Babi na 109: Rawar Aljanu
Ikenga ya ɗanyi shiru yana nazarin fuskokin waɗannan shugabanni dake gabansa kafin daga bisani ya ƙarayin murmushi ya gyaɗa kai ya ce, "a har kullum ni na yarda cewa yana daga babban rashin adalci aban ƙasa ya zamanto ka hanawa ɗan adam zaɓi. Domin kuwa a duk lokacin daka hanawa mutun zaɓi to kamar kana tursasa shi ne dole sai yayi abinda kake so. Ni Ikenga bana tursasa kowa, kuma ina mutunta duk zaɓin da mutun ya yankewa kansa. Hakan nema yasa nayi tattaki izuwa wannan ƙasa taku domin na baku zaɓi. Duk da a zahiri bawai takanas-ta-kano na taso nazo nan dan na nemi mubayi'arku ba, kawai dai ina kan hanyata ne ta zuwa wani aiki amma naga cewa ya kamata kuma na ƙaraso na baku zaɓi."
Ikenga na zuwa nan a zancensa wani daga cikin shugabannin ya tari numfashinsa ya ce, "wai wanne irin zaɓi kake zance ne?! Kana ta cewa zaɓi, zaɓi, amma kaƙi faɗan wanne zaɓi kake zance."
Ikenga ya ɗagawa mutumin hannu sannan ya amsa da cewa. "Zaɓi akan wanda ya kamata al'umma su riƙe a matsayin jagora. Shekaru masu yawa da suka gabata mutane sun yadda cewa babu wasu shugabanni da suka isa a bisu face sarakunan gidan Wilbafos. Bayan tsahon lokaci zamani ya rushe ƙarfin ikon gidan Wilbafos aka dawo biyayya ga sarakunan jinzidal da kuma Ururu. Sai dai kuma saboda wannan sauyin zamani da aka samu har yanzu akwai wanda basa biyayya ga sarakunan Jinzidal da kuma Ururu, misali daga ciki kamar ku Ƴantattun-mutane.
"Nazo ne domin na bawa irinku da har yanzu basu da wanda suke wa biyayya ZAƁI. Ku zaɓi gidan Wilbafos ko kuma gidan Bayajidda ko kuma Ururu. Babu wanda za'a tursasawa, hasalima duk da cewa zanyi farin ciki idan kuka zaɓi gida na amma bazan damu ba idan kuka zaɓi sauran gidaje. Amma dai abu guda ɗaya da nake so na gaya muku shi ne ku buɗe ido kuga waye ya cancanta. Lallai akwai yaƙi yana nan tafe nan bada daɗewa ba, waye wanda kuke gani zai iya baku abinda sarki Eyriyon
da sarki Aldaima suka kasa."
Ikenga ya ƙara yin shiru yana nazarin fuskokinsu. Can ya buɗe baki ya ce, "Idan akwai mai tambaya to, idan kuma babu zan tafi zuwa wani lokaci dazan dawo naji amsoshinku."
Mutumin daya fara magana wanda ga dukkan alamu shi ne shugaban mutanen ya ƙara jan gemunsa sannan ya dubi Ikenga ya ce, "hmm.. ZAƁI? Lallai indai da gaske kake zaɓi kake so ka bawa mutane to kazo da sabon salo. A tsahon rayuwa ta babu wanda ya taɓa zuwa daga babban gidan ya nemi zaɓin mu akan wani abu. Amma maganar muyi maka biyayya wani abu ne daban. Kaje zamu yi shawara zuwa nanda shekara ɗaya."
Koda jin haka sai Ikenga yayi murnushi sannan ya bi kowannensu ya gaisa dashi sannan ya nufi bakin ƙofa. Harya kusa fita ya juyo ya ƙara da cewa, "akwai wani abu guda da nake so duk wanda ya yanke shawara zai bini ya sani. Ni fa tsari na na ɗaukar FANSA ne da ramuwar gayya. Uba baifi uba ba, uwa bata fi uwa ba. Yadda Ururu suka kashemin uba da uwa akan idanuna haka zan halakasu dukkaninsu. Idan ka shirya bina to ka sani cewa ɗaukar fansar iyayena ita ce a gaba da komai. Nagode."
Ikenga ya juya ya fice.
Idan akwai abu ɗaya da Ikenga ya burge mutanen wannan taro a wannan rana dashi, shi ne gaskiyar daya gaya musu. Duk da kuwa yasan da dama daga cikinsu zasu ƙi binsa saboda ita. Amma bai ɓoye ba.
***
Kwanaki bakwai Ikenga da hadiminsa Ƙána sukai suna tafiya kafin su isa inda zasu. A har kullum hirarsu bata wuce yadda zasu ƙara ƙarfin izza da kuma yadda zasu haɗa runduna mafi ƙarfi a duniya.
Bayan sun tsaya suna hutawa sai Ikenga ya dubi manyan bishiyun dake kewaye dasu ya ce, "muna haura wannan bishiyu zamu tararda dajin ramikan ƙarƙashin ƙasa. Tunda duk wanda zai shiga saiya nuna shedar dutsen-izza kaga akwai matsala, domin kuwa bamu dashi."
Kána ya fashe da dariya yana girgiza kai. "To ai shugaba Ikenga koda muna da dutsen-izza bazai yi mana amfani ba. Tunda ire-iren wannan duwatsu suna kai mutun ne izuwa garin Shadeniza na daular denizawa, mu kuma ba nan muka dosa ba."
Ikenga ya ƙifta ido cikin murmushi ya ce, "ahh.. haka ne fa. Mu ƙarasa na nuna maka sabuwar fasaha ta wadda na sawa suna RAWAR ALJANU!"
Suna wannan magana suka rufe fuskokinsu da rawani sannan suka nausa cikin bishiyun suka nufi wannan sihirtaccen daji mai ɗauke da ramikan ƙarƙashin ƙasa wanda Armad yayi amfani dasu a shekarun baƴa ya isa gasar Jinzidal. Suna shiga sukai arba da sadaukai sahu-sahu suna kewaye da ramikan suna gadi. Akwai wasu mutane masu ɗauke da shedar dutsen-izza wanda suke bin layin shiga garuruwan na ƙarƙashin ƙasa amma mafi yawan mutanen dake wajen sadaukai ne ɗauke da makamai suna gadi.
Ikenga da Kána suka kewaya ta baya suna tafiya a hankali kamar basu ga kowa a wajen ba. Su kuwa ma'aikatan sai suka zuba musu ido suga gudun ruwansu.
A hankali Ikenga da Nara suka ci gaba da tafiya suna hira har saida suka zagaya can gefe inda babu mutane da yawa. A wannan lokaci ne ɗaya daga cikin ma'aikatan ya daka musu tsawa. "KAI.. Ku shiga taitayinku. Kuna tunanin nan wajen wasa ne!"
Amma ina, Ikenga da Nára hirarsu kawai suke kamar basu ga mai maganar ba. Hasalima ƙara kusantar ɗaya daga cikin ramikan sukai.
Koda ganin haka sai ma'aikacin ya fusata ya harbowa su Ikenga kibiyar dake hannunsa da niyya ya tsayar dasu. Amma wani babban abin mamaki wanda ya rikita dukkan al'ummar dake wajen shi ne da Ikenga da Nara babu wanda yayi ƙoƙarin kaucewa wannan kibiya. Hasalima bari kawai sukai tazo ta caki gefen kafaɗar Ikenga. Amma bisa mamaki wannan kibiya saita shige ta cikin kafaɗar sannan ta wuce fit ta jikinsa ta kuma shige jikin Nara shima ta wuce. Babu wani sauti dazai nuna an fasa fata ko tsoka ko ƙashi. Hasalima babi jini babu wata alama dazai nuna an harbi su Ikenga.
Kamar abin al'ajabin bai isa haka ba, kawai sai surar Ikenga da Kana ta fara yin hatsa-hatsa kafin daga bisani ta ɓace ɓat kamar an ɗauke wuta.
Koda ganin haka sai duk ma'aikatan dake wajen suka rankayo da gudu. Da dama daga cikinsu suka fara tunanin ko mafarki suke ko kuma gizo Ikenga yake musu.
Nan take suka fara dube-dube amma bayan awa ɗaya ana haka babu komai. Babu Ikenga babu labarinsa. A wannan lokaci shugaban masu gadin ya ce kowa yayi shiru da maganar har sai sun tabbatar da mai yake faruwa.
**
A can cikin rami mai lamba ta 1577 dake can tsakiyar wannan ramika Ikenga ne da Kana suka bayyana. Ko a jikinsu, kamar ma ba su ake ta nema a waje ba. Sun tala ƙafafunsu sun tokare da gefen bangon ramin yadda baza su faɗa ba.
Kana ne ya fara cire rawaninsa yai cilli dashi ƙasa sannan ya dubi Ikenga cikin jinjina ya ce, "wato da wannan sabuwar fasaha taka mai suna Rawar-Aljanu kana iya tafiya cikin tsananin sauri ta hanyar sarrafa lokaci da taurari. Saboda tsananin saurin da kake amfani dashi har tsahon daƙiƙu biyar bayan kabar waje baza a daina ganin hotonka kaba daga inda ka bari. A saboda haka mutane zasu yita kai hari suna zaton kana wajen amma a zahiri ka daɗe da bari. Lallai wani aikin sai ma'aboci taurari!!"
***
Babi na 110: Yura-shìra
Ikenga da hadiminsa Nara suka hau aljanunsu suka fara faɗawa cikin wannan rami da ƙarfin gaske. Baka ganin komai sai duhu. Jikin bangon ramin kuwa a sumulmule yake da wata irin ƙasa mai danƙo launin ja.
Bayan tsahon lokaci sai iskar wajen ta fara zafi, kan kace meye wannan sun gumi ya fara zarya a fuskokinsu. Amma ko kaɗan wannan bai tsayar dasu ba. Hasalima aljanun ƙara azama kawai sukai suka ci gaba da dannawa izuwa cikin wannan rami.
A kwana a tashi saida sukai kwana uku cir suna dannawa cikin ramin sannan suka fara hango haske. Duk bayan ɗan lokaci wajen saiya ƙara zafi amma a matsayin izzar su wannan ba abu bane dazai dame su ba.
A ƙarshen rana ta uku suka iso ƙarshen wannan rami. Suna bayyana wani haske mai tsananin zafi ya dalle musu ido. Nan take suka gane cewa duk zafin da suke ji a cikin rami kafin su ƙaraso nafila ne kawai. Lallai ba daban cikakkun ma'abota izza bane da tuni jikinsu ya narke.
Ikenga yayi murmushi tare da umartar aljaninsa daya sakko ƙasa, domin a lokacin suna gabda sararin samaniya a kusa da mabuɗar rana. Kana kuwa yana sauka ya dubi gabas izuwa mabuɗar ranar baki a buɗe.
"Shugaba Ikenga, wato idan mutun baiyi amfani da dutsen-izza da zai kaishi daular denizawa ba ya shiga wannan ramika to anan wajen kusa da rana zai tsinci kansa?"
