Dul'Ururu ya girgiza kai. "Bazai yiwu ba. Haruta yafi ƙarfinsu. Ga taimakon duniyar babban sarki yana aiki a wajen."
"Baka tunanin Armad zai iya karya fasahar duniyar?" Inji Maruta.
"Eh, zai iya, amma koda a waje ne Armad da Zaikid da dukkan wanda suke cikin gadar zaren babu yadda zasu yi da Haruta. Kai ma kasan wannan."
"Haka ne..." inji Maruta. "Sai dai kawai idan bamu lissafa ƙarfin Armad dai-dai ba. Watakila ya wuce inda muke tunani. Wanda hakan kuma zai zama mafi girman kuskure da muka yi."
Dul'Ururu yayi shiru yana lissafi. Lallai sun tafka babban kuskure idan ta tabbata an kama Haruta. Hakan zai iya ɓata musu shiri amma babu yadda zasu yi. Saboda an kama mutun ɗaya daga cikinsu baza su fasa abinda suke ƙoƙarin yi ba.
"Idan da gaske sun kama shi zasu yi amfani dashi wajen kwatar Fatima," inji Dul'Ururu. Ya miƙe ya fara kai-komo cikin ɗakin. Lissafi ya fara ƙwacewa kafin ma a fita.
Bayan ɗan lokaci Maruta ya miƙe ya saka rigarsa zai fita.
"Dul'Ururu, waye zai hau kan kujerarsa? Kasan dai baza mu barta haka ba kowa ba, ko?"
Ah, kuma fa haka ne. Dul'Ururu yaja dogon nishi. Akwai kujerarsa data Maruta da Haruta wanda zasu zauna a waje ɗaya. Yanzu tunda babu Haruta dole ya samu wani ya maye gurbinsa domin barin kujerar a haka zai zama kamar sun gaza. Yana da mutanen da zai saka wanda zasu iya aikin da yake so. To amma matsalar ita ce duk wanda ya saka sai mutane sun gane wajen Haruta ne. Dole idan aka ga Maruta ayi tsammanin ganin Haruta. Rashin ganin nasa zai jawo cece-kuce.
Ya ɗakko alkalami da takarda ya fara canja tsarin yaƙin. Dole sai yayi nasara koma ta wacce hanya. A yau zai tunawa duniya girman Ururu.
***
A wannan lokaci su Armad sun iso bangon kudu ta cikin kurkukun bango. Tuni suka yanke shawara hanyar data rage musu ta zuwa doron ƙasa na biyu tana cikin sashin Ikwatora saboda haka suka sakko daga kan bangon arewa zuwa cikin kurkukun bango. Tafiyar data ɗauke su kusan awa biyu cir duk kuwa da ɗalasiman da sukai amfani dasu. Daga nan kuma suka ɗaure ƙasa suka tafi izuwa bangon arewa. Tafiyar data ɗauke su awa uku. Suna isa jikin bangon kudu suka fara laluben hanyoyin da zasu shiga. Kada dai mai sauraro ya manta shiga kurkukun bango bashi da wahala, amma kuma fita daga shi abu ne wanda hatta manyan ma'abota izza yake wahalar dasu. Ururu basu yarda na cikin kurkukun su shiga sashin Ikwatora ba, sannan kuma basu yarda na cikin sashin su fito su shiga kurkukun ba.
A baya munga yadda Nusi ta sha wahala wajen fita daga sashin domin tazo wajen Armad a kurkukun. Zaka iya cewa kaf sashin Ikwatora babu wani mahaluki da yake da damar shige da fice sai babban sarki Ƙaraiƙisu. Sai dai kuma a kullum ma'abota izza ba ai musu shinge, idan ma kayi sukan samarwa da kansu hanya da zasu ketare duk wata iyaka da aka sa musu.
Acan baya munga yadda Armad yayi amfani da sabuwar fasahar Kaban'shisu da kuma jikinsa na walkiya ya ratsa ta cikin bangon, anan kusa kuwa Armad ko kaɗan bayan jin wahalar keta bangon. A halin yanzu zaka iya cewa wannan katanga ba matsala bace a gare shi. Sai dai kuma yana tafiya tare da Zaikid da Shata wanda bashi da tabbas ko suna da fasahar da zata wutar dasu.
Yana cikin tunani yaji muryar shata a kunnensa. "Akwai wanda bazai iya wucewa ba acikinku?"
Armad ya juya ya kalli Zaikid sannan su biyun suka juya suka kalli Shata. Babu wanda yace uffan. A tare suka juya suka nufi bangon inda suka bar kwale-kwalensu anan. Daga nesa idan ka hango su zaka ga mutum uku suna tafiya hankali kwance sun nufi bangon ruwan. Kai idan baka sani ba kace sun sami taɓin ƙwaƙwalwa domin dai babu wani mutum da zai tunkari bango da ƙafafunsa a halin yana cikin hayyacinsa. Amma su Armad ko a jikinsu, haka suka ci gaba da tafiya suna tunkarar katangar babu alamun tsoro ko baƙin ciki a tattare dasu. Suna zuwa inda ƙasar ta rabu da jikin ruwan sai suka ci gaba da tafiya ba tare da sun tsaya ba ko kuma sunyi kokwanto. Idan mai hange ya hangosu daga nesa zai ga kamar tsuntsaye ne suke tafiya akan iska: a ƙasansu rami baki-kirin amma kuma kafafunsu sun daidaita akan iska ba tare da sun faɗa ciki ba. Haka suka ci gaba da tafiya suka kai ƙarshen ramin. Zakai tunanin zasu tsaya su kira wani ɗalasimin ko kuma suyi wani surkulle, amma kurum sai suka danna kai cikin ruwan.
Bakaken idanuwa a jikin munanan kayuka marasa fata suka bayyana a gabansu suna ƙara mara sauti. Duk inda wannan halittu suka bayyana sai kaga ruwan ya fara hankoro yana neman cinye su Armad, amma idan ya kusanto su sai kaga ya baje ya kasa ƙarasowa. Ikon da yake cikin ruwan ya kasa cimmusu. Yayi-yayi, amma a banza. Suna tafe ƙafafunsu akan ruwa amma kai kace ƙasa suke takawa. Babu wanda yace uffan haka suka ci gaba da tafiya tsawon dakiku kafin su fice daga cikin bangon.
Sashin Ikwatora yayi musu sallama. Tun daga inda suke suna hango alamun rayuwa da gine-gine daga can nesa. Ga titi ya tashi tun daga nan ya shiga cikin gari. Kai tsaye su Armad suka haye ramin daya raba bangon da doron ƙasar suka hau kan titi suka nufi cikin gari.
Akan hanyarsu sun gamu da mutane da dama, da dodo, dama wasu jinsin na daban da ba'a saba gani a sashin Ikwatora ba. Suna tafe suna tattauna yadda ya kamata suyi domin su isa doron ƙasa ta biyu.
A inda matsalar take shi ne duk wanda ya fito daga kurkukun bango to kai tsaye sashin Ikwatora na shida zai shiga tun da kurkukun bata da doron ƙasa. Kuma wannan sashi shi ne na ƙarshe a sashin Ikwatora. A samansa akwai sashi na biyar, dana huɗu, dana uku, kai har zuwa sashi na daya. Kada dai a manta doron ƙasa na farko bashi da sashin Ikwatora saboda haka sashi na farko na Ikwatora shi ne a saitin doron ƙasa ta biyu kuma nan su Armad suke so suje. Daga nan sai su keta ta cikin bango su shiga doron ƙasa ta biyu.
Sai dai kuma a sashi na farko na ikwatora anan fadar sarki Ƙaraiƙisu take, anan daular samudawan sashin Ikwatora take. Su Armad sun kaucewa babbar katanga amma kuma har yanzu suna da buƙatar su hau sama su wuce sashi na biyar, su wuce na huɗu, har suje na ɗaya. Babbar sa'ar da suka ci akwai kofofin Eycigan wanda indai kana da kuɗi zasu siyar maka da tikiti kaje duk inda kake so. Sai dai kawai fatan kada Ururu su saka tsaro a hanyar.
