Skip to main content

BABI NA 240-250: Kurkukun Lokaci

 Babi na 240-244

***

Yarima Niyashi ya shafe mintuna talatin yana gudanar wannan lakca wadda dukkanin gidajen jaridu suka ɗauka suka watsa a duniya. Bayan kammala taron yarima ya koma cikin laburarin ya bar mutane da ƴan jaridu dake ta hanƙoron ya amsa musu tambayoyinsu. 


Yana komawa ciki ya sha kwana ya miƙe. Bayan taku kaɗan ya ƙara shan wata kwanar sannan ya tsaya a inda ya tabbata babu wanda ke ganinsa. Ya ɗaga hannayensa biyu ya kira wasu ɗalasimai tare da tafa hannayensa. Nan take ƙasar wajen ta dare gida biyu ya shige ciki. Bai tashi bayyana a ko'ina ba sai cikin wani lambu dake can bayan gari. Ƙasa ta dare gida biyu tayi amansa. Abin mamaki shi ne babu ko ɗison datti ko ƙasa a jikinsa, kai kace ba daga ƙarƙashin ƙasa ya fito ba. Yana dira ya wuce cikin ɗan tafkin dake tsakiyar wajen ya cire kayansa domin yin wanka. 


Wannan tafki na tsafi ne kuma shi kansa yana da izza wadda idan ka shiga ciki da kansa zai wanke duk dattin dake jikinka ba tare kayi komai ba. Saboda haka Nazára kawai gefe ya samu ya zauna aciki tayadda kawai kansa ake gani a waje. Hayaƙin izza ya fara tashi daga saman tafkin yana shiga jikinsa. A hankali Nazara ya limshe ido ya shiga tunanin abinda zaiyi a nan gaba sai dai kuma a lokacin ne yaji gyaran murya kamar daga sama. Yana buɗe ido yai arba da abin mamaki.


Ikenga ne a tsaye fuska a hasale. A bayansa wasu mutane ne guda huɗu sanye da baƙaƙen sulke. Ɗaya daga cikin wannan mutane basamude ne kuma idanunsa na Ururu ne. Ɗaya kuma yaro ne wanda duk yafi sauran ƙanƙanta amma kuma izzar dake fita daga jikinsa tasa iskar dake wajen tayi nauyi saboda yawa. Shima wannan yaron baƙaƙen idanuwa ne dashi, yana tsaye a daman Ikenga yana kallon Nazara. Ragowar mutane biyun sune dattijo Nara wanda shi aka fara gani tare da Ikenga. Sai kuma Daddaru wanda suka haɗu a lokacin daya karɓi ajiyar kakansa Amraikugyu.


Abin mamaki a wannan rana shi ne idanun Ikenga sun juye gaba ɗaya, baƙin ciki ya koma siffar takobi irin idanun da aka gani tare da wannan jarumi a lokacin yaƙin littafin-takobi. Gashin kan Ikenga baƙi ne siɗik an gyara shi sosai kai kace wani santalelen ango ne. Babu wani alamun izza a tattare da Ikenga, a gani na farko kace gama garin mutun ne amma kuma kallo ɗaya kacal daga kaifafan idanunsa zaisa ka canja shawara.


Ikenga ya katse shirun da cewa, "kasan mai ya kawo ni?"


Nazara yayi ajiyar zuciya. A zahiri bai taɓa tsammatar zuwan wannan mutane ba amma kuma lallai babu tsoro a fuskarsa. A nutse ya taka ya fito daga cikin tafkin, kayansa suka taso da kansu suka shiga jikinsa domin kuwa su ma kansu suna da izza tasu ta kansu. 


Ya tafa hannunsa biyu inda ƙasa tayi girgiza ta dare, bishiyu masu lema suka bayyana a wajen sukai musu rumfa. Sannan kujera ta farin dutse ta tsatstsafo daga ƙarƙashin ƙasa a bayansa inda ya zauna a nutse. 


"Kamar yadda kuka zo gida na babu gayyata kada kuji haushi idan ban baku abin zama ba." 


Ikenga ya gyaɗa kafaɗu cikin rashin damuwa ya ce, "koda ka bamu zaiyi wuya mu iya zama. Amma ka kyauta da kayi tunanin hakan. Kasan abinda ya kawo mu?"


Nazara ya haɗe gira ya ce, "abu ɗaya kacal nake dashi wanda kake so kuma bazan iya baka ba. Sai dai ka kwata da ƙarfin izza."


Ikenga yayi murmushi ya shafa ɗan gajeren gemunsa ya ce, "ni ɗin da kake gani ba kullum nake son faɗa ba, musamman kwana biyu da girma ya fara kama ni. Idan kana so ka wasa jini akwai ƙanina a shirye yake." Ya juyo ya nuna B. Ururu wanda ya shafa takobinsa tare da lashe baki cikin amincewa.


Nazara ya yatsine fuska yana kallon B. Ururu. Bayan ɗan lokaci yai ajiyar zuciya ya dawo da hankalinsa kan Ikenga.  "Zan iya cewa ɗaukar fansa kazo yi saboda na gayawa duniya asalinka to amma na san ba haka ne ya kawo ka ba." 


Ikenga ya miƙa hannu kan iska ya fizgo wani baƙin akwati ƙarami daga kan iska ya miƙawa Nazara. Nazara na taɓa akwatin ya gane meye aciki. Yayi mamaki da farko amma daga bisani yaja dogon numfashi ya ce, "wannan bai isa ba. Idan kana tunani zan baka ƙanwata saboda wata fasahar kwangila ka canja shawara. Kuma..."


Ikenga yai sauri ya tari numfashinsa, "duk girman wannan fasaha kawai na baka ita ne saboda girmama baba Dalja, ina ganin babu wanda ya kamata ya mallaki fasahar kwangilar Turɓaya banda ɗansa. Idan baka sani ba baba Dalja ya taimake ni tsahon shekaru kafin ya taimaki Banzirshishirui. Amma akwai kyautar da nake so na baka ta musamman idan ka bani Nusi." Ikenga ya juya ya kalli Deniz Ururu. Basamuden ya ɗakko wani littafi daga aljihunsa ya gabato gaban Nazara ya miƙa masa.


Nazara ya kalli littafin a nutse na ƴan mintuna kafin daga bisani ya karɓa. Yana riƙewa idanunsa suka zaƙulo cikin mamaki da al'ajabi. Ya buɗe baki zaiyi magana amma kalmomin suka maƙale a wuyansa. Ya ƙara kallon littafin kallo na musamman. Ansa ɗalasimai an ɗinke bakin littafin tayadda babu wanda zai iya karantawa sai mutun ɗaya kacal. Gaba ɗaya faɗinsa baifi kamu biyu ba amma kuma yana da tudu sosai. Bangon littafin ruwan ɗorawa ne mai ɗiso-ɗison ja, kamar an fesa jini akai. 


"Haka ne, na baka littafin yaƙutun izza wanda ni kaina ban karanta ba. Abinda kawai nake so shi ne ka gayamin yadda zan sarrafa Nusi na buɗe ƙofar sihirtaccen gari na ƙarƙashin ƙasa. Idan ka duba Nusi ba jininka bace, dan ka yaudare ta ba wani abu bane. Hasalima ba yaudara bace, wannan shi ake cewa kula da kai. Baza ka ƙara samun dama irin wannan ba. Idan kaji abinda na bayar kafin Abarai ya bani littafin sai ka riƙe baki."


Nazara ya kalli littafin sannan ya ɗaga kai ya kalli Ikenga cikin kokwanto yana tunani.  


Ɓangaren Armad


Jim kaɗan bayan an ɗisa jinin Nostaljiya akan dutsen sarkin duba Babara alƙaluma suka fara bayyana. Wani haske mai ɗauke da hotunan mutane ya bayyana akan dutsen. Bayan kiraye-kirayen ɗalasimai hotunan suka fito garau yadda kowa zai iya ganinsu.


Abin mamaki hoto na farko hoton babban hadimin Armad ne wato Inara. Hoto na biyu hoton Lamarudu Wilbafos, sai kuma wasu mutun biyu daga cikin rundunar Armad wanda ƴan asalin ƙabilar Wilbafos ne da aka haifa a wannan kurkuku.


Armad ya nuna hotunan yana neman ƙarin bayani.


Babara ya ɗanyi tunani kafin daga bisani ya amsa da cewa, "wannan sune hotunan mutanen da zasu gano Kurkukun Lokaci anan gaba."


Armad ya duba hotunan guda huɗu. Wanda yafi ja masa hankali shi ne Inara sai kuma Lamarudu. Tun da daɗewa Armad ya ɗauki Inara a matsayin ɗalibi na musamman kuma idan banda rashin lokaci da lalle Armad sai ya sa masa lokacin karɓar horo. Sabida haka ganin cewa Inara yana da wani sirri na musamman yasa Armad farin ciki. Ko ba komai alaƙar dake tsakanin Armad da Inara kamar alaƙar ɗa da uba ce. Shi kuwa Lamarudu kwamanda ne na musamman acikin tawagar Armad saboda haka shima samun sa yana da muhimmanci. Iya yawan mutanen da suka gano kurkukun iya taimakon da zasu iya samu.


Armad ya numfasa cikin tunani. A zahiri duk da ganin hotunan su Inara ya taimaka amma ba sosai ba. Domin kuwa bai amsa musu tambayoyinsu ba. 


"Da mamaki," inji Armad, "kamata yayi ace duk wata fasaha da ka koya acikin wannan kurkuku ta zauna dakai idan aka juya, dalili kuwa shi ne idan ka duba kowacce fasaha acikin kwakwalwa take, saboda haka indai muna iya riƙe tunanin mu ya kamata ace muna iya tunano fasahar."


Nostaljiya ta gyaɗa kai alamun amincewa. "Lallai haka ne, nima nayi wannan tunanin to amma ga dukkan alamu wanda ya shirya wannan kurkuku yana ganin idan ya bamu wannan dama to kamar ya mayarda kurkukun ta koma aljannar horo. Kuyi tunani ku gani, ace duk abinda muka koya zamu riƙe ai babu wanda zaiso ya fita daga cikin kukukun, tunda ko babu komai baza ka tsufa ba. Sai ka zauna ka ƙara ƙarfin fasahar ka har abada."


