Nusi tana bayyana akan doron ƙasa ta huɗu bata zame ko'ina ba sai garin Riyan. Cokali yana biye da ita. Har yanzu basu cewa juna komai ba. Kana ganin fuskokinsu kasan akwai damuwa a tattare dasu.
Can dai bayan sun shiga cikin garin suna tafiya acikin wani loko Nusi ta kasa daurewa ta dubi Cokali ta ce, "ka gayamin gaskiya, ka yadda da abinda na faɗa ko kuwa?"
Cokali ya buɗe baki zai bata amsa amma ganin yadda fuskarta tayi yasa ya rufe bakinsa yaci gaba da tafiya ba tare da yace komai ba.
"Tambayarka fa nake yi."
"Eh? Ah... zan iya yadda mana kinsan abu ne a duhu kuma fahimta fuska...."
Ta daka masa wata uwar harara wadda tasa dole yaja bakinsa yayi shiru.
Can bayan ɗan lokaci sun ci gaba da tafiya Nusi ta ƙara waiwayowa ta kalleshi a fusace. "Wai kana nufin ma ƙarya nake yi kenan? Ai shikenan."
Cokali ya tari gabanta da sauri. "Tsaya kiji. Kefa ƴar'uwata ce, kuma ni sabida ke nake tafiyar nan, bani da wani dalili guda ɗaya tak da zai sa na zauna idan bakyanan. Sabida haka zancen da gaske kike ko ba da gaske kike ba bai taso ba. Kawai a daina shi."
Nusi ta ƙura masa ido tsahon lokaci kafin ta girgiza kai ta shige gaba.
Ba jimawa suka iso wani gida a ƙarshen layin. Kai tsaye Nusi ta kwankwasa ƙofar gidan sau uku sannan ta koma gefe ta tsaya.
Cokali ya dubeta a nutse ya ce, "amma fa dan nace ke nake bi baya nuna zaki ringa yin abu babu bayani. Har yanzu baki gayamin wajen wa muka zo ba."
"Yanzu zaka gani. Mai kake ci na baka na zuba?"
Ai kuwa ba jimawa aka zo aka buɗe ƙofar aka leƙo. Ganin fuskar Nusi tasa wanda ya buɗe kofar yayi jim na ƴan dakiku kafin yai sauri ya juya ciki a guje. Cokali yana jin takun mutumin ya rankaya cikin gidan da gudu sannan cikin abinda bai wuce dakiku kaɗan ba ya dawo tare da wasu mutane sama da goma. Dukkanin su suka rankayo wajen Nusi da fara'a da murna. Mata biyun dake cikin su suka garzaya a guje suka rungume Nusi cikin murna da shewa. Su kuwa mazan zubewa sukai a ƙasa suka kwashi gaisuwa.
Can bayan ƴan dakiku matan guda biyu suka saki Nusi suma suka zube a ƙasa suka kwashi tasu gaisuwar.
"Barka da zuwa, Nusi-ya, izza taki sarauta taki."
Idan ka lura sosai zaka ga ɗaya daga cikin matan biyu katuwa ce mai manya-manyan damatsa kamar ƴar dambe. Ba wata bace illa babbar kuyangar Nusi, Zanshika, wadda akafi sani da Giwa.
Acikin mazan akwai sarkin Bai, Baiban Rayaya, akwai Inyaya takobin jini, akwai mai unguwa Shísu, akwai sarkin yaƙi Barilu.
Rayaya mutun ne gabjeje mai manyan kafadu da damatsa, kana ganinsa kaga sadauki kirar samudawa. Inyaya yana ɗauke da takobi rataye a wuya ta kwanto ta barin hagu. Idan ka dubeshi zaka ga mutun ne mara girma sosai, baƙar fata.
Shi kuwa Sarkin yaƙi barilu Dattijo ne mai yawan furfura amma hakan bai hanashi ɗaukan wata gabjejiyar guduma a kafaɗarsa ba. Kai kana gani kasan kullum anan wajen take a sakale. Watakila ko bacci zaiyi anan yake barinta.
Mai unguwa Shísu mutun ne kirar bakaken fulani. Yana tsaye a gefe yana kallon Nusi babu wani makami a hannunsa, sannan kuma ga kunyar fulani nan a tattare dashi kai kace idan aka saka masa hannu a baki bazai tauna ba. Amma abin mamaki shi ne ya fara magana.
"Nusi-ya, barka da dawowa."
