Shísu yayi shiru yana tunani. Bai taɓa gwada fasaharsa a irin wannan yanayi ba, amma kuma abu ne mai yiwuwa. Tunda yana iya amfani da tunaninsa ya motsa ƙarfe ai kuwa zai iya ƙara masa gudu ko kuma ya rage. Kamar yadda yake ture masu da kibbau idan an harbo masa. Sai dai kuma yana jin tsoro kada yace zai iya kuma sai lokaci yazo ya kasa. Hakan zai iya sanadiyar mutuwar Asifu dama sauran wanda suke tare dasu. Shin mai zai cewa Nusi-ya idan hakan ta faru?
"Ban taɓa... yin hakan ba, amma ina ganin watakila..."
Nusi ta ɗora hannu a kafaɗarsa lamarinda yasa ya daina kinkina.
"Zaka iya," inji Nusi. "Ni nasan zaka iya."
Shísu ya risuna cikin girmamawa. Tabbas tunda Nusi-ya tace zai iya to kuwa zai iya. Bazai bata kunya ba komai rintsi komai wuya.
"Zan iya," inji Shísu.
"Amma yaya zaku yi da ƙusar mairakana?" Inji Armad. A ganinsa babban abinda yake ƙarawa denizawa ƙarfi shi ne fasahar mairakana. Koda Asifu zai iya yanka jikin Iluru bazai samu nasara ba zarar sarkin yana sarrafa ƙusoshin mairakana.
"Amfanin ruwan bala'i kenan," inji Asifu. "Ban san mai yasa ba amma ruwana yana narka ƙusar mairakana. Tun shekaru da dama da suka wuce na gano hakan. Nayi bincike domin na gane dalili amma ban samu ba. Sai dai ƙusar dana narka ta ƙananun denizawa ce, babu makawa ƙusar Iluru zata fi tasu ƙarfi, amma dai zanyi iya ƙoƙari na."
Ruwa mai narka ƙusar mairakana? Armad ya ɗanyi tunani. Yana ganin kamar ya gane dalilin da yasa ruwan Asifu yake aiki akan ƙusar.
"Asifu?" Inji Armad. "Meye alaƙar ruwan da kake samarwa da turɓaya?"
Asifu ya ɗan haɗe gira yana mamakin tambayar. Can dai ya amsa da cewa, "idan ruwana ya taɓa ƙasa yana sawa tayi danko sosai. Idan ta bushe tana komawa dutse."
"Shi ne dalili," inji Armad da sauri. "Ai hakan shi ne yasa kake kashe ƙusar mairakana. Iluru ya gayamin ana yin ƙusar mairakana da turɓaya da walkiya. Idan aka narka turɓaya da walkiya sai a samu sinadarin da ake yin ƙusar dashi. Kaga duk sanda aka sami abinda zai dunkule ƙasar da take cikin ƙusar ya maida ita dutse kaga shikenan ƙusar ta daina aiki kenan."
Armad ya ƙurawa Asifu ido yana hango irin amfanin da sadaukin zaiyi wajen yaƙar denizawa. Babu makawa yana buƙatarsa bayan an kammala wannan yaƙi.
"Asifu da Shísu," inji Armad. "Ku tare Iluru. Saura Suwainah da Ibraham Nil. Suwainah ba matsala bace, bana jin tana da wata fasaha ta musamman banda kwaikwayon miyura da take. Zan saka mutun-mutumi ya riƙe ta. Ibraham Nil kuma ban san wacce fasaha yake amfani da ita ba."
"Ni zanje na taimaka acan," inji Shata, ya nuna tsakiyar filin yaƙin inda rundunar Ururu suke kallon-kallo da rundunar Maikiro'Abbas. "Fasaha ta tafi dacewa wajen faɗa da mutane da yawa."
Armad ya amince da hakan. Dama barin mutane irin su Shata suyi faɗa da mutun guda asara ne a filin yaƙi. Kamata yayi ka tura su kan mutun dubu su gama maka dasu.
Bayan Shata ya tafi sai Armad ya juya wajen su Sarkin Bai.
"Giwa, Inyaya, Barilu, da Sarkin Bai, ku tare Ibraham Nil. Kada ku fara kai masa hari. Ku zagaye shi ku jira ku ga mai zaiyi. Wata zuciyar tana gayamin kamar bashi da niyyar shiga faɗan a yanzu."
"An gama," su huɗun suka amsa a tare. Kowa ya kama nasa yana kallonsa daga nesa. Zaka iya cewa kawai umarnin Armad suke jira.
A ɗaya ɓangaren Rabi ce tazo wajen babanta Maikiro'Abbas ta tsaya a bayansa daga gefe tana jiran umarni.
"Yaya mayaƙan?" Maikiro'Abbas ya tambaye ta ba tare da ya waiwayo ba.
"Sama da kaso ɗaya cikin hudu sun mutu," inji Rabi. "Ragowar suna tsaye amma ƙarfin zuciyarsu ya fara raguwa."
Sarkin yayi shiru yana kallon filin cikin lissafi kafin ya numfasa yace, "muna da buƙatar mu karya kafin can. Zan tare miki su idan kina so."
Rabi ta kalli ƙasa ta runtse idanu. Shin mahaifin nata so yake ta karya kafin duk kuwa da yafi kowa sanin alwashin data ci? Shin lalacewar filin yaƙin ta kai haka?
"Anbalu ya yafe miki," inji Maikiro'Abbas. Har yanzu bai juyo ya kalleta ba. "Nima na yafe miki."
Wani hawaye yazo idon Rabi.
"Muna da buƙatar mu karɓi Fatima kafin mayaƙan mu suci gaba da mutuwa," inji Maikiro'Abbas. "Suma suna da ƙanne da mata da ƴaƴa a gida."
A lokaci na farko sarkin ya waiwayo da kansa yaga Rabi tana hawaye.
"Da zafi," inji Maikiro'Abbas. "Amma dole ne ayi hakan. Ki je na yafe miki."
Rabi ta goge hawayen dake idanunta. Sannan ba tare da cewa komai ba ta ɓace.
"Kwamanda," inji Maikiro'Abbas.
Yana rufe baki wani mutum rataye da doguwar takobi a baya ya bayyana a gabansa ya durkusa. Fuskarsa a ƙasa.
"Ina so a kare Rabi a bata hanya," inji Maikiro'Abbas.
"An gama, shugaba," inji kwamandan. Sannan ba tare da ya ɗago ya kalli sarkin ba ya ɓace.