Armad da Babara sukai ajiyar zuciya, lallai abinda Nostaljiya ta faɗa haka ne. To amma abin tambayar anan shi ne: meye dalilin da yasa tun farko za'a saka su acikin fasahar idan ba'a so su amfana? Ta mahangar Armad hakan bashi da wani amfani domin kuwa idan ba'a saka su ba suma zasu zama kamar sauran mutane basu san abinda ke faruwa ba, ta haka kaga baza suyi ƙoƙarin ficewa daga kurkukun ba. Zasu zauna ne kamar wasu makafi, kurame kuma bebaye. 


"Sai dai idan kuma shima wanda yayi fasahar bashi da ikon hana mu gano ta." inji Armad bayan ɗan dogon tunani. 


Babara ya nuna dutsen dubansa ya ce, "haka ne, wataƙila koma waye bashi da iko. Wataƙila ma bai san mun gano ba. Kai wataƙila ma shima kansa bazai iya koyar komai ba acikin kurkukun. Idan kuwa haka to kaga akwai wani dalili da yasa aka samar da kurkukun ba wai dan a samu horo ba." Babara ya kalli Nostaljiya ta gefen idonsa yana tunano farkon sanda ta gano kurkukun da yadda tayi tunanin anyi kurkukun ne domin samun horo.


Nostaljiya ta buɗe baki zatai magana amma Armad ya riga ta. "Nima nayi wannan tunanin kuma har yanzu ina kan haka. Wataƙila wanda yayi kurkukun yayi ta ne domin kansa banda kowa, ta haka shi zai iya koyar horo aciki amma banda mu. Sannan kuma ni har yanzu ban gwada da kaina ba, wataƙila na gano wata hanya da za'a iya koyon horon. A halin yanzu muna da abubuwa guda biyar: na farko ace wannan kurkuku daga ALLAH take babu wani mahaluƙi dake da saka hannu a ciki; Na biyu kuma ace wani ma'aboci izza ne wanda bamu sanshi ba bai san mu ba ya samarda wannan kurkuku; na uku ace wani ma'aboci izza ne wanda muka sani misali Bihanzin ya samarda wannan kurkuku; na huɗu ace Ikenga ne. Dalilin da yasa na ambaci Ikenga shi ne shi kaɗai ne.wanda na san yana sarrafa lokaci yadda yaga dama. Abu na gaba shi ne idan Ikenga ne to zata iya yiwuwa yana da cikakken iko akan fasahar wanda hakan yake nuni da cewa yana sane damu, ko kuma ace bashi da cikakken iko wanda hakan ke nuni da cewa ba lalle yasan damu ba. 


"A taƙaice dai ina buƙatar lokaci nayi tunani akan wannan kurkuku kafin na yanke shawarar mai zamuyi. Dani da Nostaljiya zamu fita, Babara kasa ido akan Inara da Lamarudu da ragowar mutun biyu daka gano saboda kowanne lokaci zasu iya gano wannan kurkuku."


Nan take Armad ya miƙe ya fice daga cikin fadar, Nostaljiya na biye dashi. Har sun kusa ficewa Babara ya tako da gudu ya ce, "sarki Wilbafos, zamu shiga cikin rashin kwanciyar hankali idan ka tafi kai kaɗai da mai ɗakinka. Ka rabu dani na raka ka ko kuma nasa wasu suyi maka rakiya."


Armad ya juyo a nutse, a duk cikin kurkukun bango baya jin akwai wanda zai iya tsayawa a gabansa a halin yanzu amma duk da haka yaji daɗin kulawar da Babara yake nunawa. Sai dai kuma hakan bashi ke nuna zai karɓi abin ba. "Kada ka damu babu abinda zai faru. Idan zaka taimaka da wani abu bai wuce kula da mutanen dake cikin wannan kurkuku ba."


Nan take Armad ya fiddo da Ubbaru ya ɗane kansa tare da Nostaljiya suka rankaya ba tare da jiran amsa ba. Cikin ƴan daƙiƙu suka ɓace suka daina hangen mutanen da suka bari. Nostaljiya ta ziro hannayenta ta bayan Armad ta riƙeshi ƙaƙam. Bayan ɗan lokaci ta ce, "mu tashi sama."


Armad ya ja birki ya tsaya cak cikin mamaki. Wai dama Ubbaru tana tashi sama bai taɓa sani ba? Kamar tana bashi amsa Nostaljiya ta ce masa dawo baya ka gani. Armad yai tsalle ya dawo bayanta ya bata linzamin. Cikin kwarewa ta zana wasu ɗalasimai akan kafaɗun dokin inda nan take fuka-fukai suka fito manya-manya farare. Armad ya cika da mamaki yana ɓacin ran yadda bai san dokinsa yana tashi ba. Wai ma sanda ta bashi dokin mai yasa bata gaya masa cewa yana tashi ba?


Muryar Nostaljiya ta katse shi, "ka riƙe ni sosai."


Kafin ma ta rufe bakinta dokin yayi sama ya luluƙa ya hau iska yana bubbuga kafaɗunsa cikin kwarewa. Kana gani kasan ya saba gwagwarmaya a sararin samaniya. 


"Aaaargh...." Armad yayi ƙara a yayinda dokin yayi wata kwana a sama kafin ya ƙara luluƙawa sama ya fara keta hazo.


Nostaljiya ta kyalkyala dariya tana cewa, "haha... ka riƙe ni sosai yanzu aka fara." 


"Kina sane kike ƙara yin sama... Aaargh... Ina fa da Kaban'shisu, zan ɓace na koma ƙasa... aargh..."


Yana magana amma duk sanda Nostaljiya ta luluƙa sai tasa ya kusa faɗowa. Zai iya rantsewa tana sane tasa wani ɗalasimi a jikin kayanta tayadda basa riƙuwa kwata-kwata kamar an zuba musu karkashi.


A haka suka shafe rabin awa kafin daga bisani ta yanke shawara ta wahalar da Armad haka. A dai-dai inda suke lilo akan iska babu nisa da bangon arewa. Saɓanin sauran wajaje da Armad ya gani a wannan waje ruwan ba'a tsaye yake ba. Wani gagarumin tsauni ya raba gangar ruwan gida biyu, saboda haka ruwan yana kwaranya ne ta gefen tsaunin. Wannan shi ne ya bawa tsaunin damar yanayi mai kyawun gaske; babu rana ga bishiyu da ƙanshin ruwa na tashi ta ko'ina. Babu alamun wata halitta a wajen saboda haka Nostaljiya ta nufi kan tsaunin gadan-gadan. Ta nufi ruwan dake kwaranya ƙasa, sai da ta kusa zuwa kawai ta juya dokin cikin kwarewa ta cilla Armad tana kyalkyala dariya. Lalle badan Armad na da Kaban'shisu ba da tuni ya faɗa ƙasa. Ai kuwa ya dawo ya harare ta, "wai meye matsalarki?"


Nostaljiya ta haɗe gira tare da karkata kai gefe cikin shagwaɓa ta ce, "matsala? Ni bani da wata matsala."


Nan take Armad yaji ciwon kai ya zo masa domin tuni ya gane inda aka dosa. Shi da ya futo horo domin fuskantar kurkukun lokaci amma ga dukkan alamu akwai abinda yake nufo shi.


Bayan ɗan lokaci ya numfasa ya ce, "faɗi."


Nostaljiya ta watsa gashin kanta baya inda hasken fatarta ta ƙara fitowa ta haskaka tsibirin. Ance idan ka daɗe kana ganin kyau ɓacewa yake amma banda na Nostaljiya. Madaidaicin wuyanta na ɗauke da hijabin da a kullum take ɓoye kyawunta dashi domin sauran mutane. Ta miƙe hannu ta cire wannan hijabi inda nan take surarta ta ainihi ta bayyana. Haske mai haska haske, lallai da sarkin-sarki zata ga Nostaljiya da ta ji kishi. Idanun Nostaljiya farare ne masu ƙawa da nutsuwa, ga gashin ido dana gira masu armashin izza da kamalar fararen aljanu. Ta motsa leɓenta cikin kisisina ta ce, "wata nawa rabonda ka ganni? Ka dawo amma kuma baka damu dani ba kawai ta izza kake, kana nufin izza tafi ni muhimmanci? Ko kuma horon naka ne yafi ni muhimmanci? Shi yasa na wahalar dakai, naso ma ka faɗo ƙasa izzarka ta zuƙe kaga daga nan sai a daina zancen izza a tsaya a kula a iyali."


Armad ya rasa abinda zaice saboda tsananin mamaki. A zahiri yama manta rabon da ya ziyarci Nostaljiya a matsayin matarsa to amma kuma ai bai zauna ba shi yasa. Bayan ɗan tunani ya yanke shawarar ya bada haƙuri amma kafin yayi magana Nostaljiya ta ce, "wai ma meye dalilin da yasa ka taho dani?"


Ya buɗe baki zai amsa amma ya fasa ganin cewa gaya mata ya ɗakko tane dan ta taimaka masa wajen koyon yanayin-izza irin na ƙabilar Elbis bazai haifar masa ɗa mai ido ba. 


"Gayamin mai yasa ka ɗakko ni?"


Armad yai gyaran murya, a zuciyarsa yasan cewa yau lallai sai ya ɗanyi ƙarya ko yayane. "Na ɗakko ki ne saboda mu gana a matsayin mata da miji. Kinsan yadda nake kewarki a yayin gasar can? Shi yasa na yanke komai na ɗakko ki muka fito. Amma idan kina ganin ƙarya ne to..."


"Karya ne ma." Ta katse shi cikin ɓacin rai. Tunda yake bai taɓa ganin ɓacin ranta irin na wannnan rana ba domin kuwa bata taɓa ce masa yana ƙarya ba sai yau.


"Tunda kaga waccan tsohuwar matar Nusi shikenan ka manta dani. A yanzu ma bata nan amma lissafin ka ka fara nemanta ba tare da ka kula ni ba. Ana nan zaka ce ka daina so na ita kake so..." Tana zuwa nan a zancenta ta fashe da kuka da hawaye mai zafi yana kwaranya daga idanunta. 


"....." Armad ya buɗe baki zaiyi magana amma ya fasa. Akance iyakacin yawan ƙauna yawan ɓacin rai. Bai taɓa shiga irin wannan yanayi ba saboda haka ya tsaya yana tunani mai ya kamata yayi. Bayan ɗan lokaci ya tako ya rungume ta a ƙirjinsa. A haka suka tsaya tsahon lokaci har sai da ta daina kuka sannan Armad ya ɗau bayani akan ƙauna har saida ta fara murmushi. 