Ikenga ya girgiza kai yayi murmushi mai cike da izza. "Hakane. Kuma kaga tunda denizawa a matsayinsu na daula ɗaya tak da suke rayuwa a ƙarƙashin ƙasa su kaɗai suka mallaki wannan dutsen-izzar da ake amfani dashi wajen zuwa garinsu na Shadeniza. Duk wanda ya shiga wannan ramika ba tare da dashi ba to a wannan waje zai tsinci kansa."
Kana ya gyaɗa kai ya amsa da cewa, "kaga duk wanda bashi da babban aljanin da zai fito dashi daga cikin ramin tun a farko zai mutu. Banda wannan hamshaƙin zafin ranar dazai iya narka mutun. To amma yanzu gamu tsaye a sararin samaniya, ina zamuyi daga nan?"
Ikenga ya zaro wata tagarda mai ɗauke da taswirar wannan waje sannan ya fara duba hanyar daya kamata subi.
Tsahon lokaci suna iyo a sararin samaniya akan iska kafin su fara hango doron ƙasa. Bayan sun sakko sai suka sallami aljanun nasu sannan suka ci gaba da tafiya a ƙasa.
Ƙasar wajen kamar kowacce ƙasa ce sai dai amma launin ta fari ne. Wata ƙila saboda rashin taka ta da ba'a yi domin kuwa kallo ɗaya zaka san babu wani abu mai rai a wannan waje face bishiyu da kurum. Duk da yake a cikin bishiyun baza a rasa namun dawa ba amma dukkaninsu sun tsorata da yanayin izzar dake tashi daga jikin Ikenga.
Sai da sukai kwana ashirin suna tafiya basu tararda kowa ba sannan suna iso wani waje mai yawan duwatsu. Ikenga ya kalli taswirar dake hannunsa sannan ya ƙara kallon wajen. "Munzo, Kana. Lallai nanne wajen."
Wani murmushi ne yazo fuskar Kana domin a ransa tuni ya fara shiga damuwa. Babu yadda baiyi ba kada Ikenga ya taho wannan aiki saboda hatsarinsa amma Ikenga yaƙi. A cewar Kana Ikenga mutun ne wanda yake da matuƙar muhimmancin da baza a iya yi bashi ba. Kuma irin wannan aiyuka masu wahala kamata yayi a barwa wasu. Amma ina, Ikenga yaƙi.
Ikenga ya dubu gindin wata bishiya ya ce, "Mu zauna a nan mu jira." Kana ya gyaɗa kai ya nemi waje ya zauna tunda daman tuni yasan wajen su wa akazo.
Bayan sun zauna Kana ya futo da gora cike da ruwa ya miƙawa Ikenga. Bayan yasha ya dawo masa da ita. Sannan suka fara tattaunawa akan abinda yasa suka yiwo wannan tattaki izuwa wannan waje da babu kowanne mahaluƙi saisu.
Ikenga ne ya fara da cewa, "da sannu zan haɗa runduna wadda dukkan duniya zasu iya tsorata da ita. To amma wannan aiki namu babba ne kuma yana buƙatar sadaukarwa da lokaci."
Kana ya girgiza kai domin a duk faɗin duniya za'a iya cewa shi kaɗai ne ya fuskanci haƙiƙanin shirin Ikenga. Haka su biyu suka ci gaba da hira zuwa mintuna goma masu zuwa kafin daga bisani wani dattijo ya fito daga cikin dajin dake kewaye dasu ya nufo inda suke.
Suna ganinsa suka miƙe suna murmushi. Kana gani kasan sun san juna yadda ya kamata. Mutumin na isowa yayi musu murmushi sannan ya fara bayani da cewa, "a matsayina na ma'ajin shugaba Amraikugyu Bayajidda ina umartarka daka nuna min shedar cewa kai jikan Amraikugyu Bayajidda ne domin na gani ko ka cancanta nayi magana dakai."
Ikenga najin haka yayi murmushi sannan yasa takobinsa ya yanki tafin hannunsa na dama jini ya fito. Wannan ma'aji ya tako ya ƙaraso waken ya fara ɗisa jinin akan wata takarda mai ɗauke da hatimai. Jinin yana taɓa takardar ta fara haske kamar rana. Sannan daga bisani hasken ya ɗauke yabar wani zanen mutun-mutumi.
Abin al'ajabi sai mutun-mutumi ya fara tafiya taku ɗai-ɗai har saida yayi taku bakwai. Sannan daga bisani ya ɗauke. Nan take wannan mutun ya zube a ƙas yana mubaya'a ga Ikenga.
Dattijon baƙi ne ruwan tarwaɗa mai sanƙo. Fuskarsa nada tsayi da faɗi, sannan idanunsa na nuna jarumta da tsananin daɗewa a duniya. Ya fata bayani da cewa, "suna na Daidar Bayajidda. Kuma kamar yadda na faɗa ni ne ma'ajin kakanka wanda ya mulki dukkan daulolin ƙasa wato sarki Amraikugyu Bayajidda. A matsayinka na jinin sarki Bayajidda dole kasan tarihin sarki Amraikugyu Bayajidda, da kuma tsakaninsa da Ururu da Wilbafos. Ka kuma san yabar wasu sirrikan izza guda huɗu ga magadansa. Abu na farko TAKOBIN BAYAJIDDA wadda ake kira da YURA-SHÎRA. Na biyu hatimin-sirrin duniyar ƙarƙashin ƙasa. Na uku kuma littafin-ɗalasimai dake koyarda yadda za'a sarrafa fasahar takun-sarki wadda aka fi sani da SHAIBAL-SHÍSU. Sannan na huɗu kuma abinda ake kira da HATIMIN-IZZA." Dattijon na zuwa nan ya fara hawaye. Kana gani kasan akwai takaici acikin ransa mai yawa.
Yana hawayen yaci gaba da bayani. "A matsayina na ma'aji ina baka haƙuri akan abinda ya faru wanda ya jawo Bihanzin ya sace TAKOBIN-BAYAJIDDA, sannan kuma daga baya ya haɗa kai da wannan yaro ɗan gidan Wilbafos ya sace Hatimin-izza. Bani da wani isasshen uzuri, kawai ka ɗauki raina na huta." Dattijon ya miƙo wuyansa yana jira Ikenga ya aiwatar masa da hukunci. Amma Ikenga kawai murmushi yayi ya girgiza kai ya ce, "ai kowa yakanyi kuskure. Kuma abinda ya faru kaga ai ya nuna mana waye Bihanzin, wanda a yanzu duk duniya babu wanda ƴasan haƙiƙanin waye Bihanzin banda mu, hatta Ururu basu sani ba. Da dama kawai sun sanshi da Bihanzin Sisiyu amma basu san asalin sunan ƙabilarsa ba. Wanda muma bada ban abinda ya faru ba da baza mu sani ba."
Dattijon najin haka yayi murmushi. A zuciyarsa yana tuna sarki Amraikugyu da irin ƙarfin mulkinsa domin kuwa irin ƙarfin ruhin da yake ji kenan idan ya kalli Ikenga.
Bayan ɗan lokaci dattijon ya ci gaba da cewa, "abu na uku wato bayanin ɗalasimai akan yadda za'a sarrafa takun-sarki shima kamar yadda ka sani Ururu sun saci wani abu daga ciki amma mu kaɗai muke dashi gaba ɗaya. Abu na ƙarshe wato Hatimin-sirri akan duniyar ƙarƙashin ƙasa shi kaɗai ne wanda ba'a taɓa satarsa ba."
Yana zuwa nan a zancensa ya miƙe ya zaro wata doguwar takarda mai ɗauke da hatimi da kuma wani ɗan ƙaramin littafi da baifi girman tafin hannu ba ya miƙawa Ikenga. Ikenga ya karɓa ya dudduba sannan ya buɗe ƙofar zoben dake hannunsa ya zura su ya rufe.
Ikenga yayi wa wannan dattijo jinjina. "An gaida kai daka ajiye wannan sirrika tsahon wannan ɗaruruwan shekaru. Daga yau na ƴanta ka, kana da damar kayi duk abinda kake so."
Ikenga da Kana suka juya zasu tafi amma Daidar Bayajidda ya ƙara zubewa a ƙas yana cewa, "indai zaka karɓeni zan ci gaba da yi maka hidima har iya tsahon rayuwata kamar yadda nayi wa kakanka alƙawari."
Ikenga ya waiwayo cikin farin ciki da murna. Yasan sarai ƙarfin iko da buwayar izza ta wannan dattijo mai suna Daidar. Yana ɗaya daga cikin kaɗan da suka ga jiya suka ga yau. Waɗanda suka san tarihin ƙasa bakwai.
Ikenga ya buɗe baki ya ce, "Ina maka barka da zuwa sabuwar rundunar Bayajidda."
***
Abin mamaki kwanaki bakwai bayan faruwar wannan abu Ikenga da Kana da Daidar suka bayyana a daular Sisiya ta sarki Bihanzin. Suna zuwa suka nemi waje a bayan gari cikin wani kogo suka zauna.
Komai ya kawo su wannan daula??
***
Babi na 111: Ikenga da Bihanzin
Wayewar gari keda wuya Ikenga da Kana da Daidar suka futo bakin wannan kogo suka tsaya. Kallo ɗaya kacal zakai musu kasan cewa ba'a son ransu suka zo wannan daula ba, kuma idan da da yadda zasu yi da tuni sunyi nasu waje.
Daidar Bayajidda ya dubi Ikenga ya ce, "ya shugaba na meye zai hana mu turawa jaridar aminiya labari akan waye Bihanzin? Na tabbatar basu kaɗai ba, duk wata jarida dake doron ƙasa zata sayi wannan labari akan miliyoyin kuɗi."
Ikenga najin haka yayi murmushi a nutse ya amsa da cewa, "kada ka damu, sama da shekara ɗaya mun gama shirya komai akan yadda zamu ɓullowa Bihanzin idan yaƙi amincewa da abinda muka zo masa dashi."
Daidar ya gyaɗa kai tare da komawa baya ya tsaya. Bayan kimanin sa'a ɗaya sai wani haske ya fara bayyana akan wani dutse dake gabansu. Ba jimawa wannan haske ya juye izuwa siffar kwamanda Damjinu Djinn. Abin mamaki, ko kaɗan babu wanda ya motsa a cikinsu, kana gani kasan sun san da zuwansa.
Damjinu fuskarsa cike take da murmushi, amma kana gani kasan bai kai zuci ba. Ikenga kaɗai yake kallo kamar su Kana basa wajen ko kuma basu isa yayi musu magana ba. Ya dubi Ikenga ya ce, "Sarki Bihanzin yana jiranka."
Yana faɗar haka ya tafa hannunsa tare da kiran wasu ɗalasimai a zuci lamarinda yasa ƴar-ƙaramar ƙofar Eycigan ta bayyana a gabansa. Inda yayiwa Ikenga inkiya da ido daya shiga.