A nasa ɓangaren har yanzu Armad bai bawa mutanensa umarni ba. Daga abinda Najunanu ya gaya masa yasan Rabi zata iya karya kafin, sai dai baza ta karya ba saboda wani abu daya faru da ita a baya. Idan ba ita ba to babu wanda zai iya karya kafin sai Maikiro'Abbas. Saboda haka Armad yasan kodai Maikiro'Abbas yayi da kansa, ko kuma yasa Rabi tayi. Duk yadda ta kasance dashi da mutanensa zasu taimakawa wanda zai karya kafin. Saboda haka ya jira yaga waye zai shiga gaba.
Suna tsaye anyi cirko-cirko ana kallon juna, kowane ɓangare yaƙi motsawa, sai kwatsam saman rundunar Ururu ya fara haske. A tsakiyarsu wani mutun ya bayyana da zabgegiyar takobi a bayansa. Mutumin ya zare takobin ya saukar musu da sara.
Dai-dai inda ya sara ya fara haske yana tartsatsi. Farin haske samfurin takobi yayi kan mayaƙan Ururu.
"Arnen daji Burjan," inji mayaƙan Ururu da suka ga mutumin. "Ku kaucewa saran."
Ina, sun makaro, kafin su ƙarasa matsawa saran takobin ya datsa duk wanda ke kan hanya gida biyu sannan ya zarce ya datsa ƙanƙarar dake ƙasa. Daga nan yaci gaba da tafiya yayi kan su Dul'Ururu kamar bai yanka komai ba. Yana gudu yana ƙara kauri. Duk inda ya gilma sai kaji ƙasa tana girgiza.
Armad ya ƙurawa saran ido. Tabbas ba gama-garin sara bane. Tun da daɗewa Armad ya koyi saran takobi mai tafiya. Sannan kuma ya koyi haɗa fasahar takobinsa da walkiya domin ya ƙara mata gudu. Saboda haka idan Burjan haɗa fasahar takobi mai tafiya da walkiya yayi to Armad zai gane. Sai dai ba haka abin yake ba. Akwai wani sirri acikin saran takobin wanda Armad bai fahimta ba. Shin har yanzu akwai sabuwar fasaha wadda Armad bai sani ba kenan?
"Armad," Najunanu ya matso kusa da Armad. "Duk abinda zai faru yanzu zai faru. Ko Rabi, ko sarki."
Armad ya fahimci abinda yake nufi. Tabbas wannan mutun da Maikiro'Abbas ya fito dashi wani ɓoyayyen makami ne, kuma baka fito da ɓoyayyen makami a filin yaƙi sai zaka yi tsiya.
"Waye shi?" Armad ya nuna Burjan da hannu.
"Kwamanda Burjan kenan," inji Najunanu. "Asalinsa arnen daji ne shekaru dubu da suka wuce. A yanzu shi ne garkuwar Maikironomada. Wanda kaɗai ya fishi ƙarfi a daular baki ɗaya shi ne sarki da kansa. Tunda sarki ya fito dashi to ta ɓaci."
Kwamanda Burjan? Armad ya tauna sunan a harshensa. Tabbas kowace daula suna da nasu kwamandan wanda ya shahara. A Sisiya akwai kwamanda Djinn. A rafiya akwai Asifu da jan doki. A maikironomada kuma ga Burjan.
A yayinda Armad suke magana da Najunanu, saran takobin Burjan ya shige ta cikin mayaƙan Ururu ya kashe na kashewa ya watsa na watsawa sannan ya wuce kan gadon aba'in da aka ajiye Fatima zai raba shi gida biyu.
Kwamanda Binani yayi tsalle ya tari gabansa. Kakkauran bangon ƙarfe ne ya shiga tsakaninsa da saran. Saran ya yanke bangon biyu ya wuce kan Binani. Cikin sauri Binani ya samar da wani bangon a bayan na farkon amma saran ya yanka shi kamar yana yanka ruwa ya wuce kan Binani. Kafin Binani ya ƙara haɗa wani ƙarfen saran ya cimmasa. Yayi maza ya mirgina gefe ya kaucewa saran dan gudun kada ya raba shi gida biyu.
Saran ya wuce ya daki kafin dake tsare da Fatima ya yanka ta ciki ya wuce ya sari gadon da Fatima ke kai. Wata ƙara tayi sama. Tartsatsin haske da walkiya ya rufe ko'ina. A hankali ƙura ta lafa gadon ya bayyana.
Gadon yana nan lafiya sai dai ginin dake bayansa ya rabe gida biyu. Babu wanda yasan tayaya amma saran takobin ya kewaye gadon ya wuce ta baya ya raba ƙatoton ginin shalkwatar Ururu dake baya.
"Ya... Ya... Ya... raba toluwar Ururu!"
"Ya raba toluwar Ururu!"
Nan da nan mayaƙan Ururu suka fara kiraye-kiraye a firgice.
"Ginin da aka gina shekaru dubu da suka wuce tun kafin saukar Ururu ƙasa?" Wani sadauki ya tambayi kansa kamar yana kokwanton faruwar abin. "An yanka toluwar Ururu, an yanka toluwar gaskiya."
Zaka iya cewa wannan shi ne mafi girman nasara da mayaƙan Maikiro'Abbas suka samu kawo yanzu. Domin kuwa a lokacin mayaƙan Ururu sun gama firgita. Toluwar dake saman ginin ta fado ƙasa ta tarwatse. Ƙura ta turnuke ko'ina. Saboda da firgici duk mutane sun kasa tsayawa su tambayi kansu meye dalilin da yasa saran ya shallake gadon da Fatima take kai ya wuce ya sari gini dake bayansa. Shin kafin ne yasa haka, ko kuma akwai wani sirri na daban dake kare gadon, ko kuma Maruta ne ya jawo hakan?
Armad yana ganin abinda ya faru ya tashi a sama yayi kan Dul'Ururu. Duk mutanensa suka mara masa baya. Idan ka hange su daga nesa kace wasu yan aiken mutuwa ne suka tafi kai sako.
Kafin su ƙarasa wani guri babu nisa da kafin ya fara haske. A wajen Rabi ta bayyana. Tana tare da kwamanda Burjan. Su biyun suka tunkari kafin.
Diwani, Binani da Yurba suka sha gabansu. Diwani yayi tsalle sama ya kawo duka da al'amudinsa, Binani ya saukar musu da murfin kwano, shi kuma Yurba ya kira turɓayar daɓe. Al'amudin ne ya fara sauka a kansu. Sannan murfin kwanon ya rufe su. Sannan kuma baƙar ƙasa irin wadda ake daɓe da ita a zamanin da ta bayyana ta rufe murfin kwanon.