Su Armad suka bi layi a bakin gari na farko da suka tarar. Masu gadin suka tambaye su sunayen su inda suka bada na ƙarya domin gudun faɗan da basu shirya ba. A wannan ƙauye suka hau keken doki ya tafi dasu zuwa gari na gaba wanda anan ƙofar Eycigan take.
"Ah, Armad, idan zan iya tunawa anan Nusi tayi mulki, ko?" Inji Zaikid.
Wato labarin duniya baya buya, abinda ya faru a sashin Ikwatora har ya fita waje ya samu Zaikid. Watakila Zaikid bazai rasa abokai a sashin Ikwatora ba.
"Eh, anan tayi mulki," Inji Armad. "Amma kusan wata guda kenan data a jiye muƙamin saboda ni. A halin yanzu akwai yiwuwar wani ya maye gurbinta."
Idanun Armad suka koma kan tagar dake gefensa inda yaga dazuka suna ta wucewa. Duk girman daji sai kaga ƙanƙara ta cinye shi. Ga wata irin iska mai ƙarfi tana ɗiban dusar ƙanƙarar tana watsa ta ko'ina. Hankalinsa ya koma kan Nusi. Ji yake kamar zai hangota acikin dajin. Bayan mintuna ya fuskanci hakan baza ta yiwu ba, babu wanda zai gani a wajen komai tsananin son da yake yi.
Wata dusar ƙanƙara ta daki dokin dake jan su amma dokin ya shanye yaci gaba da tafiya. Armad baya jin sanyin saboda yanayin jikinsa na walkiya, amma hakan ba shi yake nufin Shata da Zaikid baza suji sanyin ba. Ya juya ɓangaren da Shata yake inda ya lura cewa tuni Shata ya dukunkune acikin bargo, ko fuskarsa ba'a gani. Shi kuwa Zaikid ya zaro wata alkyabba daga cikin jakar tsafinsa ya rufe jikinsa tun daga kafaɗa har zuwa ƙafa. Duk da keken dokin bashi da girma sosai wanda hakan yasa su ukun jikinsu yana gugar juna. Ya kamata hakan ya rage musu sanyin da suke ji amma babu alamun hakan.
Shi kuwa direban wanda yake gidan gaba rigar dake jikinsa ba wata mai nauyi bace. Ba tafi ta Armad ba. Armad ya leƙa ta ƴar-tagar dake tsakaninsu, ya ce, "malam, sannu da ƙoƙari."
"Sannunka," inji direban.
"Naga ka bar ƙofar ka a buɗe kuma babu kayan sanyi a jikinka, hala dai sanyin baya damun ka?"
Direban ya juyo ya ƙara kallon Armad. "Kaima zan iyai maka wannan tambayar, ɗan samari. Gashi dai yanayin harshen ka kamar na baƙi amma kuma sanyin baya damun ka. Ba kamar mu da aka haifa anan muka saba da sanyin ba. Ko akwai wata fasaha ne da za'a bani?"
Hmm. Wato sabo ne yasa direban bai damu da sanyin ba, shi kuma direban yana tunanin Armad fasaha yake amfani da ita.
"Ina da fasaha da take hanani jin sanyi," Inji Armad. "Amma baza ka iya amfani da ita ba. Sai dai ina da wasu fasahohin idan kana so."
Direban najin haka ya zare ido. "Da gaske zaka bani fasaha?"
"Eh mana, mai zai hana?"
Direban najin haka yayi wata dariya mai nuna yasan inda Armad ya dosa. "Nawa ne kuɗin ko wace fasaha? Domin dai ina fatan ba zuwa kai ka kwace min ƴan kudi na ka koya min fasahar ƙarya ba."
Ko da Armad yaji haka sai ya zura hannu acikin zobensa ya ɗauko takarda. Ya zaro alkalaminsa na tsafi ya zana hatimi a jikin takardar sannan ya nannade ta izuwa laya ya miƙawa direba. .
"Indai kana riƙe da wannan layar a jikinka babu wata wuƙa da zata kama ka, idan kuma kayi musu ka gwada."
A hankali direban ya zuro hannu ta cikin taga ya karɓi layar. Yana jin ya damƙi layar a hannu yayi sauri ya sata a aljihun gaban rigarsa kamar yana tsoron kada Armad ya fasa. Ya ɗauko wata wuƙa dake sakale a gaban keken dokin ya nufi cinyarsa zai gwada. Har ya kusa sai yaji kokwanto. Ya waiwayo ya kalli Armad. Armad ya gyaɗa masa kai tare da zura hannu ta tagar ya dafa kafaɗarsa. Direban bai san mai yasa ba amma hannun Armad yana taɓa shi yaji wani aminci ya sauka a gareshi. Ya san Armad bazai masa ƙarya ba. Ya ɗaga wuƙar kai tsaye ya daɓa a cinyarsa.
Wuƙa ce farin karfe amma tana taɓa cinyarsa ta karye gida biyu. Fuska cike da al'ajabi ya juyo ya kalli Armad baki a buɗe amma ya kasa cewa komai. Armad ya gyaɗa masa kai yana murmushi. "Ga wata." Ya rubuta masa wata layar ya miƙa masa."Ita kuma wannan idan kana ɗauke da ita zaka iya ganin abu komai duhun waje, sannan kuma aljanu baza suzo inda kake ba."
Nan take jikin direban ya fara ɓari, ya buɗe baki yana karkarwa ya ce, "Farar laya? A'a, bazan iya siya ba. Ina nake da kuɗin da zai sayi farar laya? Ita kanta ta farkon daka bani ba lallai na iya biyan kuɗinta ba. Idan kuwa ina so to sai dai na siyar da dawakan nan nawa da keken dokin wanda kuma dashi nake cin abinci. Saboda haka ina ganin kawai sai dai... Na haƙura."
Armad ya fashe da dariya. "Ai kyauta na baka."
"Kyau... ta? Da gaske?!"
Armad ya gyaɗa masa kai alamun da gaske yake. Kawai sai hawaye ya fara zuba daga idanun direban. Armad yaja wani dogon nishi ya kuma tuna da yanayin tsadar kayan tsafi a sashin Ikwatora. Kamar yadda Nusi take faɗa babu ma'abota izza da yawa a sashin Ikwatora saboda wasu dalilai. Na farko dai shi kansa babban sarki Ƙaraiƙisu baya amfani da izza. Sannan kuma duk sarakunan dake sashin baƙar guguwa ce take basu fasaha wadda zasu yi amfani da ita su mulki jama'arsu. Daɗin daɗawa ba'a gasar jinzidal a sashin Ikwatora saboda haka yara suna tasowa bada niyar yaƙi ba. Idan yaro ya taso yana tunanin za'a siyar da ƴan gidansu a matsayin bayi idan bai zama ma'aboci izza ba to lallai kowa zai dage ya koyi fasaha. Hakan zai sa ma'abota izza su yawaita kamar a sashin kudu da sashin arewa na doron ƙasa, saɓanin ikwatora inda ba'a jinzidal. A cewar Nusi waɗannan su ne dalilan da suka sa kayan izza irin su farar laya suke tsada a sashin Ikwatora.
Amma yana da kyau a fahimci cewa ko a sashin arewa na doron ƙasa inda Armad yake rayuwa, farar laya tana haura Ayrid dubu ɗari. Yaya kake tunanin farashin a ikwatora? Saboda haka ba abin mamaki bane idan wannan direban ya fashe da kuka. Zaka iya cewa kyautar yanke-talauci Armad yayi masa.
"Sunana Biyri," inji direban, murya tana rawa. "Nagode, nagode, bazan taɓa mantawa da wannan kyauta da kai min ba, iyali na ba zasu manta ba. Ko zan iya sanin sunan shehun malamin?"
"Sunana Armad Wilbafos."