Kai tsaye Ikenga ya taho ya shige cikin ƙofar. Kána da Daidar suna biye dashi, amma koda suka zo shiga sai Damjinu ya shiga gabansu ya tsayar dasu. "sarki Bihanzin Ikenga kaɗai ya ce a kawo."
Nan take Daidar yakai hannunsa kan takobinsa a fusace amma Kana ya hanashi. Haka suka haƙura suna gani Damjinu ya shige ƙofar, sannan ƙofar ta fara yin duhu kafin daga bisani ta rufe.
Ikenga na bayyana ya waiga bayansa yaga su Kana basu taho ba, nan take ya gane mai ke faruwa. Amma ko a jikinsa. Yana ganin Damjinu ya bayyana amma ko gezau baiyi ba.
Ya duba gefensa ya ganshi acikin wani fili mai cike da rairayi, wanda da Armad yana nan zai gane a wannan waje mahaifiyarsa ta karɓi izza. Babu komai a wajen sai wata ƙatuwar karaga wadda Bihanzin ke kai ɗauke da hankakan mutuwa a kafaɗarsa.
Bihanzin na ganin Ikenga ya bayyana yayi wani ɗan ƙaramin murmushi ya ce, "sai yanzu daka fara girma naga kuna kama da kakanka Amraikugyu. Lokaci na karshe dana ganshi ya tsufa sosai amma duk da haka yana nan da irin idonku na gidan Bayajidda."
Ikenga yayi murmushi mai kama da yaƙe, zuciyarsa na dukan uku-uku badan komai ba saboda yasan mutumin dake gabansa. "Ni Ikenga nayi murna daka yabe ni, amma kayi sani bani da lokacin tsayawa anan muyi hira. Abinda ya kawo ni shi ne takobin kakana Yura-shìra dake wajenka. Kamar yadda muka amince akai na bar maka Hatimin-izzar daka ɗauka kasa aka fasara maka, amma zaka dawo min da wannan takobi. Idan har ka yadda ka dawo min da ita ni kuma a matsayin godiya zan baka Ɗalasiman sirrin duniyar ƙarƙashin ƙasa na kakana Amraikugyu.
"Amma idan kaƙi amincewa ko kuma wani abu ya same ni anan ban koma wajen mutane na ba nan da minti goma, to nan bada daɗewa ba zaka ji sanarwa a dukkanin jaridun ƙasa bakwai akan asalinka. Domin tuni mutane na sun isa shalkwatar kowacce jarida daka sani, lokaci kawai suke jira su miƙa labarinka ga idon duniya."
Bihanzin najin wannan labari ya ɓata rai, nan take wajen yayi duhu tamkar an buɗe idanuwan Ururu. Hankakan mutuwar dake kafaɗar Bihanzin ya fara ƙara mai ratsa ƙashi kai kace ƙahon mutuwa ake busawa. Nan take Ikenga ya fara gumi yana jada baya, zuciyarsa na bugawa.
Ana cikin haka sai kawai Ikenga yaji Bihanzin ya fashe da dariya. Nan take wajen yayi haske, shima hankakan-mutuwar ya fara dariya yana kaɗa jela. Kai kace ba shi bane ɗazu.
Ikenga na ganin haka yayi ajiyar zuciya ya haɗe gira. Da ace duniya sun san waye Bihanzin, kuma suka ji Ikenga yazo fadarsa shi kaɗai da sunce mahaukaci ne. Amma kash, babu wanda ya san wannan sirri sai shi kaɗai.
Bihanzin ya dubi Damjinu ya ce, "Kawo takobin."
Yana rufe baki Damjinu ya ɓace, cikin ƴan daƙiƙu kaɗan ya ƙara bayyana. A hannunsa yana ɗauke da duguwar takobi tsirara. Jikinta baƙi-ƙirin amma ƙotar ta jace ruwan jini. A tsaye wannan takobi takai tsayin Ikenga duk kuwa da cewa ba ƙaramin dogo bane shima. Amma faɗinta baifi rabin tafi ba.
Bayan Damjinu ya shigo ya tsaya sai Bihanzin ya umarce shi daya miƙawa Ikenga takobin.
Ikenga ya miƙa hannu ya karɓa. Yana taɓa takobin, ƙarfen ta ya fara haske. Yana bada baƙin walwali mai kama da baƙin hayaƙi. Ikenga ya juya ta ya ƙara juyata. Bashi da buƙatar a gaya masa ita ce koba ita bace domin acikin jininsa yake jinta. Tamkar ta zama ɓarin jikinsa.
Bayan ya gama gani ya ɗaurata a bayansa. Sannan ya buɗe zobensa ya cilla tsohuwar takobinsa ciki. Idan ka kalli Ikenga zaka ga kamar ya zama wani sabon mutun: fuskarsa da kafaɗunsa sun ƙara cika. Idanunsa na nuna alamun cika da izza.
Ikenga na cikin haka yaji maganar Bihanzin a kunnensa. "Na cika ɓangare na, saura kai."
Ikenga ya ɗanyi shiru yana tunani kafin daga bisani ya ƙara buɗe ƙofar zoben ya ɗakko takardar mai ɗauke da ɗalasiman duniyar ƙanƙashin ƙasa ya bawa Damjinu shi kuma ya miƙawa Bihanzin.
Haka na faruwa Ikenga ya juya zai fice, harya kusa bakin ƙofa yaji muryar Bihanzin yana cewa, "sunan wannan ɗalasimai na duniyar ƙarƙashin ƙasa ƘURU!! Nan bada daɗewa ba zaka san dalilin da yasa na baka takobin data fi kowacce ƙarfi a duniya domin na karɓi ɗalasiman ƘURU."
Cije baki kawai Ikenga yayi ya fice daga fadar baice komai ba
***
Kána da Daidar suna tsaye suna ta jimami suna jiran Ikenga suka hangoshi ya doso inda suke a hankali. Nan take suka rankaya izuwa gareshi suna dudduba jikinsa. Abadda ta fara yi musu sallama ita ce doguwar takobin Yura-shìra wadda ke ɗaure a bayan Ikenga. Jar ƙotarta na walƙiya acikin hasken rana.
Ikenga baice komai ya dube su ya ce, "Kafin muje TSIBIRIN SIDO-URURU mu fara zuwa daular Maikironomada ina so na shiga nayi amfani da Non-toch-teka."
Suna jin haka suka zare ido cikin mamaki amma ganin halinda Ikenga ke cikin basu ce komai ba suka rankaya izuwa daular Maikironomada.
***
A can doron ƙasa na bakwai kuwa, sashin arewa, Armad ne ke zaune cikin kwale-kwale tare da Inara da Iliyasis da Cokali akan wani kogi dake kewaye da garin da zasu shiga. Sunan wannan gari DUKA.
Tuni dai suka shige garuruwa uku a ƙoƙarinsu na zuwa wannan gari inda shalkwatar ajiye bayane-bayane ta Ururu take. Tun daga cikin kwale-kwale suke hango matakan tsaro sanye da baƙaƙen kaya a gindin ƙofar garin. Kamar ana yaƙi.
Amma bisa mamakin wannan bai hana Inara yin rubutu akan wata farar takarda ba. Bayan ya gama rubutun ya karanta abinda ya rubuta sau kamar uku sannan ya ɗago kai ya dubi Armad ya ce, "bari kaji, da fatan banyi kuskure ba. Mahaifinka sunan sa Taidara Wilbafos, kakanka na wajen uba sunansa Zaikid Wilbafos. Mahaifiyarka sunanta Fatima Wilbafos, amma kafin mahaifinka ya aureta sunan ta Fatima Bayajidda wato dai ta fito daga gidan Bayajidda. Kana da yaya, uwa ɗaya uba ɗaya, mai suna Hidaya Wilbafos."
Armad ya gyaɗa kai yana cewa, "eh.. haka ne. Dai dai ka rubuta." Kana gani yadda Armad yake cije baki kasan ya gaji da tambayoyin da Inara yake masa akan gidansu.
Koda Iliyasis yaga haka sai ya dubi Armad ya ce, "kayi haƙuri a daular Maikironomada duk wani ɗalibi dole ne yasan dukkanin iyalan gidan malaminsa da shekarunsu. Kaga yanzu saura shekarunsu zaga gaya masa."
Armad najin haka ya haɗe gira kamar yasa kuka. Amma kafin ya ce wani abu Iliyasis ya ƙara da cewa, "kaga a ƙa'ida jinin mahaifiya na ƙabila bashi da ƙarfi sosai amma kai naka naga yana da ƙarfi matuƙa. Kamar yadda ka gaya mana a gasar Jinzidal kaga ruhin Bayajidda yana ganawa da Ikenga a lokacinda babu wanda yake iya ganinsa a wajen, ina ganin jininka ta ɓangaren mahaifiya na Bayajidda ne yake aiki."
Armad najin haka ya gyaɗa kai, domin kuwa tun a lokacin yayi tunanin haka. Tunda babu wata hanya da zai iya samun jinin Bayajidda inba daga nan ba.
Amma tun kafin Armad ya ce wani abu Inara ya durƙusa ya tambayeshi shekarun Hidaya dana mahaifiyarsa dana babansa da kakansa. Kana ganin fuskar Armad kasan gab yake daya nutse saboda takaicin wannan al'ada dabai santa ba kwata-kwata.
***
Babi na 112: Shiri
Bayan ya rage kimanin tafiyar sa'a ɗaya tsakaninsu da garin Dúka sai Armad ya nemi a tsayarda kwale-kwale.
Tuntuni dai sun riga sun tsara hanyarda da zasu shiga wannan gari, to amma har kullum ƙara bi takan shirye-shirye yana da muhimmanci acikin tsarikan Armad.
Armad ya fara bayani da cewa, "wannan gari na Dùka yana ɗaya daga cikin garuruwa uku wanda suka fi kowanne yawan mayaƙan Ururu a ƙasashen-ƙasa. Kuma acikinsa ne Ururu suke ajiye sirrika da bayanai da suka shafi ƙasashen-ƙasa. Abinda ya kawo mu shi ne mu samu sirrin bayanai na mutanen da suka shiga sashin Ikwatora a shekarar data gabata domin muga ko sunan Nusi yana ciki. Saboda haka mun raba kanmu izuwa gida biyu; gida na farko zasu yi bincike ta ƙarƙashin a sirrance, gida na biyu kuma zasu ɗauke hankalin mayaƙan dake cikin garin ta hanyar tayarda tarzoma a tsakiyar garin.
"To amma duk wannan tsarin namu dole sai mun ga haƙiƙanin tsarin yadda garin yake da kuma yawan mayaƙan da suke ciki da kuma inda ake ajiye bayanan. Saboda haka dole sai mun shiga a sirrance, idan ba haka ba kuwa kafin mu shiga zasu iya ɓoye bayanan da muke nema. Sannan kuma idan suka san muna tafe zasu zamo cikin shiri." Bayan ya gama bayani ya dubi Iliyasis ya ce, "Iliyasis, ƙara mana haske akan mayaƙan Ururu dake ƙasashen-ƙasa domin musan abinda muke tunkara."
