Skip to main content

BABI NA 274: Karkashin kasa

 A yayinda Iliyasisi, Nostaljiya, Cokali da Babara suke rangadi a bakin garin Jekis, su kuma su Nazara da Nusi da Lamarudu da Inara suke rangadi cikin garin Faideba na sarki Hanibal, shi kuwa sarkin yaƙi Ayubu na tsaye a wani daji dake doron ƙasa ta huɗu. Ramika ne masu zurfin gaske iyakacin ganin ka. Kowanne rami na sheƙi kamar yau aka gina shi. Wannan rami ka sun shige ƙarƙashin ƙasa kai tsaye zuwa duniyar ƙarƙashin ƙasa. 


Mutane irinsu Bihanzin da Ikenga wanda suka mallaki taswirar duniyar ƙarƙashin ƙasa basu da matsala wajen shiga ramikan, amma Armad bashi da wannan taswira. Hanya ɗaya da zai iya shiga daular denizawa ta ƙarƙashin ƙasa ita ce idan an gaiyace shi. Idan denizawa sun bashi goron gayyata, kamar yadda sukai a baya lokacin gasar Jinzidal. Sai dai kuma kash, a wannan lokaci Ayubu ba gayyatar sa akai ba. Hasalima shi manzo ne daga Armad wanda yazo domin dakatarda cinikin bayi. 


A tare da Ayubu akwai sadaukai ma'abota izza guda dubu ɗaya. Dukkaninsu zuri'ar Wilbafos ne wanda tunda aka haifesu suke tsare a kurkukun Bango. Hakan na nuna cewa kowa acikinsu yana iya sarrafa izza. Sannan kuma ƙarfin alaƙar su da zaren izzar Armad yafi na sauran gama-garin mutane. Ɗan taƙaitaccen misali shi ne suna iya ganin zaren dara-dara, harma su iya kama shi suyi lilo akai. Babu wanda yasan hanyar da Ayubu yabi ya fiddo da duk mutanensa dake cikin kurkukun Bango, amma a tsaye a wajen ƴan zuri'ar Wilbafos ne wanda suka fito ɗaukar fansar abinda akai musu da abinda akai wa iyayensu da kakanninsu. 


A gaban Ayubu masu tsaron ramikan ne. Yawansu yakai dubu uku, suna sanye da tufafin yunifom na denizawa: shuɗiyar rigar da baƙin wando. Sai dai kuma kaf ɗinsu a kwance suke ƙasa a sume. Izzarsu bata kai su tsaya a gaban sarkin yaƙi, limamin izza ba.   


Cikin kwanciyar hankali da yarda dakai Ayubu yai tsalle ya faɗa cikin rami mafi kusa dashi. Sauran Wilbafos dake bayansa suka biyo shi. Kowannen su riƙe da zare guda na izza wanda tuni Ayubu ya saita a kan hanyar zuwa ƙarƙashin ƙasa, daular denizawa. 


Idan mai karatu bai manta ba duniyar ƙarkashin ƙasa nada birane da dama. Da yawa daga cikin wannan birane an manta su a tarihi, wasun su kuma irin garin su Nusi ne wato Shadeniza wanda aka killace aka ɓoye ga idanun bayi. A shekarun baya anga yadda Ikenga ya ziyarci wannan duniya ta ƙarƙashin ya karɓi saƙo a wajen Daddara. Wajen da Ikenga yaje yana da nisan gaske daga daular denizawa, zaka iya cewa wata duniyar ce ta musamman sabida nisa. Tambayar anan ita ce wai wane hatsabibin ne ya fafake ƙarƙashin ƙasa yai wannan gini? Kuma meye dalilin sa. An bayyana cewa a bayan daular denizawa akwai sahara, a bayan saharar akwai babban daji, a bayan dajin akwai katanga maɗaukakiya. Yawaicin biranen da suka ɓace sun ɓace ne a tsakanin wannan wajaje uku. Wai meye sirrin? Yaushe aka gina wannan birane harma sukai rayuwar su suka ɓace? Shin akwai wata ɓoyayyiyar ƙabilar ne da aka ɓatar?