"Armad... Wilbafos...?" Direban yayi shiru yana tunani. Kamar ya taɓa jin sunan amma kuma ya rasa gane a ina. Can dai abin ya faɗo masa. "Kai ne Armad Wilbafos ɗin da masu bakaken idanuwa suke zance?"
Armad ya yamutse fuska cikin mamaki. Ya gayawa mutumin sunansa ne bada wata niya ba, domin dai sashin Ikwatora waje ne da yake a killace, saboda haka zaiyi abinda ke faruwa a wajen duniya yazo musu. A cikin ƴan-shekarun nan idan ka ɗauke Nusi da sarki Ƙaraiƙisu dasu Armad da Ikenga to zaka ga babu wani mahaluki daya shigo sashin Ikwatora. Saboda haka Armad zaiyi mamaki ace wannan direban yasan sunansa da kuma ƙabilar Ururu masu bakaken idanuwa.
"Biyri, kai kuwa a ina ka gamu da masu bakaken idanuwa? Nasan a iyakacin sani na sun kai shekaru daruruwan rabonsu da wannan sashi."
Biyri ya kalli Armad cikin mamaki. "A'ah, wai baka san abinda ya faru a wannan watan ba?"

****

Llll
"Amma kasan da harin da masu bakaken idanuwa suka kawo mana?"
Armad yayi shiru.
"Basu kaɗai ba, da dama mutane sun shigo mana daga duniyar waje ta dalilin harin."
Hmm. Wato abubuwan da suka faru a wannan wata da baya nan suna da yawa. Liman Umaru ya faɗa masa sarki Ƙaraiƙisu yaje da kansa ya taka rawa a gasar jinzidal data gabata. Hasalima shi ne yayi nasara a gasar kuma shi aka siyarwa da Fatima da Zaikid a matsayin bayi. Saboda haka Zaikid zai san abubuwan da suka faru. Armad ya juya inda Zaikid yake kishingide da niyar yayi masa tambaya amma Zaikid ya riga shi yin magana.
"Ina ganin Ƙaraiƙisu yana daga cikin wanda zasu taimakawa Ururu a wannan yaƙi," Inji Zaikid. Ya gyara zama ya fuskanci Armad. "Zancen an siyar damu a matsayin bayi a jarida ne kawai. Kaga tunda muka shiga hannun Dul'Ururu bamu motsa ko'ina ba. Sau ɗaya kacal na taɓa ganin Ƙaraiƙisu. Zancen ya tafi damu sashin Ikwatora sannan wai daga baya Dul'Ururu yace ya dawo damu zai siya wannan duk a shafin jarida ne kawai. Da ni da mahaifiyarka Fatima muna cikin kurkuku mafi tsaro a doron ƙasa na biyu tun daga sanda Ashura suka kai mu har zuwa sanda akai kamfen aka gama, akai jinzidal aka gama. Lokaci ɗaya da suka fito damu shi ne ranar ƙarshe ta cinikin bayi bayan da aka ce ƙaraiƙisu yayi nasara. A ranar suka fito damu gaban jama'a da sunan za'a siyar damu. Su kuma jaridu wanda suke goyon bayan Ururu da kuma ƴan-bani-na-iya suka buga labari an siyar damu. Saboda haka bani da masaniya akan abinda ya faru a sashin Ikwatora."
Armad ya fahimci abinda Zaikid yake faɗa. Dama kuma yasan ba komai aka rubuta a jarida zai aminta dashi ba. Amma dai abin tambayar shi ne mai ya faru a sashin Ikwatora har Ururu suka shigo musu? Sannan kuma meye alaƙar sarki Ƙaraiƙisu da Ururu?
"Meye ya kawo masu bakaken idanuwa sashin Ikwatora?" Armad ya tambayi direban mai suna Biyri. "Ka ɗauka kawai mu baƙi ne da muka shigo daga waje wanda bamu san abinda ya faru ba."
Mutumin ya ɗan kalli Armad cikin kokwanto yana tsoran yin magana. Bayan ɗan lokaci ya buɗe baki yace "naji ance masu bakaken idanun sune suke mulkin doron ƙasa ta farko. Wai sun zo ne domin suyi kamfen. A cewarsu akwai wani tsarin rayuwa mai suna jinzidal da suke so su kawo sashin Ikwatora. A farkon watan nan suka buɗe manya-manyan ƙofofi a jikin bangon kudu da arewa suka shigo da mayaƙansu domin su yaƙe mu. Alkalai suka yadda sarki ƙaraiƙisu yayi amfani da ƙarfin baƙar guguwa ya tarwatsa rundunar masu bakaken idanun, ya fatattake su ya kora su inda suka fito. Amma a ɗan-tsukin da suka shigo sai da suka haddasa matsaloli da dama a sashin ikwatora wanda har yanzu ake ƙoƙarin a magance su.
"Abu na farko sun kawo mana kiyayya wadda bamu santa ba. Sun zo da hotuna da kuma sunaye na mutane wanda suka ce suna nema kuma idan an kawo musu zasu biya kuɗaɗe masu ciwo. Anan naji sunan ka. Armad Wilbafos. Babu hoton ka amma saboda yawan kuɗin da suka sa akanka kusan babu wanda bai san sunanka ba. Sun jawo mana matsalar tsaro. Kaga yawancin mutanen da suka biyo su suka shigo ta ƙofar da suka buɗe, yan fashi ne da yan sane da yan ta'adda. Kaga ko wannan makon sai da aka sace mai unguwar Dara aka nemi kuɗin fansa Ayrid dubu takwas."
Tun dai bayan shigowarsu Armad yake baza yanayin izzarsa yana ƙoƙarin jin izzar Babara. Kada dai a manta Babara shi ne kwamandan da Armad ya turo sashin Ikwatora domin ya kula da abubuwan da suke faruwa. A yayin da Iliyasisi yaje ƙarƙashin ƙasa domin kula da abubuwan da Bihanzin yake aikatawa. Armad yana da yaƙinin idan da zai samu Babara da lallai zai ji dukkan abinda ya faru.
Haka suka ci gaba da tafiya Armad yana yiwa mutumin tambayoyi, shi kuma yana bashi amsa. Wani abu daya basu mamaki shi ne har yanzu Nusi ita ce sarauniya a sashi na shida. Wazirinta wanda ta bari shi ne yake mulki a maimakonta. Sarki Ƙaraiƙisu yayi ƙoƙarin cire Nusi daga muƙaminta ya naɗa wani amma alkalan baƙar guguwa suka ƙeƙasa ƙasa suka ce basu san kowa ba sai ita domin ita baƙar guguwa ta zaɓa kuma baza a sake wani zaɓen ba sai nan da shekaru hamsin da takwas. Dole ƙaraiƙisu ya haƙura ya rabu da Nusi. Wani abu daya ƙara bawa Armad mamaki shi ne abinda ya faru da mayaƙan Ikenga daya bari a sashin ikwatora. A cewar Biyri, tuni sarki Ƙaraiƙisu ya kama duk wani mai goyon bayan Ikenga ya ɗaure.
Abinda Armad bai gane ba shi ne shin da gaske an samu saɓani tsakanin Ikenga da Ƙaraiƙisu, ko kuma kawai shiri ne suke yi domin su yaudari idon duniya? Domin dai yasan kaɗan daga cikin aikin Ikenga yayi haka. Lokaci na ƙarshe daya ga Ikenga suna tare da Ƙaraiƙisu. Armad yayi amfani da fasahar Wilbafosiyan Siwod Dans yayi cilli dashi. Bai san ina ba kuma bai san mai ya faru bayan nan ba. Babban abinda yafi damun Armad shi ne iyalinsa. Har yanzu bai ga gilmawar Nostaljiya ba, kuma bai ji wani ya ambaci sunanta ba. Kai acikin kwamandunsa Nusi kaɗai yaji labari.