Burjan ya juya takobinsa ya sari al'amudin. Takobin ta yanka ta cikin al'amudin ta raba shi biyu sannan ta wuce kan kwanon Binani ta yaga shi kamar wata takarda. Takobin ta wuce suka haɗu da bangon ƙasar Yurba. Tartsatsin wuta yayi sama. Al'amudin daya rabe gida biyu yayi bindiga ya haɗu da wuta.
Idon kowa yana kai ana jira a ga mai ya faru dasu Rabi. Bayan ƙura ta lafa kawai gilmawar takobin Burjan aka gani. Kafin kwamandun uku su ankara Burjan da Rabi sun wuce gaba wajen kafin. Baki buɗe mutane suka fara salallami cikin mamaki.
"Ya yanka su," inji wani sadauki daga mayaƙan Ururu.
"Hatta kwamanda uku sun kasa tare su," inji wani.
"Burjan da Rabi amanar Maikironomada," inji wani.
Haka dai aka ci gaba da faɗar irin wannan maganganu.
Yurba da Binani da Diwani suka juya a fusace sukai kan su Rabi.
Burjan ya bar Rabi ta wuce gaba, shi kuma ya juyo ya tare su. Shi kaɗai su uku.
"Ba ku wucewa," inji Burjan. Ya kaɗa takobinsa ya kai sara gaba, ya kai sara hagu, sannan ya kai sara dama. Wuta da walkiya suka yi sama suka rufe ko'ina. Ƙasa tana girgidi kamar zata fashe. Maɗauran gadon da Fatima ke kai suka fara rawa zasu fice.
Binani yasa katangar ƙarfe domin ya tare takobin Burjan amma banza. Saran ya yanka ta cikin ƙarfen ya fice ta baya yayi kan mayaƙansu. Yurba da Diwani basu yi ƙoƙarin tare wa ba, kawai waje suka bashi ya wuce.
Cikin ƙanƙanin lokaci Armad ya cika da mamaki. Mutun guda ya bayyana yayi abinda dukkansu sun kasa. Abin haushin shi ne Burjan bashi da wata fasaha ta musamman kamar su Armad ko kuma kwamandun Ururu, kawai takobi ce yake juya ta, amma kuma ya gagara. Armad ya ƙara yin karatun-ta-nutsu akan takobin mutumin ko zai fuskanci dabarar da Burjan yake yi wajen karfafa saran sa, amma bai ga komai ba.
A dai-dai wannan lokaci su Armad suka ƙaraso. Ba tare da tambaya ko neman ba'asi ba suka afkawa kwamandun uku kamar yadda suka tsara. Najunanu da Cokali suka yi hagu kan Han'ibal. Asifu da Shísu suka faɗa kan Iluru. Jan doki da mutun-mutumi ɗaya suka faɗa kan Ayubu.
Armad ya tafi kai tsaye ya faɗa kan Dul'Ururu. Zaikid ya tari Yurba. Nazára ya tari Binani. Ita kuma Nusi ta tari Diwani.
Abin mamaki iyakacin tawagar Armad kenan. Babu Giwa, babu sarkin Bai, babu Inyaya, babu Barilu. Sun ɓace ɓat, babu su babu alamun su. Kada dai a manta wannan su aka bawa alhakin kula Ibraham Nil da Suwainah. To ko ina suka tsaya?
To koma dai ina su Giwa suka tsaya babu wanda ya tambaya. Kai tsaye su Armad suka wuce gaba inda aka fara yaƙin ɗaya-da-ɗaya.
"Ɗorawa Abada."
Armad ya sauka akan Dul'Ururu da babban sara. Ko kaɗan a jikinsa babu tsoro. Baza ka taɓa cewa sarkin dukkan doron ƙasa ta biyu yake faɗa dashi ba. Wani ma zai iya cewa Armad ya zaƙe da yawa. Sai dai a nasa ɓangaren Armad dama horon daya karba a duniyar aljanu kenan. Ya riga yayi shirin faɗa da mutane irin su Dul'Ururu. Zaka iya cewa wannan shi ne lokacin da zai gwada ƙarfin izzarsa. Shin ya samu abinda yake so a duniyar aljanu? Shin zai iya faɗa da Dul'Ururu da Ikenga da Bihanzin? Shin yana da dama akan wannan tsoffin ma'abota izzar?
Saukarsa saukar izza. Armad ya sauka da dukkan ƙarfinsa. Takobinsa takobin Wilbafos ruwan ɗorawa mai ɗauke da taurari. Tunda zuƙe Dul'Ururu cikin duniyar Negrinki bazai yiwu ba a wannan lokaci, sai Armad ya maida hankali wajen lalata izzarsa sarkin. Kodai ya zuƙe ta, ko kuma ya rikita ta.
Dul'Ururu yana zaune akan kujerarsa har Armad ya iso. Daga zaunen ya saka sandar da yake farauta da ita ya tare takobin Armad.
Suna haɗuwa izzar Dul'Ururu ta fara fita daga jikinsa tana dawowa wajen Armad. Armad bai bari ta haɗu da izzarsa ba saboda gudun ko Dul'Ururu ya saka wani abu a jiki sai ya tura ta jikin mutun-mutuminsa daya haɗa saboda haka. Dama biyu ya kirkira: ɗaya yana tare da jan doki, ɗaya kuma yana cikin jikinsa.
Sai dai kamar yadda ya faru a faɗansa da Iluru, kafin ya ankara Dul'Ururu ya dawo da izzarsa. Armad ya ƙara fincikar izzar, amma Dul'Ururu ya dawo da ita.
Armad ya haɗe gira cikin tunani. Idan Iluru ya dawo da izzarsa ba abin mamaki tunda yana da kwangila. Amma Dul'Ururu bashi da kwangila, shin akwai wata hanya da ake iya samun izza banda kwangila da jinin Wilbafos?
Idan zuƙe izza ba zaiyi aiki ba kaga an yanke sama da rabin fasahan Armad kenan. Anya kuwa? Armad yasan yana daga cikin ma'abota izza masu yawan fasaha. Bai daɗe da fitowa ba, musamman idan aka kwatanta da wanda sukai shekaru dubu suna yi, to amma ya tara abubuwa masu tarin yawa. Ya karɓi horo daga ƴan duba da mutane da kuma aljanu. Shin ana nufin ace duk abubuwan daya tara a banza kenan? Kai, ƙarya ne.