A wannan lokaci sarkin Bai dasu Inyaya da Giwa suka shige gaba, su kuma ragowar mutun taran suka tsaya a bayansu.
Nusi ta dube su baki a cije tace, "wai ba nace ku koma gida wajen iyalan ku ba?"
Sarkin Bai wanda zaka iya cewa shi ne babbansu ya durkusa ƙasa ya fara bayani, "Nusi-ya, bamu da kowa a gida daya fiki. Yadda muka fito dake haka zamu mayar dake domin kuwa har yanzu kece shugabar sashi na shida na ikwatora, kuma zaki ci gaba da kasancewa akan muƙaminki har zuwa sanda za'a sake zabe nan da shekaru hamsin. Kuma ke zamu ƙara marawa baya."
Giwa ta amsa da cewa, "na tabbatar waziri da Galadima suna kula da fada yadda ya kamata. Kuma basa buƙatar mu."
Nusi tayi ajiyar zuciya sannan bayan ɗan lokaci tayi murmushi mai cike da godiya.
"To, al'umma ta, kowa ya shirya akwai aiki babba a gaban mu. Armad ya ɓata kuma mu zamu nemo shi duk ma inda ya shiga."
***
Idan muka koma ɓangaren bango zamu hango wani ɗan-wadan mutun mai fuska cike da baƙin gemu yana tafe yana dogara ɗan-sanda. Wani abin mamaki shi ne yadda duk wata gaɓar bangon ta cika da matakan tsaro daga rundunar mayaƙan Ururu. Zaka iya cewa hatta jiragen ruwa na matafiya ba'a bari su wuce ba tare da sunsha caji ba. Kuma ko'ina haka abin yake babu wani banbanci. Komai yasa Ururu suka turo mayaƙa wannan gaɓoɓi?
Shi dai bango gangar ruwa ce data taso tun daga doron ƙasa ta farko har zuwa ta bakwai. Akansa ake tafiye-tafiye daga wata ƙasa zuwa wata. Akwai bango ɗaya a ɓangaren kudu, akwai ɗaya a ɓangaren arewa. Akwai gaɓar ruwa akan iyakar kowacce ƙasa (a ɓarin kudu dana arewa), wanda idan ka lissafa zaka ga ya tashi gaɓa goma sha-biyu kenan muke dasu. Yazo a tarihi cewa akwai duniya ta daban a tsakanin wannan bangwaye biyu wadda ake kira da duniyar ikwatora. A zahiri babu wani mahaluki dake rayuwa a sashin kudu ko arewa daya taɓa taka ƙafa a sashin ikwatora sai yan ƙalilan, amma mutane sun yadda akwai sashin kamar yadda suka yadda akwai doron ƙasa ta farko duk da babu wanda ya taɓa zuwa. Babban dalilin da yasa ba'a iya zuwa sashin ikwatora shi ne ba'a iya ratsa bango. Shekaru da dama da suka wuce ƴan-ƙalilan daga cikin masu gangancin da suka shiga sun ɓace ɓat an neme su an rasa.
A lokaci guda suma al'ummar dake sashin ikwatora basu da damar fitowa su shigo duniyar sashin kudu ko arewa. Gama-garin mutane basu san dalilin da yasa ba'a iya shiga ko fita daga sashin ikwatora ba. Kaɗan daga cikin masana wanda suke da masaniya akan kurkukun bango suna ganin ita ce dalilin da yasa ba'a iya shiga, to amma abin ba haka yake ba. Eh, akwai kurkukun bangon. To amma shi kansa bangon ruwan akwai tsafi a jiki. Kuma zamu yadda da haka idan muka lura cewa a sashin ikwatora sarki ƙaraiƙisu shi kaɗai ne yake da hanyar ratsa bangon ya fita daga sashin ikwatora zuwa kurkukun bango. Ta waje kuma Babara shi kaɗai ne wanda muka ga ya taɓa ratsa bangon. A ƴan shekarun baya munga Armad yayi ƙoƙarin ratsawa da jikinsa na walkiya amma ya kasa. Sai daga baya daya haɗa da sabuwar fasaharsa ta Kaban'shisu sannan ya iya shiga.
To wannan kenan.