Iliyasis yayi gyaran murya sannan ya fara da cewa, "mayaƙan-Ururu sun kasu izuwa gida biyar. Kowanne kaso yana ƙarƙashin ikon Kwamandan Ururu guda ɗaya. Kuma kowanne kwamanda yana da kyaftin biyar a ƙarƙashinsa. Kwamanda na farko shi ne Dul'Ururu, sarki bisa doron ƙasa ta biyu, kuma shi ne shugaban wannan kwamandoji biyar. Kwamanda na biyu shi ne Uznu Ururu, wanda shi ke mulkin wannan gari na Dùka. Kwamanda na uku shi ne wanda ake kira da Ra'adú Ururu wanda shi ne ke mulkin shalkwatar Ururu dake doron ƙasa ta biyar sashin arewa. Sauran kwamandojin biyu har yanzu babu wanda yasan sunansu, amma dai ɗaya ana ce masa BAƘIN-JINI ɗaya kuma FARIN-ZAKI. Kuma su biyun duk suna mulki a wasu garuruwa dake doron ƙasa ta biyu.
"Da dama daga cikin masu nazari suna ganin ƙarfin waɗannan kwamandoji guda biyar da garuruwansu dai-dai yake da ƙarfin sarakunan Jinzidal biyar. Koma dai yaya ne suna da ƙarfin da hatta sarakunan Jinzidal basu isa su juyawa Ururu baya ba.
"A sau da dama mutane suna ganin ƙarfin waɗannan kwamandoji biyar shi ne dalilin da yasa sarakunan Jinzidal biyar basu taɓa tunanin afkawa doron ƙasa ta farko ba. Ko kuma su ce suma sai sun koma rayuwa a bisa doron ƙasa na farko. Sannan kuma kowa yasan bawai Jinzidal kaɗai waɗannan kwamandu biyar suke karewa ba, suna taka rawa wajen ragewa da daidaita ƙarfin sarakunan Jinzidal. Domin kuwa da babu su da tuni sarakunan Jinzidal sun mallake dukkan ƙasashe shida daga doron ƙasa na biyu zuwa na bakwai.
"Akwai kyaftin guda biyar wanda kowanne yana da izza sama da shekaru dubu ɗaya dake cikin wannan gari wanda duk suna ƙarkashin Uznu Ururu ne. Lallai indai har suka riga suka san abinda ya kawo mu to zaiyi wuya mu samu abinda muka zo nema. Saboda haka shiga cikin garin a salin-alin yana da muhimmanci. Kafin su farga munyi musu illa.
"Saboda yanayin sirrika da bayanai da ake ajiyewa a wannan gari duk wani mai shiga da fita an sanshi. Hasalima saƙo da loko na cikin garin duk ma'aikata ne. Kuma indai zaka shiga ta ƙofa saika nuna katin shaidar ɗan ƙasa. Saboda haka bamu da damar shiga ta ƙofa a haɗe. Kuma haura katanga bazai yiwuba tunda akwai Tsari na ɗalasimai a jikin katangar.
"Akwai matafiya dake shige da fice, munyi sa'a yau ranar kasuwa. Saboda haka mutun ɗaya daga cikin mu zai iya yin amfani da wannan hanya ya bada cin hanci a shiga dashi.
"Armad bashi da matsala, zai iya amfani da ɗalasiminsa na Kaban'shìsu ya shige. Nima ina da fasaha ta da zanbi ta sama da ita na shige. Saboda haka saura mutun ɗaya acikinmu. Zoben Armad baya ɗaukar mutun indai ba'a sume yake ba, saboda haka dole abi ta wata hanyar."
Nan take Inára yai caraf ya amshe da cewa, "ina da hanyar dazan shiga. Har yanzu ina da shaidata ta tuƙin jirgi. Kawai nunawa zanyi nace nazo neman aiki."
Nan take suka amince. Cokali shi zai saje da ƴan kasuwa, Iliyasis da Armad suna da fasaharsu, shi kuma Inara yana da shedar tuƙin jirgi.
Armad ya numfasa ya ce, "kada ku manta, idan kun ƙaraso ga wannan ayrid ɗin, zan turo muku saƙon dazai nuna muku dai-dai inda nake. Idan kuma wani ya samu matsala acikinku shima ya turomin saƙo zanzo da kaina."
Kowa ya gyaɗa kai acikinsu sannan kowa ya fara azama.
Iliyasis shi ne na farko, bayan ya karanta wasu ɗalasimai kawai sai dukkan siffar jikinsa ta rikiɗe izuwa ta ƙaton shaho, fari. Nan take yayi kuka sau uku irin ma shaho sannan ya tashi sama ya nufi sararin samaniya. Abin yayi matuƙar bawa Armad da Inara mamaki amma daman Cokali yasan da wannan fasaha ta Iliyasis. Kansu na sama suna kallon ikon ALLAH, mutun ya koma tsuntsu. Tun suna hango shi har saida ya ƙule.
Armad ya dube ya ce, "saiku ƙarasa a kwale-kwalen. Muna ciki muna jiranku." Yana rufe baki ya kira Kaban'shìsu ya ɓace.
Saura Cokali da Inara.
Cokali ya dubi Inara cikin tsokana ya ce, "Kasan ban iya ruwa ba, saboda haka ni zan ƙarasa a kwale-kwalen."
Inara ya fashe da dariya yana cewa, "ai daman faɗawa ruwan yana cikin lissafi na." Yana rufe baki ya afka ruwan ya fara iyo izuwa bakin wannan gari. Abin ka da wanda ya gaji sana'ar tuƙi.
***
Babi na 113: Ƙabilar Yeren
Ƙofar garin Dùka cike take da mutane a layi suna nuna katin shedarsu suna shiga. Garin gaba ɗaya akan wani tsiburi yake wanda daga zaka ga yayi sama sosai amma idan ka matso kusa zaka ga baikai haka ba. Daga cikin mutanen dake layin shiga garin akwai wani ɗan kasuwa tafe da amalanke cike da kayan gwari.
Daga can nesa kuma Inara ne sanye da ƙatuwar hular fulani yana riƙe da ƙatuwar jakar bakko.
Layi yana isowa kansa ya zaro wani farin kati mai ɗauke da hotonsa da rubuce-rubuce ya miƙa. "Ni matafiyi ne kuma ɗan kasuwa. Nazo ne daga daular Sisiya."
Ɗan-dokar dake gadin ya ƙurawa Inara ido yana nazarinsa sama da ƙasa. Abun mamaki wannan Ɗan-doka wani irin wuya ne dashi mai ban al'ajabi kamar sauran masu tsaron ƙofar.
Wuyan nasu dai yakai tsahon kamu biyar zuwa shida. Sannan ya laƙwaso gaba kamar mariƙin lema. Daga ɓangaren hagu a jikin wuyan akwai wasu ƙullutai dogaye guda biyu da suka bulluƙo waje.
Nan take Inara ya tuno da wani fasinja da suka taɓa ɗauka. Bayan dogon tunani ya tuno abinda wannan fasinjan ya gaya musu a game da ƙabilarsa. Ita dai wannan ƙabila gaba ɗaya rayuwarsu a doron ƙasa na bakwai suke yinta. Ana kiransu da YEREN. Basa shiga cikin mutane sosai saboda ƙabilanci da mutane ke nuna musu shi yasa indai ba doron ƙasa ta bakwai kazo ba da wuya ka gansu.
Abu guda da kowa ya sani akansu shi ne basa son kallo. Saboda haka nan take Inara ya ɗauke idonsa daga wuyan wannan mutun.
Bayan ɗan lokaci mutumin ya buga sitamfi akan katin Inara sannan ya ɗauki hoto da suna da duk wasu bayanai dake jikin katin ya saka a takarda kafin ya miƙowa Inara katin. "Zaka biya Ayirda ɗari biyu kuɗin haraji, sannan ka sani idan wani abu ya faru mun san inda zamu nemo ka."
Inara ya karɓa gami da gyaɗa kai yana godiya. Sannan ya shige. Bayan wani lokaci aka iso kan mai kayan gwarin. Ɗaya daga cikin ƴan-dokar ya zagayo kan amalanken yana duba kayan sama da ƙasa. Ɗaya kuma ya dubi mai amalanken daga gaba ya ce, "Urasa, ya kasuwa?"
Urasa ya girgiza kai, "kasuwa sai a hankali. Kasan tunda aka fara jita-jitar yaƙi tsakanin Bihanzin da sarakunan Jinzidal kasuwa taja baya. Jama'a sun ɓoye kaya."
Yana cikin bayani yaji muryar na bayan yana cewa, "anya kuwa... ka sauke mana komai mu gani kawai, yau naga kayan naka ya ƙara yawa."
Urasa najin haka ya zaro ayrid da dama a dunƙule a hannunsa ya danƙawa na gaban acikin sake. "Sauri nake, kuma kunsan kayan namu yadda suke. Yawan saukewa da mayarwa na sawa suyi ruwa su farfashe."
Ɗan-dokar ya dunƙule ayrid ɗin ya jefa a aljihu ba tare da na bayan sun gani ba. Sannan a lokaci guda yayi wa na gabansa inkiya suka buɗewa Urasa ƙofa.
Bayan ya shige yayi nisa acikin garin saiya nemi wani loko ya tsaya. Ya waiwaiga babu kowa sannan ya ɗaga amalanken saiga ƙatoton mutun kwance a ƙarƙashi. Idan ka duba sosai zaka ga ba kowa bane illa Cokali.
Da kyar Cokali ya kama ya daddagara ya fito saboda ƙiba, sannan ya zaro ayird ɗari biyar a aljihunsa ya miƙawa Urasa. "Na cika alƙwari. Godiya dubu."
Nan take Cokali ya miƙe. Yana shan kwana ya zaro irin ayrid ɗin da Armad ya bashi ya binne. Ba jimawa filawar-saƙo ta fito ɗauke da takarda dake bayanan wajen da su Armad suke.
A ɗan wani waje nesa kaɗan da inda Cokali yake, Inara ne shima ɗauke da takardar dake bayanin wajen da Armad yake. Saboda haka nan take suka nufi wajen.
Bayan kimanin tafiyar sa'a guda suka iso cikin wata kasuwa. Cokali ne ya fara hango Inara inda suka haɗu suka ci gaba da neman wajen da Arnad yayi musu kwatance.
Gine-ginen garin Dùka basu da girma sosai amma suna da tsari matuƙa. Domin kowanne layi a jere yake a tsare. Babu datti ko hayaniya da yawa. Hatta kasuwar da suke ciki a tsare take da shaguna akan benaye a tsakiyar kasuwar. Sannan hanyoyi sun kewaye shagunan.
Abu na farko da zaka fara tunani shi ne lallai ma'abota aljanun ƙasa sunyi aiki a wannan garin.