Armad yayi ƙaraji ya saukarwa da sarkin Hannun Aradu. Hannun walkiyar ya sauka a wuyan Dul'Ururu ya ƙone wuyan ya narke. Dul'Ururu ya faɗi ƙasa matacce. A lokaci guda kuma Dul'Ururu ya tare hannun walkiyar da sandarsa. Wancan zamanin da aka kashe Dul'Ururu sai ya ɓace ɓat, masu kallo suka manta dashi, a yayinda shi kuma wannan zamanin da Dul'Ururu ya tare hannun Armad ya tabbata ya zama gaskiya rubutacciya.
Armad bai gajiya ba ya ƙara kiran wani ɗalasimin.
"Sikai!"
Jikinsa ya koma walkiya. Samaniya ta kaɗa. Manyan guma-guman walkiya suka fara sauka daga sama suna haɗuwa da jikin Armad. Cikin ƙanƙanin lokaci jikinsa ya koma jajawur. Walkiyar taci gaba da taruwa a jikinsa. A hankali jikin ya koma baƙi.
"Hannun Aradu!"
Baƙar walkiya ta dunkule izuwa siffar hannu ta sauka akan Dul'Ururu. Sarkin yana zaune daga kan kujerarsa ya saka sandar tsafinsa ya tare hannun Armad. Armad ya danno, shima ya danna. Bayan ƴan dakiku sai sarkin ya kaɗe hannun Armad gefe, walkiyar ta wuce ta bayansa ta sauka akan toluwar Ururun da Burjan ya sara gida biyu ta ƙarasa ruguza ta.
Armad yana ƙoƙari duk rintsi yaga ya kwantar da hankalinsa a yayin faɗa. Amma a wannan lokaci tabbas hankalinsa ba'a kwance yake ba. Wannan fa shi ne harin walkiyarsa mafi girma. Dashi ya lalata Uznu. Ta yiwu ace Dul'Ururu ya tare shi yana zaune? Kuma babu ko alamun sarkin ya sha wahala wajen tare harin. To kodai akwai wani sirri a game da izza wanda har yanzu Armad bai tsinkaye shi ba?
Armad yaja da baya ya danne zuciyarsa ya kuma rufe Idanunsa. Kasancewar Dul'Ururu yana faɗa dashi a zaune kaɗai ya isa ya tunzura shi. Amma duk da haka ya kwantar da hankalinsa ya fara nazarin faɗan nasu. Shin akwai wani abu da Dul'Ururu yake yi wanda Armad baya yi? Idan dai ɓangaren yawan fasaha aka zo to Armad baya ji an fishi. To amma meye matsalar? Shin canza zamani da Dul'Ururu yake yi shi ne yake bashi damar dawo da izzarsa da Armad ya zuƙe? Armad ya girgiza kai. Watakila sauya zamanin zai iya sawa Dul'Ururu ya dawo da izzarsa, to amma Armad baya jin hakan shi ne dalilin domin kuwa harin Maikiro'Abbas yana aiki akan Dul'Ururu duk da yana iya canja zamanin. Sannan idan Armad zai iya tunawa harin Hidaya shima yayi aiki akan Dul'Ururu a yayin fafatawarsu a ƙarshen yaƙin sarakunan jinzidal. To wai daga ina matsalar take? Armad yana ji a ransa idan ya gano wannan matsalar to babu makawa zai gane dalilin da yasa idan ya saka mutane a cikin duniyar Negrinkinsa suke guduwa. Watakila kuma ya gano dalilin da yasa idan ya zuƙe izzar mutane suke dawo da ita.
"Ka gama?" Dul'Ururu ya tambaye shi. Sai dai kafin ya bada amsa yaji saukar sandar Dul'Ururu a fuskarsa.
Tartsatsin jan hasken yayi sama. Jini yayi feshi daga ko'ina a jikin Armad duk da cewa kawai fuskarsa aka daka. Duk da cewa jikinsa yana walkiya. Iska tayi jifa dashi can ƙasa cikin tsakiyar mayaƙan Ururu.
Armad ya daki ƙasa yayi sama ya ƙara faɗowa ƙasa tim. Inda ya faɗo yayi rami. Jikinsa ya juye ya dawo na mutane. Da ƙarfin hali yayi ƙoƙarin miƙewa tsaye amma jiri ya ɗebe shi ya kife akan fuska a ƙasa.
Mafi yawa idan suka dake shi a jikinsa na walkiya yana jin zafi amma ko kaɗan bayan jin ciwo balle har ya fitar da jini. Amma kaɗan daga ma'abota izza suna iya ji masa rauni su lahanta tashi koda kuwa yana walkiya. Misali Hidaya a faɗan su sanda yaje makarantar Babila. Yana da yaƙinin yayar tasa zata iya halaka shi koda kuwa yana walkiya. Yanzu kuma ga Dul'Ururu ya nuna shima zai iya lahanta Armad koda kuwa yana walkiya.
"Armad?" Nusi ta kwala masa kira daga inda suke faɗa da Diwani, hankalinta a tashe.
Ai kuwa tana ɗauke kai Diwani ya samu dama ya saukar mata da al'amudi a baya. Ƙasusuwan bayanta sukai ƙara. Nazára yana ji yana gani haka ya rabu da ita ya tsaida hankalinsa akan Binani domin yana ɗauke kai kwamandan zaiyi masa aiki.
Zaikid kuwa ya riga shagala da Yurba. Sunyi sama kawai sai wuta suke tashi. Zaikid yana amfani da takobinsa maimakon ƙoƙarin zuƙe izzar Yurba duk kuwa da kasancewarsa Wilbafos. Hakan yasa Armad ya ƙara faɗawa cikin tunani. Shin akwai wani abu da bai sani ba game da zuƙar izzar mutane? A baya sanda Hidaya ta fafata da Bihanzin da sauran sarakunan jinzidal bata yi ƙoƙarin zuƙe izzar su ba, maimakon haka sai ita ma ta fito da nata fasahohin suka fafata. Watakila Hidaya da Zaikid sun san cewa zuƙe izza bashi da amfani domin dai abokan karawarsu zasu iya dawo da ita.
Yana cikin wannan tunani ne yaji saukar Dul'Ururu akansa.
"Armad?" Fatima ta kwala ƙara.
Armad yayi ƙoƙarin kaucewa amma kafin ya motsa Dul'Ururu ya sauke masa sandar tsafinsa a kai. Wani haske mai ɗauke da ƙarfin izza ya shiga jikin Armad.
Tsahon dakiku numfashin Armad ya ɗauke kafin daga bisani ya fara gani dishi-dishi. A hankali ya yanke jiki ya faɗi. Bai san adadin dakikun da suke wuce ba sanda ya buɗe ido yaga Dul'Ururu tsaye akansa.
"Akwai kuɗi akan ka, Armad Wilbafos," inji Dul'Ururu. "Idan babu damuwa zan ɗauke ka."