A wannan rana dai ba'a ƙara zancen izza ba. Soyayya aka kwana anayi yadda kasan ango da amarya. A lokacin Armad ya gane lallai yana kewar matar tasa. 


Da safe Armad ya tashi ya nemi Nostaljiya ya rasa. Da farko baiyi tunanin komai ba, yayi tunanin kawai taje biyan buƙatar ɗan adam ne amma daga bisani yaji baya jin yanayin-izzar ta saboda haka nan take ya miƙe ya zagaye dukkan tsibirin amma babu ita babu alamunta. Nan fa hankalin Armad ya fara tashi yana haki haka yaci gaba da nema kafin kwatsam yaji ta a bayansa ta rungume shi. 


Ya waiwayo a nutse domin ya tabbatar ita ce. Bayan yaga dariyar muguntar dake fuskarta ya ɓata ya ce, "wai ke baza ki haƙura ba? To kuwa nima zan fara..."


Ta katse shi da cewa, "nifa ba wani abu nayi ba kawai ina nuna maka cewa da kana sani acikin abubuwanka da fasahar yanayin-izza da kake so ka koya ta ƙabilar Elbis da tuni na koya maka. Kada ka manta akwai fasahohi da Bihanzin ya koyamana tun muna yara."


Tana rufe baki Armad ya tuno yadda Nostaljiya ta ɓoye yanayin-izzarta ta kuma ɓace ta yadda ya kasa ganinta kamar yadda ƙabilar Elbis suke yi. 


Lallai akwai rashin kulawa a tsakaninsu. Armad bai san sanda abin ya fara ba domin kuwa baya sane. Tun bayan sanda Bihanzin yai sanadiyyar mutuwar Hidaya Armad yake baya-baya da ita ba tare da ya sani ba, abin ya fara cutar da alaƙarsu wanda kuma Armad baya farin ciki da hakan. Bama ita kaɗai ba, Armad baya tattaunawa da sauran mabiyansa yadda ya kamata. Zaka iya cewa babu lokaci to amma a zahiri akwai fasahohi da zai koya musu musamman daga cikin waƙar-maƙabarta wanda zasu yi matuƙar taimakawa rundunar tasa amma kuma bai taɓa yin hakan ba. Kai shi kansa ma zai iya koyar abubuwa da dama daga gare su kamar misali wannan fasaha ta Nostaljiya.


Tun daga wannan lokaci Armad yayi alƙawarin zai zaɓi mutane a hankali a hankali daga cikin rundunarsa ya sanar dasu fasahohi daga cikin waƙar-maƙabarta sannan shima ya ga idan akwai abinda zasu iya koya masa. Amma a yanzu zai fara da Nostaljiya da Babara da kuma Lamarudu da Inara da mutun biyu da Babara ya gano zasu gano kurkukun. Bayan an gama da kurkuku za kuma a ɗebi sauran ayi musu horo. 


Daga wannan rana akan wannan tsibiri Nostaljiya ta fara koyawa Armad wannan fasaha. A cewar Bihanzin sunan wannan fasaha Layar-zana. Armad ya san cewa ba haka ƴan ƙabilar Elbis suke kiranta ba amma ya manta yadda suke ce mata. Sai dai kuma suna bai dame shi ba, koma mai ake ce mata a yau yayi niyyar ya koye ta.


***


Nostaljiya ta gabato gabansa a hankali da kokara a hannunta. "Zan ɓace na ringa kawo maka duka, idan ka kauce shikenan amma kayi sani cewa dole sai ta hanyar fasahar Layar-zana zaka iya gano ni."


Tana rufe baki ta ɓace ɓat da ita da sandan dake hannunta sannan ta fara kai masa duka ta sama ta ƙasa. 


Duka na farko sai da ya kumburawa Armad kai, ba shiri ya ƙaddamar da fasahar Ƙashin Wilbafos. A zahiri gano fasahar Layar Zana nada wahalar gaske domin kuwa mutun yana iya ɓoye surarsa da izzarsa baki ɗaya kamar ma baya raye. Armad yana da sirri na musamman daga Miyurarsa dake sawa yana jin ƙanshin izza amma kuma duk da haka baya ganin Nostaljiya. Ga dukkan alamu akwai wani sirri da bai gane ba.


"Idan har ka gane Layar-zana to hatta aljanu baza su ɓoye maka ba." Inji Nostaljiya. 


Armad ya cije baki ya rufe ido. Babban al'amarin shi ne bai san mai ya kamata ya duba ba. A lokacin da ya koyi fasahar yanayin-izza yasan mai yake nema, misali yasan abinda yake so ya gani idan ya rufe idonsa. Wannan abu shi ne izza, saboda haka a duk sanda ya rufe idonsa to izza zai nema. Ta haka ya gane fasahar yanayin-izza. Amma a yanzu bai san idan ya rufe idonsa mai zai nema ba. A duk sanda kake neman ma'aboci izza zaka iya amfani da abubuwa guda huɗu: gangar jiki, ruhi, izza, da kuma tunani. Ganin gangar jiki yafi komai sauƙi domin kuwa da idanu kowa zai iya gani. Ganin izza sai mai yanayin izza. Acikin waƙar-maƙabarta akwai fasahohi wanda za'a iya ganin ruhi da tunani dasu to amma duk wannan bai taimaka ba. A duk sanda Nostaljiya ta ɓace komai nata ɓacewa yake yi kamar bata raye. Kai ta ɓangarori da dama fasahar da Nostaljiya take amfani da ita tafi wadda sauran gama-garin ƴan ƙabilar Elbis suke amfani da. Domin kuwa idan zai iya tunawa Dinanduil bata iya ɓoye ruhinta da tunaninta. Abinda take ɓoyewa shi ne izzarta da gangar jikinta. 


Bayan tsahon lokaci suna kai komo Armad ya yanke shawarar a tsaya a huta domin kuwa duk jikinsa a kumbure yake. Sau ɗaya kacal yayi hasashe mai kyau ya kaucewa sandar.


Nostaljiya ta bayyana inda ta kwanta akan cinyarsa tana gaya masa sabbin matsaloli. Armad ya yamutse fuska, ta gama lodarsa da sanda da sunan koyon horo sannan kuma tazo tana yi masa bayanan 'na-fika-sani', banda matarsa ce kuma yasan har yanzu bata gama hucewa ba da tuni ya rufe ta duka. 


Ko kaɗan Nostaljiya bata nuna ta damu da irin yamutse fuskar dayayi ba. "Ka laru da wakar-maƙabarta sosai shi yasa ka manta fasahohinka da yawa. Na yadda waƙar-maƙabarta daban ce amma kuma duk da haka akwai abubuwa da dama da kake buƙata. Misali, duk da akwai ta amma hakan bai baka nasara akan Ƙaizadu ba. Kuma ina tunanin bazai baka nasara akan Ikenga ba, saboda haka ya kamata ka miƙe ka ƙaro wasu fasahohin."


Armad yai murmushi ya ce, "kina tunanin ban san haka ba? Ina sane cewa fasahohin cikin waƙar-maƙabarta basu isa ba to amma wannan ɓangare ɗaya ne kawai na littafin-takobi."


Da farko Nostaljiya bata fahimci mai yake nufi ba amma ba jimawa ta gane. Cikin sauri ta miƙe ta ce, "ƙaramin haske."


Armad ya ja dogon numfashi ya ce, "Littafin-takobi abu biyu ne: littafi da kuma takobi. Waƙar-maƙabarta ita ce ɓangaren littafin, akwai ɓangaren takobin wanda har yanzu ban gama gane shi ba. Acikin baiti kan da Hidaya ta bari acikin waƙar-maƙabarta akwai bayani kan yadda zan sarrafa wannan takobi amma abin yana buƙatar na kai ziyara duniyar aljanu."


"Hmm... idan kana so ka gane ɓangaren takobin sai ka shiga duniyar aljanu kenan. To ai idan haka ne Babara ya san hanya, kaga abinda nake nufi na cewa ya kamata ka ringa shiga rigar na ƙasa da kai kamar yadda suma zasu shiga taka."


Bayan ɗan lokaci Armad ya yadda da abinda take faɗa sannan daga bisani suka dawo kan horo.


"Wai meye matsalar ne? Armad ɗin dana sani yana da saurin gane abubuwa amma ka kasa gane Layar-zana?" 


Armad yai ajiyar zuciya ya ce, "idan babu gangar jiki babu izza babu ruhi babu tunani to sai kuma me? Me kike so na laluba? Duk yadda nayi na ganki bana ganin komai sai duhu."


Nostaljita tai firgigit ta tare shi, "ah... ita ce matsalar ai. Kai cewa kake sai ka nemi wani ɓangare na rayuwa daga cikin ɓangarori huɗun nan to amma ba haka za kayi ba. Ka ɗauke tunanin ka daga kan rayuwa kwata-kwata. Kayi tunanin mutuwa, tayaya zaka ji gilmawar mutuwa? Tayaya zaka ga tafiyar mutuwa? Misali ace abu matacce kamar wannan sandan na hannuna, kaga bashi da izza bashi da ruhi kuma bashi da tunani to idan ya ɓace tayaya zaka ganshi?"


A ƙoƙarin nuna masa sandan dake hannunta ya ɓace ɓat. Armad yai shiru yana tunani kafin daga bisani ya ce, "wai ke tayaya kika koya?"


"Na gaya maka ta idanunsu nake gane wa."


Armad ya miƙe a fusace. "Wai kamar yaya ta idanunsu? Ban gane mai kike nufi ba, wataƙila da kin yimin bayani sosai da tuni an wuce wajen."


"Kaga a lokacin da Bihanzin ya koyamana bai bamu gundarin fasahar ba, mu kuma bamu tambaya ba muna ganin a duk sanda muke buƙata zamu iya karɓa. Amma abinda ya koya mana yasa indai mutun yana kallon mu to zan gano inda yake koda kuwa ya ɓoye komai nasa. Hatta mutuwa indai zata kalleni to kuwa zanyi amfani da idanun data kalleni dasu na gano ta."


"Haha... saboda haka kina gayamin indai wanda ya ɓace baya kallonki to baza ki ganshi ba? Amma kuma komai nisa indai mutun yana kallonki zaki gane?"


Ta gyaɗa kai alamun amincewa tana cewa, "abinda kawai nake buƙata shi ne ka kalleni, ni kuma zan sarrafa kallon kamar zaren saƙa na biyo ka dashi na ganka."