Ba tare da tambaya da yawa ba suka tsinci kansu a bakin wajen cin abincin da Armad ya kwatanta musu. Mafi yawan mutanen wannan gari irin wannan dogon wuya ne dasu. Sai dai wasu nada ƙullutai biyu wasu uku ko sama da haka. Wanda basu dashi yawanci baƙi ne ko kuma ƴan kasuwa. Duk bayan ƴan daƙiƙu sai Inara ya tunawa Cokali cewa basa son kallo amma duk da haka Cokali saiya ƙara mantawa.
Suna shiga suka tarar da mutane zazzaune kan kujera a cikin wajen. Armad da Iliyasis na zaune daga can gefe ɓangaren kudu.
Cikin sauri suka ƙarasa. Kafin kowa ya ce wani abu Cokali ya rufarwa abincin dake zube akan teburin. Yana ci yana gayyatar Inara. "Inara, kaci in zaka ci. Wa yasan kwano nawa sukai kafin muzo."
Murmushi kawai Inara yayi domin baya jin yunwa ko kaɗan. Dama dai wannan abinci saboda Cokali aka siyoshi, ansan yana buƙata.
Ko'a jikin Cokali. Yana gamawa ya kora da lemo sannan bayan ya shirya ya buɗe baki zaiyi tambaya amma Iliyasis ya tsayar dashi. Tare da yi musu inkiyar akwai ƴan-leƙen asiri a wajen sabida haka kada suce komai sai sun fita.
Haka kuwa akai, suna tashi suka nufi ɗakin kwanan da suka kama domin bi takan shirye-shiryensu.
***
Bayan sun isa Armad ya fara jawabi a matsayinsa na mutun na farko daya fara zuwa acikinsu. "Mutanen wannan gari ƴan ƙabilar Yeren ne. Kuma daga ɗan binciken da nayi na gano suna da matuƙar biyayya ga ƙabilar Ururu. Hasalima zaka iya cewa akwai soyayya a tsakaninsu da girmamawa. Tarihi ya nuna cewa shekaru da dama da suka gabata al'ummar ƙasa bakwai suna ƙyami da kyarar wannan ƙabila, har saida Dul'Ururu, sarki bisa doron ƙasa ta biyu yazo ya hana. Kuma tun daga wannan rana suke ƙarƙashin kulawarsa. Hasalima shi yasa aka kawo wannan shalkwatar wannan gari wanda ya mallaka musu."
Armad ya numfasa tare da fito da taswirar dake aljihunsa ya buɗe ta akan teburin dake tsakiyar ɗakin. Duk su huɗun suka nutsu suna kallo. Armad ya nuna wani ƙaton gini dake tsakiyar garin ya ce, "wannan shi ne wajen da ake ajiye bayanan, amma akwai mayaƙan-ururu dubu biyar a kewaye da wajen. Akwai kyaftin guda biyar a kewaye dasu. Abinda har yanzu bamu sani ba shi ne ko Uznu Ururu shima yana cikin ginin. Sannan kuma matsala ta gaba kamar yadda na gaya muku mutanen wannan gari suna bawa Ururu kariya kamar yadda suke bawa kansu. Saboda haka ina saurare, menene shawarar ku?"
***
Babi na 114: Shirin Armad
Kowa acikin wannan ɗaki yayi jugum yana kallon wannan taswira ta garin Dúka da kuma ƙatoton ginin da zasu shiga domin ɗakko wannan bayanai.
Ana haka sai Iliyasis ya buɗe baki ya ce, "ni ku barmin alhakin shiga nemo bayanan, ku janye musu hankali. Saboda wannan gini yana da matuƙar tsayin gaske kuma bashi da wata ƙofar shiga sai guda ɗaya tak. Tunda ina da fasahar da zan iya rikiɗa izuwa tsuntsu, shiga baza tai min wahala ba. Sannan bayan na shiga akwai hanyoyi da zanyi amfani dasu na ɓoye kaina."
Bayan Iliyasis ya gama bayani, Armad ya dube shi ya ce, "kai kaɗai zaka iya?"
Iliyasis ya gyaɗa kai. "Indai har kun ɗauke musu hankali yadda ya kamata, ba matsala."
Armad ya dubi Inara da Cokali ya ce, "to kunga aikinmu ne tare mayaƙa dubu biyar. Acikinsu akwai kyaftin biyar wanda kowanne yana da izza aƙalla dubu ɗaya sannan kuma akwai yiwuwar Uznu Ururu yana nan. Zaku iya?"
Inara kawai sunkui da kai yayi ya ɗora hannunsa akan takobinsa. Shi kuwa Cokali bugar ƙirji yayi ya ce, "kada kuji wani abu ni kaɗai zan iya ji da sadaukai dubu biyar. Ai bawai kashe su muke buƙata muyi ba, janye musu hankali kawai zamu yi."
Armad najin haka ya jinjinawa Cokali cikin tsokana sannan ya dubi Inara ya ce, "kaima Inara izzarka bata kai matsayin ka kara da muƙamin kyaftin ba saboda haka kabi Cokali ku janye hankali. Ni zan janye hankalin kyaftin din."
Koda Inara yaji haka sai hankalinsa ya tashi, ya dubi Armad cikin hanzari ya ce, "ya shugaba na idan Uznu yana nan akwai matsala. Da Uznu da kyaftin biyar zasu iya tarar maka. Ina ganin kamata yayi duk mu cure a waje ɗaya yadda wani zai kare wani, kuma muyi musu kwarjini."
Yana rufe baki kafin Armad ya bada amsa Cokali ya buɗe baki ya ce, "eh.. gaskiya da wannan. Bawai ina raina ƙarfin izzarka ba amma Uznu shi ƙaɗai yakai matsayin sarakunan Jinzidal, tabbas shi kaɗai zai cika maka hannu. Ya za'ai da sauran kyaftin biyar ɗin. Nima kyaftin ɗaya ya ishe ni. Inara kuma bazai iya jada koda kyaftin ɗaya ba. Sannan kuma akwai yiwuwar mutanen wannan gari su shigar musu. Lallai indai Uznu yana wannan gari ya kamata mu canja shiri."
Koda Armad yaji haka saiya dubi Iliyasis domin yasan Iliyasis ba mutun bane da zaiyi saurin yanke hukunci ba. Iliyasis na ganin haka ya girgiza kai cikin nutsuwa ya ce, "gaskiya na yadda da abinda suka ce. Saboda haka ina ganin kafin muyi komai kamata yayi mu tabbatar ko Uznu yana nan ko baya nan."
Armad ya ɗanyi shiru kafin ya ɗago ya kallesu cikin nutsuwa. "Duk shawarwarinku sunyi to amma akwai abu guda ɗaya da kuke mantawa. Tuni munyi kwana uku da baro gida. Na kuma riga nayi wa Gimbiya Zahra alƙawarin komawa cikin kwana bakwai. Saboda haka dole komai zamu yi muyi shi cikin sauri. Sannan kuma daɗin daɗawa mutanen garin nan a ƙirge suke, kowa yasan kowa, duk sa'a ɗaya da muka ƙara anan ana ƙara ganomu ne. Sannan kuma indai Uznu Ururu ne kada ku damu.. Kamar yadda kuka sani mun taɓa fafatawa dashi. Kuma shi ne sanadiyyar ɓatan Nusi. Kada kuyi tunanin ban shirya masa ba. Amma dai kamar yadda kuka faɗa na yadda mu tsaya a kusa da kusa saboda haka zai bamu dama idan wani yana neman taimako mu kai masa ɗauki.
"Iliyasis komai ya dogara dakai. Koda Uznu yana nan ni nayi alaƙwarin zan riƙe shi, da shi da kyaftin ɗin nasa biyar har tsahon wani lokaci. Iyakacin saurin da kayi wajen fitowa, iyakacin nasarar mu."
Koda Armad ya gama bayani sai suka fara kallon juna suna kai-komo da maganar a zuciyarsu. Can bayan wani lokaci sai Cokali yayi ajiyar zuciya ya ce, "na amince da wannan shiri."
Nan take shima Inara ya amince. Shi kuwa Iliyasis fara haɗa kayansa yayi yana cewa, "cikin dare zamu fara aiki ko zamu jira wayewar gari?"
Armad yayi murmushi tare da jin daɗin amincewarsu. Sannan shima ya fara shiri. Da yammaci Inara ya fita ya siyo musu abinci suka ci suka sha sannan Cokali yayi guzuri. Tsakar dare ƙarfe sha biyu da rabi sukai azama suka fito kan hanya suka nufi shalkwatar ajiye bayanai.
Duk da dare ne amma mutane ɗai-ɗai haka na harkokinsu akan titi. Duk su huɗun na sanye ƙatun-ƙatun huluna na filani tayadda baza ka iya gane su ba koda ka ƙura musu ido. Armad ne tsaye a ɓangaren dama shi kuma Iliyasis ta ɓangaren hagu, sai kuma Cokali da Inara a tsakiya. Idan ka dubi Cokali zaka ga kamar ya ƙara ƙiba amma ba komai bane illa soyayyiyar cinyar rago dake naɗe cikin rigarsa. Duk bayan ƴar-tafiya zai baɗa yaji akai ya yaga.
Duk inda suka hangi ma'aikata sai su yanke su canja hanya. Bayan tafiyar sa'a guda sai suka fara hango toluwar ginin da suka dosa. Nan take Armad ya zaro taswirar dake aljihunsa ya kara duba ginin yaga yana can nesa, tsayinsa ne yasa suke iya hangoshi.
Saboda haka suka ci gaba da tafiya. Suna ƙara kusantar wajen ma'aikatan na ƙara yawa saboda haka Armad ya fara amfani da fasahar yanayin-izza domin su kauce musu. Amma duk da haka ba jimawa suka iso wata mararraba Armad ya tsayar dasu yana cewa. "Duk hanyoyin gaba a toshe suke. Bana ganin zamu iya zille musu."
Iliyasis najin haka ya girgiza kai sannan ya ce, "zanyi ƙoƙari ka gama komai acikin awa ɗaya. Ku janye musu hankali har zuwa wannan lokaci. Idan mun gama kada ku manta zamu haɗu a bayan gari inda muka yarje." Yana gama magana ya juye izuwa siffar shirwa yabi sararin samaniya.
Nan take Cokali ya zuge ragowar naman daya rage ajikin ƙashin dake hannunsa yayi cilli da ƙashin. Shi kuwa Inara zare takobinsa yayi.
Armad ya dube su ya ce, "ku afkawa masu tsaron dake bakin ƙofa ni kuma zan jawo hankalin kyaftin ɗin waje. Na tabbatar suna cikin ginin, barinsu aciki zai jawo wa Iliyasis matsala."
A wannan lokaci kowa ya ɗau aikinsa suka fara aiki.