Armad yayi ƙoƙarin tashi zaune amma ya kasa. Jikinsa kamar ba nasa ba. Babu wata gaɓa da take bin umarninsa. Wannan harin na ƙarshe da Dul'Ururu ya saukar masa kwata-kwata ba izza bace acikin kuma abin mamakin ba Negrinki bace. Dama dai abubuwan da suke bawa hari ƙarfi sune izza ko kuma Negrinki. Babu yadda hari zai samu ba tare dasu ba. Amma kuma ga wani hari Dul'Ururu ya saukar masa wanda babu izza kuma babu Negrinki acikinsa.
Armad yana da tabbas ba ruhinsa aka hara ba balle yace harin ruhi ne. Kuma hatta harin ruhi ai da izza ko Negrinki yake amfani. Kuma Dul'Ururu jikinsa ya hara, amma sinadarin da aka yi harin dashi shi ne bai gane ba. Shin wani sabon sinadari ne na musamman daga doron ƙasa ta farko?
"Taho wajen Dul'Ururul Ururiy," inji sarki Dul'Ururu, ya ɗaga hannu ya nuna Armad. Wata izza tsohuwa ta fara jan Armad wajen sarkin.
Armad yasan jikinsa yana gargara. Idan ya bari Dul'Ururu ya ƙara loda masa sandar tsafin to al'amarin ba zaiyi kyau. Ko ya kira Saif-Al-Barzak ta kawo masa agaji? To amma kuma hakan kamar ya dawo da Ƙaraiƙisu filin yaƙin ne wanda kuma bazai haifar musu da ɗa-mai-ido ba. Shin akwai fasahar miyura da zata yi amfani? Zaren Babbar Mutuwa ita ce fasaha mafi girma da miyura take da, shin tura sarkin cikin duniyar Negrinki abu ne mai kyau? Armad ya girgiza kai. Hakan kawai zai nunawa Dul'Ururu inda Haruta yake ne. A hakan ma filin yaƙin an fisu yawa to ina ga an ƙaro Haruta.
Sai dai kuma akwai mutun-mutumin dake tsakiyar miyura wanda Armad yake amfani dashi ya kirawo ruhin gidan Wilbafos...
Da sauri Armad ya tattara dukkan ƙarfinsa ya ciji harshensa jini ya fito. Ya dangwali jinin ya saka a goshinsa. Miyurar tayi haske inda takubba ukun dake kewaye da ita suka fara zagayawa. Mutun-mutumin dake tsakiya ya motsa. Kafin Armad ya ƙarasa hannun Dul'Ururu goshinsa ya tsaye gida biyu. Ɗigon jini ya fito ya juye izuwa mutum-mutumi riƙe da takubba biyu a hannu. Idan ka lura zaka ga a goshin Armad babu mutun-mutumi acikin miyurarsa sannan kuma takobi ɗaya ce ta rage.
Dul'Ururu ya ƙara ɗaga sandarsa zai bugawa Armad. Mutun-mutumin ya tare sandar da takobi biyu. Wata guguwa tayi jifa da Armad da dukkan wanda ke kusa gefe guda.
Bayan ƙura ta lafa sai mutun-mutumin da Dul'Ururu suka bayyana. Suna tsaye suna kallon juna babu wanda ya samu rauni acikinsu.
"Ruhi ne kai," Dul'Ururu ya gayawa mutun-mutumin. "Ruhi kuma yana biyayya a gare ni."
Yana rufe baki taskar ruhin dake saman kansa ta fara haske. Wani siririn layi ya bayyana akan iska ya haɗe taskar ruhin da sandar tsafin. Sannu a hankali sai taskar ruhin ta fara rage faɗi da girma. Ita kuma sandar tsafin ta fara baƙi. Idan ka lura zaka ga taskar ruhin shigewa cikin sandar take yi. Idanun Dul'Ururu suka fara sheki suna ƙara baƙi.
Ruhin Wilbafos ya jada baya ya juyar da takubban dake hannunsa zuwa al'amudi. A wani salo na ɓacin rai ya tashi sama ya sauka akan Dul'Ururu. Sarkin ya buɗa ya ɗan canja tsayuwa yana jiran ruhin ya ƙaraso.
Sai da ruhin yazo gab-da-gab zai daki Dul'Ururu sai sarkin ya zame gefe guda cikin tsananin sauri da kwarewa. Yana zamewa al'amudin ruhin ya wuce ƙasa. Kafin ruhin ya dawo da al'amudin, Dul'Ururu ya tashi sama ya bayyana a gabansa. Yasa sandar tsafinsa wadda a yanzu ta koma baƙa ya daki ƙirjin ruhin. Haka na faruwa kawai ruhin da al'amudin suka ɓace ɓat. Babu ƙara, babu jini, kawai ɓacewa ruhin yayi kamar dama babu shi a wajen. Armad ya sosa ido kamar bai yadda da abinda ke faruwa ba. Ruhin da yayi wa Uznu Ururu duka ɗaya ya halaka shi amma ya kasa yiwa Dul'Ururu komai.
Ɗorawa Abada ta kasa. Ruhin Wilbafos ya kasa. Zuƙe izza batai ba. Saif-Al-Barzak bata nan. Sannan babu damar amfani da Negrinki, to meye ya ragewa Armad kenan?
Kada a manta a dai-dai lokacin da Armad yake fafatawa da sarki Dul'Ururu a lokacin Rabi take ƙoƙarin karya kafin daya tsare fatima. A tsaye a bayan Rabi kwamanda Burjan ne, takobinsa a zare yana kallon Maruta ko zai kawo mata hari. Sai dai duk da ƙoƙarin da kowa yake yi wajen taimakawa Rabi da kare ta, idan muka dubi Rabin zamu ga tana zaune a gaban kafin tana kallon ƙasa. Idanunta hawaye ne suka ciko kamar zata yi kuka.
"Rabi?" Inji Burjan. "Sai kin hanzarta. Bana tunanin zasu iya riƙe kwamandun Ururu tsahon lokaci."
Burjan ya nuna inda ake fafatawa tsakanin su Armad da Ururu.
Rabi ko kaɗan bata ji abinda yace ba. Hankalinta ya riga ya shagala cikin tunani.
Burjan ya cije baki. Idan abin yaci gaba da tafiya a haka to babu makawa zasu yi zuwan banza domin kuwa babu wanda zai iya sai Rabi.