*Kamar zaren saƙa?!"*


Armad ya ja dogon numfashi domin ya tabbatar bazai iya samar da irin wannan fasaha ba domin kuwa bai ma san ta ina zai fara ba. Sai dai kuma bayanin Nostaljiya ya nuna masa akwai abinda zai iya yi wanda shima shi kaɗai zai iya. Wanda kuwa shi ne... Zaren-izza! Sarrafa zaren-izza. Kamar yadda yake sarrafa zaren ya futo daga duniyar Negrinkin sa, kamar yadda yake sarrafa zaren ya nemo duk abinda yake nema haka zaiyi amfani dashi ya gano Layar-zana. Dan mutun ya ɓoye izzarsa ai bai isa ya ɓoye zaren izzarsa ba domin kuwa da dama basu ma san dashi ba. Idan sun san dashi to kuwa basu da iko akansa. Shi kansa ta hanyar Miyurar sa kaɗai ya gano Zaren.


"Ɓace na ƙara gwadawa." 


Nan take Nostaljiya ta ɓace inda Armad ya rufe ido ya shiga aiki. Abu na farko daya fara yi shi ne lalubo zaren-izzar ta daga cikin miliyoyin zarurruka dake gabansa. Daga nan kuma ya fara nazari akansa. Zaren fari ne mai haske mara kauri, a ɓangare ɗaya yana liƙe da Miyurarsa a ɗaya ɓangaren kuma ya haɗe da jikin Nostaljiya wanda a yanzu baya gani. Armad ya himmatu wajen juya siffar zaren izuwa siffar Nostaljiya domin ya ganta amma ya kasa. Duk abinda yayi yaƙi haifar da ɗa mai ido. A ƙarshe kawai ya rufe ido kamar wasa ya umarci Miyurarsa data fito masa da mai zaren ta nuna masa shi. Bai taɓa tunanin hakan zaiyi wani abu ba amma bisa mamaki Miyurarsa ta amsa kiransa.  Cikin ƴan daƙiƙu gangar jikin Nostaljiya ta bayyana akan idanunsa.


A dai-dai wannan lokaci Nostaljiya ta kawo masa duka sauran ƙiris ta daki kansa amma ya kauce. Tayi tunanin cewa canki-canka yake saboda haka ta ƙara kawo masa wani saran ta sama amma ya kauce. Ta kawo masa wani ta hagu, nan ma ya kauce. Idanu a rufe amma yafi mai gani iya shege. 


Nostaljiya ta tsaya tare da buɗe baki cikin mamaki ta ce, "ya akai...?" 


Armad ya katse ta cikin sauri. Sannan ba tare da cewa komai ba ya ɓace ya bayyana a gaban ɗaya daga cikin kogunan dake kan tsibirin. 


"Zan baku daƙiƙa uku ku fito waje."


Nostaljiya ta kalleshi cikin mamaki ta ce, "da suwa kake magana?"


Maimakon ya bata amsa sai kawai ya ɓace ya shiga cikin kogon inda ya futo da wasu mutane biyu a hannunsa; mace da namiji. Babban abin mamakin shi ne yadda Nostaljiya bata san dasu ba amma Armad ya zaƙulo su cikin sauƙi. Shi kansa a ƴan daƙiƙu da suka wuce bai san da su ba. Ga dukkan alamu fasahar sa sabuwa ta fi wadda Nostaljiya take amfani da ita.


"Kuyi bayanin kan ku." 


Namijin gajere ne mai kauri, ita kuma macen dogowa ce siriri. Dukkansu suna sanye da kayan fata, riga da wando. Abin tambayar anan shi ne tun yaushe wannan mutane biyu suke kan wannan tsibiri kuma dame-dame suka gani na al'amarin aure daya gudana tsakanin Armad da matarsa. Kuma su kaɗai ne akan tsibirin ko kuma akwai wasu. Nan take Armad yayi amfani da sabuwar fasaharsa wadda har yanzu bai saka mata suna ba ya duba kan tsibirin amma bai ga kowa ba saboda haka ya dawo da hankalinsa kansu.


Namijin ya ƙura masa ido yana kallonsa kafin daga bisani ya ce, "suna na Gajere Kunkuru Dabda-ƙasa, wannan kuma ƙanwata ce Doguwa Taliya Ƴar-hausa. Kai ne mutun na farko daka iya ganin mu a tsahon shekaru."


Gajere Kunkuru Dabda-ƙasa? Doguwa Taliya Ƴar-hausa? 


Kuturu! Armad bai taɓa jin wannan sunan ba. Ga dukkan alamu ya gamu da wasu sabbin mutane masu ban al'ajabi. 


***

Babi na 245-248

***

Shekara ta biyu Bayan Amri [02BA]

***

Shekara biyu kenan bayan kammala yaƙin rukunai biyu tsakanin gidan Wilbafos da Ururu. Jini ya kwarara a doron ƙasa na farko irin wanda bazai misaltu ba. Dukkan ciyayin dake filin yaƙin sun canja launi daga kore zuwa jajawur saboda yawan jinin da suka zuƙa. A lokacin ana kan yaƙin sai da ƙasa ta jiƙe lugub da jini har ma jinin ya fara ɗisa ƙasa zuwa ƙasashen ƙasa. 


A dai-dai wannan lokaci wani ƙatoton masallaci ne akan iska yake yawo yana kewaya filin yaƙin. Dukkan ƙofofin masallacin a rufe suke, amma ta cikin gilashin kana iya hangen mutanen aciki. Abin mamakin shi ne launin masallacin kore ne shar gaba ɗaya tun daga saman toluwarsa har ƙasa. Akwai dakaru dake gadin filin amma babu wanda ke iya ganin masallacin, kai kace babu shi kwata-kwata.


Bayan tsahon lokaci, masallacin ya bar filin yaƙin ya sakko ƙasa yabi ta sashin ikwatora ya sakko ƙasashen ƙasa. A wannan lokaci babu komai a sashin ikwatora sai guguwa. A kullum guguwa ce mara iyaka take ruruwa tana juyawa tana ambaliya. Ƴan tsirarun mutanen da suke rayuwa a wajen suna kiran wannan guguwa da Baƙar guguwa. Wannan masallaci ya zauna a sashin ikwatora tsahon shekaru yana shawagi. A kullum ana kiran sallah ayi iƙama amma babu wanda ya ke jin wannan kiran salla sai na cikin masallacin.


Bayan tsahon lokaci masallacin yabar sashin ikwatora ya wuce izuwa doron ƙasashen ƙasa. A wannan ɓangare babu baƙar guguwa, garuruwa ne da ƙauyuka da kasuwanni. Ga dukkan alamu shima masallacin yafi jin daɗin wannan ɓangaren saboda waje ya samu ya zauna sama da shekaru ɗari yana nazarin ƙasashen ƙasa da mutanen dake cikinsu. A duk wannan shekaru babu wani mahaluƙi guda ɗaya tak daya ji kiran sallar da ke tashi daga masallacin ballantana ya ganshi. Sannan kuma a duk wannan shekaru ƙofar wannan masallaci da tagoginsa a rufe suke ruf, amma kuma na ciki suna sane da duk abubuwan dake faruwa a waje. 


Watarana da tsakar dare kimanin ƙarfe uku ƙofar masallacin ta buɗe, wata budurwa sanye da fararen kaya na haske da baƙin Niƙab ta taka ƙafa ta fito daga cikin masallacin. Ta sakko ƙasa cikin duniyar mutane inda ta bayyana a doron ƙasa na uku sashin arewa acikin kasuwar wani ƙauye da ake kira da Kanyu. Ta nemi wata rumfa ta kwanta aciki. Kafin safiya kayan jikinta suka juye daga na haske zuwa irin na auduga, yagaggu.


Da safiya ƴan kasuwa suka fito suka tadda ita. Tunda kayan jikinta duk a yage suke kuma fuskarta ta kukkurje tayi baƙi duk wanda ya ganta zaiyi tunanin almajira ce. Mai rumfar yana zuwa ya kore ta, amma maimakon ta tafi sai ta koma rumfar kusa dashi. Shima ya kore ta ta ƙara matsawa gaba. A haka har saida ta koma rumfar wata mata mai suna Fatima. Fatima tana aiki ne a wata ƴar ƙaramar makarantar izza dake makwabtaka da ƙauyen amma duk ƙarshen sati takan kawo kaya kasuwar wannan ƙauye musamman duba ga cewa a ƙauyen suke zaune da mijinta da kuma ƴaƴanta biyu. 


"Kin ci abinci?" Fatima ta tambayi wannan budurwa ganin yadda take a galabaice kamar zata faɗi. 


Budurwar ta girgiza kai. "A'a." 


Fatima tayi tsam tana tunani. Abincin kawai data tawo dashi na ɗanta ne ɗan shekara shida wanda baya jure yunwa. Kuma babu kuɗin da zata bata ta siyo wani.


Ɗan nata mai suna Armad yana jin mai ake cewa ya gangaro daga cikin ɗakin ya kawo mata abinci nasa. 


Wannan budurwa ta karɓi abincin ta cinye sannan ta juya ta tafi ba tare da tace ta gode ba.


Washe gari da safe ta ƙara dawowa ta cinyewa Armad abinci. Haka aka jera sati huɗu anayi, kullum sai tazo tace tana jin yunwa kuma koda Fatima ta hana sai Armad ya bata abincin sa. A ƙarshe Fatima ta koma tawo mata da nata abincin daga gida. 


Su basu san wace ce ita ba, ita ma bata san su waye su ba.


Watarana bayan wannan budurwa almajira ta karfi abinci ta tafi sai wata budurwar mai irin shekarun ta ta tare mata hanya.


Ita wannan sabuwar budurwar tana riƙe da takobi a zare babu alamun tsoro a fuskarta. Ta nuna almajirar ta ce, "suna na Hidaya Baƙar-wuta, ina umartar ki da kiyi bayanin kan ki kafin na sare miki kai."  


Almajirar ta haɗe gira. A fuskarta akwai alamu na mamaki da kuma haushi. Har ta buɗe baki zatai magana sai ta fasa kawai ta ɓace. Bata bayyana a ko'ina ba sai a bakin masallacin nan mai yawo akan iska, wanda babu wanda yake gani. 