To amma kuma akwai wani mutun guda wanda yake shige-da-ficensa a sashin ikwatora ba tare da wata matsala ba kamar ɗakinsa. Kuma ba shi kaɗai ba, harma wasu yake tafiya tare dasu. Wannan mutun ba wani bane illa Ikenga. Ko ta wacce hanya yake amfani da ita, oho. Kuma tunda ba shi kaɗai muke gani ba kaga dole mu tambaya shin Ikengan ne yake buɗe hanyar idan zasu shiga ko kuma wani ne daga cikin mabiyansa.
Muhallish shahid anan shi ne indai Babara ya shiga cikin bangon ta irin hanyar daya shigar da Armad a shekarun to lallai iyakacin sa kurkukun bango, domin kuwa bashi da hanyar shiga sashin ikwatora. Kuma aikin da Armad ya bashi a sashin ikwatora yake. Hasalima wannan shi ne dalilin da yasa Babara baiyi saurin shiga bangon ba. Idan ta ɓaci babu yadda zaiyi to akwai wani mutun mai suna Boka Sakaradisa (wanda shi ne ya canji Babara daga muƙaminsa na sarkin duba), wanda Babara zai yiwa magana domin ya samar masa da hanyar shiga. To amma sai ya zama dole. Domin kuwa kwata-kwata Babara baya son wani abu ya ƙara haɗa shi da ƙungiyar duba.
Ganin mayaƙan Ururu sunyi dandazo a wajen yasa Babara ya dakata. Watakila idan yaci sa'a su samar musu da hanyar shiga tunda yaji wasu daga cikin sojojin suna cewa sashin ikwatora zasu shiga kamfen.
Yau kwanan Babara uku a wajen yana zagaye yana zuba ido amma babu wani labari.
Wataran ɗaya daga cikin sojojin ya dakawa Babara tsawa. "Kai, mai kake yi anan tun juya?!"
Duk da akwai mutane a wajen amma dole kowa hankalin sa zaifi tafiya kan wada.
"S...sannu ku da aiki, yan yaroki, jirgi na nake jira har yanzu bai ƙaraso ba." Inji Babara cikin kinkina da tsufa.
Da haka suka rabu da Babara ya ƙara kwana biyu a wajen. Daga ƙarshe da yaga sun fara gane shi sai ya koma can nesa ya shiga cikin bishiyu yake hangosu da yanayin izza.
A rana ta gaba haƙansa ya cimma ruwa. Yana zaune yaga wasu manya-manyan mayaƙa masu muƙamin kyaftin sun bayyana. Ba jimawa suka zuba dutsen ayrid mai mataki na goma da kuma mangwaron negrinkin suka fara kiran ɗalasimai. Jim kaɗan ƙofa ta bayyana a jikin bangon. Ba'a hango cikin ƙofar amma Babara yana ji a jikinsa yasan inda ta nufa. Nan take Babara ya sauya kamanni ya zama dogo sannan ya zira kayan daya kwata daga wani soja daya kwantar a daji, ya garzaya ya shige cikin tawagar a matsayin sojan Ururu.
Bayan ɗan lokaci ana iface-ifacen yaƙi sai kyaftin sukai kukan kura suka faɗa cikin ƙofar, sojoji suka bi bayansu da makamai a zare. Sabida sauri da hayaniya da kuma hargowa babu wanda ya kula da shigar Babara. Duk da Babara ya ƙara tsayi da kafa uku da sun lura da zasu gane.
Ba jimawa suka bayyana a bayan ƙofar. Koda Babara ya kyalla ido yaga babu ƙanƙara nan take ya gane cewa ba'a cikin kurkukun bango suke ba, lallai suna cikin sashin ikwatora, amma bai san doron ƙasa ta nawa ba.
Abin mamakin shi ne akwai dubban mayaƙan Ururu sanye da baƙin kaki sun taru a wajen. Akwai kofofi guda goma sha ɗaya duk irin wanda Babara ya shigo ta ciki sun buɗe suna ta tuttulo mutane cikin wajen.
Wajen dai yayi kama da ɗakin taro sabida a kewaye yake. To amma girmansa yafi na duk wani ɗakin taro da Babara ya taɓa gani. A ƙalla ko a yanzu akwai mayaƙa dubu biyar da doriya a wajen, kuma ƙaruwa kawai suke yi. Cikin sa'a guda sai da wajen ya cika taf babu masaka tsinke. A halin yanzu akwai akalla mutun dubu goma a wajen suna ta iface-ifacen yaƙi da shewa.