Sai dai kuma saɓanin yadda Burjan yake tunani, kwamandun Armad sun riƙe abokan karawarsu yadda ya kamata. Zaikid yayi can sama shida Yurba ba'a ganin yadda faɗan nasu yake kasancewa. Idan ka sakko ƙasa zaka ga Nusi da Diwani. Duk da ƙasusuwan bayan Nusi da Diwani ya karya ɗazu hakan bai bashi nasara akanta ba. Kada dai a manta tun can Nusi ta kware wajen haɗa magani da warkarwa. Tabbas bata kai matsayin Rabi ba, amma kuma dan wata karaya ko ƙonuwa ba zasu bata matsala ba. Da sauri ta shafa magani a bayanta lamarinda yasa ƙasusuwan da suka ɓalle suka dawo dai-dai. Zafi kuwa dama bata ji domin tun shigowarsu filin yaƙin tasha kwalbar magani wadda zata kashe duk wani zafi da zata iya ji.
"Haha.." Diwani yayi dariya. "Nusi Djinn, Nusi Djinn. Kina cikin ƴan kaɗan da suka kufce mana tun a wancan lokacin."
Nusi ta ɓata rai. Tunda suka fara faɗan kwamandan yake yarda irin wannan maganganu.
"Nasan sarai yadda akai kika fito daga Shadeniza. Zancen wai kin fito ne kafin a kulle ƙofa ƙarya ne."
Nusi ta yamutse fuska. A zahiri bata tuna hakikanin yadda ta fito daga garin ƙarƙashin ƙasa na Shadeniza. Abinda kawai take iya tunawa a lokacin shi ne abinda mahaifinta ya gaya mata wanda kuma shi ne mutumin da suka fito tare dashi. A cewar mahaifinta ita ƴar ƙabilar Djinn ce. Sai dai daga baya ya bayyana a gare ta cewa asalinta ƴar ƙabilar Kil'zanki ce.
"Hahah.." kwamandan ya kyalkyala dariya. "Da sannu zamu haɗe ku a guri guda muyi hukunci."
Ya ƙara kawo mata duka. Nusi ta saka rassan bishiya ta rufe al'amudin. Al'amudin ya kumbura ya fashe. Nusi ta haɗe yan'yatsunta guri guda lamarinda yasa rassan bishiyar suka fara girma suna rarrabuwa. Kafin kace kwabo sun rufe ko'ina tayadda babu wata ƙofa da wutar zata fita.
Al'amudin yayi nakiyarsa ya gama acikin kejin da Nusi ta saka masa.
Ana haka wani barangwal ya fito daga cikin ƙasa dai-dai bayan Diwani ya kawo masa wafta da ƙasusuwan hannunsa.
Diwani yayi tsalle sama ya bar al'amudin a ƙasa.
"Fasahar Noma," inji Diwani. "Kin kware a fasahohin gidan Djinn da Kil'zanki duk kuwa da cewa baki yi rayuwa dasu ba."
Kwamandan ya ɗanyi shiru yana tunani kafin ya numfasa. Ya nuna al'amudinsa a inda yake a ƙasa lamarinda yasa al'amudin ya fasa ta cikin rassa bishiyar ya taso ya dawo hannunsa.
"Mai zai hana ki dawo ɓangaren Ururu?" Inji Diwani.
Nusi tayi murmushi a lokaci na farko.
"Ni, na dawo ɓangaren Ururu?"
Nusi ta ɗan karkata kai kamar tana tunani.
"Mai zaku bani idan na dawo?"
"Abinda kika rasa," inji Diwani.
"Ni kuwa mai na rasa?" Ta tambayeshi.
Diwani ya fashe da dariya.
"Da gaske bakya iya tuna komai, ko? Amma baki taɓa tambaya ba?"
Nusi tayi murmushi mai ɗaci. Kamar akwai wanda zata tambaya.
"Kin fito daga Shadeniza duk kuwa da garin a kulle yake, kin zama sarauniya a sashin ikwatora ba tare da kin taɓa rayuwa a sashin ba, kina da fasahar Djinn da Kil'zanki... Duk da haka amma baki san komai ba? Kuma baki taɓa zama kin tambayi kanki dalili ba. Maikiro'Abbas shi ne ya fara gano ki saboda haka yasa sukai miki muƙami a garin Khan. Duk da cewa akwai wanda suka fi ki cancanta.
"Daga nan sai Daljari ya ankara dake. Muna sane da cewa ya tura Nazára ya taimake ki tun kina ƙarama. Ko kina tunanin akwai abinda zai ɓace mana a ban ƙasa ne? Duk abinda yake faruwa muna sane dashi kuma muna ganinsa. Sai dai kurum muyi kamar bamu gani ba. Amma dai kin san kuɗin ayrid da aka saka a kan ki akwai dalili ko? Baki da izzar da zaki samu wannan kuɗin da yawa haka."
Ba tare data sani ba ta juya ta kalli inda Nazára yake fafatawa da Binani. Tabbas idan akwai wanda zai san asalin labarin ta to Nazára ne. Amma kuma yariman yaƙi bayyana mata komai.
"Akwai wasu daga cikin mutane da suke ƙoƙarin amfani dake wajen cimma burinsu," inji Diwani. "Ina da tabbas Armad da gidan Wilbafos suna daga ciki. Sai dai a banza, tuni maɗaukakiyar masarauta ta gama mallakar komai. Yadda mutane suka manta ki da ƙabilar ki, yadda ke kanki kika manta kanki, haka zamu shafe ku a manta daku. Lokaci kawai muke jira."
Zuwa yanzu Nusi ta fuskanci kwamandan bashi da niyyar gaya mata wani abu mai amfani ba. Yana sane yake kwan-gaba kwan-baya a zancensa domin dai kada ta fahimta. Dama dai tasan akwai wani abu a dangane da ita wanda yasa baƙar guguwa ta zaɓe ta, amma har yanzu bata gane ko menene ba. Sai dai watakila hakan yana da alaƙa da garin Shadeniza da kuma kulle shi da akai. Koma dai meye amsar wannan tambaya sai sun fara ganin ƙarshen wannan yaƙi tukun. Domin idan ta mutu komai ya ƙare.
Sannan kuma surutun da kwamandan yake yi bai damu Nusi ba. Hasalima zata so yaci gaba. Musamman tunda dama zuwa tayi ta tsayar dashi kawai har su samu dama su karya kafin. Saboda haka bata damu ba idan zaiyi ta magana har zuwa sanda Rabi zata samu dama ta karya kafin.