Tana niyyar shigewa ciki ta rufe ƙofa sai Hidaya ta bayyana gabanta. "Kina zuwa wajen ƙani na da niyyar cuta, kina tunanin babu wanda yake ganinki? A DUK FAƊIN DUNIYA BABU ABINDA YAKE ƁOYEWA IDANUNA. Me kike so a wajen ƙani na? Wannan ce damarki ta ƙarshe ki kafin na sare kanki."


Budurwar tai ajiyar zuciya ta amsa da cewa, "WANDA AKA ZIYARTA DA WANDA SUKAI ZIYARAR BABU WANDA YASAN DALILIN ZIYARAR!! Doka ce tazo daga mai masallaci, saboda haka na cikin masallacin basu da iko banda su aiwatar. Suma wanda aka kaiwa ziyarar basu da iko banda suyi biyayya. Ikon mai iko; wanda ya kasa kaya ai shi zai sawa kayansa kuɗi." 


Hidaya ta yamutse fuska a fusace ta ce, "Mai kike son ki ce?"


"Abinda nake cewa shi ne na sama suke da mulkin na ƙasa." Inji Budurwar.


Baya tsahon lokaci ana kallon kallo babu wanda ya ce uffan sai Hidaya ta numfasa ta ce, "daga yau babu ruwanki da ƙani na. Idan na ƙara ganinki zan sare miki kai sai ki turo na saman su shigar miki." 


"Bani da buƙatar dawo wa domin tuni aikin gama ya gama. Abinda zai afku ya riga ya afku." Budurwar tana rufe bakinta da ita da masallacin suka fara ɓacewa. 


Hidaya ta fusata ta kai mata sara cikin tsananin zafin nama inda ta same ta a goshi kafin ta ƙarasa ɓacewa. Duk da wannan budurwa da masallacin sun ɓace amma saran da Hidaya tayi mata a goshi yana nan har izuwa wannan rana.


Masallacin ya ci gaba da yawo akan iska, shekaru sittin ana kiran sallah amma babu wanda yaji. Watarana, a doron ƙasa na huɗu, wani saurayi ɗauke da ƙatotuwar takobi wadda tafi shi tsayi yaji wannan kiran sallah.


Saurayin yana da farar fata da gashi ruwan silba. A fuskarsa akwai alamu na kafiya da taurin rai irin na baƙaƙen muridan aljanu. A saman kafaɗarsa ta dama akwai hankaka baƙi yana lilo. 


"Suna na Banzir Shishirui, ina so nasan mai ake cewa a kiran sallah?" Saurayi ya ɗaga murya a ƙoƙarinsa na son wanda suke cikin masallacin su ji. 


Tsahon lokaci babu wanda ya amsa masa.


Daga bisani wannan budurwa mai tabon Hidaya a goshi ta buɗe ƙofa ta leƙo ta taga ta ce, "kira ne izuwa addinin gaskiya, zaka karɓa?"


Bihanzin ya kalleta ya ce, "addinin gaskiya?" Sannan ya juya takobinsa ya ɗaga ta sama ya ce, "addini na TAKOBI. Ita take rayawa kuma ta kashe."


Budurwar ta girgiza kai cikin ɓacin rai ta ce, "idan baza ka karɓi addinin ba mai ya kawo ka?"


"Ina neman ƙarfin izza wadda tafi ta babban sarki Kuyurussa'ayi, boka na ya ce acikin masallacin nan ne kaɗai zan iya samun hakan."


"Ka juya ka tafi, wannan izza ba taka bace." Inji budurwar.


Bihanzin ya fashe da dariya. "Kina gayamin cewa akwai izzar amma baza ku bani ba? Lallai ni mai dauwamammen sara sai na samu wannan izza ko ta wane hali."


Bayan tsahon lokaci ana kallon kallo tsakaninsu wannan budurwa ta buɗe masa ƙofa, a lokaci na farko Bihanzin ya faɗa cikin wannan masallaci babu alamun tsoro a ransa.


***


Babu wanda yasan mai Bihanzin ya aikata acikin wannan masallaci amma bayan shekara arba'in masallacin ya fito dashi ya ajiye yaci gaba tafiyarsa. 


Zamani bayan zamani sai da aka shuɗe zamani goma sannan masallacin ya iso sashin ikwatora cikin kurkukun Bango, ya nemi gefen wani tsibiri ya tsaya yaci gaba da kiran sallah.


Bayan shekaru ɗari biyar wannan masallaci yana jira a wannan tsibiri sai Armad da Nostaljiya suka iso kan wannan tsibiri. 


Kwana ɗaya da isowarsu ƙofar masallacin ta buɗe a hankali inda Doguwa Taliya Ƴar-hausa da Gajere Kunkuru Dabda-ƙasa suka fito.


An yiwa rigar Doguwa Taliya Ƴar-hausa kwalliya da wasu filawowi ruwan hoda. A kallo na farko ba lallai ka lura ba amma idan ka nutsu zaka ga akwai ƴan ƙananun rubutu na ɗalasimai akai. Shima Gajere Ƙunkuru Dabda-ƙasa yana da irin wannan zanen a rigarsa. Kayansu na fata ne amma kuma an jeme fatar an gyara ta tana haske kamar alharini. 


Suna ɗauke da farin kyalle dogo wanda shima yake da irin wannan zane-zane. Gejere Kunkuru ya naɗa nasa kyallen kamar rawani inda ita kuma Doguwa Taliya ta naɗa nata kamar ɗan-kwali. Bayan ɗan nazari Armad ya gano wannan shiga tasu tayi kama da shigar malaman wani tsohon addini daya taɓa ji. Ko meye sunan wannan addini? 


Armad ya numfasa ya ce, "kuyi bayanin kanku."


Kunkuru zai fara magana kenan sai wani haske mai kashe ido ya bayyana a bayansa. Armad yaja da baya ya kai hannu kan mariƙin takobinsa. Nostaljiya ita ma ta gyara tsaiwa domin shirin kota-kwana. 


Sannu a hankali hasken ya ragu inda ya juye izuwa siffar wata mata tsohuwa mai yawan furfura. Tana riƙe da sanda wanda aka zane jikinsa da ɗalasimai. Fuskarta babu alamun tsufa da yawa aciki musamman idan ka kwatanta da yawan furfurar dake kanta, wani ma sai yace furfurar ba tata bace. Sai dai kuma akwai ƙatoton tabo a goshinta wanda kana kallonta zaka ganshi. A lissafin Armad wannan mata zata kai shekaru hamsin da biyar zuwa sittin. Irin mutanan ne da suke fara furfura tun suna ƙananu.


Abu guda ɗaya daya sa Armad ya gane cewa wannan mata suna da alaƙa dasu Kunkuru shi ne ita ma tana ɗauke da irin farin kyallen su wanda ta ɗaura kamar ɗan-kwali. Har zanen ɗalasiman dake kai iri ɗaya ne sak. Armad yayi ƙoƙarin karanta izzar wannan mata amma ina, babu komai na izza a jikinta kai kace mutun ce gama-gari. Amma a zahiri Armad yasan abin ba haka yake ba. Kawai ƙarfinsa ne bai kai ya iya jinta ba.


Kunkuru da Taliya suka zube a ƙasa suka kai gaisuwa. "Barka da zuwa Maulaya Furfura Farar-ƙasa Mai-yashi."


[Kalmar Maulaya mataki ne na girma a addininsu.]


Dattijuwar ta dubi su Armad ta ce, "Inai muku sallama irin ta addinin islama, ni ce Furfura Farar-ƙasa Mai Yashi, shugabar wannan masallaci. Barkan ku da zuwa wannan tsibiri."


Kaaai! Furfura Farar-ƙasa Mai-yashi?! Wannan wanne irin suna ne? Armad ya cika da mamaki a ransa amma bai faɗa a fili ba ballantana ta ce ya raina musu al'ada. Babban abinda ya ɗaure masa kai shi ne yadda bai ji zuwanta ba, idan da sara ta kawo masa da sai ta fille masa kai zai ankara. Lamarinda yasa nan take gumi ya keto masa. 


"Sannun ki Farar-ƙasa Mai-yashi," inji Armad, "naji kince barkan mu da zuwa kamar dama kina jiran zuwan mu."


Farar-ƙasa ta gyaɗa kafaɗa ta ce, "tun a Farkon-lokaci aka rubuta a sama cewa zaka zo wannan guri, kuma tuni muka shiryi zuwanka. Muna barka da zuwanka kamar yadda mukai barka da zuwan mutun biyu da suka gaba ce ka." Tana rufe baki ta tafa hannayenta inda dukkan tsibirin yai girgiza sannan wani koren haske ya gauraye wajen. Hasken yana ɗaukewa wani ƙaton masallaci mai dogayen toluwa ya bayyana akan tsibirin. 


Armad da Nostaljiya suka jada baya cikin mamaki da buɗe baki. Gari guda ne a gabansu da mutane, manya da yara, suna yawo aciki amma ko kaɗan basu ji su ba. Idan da wannan mutane sun so halaka su da tuni suna lahira. 


Bayan an ɗau lokaci babu wanda acikinsu ya ce uffan sai Maulaya Furfura tai nuni izuwa masallacin ta ce, "mu ƙarasa ciki yadda zamu tattauna a nutse."


Kafin ta rufe baki kawai yaji ƙafafunsa sun fara tafiya da kansu suna binta. 


Fasahar Kamalar-ruhi!!


Armad ya ƙaddamar da izzarsa ya jawo kansa baya, ya kuma hana ƙafafunsa binta ta ƙarfin tsiya. Amma Nostaljiya tuni ta fara bin ta saboda haka yai sauri ya janyo ta baya. "Babu inda zamu je ba tare da kin gaya mana abinda ke faruwa ba. Ki gayamin ya akai kika san zamu zo? Me kike so mu a wajen mu? Kuma wannan wanne gari ne?"


Maulaya Furfura tayi murmushi ta nuna garin ta ce, "Wannan masallaci na ne, wani yanki ne daga tsohuwar duniya. Masallaci na yawo yake a ban ƙasa amma tsahon lokaci muna nan muna jiranku da kai da ragowar mutun biyun."


Armad ya numfasa ya ce, "su waye mutun biyun kuma meye alaƙa ta dasu?"


Maulaya Furfura ta numfasa ta ce, "bani da hurumin gaya maka su amma ka biyo ni idan kana so kaji abinda zan ce." Tana rufe baki ta juya zata tafi amma Armad yai hanzari ya ce, "har yanzu ban yadda dake ba kuma indai kina so mu biyo ki sai kin bani wani tabbataccen abu."