Ba jimawa daga can ƙarshen filin wani waje ya fara haske. Ana haka gadon aba'i ya bayyana acikin hasken yayi sama can kololuwa, tayadda kowa zai iya ganin abinda ke kai. A samansa akwai mutun biyu suna sanye da baƙar alkyabba samfurin mayaƙan Ururu. Ita dai wannan alkyabba an ɗinka ta da audugar jamsika mai kaurin gaske. Tana da faɗi kamar malun-malun amma kuma hannuwanta a matse suke. Wuyan anyi masa ado da bezar aljanin kifi. A bayan kowacce akwai rubutu. Inda na ɓangaren daman aka saka 'ASHURA' da manyan baki sannan daga ƙasa aka saka lamba biyar (5) da yaren Aldurish. Idan ka tsaya tsam zaka ga wannan mutun ba wani bane illa mafarauci, wato sarkin doron ƙasa ta biyu - Dul'Ururu.
Ɗayan kuma a bayan rigarsa an saka 'ASASIN ZERO' da manyan baƙi. Sannan daga ƙasa an saka lamba 9 da Aldurish. Wannan mutun ba wani bane illa Ibraham Nil wanda yayi amfani da Suwainah ya kwafi miyuwar Armad, harma yake ƙirƙirar mutun-mutumi wanda suke iya amfani da wannan miyura. Rukunin ASASIN ZERO dai rukuni ne wanda basa shiga harkokin mutane, ko a sama ko a ƙasa. Hakan nema yasa ba'a sansu ba. Aikin su kaɗai shi ne hana mutane hawa sama zuwa doron ƙasa ta biyu data farko. Suna zaune a KWAZAZZABON MUTUWA dake tsakanin doron ƙasa ta farko data biyu, da kuma GADAR ZARE dake tsakanin doron ƙasa ta biyu data uku, sun zuba ido shekara bayan shekara, ƙarni bayan ƙarni, zamani bayan zamani tun daga Farkon Lokaci har zuwa Dogon Zango zuwa Rawar Sani. Suna nan zaune suna gadi babu wani mahaluki daya taɓa gilmawa ta inda suke ya tsira da ransa.
Wannan lamba kuma tana nuna a rukunin ASHURA Dul'Ururu shi ne na biyar a ƙarfi. A rukunin ASASIN kuma Ibraham Nil shi ne na tara.
Mayaƙan na ganinsu suka fashe da kuwa da amshi irin na yabo. Suna kiran sunayensu suna kurantasu kai kace ababen bauta ne. Bayan ɗan lokaci Dul'Ururu ya ɗaga hannu sama. Nan take kowa yayi tsit kamar mutuwa ta gilma.
Cikin murya mai kaushi da amo kamar ana hura wuta Dul'Ururu ya fara bayani, "a kamfen na farko mun yadda a killace sashin ikwatora a basu dama su ci gashin kansu. To amma a yanzu wannan yarjejeniya tazo ƙarshe. Daga bana za'a fara jinzidal a sashin ikwatora."
***
A can doron ƙasa ta biyar kuwa, a garin Linta dake tsohuwar daular rafiyawa ta marigayi sarki Daljari, akwai wani wajen taruwa a sha fura da nono. Wajen ya haɓaka har yakai akan iya saida abinci da kayan makulashe. Bayan ɗakin da aka gina a tsakiya ake taruwa ana cin abinci, a yanzu anyi wasu ɗakunan a gefe inda kwastoma zai iya kamawa yayi bacci ko wanka. Sunan wannan wajen cin abinci Shagon Tasa. Mai wajen tsoho ne wanda ake yiwa inkiya da Jar Miya. Yana da ma'aikata guda biyu. Dukkansu sun manyanta tayadda idan ka ƙura ido baza ka rasa silin furfura a gashin kansu ba. Dan ma suna dabara suna rufewa da izza a ɗanyi kwalliya.
Ko a wannan lokaci ɗaya daga cikinsu yayi wa gemun sa ƙunshi zuwa ja. Dukkansu kayan jikinsu yar-shara ce mara tsada, babu wata kwalliya a jiki.
A dai-dai wannan lokaci wani murdadden saurayi ne yake shan fura acikin wajen daga kan wata kujera a baya. Saurayin ya rufe fuskarsa da rawani tayadda a duk sanda zai kurbi furar sai yaja rawanin ƙasa domin ya samu damar kai ƙoƙon bakinsa.
