Skip to main content

420-421

 "Maikiro Rabi," inji shugaban. "Kece yaya a wajen Shema'u da Anbalu da Kulu da Fulafunu. Ance a duk zamanin dogon zango babu wanda ya kai ki kwarewa a fannin magani da warkar da marar lafiya. Abin haushin shi ne tun a wancan zamani Maruta ya kashe ki amma kuma gashi har yanzu kina raye kina bada matsala. Yanzu mai kike so nayi miki?"


Rabi mace ce doguwa fara fat. Ko kaɗan bata yi duhun Maikiro'Abbas ba. Tana da hanci siriri da gira mara yawa sosai. Idanunta akwai alamun daɗewa da kuma sani acikinsu. Watakila kamar babarta tayi domin kuwa babu wani abu data haɗa da Maikiro'Abbas. 


"Waye kai?" Inji Rabi. Muryarta tana da kaushi kamar ta maza. Watakila daɗewa a duniya ne ya janyo hakan. Ko kuma dama can muryarta a haka take. 


"Ahh... Yi haƙuri ban gabatar da kaina ba. Ni ne kyaftin Lilut Dul'Ururu. Babban kyaftin a karkashin rundunar mayaƙan Ururu kuma ɗa a wajen sarki Dul'Ururu na Farkon Lokaci."


"Kyaftin Lilut Dul'Ururu," inji Rabi. "Mai ya kawo ka nan?"


"Har sai kin tambaya?" Inji Lilut. "Kashe ki nazo yi mana."


Rabi ta ɗan haɗe gira kaɗan kafin ta ja dogon numfashi ta kada kafada.


"To amma tayaya zaka kashe ni?" 


Lilut yayi murmushi. 


"Nasan sirrin ki kaf. Banzo nan ba sai da na shirya."


Yana rufe baki ya kawo mata suka da takobi a kirji. Ko kaɗan Rabi bata kauce ba. Tana tsaye takobin tazo ta shige kirjinta. Lilut ya kaɗa hannunsa mai ɗauke da ƙawanyar iska. Wani farin faifan iska ya fita daga cikin ƙawanyar iskar yayi kan Rabi. Watakila batai niyyar kaucewa ba, watakila kuma takobin dake ƙirjinta ce ta hanata motsi, amma tana tsaye haka faifan iskar yazo ya sari hannunta na dama. Wani faifan ya biyo bayansa ya daki cikinta. Kamar ansa wuka faifan na farko ya sare hannunta yayi sama. Na biyun ya raba ta gida biyu. Bai haƙura haka ba, a take ya saki faife goma na iska, dukkansu suka rufu akan Rabi. Kowanne yana saran inda ya samu. Kan kace kwabo sunyi daga-daga da Rabi. A ƙasa naman jikinta ya zube, jini yabi ƙasa. 


Mayaƙan Ururu suka fara shewa suna kiran sunan kyaftin Lilut. Mayaƙan Maikiro'Abbas tsayawa sukai suna kallo a nutse. A idanunsu babu damuwa sai nutsuwa. Kai kace ba na cikinsu aka kashe ba. 


A hankali naman jikin Rabi ya fara narkewa yana zama haske. Hasken ya shiga jikin mayaƙan Maikiro'Abbas dake kusa. Idan mutun yana da ciwo (ƙarami ko babba) sai kaga ya warke da zarar hasken ya taɓa shi. Daga can baya akwai wani sadauki wanda ke kwance a sume. Hannunsa na dama baya jikinsa. Koda hasken ya taɓa shi sai kurum ya buɗe ido ya tashi zaune. Da farko bai lura da abinda ke faruwa ba sai bayan ƴan dakiku sannan ya fara ihu yana riƙe kafaɗar da hannun ya fita. Sannu a hankali hannun ya fara yin tofo yana fitowa. Cikin dakika ashirin ya samu sabon hannu. 


"Madalla dake Maikiro Rabi," inji sadaukin.


Haka dai duk wanda hasken ya taɓa sai kaga ya samu waraka. 


A dai-dai gaban Lilut kuma ƙafafun Rabi tuni sun samu. A hankali gwiwa ta fito sannan cinya sannan ƙugu. Akan idon kowa halitta ta samu. Ciki da kirji da wuya da kai suka samu. Rabi ta buɗe ido ta kalli Lilut wanda ke tsaye yana jiranta. 


"Tunda baza ka iya kasheni ba mai zai hana ka kama gabanka?" Inji Rabi. 


"Hmmm. Kina tunanin na gama kenan?"