A gefe guda kuma faɗan Nazára da Binani ya koma kamar wata takara. Kowa ƙoƙari yake ya samar da makamin da yafi na ɗan uwansa ƙarfi. Binani ya samar da ƙatotuwar guduma ta farin ƙarfe. Nazára ya tara yashinsa na ƙarfe guri guda ya cure shi a tsakiya yayi masa siffar guduma irin ta Binani. Kowa ya ɗauki gudumarsa ya kaiwa ɗan uwansa duka. Suna haɗuwa gudumar kowa ta tarwatse. Suka ƙara jada baya suka samar da takubban ƙarfe suka afkawa juna. Kafin wani lokaci sun lalata makamai sama da goma-goma amma ko kaɗan basu da niyyar tsayawa.
A gefe guda kuma Najunanu da Shísu sun saka Han'ibal a gaba. Najunanu ya samar da wani farin ruwa wanda saboda haskensa kana iya ganin kanka a ciki kamar madubi. Duk girman ƙawanyar wutar da Han'ibal ya harbo sai kaga ta daki ruwan ta narke. Idan ma tayi ragowa sai kaga ta rage girma sosai da sosai. Shi kuma Cokali sai ya zuƙe ta cikin littafinsa.
Ibraham Nil da Suwainah basu shigo yaƙin ba. Suna gefe suna nazari. Ibraham Nil dama bai shiga ba tunda aka fara, Suwainah ita ce mai giggiwa sai dai watakila jan kunnen da Armad yayi mata yasa ta ladabtu.
Wani faɗa mai ban sha'awar kallo shi ne tsakanin Ayubu da jan doki da kuma mutun-mutumin Armad. Watakila maimakon faɗa zaifi kyau a kira abin da kallon-kallo domin kuwa babu wanda acikinsu har yanzu ya kaiwa ɗan uwansa hari ko guda ɗaya.
"Na kasa gane tsakaninka da Armad," inji Ayubu. "Idan tarihi yazo min dai-dai a lokacin yaƙin sarakunan jinzidal da Armad da Bihanzin suka haɗa kai suka kashe ubangidanka Daljari. Meye yasa ka shigarwa Armad wannan faɗan?"
"Baza ka gane ba, Ayubu," inji jan doki. "Kasan akwai abinda butulu basa iya ganewa duk ƙoƙarinsu."
Maimakon Ayubu yaji haushin maganar sai kawai ya fashe da dariya.
"Butulu dai, butulu dai, kowa yace butulu amma babu wanda yake tambayar dalilin da yasa akai butulcin. Kasan masu iya magana sukan ce idan kaga anyi wa mutum butulci to ka binciki mutumin. Tunda kake ka taɓa ji ance wani ɗan gidan Wilbafos ya shiga yaƙi saboda wani wanda ba ɗan ƙabilarsa ba? Armad zaiyi komai saboda Fatima ko Hidaya ko kuma wani Wilbafos, amma ka sani dani dakai a matsayin banza muke a wurinsa. Yanzu kana tunanin, jan doki, da kai aka kama ake ƙoƙarin sare maka kai Armad zaizo yayi yaƙi saboda kai? Ku dawo cikin hankalinku, ku fahimci yadda al'amarin yake. Da Wilbafos da Ururu duk abu ɗaya ne, kansu kawai suka sani basu damu da wani ba."
Jin haka jan doki ya ɗaga kafaɗa. "To naji. Watakila duk abinda ka faɗa haka ne gaskiya ne, amma kai mai ya kawo ka wannan yaƙi? Kazo ne saboda kiyayyarka da Armad da gidan Wilbafos, ko kuma kazo ne saboda wata manufa?"
"Nazo ne saboda na taimaki Ururu su kassara Armad," inji Ayubu. "Idan Ururu sukai nasara zasu naɗa ni muƙamin sarkin jinzidal sannan kuma a lokaci guda sun kawar min da Armad."
Jan doki ya haɗe gira. Wato Ururu alƙawarin sarkin jinzidal sukai wa Ayubu shi yasa yazo. Dama dai yayi tunanin akwai wani abu a ƙasa tunda yaga Ayubu da Iluru sunzo.
"Kai mai zaka ƙaru dashi idan Armad yayi nasara?" Ayubu ya tambayi jan doki.
"A zahiri babu abinda zan karu dashi," inji jan doki. "Amma nazo ne bisa umarnin shugabana Nazára. Bana tunanin zaka fuskanci mai hakan yake nufi."
Ayubu yayi dariya.
"Ba lalle na fahimta ba gaskiya tunda ni na dawo daga rakiyar makauniyar biyayya. Amma ina so na baka goron gayyata zuwa sabuwar daular da zamu gina bayan wannan yaƙi. Kazo kayi mubaya'a mu baka ƙasa da mulki da mata. Baka buƙatar kaci gaba da yiwa ɗa biyayya bayan ka yiwa ubansa."
"Zan duba na gani," inji jan doki. "Amma yanzu dai ina buƙatar kada ka motsa daga inda kake domin akwai layi a bayanka."
Ayubu ya waiwaya baya inda jan doki ya nuna. A lokacin ya lura akwai wani layi an zana shi akan ƙasa dai-dai bayansa. Babu wanda yasan sanda aka zana layin ko kuma waye ya zana shi, amma dai akwai layi a wajen.
Ayubu ya ɓata rai. Tabbas yaji labarin fasahar jan doki. Mutumin sammai ne wanda yake iya sarrafa fasahar Negrinkinsa. Babu wanda yasan hakikanin yadda abin yake tunda babu wanda ya taɓa faɗawa komar jan doki ya tsira. Amma dai da dama suna ganin fasahar tana da alaƙa da nauyi da kuma ƙasa. Iluru ya gayawa Ayubu cewa a duk sanda jan doki zaiyi amfani da fasahar ana ganin tsauni ya bayyana, sai dai yau babu tsaunin, kawai dai layin ne. Hakan yasa aka shiga kallon-kallo tsakanin jan doki da Ayubu.
Daga can gefe kuma faɗa ya ɗau zafi tsakanin Iluru da Asifu da Shísu. Zaka iya cewa babu wanda suke yi da gasken-gaske kamar su. Iluru ya zama basamude ya baje filin yaƙi da ƙafafunsa. Duk inda yayi sai dai kaga na ƙasa na gudu.
Girman basamuden baya bawa Asifu tsoro. Yana haye kan hadarinsa yana binsa duk inda yayi. Shísu yana gefensa yana taimaka masa.