Minti goma saurayin ya ɗauka ya gama da furar. Bayan yayi gyatsa ya miƙe ya isa kan teburin Jar Miya ya biya ayrid goma sha biyu sannan ya juya zai fita.
Har yakai bakin ƙofa sai mutumin nan mai ƙunshi a gemu ya ɗauki kwanon tasa ya cilla masa. Kwanon ya tafi kai tsaye ya daki bayan saurayin wanda ya juyo a fusace. Ba tare da cewa komai ba shi ma ya ɗauki kwanon ya cilla wa mai jan gemun inda yaci sa'a ya same shi a kai ji kake kwas. Ga dukkan alamu abin ya fusata mai ƙunshin duk kuwa da shi ne ya fara tsokanar. Nan take yayi tsalle ya haura ta saman teburin ya cafi kwalar saurayin suka fara kokawa. Kafin kace kwabo waje ya hargitse. Tun Jar Miya yana iya magana har ya koma gefe. Shima ɗaya ma'aikacin yayi ƙoƙarin rabawa amma ya kasa.
Kai daga karshe dai aka tuje rawanin kan saurayin. Abin mamaki ba wani bane illa Nazára. Idan ka matso kusa zaka ga mai jan gemun ba wani bane illa kwamanda jan doki.
Duk da haka basu rabu ba, har saida hadari mai ɗauke da ruwan zafi ya fara haɗowa a iyakacin saman kansu sannan suka rabu kowa ya jada baya suna huci, kai kace tsoffin karnuka.
Dattijo Jar Miya ya daka musu tsawa. "To wallahi idan baku rabu ba zan kira ƴan-sanda."
Asifu ya ƙarasa wajen Jar Miya ya raɗa masa magana a kunne lamarinda yasa tsohon yayi jim yana tunani kafin daga bisani ya gyaɗa kai ya juya ya tafi. Asifu ya juyo wajen su Nazára. Yana ƙarasowa ya fashe da dariya. "Hahaha... yarima yarima, tun yaushe kasa muke ta jiranka anan, dole jan doki ya naushe ka."
Da wannan suka sarara aka nemi waje aka zauna. Shima Nazára ya sakko ya saki fuska. Amma har yanzu jan doki muzurai yake baice komai ba.
Can dai Nazára ya buɗe baki ya fara da cewa, "ahh... kuyi haƙuri. Abubuwa da dama sun faru amma har yanzu muna kan bakanmu."
"Yi bayani." Inji jan doki kai tsaye.
Nan fa Nazára ya kwashe duk abinda ya afku tun bayan haɗuwarsa da Armad har zuwa kurkukun lokaci ya gaya musu.
Asifu ya dube shi a nutse ya ce, "ina Nusi?"
Nazára yayi murmushi tare da girgiza kai, ya ce, "idan kaga Nusi ta rabu da Armad to mutuwa tayi. Kaga sabida haka dole mu shigo da Armad cikin shirin indai muna neman haɗin kanta."
"Ina Cokali da Iliyasis?" Inji jan doki.
Nazára yayi ajiyar zuciya. "Suna inda Nusi take."
Asifu ya dunkule hannu ya ce, "amma kana ganin anya kuwa shirin nan bazai samu matsala ba kuwa? Komai fa yana da alaƙa da Nusi. Kada ka manta dalilin da yasa baba Dalja yasa aka raineta harta girma ta kawo haka."
Nan fa wajen sukai shiru kowa yana tunanin mai ya kamata ayi. Bayan ɗan lokaci Nazára ya girgiza kai a hankali ya ce, "watakila da tun wuri mun gaya mata halin da ake ciki bamu ɓoye mata komai ba da haka bata faru ba."
"To ai umarnin Baba Dalja aka bi na ƙin gaya matan, kuma nasan dole akwai hikima acikin hakan koda a yanzu mu bamu gani ba."
Haka dai wadannan mutun uku suka ci gaba da tattaunawa akan Nusi. Daga bisani tattaunawar ta canja salo.
Nazára ya dubi jan doki ya ce, "wai har yanzu baka gano inda Kashin Shanu da Iskar Sahara suke ba? Dole muna bukatar ƙarfinsu. Kuma ace a salsan baba Dalja kawai Farin Yashi muka gani ai bazai yiwuba. Ka ƙara dubawa Jan Doki, ina kyautata zaton suna nan har yanzu a duniya domin bana ganin zasu mutu ta sauki."
Jan Doki ya kaɗa kafaɗa, ya ce, "ai ashe kasan amfanin mu da zaka bar mu anan muna saida fura."