Banda ƙaraiƙisu, a lokacin Ikenga yana tare da Kana da Dadára da kuma Ginad Ururu. Bayan ɓacewarsa wannan mutane zasu iya komawa daular denizawa suyi ƙoƙarin cutar da kwamandunsa daya bari. To amma Nusi suna tare da Nostaljiya, da Cokali, da Lamarudu, da Inara. Tunda ya ganta yasan ragowar ma suna lafiya saboda haka ya ɗan kwantar da hankalinsa. Bai ga abinda zai raba Nusi da ragowar kwamandun ba. Ko dai suna tare, ko kuma tasan inda suke. Duk yadda ake ciki idan sun haɗu da Nusi zaiji labari.
A dai-dai wannan lokaci suka iso ƙofar garin da zasu je domin shiga Eycigan. Saɓanin garin da suka baro, tsattsauran tsaro ne a ƙofar. Duk wanda zai shiga sai anyi masa tambayoyi kuma an karbi katin shaida na ikwatora. Watakila waɗanda suka shigo sashin ba tare da ka'ida ba sune suka jawo aka tsaurara tsaron.
Daga ɓangaren hagu an tara mutane wanda basu da sheda. Yawansu yakai ɗari da doriya. Daga ɓangaren dama kuma masu shaida ne wanda ake bari su wuce kai tsaye. Waɗanda kuwa basu da shaida an bar su a rana babu wani alamun za'a kula su.
"Anan zaku sauka," inji Biyri. "Ba'a barin keken doki ya shiga sai ya biya ninki. Da fatan kuna da shaidar shiga?"
Armad ya girgiza kai. "Bamu da ita."
"Kai... to ai kuwa zaiyi wuya ku shiga. To amma ku tsaya mu gani. Akwai wanda na sani acikin ma'aikatan."
"Mun gode," inji Armad. "Amma kada ka damu muna da hanyar da zamu bi."
Tuni Armad ya gama janyo izza domin yin amfani da Aiban'shisu.
"Ka tabbata?" Inji Biyri. "Kace sashi na farko kuke son zuwa, ko? To idan ka tada hayaniya anan wajen kai tsaye ma'aikatan zasu kira sashi na farko, su rufe duk ƙofofin Eycigan dake cikin garin. Su kan ɗauki kwana biyu zuwa uku kafin a turo mayaƙa daga can su zo suyi bincike sannan a ga yiwuwar buɗewa. Kasan tunda masu bakaken idanuwa suka kawo hari aka koma kula da ƙofofin daga sashi na farko maimakon a kowanne gari da ƙofar take."
Armad ya kalli Zaikid da Shata yana neman shawara. Idan haka ne to kuwa akwai damuwa. Tabbas ko shakka babu idan Armad ya kirawo Aiban'shisu zai iya ɗauke su duk su ukun zuwa cikin garin ba tare da kowa ya kula ba. Duk da zai haɗa da keken dokin da ƙasar da suke kai amma wannan ba matsala bane. Inda matsalar take shi ne akwai alamun za'ai tashin hankali a wajen bada jimawa ba. Mutanen da aka ware gefe aka hana shiga sun fara hayaniya. Tun daga inda Armad yake yana ganin wasu Sammai acikinsu suna guna-guni.
"Mu jira mu ga mai zai faru," inji Zaikid. "Shata, ya kake gani?"
Shata ya gyaɗa kai. "Watakila jiran ya haska mana abinda yake faruwa na zahiri a sashin ikwatora saɓanin abinda jaridu suke wallafawa. To amma kuma muna kan lokaci. Ina ganin kada mu wuce minti talatin anan."
Suka amince da hakan saboda haka suka koma can gefe suna kallo. Ai kuwa ba jimawa wata mata daga cikin wanda aka ware gefe tayi tsalle sama, hannu a dunkule, takai duka kan ma'aikatan. Wani faifan iska ya fice daga hannunta yayi kan ma'aikatan. Mutanen dake layi suka dare suna ihu. Su kuwa ma'aikatan kamar daman sunyi tsammanin hakan kawai makamai suka zare. Wasu gungun mutun biyar daga cikinsu suka shigo gaba suka ɗaga hannu sama a tare suna kiran ɗalasimai. Wata bango na koren haske ya bayyana a gabansu ya tare harin da matar ta aiko musu. Ragowar ma'aikatan suka fara aiko da nasu sakon. Abin mamaki duk harin ma'aikatan sai kaga ya shige ta cikin bangon koren haske ya sauka akan ɗaya ɓangaren. Su kuwa koda sun aiko da nasu harin sai kaga ya daki koren hasken ya zube a kasa.
Banda matar data fara, wasu maza guda goma suka haɗa hannu waje guda suka samar da bulalar wuta wadda ta daki koren bangon. Bangon yayi girgiza kamar zai faɗi amma ya shanye. Kafin su ƙara aika wani harin wani mutun-mutumi na ruwa ya sauka akansu. Ƙarfin ruwan ya kashe bulalar wutar sannan yayi jifa dasu gefe guda. Wasu daga cikinsu suka ƙara fitowa gaba domin ƙara kai wani harin.
A lokacin Armad ya gane dukkan wanda aka hana shigar bakinsu ɗaya. A tare suke kuma dama sun shirya abinda zasu yi. Wato maganar Shata ce - ganin abinda zai faru zai ƙara bayyana musu halin da sashin ikwatora ke ciki.
"Ƴan-tawaye ne," inji Biyri. "Naji ance Ikenga suke yiwa aiki. Wai san an saki mutanensa da aka kama."
"Ikenga?" Inji Armad, rai a ɓace.
"Eh, kasan yazo da mayaƙansa tun asalin sanda suka haɗa kai da babban sarki Ƙaraiƙisu, duk da wasu suna ganin akwai wanda suka zo daga baya, bayan masu bakaken idanu sun zo. Wasu ma suna ganin daga kurkukun bango suke."
Ah, idan Armad zai iya tunawa da daɗewa Ikenga yake tara mayaƙa a kurkukun bango. Har wata doguwar gada suka gina acikin kurkukun suna ƙoƙarin hawa sama. Armad bai san yadda ta ƙarke ba amma tabbas sama da rabin fursunonin suna tare da Ikenga. Musamman bayan da ya nuna ikonsa na shiga da fita daga kurkukun cikin sauki. Zata iya yiwuwa wannan mayaƙan daya ɓoye a kurkukun bango saboda shirin kota-kwana sune suke shigowa suna tada hankali a sashin ikwatora.
Armad ya juya wajen Zaikid. "Kace kana tunanin Ƙaraiƙisu ya tafi yaƙin nan?"
"Eh.. akwai yiwuwar hakan," inji Zaikid. "Ko kana ganin mutanen Ikenga suna so suyi amfani da wannan damar wajen tashin hankali a ikwatora ne?"
Armad ya gyaɗa kai. "Haka nake tunani. Amma Shata mai kake gani?"
"Tabbas akwai yiwuwar hakan," inji Shata. "Amma dole suna buƙatar Ikenga kafin suyi nasara. Daga abinda na sani akan ikwatora wannan alkalan da mutane suke rainawa sune sashin. Idan sukai magana hatta ƙaraiƙisu baya haurewa."
Alkalan ikwatora suna ƙarfi. Hasalima acikin baƙar guguwa aka san su. Akan tsibirin da baƙar guguwar take anan suke rayuwa. Babu wanda yasan asalinsu ko kuma alaƙarsu da baƙar guguwar. Kai babu wanda yasan yadda aka naɗa su ma. Amma tabbas sune suke juya tsarin mulkin sashin. Wasu suna ganin duk wani zaɓe da sa-hannun su aciki. Hakan ne a baya masu neman takara sukai ƙoƙarin basu cin-hanci ta hanyar zama abokansu amma hakan bai haifarwa da ƴan-takarar ɗa mai ido ba. Ko ma dai yaya ake ciki, baza kai zancen ƙarfin iko a sashin ikwatora ba sai ka saka wannan alkalai.
"Bana jin Ikenga yana sashin ikwatora," inji Armad. "Bana jin yanayin izzarsa. Wanda zata iya yiwuwa ɓoye shi yayi, amma kuma akwai yiwuwar har yanzu bai dawo daga inda na tura shi ba. Watakila sai nan da sati guda zai bayyana."