***
Babi na 115: Wadda bata da suna
Armad ya zare takobinsa ya nufi babbar ƙofar shiga ta ginin. Shi dai ginin anyi shi da manyan duwatsu wanda akaiwa fentin ja da baƙi. Ya nada faɗi da yakai zira'i dubu, a tsaye kuma ya ninka haka. Daga can samansa akwai toluwa wadda ke ɗauke da tuta mai kan mutun da baƙaƙen idanu wato tutar gidan Ururu.
A gaban ƙofar akwai mayaƙa guda aƙalla ɗari suna gadi, sauran mayaƙan sun kewaye ginin. Ita kanta ƙofar takai tsahon zira'i sittin a tsaye, amma a ƙulle take. Ga dukkan alamu babu wanda ke shiga wajen sai masu shaidar Ururu.
Armad na ƙarasowa kusa suka hangeshi. Ɗaya daga cikinsu ya ɗaga takobinsa yai masa tsawa. "Kai yaro. Tsaya cak a inda kake."
Armad yayi kamar baiji ba, lamarinda ya jawo hankalin duk masu gadin dake wajen suka juyo a fusace. "Idan ka ƙara taku ɗaya sai dai a haifi wani."
Tunma kafin su rufe baki Armad ya ɗaga takobinsa sama, sannan cikin nutsuwa ya juya ta yakai sara kan wannan masu gadi.
Masu gadin ko alamun zasu kauce basu yi ba saboda aƙalla tazarar dake tsakaninsu da Armad takai taku ashirin. Sun san indai ba takobin ce zata ƙara tsayi ba babu yadda za'ai ta ƙaraso kusa dasu.
To amma bisa tsananin mamaki kawai sai suka ga wani siririn farin haske ya fice daga ƙarshen tsinin takobin ta Armad ya nufo su cikin tsananin sauri kamar walƙiya. Kafin ya ƙaraso wajensu sai suka ga ya tashi sama ya miƙe izuwa can toluwar saman ginin inda tutar Ururu take. Hasken ya juye izuwa siffar takobi, yana ƙarasawa ya shige cikin toluwar ginin sannan ya fice ta baya. Haka na faruwa wata ƙara mai kama da ƙarfe ya sari gini ta tashi. Haka na faruwa saiga toluwar ginin ta cire tayi sama kamar an fille kan mutun. Dai-dai wajenda hasken takobin Armad ya fice shi ne ya cire. Idan ka lura zaka ga kamar ansa takobi an sara.
Nan take kallo ya koma sama kan wannan ƙatuwar toluwa wadda ke lilo a sararin samaniya tana shirin faɗowa ƙasa. Tutar Ururu tai can gefe zata faɗi amma wasu daga cikin mayaƙan Ururu sukai sauri suka shiga ƙarƙasdinta suka tare. Ita kuwa toluwar tana dira a ƙasa ta tarwatse tare da bada wata ingantacciyar ƙara wadda tasa kowa a garin tashi daga bacci.
Da dama daga cikin masu tsaron wajen murza ido suke suna so su tabbatar ba mafarki suke ba. Duk da cewa toluwa ce kawai amma girmanta yafi zira'i goma, sannan kuma da dutse aka gina ta. Lallai za'a sha wuya kafin a samu takobinda zata iya ratsa ta. Amma wannan bashi ba ne abin mamakin ba, babban abin mamakin shi ne yadda akai saran Armad ya tashi daga jikin takobinsa ya kai can ƙololuwar ginin ya samu toluwar.
Ana cikin haka su Cokali suka ƙaraso wajen. Cokali ya kalli Armad cikin mamaki ya ce, "gaskiya ne sarki. Ya sunan wannan fasahar?"
Armad yayi murmushi tare da girgiza kai ya ce, "har yanzu na rasa sunan daya dace da ita. Ƙarfin fasahar walƙiya ta na zuba acikin takobin. Tayadda komai nisa da tsayin waje zan iya kai masa sara da takobi na. Idan na juya takobin nakai sara sai sinadarin walƙiya ta ya ɗauki ƙarfin saran ya kaishi inda nake buƙata. Kaga ta haka kafin abokin gaba ya ƙaraso na gama dashi."
Cokali ya gyaɗa kai cikin jinjina. Sannan dashi da Inara suka ja daga.
Ana haka.ƙofar ginin ta buɗe mayaƙa suka fara fitowa kamar tururuwa suna nufo su Armad.
Armad ya dubi ɗaruruwan mayaƙan dake sanye baƙaƙen kayan yaƙi yayi murmushi tare da cewa, "Ina ganin mun janyo hankalinsu da yawa."
Ana haka saiga wasu sadaukai nan guda huɗu sun futo daga cikin ginin. Suma kayansu baƙaƙe ne amma da ratsin ɗorawa. Kowannensu na riƙe da makami daban-daban.
Armad na ganinsu ya gane sune kyaftin ɗin da ake faɗa. Sai dai kuma kamata yayi ace su biyar ne amma huɗu ne suka fito. Ana haka wannan dubunnan mayaƙa suka kewaye Armad da Inara da Cokali. Saboda yawan mayaƙan zaka iya cewa koda naman jikin su Armad za'a raba wani bazai samu ba.
Lallai akwai matsala. Armad baida damuwa amma Inara da Cokali zasu iya halaka cikin ƙanƙanin lokaci idan Armad baiyi wani abu ba. Sai dai kuma Armad bazai iya amfani da hannun-aradu ba, saboda tamkar yin tallan kansa ne a idon duniya cewa shi ne magajin sarki Eyriyon wanda hakan abu ne da zai jawo matsala da yawa. Fasahar sanyin-babban-sihiri kuma bata da ƙarfin da zata iya halakar da dukkan mutanen. Sannan kuma tana zuƙe ƙarfin izza da yawa. Amma a wannan lokaci Armad bashi da yadda zaiyi, dole ne ya ragewa su Cokali yawan mutanen dake kewaye dasu domin ko ƙarshensu ba'a gani.
Nan take Armad ya tafa hannayensa, lamarinda yasa ƙanƙara ruwa toka ta fara fita daga jikinsa tayi kan wannan mayaƙa. Amma bisa mamaki wannan jarumai basu ji tsoro ba, kukan kura kawai sukai suka afka kansu Armad suna kiran sunan Ururu. Kana ganin idanunsu zaka san cewa akwai tsananin biyayya da imani na gidan Ururu acikin ransu.
Ƙanƙarar ta fara cinyesu tana ruguza ƙasusuwansu amma na baya na ƙara afkowa. Bayan kimanin daƙiƙa talatin ƙanƙarar Armad ta ƙare sabida amma wannan mayaƙa ko rabinsu ba'a ciba. Sannan kuma ga kyaftin guda huɗu na tunkaro su.
Armad ya dubi Cokali da Inara ya ce, "sai dai kuji da dubu ukun nan. Na rage muku dubu biyu. Bari na.da wancan huɗu." Yana faɗar haka ya ɓace daga inda yake ya bayyana a gaban wannan kyaftin huɗu dake tunkaro filin dagar.
Ɗaya daga cikinsu ya dubi Armad sama da ƙasa cikin tsananin jin isa, yana duba wata jarida a hannunsa. Bayan ɗan lokaci ya ɗago ya dubi Armad ya ce, "Armad Wilbafos, kan ka yana da tsada ayrid miliyan ɗaya da rabi. Mai ya kawo ka wannan waje?"
Armad yayi murmushi tare da gƴada kai ya ce, "idan na gaya maka abinda ya kawo ni zaka taimako ne?"
Ɗaya daga cikin kƴaftin ɗin yai tsaki ya ce, "taimako kala-kala ne. Amma ka riga kasan tunda ka kawo hari shalkwatar Ururu kwananka ya ƙare. Koda ace wani abun al'ajabi zai faru ka samu ka fice daga nan Ururu da kansu zasu kamo ka. Lallai ƙarshenka yazo."
Armad yayi murmushi. Inda ace su biyar ɗin duk suna gabansa da bazai damu ba su zauna suyi ta hira har Iliyasis ya fito, sai dai kuma ragowar ɗayan da bai futo ba shi ne damuwar Armad. Sannan kuma ga Uznu.
Armad ya ɓata rai. "Ko zaku gwada kama ni ne? Kunga idan kukai nasara saiku raba miliyan ɗayan da rabin a tsakaninku. Ku biyar kowa nada izza sama da dubu ɗaya. Ku gwada sa'ar ku kawai."
Kyaftin ɗin najin haka suka dubi jina suka fashe da dariya.
***
Babi na 116: Fasahar Cokali
A dai-dai wannan lokaci da wannan kyaftin suka fashe da dariya bayanda suka ji kalamin Armad su Cokali da Inara na gabda fuskantar rundunar mutun dubu huɗu da ɗoriya.
Cokali ne a kan gaba, inda ya zaro wani ƙaton alƙalami daga cikin rigarsa da wani ɗan ƙaramin littafi. Idan ka lura zaka ga alƙalamin anyi shi ne da busasshen ƙashi.
Cikin sauri Cokali ya buɗe littafin ya rubuta 'ALJANIN-ZAKI-DUBU'. Sannan yabi rubutun ya kewaye shi da zanen ɗalasimai. Yana gamawa ya tafa hannunsa tare da rufe ido, lamarinda yasa hasken izzarsa ya fito ya shige cikin littafin.
Inara yai tsalle ya tare wani mashi da aka shillowa Cokali. Amma ana haka sama da mutun goma sukai tsalle suka afka masa. Inara ya ja takobinsa yakai sara dama ya zubarda mutun uku sannan ya sunkuya sauran mutun ukun da suka kawo masa suka ta ɓangaren hagu suka cake ragowar na daman. Inara yai tsalle ya fice daga cikinsu ya koma gaban Cokali ya tsaya. Baisan wacce fasaha Cokali yake ƙoƙarin haɗawa ba amma dai yasan idan har Cokali bai buɗe ido sun fara rage mayaƙan ba to ƙarshensu ya kusa zuwa.
Shi kuwa Cokali ƙara nutsuwa kawai yayi yana zuba ƙarfin izzarsa acikin wannan littafi. Can yaji muryar Inara cikin haki yana cewa, "baka gama bane, Cokali?"
Aƙalla mutun ɗari ne suka kewaye Inara, wasu daga cikinsu ma ko rigarsa basa hangowa. Lallai idan aka ci gaba da haka nan bada daɗewa ba zasu cimmasa. Sannan kuma daɗin daɗawa ga Cokali da yake ƙoƙarin karewa.
To amma ana cikin haka wani farin haske ya fara tashi daga cikin littafin dake hannun Cokali. Nan take Cokali ya buɗe idonsa yana murmushi. Kafin ya rufe baki wani haske dunƙulalle ya fice daga cikin littafin. Hasken na fita ya rabe izuwa gida dubu, kowanne dunƙule ya fara juyawa yana ɗaukan siffa. Kafin kace meye wannan tuni kowanne dunƙulen haske ya ɗauki siffar gawurtaccen zaki. Abu kamar wasa wannan zaki ya juye ya zama na gaske. Zakuna ɗai-ɗai guda dubu sun samu ta hanyar fasahar Marubutan-farko. Koda yake dama ba abin mamaki bane ganin Cokali daga ƙasar Maikironomada ya fito amma duk da haka sai da Inara ya zare ido cikin tsananin mamaki da al'ajabi.