Maulaya Furfura ta waiwayo a hankali, da kamar baza ta ce komai ba amma daga bisani ta ce, "kana shekara shida nazo ƙauyen ku. A kullum ina zuwa rumfar cinikin mahaifiyarka na karɓi abinci. Daga baya na daina zuwa kwatsam." 


Bayan ɗan gajeren tunani Armad ya tuno ta. Lallai akwai wata budurwa wadda take zuwa rumfar su tana karɓar abinci a matsayin almajira. Zaiyi wuya ya mantata saboda yawan lokutan data karɓar masa abinci ta cinye. Kuma a wannan lokacin Armad yana wannan rashin lafiyar saboda haka baya iya jure yunwa. Amma kuma wadda ya sani bata da furfura kuma bata da tabo a goshi, duk da mutane suna canjawa. 


Armad ya lissafa ya ga amfanin da zai iya fitowa daga wannan tattaunawa yafi sharrin saboda haka nan take ya ja hannun Nostaljiya suka bi bayan Furfura. 


Suna shiga masallacin, duniyar da suka bari a baya ta ɓace ɓat. Yanayin hasken dake sararin samaniya ya canja ya koma kore shar, sannan korayen rana manya guda biyu suka bayyana a sama suna juyawa. Nan take Armad yasan cewa ya bar duniyar mutane. Hatta ƙasar da yake takawa koriya ce shar babu wani launi akanta banda kore. Gine-ginen dake gabansu koraye ne fatau. Kowanne gini a zagaye yake da korayen bishiyu. Babu abinda ya faɗowa Armad sai Koriyar Duniya. 


Furfura ta kira wasu ɗalasimai ƙasa-ƙasa, nan take filin dake gabansu ya kaɗa ya juya ya yamutse kamar wanda ake tuƙa tuwo. A dai-dai wajen ƙofar Eycigan ta bayyana. Furfura ta shige gaba sannan tayi musu nuni dasu taho. Armad yai tunani yaga cewa tunda ya riga ya shigo tsaye-tsaye bashi da amfani. Idan mutanen nada buƙatar su cutar dasu da tuni sunyi. Dashi da Nostaljiya suka shige cikin ƙofar.


Suna shiga ƙofar ta ɗauke su ta kaisu can tsakiyar masallacin, cikin wani tafkeken fili. Ƙasar wajen an shimfiɗe ta da koren dinare kuma anyi mata kwalliya da bezar koriyar zakanya. Akwai ƙanshi na almiski dake tashi yana dukan hancinsu. Daga can nesa kana iya hangen toluwar masallaci da ginin masallaci a ƙasa. Wanda hakan ya nuna musu cewa tunda suka shigo a masallaci suke, sai dai kuma gagarumin masallaci ne wanda girmansa bazai misaltu. Hasalima yafi girma ta ciki akan ta waje. Akwai mutane da dama dake giftawa kowa yana harkokinsa. Ga gine-ginen makarantu can daga nesa suna hange. Wajen yafi kama da gari akan masallaci.


Yawancin mutanen da suke giftawa suna risunawa su miƙa gaisuwa izuwa maulaya Furfura kafin su wuce. 


Maulaya Furfura ta sallami Kunkuru da Taliya sannan ta ja su Armad izuwa wani ɗan ƙaramin gini dake ƙuryar gabas acikin masallacin. Wani abin mamaki shi ne ga rana a sama dalleliya har guda biyu amma hasken ranar baya ƙarasawa jikin wannan gini duk da kuwa babu bishiya ko wani abu da zai tokare shi. Akwai koriyar gansa-kuka ta bi jikin ginin ta rufe ruf, kai kace an shekara maitan ba'a taɓa wajen ba. 


Furfura ta nuna ɗakin ta ce, "kai kaɗai zaka iya shiga ciki. Matar ka a waje zata tsaya."


Armad ya kalleta a hasale ya ce, "wai kina tunanin zan danna kai ciki kawai ba tare da sanin meye aciki ba?"


Furfura ta girgiza kai a nutse ta ce, "idan muna son cutar dakai da tuni munyi tun kana yaro. Wannan ita ce dama ta ƙarshe da kake da ita ka gano bayani akan kurkukun Lokaci, ka san bayani akan ruhin da aka ara maka. Mutun biyu da aka ara muku ruhi tare sun riga ye ka. Amma baza mu takura ka ba, ko ka shiga ko ka juya duk ɗaya ne a wajen mu. Mudai mun cika aikin mu mun kawo ka. Ni kaina bani da masaniya akan haƙiƙaƙanin abinda na ciki zai gaya maka, amma tabbas nasan zaka fito a raye ba tare da an cutar da gashin kan ka ba."


Armad da Nostaljiya suka ja gefe sukai shawara kafin daga bisani Armad ya dawo ya shiga. Yana takawa kusa da ginin ƙofa ta bayyana a gabansa kamar dama shi ake jira.


Yana shiga wani koren haske ya dalle masa ido. Bayan ya lafa ya tsinci kansa yana lilo akan iska. Wani ikon izza na musamman wanda ya keta Kamalar-ruhi ya ƙanƙame jikinsa yadda ko motsi baya iya yi. Yayi ƙoƙarin mayarda jikinsa walƙiya amma yaji gaba ɗaya izzarsa ta ɗauke baki ɗaya. Ko ɗan'yatsa baya iya motsawa. 


A kewaye dashi filin ɗaki ne kawai babu kowa aciki sai shi kaɗai. Yana cikin kai-komo a ransa yaji murya a kunnensa. "Sannu da zuwa, ƁARIN RUHI NA." 


Akwai yana yi na murna acikin muryar.


Armad ya dudduba amma bai ga mai maganar ba. Al'amarin shi ne bai ma ji sanda akai maganar ba. Abinda bai sani ba shi ne saka masa maganar akai a kwakwalwarsa ba tare da an furta taba. Wani saurayi ya fito daga jikin bangon ɗakin kamar yadda ake tsamo ƙosai a mai, yana fitowa bangon ya koma ya haɗe.


Kamannin saurayin dai-dai suke da ɗan-saurayi wanda Armad ya gani acikin ruhinsa lokacin daya ƙaddamar da Miyurarsa. Sai dai a fuskarsa babu alamu na cewa ya taɓa ganin Armad. Kai a fuskarsa babu komai, babu murmushi, babu ɓacin rai kuma babu farin ciki. Kawai dai gashinan kamar gunki.


"SUNA NA TARIFIL-FAKTA." 


Muryarsa ma haka take babu komai acikinta kamar ta robot. Armad ya ƙifta ido tare da buɗe kunnuwa, yana kyautata zaton bai ji dai-dai ba.


"Kai ne Tarifil-fakta?!" Armad ya tambaya cikin mamaki da al'ajabi.


Maimakon Tarifil-fakta ya bashi amsa sai ya wuce yaci gaba da bayani. "A RANAR DA ZAN BUƊE KURKUKUN LOKACI A RANAR ZAN KARƁI RUHI NA. KANA ƊAYA DAGA CIKIN MUTUN UKU DA SUKA KARƁI RUHI NA SUKAI AMFANI DASHI. INA ZARE RUHI NA ZAKU MUTU HAR ABADA. AMMA MASALLACI YA YANKE SHAWARAR RAYA ƊAYA DAGA CIKINKU. SABODA HAKA MUTUN ƊAYA KAƊAI ACIKIN KU UKU ZAI RAYU."


Kafin ya gama gane yadda akai ɗan saurayi ya zama Tarifil-fakta zancen mutuwa ya taso wanda dole ya janye hankalin Armad daga miliyoyin tambayoyin da yake son yayi akan yadda akai ɗan saurayi ya zama Tarifil-fakta. Armad yayi ƙoƙari ya tara hankalinsa waje guda. Ga dukkan alamu wannan ita ce damarsa ta ƙarshe ya tambayi duk abinda yake so.


"Ya sunanka na gaskiya? Domin nasan Tarifil-fakta ba sunan gaskiya bane. Kuma yaushe nace ka ara min ruhi har da zaka fara maganar zaka karɓi abin ka. Kuma ko ka karɓi ruhinka mai yasa zan mutu? Ni ina nawa ruhin?"


"Baka da ikon sanin suna na na gaskiya a yanzu, mutun ɗaya daya rayu a cikinku shi ne zai san suna na cikakke. Zancen aron ruhi kuma ka tambayi Taidara da Zaikid da Fatima. Na gaya musu abinda zai faru idan nazo karɓar ruhi na kuma a haka suka amince."


Armad ya cije harshe a fusace domin kuwa Tarifil-fakta ya rufe masa baki tunda ya ambato sunan mahaifiyarsa. A zuciyar Armad koma mai Fatima tayi dai-dai ne. 


"Banda ni su waye mutun biyun da ka arawa ruhi?"


Tarifil-fakta ya amsa da cewa, "Ikenga da Bihanzin."


"Kuma dole mutun ɗaya ne zai rayu acikin mu?" Inji Armad.


Tarifil-fakta ya gyaɗa kai. "A ƙa'ida duk ku ukun mutuwa zaku yi, adalcin masallaci ne ya yanke shawara a bar mutun ɗaya. Da farko masallaci ya ce a zaɓi Ikenga amma daga bisani Sarkin-sarki tayi wa masallaci kyautar da ba'a taɓa yi ba a duniya, wanda hakan yasa dole aka bawa Bihanzin dama. An tsara komai tsakanin Bihanzin da Ikenga, amma a ƙarshe masallaci yayi adalci ya ce kai ma a baka dama. Saboda haka ku uku, mutun ɗaya ya rayu. Zaku iya sasantawa ku bar mutun ɗaya ko kuma mai ƙarfi ya ci."


Akwai miliyoyin tambayoyi a kwakwalwar Armad, saboda yawansu yama kasa zaƙulo wanda suka kamata. Yaci gaba da kwantarwa da kansa hankali yana gayawa kansa cewa wannan wani mummunan mafarki ne wanda zai farka ya manta. 


"Kai ka haɗa kurkukun lokaci?"  


"Ni ne."


"Yaya kurkukun take aiki? Yaushe zaka buɗe kurkukun? Kuma yaushe zaka zare ruhinka wanda ka aramin bada sani na ba?"


Saurayin ya ɗan jinjina maganar a ransa kamar zai tanka amma daga baya ya fasa. 