Nan take suka shiga tattaunawa akan abubuwan da zasu iya faruwa bayan Armad yayi amfani da Wilbafosiyan Siwod Dans. Zata iya yiwuwa Ikenga a sati guda bayan ranar ya bayyana, ko kuma sati biyu, ko sati uku... Ko gaba da haka. Za kuma ta iya yiwuwa wata guda ne, dai-dai dana Armad. Abinda zai faru ya danganta da lokacin da Ikenga zai dawo. Wato fasahar ta samar da wasu sabbin hanyoyin masu rikitarwa. Yanzu ace Ikenga bazai bayyana ba sai shekara guda bayan wannan rana, kaga duk wata matsala ta Armad ta kau, baya buƙatar yayi tunanin yadda zaiyi faɗa da Ikenga da Bihanzin a lokaci guda. A nutse zai gama da Bihanzin sannan ya juyo kan Ikenga. To amma matsalar Armad bashi da tabbas ina ya tura Ikenga, kuma yaushe zai dawo. Wai shin idan Ikenga ya dawo haka zai dawo lafiya kau babu wata lalura a tare dashi? Kusan duk wanda aka jefa acikin lokaci yakan samu matsala da sarrafa izzarsa. Kaga Armad fasaharsa ce saboda haka bashi da matsala, amma Ikenga dole akai masa. Armad yana ganin koda Ikenga ya dawo bazai rasa wata lalura ba. Kuma koda zai wartsake sai a hankali.
A lokacin Zaikid ya ƙara duba Armad ya tabbatar babu wata babbar matsala da fasahar take jawo masa idan yayi amfani da ita. A kowanne lokaci daya bayyana yana rasa ainihin shekarunsa na haihuwa biyar zuwa goma. Da ace ba daga gidan Wilbafos ya fito ba da hakan sai ya jawo matsala. Amma Armad bana yau ba ne, yana bada izza ga wasu, balle kuma kansa. Bayan dogon bincike Zaikid ya bayyana cewa Armad ya fishi iya amfani da fasahar Wilbafosiyan Siwod Dans. Wato kamar hatsari ne ya faru wanda ya juye izuwa alkhairi. Rashin kwarewar Armad wajen sarrafa takobin sai yasa yake juya ɗalasimin fasahar. Amma kuma hakan sai ya samar da wani abu mai ban tsoro. Wato Armad zai iya guduwa idan faɗa yayi zafi zuwa mako guda ko kuma gaba da haka. Haka nan kuma zai iya tura abokin gabarsa idan yana kusa dashi.
Sai da suka shafe mintuna suna magana akan fasahar sannan suka juyo kan abinda ke gabansu.
"Ina ganin duk ba wannan ce tambayar da yafi kamata mu maida hankali akai ba," inji Zaikid. "Waye zai fi amfana da tashin hankali a ikwatora? Mu ne, saboda da Ƙaraiƙisu da Ikenga duk maƙiyan mu ne, su kashe kansu mana. Abinda kawai zamu yi shi ne muyi ƙoƙari muga yadda abin zai taimake mu."
"Shi yasa na turo Babara," inji Armad. "Tun farko nayi tunanin idan na fara yaƙar Ikenga to Bihanzin zaiyi amfani da damar ya yaƙe ni ta baya. Ko kuma idan na fara da Bihanzin, Ikenga ya shigo min ta baya. Haka idan na fara da Ururu, da Bihanzin da Ikenga zasu iya kawo min cikas. Ko kuma su jira ƙarfi na ya ƙare kafin su ƙarasa ni. Hakan yasa nayi ƙoƙarin tashin Hidaya ta hanyar amfani da jikin Ayubu da kuma fasahar denizawa domin ta zama kariya a gare ni a yayin yaƙin, to amma kuma hakan bata samu ba. Ko a yanzu akwai yiwuwar muna cikin yaƙi da Ururu wani daga cikinsu ya kawo mana hari ta baya. Saboda kada hakan ta faru na tura Iliyasis ƙarƙashin ƙasa ya kula da Bihanzin, na tura Babara ikwatora domin ya kula da Ikenga. Amma kaga yaƙi ya canja lissafi ya kwace. Tun daga sanda na turo su babu wanda na ƙara ji. Dama ta cikin littafin marubutan farko na Cokali mukai zasu ringa bani rahoton abin da yake faruwa. Cokali ya bawa kowa acikinsu kwafi na littafin da kuma alkalami. Duk abinda suka rubuta zai gani sai ya gayawa Armad. Wannan shi ne lissafin tun farko. Amma rabuwa dasu Cokali da nayi zata iya yiwuwa sun tura saƙon ban gani ba."
"Hakane, watakila sun tura. Kuma kayi dabara. Amma, Armad, shi tashin hankali ai haɗa shi ake ba jira ake ya faru ba. Bari ka gani."
Babara ya shafa wani sinadari a fuskarsa ya canja kamanni kafin ya ɓace daga cikin keken dokin. Can Armad ya hango shi acikin masu faɗan. Zaikid yayi tsalle ya daki koren hasken da hannu. Tartsatsin walkiya yayi sama ya rufe ko'ina. Bayan ya lafa Zaikid yana kwance a ƙasa yana numfarfashi, shi kuwa bangon ya ɓace. Da sauri wasu suka shigo suka janye shi a yayinda wasu kuma sukai amfani da damar suka danna cikin ƙofar. Ance sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi. Ba jimawa suka ture ma'aikatan suka shiga ciki. Ta haka aka karya masu gadin, su Armad da Shata da keken dokinsu suka samu hanya suka shiga garin. Minti bakwai suka ɓata a bakin ƙofar.
Wani abu da yake burge Armad da ikwatora shi ne yawan fili da suke dashi. Kowanne gida da gindinsa yake zaune kuma baya jikin wani. Ko ta wane ɓangaren iska zaka sha.
Mutanen garin suna hango ayarinsu suka fara gudu. Masu shiga gida nayi, masu shiga daji nayi. Kai tsaye ƴan-tawayen suka wuce gidan dagaci. Su kuwa su Armad hanyar ƙofar Eycigan suka nufa. Suna kan hanya sai ga Zaikid nan ya bayyana acikin keken dokin. Ko kaɗan babu alamun ciwo ko gajiya a tare dashi. Kana gani kasan abinda yayi ɗazu na faduwa kawai shiri ne.
"Yanzu wane hali mutanen garin nan zasu shiga?" Inji Armad.
"Kai kada ka damu da wannan," inji Zaikid. "Mafi ƙarfin izza acikinsu Sammai ne. Kawai dai zasu ɗagawa hukuma hankali ne. Duk inda Ikenga yake zaiyi ƙoƙarin zuwa ya ribaci wannan damar maimakon kawo mana hari a yayin faɗan mu da Ururu. Idan ma ya dawo daga inda ka cilla shi kenan."
Armad ya fahimci abinda Zaikid yake ƙoƙarin yi amma bai kwanta masa a rai ba.
"Za'a cutar da wanda babu ruwansu," inji Armad. "Kada ku manta muna faɗa ne domin mu kare mara ƙarfi."
Zaikid da Shata suka kalli juna sannan suka kalli Armad cikin mamaki. Wai mai yake cewa ne?
"Wannan ai ba wani abu bane," inji Zaikid. "Kana tunanin akwai wani yaƙi da ake samun nasara babu zamba aciki? Idan kai bakai ba, to za'ai maka."
Armad ya girgiza kai. "A'a, tsarin shi ne taimakon bayi marasa ƙarfi da bawa mutane dama su zaɓi yadda suke so suyi rayuwarsu. Bazan fara bi gari-gari ina haddasa fitina ba kawai saboda ina so na samu nasara."
Zaikid da Shata sukai shiru suna kallonsa. Wai shi so yake yaci nasara ba tare da wani surkulle ba?
