu san hannun juna ba. Mutun dubu goma dake cikin rundunar Lamarudu bai taɓa ganin su ba sai a ranar. Yawanci mutanen Nusi ne da kuma na Nazara wanda Farin Yashi ya kawo. 


Lamarudu ya katse tunanin sa tare da yin tsalle ya tashi sama ya tunkari dunkulen wutar a sama. Abin mamaki wutar na taɓa jikin sa sai ta tsaya cak, kamar ta daki bango. Lamarudu yaso ya adana izzar sa zuwa sanda zasu shiga cikin garin sabida shirin kota-kwana, to amma bazai tsaya yana gani mutanen sa (duk da ba daga rundunar sa suka fito ba) su ringa mutuwa bai yi komai ba. 


Abu kamar wasa wutar na taɓa jikin sa ta fara raguwa: daga faɗi zira'i sha biyar ta dawo sha uku, sannan bayan daƙiƙu biyar ta ƙara dawowa goma. A hankali ta zuƙe ta dawo ƴar ƙarama. Wanda yake kallon abun daga nesa zaice jikin Lamarudu wutar ta shiga, to amma idan kayi amfani da yanayin izza zaka gane cewa abin ba haka yake ba. A zahiri izzar dake jikin wutar, wadda ita ce mai (ko kuma fetur) da wutar ke amfani dashi, ya zuƙe. Kada ku manta sunan sa Lamarudu Wilbafos. Bashi da wata babbar fasaha ko aljani na kuzo-mu-gani, to amma yana daga cikin ƴaƴan Wilbafos wanda suka fi kowa kwarewa wajen kwatar izza daga hari. 


Lamarudu ya ɗagawa mutanen sa hannu, yayi musu inkiya dasu taho. Ba tare da ɓata lokaci ba suka kama gadar suka ci gaba da ɗanewa. Shi kuwa Lamarudu tsayawa yayi tsayin daka ya fuskanci masu jefo musu da hare-haren. Tunda da akwai nisa a tsakanin rundunar biyu, babu wata hanya da Tagwayen-Auni ke da ita banda su tsaya su jira hawowar mutanen Lamarudu. 


Ai kuwa haka akai, cikin daƙiƙu kaɗan suka ƙarasa saman tsaunin. Suna hawa suka afka musu. Lamarudu na nesa ya girgiza yai ajiyar zuciya. Dama ya faɗawa Farin Yashi kada ya tafi. Dole ana buƙatar wanda ya fi kusa da sojojin ya shugaban ce su. "Shugaba Nazara yana neman taimako, nasan zaka iya kula dasu kafin na dawo." Inji Farin Yashi a lokacin da zai tafi. Gashi yanzu rabin sa'a har yanzu bai dawo ba. Lamarudu ya ja dogon numfashi. A marsayin sa na kwamanda ya kamata ace su tsaya su jira umarnin sa kafin su afka. To amma babu wanda ya kula shi. Niyar sa yasa su kewaye su, su saka su a tsakiya tunda sun fi su yawa, sannan su afka musu. To amma yanzu wannan damar ta kufce tunda tuni sun yi gaba-da-gaba. Wannan ita ce matsalar a haɗa ka da baƙuwar runduna.


Tagwayen biyu sune matsalar tunda duk ragowar na bayan su ƙananun Sammai ne, wasu ma Jemai. Bayan ƴan lissafe-lissafe yai tsalle ya dira a gaban tagwaye. Yau za'a yita ta ƙare.


***


A gefe guda tuni yaƙi yayi tsamari tsakanin Inara da Ururu. Mutane shida masu baƙaƙen idanuwa suna fuskantar mutane goma sha ɗaya ma'abota walƙiya, wanda Inara yake jagoranta. Idan mai karatu bai mantaba ƴan goma sune mutane goma da Nostaljiya ta haɗa da Armad suka karɓi kwangila a wajen sa. Inara kuma ba baƙo bane. Shi ne saurayin nan da suka haɗu da Armad a jirgin ruwa mai suna Gashin Balbela, bayan mutuwar mahaifin sa. Inda Armad ya riƙe shi a matsayin ɗa kuma ɗalibi. 