Shidai Ayubu manzo ne, sabida haka duk wannan tambayoyi basu shafe shi ba. Aikin sa ya isar da saƙo, sannan yai hukunci ga waɗanda suka ɓata. 


Tsahon lokaci Ayubu da mutanensa suna sukuwa cikin wannan rami kafin su faɗo ƙasa - ko kuma kace kafin su faɗo sama. Domin kuwa ramin cikin gajimare ya watso su. To amma suna tare da zaren izza sabida haka babu tsoro a tattare da su. Zaka iya cewa girman izzar takai tayadda shi kansa zaren yana da tunani nasa na kansa. Yana da ruhi kuma yana da iko. Sannu a hankali zaren ya kai su dai-dai iyakar saharar. Daga inda suna iya hangen daular denizawa da manyan gine-ginen ta.   


Ayubu ya yamutse fuska. Badan komai ba sai dan runduna daya hanga a tsaye a bakin ƙofar garin suna jira. Babu ko kokwanto su ake jira. Runduna sahu goma, kowanne sahu akwai sadaukai ma'abota izza guda dubu a tsaye. A gabansu akwai sarki Deniz Iluru da yarima Deniz Bizaya. Kowannensu cikin shirin yaƙi sun daidaita akan dawakansu. 


Ayubu dashi da mutanensa su dubu ɗaya ne. Amma a yanzu suna fuskantar mutun dubu goma wanda sarkin Jinzidal Deniz Iluru yake jagoranta. Kai ma kasan daular ƙarƙashin ƙasa batai bacci ba wajen shiri. Domin kuwa banda sarki Deniz Iluru da ɗansa Deniz Bizaya akwai Salsa ɗinsa a bayansu. Daga gefe guda kuma akwai Haruta da Maruta Ururu, ƙannen babban sarki Kuyurussa'ayi. 


To fa, ana dara ga dare yayi. A dukkan garuruwa uku da Armad ya tura mutanensa an samu tsattsauran tsaro. Ururu sun haɗa kai da sarakunan Jinzidal a wani salo na tabbatar da cinikin bayi. Kuma koda Armad yai nasara akwai mazaje biyu da rundunarsu na jiransa. 


Bayan tsahon lokaci ana kallon-kallo Ayubu ya shige gaba. Yana taku ɗai-ɗai har ya isa gaban sarki Iluru. 


Iluru na sanye da jar alkyabba mai ratsin fari-fari. Kamar yadda aka labarta Iluru yana da girman jiki, tayadda ba kowanne doki bane ke iya ɗaukansa ba. Ƙusar tsafi, Mairakana, wadda tsayin ta yakai zira'i goma na yawo a saman kansa. 


Amma duk da wannan abu Áyúbu hankalinsa a kwance yake. "Suna na Ayubu Wilbafos, an aiko ni izuwa gare ku. Daga yau sarki Wilbafos ya haramta cinikin bayi. Zaku fito da duk bayin dake cikin garin ku. Zaku bawa kowanne bawa haƙuri ku nemi yafiyar sa da ayrid dubu..."


Tun kafin ya ƙarasa sarki Iluru ya katse shi. "Haha.. wannan ɗan tatsitsin yaron har yana tunanin yakai matsayin yin jayayya da mu? Kaje ka gaya masa, idan yana da saƙo da kansa zai tako yazo. Hukuncin laifin daya aikata shi ne kisa. Zamu kashe ku, sannan mu tura masa da gawarwakin ku a matsayin saƙo." Inji sarki Iluru. 


Ayubu ya ja dogon numfashi. Ga dukkan alamu har yanzu sarki Iluru bai gane abinda ke faruwa ba. Yadda abin yake shi ne: Ayubu umarni ne yake bashi bawai shawara ba.