"A lokacin dana turo Babara na gaya masa," Armad yaci gaba da bayani. "Idan yaga rigima zata tashi tsakanin Ikenga da alkalan sashin to kada ya hana. Idan akwai yadda zaiyi ya taimakawa alkalan suci galaba akan Ikenga to yayi. Amma bance yayi irin abinda ku kayi yanzu ba."
"To meye bambancin?" Inji Shata.
"Akwai bambanci," inji Armad. "Ikenga maƙiyi ne kuma abokin yaƙi ne, saboda haka yaƙarsa ya halarta. Taimakon abokan gabarsa (wanda suka haɗa da alkalan wannan yanki da basa goyon bayansa) shi ma ya halarta. Amma haddasa fitina a gari saboda a samu tashin hankali da zai jawo hankalin Ikenga yazo ikwatora bai dace ba. Eh, hakan zai iya samar da abinda muke nema a ƙarshe, amma kuma mun kaucewa hanyar da muka ɗakko tun farko."
Armad yaja dogon numfashi. A kullum ƙoƙari yake kada ya kauce daga gaskiya - taimakon iyalan gidansa da kuma ragowar mutane. Zaka iya cewa a lokuta da dama Armad ya kaucewa wannan tsari musamman lokacin da ransa ya ɓaci akan kashe Hidaya, amma a kullum yana ƙoƙarin gayawa kansa gaskiya domin ya dawo kan tsari. Idan kuma yayi kuskure ya gyara.
Zaikid da Shata basu ce komai ba har suka isa inda zasu. Gida ne ƙatoto wanda za'a iya kira da ma'aikata. Ga ƙatuwar ƙofar shiga amma mutun ɗaya ne tak yake gadinta.
"Ka jira mu anan minti goma," Armad ya gayawa direba Biyri. "Idan bamu fito ba zuwa lokacin zaka iya tafiya."
Har sun juya zasu tafi Biyri ya fito da sauri ya bisu.
"Armad Wilbafos, a bani dama nayi mubaya'a." Ya zube a gaban Armad. "Tabbas ban taɓa jin ma'aboci izza kamar ka wanda ya damu da gama-garin mutane irin mu ba. Ina addu'a ka samu nasara akan duk abinda ka saka a gaba. Ina kuma addu'a ka samu nasara akan masu bakaken idanu da suke neman ka domin su cutar dakai."
Armad ya kama hannunsa ya ɗago shi. "Abinda ya kamata kowa yayi ne kawai. Amma nagode. Ina yi maka da iyalanka wasiyya da kada ku aminta da masu bakaken idanu. Duk abinda zasu kawo muku akwai zamba aciki da manufa."
Anan suka bar Biyri suka shiga cikin ƙofar. Mai gadin yayi ƙoƙarin hana su shiga amma yana haɗa ido da Armad ya fara karkarwa.
Suka shige ciki. Gaba ɗaya ma'aikata huɗu ne kacal acikin wajen. Duk ragowar sun tafi fadar dagaci domin hana ƴan-tawayen shiga. Suma Shata ya kada musu garaya sukai bacci. Hankali kwance suka shige har inda ƙofar da zata kai su sashi na farko take. Duk su ukun suka shiga ciki a tare. Yanayin juwa da hajijiya ya ɗebe su suka rufe ido. A lokacin da suka buɗe ido suka gansu a sashi na farko na ikwatora.
Armad ya yamutse fuska cikin mamaki. Duk lokutan daya shiga ƙofar Eycigan a baya a wata ƙofar yake samun kansa bawai a waje ba. Ya waiga gabansa da bayansa amma bai ga ƙofa ba. A ka'ida a yanzu daya shiga ta ƙofa to zai tsinci kansa acikin wata ƙofar amma kuma a inda zashi - wato sashi na farko. Abinda ya ɗaurewa Armad kai shi ne ya ganshi a filin ALLAH ta'ala. Babu gida gaba, babu gida baya.
Sai dai bashi kaɗai ne acikin mamakin ba, Shata da Zaikid duk dube-dube suke yi.
"Wai... ina muke ne?" Armad ya tambaya.
Shata da Zaikid sukai shiru suna tunani. Bayan ɗan lokaci Zaikid ya guntsi ƙasa a hannunsa ya shanshana.
"Ina jin fa a tsakiyar kurkukun bango muke," inji Zaikid.
"Kurkukun bango?!" Inji Shata da Armad a tare.
Zaikid ya gyaɗa kai.
Nan take suka fara dube-dube. Saboda dusar ƙanƙara da duhu irin na kurkukun basa iya hangen nesa balle su iya hango bango. Kuma a inda suke babu wani mutum a kusa balle su tambaya. Rai a ɓace, Armad ya kirawo Aiban'shisu yayi dama inda ya bayyana a bakin bango. Bai tantance bangon kudu ko kuma na arewa bane saboda haka ya ƙara kiran ɗalasimin ya bayyana a ɗaya bangon. Duk faɗin ƙasa bakwai, kurkukun bango da sashin ikwatora su kaɗai ne wajajen da bango zaiyi maka iyaka ta ɓangaren dama da hauni. Misali, idan kana sashin arewa na doron ƙasa to a ɓangaren kudu kaɗai zaka ga bango, kamar yadda idan kana sashin kudu to a ɓangaren arewa kaɗai zaka ga bango. To amma kurkukun bango da sashin ikwatora suna tsakiyar bango, ta kudu da arewa. Tunda babu alamun gida ko kuma wata alƙarya yasan baya sashin ikwatora. Saboda haka yana kurkukun bango.
Ya ƙara kiran Aiban'shisu ya dawo inda su Zaikid suke.
"Muna kurkukun," inji Armad. "To amma mai ya faru? Ta yaya muka dawo nan? Ji nake ƙofar da muka shiga ta sashi na farko ce."
"Ko dai ba ƙofar muka shiga ba?" Inji Zaikid.
Shata ya girgiza kai. "Tabbas ƙofar muka shiga. Sai dai idan sunan suka rubuta ba dai-dai ba."
"To ai koda ba ƙofar muka shiga ba ya kamata ace acikin wata ƙofar muka bayyana ba'a nan ba," inji Armad. "Ba haka tsarin Eycigan yake ba."
Nan fa suka shiga tunani. Ta yaya zasu shiga ta cikin ƙofa amma su bayyana a daji? Kowa ya kawo shawararsa amma daga ƙarshe suka yanke shawarar tabbas akwai wani sihiri da yayi aiki a kansu. Kodai wanda suke kula da ƙofar daga sashi na farko sun ga zuwansu sun canjawa ƙofar hanya, ko kuma da gaske ba ƙofar daya kamata su shiga suka shiga ba.
Babu musu suka dawo sashin ikwatora. Maimakon su hau keken doki su ƙara ɓata lokaci sai suka kirawo Kaban'shisu. Ba jimawa suka iso inda zasu. Abu na farko da suka tarar shi ne wuta. Duk inda ka kalla a garin wuta ce ke ci. Ƴan-tawayen da Zaikid ya taimakawa ɗazu sun bunkawa garin wuta. Armad ya kalli Zaikid, kallo mai cike da ma'ana. A ransa yana cewa 'ka gani'.
Zaikid bai ce komai ba har suka isa ƙofar Eycigan. Suka duba suka tabbatar ƙofar daya dace suka shiga, ba kuskure aka samu ba domin kuwa kowacce ƙofa da sunanta. Sannan suka ƙara shiga ƙofar. Abin mamaki sai gashi sun ƙara bayyana a kurkukun bango.
Cikin haushi suka dawo suka ƙara komawa. A wannan karan sai suka shiga wata ƙofar da zata kai su sashi na biyar. Suna so su gani ko sashi na farko ne kawai yake da matsala.
Suna shiga suka buɗe ido suka tsinci kansu a kurkukun bango. Wato duk ƙofofin haka suke. Dama Biyri ya gaya musu an canja tsari kuma yanzu daga sashi na farko ake kula da ƙofar.