Nazára yayi murmushi. "Wai kai har yanzu baka haƙura ba. Na gaya maka matsala aka samu ta kurkukun lokaci, a'a."
To da wannan suka kammala hirarsu. Jaruman biyu suka yiwa Jar Miya sallama. Kwamanda jan doki har da kuka. Aka kawo musu dawaki suka hau suka rankaya izuwa garin Tarara wanda yake yamma da inda suke.
Wani abin mamaki shi ne ko caje su ba'a yi ba a ƙofar garin. Kawai Asifu ne ya ɗan buɗe fuskarsa masu gadin suka ganshi ai kuwa nan take suka risuna suka buɗe musu kofa. Haka ma acikin garin duk inda sukai kawai gani zakai ma'aikatan da masu tsaron suna risuna musu. Wato baka buƙatar bayani kasan cewa kowa a garin yasan fuskar Asifu da Jan Doki.
Garin Tarara dai ɗaya ne daga cikin garuruwan dake tsohuwar daular rafiyawa. Sabida haka ganin cewa an san su Jan Doki ba abin mamaki bane, abin mamakin shi ne yadda ake girmama su kuma ana risuna musu duk kuwa da cewa ba sune akan mulki ba. Sai dai mai karatu zai iya cewa juyin mulkin da Bihanzin yayiwa Daljari bai kammalu ba, domin kuwa gashi har yanzu tsoffin kwamandun Daljari suna da iko a garuruwansu. Watakila hakan ya samo asali ne daga halin ko-in-kula da sarki Bihanzin ya nunawa daular rafiyawa. Tunda yaci su da yaki babu wani babban kwamandan sa ko kuma ɗansa daya tura daular domin mulki. Kai zaka iya cewa kwata-kwata babu wani hobbasa da Bihanzin yayi a zahiri ko kuma a baɗini na karkade ikon baba Dalja daga garuruwan da marigayin ya mulka. Zamu kula da hakan idan mukai duba da yadda Nazára yayi sharafinsa a baya harma taron ƴan-jarida yake yi babu wani tsoro aciki. Idan da Bihanzin yaga dama da zai iya hanawa ko kuma ya tura a kama Nazára tunda garin sa ne, to amma ko kaɗan Bihanzin bai damu ba.
Idan mukai duba da yadda kwatsam Bihanzin ya tattare kayansa ya fice daga babban birnin jekis wanda shi ne gari mafi girma da ƙawa a daular Sisiya wadda yake mulka to zamu ga cewa Bihanzin kamar bai damu da mulki ba. Kunga dai Bihanzin shi ne ya gina daular Sisiya baki ɗayan ta tun daga ƙasa har sama, amma lokaci ɗaya ya tashi ya koma wani waje can a ƙarƙashin ƙasa. To wai meye shirin Bihanzin? Idan baya son mulki to mai yake so? Shekarun baya munga inda yake gayawa Armad da Ikenga cewa yana so ya samar da ZURI'A ƊAYA dashi da Sarkin-sarki. To amma idan ka lura zaka ga tabbas akwai lauje cikin nadi. Shin da gaske Bihanzin so yake ya kashe kowa? Domin hakan yana nuna sai ya kashe kowa harda su tarifil-fakta da Kuyurussa'ayi da ASHURA da su Taidara da Maikiro'Abbas dama duk wani sauran hatsabibi a duniya. Lallai komai ƙarfinsa hakan ba abu ne mai yiwuwa ba. To amma baka ƙwacewa ma'aboci garma, bari muga shirinsa.
A ɗaya ɓangaren kuma sakacin Bihanzin yasa babu wata tangarda dasu Nazára suka samu a duk garin da suka je. Idan baka sani ba sai kace har yanzu su suke mulki. A garin Tarara maƙabarta suka je suka haƙe wani kabari. Al'adar mutan rafiya suna saka gawa a akwati kafin su binne, sabida haka su Nazára suna haƙe kabarin suka tsinci akwati aciki. Ba tare da wani ɓata lokaci ba suka janyo shi suka cillashi cikin jakar tsafin su sannan suka kaɗe rigar su suka wuce zuwa gari na gaba.