Lilut ya ɗaga hannu sama ya kira fasaha. 


"Saɓani, Bayani, Hakika, Baƙar wuta!"


Ya kyalkyale da dariya cikin alfahari. Wannan sune manyan fasahan idanun Ururu. Ko acikin ƴaƴan Ururu ba kowa ne yake iya sarrafa dukkansu ba. 


Fasahar Saɓani ita take basu dama su ga gaba. Ta haka suke ganin abinda zai faru kafin ya faru. 


Fasahar Hakika ita kuma bayani take basu akan abokin karawarsu da ƙarfinsa da ƙabilarsa da sihirinsa. A halin yanzu daga dai-dai saman fuskar Rabi bayani ya bayyana a rubuce yana bayyana sirrinta. 


Kyaftin Lilut ya karanta rubutun:


***

Suna: Rabi

Ƙabila: Maikironomada

Izza: shekara 1733

Fasaha: Warkarwa, littafin marubutan farko, takobin waraka

***


Lilut ya haɗe gira. Yasan mai fasahar Warkarwa take yi. Ita ce take bawa Rabi dama ta warkar da jikinta da al'umma duk abinda ta taɓa. Littafin marubutan farko shima ba boyayye bane. Amma inda gizo yake sakar shi ne fasahar takobin waraka. Shin mai wannan fasaha take yi? Bayan ɗan tunani Lilut yayi tsaki. Bai damu da mai wannan fasaha take yi ba. Koma meye yafi ƙarfinsa indai yana da idanun Ururu. 


Hasalima yana da fasahar Bayani wadda take bashi labarin abinda mutun yayi a baya. Duk da yawanci wannan fasaha bata fiya amfani a yaƙi ba. A wajen hukunci da shari'a suke amfani da ita tayadda suke ganin abinda mutun ya aikata. Ururu sukan yi amfani da wannan ilmi suyi wa mutum hukunci. Zaka iya cewa hakan shi ne yasa ayyukan laifi suka yi ƙaranci a doron ƙasa ta farko. Domin ana iya gane mai laifi cikin sauki.


Babbar tsiyar Ururu tana fasahar shankil da baƙar wuta. Shankil tana basu dama su nunawa ƴan'uwansu abinda suke gani da idanunsu. Ita kuma baƙar wuta ita take ƙone ruhi ta cillashi cikin duniyar Kuyurussa'ayi. Sau biyu ana cilla Armad cikin wannan duniya yana fitowa. Watakila duniyar Kuyurussa'ayi bata da bambanci sosai data Armad tunda dai kowacce idan kasa mutun aciki yana iya guduwa.


"Baƙar wuta!" Inji Lilut.


Wani baƙin haske ya fara fita daga idanunsa. A gefen hasken wuta ta kama. Tana ci launinta yana ƙara baƙi. Sannu a hankali wutar ta taru. 


Lilut yayi kururuwa. 


"Shin zaki iya tserewa daga baƙar wuta? Shin dabarar ki ta warkar da ciwo zata iya kubutar dake daga sharrin baƙar wuta?"


Rabi ta tsaya tana kallonsa bata ce masa komai ba har ya gama surutunsa. 


Lilut yayi amfani da Saɓani ya jefa mata wutar.


Rabi ta kira ɗalasimi a ɓoye. Take farin haske ya rufe jikinta. Baƙar wutar tazo ta daki hasken ta baje a ƙasa. Babu abinda ya samu Rabi amma duk abinda wutar ta taɓa sai kaga ya ɓace. Babu wanda yake ganin sanda abinda wutar ta taɓa yake ƙonewa. Kawai sai dai kaga abu ya ɓace. Tarihi ya bayyana cewa ƙonewar baƙar wuta ba kamar kowacce ƙonewa bace. Ance tana ƙone abu matuƙar ƙonewa tayadda ko tokar abun ba'a gani. Amma Armad yasan wannan tarihi ƙarya ne. A zahiri bawai saboda wutar tana ƙone abu har toka shi yasa ba'a ganinsa ba, ba'a ganin duk abinda wutar ta taɓa ne saboda tana haɗiye shi cikin duniyar Kuyurussa'ayi. 


Sai dai fa Rabi tana nan tsaye kikam. Lilut ya ƙara harba mata wata wutar a karo na biyu amma a banza. Daga zarar wutar ta haɗu da hasken jikinta sai kaga ta baje a ƙasa. Duk inda wutar ta zuba sai kaga ta cinye ƙasar tayi rami.