Duk da haka sai da suka ƙara gwadawa sannan suka samu nutsuwa babu hanya - shiga ƙofar Eycigan bazai yiwu ba. A yayin da suke ƙoƙarin samo bakin zaren, Armad cikin garin ya shiga ya tarwatsa ƴan-tawayen. Duk wata wuta da suka tayar, ya kashe. Duk wani gida da suka kona, ya gina. Duk wani ciwo da suka ji, ya warkar. Sannan ya biya dagacin garin diya. Mutane suka ringa kallonsa suna mamakin daga ina yake.
Yana dawowa ya tarar Shata da Zaikid suna ƙoƙarin yin tsalle tun daga sashi na shida har zuwa sashi na biyar da hanyar fasahohi irin su Kaban'shisu da Aiban'shisu, amma abin yaci tura. Suna iya yin tsalle mai nisa har ma su ɓace a daina ganin su, amma kuma kash, nisan da yake tsakanin doron ƙasa da doron ƙasa yafi gaban misali. Hatta Aiban'shisu baza ta iya ɗaukar mutun tun daga wannan doron ƙasa ta kai shi wani ba. Armad ya daɗe da gwadawa. Babu wata fasaha a duk faɗin duniya (ta sauri) wadda zata iya yin hakan. Indai kana so to dole kayi amfani da ƙofar Eycigan, ko kuma ka hau ruwa. Armad yana ganin banda nisa akwai sihiri a jikin doron ƙasashen wanda yake hana hakan.
"Yanzu meye abin yi?" Inji Armad. "Babu ƙofar Eycigan, kuma baza mu iya hawa da kan mu ba, yaya zamu yi, lokaci yana ƙurewa?"
"Sai dai mu hau bango," inji Zaikid.
Shata ya juya da sauri ya kalli Zaikid. "Bango, farfesa?"
"To yaya zamu yi?" Inji Zaikid. "Bamu san takamaimai yawan awannin da suka rage kafin su yankewa Fatima hukunci ba. Dole muyi amfani da abinda muke dashi."
Zaikid ya fara kai-komo yana kallon ƙasa. Yafi kowa sanin sharrin ƴan-ruwa. Amma kuma basu da wata hanya data rage. Baza su iya hawa da kansu ba, kuma baza su iya amfani da ƙofar Eycigan ba. Dama abubuwa uku ne suka sa suka zaɓi subi ta ƙofar Eycigan. Na farko, Armad yana so yayi amfani da yanayin izzarsa ya nemo Babara. Na biyu, suna so su ga halin da sashin ikwatora yake ciki. Na uku, basa son suyi faɗa da ƴan-ruwa.
Wato saboda yawan ƴan-ruwa da aljanun dabbobin dake kan bangon shi ne yasa babu wani tsaro da ikwatora suke sawa akan ruwan. Duk wanda yake ganin zai iya ya hau.
"Zan iya ɗaurawa jirgin Kaban'Zishu," inji Armad. "Hakan zai ƙara mana sauri sama da lissafi. Tafiyar shekara zamu yi ta a ƴan dakiku. Kuna ganin duk da haka sai ƴan-ruwan sun hana mu wucewa?"
"Zai rage yawan hare-haren da suke kawo mana amma bazai hana ba," inji Zaikid. "Amma mu gwada. Kawai dai ko mai zai faru kada ku kashe su. Idan son samu ne kada ku taɓa su, koda sun zage ku."
Suka shiga shirye-shirye akan yadda zasu ɓullowa abin. Bayan minti biyar suka kammala. Zaikid ya ɗora musu kwale-kwale akan ruwa suka hau suka nufi sama. Daga nan zasu isa sashi na biyar, sannan na huɗu, sannan na uku.... a haka har zuwa na ɗaya wanda daga nan zasu shiga doron ƙasa na biyu. Babu wani tsaro da zasu fuskanta akan hanya amma akwai yiwuwar su tarar da ƴan-ruwa da iyalansu.
Haɗuwar jirgin da Kaban'Zishu ya ƙarawa jirgin sauri na gaban misali. A lissafin Armad ƴan awanni zasu ishe su suje inda suke buƙata. Idan mai sauraro bai manta ba wannan ita ce fasahar da Armad yayi amfani da ita a lokacin da suke zuwa duniyar aljanu neman K'narbig babbar izza.
Cikin rabin sa'a sun haura sashi na biyar sun nufi sashi na huɗu. Duk tsahon wannan lokaci aljanun dabbobin basu ankare dasu ba. Sai da suka fara hango sashi na huɗu sannan kifaye suka fara taruwa a ƙasan jirgin. Armad ya kunna walkiya a ƙasan jirgin. Duk kifin daya matso sai kaga ya juya da gudu. Wanda kuwa sukai taurin kai su ƙone.
Suka ci gaba da baza izzarsu domin su firgita kifayen dake nesa kada su matso. Hakan ya basu damar tsallakewa har zuwa sashi na huɗu. Saboda tsananin gudu da jirgin yake yi basa ganin komai sai hazo. Koda sun matso saitin doron ƙasa basa ganin komai, sai dai kawai yanayin hazon da suke gani ya juye izuwa ruwan ƙasa.
Bayan minti talatin sai suka fara hango sashi na uku. Amma kafin su ƙarasa wani bango ya bayyana a gabansu. Tun daga nesa suke ƙoƙarin kauce masa amma har suka iso hakan bata samu ba. Suna zuwa suka daki tsakiyar bangon. Maimakon su ji tauri sai suka ji laushi. Suna ƙoƙarin gane mai suka daka sai ruwan dake ƙasansa ya fara hatsaniya yana juyawa yana ƙoƙarin kifar dasu. Wani rami ya bayyana a tsakiyar bangon ya fara jan ruwa. A lokacin suka fuskanci ba bango bane; katon kifi ne samfurin ƴan-ruwa. Ramin kuma da suka gani yana jan ruwa bakin kifin ne. Armad ya zare takobi yayi sama. Cikin kwarewa da daɗewa anayi ya saukarwa da kifin Dorawa Abada. Kifin ya dare gida da biyu, koren jini yayi feshi sama. Kafin jinin ya sauka ƙasa ya zubo musu Zaikid ya saka wani mayafin tsafi ya tare. Duk inda jinin ya taɓa ruwan sai kaga ya kama da hayaki. Suna cikin haka kifin ya harbo musu ƙasusuwan dake ƙirjinsa. Armad ya haɗe rai yana kallon ikon ALLAH. Ga abu a tsage gida biyu, amma kuma duk da haka faɗa yake kamar ma babu abinda ya faru. Kowanne ɓangare daya rabe ya haɗe ya zama kifi mai zaman kansa. Jirginsu yana ƙoƙarin wucewa ta tsakiyar inda Armad ya yanka amma kifayen biyu suna ƙoƙarin haɗe su. Ga wani kuka mara daɗin ji da kifayen suke yi.
"Zaren Babbar Mutu...!"
Zaikid yayi sauri ya riƙe Armad. "A'a, kada ka kai su cikin duniyar ka. Ko ka manta muna da ajiya aciki ne?"
Armad ya tuno da Haruta saboda haka ya fasa kiran fasahar ya kirawo wata.
"Saif-Al-Barzak!"
Kowanne kifi ya rabe gida barkatai. Jini yana ƙoƙarin yi musu wanka Zaikid ya bude mayafinsa ya tare. A lokacin Saif-Al-Barzak ta bayyana.
Shata ya ƙara kallon Saif-Al-Barzak. Siffar ta siffar takobi. Abinda kawai yazo ransa shi ne baiji sanda tazo ba. Hasalima sai bayan ta gama aiki ya ganta. Saboda haka da ace shi yazo kashewa da tuni yana lahira. Lallai wannan takobi yana da girman al'amari. Daɗin daɗawa Armad bashi da buƙatar ya riƙe ta da hannunsa.
Yana cikin tunani kowace guduwa da Saif-Al-Barzak ta yanka ta juye izuwa kifi mai zaman kansa.