Fasahar marubutan farko ba abu bane gama gari ba koda kuwa a tsakanin sadaukan daular. Sannan kuma ana auna girman kwarewarka da iyakacin yawan abubuwan da zaka iya sarrafawa da fasahar. Duk wanda zai fitar da aljanun-zakuna dubu ba ƙaramin hatsabibi bane.
Ba Inara kaɗai ba, tuni wannan sabbin zakuna suka ja hankalin kowa a filin. Wannan mayaƙa da suke neman halaka su suka ja tunga suna kallon ikon ALLAH. Shima Armad da kyaftin guda huɗu dake gabansa waiwayowa sukai suna kallo.
Nan take wannan zakuna sukai gunji suka afka kan wannan runduna. Wani sabon ƙazamin yaƙi ya rincaɓe, babu abinda kake ji acikin wannan dare sai kururuwa da ƙarar fitar rai. Cokali ya koma gefe ya fito da ragowar abincin da yazo dashi ya fara ci. Armad murmushi kawai yayi ya dubi kyaftin dake gabansa ya ce, "yaushe kuke niyyar kama ni? Ko kun fasa?" Armad na magana yana jijjiga takobinsa yana kallonsu.
Nan take sukai tsalle suka sashi a tsakiya, kowannensu ya zare takobinsa yayo kansa.
Armad ba mutun bane mai wasa a filin daga ba, kuma a kullum da gaske yake yaƙi babu wasa ko jan rai. Saboda haka nan take ya ƙaddamar da takobinsa akansu.
Babu shakka kowanne acikinsu yana ji da isa da izza irin tasa, amma tayaya zasu iya yaƙar abinda basa gani? Domin kuwa suna doso Armad ya ɓace ɓat suka nemeshi suka rasa. Kafin kace meye wannan ya ƙaddamar da fasahar Wasu-wasi akansu.
Can a ƙofar shiga cikin wajen Armad ya bayyana ta hanyar ɗalasimin Kaban'shìsu. Wannan kyaftin huɗu na ganinsa suka rankaya suka afka masa cikin fushi. Armad ya tsaya cak ko motsi baiyi ba yana jiransu. Tuni dai Armad ya daɗe yana hango ranarda zai haɗa fasahar Kaban'shìsu da fasahar Wasu-wasi a waje ɗaya. Ita kanta fasahar wasu-wasi tana ƙara masa tsananin gudu da sauri tayadda zai sari mutun amma ciwo bazai bayyana ba tsahon lokaci har sai mutun ya fara kokwanto akan abinda ya faru. Idan aka haɗa wannan fasaha da fasahar Kaban'shísu wadda ita kanta sauri ce kawai. Kaga za'a samu wata sabuwar fasahar ta daban.
Wannan kyaftin huɗu na gabda cimma Armad suka tsaya cak a yayinda suka ji hannunsu ya fara karkarwa. Kafin suyi aune jini ya fara feshi daga jikinsu. Mamaki da kokwanto ya bayyana a fuskokinsu da zuƙatansu, wanda ya juye izuwa tsoron Armad. Kowa acikinsu tambayar kansa yake yaushe? Yaushe ne har aka sare shi bai sani ba?
**
Acikin wannan ƙasaitaccen gini kuwa Iliyasis ya bayyana a siffarsa ta shaho. Kamar yadda suka tsara babu kowa acikin ginin sai ƴan tsiraru. Duk mayaƙan sun fice yaƙi dasu Armad. Yana shiga ya juye izuwa siffar ɗan ƙaramin kiyashi sannan yabi bango ya fara bibiyar ɗakunan dake cikin ginin.
Ba jimawa ya tadda bayanan da yake nema acikin wani ɗaki mai ɗauke da kantocin karatu. Bayan Iliyasis yayi shiru ya tabbatar babu kowa sai ya juye izuwa siffarsa ta mutun sannan ya fara buɗe takardun. Da dama dai bayanai ne akan tarihi da kuma adadin waɗanda suka mutu a shekarun da suka gabata. Babu wani abu na haƙiƙa.
Ba jimawa Iliyasis ya tabbatar babu sunayen da yake nema anan. Nan take cikin sauri ya juye izuwa siffarsa ta kiyashi ya wuce ɗaki na gaba. Kan kace meye wannan tuni ya ci rabin awa yana lalube acikin duhu.
A hankali yazo ɗaki na huɗun karshe. Akwai masu gadi huɗu da suka rage a bakin ƙofar amma ga dukkan alamu dukkaninsu basa iya amfani da fasahar yanayin izza saboda ta ƙarƙashinsu ɗan ƙaramin kiyashin yazo ya wuce basu ganshi ba.
Abu na farko da Iliyasis ya gani a ɗakin shi ne yasa yasan lallai yazo wajenda yake nema. Kantoci ne guda biyu, ta ɓangaren dama ansa Ikwatora, ta ɓangaren hagi kuwa ansa Kurkukun bango.
Kai tsaye Iliyasis ya juye izuwa siffarsa ta mutun sannan a hankali yadda masu gadin bakin ƙofar baza suji ba ya fara duba takardun sirrin.
Abin mamaki sama da shekaru ɗari bakwai babu wanda ya shiga cikin wannan sashi na Ikwatora sai mutun ɗaya kacal. Wata mace mai suna NUSI, NUSI NÁRA. Sai dai Nusin daya sani sunanta Nusi Djinn. Nan take ya shiga mamaki. Wacece wannan?
Yana haka yaji magana a bayansa. "Wato abinda kuka zo nema kenan? Shi ne kuka ɗauke hankalin mayaƙa."
Iliyasis ya zare takobinsa ya waiwayo ɓangaren da yaji maganar. Inda yayi ido biyu da wata siffa tana fitowa daga cikin bango.
***
Babi na 117: Mafarauci
Iliyasis yaja baya tare da zare takobinsa ya nufi bakin ƙofa. A ganinsa tuni sun riga sun cimma abinda ya kawo su, tsayawa ƙara ɓata lokaci da fafatawa duk daga baya ne.
Surar dake bayyana daga jikin bangon ta zama babban mutun mai dogon gashi baƙi. "Idan da kunsan wannan kaɗai kuke nema da kun tambaya, wataƙila mu baku kai tsaye ba tare da matsala ba. Amma tunda kuka tozarta toluwar ginin wannan shalkwata, ƙarshen ku yazo. Sa'ar da kuka taka shugaba Uznu bayanan, amma tuni mun tura masa saƙo kuma yana kan hanya. Sannan kuma tuni nasa aka kewaye garinnan da tsarin ɗalasimai, babu wanda zai ƙara shiga ko fita sai Uznu ya ƙaraso."
Yana magana ya kawowa Iliyasis sara da ƙarfin gaske, lamarinda yasa iska ta tashi saboda ƙarfin saran. Da kyar Iliyasis ya kaucewa takobin ta wuce ta samansa, inda ta datsa saman ginin tare da bayarda wata ƙara mai ɗimautarwa. Iliyasis baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen mayarwa da kyaftin ɗin sara da takobinsa. Nan take ƙazamin yaƙi ya rincaɓe tsakaninsu.
Armad na shirin shiga ƙofar ginin ya kawo wa Iliyasis ɗauki yaji wata ƙara kamar ansa bom a saman ginin. Yana ɗaga kai ya hango ƙura da ƙasa a saman ginin, wasu mutane guda biyu sun fasa ginin sun fito. Duk da a sama suke amma basu daina fafatawa ba, babu abinda kake ji sai ƙarar takubba.
Daga gefe aljanun-zakunan Cokali ne kawai ke aiki suna tarwatsa dubunnan mayaƙan nan. Shi kuwa Inara duk inda ya samu dama kawai aika sara yake, sannan kuma yana ƙoƙarin kare kansa daga masu da kibbau da ake harbo musu.
Cokali har yanzu bai tsagaita cin naman dake hannunsa ba, amma a duk lokacinda wata kibiya ko mashi yayo kansa ɗaya daga cikin zakunan sai yai tsalle sama ya tare.
Koda Armad yaga bayyanar Iliyasisi saiya juya ya kalli wannan kyaftin huɗu dake kwance ƙasa cikin jini ya tabbatar basu da damar ƙara tashi nan kusa sai kawai ya ɓace ya bayyana a kusa da Iliyasis. Kafin kyaftin ɗin dake fafatawa da Iliyasis ya ankare tuni Armad ya tambayi Iliyasis ko ya samo abinda ya shiga nema. Inda Iliyasis ya bayyana masa abinda ke faruwa. Da kuma sunan ''Nusi Nara'' da ya gani.
Wannan kyaftin yai mugun fusata da ganin yadda suke tsakiyar fafatawa amma Armad da Iliyasis suna hira, nan take yai ƙaraji wani baƙin haske ya fara bayyana a jikin takobinsa sannan ya afka kansu Armad.
Amma a dai-dai wannan lokaci Armad ya zare takobinsa, amma maimakon yai kan kyaftin ɗin sai ya daki gefen wuyan Iliyasis da takobin, lamarinda yasa Iliyasis ya faɗi a sume. Sannan kan yaje ƙas Armad ya cillashi cikin zobensa. Tunda dai dama shi wannan zobe a ƙa'idarsa baya ɗaukar mutun mai rai.
Armad yai amfani da fasahar Kaban'shìsu ya ɓace daga inda yake ya bayyana a gefen Cokali ya sumar dashi ya cillashi cikin zoben, sannan ya cilla Inara.
Cikin ƙiftawar ido Armad ya ɗebe muƙarrabansa ya ɓace ɓat aka neme shi an rasa.
Kan kace meye wannan Armad ya bayyana a bayan gari tunda babu wani tsarin ɗalasimai dazai iya tare Kaban'shisu. Bayan ya bayyana a bayan gari ya fito da dokinsa Ubbaru daga zoben ya hau ya nausa cikin daji ya nufi garin da ƙofar Eycigan take domin komawa daular Sisiya ta sarki Bihanzin. Yau kwanansu huɗu kenan da fitowa.
**
Acan doron ƙasa na biyu kuwa, akan wasu manya-manyan tsaunuka dake kewaye da babban birnin daular, wani mutun ne zaune a saman wani katafaren tsauni wanda yafi kowanne tsauni girma a wajen. Saboda tsabagen girman wannan tsauni daga ƙololuwar samansa ana hango taurarin dake sararin samaniya. Sannan kuma idan kana da ƙarfin idanuwa irin na ƴaƴan Ururu zaka iya ganin gudu da tafiyar wannan taurari kamar a tafin hannunka.
Abu ne sananne kamar yadda kowanne mutun ake haifarsa da aljaninsa, kowanne mutun ana haifarsa akwai tauraruwar dake wakiltar ruhinsa. Idan wannan tauraruwa ta mutu shima wannan mutun ya mutu. Wasu da dama sun yadda cewa haske da lafiyar tauraruwa yana nuni da lafiyar bil-adaman da take wakilta.