Ganin hari daga nesa baiyi aiki ba sai Lilut yayi tsalle sama ya kawowa Rabi naushi. Kafin ya ƙaraso yayi amfani da fasahar Saɓani yaga inda zata kauce kuma ya tare wajen. Dole Rabi ta tsaya ya same ta. Ya danna hannunsa mai ɗauke da baƙar wuta cikin ƙirjinta. Ƙirjin Rabi gaba ɗaya ya fafake ya shige duniyar Kuyurussa'ayi. 


Lilut ya fara dariyar farin cikin samun nasara. 


"Kika ce bakya ji?"


Ya ƙara danna hannunsa cikin ƙirjinta yana dariya. Bayan ya tabbatar ta daina motsi sai ya koma baya ya zuba mata ya gani idan zata tashi.


Da farko haske ne ya bayyana ya cika ramin ƙirjin. Daga nan sai naman ya fara dawowa yana tsurowa yana yin tofo. A hankali a hankali komai ya dawo dai-dai. 


Ganin haka ya firgita Lilut. Dole yaja da baya yana zare ido. 


"Kai ɗin har yanzu yaro ne," inji Rabi. "Ni kuma bana kashe yara sai dole. Tunda dai baka da fasahar da zata yi aiki a kaina, ni kuma bani da niyyar kashe ka, mai zai hana ka tafi naka guri?" 


Ta juya zata tafi.


Cikin fushi Lilut ya tare ta.


"Ƙarya ne wallahi! Karya kike, bil'adama."


Baƙar wuta ta rufe jikinsa. Sannan guguwa ta rufe baƙar wutar. Wata iska mai ƙarfi tayi sama wadda taja hankalin duk wanda ke filin yaƙin. Ya tafi a fusace ya haɗu da Rabi. Suna haɗuwa jikin Rabi ya tarwatse yayi daga-daga. Baƙar wuta ta zuƙe naman da jinin cikin duniyar Kuyurussa'ayi.


Lilut ya jada baya yana nazarin wajen da Rabi ta mutu. Shi kansa bai samu nutsuwa ba. A kowane lokaci gani yake kamar zata tashi.


Ai kuwa haka akayi. Ba jimawa ɗan abinda ya zuba ƙasa na jinin Rabi ya tashi ya fara haɗewa yana dunkulewa guri guda. 


Gudan jini ya zama tsoka. Tsoka ta zama ƙashi. Ƙashi ya zama mutum. Da fari tana jaririya. Bayan dakika goma ta girma ta koma cikakkiyar siffarta.


"Shikenan tunda ka takura," inji Rabi. Ta zare wata ƴar ƙaramar takobi daga kufenta. 


Lilut ya tunkaro ta a fusace. Sai da ya ƙaraso gab da ita sai kawai a wani salo mai ban sha'awa ta matsa gefe ya wuce. Ya juyo da fasahar Saɓani a idanunsa ya kawo mata suka da takobi. Maimakon ta kauce a wannan karon sai ta tare shi kai tsaye.


Takobinsa ta shige cikinta. Ita kuma ta sari kafaɗarsa. 


Lilut ya juya takobinsa a cikinta inda kayan cikin suka zubo ƙasa. Ta faɗi matacciya. 


Shi kuwa Lilut ɗan ƙaramin ciwo yaji a kafaɗa wanda baifi hannu ɗaya ba. Abin mamaki ko jini bai gama zuba daga ciwon ba ya fara warkewa. Cikin dakika ashirin ciwon ya warke gaba ɗaya. Lilut yasa hannu ya taɓa domin ya tabbatar da gaske ya warke. 


Yana shafa gurin sai yaji zafi a kafaɗarsa. Ya duba sai yaga ciwo ya buɗe ya dawo sabo. 


"Mai ke faruwa?" Ya tambayi kansa cikin rashin fahimta. 


Kafin ya samu amsa sai ciwon ya ƙara warkewa. Sannan bayan dakika goma ya ƙara fashewa. Baki a buɗe ya tsaya yana kallon ikon ALLAH. Sai ya warke, ya fashe. Kafin Rabi ta tashi sai da yayi haka sau goma. Yasa sulke ya rufe wajen dan ya daina gani. 


"Wacce irin fasaha ce wannan?" Ya tambayi Rabi bayan ta tashi. "Ki warkar sannan ki lalata. Mai kike so ki cimma ta hakan..."


Kafin ya ƙarasa yaji jiri ya ɗebe shi. Dole ya dakata domin ya duba lafiyar jikinsa. Meye dalilin da zai sashi jiri? 