Suna matsowa, suna matsowa basu san sanda suka taka ƙanƙarar da Maikiro'Abbas ya samar ba. Ƙafar Iluru ta burma ciki. Kafin ya zaro ta Asifu ya dira a kafaɗarsa ya kafta masa sara. Shísu ya ɗaga hannu sama inda nan take takobin ta fara haske. Da farko bata iya ratsa fatar Iluru ba, amma tana fara haske sai kurum ta shige ciki. Basamuden yayi ƙara mai razanarwa. Dole Asifu da Shísu suka rufe kunnuwansu. Iluru yasa hannu ya zare takobin daga cikin jikinsa sannan ya kai musu wafta. Sukai tsalle sama dan su kauce amma kafin su ƙarasa basamuden ya damƙi ƙafar Shísu. Ya wujijjiga ba-ikwatoren a sama sannan yayi jifa dashi ɓangaren Maikiro'Abbas.
A fusace Iluru yabi Shísu da guda zai tatsile shi. Duk inda ya taka sai kaji ƙasa tana girgiza, ƙanƙarar tana darewa. Mayaƙan Maikiro'Abbas suka tare shi da sara da suka da harbi. Amma ina, abin ba ɗaya ba, girman jikin ma ba ɗaya ba. Duk inda Iluru ya wurga hannu sai kaga ya share mayaƙan. Babu wanda ya iya tare shi har sai da ya ƙarasa wajen Shísu. Ya ɗaga ƙafa zai tatsile shi amma Asifu ya bayyana a gaban Shísu ya tare ƙafar basamuden da takobinsa.
Basamuden ya danna Asifu da ƙarfin tsaya da niyyar ya haɗa da takobin da Asifu da Shísu duk ya danne, amma Asifu ya saka hannu biyu ya riƙe takobinsa ya tare shi.
A wani salo na ƙeta sai Iluru ya danna takobin da ƙafa ɗaya sannan ya ɗaga ɗayan ƙafarsa dake ƙasa tayadda dukkan nauyinsa zai dawo kan takobin. Kafin Asifu ya ankara takobin ta ɓalle gida biyu, Iluru ya diro akan su. Dole yayi amfani da jikinsa ya kare Shísu wanda tuni ya suma. Basamuden ya danne shi a ƙasa. Tun yana gani dishi-dishi har sai da ya daina gani gaba ɗaya.
"Anan dama zan rasu?" Asifu ya tambayi kansa gaba da zai suma.
Shi kuwa Iluru ƙafa ya saka ya buga su gefe.
Mayaƙan Maikiro'Abbas sukai kukan kura suka afka kan Iluru a fusace. Kafin su ƙarasa basamuden ya durkusa ya daki ƙasa da hannunsa. Ƙarfin dantsensa yasa ƙasa ta daddare, mayaƙan suka faɗa ciki. Iluru ya miƙe tsaye yayi kururuwa yayi ihu kamar yana nunawa duniya ƙarfin denizawa.
Sai dai hakan ya janyo hankalin manya.
"Kai," inji Maikiro'Abbas. Babu wanda yasan ya akai ko kuma yaushe amma sarkin ya bayyana a gaban Iluru. "Sarkin jinzidal ne kai, ni ne abokin karawarka."
Iluru ya durkuso ya kalli Maikiro'Abbas. Kamar yana nuna amincewarsa da abinda Maikiro'Abbas ya faɗa sai ya dunkule hannu ya ɗaga shi sama sannan ya gyara tsayuwa.
Maikiro'Abbas ya buɗe tafin hannunsa na dama. Wata ƙawanyar ƙanƙara ta bayyana akai. Ya ɗaga hannu ya dannawa Iluru ita. A nasa ɓangaren, Iluru samar da ƙatotuwar ƙusar mairakana yayi ya tari ƙawanyar Maikiro'Abbas.
Suma haɗuwa ƙusar ta shige cikin ƙanƙarar ta fice ta baya a ƙanƙare. Ƙawanyar ƙanƙarar ta wuce ta daki Iluru a kirji, a yayinda ƙusar mairakana ta wuce ta caki wuyan Maikiro'Abbas. Dai-dai inda ƙanƙarar ta taɓa Iluru yayi fari fat. Iluru ya buɗe baki zaiyi ihu amma tuni dukkan kirjinsa ya daskare. Ƙanƙarar ta bazu ko'ina ta cinye jikinsa cikin ƴan dakiku. Idan ka hange shi daga nesa sai ka rantse mutun-mutumin ƙanƙara ne aka haɗa. Ita kuwa ƙusar data caki Maikiro'Abbas tarwatse tayi tunda daman ta zama ƙanƙara.
Maikiro'Abbas yayi tsalle saman kan Iluru ya daki kan basamuden da ƙafa. Nan take basamuden ya tsatstsage sannan ya fashe ya tarwatse. Kafin ƙanƙarar ta zuba ƙasa Maikiro'Abbas ya juya a sama ya dunkule hannu ya daki iska ya tarwatsa ta tayi ko'ina. Can sai kaga kunne a ƙanƙare, can kaga yatsa, can kaga ido, gaba ɗayan Iluru yayi daga-daga ya zama babu. Ko binne shi iyalinsa baza su samu damar yi ba.
"I...I....Iluru ya mutu," wani sadauki ya faɗa cikin kinkina. Kana gani kasan sun kasa fahimtar abinda ke faruwa. Musamman duba ga cewa Iluru fa sarkin jinzidal ne guda. Ace duka ɗaya ya gama dashi. Sai dai kuma hakan ba abin mamaki bane idan akai la'akari da wanda suke faɗan.
"Maikiro!"
"Maikiro!!"
"Maikiro!!!"
Mayaƙa suka hau murna da ihu.
A nasa ɓangaren Maikiro'Abbas bai koma wajen daya baro ba. Tsayawa yayi anan yana kallon Dul'Ururu da mayaƙan Ururu kamar yana ce musu idan sun isa su taho. Ga dukkan alamu sarkin ya fara gajiya da jira.
A dai-dai lokacin da Iluru ya zama ƙanƙara ya tarwatse a lokacin faɗa ya ƙara tsamari a ɓangaren Ururu. Ganin abinda Maikiro'Abbas yayi wa Iluru yasa Dul'Ururu ya taka a fusace wajen da Armad yake kwance da niyar ɗaukar fansa.
Armad yaji tahowar sa. Jikinsa ya ɗan fara dawowa dai-dai saboda haka yayi ƙoƙari ya miƙe ya fuskanci Dul'Ururu. Mayaƙan dake gurin suka basu guri.
"Mutu, Armad Wilbafos." inji Dul'Ururu. Ƙarfin izzar Kamalar-ruhi ta shiga sautinsa tayi kan Armad.
Armad ya ɗaga hannu ya nuna shi. "Mutu, Dul'Ururul Ururiy."
Ƙarfin ikon Armad ya fito ya daki na Dul'Ururu. Wuta ta tashi tayi sama.
Comments
Post a Comment