Tarara, Eileen, Rines da kuma Habal. Wannan sune garuruwa huɗu da suka ziyarta a daular rafiyawa, kuma duk inda suka je kawai kai tsaye suke ƙarasawa maƙabarta su nemi kabari guda su hake. Babu wata alamun sheda ko kuma kamanceceniya a tsakanin kaburburan da suke hakewa, amma ga dukkan alamu sun san kaburburan sosai da sosai domin idan suka je ko tsayawa dubawa basa yi suke fara haƙa.
Bayan sun gama da daular rafiya, kai tsaye suka wuce doron ƙasa ta hudu daular sisiya. Basu zame ko'ina ba sai makabartar babban birnin ƙasa wato Jekis. Suna zuwa suka fara haƙa. Ba jimawa sai gasu da akwatin gawa. Abin mamaki shi ne, saɓanin daular rafiya, daular Sisiya basa saka mutane a akwati idan zasu binne, amma kuma duk da haka wannan gawar a akwati take.
"Biyar kenan. Ragowar huɗun suna maikironomada." Inji Asifu.
Nazára ya gyaɗa kai. "Wannan ma sun isa. Maikiro'Abbas bazai bari mu ɗakko nasa ba."
Jan doki yai tsaki. "Ai kabar wannan tsohon. Idan fa ba mutuwa yayi ba babu wanda zai sarara. Ka duba kaga yadda yaƙi ya shiga yaƙin sarakunan jinzidal da kuma yadda yaso yayi wa Bihanzin mubaya'a harma ya karɓi fasahar Al'yaya a wajensa. Daga baya kuma ya juya yana so ya haɗa kai da Taidara. Yanzu kuma naji ya haɗa kai da Ururu. Wai waye Maikiro'Abbas ne?"
Asifu ya yamutse fuska. A zahiri baya son maganar Maikiro'Abbas sabida wasu dalilai nasa na kansa, amma tabbas shima abin Maikiro'Abbas yana ci masa tuwo a kwarya. "Kawai shi fa Maikiro'Abbas ina ganin matsoraci ne kawai. Duk inda yaga zata bulle masa nan yake yi. Lokacin yaƙin sarakunan jinzidal yaƙi shiga yaƙin saida yaga an gama komai sauran kiris, sabida kada Ururu su zarge shi sai yazo aka ƙarasa Hidaya dashi. Daga baya da yaga Bihanzin yayi nasara sai ya koma wajensa yana ganin zai iya kare shi. To amma daya fuskanci ba mulki ne a gaban Bihanzin ba sai ya janye ya koma wajen Ururu. Kafin nan ance yayi tarurruka da Taidara akan komawar sa tafiyar Wilbafos. Yanzu kuma da yaga Ururu sunyi fushi sun fara kamfen sai ya koma ɓangaren su. Wai kunsan shi suka naɗa shugaban gudanarwa na wannan jinzidal din da za'ayi a doron ƙasa ta biyu kuwa?"
Suka gyaɗa kai a tare. "Eh mun sani."
"To kun gani. Mu bari kawai sai ya tafi sai muje mu fashe kaburburan mu ɗebe akwati nan." Inji Asifu.
Shi dai Nazára yayi shiru yana nazari. A zahiri bayanin Asifu yana kan layi idan aka lura da abubuwan da Maikiro'Abbas yake yi na canja sheka akai-akai kamar wani ɗan-siyasa. To amma har yanzu bai san yadda akai Abbas ya mallaki littafin takobi har ma ya ɓoye shi acikin fasahar sa ta Non-toch-teka ba. Anya kuwa matsoraci zai iya kaiwa wannan matsayi?
Kamar yana bashi amsar tunaninsa Jan Doki ya dubi Nazára ya ce, "kai nifa ina ganin kawai sa'a ce takai littafin takobi Non-toch-teka, ko kuma Hidaya ce ta saka shi aciki bai sani ba. Ko kuma Taidara. Amma dai Maikiro'Abbas bai kai matsayin da zai mallaki littafin takobi ba. Musamman duba ga tsoron sa a fannin yaki."
Nazára ya gyaɗa kai a hankali. "Toh, watakila. Yanzu dai ku ajiye maganar Abbas a gefe. Mu ƙarasa maboya mu tashi mutanen cikin akwati nan nan."
Nan take suka tashi sama suka rankaya izuwa wani ɗan ƙaramin daji dake kusa da cikin garin. Ba jimawa suka bayyana acikin kogon tsafin da suka tanada inda suka ajiye akwati nan a tsakiya. Jan doki da Asifu suka fara ƙoƙarin budewa.