"Takobin Waraka kenan," inji Rabi. "Ita ce ajalinka."


"Ajalina? Karya kike, Rabi. Ni ne Lilut Dul'Ururu. Naci dubu sai ce...to..."


Kafin ya ƙarasa jiri ya ɗebe shi yayi taga-taga zai faɗi. 


"Lilut sunanka, ko? Kayi sani fasahar takobin waraka bata da magani. Zata ji maka ciwo sannan tayi amfani da ƙarfin jikinka ta warkar dakai. Bayan ka warke sai ciwon ya fashe sannan fasahar ta ƙara amfani da ƙarfinka ta warkar dakai. A haka har sai dukkan ƙarfin jikinka ya ƙare. Takobin Waraka kenan."


"Ƙarya ne, ƙarya kike, ƙarya..."


Kafin ya rufe bakin ya faɗi. Ciwon kawai zuƙe ƙarfinsa yake yi amma kuma babu yadda zaiyi.


Rabi ta kalleshi tsahon dakiku kafin ta juya ta tafi. Mayaƙan Maikiro'Abbas suka fara yi mata kirari. Wasu daga cikinsu suka yi kan Lilut wanda ke kwance ya kasa tabuka komai da niyyar su ƙarasa shi. Mayaƙan Ururu da suka rako shi sukai sauri suka ɗauke shi suka gudu.


Rabi ta shige cikin mutanenta. Duk wanda yaji ciwo sai kaga ta bayyana ta warkar dashi. Ko ƙafa ko hannu, duk abinda ya cire sai kaga ta mayar dashi. Indai ba daina numfashi mutum yayi ba sai ta warkar dashi. Duk inda tayi sai kaga ƙarfin rundunar Maikiro'Abbas ya ƙaru. Ita kaɗai gayya. Watakila ita ce likitan da Najunanu ya gayawa Armad suna da ita.


A can gaba kuma Armad yayi azama wajen kashe maƙiya. A gabansa Sarkin Bai ne da mai unguwa Shísu. A bayansa kuma Barilu da Inyaya. A tare dashi akwai Nusi, Nazára, Cokali, Giwa, Asifu da jan doki. Koma meye ya taho, kowane irin hari ne baya tarar da Armad. Duk bayan dakika ƙara kusantar Fatima suke yi. 


Hakan ya ɗau hankalin Dul'Ururu. Bayan ɗan nazari, sarkin ya juyo ya dubi kwamandunsa. "Waye zai tare su?"


Kwamanda Diwani ya ɗaga al'amudinsa sama. "Zan ƙarasa abinda na fara."


"Jeka da sunan Ururu," inji Dul'Ururu. 


Diwani ya saɓa al'amudinsa ya tashi sama. Ƙaraiƙisu ya tari gabansa. 


"Har ka manta alƙawarin da muka yi?" 


Diwani ya kalli Ƙaraiƙisu. Abin kunya ne a wajensa ace ya haɗa ƙarfi da wani. Sai dai kuma bazai iya hana baƙin basamuden shiga faɗan ba.


"Shiga gaba," inji Diwani. 


Ƙaraiƙisu ya juyo a fusace. 


"Idan kana so na fara kashe ka to ka ƙara bani umarni," inji Ƙaraiƙisu.


Sukai kallon-kallo da Diwani. Kowa ya haɗiye kalamansa suka yi kan Armad.


Sama ta fara duhu. Dole Armad ya rage gudu ya ɗaga kai ya duba mai yake faruwa. 


Wani ƙatoton al'amudi ne ya rufe sama. Kamar almara sai al'amudin ya ɓace daga sama ya dawo dai-dai saman kansu. Kafin su kauce ya danno kansu.


"Aiban'shisu!"


Armad ya kira ɗalasimi domin ya tseratar dasu amma kafin ɗalasimin ya gama saituwa al'amudin ya danne su. Dolen Armad yasa hannu ya tari al'amudin. Hakan ya bawa su Nusi damar gocewa. Bayan ya tabbatar sun tsira sai yayi ƙoƙarin kaucewa gefe ya bawa al'amudin waje ya dira ƙasa. Amma kamar a baya sai al'amudin ya riƙe hannunsa ya fara ƙara nauyi.


Dukkansu sun ga abinda ya faru ɗazu tsakanin Armad da al'amudin saboda haka nan take suka fuskanci abinda zai faru. Cokali da Giwa suka rufe Nusi da jikinsu a wani yanayi na bada kariya. Asifu da jan doki suka tsaya a gaban Nazára suka ɗaga hannu dan su tare masa wutar. 