Wannan mutun nada tsayi madaidaici, haɗe da manyan kafaɗu. Gashin kansa ɗauke yake da ratsin furfura wadda ke nuni da yawan shekaru. Amma idanunsa baƙaƙe ne dunhum kamar duhun dokar daji. Kana ganinsu zaka ji tsigar jikinka na tashi kamar wanda yai ido huɗu da mutuwa. Fuskarsa na ɗauke da nutsuwa irin wadda mutun ke samu idan yasan yafi ƙarfin dukkan talikai. Idanunsa sunyi kama dana mafarauci a yayinda yake farauta.
Wannan mutun kwance yake akan wani ɗan ƙaramin gado yana nazarin taurarin dake sama. A hannunsa akwai wata sandar tsafi baƙa wadda keda matuƙar tsayi. Idan ya ɗaga sandar sai kaga ya taɓo taurarin dake sararin samaniya.
Wannan mutun yai murmushin izza sannan ya ɗaga sandar tasa, yasa maƙatar dake ƙarshen sandar ya saƙalo ɗaya daga cikin taurarin sannan ya jawo ta ƙasa.
Koda haka ta faru sai wannan tauraruwar ta fara wutsil-wutsil tana ihu tana roƙon gafara. Amma wannan mutun ya finciko ta ƙasa, sannan yasa hannunsa akanta. Nan take tauraruwar ta fara ƙanƙancewa tana dunƙulewa har saida ta dawo ƴar ƙarama sannan yasa hannu ya matse ta ya fasa ta. Wata ƴar ƙaramar ƙara mai kama da an fasa kwai ta tashi.
A can birnin Daldas kuwa dake doron ƙasa ta biyar, hira kawai ake a wajen cik abinci da wani ɗan tawayen Ururu kawai sai gani akai ya fara haɗa gumi kafin daga bisani ya faɗi ƙasa matacce.
Wannan mutun mai idanun Ururu ya fasa tauraruwarsa ya kasheshi ba tare da kowa ya sani ba. Wannan mafarauci ba wani bane illa sarki Dul'Ururu ɗan sarki Kuyurussa'ayi Ururu. Wanda akanyi wa laƙabi da MAFARAUCI, amma na ruhi.
Murmushi kawai Dul'Ururu yayi yaci gaba da laluben wacce taururuwa zai ƙara fasawa. Yana cikin haka saiga wani ma'abocin Ururu nan ya bayyana a gefensa. Idan ka lura zaka ga wanda ya bayyana ba wani bane illa Uznu Ururu.
Yana bayyana ya faɗi ƙasa yayi gaisuwa ga wannan mutumi sannan ya ce, "shugaba Dul'Ururu, kamar yadda ka faɗa wannan yaro mai ɗauke da Littafin-takobi ya isa birnin Duka, kuma ya nemi yasan sunayen wanda suka shiga sashin Ikwatora. Sannan kuma kamar yadda ka umarta ban hanashi ba. A halin yanzu ma ya fice daga garin."
Koda jin haka sai Dul'Ururu ya tashi zaune ya fara magana cikin wata murya mai kama da ana goga tsohon ƙashi a jikin bango. "Yanzu ka samu cikakkiyar hujjar da zaka shiga cikin yaƙi mai zuwa da zai afku tsakanin sarakunan Jinzidal."
Yana gama magana ya ƙara kwantawa ya ci gaba da farautar da yake.
***
Babi na 118: Denizawa
Yau kwanaki biyu kenan da tserewar su Armad daga garin Dùka dake doron ƙasa na bakwai. A wannan rana sun iso ƙofar garin Jekis na daular Sisiya ta sarki Bihanzin. Babu alamar gajiya a tare dasu, da alama tuni sun huta kafin su iso ƙofar garin.
Iliyasisi ne ya fara hango banbanci a tsarin ƙofar shiga ta garin. Domin kuwa a wannan rana ƙofar a buɗe take hanhai. Tun daga nesa zaka hango baƙi suna ta zarya ciki da waje. Masu tsaron ƙofar kawai sai dai su duba ka su tabbatar baka ɗauke da kowanne kayan hatsari amma basa karɓar kuɗin shiga. Su kansu ƙofofin anyi musu ado da wasu sabbin kaya masu launin ja da fari. Komai dai yana bada kyalkyali kamar ɗakin amare.
Sai dai duk da wannan hankalin Cokali na kan wata jarida da yake karantawa. A shafin jaridar akwai hotunansu duk su huɗun. Cokali ya ƙara liƙa shafin jaridar a idonsa don ya tabbatar abinda yake gani dai-dai ne kafin daga bisani yai tsaki ya ce, "Wai ma ya akai suka samu hotunan mu?"
Inara ya kalli Cokali ya fashe da dariya. "Cokali yadda kake nuna tsoro yanzu babu wanda zaice kaine mai aljanun-zakuna dubu."
Shima Armad yai dariya yana cewa, "ka rabi da Cokali kawai Inara."
Cokali ya kara yamutsa fuska kamar zaiyi kuka ya ce, "kai Armad baza ka gane bane. Kai dama da kuɗi akanka, dan an kara shi daga miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar zuwa miliyan talatin ba wani abu bane. Amma ni babu wanda ya damu dani ada amma yanzu ansamin miliyan huɗu, yanzu yaya ake so nayi kenan."
Armad ya ƙara fashewa da dariya ya amsa da cewa, "to ai Inara ma ansa masa miliyan biyu, sannan Iliyasis da aka sawa miliyan bakwai ya ce me?"
Haka dai suka ci gaba da tsokanar Cokali har suka shiga ƙofar garin. Sai a lokacin suka gane mai yasa Iliyasis yayi shiru yana tunani baisa baki a tsokanar Cokali ba.
Shigarsu suka iske an shimfiɗe hanyar da shimfiɗu na musamman, a gefen shimfiɗun sadaukai haye bisa dawakai sun tsattsaya. Kana ganin irin samfurin kayan dake jikin mahayan kasan ba daga wannan daula suke ba. Jar zilaika ce mai ratsin fari-fari a jikinsu tana jan ƙasa.
Iliyasis na ganinsu ya gane daga ina suke. "Armad, sadaukan daular Denizawa ne."
Armad najin haka ya gane abinda ake ciki. Nan take fuskarsa ta canja yasan mai ya kawo su domin kuwa yau kwanansu bakwai dai-dai da tafiya. Kuma dama bayan kwana bakwai Nostaljiya ta gaya masa yarima Bizaya zai kawo ziyara domin neman aurenta.
Armad ya rankaya da sauri izuwa cikin gari yana sassarfa, Inara dasu Iliyasisi suka bi bayansa. Kana ganin Armad kasan ran maza ya ɓaci. Ba jimawa suka fara hango toluwar ginin fadar, inda suka ƙara sauri. Suna isowa kimanin taku dubu inda babu gidaje sai filin daya isa fada suka ga wasu dakarun. Sannan kuma an jere tubalan dinare manya-manya mafi tsada a duniya tun daga farko har izuwa ƙofar shiga faɗar. Hasalima mutane da dama akan wannan tubala suke tafiya saboda yawansu yasa sun shimfiɗe ko'ina. Kana gani kasan kawai ƙasaita da isa da kuɗi ake nunawa. Mutane da yawa ƴan kallo daga nahiya-nahiya sunzo suna kallo.
Su Armad suka wuce ta gefe a hankali suka nufi ƙofar fadar. Suna zuwa suka tararda wasu sabbin masu gadi suna ta muzurai. Armad ya miƙa katin shedarsa da kwamanda Damjinu ya bashi. Mai gadin ya murza gashin baki yai muzurai yana duba katin gaba-da-baya. Can dai ya yamutsa fuska ya miƙo musu katin ya ce, "ku ɗanyi haƙuri a gama abinda ake aciki, indai ba jinin sarauta ba yau an hana kowa shiga saboda..."
Armad baima gama jin abinda zai faɗa ba ya ture shi ya wuce. Mai gadin ya bishi da sauri zai riƙe shi amma Inara ya shiga gabansa. Sauran masu gadin suka hayayyaƙo amma su Cokali da Iliyasis suka tare su. Ana cikin kace-nace sai hankalin jama'ar wajen yayo kansu, hatta sauran sadaukan da suka zo daga daular Denizawa duka suka rankayo domin jin mai ke faruwa.
Shugaban Denizawan wanda wani ƙaton sadauki ne cikin Zilaika ya ce, "wai su waye ne?!"
"Wai wannan ne dole saiya shiga kuma... " Masu gadin sun fara bayani amma suka juyo suka nemi Armad ko sama ko ƙasa suka rasa. Tuni yayi amfani da fasahar Kaban'shisu ya ɓace.
Armad na shigewa ya fara amfani da fasahar yanayin-izza yana nan inda Nostaljiya take. Ba jimawa ya jiyo ta, sai dai kuma a gefenta akwai wasu samari gida biyar wanda bai gane ko su wane ba. Kai tsaye ya tunkari wajen.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya iso cikin wani shinge inda ya hangi wasu samari guda biyar a zaune suna fuskantar ƴammata uku. Kewaye dasu guyangi ne suna ta hidima. Sannan kewaye da kuyangin wata ƙorama ce mai bada ni'ima tana kwaranya.
Wannan samari sun sa Deniz Bizaya a tsakiya. Su kuma ƴammatan sun sa Noltajiya a tsakiya. Dukkaninsu sun sha kwalliya irin ta ƴaƴan sarakunan farko amma kwalliyar Deniz Bizaya tafi ta kowa acikin samarin. Rigarsa ta alharini ce mara nauyi, mai launin shuɗi. Akansa akwai hula irinta saƙi wadda tasha ado da gashin-bakin fararen aljanu. Fuskarsa ta ƙara cika ta ƙara kyau sama da yadda Armad ya ganshi a gasar Jinzidal.
Sai dai amma duk wannan idan ka kwatanta shi da wacca ke gabansa zaka ga nan take ya koma baƙi. Nostaljiya haske kawai take bayarwa kamar rana lokacin da take tsakiyar sama. Siffar kyau takai ƙololuwar bayyana a jikinta. Tana sanye da wata riga doguwa ruwan hoda mai beza a wuya. Nan take Armad yaga kamar tafi jiya kyau.
Daga inda Armad ke tsaye baya jin mai suke cewa amma lallai yaga Bizaya yana magana ita kuma Nostaljiya tayi shiru. Ba jimawa sai yaga wannan samari da ƴammata sun tashi sun basu waje.
Armad ya nemi waje ya ɓoye yana jira yaga yadda ganawa tsakanin Bizaya da Nostaljiya zata kasance. Wata zuciyar tana ta ingiza shi yaje ya rikita wajen amma ya daure ya tsaya a baya yaga mai zai faru.
Comments
Post a Comment