Sai da suka shafe awa guda suna fama sannan suka buɗe guda ɗaya. Nazára ya matso kusa suka leƙa domin ganin abinda ke ciki. Duk da zaka iya cewa sun san hakikanin meye aciki domin kuwa ba wannan ne karo na farko da suka taɓa buɗe akwati nan ba. Idan mai karatu bai mantaba tun a littafi na farko munga inda mutan cikin wannan akwatina suka buɗe ido sukai magana a sanda Armad ya farkar da idanunsa na Wilbafos. Amma tun daga wannan lokaci bamu ƙara ganin bayyanarsu ba. Ko wane shiri Nazára yake ƙoƙarin yi da wannan mutane wanda su ba matattu ba kuma suba masu rai ba? Wani zai iya cewa ai suna da rai tunda suna motsi kuma suna magana amma kuma mai yakai mai rai cikin kushewa harma aka binne shi? To koma dai mai ake ciki tabbas zamu ji daga bakin na cikin akwatin idan sun farka.
To amma fa da kamar wuya, ana ƙarasa buɗe akwatin aka iske shi wayam, babu komai aciki sai ƙura. To fa! Ga dukkan alamu an riga su. Watakila akwai barayin kabari na musamman da suke tunanin kuɗi ne aciki, ko kuma na cikin kabarin sun gaji da zama sun fito shan iska.
Cikin tsananin zafin nama Nazára ya taya su suka buɗe ragowar akwatin huɗu. Ai kuwa abin al'ajabi duk huɗun babu komai aciki. Watakila idan ɗaya ne ko biyu suka ɓata za'a iya cewa matsalar barayi ce, to amma duk biyar din, kuma kowanne a gari daban yake.
"Wani ya riga mu." Inji Nazára fuska a murtuke.
Mudai masu karatu babbar tambayar mu anan ita ce su waye acikin wannan kaburbura?!
***
Bari mu koma ɓangaren Nusi. Ba jimawa da ita da tawagar ta suka iso doron ƙasa ta uku sashin arewa, wani ƙauye da ake kira da Kanyu. Gaba ɗayan garin baifi gidaje dubu biyu zuwa dubu uku ba, sai makaranta da kasuwa da asibiti guda uku, amma kowa yana zaune hankalinsa kwance ana siye da siyarwa. Duk wanda ka gani da fara'a a fuskarsa kai kace duniya ba yaki ake ba. Kai tsaye su Nusi suka tambayi inda gidan Wilbafos yake, kuma aka nuna musu.
Gidan yana ɗan-wajen ƙauyen ƙuryar kudu maso gabas. Watakila sabida girman sa ne, domin kuwa shi kaɗai kusan gida hamsin ne. Tun daga nesa zaka hango ƴar-farfajiyar gidan cike da bishiyoyin ɗorawa. Mutanen ƙauyen basa zuwa kusa da gidan domin tuni jami'an tsaro suka tsorata su akan cewa mutan gidan masu laifi ne. Kasancewar hakan tuni gidan ya tara ƙura, ganyayyakin bishiya sun zubo ƙasa sun cika ko'ina har sun ruɓe a ƙasa.
Koda Nusi ta tura ƙofar shigar sai kawai ta buɗe da kanta, alamun an daɗe ba'a taba taba. Kai harda wata yana a jiki.
Suka bi takan yar-siriyar hanyar data shiga cikin gidan wadda a yanzu ganye da kura duk sun rufe ta ba'a ganinta sosai. Ba jimawa suka iso inda barandar gidan take. Daga nan suna iya hango ɗakunan gidan.
Abin mamaki da dama daga cikin tagogin sun farfashe tayadda ana iya hango cikin ɗakunan tun daga waje. Ƙofar falon a buɗe take lamarinda yasa nan take Inyaya ya zare takobi ya taka a hankali cikin kwarewa zuwa cikin ɗakin domin ganin waye aciki. Akwai yar-fitila aci balbal tana ci akan teburin dake tsakiyar ɗakin. Sannan kuma daga can gefe akwai wani tsoho kwance kan kujera yana numfarfashi.
Bayan Inyaya ya hanga ko'ina ya tabbatar babu komai sai ya ɗagowa su Nusi hannu alamun su ƙaraso.
Suka ƙarasa cikin falon suka saka wannan ɗan-tsoho mai numfarfashi a tsakiya. Shin waye wannan tsoho?
Mu haɗu a karatu na gaba.
Comments
Post a Comment