"Acikin kurkukun kwana ɗaya zai rinƙa maimaita kansa tsahon kwanaki saba'in. Banda ku akwai wasu ƴan tsirari da zasu iya gano wannan kurkuku amma ku kaɗai ne zaku iya karɓar horo aciki. Sauran mutanen ko mai suka koya zai goge idan gari ya waye. Ikenga, shi kaɗai, yana da damar ya ƙara mutun daga ɗaya zuwa goma acikin kurkukun wanda suma zasu iya karɓar horo. Masallaci ya ce duk mutun ɗaya da Ikenga ya ƙara kuma a baku dama ku saka mutun ɗaya."


A wannan lokaci wani tsakin ɓacin rai ya kwacewa Armad. Wai me yasa komai ace Ikenga? Mai Ikengan ya fisu?"  


A wannan lokaci Tarifil-fakta ya kalli agogon dake hannunsa ya ce, "kana da sauran daƙiƙa ashirin."


Armad ya cije harshe kamar ya daki saurayin. Mai yasa tun farko bai gaya masa akwai lokaci ba. Yana da tambayoyi da dama kuma ba lokaci. 


"Mai yasa ka samarda kurkukun lokaci? Meye amfanin ta?"


Tarifil-fakta ya ɗaga kafaɗa ya ce, "bana son Ururu su san da dawo ta shi yasa na tsayarda lokaci na samarda Kurkukun Bango."


A lokacin wata tambaya ta faɗowa Armad a rai wadda tuntuni ya kamata ace yayi ta. "Wai daga ina zuwa ina kurkukun ta shafa?"


"Daga doron ƙasa na farko zuwa na bakwai." Inji Tarifil-fakta kamar irin wasan yaran nan.


"Daga doron ƙasa na farko zuwa na bakwai?! Kana nufin ƙarfin izzarka ya kai ka samarda fasahar da zata shafi ko'ina a duniya? Mutun mai jini bashi da wannan ikon. Kai ko aljanu basu isa ba, sai dai mahalicci."


Armad yai shiru yana jiran amsa amma Tarifil-fakta yai masa shiru. Abu na farko da yake buƙata shi ne ya zauna yayi tunani akan dukkan abubuwan da suke faruwa ya nemo mafita. To amma yasan cewa zaiyi wahala ya ƙara samun wata damar irin wannan indai ya fita, sabida haka ya ci gaba da kwararo tambayoyi. 


"Ka gayawa Ikenga da Bihanzin wannan zancen?"


Tarifil-fakta ya gyaɗa kai. "Na gaya musu."


"Yaushe?" Inji Armad.


"Yanzu, a lokaci ɗaya nake gaya muku, acikin wannan ɗaki. Na rufe ganinku ne shi yasa baza ku iya ganin juna ba."


Armad ya waiga ya ƙara duba cikin ɗakin amma bai ga kowa. Ana haka lokacin sa ya cika. Tarifil-fakta ya ɓace sannan wata iska ta ɗebe shi tayi waje dashi. Bayyanarsa a waje yai arba da Nostaljiya da Maulaya Furfura suna tsaye suna jiransa. Daga can gefe kuma ya hangi wasu mutun biyu a tsaye. 


Na farko saurayi ne sanye da farar riga mai ratsin ruwan toka da kuma hular ƴan fulani mara faɗi sosai. Yana tsaye ƙiƙam kamar gunki yana kallon Armad da ido ɗaya. Da ɗaya idon kuma yana kallon ɗaya mutumin mai sanye da baƙaƙen kaya da alkyabba.


Ga dukkan alamu da gaske Tarifil-fakta yake da yace ragowar mutun biyun suna wajen, domin kuwa saurayin mai hular fulani Ikenga ne shi kuma mai baƙaƙen kayan ba wani bane illa Bihanzin. Kowannensu na kallon kowa yana lissafin yadda zai kashe sauran.


Ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa! Ta faru ta ƙare ga kowa ya bayyana. Hanya ɗaya kacal da zasu rayu shi ne su kashe junansu. 

***

Babi na 249-250

***

Armad da Ikenga da Bihanzin. Suna tsaye suna kallon juna kowa na lissafi, lissafi na musamman akan abubuwa masu yawa. Nisan dake tsakanin Bihanzin da Armad bai fi taku bakwai, saɓanin taku goma sha-ɗaya dake tsakanin Armad da Ikenga. Ganin Bihanzin kaɗai ya sosawa Armad wani miki acikin ransa mai raɗaɗi. Wuta abar ruruwa, wuta irin ta ƙiyayya ta fara ci acikin idanunsa da zuciyarsa. Ya dunƙule hannuwansa da ƙarfi har saida jini ya ɗauke a hannun wajen yayi fari alamar rashin jini. 


Bihanzin kawai murmushi yayi kamar babu wani abu daya taɓa faruwa a tsakaninsu. Ita kanta Nostaljiya nunawa yayi kamar bai taɓa ganinta ba.


Shi kuwa Ikenga yana tsaye yayi tigijim cikin wani irin kallo na isa da ƙasaita. Babu wani tashin hankali ko kaɗan acikin idanunsa, kai kace baya daga cikin wanda aka ce an basu kwana sittin su kashe kansu. 


Har izuwa wannan lokaci babu wanda acikinsu ya ce uffan, kowa yayi shiru yana jiran na kusa dashi. Ana haka Ikenga ya dubi Bihanzin ya ce, "zanyi mamaki ace mutun kamarka yana yawo da ruhin aro, musamman idan aka ce baka ma san da ruhin a jikinka kaba. Duk da yanayin tsayuwarka ya nuna abin ba haka bane. Ko yaushe mai dauwamammen sara ya haɗu da Tarifil-fakta?"


Bihanzin ya ɗaga kafaɗa tare da murmushi. Maimakon ya bawa Ikenga amsa sai shima ya cillo tasa tambayar. "Tun farko Ikenga shi aka so a raya a kashe mu, ni da Armad. Haka kuma Ikenga shi kaɗai aka yadda ya ƙara mutun acikin kurkukun lokaci, wai shin meye alaƙar Ikenga da Tarifil-fakta? Ni Bihanzin ƙarfi na ne yasa Tarifil-fakta ya bani ruhi, Armad kuma saboda shi ne babban maƙiyin Ururu, to amma zan so naji dalilin da yasa kamar jinin Oduduwa da Bayajidda ya karɓi ruhin aro."


Ikenga bai bada amsa ba.


Armad yana gefe bai ce komai ba. 


Can bayan ɗan lokaci Ikenga ya numfasa ya ce, "kun san Tarifil-fakta ya samarda kurkukun lokaci ne saboda kada mu kashe juna kafin ya gama haɗa jikinsa. Koda wanin mu ya mutu idan gari ya waye aka juya ƙara tashi zaiyi. Haka suma mutanen da na ƙara aciki koda sun mutu dawo wa zasu yi. Hanya ɗaya kacal da Tarifil-fakta zai dawo shi ne ya zari ran biyu daga cikinmu ya haɗa da nasa ya tashi. Shekara sama da dubu kenan ina aiki akan fasahar raba ruhi, nima zan iya sarrafa ruhi kamar yadda Tarifil-fakta yake. Idan na cire ɓangaren ruhin Tarifil-fakta dake jikinku na haɗa a nawa, Tarifil-fakta ba zai dawo ba. Sannan kuma baza ku mutu ba."


Bihanzin ya fashe da dariya. "Mai kake so ka ce?"


Ikenga ya ɗaga hannu biyu da kafaɗa a wani yanayi mai nuna cewa taimakon su yake so yayi. "Hanya nake baku da zaku rayu. Saboda daɗewar da ruhin Tarifil-fakta yayi a jikinmu yasa da namu ruhin da nasa duk sun haɗe sun zama abu ɗaya. Ta haka ne muka mallaki fasahar-mutuwa da ƙarfin izza irin wanda bamu isa mu samu ba."


Shin Ikenga yana nufin suma suna da Fasahar-mutuwa kenan? Armad yaji buƙatar yayi wa Ikenga wannan tambaya amma ya zaɓi yai shiru. A irin wannan yanayi da kowa ke ƙoƙarin hallaka ɗan'uwansa tambayar baza tai amfani ba. 


Ikenga yaci gaba da bayani. "A ƙa'idar yadda abin yake shi ne indai an zare ruhi to za'a mutu, to amma ina da fasahar da zata zare kaso casa'in cikin ɗari na ruhin dake jikinku ya bar muku ragowar yadda zaku ci gaba da amfana da sirri kan Tarifil-fakta."


"A ce na yadda duk abinda ka faɗa babu ƙarya aciki, idan hakan ta faru kai zaka zama kafi kowa izza, mu kuma izzar mu tayi ƙasa." Inji Bihanzin. 


Ikenga ya ce, "menene saɓanin hakan? Mutuwa zaku yi indai kuka bari kwana sittin ɗin nan ta ƙare. Cikin kyautayi da jin ƙai yasa na baku wannan dama bawai dan kun cancanta ba, domin ina da tabbas ni ne zanyi nasara a wannan yaƙi mai zuwa. Kai bari ma, kamar ma nayi nasara ne."


A karo na farko Armad ya ja numfashi a hankali, yadda idan baka nutsu ba baza kaji ba, ya dubi Ikenga ya ce, "idan kana da tabbas kayi nasara mai yasa har yanzu kake tsaye anan?"


Bihanzin da Ikenga suka juyo suka kalleshi. Bihanzin yana masa wani irin kallo wanda ke cike da mamaki, wai dama Armad zai iya magana a gabansu?! Shi kuwa Ikenga kawai murmushi yayi ya ce, "ko zanyi nasara ai dubban mutane zasu halaka a sakamako, idan za'a kaucewa faruwar hakan abin zaifi. Duk da bawai damuwa nayi ba, akan nayi nasara to komai zan iya sadaukarwa."


Koda akazo nan sai fuskar Bihanzin ta canja, buri da kafiya irin na baƙaƙen aljanu ya bayyana akanta. "Kun san cewa dukkan mutanen dake rayuwa a doron ƙasa daga mutun ɗaya suka samu. Wato mutun ɗaya ne da mace ɗaya suka haifesu. To amma wannan mata da miji sai ya zamana ƴaƴan da suke haifa suna da banbance-banbance na jinsi da ra'ayi. Wannan banbance-banbance su ne suka sa ake samun saɓani wanda har yakan kai ga yaƙe-yaƙe da zubda jini. Idan har ana so a samu zaman lafiya mai ɗorewa sai an kashe kowa sannan mutun ɗaya ya zaɓi mata wadda ta dace wadda zasu samarda sabuwar zuri'a a ban ƙasa. Zuri'a irin wadda bata da banbance-banbance. Zuri'a guda ɗaya tak. Babu wanda zai iya samarda wannan sai NI da SARKIN-SARKI. Indai kuna so a samu zaman lafiya a ban ƙasa to lalle ku sadaukar da rayukan ku a gare ni. Ni zan samarda zaman lafiya mai ɗorewa ta hanyar shiri na mai suna SABUWAR ZURI'A."