Shata ya fara kida a ƙoƙarinsa na saka kifayen baccin dole. Armad ya kira Saif-Al-Barzak suka ja baya tare da Zaikid suka zubawa Shata ido. Sara baya aiki. Kawai ƙarawa kifayen yawa yake yi. Saboda haka kiɗan Shata shi suke buƙata.
Bayan minti guda sarewa tana tashi suka fuskanci aikin banza Shata yake yi. Kiɗan baya aiki akan kifayen. Watakila basu da kunne.
Armad ya ɗora hannunsa akan jirgin ya ƙara musu gudu. Kifayen suka tusa su da gudu. Daga nesa idan ka hango abin zaka ga jirgin su Armad yana gudu, Armad ya ɗora hannunsa akan jirgin yana zuba masa izza, Zaikid da Shata kuma suna ƙoƙarin tare kifayen dake binsu da gudu. Har yanzu Armad bai yadda kifaye bane. Wane irin kifi ne baya mutuwa?
Abin haushin kamar tsokano kifayen suke yi. Wasu kifayen na daban sun fara bayyana suna zarya suna kawo musu hari. Wai duk gudun Kaban'Zishu amma kifayen sun ƙure musu wuta.
Bayan ɗan lokaci Armad ya ajiye duk wani tunanin kada ya ɓatawa ƴan-ruwan rai ya zage ya fara gyara musu hanya. Ya samar da mutun-mutumi biyu. Kowanne ya riƙe kusurwa ɗaya ta jirgin. Shata da Zaikid suka kama kusurwa ɗai-ɗai. Shi kuma Armad yaci gaba da ƙarawa jirgin gudu.
Abu kamar wasa ba sai ƴan-ruwan gasken suka fara fitowa ba. Kwatsam wani ya bayyana a gabansu. Abin haushi wai ƙoƙarin kifar dasu. Armad yasa ƙafa ya doke shi. Wasu ƴan-ruwan guda biyu suka ƙara bayyana. Tun Armad yana yi musu kara, baya so ya kashe su, har ya daina. Ya kirawo ɗaya daga cikin mutun-mutuminsa yasa ya fara tsargesu.
Mutun-mutumi ya kai sara da takobin Wilbafos amma kawai sai ɗan-ruwan yasa hannu ya tare. Armad yayi tunanin zai ga hannu ya tsinke amma kawai sai yaga ɗan yanka a jikin hannun. Kamar wanda aka shafawa wuƙa. A lokacin ya tuna da abinda da Zaikid ya gaya masa akan fatar ƴan-ruwan da gwarinta. Ance abubuwan da suke iya yanka ta basu da yawa.
Faɗa ya dawo sabo. A hankali, a hankali ƴan-ruwan suka fara ƙaruwa. Sai da suka kai su biyar. Kwatsam sai ga wani acikin jirgin. Kafin kowa ya ankare ya cafi hannun Shata sun fara kiki-kaka. Ana haka wani ya bayyana a ƙasan jirgin ya fara ƙoƙarin kifar dasu.
Gashi har yanzu ko ɗaya basu kashe ba. Armad ya juya ya kalli Zaikid wanda ya girgiza masa kai.
"To, farfesa, idan banyi amfani da Negrinki ba, ta yaya kake so mu gama dasu?"
"A'a, Armad, muna da ajiya aciki kuma zasu ɓata maka duniya. Ka gwada Saif-Al-Barzak mana."
Dukkansu suna magana da ƙarfi saboda hatsaniyar dake faruwa.
Saif-Al-Barzak ta bayyana. A lokacin ta samu hannun wanda yake faɗa da Shata ta tsinke shi. Amma kafin hannun yaje ƙasa wani hannun ya bayyana. Su goma suka rufarwa Saif-Al-Barzak a yayinda wasu goman suka shiga cikin jirgin. Ga wasu sun kewaye su. Tuni Armad ya daina ƙoƙarin ƙarawa jirgin ƙarfi, ya miƙe ya shiga faɗan.
Ba jimawa suka tsaya cak. Basa gaba, basa baya. Kawai fafatawa ake yi. A zahiri sun fi ƙarfin abubuwan, amma kuma sun fisu yawa. Ga kuma rashin jin sara. Daka sare su da sun haɗe sun dawo da abinda ka sare. Babu wani abu da yake yi musu illa.
Minti biyar da fara faɗan suka kifar da jirgin. Dolen su Armad suka tashi sama kan iska. Zaka yi tunanin sun sha tunda ƴan-ruwan basu da fiffike, ko? Amma ina, nan take suka bisu sama aka ci gaba da fafatawa kamar masu fiffike.
A wani lokaci bayan kowa yaji jiki, Armad ya kirawo Negrinkinsa ya fara aika wannan halittu cikin duniyarsa ba tare da ya nemi shawarar Zaikid ba. Shi kansa Zaikid kansa ya ɗau zafi ko kula baiyi ba. Sai da suka ga sun fara raguwa sannan suka lura da abinda ke faruwa. Aikin gama ya riga ya gama. Tuni Armad ya aike da guda biyar ciki. Kafin minti guda ya ƙara aikewa da wasu biyar ɗin. Koda ƴan-ruwan suka fuskanci shi ne matsalarsu sai suka rabu da su Zaikid suka rufar masa. Dama haka yake so. A lokacin ya samu yayi musu ɗauka ɗaya. Lokaci guda ya jefa goma ciki. Kafin kace kwabo babu kowa a wajen sai su kaɗai. Yau ƴan-ruwa sun gamu da babbar fasaha irin wadda ta shallake tunaninsu.
Zaikid da Shata suka ɗaga jirginsu suka dawo dashi kan hanya. Armad ya kirawo Kaban'Zishu aka ci gaba da tafiya.
Ƴan-ruwan basu hakura ba, amma kuma a banza. Duk wanda ya matso kusa sai dai kaga ya ɓace babu shi babu alamun sa. Kafin wani lokaci Armad ya manta adadin nawa ya jefa ciki. Daga ƙarshe dai ƴan-ruwan suka yadda anfi ƙarfinsu suka koma gefe. Suna binsu da gudu suna jira ko zasu samu wata damar su kawo musu hari.
A haka dai su Armad suka iso sashi na farko na ikwatora. Har yanzu Zaikid bai ce komai ba akan tura ƴan-ruwan cikin duniyar Negrinki da Armad yayi, shi ma Armad bai tayar da maganar ba. Shi kuwa Shata godewa Armad yayi akan ceto su da yayi.
Suna zuwa bakin gaɓa Armad ya buɗe ƙofar duniyarsa yayi ƙoƙarin fito da abubuwan daya cilla ciki. Abin mamaki babu abinda ya fito. Ya ƙarawa ƙofar daya buɗe girma ko zasu fito amma a banza. Ya ɗan leƙa ciki ko zai hangosu amma bai ga komai ba. Aƙalla yasan ya jefa hamsin zuwa ɗari ciki saboda haka babu zancen ace basa ciki ko kuma duk sun fice. Bari kawai ya shiga ya duba da kansa. Ya yunkura zai faɗa ciki.
Zaikid yayi sauri ya riƙe hannunsa yana girgiza kai. "A'a, kada ka shiga."
Armad ya haɗe gira cikin mamaki. Wane dalili ne zai saka kakan nasa ya hana shi shiga duniyar.
Bayan ɗan tunani ya haƙura ya koma ya zauna. Zaikid ya koma gefe ya zauna ya tankwashe ƙafa. Idonsa a rufe bai kula da wasu gungun ma'aikatan tsaro sanye da fararen kaya ba. Shata da Armad suna hango ma'aikatan amma babu wanda yayi ƙoƙarin yin wani abu acikinsu. A nasu ɓangaren ma'aikatan kawai tsayawa sukai, baki a wangame, suna kallonsu.
Su Armad suka tako har kan ƙasa inda ma'aikatan suke. Shugaban ma'aikatan yayi ta maza ya tsaya a gabansu.
"Ta ina kuka biyo?" Ya tambaya.
Shata ya nuna masa bangon ruwan da ɗan'yatsa.
Comments
Post a Comment