Al'amudin ya fashe. Wata narkakkiyar wuta ta bayyana a dunkule ta fashe. Kafin su Nusi suyi nisa ta rufesu.  


Wani abin haushi shi ne har yanzu hannun Armad a riƙe yake. Idan ka lura zaka ga dai-dai inda ya riƙe hannun bai canja ba yana nan a al'amudinsa. Ragowar jikin al'amudin shi ne ya zama nakiya yayi bindiga. 


Armad ya tura izzarsa ƙafa. Ta nan ya saki Negrinkinsa ta fita ta rufe mutanensa. Duk wutar da tayi kan su sai kaga Negrinkin ta zuƙe ta. Kamar wutar tana da rai sai ta daina bin Negrinkin tayi sama kan Armad ta rufe shi.


Armad ya koma walkiya. Wutar taci-taci amma ta kasa ƙoneshi. Dole ta rabu dashi ta koma baya. Sai dai duk da haka Armad yana ji ta cikin jikinsa tayi masa rauni. 


Kafin ya gama wartsakewa Ƙaraiƙisu ya bayyana ta bayansa. Gwiwa a dunkule ya daki bayan Armad da ƙarfi har saida ƙashin yayi ƙara. A wani yanayi na rashin imani ya dunkule hannu zai ƙara dukan Armad a ciki. Nusi ta bayyana ta tare da hannunta. Wasu rassan bishiya suka haɗu suka ƙarawa hannunta girma. 


Abin tambaya anan shi ne: tayaya fasahar Nusi take iya taɓa Ƙaraiƙisu. Hatta Armad da jerin fasahohinsa baya iya taɓa jikin ƙaraiƙisu. Amma fasahar Nusi tana yin aiki akan basamuden kamar yadda muka gani yanzu da kuma sanda suka fafata a gasar jinzidal. Wasu zasu iya cewa saboda baƙar guguwa ta taɓa Nusi shi yasa musamman tunda shima Ƙaraiƙisu baƙar guguwar ce ta bashi nasa sirrin. To amma wasu zasu iya cewa ba haka bane tunda dai tun can asali Nusi tana da fasahar sarrafa bishiya tun kafin ta shiga ikwatora. Idan ba'a mantaba tayi amfani da wannan fasaha a fafatawar ta da Uznu Ururu a waccan gasar jinzidal ɗin. Nusi dai ita kaɗai tasan gaskiyar yadda abin yake. A yanzu babban abinda Armad ya damu dashi shi ne tana iya tare Ƙaraiƙisu. Sauran bayani daga baya ne. 


"Nusi," inji Ƙaraiƙisu. "Bani da niyyar kashe ki a yau amma idan kika ci gaba da shiga gaba na babu yadda zanyi."


"Sarki Ƙaraiƙisu," inji Nusi. "Tunda kana son kashe ɗan uwana meye bambanci."


"To shikenan," inji Ƙaraiƙisu. "Tunda abinda kika zaɓa kenan."


Ƙaraiƙisu ya kawo mata tunkuyi da ƙaho. Armad ya saka Negrinki ya narka al'amudin dake hannunsa. Sannan yayi amfani da Kaban'shisu ya shiga tsakanin Nusi da Ƙaraiƙisu.


"Nusi koma ƙasa, Nazára dawo sama," inji Armad. Nusi ta sauka ƙasa babu musu. Nazára kuma ya tashi sama ya tsaya a dai-dai ƙasa Armad. "Cokali, Giwa, kuna tare da Nusi. Shísu, sarkin Bai, kuna gaba. Inyaya, Barilu, kuna baya. Formation C."


Yana rufe baki kowa ya kama waje. Kamar ɗazu duk wata kibiya ko mashi da aka harbo Shísu ne yake tare su. Sarkin Bai yana gefe yana bashi kariya. Ta baya kuma Inyaya da Barilu sun tare hanya babu wanda yake wucewa. Giwa da Cokali sun saka Nusi a tsakiya suna bata kariya. Shi kuwa Armad yana can sama yana ji da Diwani da Ƙaraiƙisu. A yayin da Nazára da Asifu da Jan doki suke tsaye a ƙasansa suna tare duk wani abu daya wuce shi. 


Bayyanar kwamanda Diwani tasa su Armad sun tsaya, amma suna yin wannan shiri mai suna formation C sai kawai suka ci gaba da tafiya kamar babu abinda ya faru. 

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...