"Haha..." Ikenga yai dariya, "kamar ka kamar Kuyurussa'ayi. Shima haka yace min wai hanya ɗaya da za'a samu zaman lafiya shi ne ta hanyar Rukunai biyu: rukunin Amri da Jinzidal. Yana ganin mutane baza su iya zama lafiya da juna ba indai suna zaune kan doron ƙasa ɗaya, saboda haka ya sakko da duk wanda baɗan ƙabilarsa ba ƙasa. Sannan yana ganin mutane baza su zauna lafiya ba har sai ɗayansu ya zama bawa ɗaya kuma ubangida. Hakan yasa ya samarda rukunin Jinzidal. Amma a zahiri da kai dashi duk ƙoƙari kuke yi kawai ku mayarda duniya taku ta hanyar ƴan'dabaru. Ni Ikenga na Farkon Lokaci babu wani ɓeye-ɓoye a al'amura na; tunda aka haifeni bani da buri sai na mallaki duniya, badan komai ba saboda ina son mulki kuma dole ne a bani mulki. A haƙura a bani na yi, dalili na guda ɗaya shi ne: na kan mulkin ba wani abu suka fi ni ba, babu wani abu da suke dashi da bani da shi. Idan ana son zaman lafiya a bani, bazan yi ƙoƙarin rufe buri na da wasu dabarun samarda zaman lafiya ba. Kawai ina so, kuma dole a bani. Kamar yadda a wancan lokacin nace ina son ruhin Tarifil-fakta kuma dole aka bani."


Bihanzin bai nuna damuwa ko kaɗan da bayanin Ikenga ba. Kana gani kasan cewa dama yasan lissafin Ikenga. A maimakon haka sai ya juyo kan Armad ya ce, "ni na faɗi buri na da dalili na, shi ma Amraikugyu ya faɗi nasa, saura kai. A sanda na fara ganinka burinka guda ɗaya ka samu ƴan shekarun izza ka taimaki babarka, daga baya naji labari kana so ka hana cinikin bayi. Duk wannan yaƙin wasu kake shiga amma kai a zahiri baka da naka yaƙin. Idan kana dashi ka gaya mana."


Kai tsaye Armad ya ce, "buri na a bayyane yake amma saboda wanda basu da saurin fahimta zan dunƙule shi guri guda. Buri na shi ne: hallaka duk wani mahaluƙi daya cutar da iyalan gidana na, ko kuma yake da niyyar cutar dasu a nan gaba."


Bihanzin ya kashe Hidaya kuma yayi ƙoƙarin kashe Nostaljiya matar Armad, wadda kamar ƴa ce a wajensa. Sannan kuma anan gaba ma yana da niyyar kashe duk wanda ke yawo a ban ƙasa, wanda ya haɗa da ragowar ƴaƴan wilbafos. Saboda haka babu wanda bayanin Armad ya hau kai sama dashi. Sai dai kuma dama can Bihanzin yasan matsayinsa a wajen Armad, kawai dai bai damu bane.


"A gaban ƴa kake cewa zaka kashe ubanta." Inji Bihanzin, yana duban Nostaljiya a karo na farko tun bayan haɗuwarsu. Nostaljiya bata ce komai ba. Idan ka kalleta zaka rantse bata taɓa ganin Bihanzin ba saboda irin kallon da take bashi na adanki-yafi-dam. Amma a zuci babu wanda ta tsana kamarsa, shima ya sani kuma Armad ma ya sani.


Bihanzin ya ci gaba da cewa, "koda yake a wannan ƙarnin ne take ƴa ta, amma ƙarni biyu kafin shekarar miciji a wani matakin ta zo. Bari na baki labari nasan kin manta. A wancan lokaci, kafin na haɗu da sarkin-sarki, nayi yawo a ban ƙasa shekara da shekaru ina neman matar aure wadda zan aura na samardar SABUWAR ZURI'A da ita.


"Ina cikin yawo naji labarin wata farar mace mudubi mai yawan izza, sarauniyar tsohon birnin Fira dake doron ƙasa na huɗu sashin kudu. Na rankaya da asubahin fari domin ganewa ido na. Wannan sarauniya ba wata bace illa ke. Ina ganinki nasan akwai alamun kece wadda nake nema amma kafin komai ina buƙatar na gwada ƙarfin ruhinki ta hanyar jima'i. Rana tsaka na shiga fada na bayyana buƙata ta acikin jama'a. A lokacin kika bada umarnin a sare kai na. Sakamakon haka na kashe kowa a garin, tun daga tsoffi har zuwa na ciki, ke kuma na sace ki na tafi dake ta ƙarfin tsiya. Daga nan baki da buƙatar na ƙarasa miki bayanin abinda ya faru. Amma a taƙaice na sadu dake ta ƙarfin tsiya sama da sau...."


Tun daga lokacin da Bihanzin ya fara bayani Armad ya dunƙule hannunsa da ƙarfin tsiya har sai da farcensa ya shige cikin tafin hannunsa, jini ya fara ɗisa a ƙasa. Idanun Armad sukai jajawur. Wani baƙin jini ya fara zuba ta gefen bakinsa. A sanda Bihanzin yazo nan a zancensa tuni Armad ya daina tunani. Armad ya ɓace daga inda ya bayyana a gaban Bihanzin da jikin walƙiya jikin izza. Armad ya miƙa hannu ya cafi wuyan Bihanzin ya matsa har sai da ƴan'yatsunsa suka shige ciki, jini yai tsartuwa. Takobin walƙiya da izza da Negrinki ta sauka a tsakiyar kan Bihanzin ta tsarge shi gida biyu. 


Abin mamaki a wannan lokaci Ikenga ya bayyana a gaban Armad ya miƙa hannunsa guda biyu kan iska, ya kama ya yaga gida biyu. Dai-dai wajenda ya yaga sai wani baƙin jini ya fara zuba. Ikenga ya zare takobinsa ya kai sara yamma kan iska sannan ya dawo ya kai wani saran gabas, kudu da arewa. Ya tafa hannayensa guda biyu ya ɗaga su sama inda wani baƙin hatimi ya bayyana akan iska. Hatimin yana bayyana dukkan duniyar da suke ciki ta tarwatse ta fashe wata duniyar ta daban ta bayyana kamar yadda idan ka fasa mudubi wani abu daban zai bayyana a bayansa. A wannan duniyar babu komai sai hankakan mutuwa sama da miliyan suna yawo. Kowanne hankaka yana ɗauke da ruhi a ƙafafunsa yana yawo. Wata ƙatotuwar takobi baƙa ta kalli sama ta tokare da sararin samaniya. Ƙarfen takobin yana ɗisar da baƙin jini. Bayan daƙiƙu uku wannan duniya ta ɗauke inda wani Bihanzin ɗin sabo ya bayyana a bayan Armad da irin wannan takobin dake cikin duniyar data ɓace. 


Armad ya kira Kabanshisu da niyyar ɓacewa daga wajen da yake domin gujewa baƙar takobin. Amma abin mamaki shi ne kafin ya ƙaddamar da ɗalasimin takobin ta bayyana a wuyansa cikin saurin da yafi na Kaban'shisu. Abinda kawai ya taimaki Armad bai rasa wuyansa ba shi ne takobin Ikenga wadda ta bayyana ta tare baƙar takobin, amma duk da haka jini na ɗisa a wuyansa inda takobin taso ta yanka. Wasu baƙaƙen aljanu sama da dubu suka bayyana suka saka Armad a tsakiya. Amma kafin su aikata Armad wata rundunar ta jajayen aljanu ta bayyana ta tare su. Nan take Bihanzin da Ikenga suka shiga kaiwa juna sara cikin tsananin sauri da kwarewa. Kafin daƙiƙa ɗaya ta cika sun kaiwa juna sara sama da dubu. 


Bayan ɗan lokaci Ikenga da Bihanzin suka ja baya, kowa yana kallon kowa. Bihanzin shi ne ya fara mayarda takobinsa kafin daga bisani baƙaƙen aljanun su ɓace. Sannan Ikenga ya maida tasa takobin, suma jajayen aljanun suka ɓace. Duniyar da suke ciki ta ƙara ɓace wata ta bayyana. A wannan duniyar Armad yana tsaye a gefen Nostaljiya da Maulaya Farar-ƙasa Mai-yashi. Ikenga da Bihanzin suma duk suna wajensu a tsaye. Kai kace duk abinda ya faru a baya a mafarki ne. Abinda kawai zai iya nuna maka da gaske ne shi ne jinin da yake ɗisa a wuyan Armad.


Bihanzin ya fashe da dariya ya dubi Ikenga ya ce, "ban taɓa tunanin ban dani da sarkin-sarki akwai wani mahaluƙi da yake amfani da Kamalar-ruhi a matakin ƙarshe ba sai yau. Ga dukkan alamu bazan samu wannan ruhi a kyauta ba."


"Amfani da Kamalar-ruhi a irin wannan hali bai kamace ka ba. A ƙarshe dai mutun ɗaya ne kacal zai rayu," Inji Ikenga, "ko ni, ko kai ko Armad ko Tarifil-fakta ko Kuyurussa'ayi. Ina ganin bai kamata ka nunawa ragon-layya wuƙar da za'a yankashi ba tun ɗaya ga azumi. Ka ajiye fasahar ka, a kwana sittin masu zuwa za'a banbance aya da tsakuwa." 


Yana rufe baki ya juya zai tafi. 


Shima Bihanzin murmushi kawai yayi ya ce, "kwana sittin masu zuwa." 


Da Ikenga da Bihanzin suka ɓace. 


Har yanzu jikin Armad rawa yake. Wani sanyi irin na kabari yana fifita shi. Idanunsa suna kan wajen da su Bihanzin suka ɓace. A karo na farko Armad ya fahimci ratar dake tsakaninsa da wannan mutun biyu, ya kuma san mai ya kamata yayi acikin wannan kwana sittin.


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...