Su kuma wannan mutane shida na Ururu duk fuskokin su a rufe suke. A wannan lokaci suka miƙa hannu a tare suka cire niƙabin dake fuskar su. Inara ya yamutse fuska. Akwai abin al'ajabi tun daga yadda mutanen shida suka miƙa hannayen su sama suka cire niƙabin. Tun farko daya gansu ya fuskanci cewa akwai wani abu a tattare dasu, to amma sabida yadda suka rufe izzar su da jikinsu da fuskokin su bai tantance menene ba. Amma a yanzu da suka motsa ya fara ɗaukar haske. 


Na farko dai kauri da launin hannayen su iri ɗaya ne sak, babu maraba tsinke. Kai bama wannan ba, tsayi da faɗi da fasali da ƙira ta waɗannan mutane shida duk iri ɗaya ne sak. Ba abin mamaki bane a samu mutun biyu masu tsayi da faɗi iri ɗaya, to amma daga inda ya wuce biyu ya zama uku ko huɗu ko shida to lallai zakai mamaki. Musamman duba ga cewa duk wannan mutane Ururu ne. Duk wannan bai sa Inara ya kaɗu ba sai da suka cire niƙabin dake fuskar su ya ga fuskokin su. Abu na farko da yafi jan hankalin sa shi ne MIYURA. Akwai ɗamfareriyar miyura sak irin ta Armad a goshin su. 


Wani ƙarin abin mamakin waɗannan mutane shida kamar su ɗaya sak. Zaka iya cewa ƴan-shida ne, sabida rashin datacciyar kalma, to amma kamar dake tsakanin su tafi ta ƴan'biyu. Mata ne to amma babu komai a ƙirjin su... idanun Inara sukai ƙasa zuwa ƙirjin waɗannan mata. Nan take ya gane cewa akwai sulken auduga a jikin su, wanda yake ɓoye siffa tayadda baka iya gane mace ko namiji ba. 


Ko mai mata shida ƴan ƙabilar Ururu suke yi da miyurar Armad?! Inara ya girgiza kai ya mittsika idanun sa domin ya ƙara ganin miyurar sosai. Ita ce dai. Tambari mai ɗauke da zagaye uku: na farko rubuce-rubucen ɗalasimai, na biyu takubba uku masu kewaya juna, na uku mutun-mutumi. 


"Suna na Suwainah Ururu. Ina ubangidan ka Armad Eyriyon? Ko ku fito dashi ko na kashe kowa da komai." Sautin murya shida masu magana a tare ya ƙara rikita Inara. Idan ka ɗauki kowacce murya tana bada amon izza mai ɗaukan hankali. Haɗa muryoyin waje guda yasa iska girgiza tana darewa sabida bata iya ɗaukan nauyin izzar.


"Armad?" Kiran sunan 'Armad' da Suwainah tayi yasa hankalin Inara ya ɗugunzuma. Hankalin sa kwata-kwata bai kan wajen sunan 'Eyriyon' data haɗa dana Armad ba. Duk wani tsoro da fargaba dake zuciyar sa ya kauce. Idanun sa sukai jajawur kamar ɗan-bida, hancin sa ya fara tiriri kamar ziga-zigi. "Ba sosai nake son kisan mace ba... Amma ke har kin isa ki kira sunan shugaba gatsal-gatsal?" Inara yai kururuwa ya afkawa matan shida. Ƴan-goma, wanda dama can basa jin bari, suka bi bayan sa da manyan fasahai da baƙin nufi irin na arnan daji. 


Ɗaya daga cikin Suwainah shida ta shige gaba, ta ce, "Ku barni na yi." Ragowar biyar ɗin suka gyaɗa kai tare da ƙyale ta ta shige gaba. 


Sai da ta jira saura taku uku su haɗu da Inara sannan ta tafa hannayen ta tare da kiran babban ɗalasimi.


"[Zaren Manyan Mayu] [Zaren Mutuwa]." 


Tana rufe baki izzar su Inara da ƴan-goma ta ɓace ɓat. Kai kace ba'a taɓa haliitar izza a jikin su ba. Bayanin zaifi shiga kunne idan mai karatu ya tuna cewa Inara jikin Sikai ne dashi, sannan biyu daga cikin ƴan-goma arnan daji ne wanda saura ƙiris su shiga Deba. Ragowar manyan Sammai ne. 


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...