***


A dai-dai wannan lokaci, a can gaɓar doron ƙasa na farko dana biyu wani abin mamaki ne ke afkuwa. Mutun tara na Tasu'a wanda ada akafi sani da Ashura (kafin mutuwar Uznu Ururu) su ne tsaye cikin shirin yaƙi. Gab suke dasu afkawa ƙasashen ƙasa. Amma kafin hakan ta faru mahaifiyar Armad, da kuma hadiminta Shata Kil'zanki suka dira a gabansu. Babu ƙura babu ƙara, mutanen biyu kawai sun bayyana ne kamar an jefo su daga sama. 


"Ina zaku je cikin sauri haka?" Fatima ta tambayi Tasu'a cikin murya mai nuna isa da rashin tsoro. Idan ka lura zaka ji ɗan kaushi mai tattare da azabar marmarin yaƙi acikin sautin muryar tata. Kamar kullum Fatima na sanye cikin doguwar riga fara mara ado. Fuskarta babu alamun fushi ko damuwa, kai kace ba a gaban Tasu'a take ba, ko kuma an gama lissafa komai tayi nasara. Shi kuwa Shata yana riƙe da shantun kiɗa a hannunsa - irin riƙon da ake yiwa al'amudi ko takobi. 


Tasu'a suka jada baya. Kamar kullum suna sanye da baƙaƙen idanuwa da baƙaƙen kaya. Fuskokinsu a rufe da hijabin ruhi. Kowannen su na ɗauke da faifan Taskar-ruhi a saman kansa. 


"Dul'Ururu, Yurba, Maruta, Haruta, Suwainah... Bakwa ganin mutanen da kuka tura ƙasashen ƙasa sun isa haka?" Inji Shata. 


Yarima Dumaƙisu ne ya shige gaba ya fuskance su. A hankali kyallen dake rufe da fuskarsa ya yaye. Fuskarsa ta bayyana. Dan saje siriri baƙi da gyararren gemu baƙi ya bayyana akan farar fuska da baƙaƙen idanuwa ababan firgici da nufaƙa. Bayyanar wannan idanuwa kaɗai ya samarda [Babbar Waƙar Izzar] mara sauti wadda manyan ma'abota izza kaɗai ke iya ji.


Dumaƙisu yai kyaran murya ya ce, "har dake Fatima? Kada kiyi tunanin samun rangwame. Anyi umarni daga sama, dole bayi subi umarni."


Fatima tayi murmushi a karo na farko ta ce, "da mutuwa da hisabi ai duk suna da lokaci. Dani da Shisu O. Bayajidda mu aka wakilta mu hana ku sauka ƙasa bawai yau ba, tun a Farkon Lokaci. Shisu ya mutu saura ni. Koda zan mutu bazan bari ku sauka ƙasa ba. Hasalima an halicce ni ne sabida na hanaku sauka a rana irin ta yau."


Shata ya gyaɗa kafaɗa gami da gyara shantun sa, ya ce, "yau zan rubuta waƙar ƙarshe. Wannan waƙa bata da suna, ba kamar Waƙar Maƙabarta ba."


Yarima mai jiran gado ya dubi na ɗan lokaci kafin daga bisani ya fashe da dariya. Acikin dariyar akwai fahimta da nutsuwa irin wadda ke nuna ba dariyar yara bace. Bayan ƴan dakiƙu ya numfasa ya ce, "Babban mawaƙi Shata wanda ya rubuta Wakar Maƙabarta. Fasahar ka a fannin waƙa babban al'amari ne. Amma bakai dabara ba wajen zaɓar ɓangare. Tarifil-fakta, K'Narbig, Bihanzin, Ikenga duk sun daɗe suna shiri, to amma komai nisan jifa ƙasa zai dawo. Maɗaukakiyar Fada na madakata tana jira. Talala ce kawai. A duk sanda tsayin igiyar ta ƙare za'a tsaya."


Da wannan sukai azama suka afkawa juna da azababben yaƙi. 

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...