Skip to main content

BABI NA 271: Yaƙin Sisiya

 Babara yai tsalle ya dira kan katangar garin Jékis. Guguwar iska mai ƙarfi tai watsi dashi gefe guda kamar busasshen rake. Sai dai kuma hakan na cikin lissafi. Jikin Babara sai ya zama kamar wani mayan ƙarfe na iska. Duk iskar data taɓa shi sai ta manne a jikinsa. Sandarsa ta tsafi ta zama kamar wani kogo mai zurfi mara iyaka. Idan ka hango daga nesa zaka iske baƙar guguwa ta kewaye Babara zata halaka shi. Amma idan ka matsa kusa kaɗan zaka fuskanci cewa zuƙe iskar kawai yake. A ɓangare guda kuma ƙarfin iskar dake kewaye da garin ya fara raguwa. Ɗan kallo bazai gane ba amma Deba kallo daya zai ankare. 


A lokacin da Babara ke ƙoƙarin shanye wannan katanga, Cokali na gefe ya raja'a wajen zane. Littafi ne fari mai ɗiso-ɗison kaɗanya a jikinsa. Faɗin littafin ya kai kamu uku a kowanne ɓangare. Bangon nada kauri amma babu rubutu akai. Yanayin tsohuwar izza da tsufa na tashi daga jikin littafin. Ita dai fasahar marubutan farko kamar yadda aka sani fasaha ce da Maikiro Abbas da sauran marubutan farko suka samar. A shekarun baya Armad yayi arba da ita a Non-toch-teka wajenda ya samu littafin-takobi. Zaka iya taƙaice fasahar a jimla ɗaya tak: juya rubutu zuwa zahiri da kuma juya zahiri zuwa rubutu. 


Izzar Cokali takai matakin da yana iya juya rubutu zuwa zahiri tun kafin shiga duniyar aljanu. Abinda baya iyawa shi ne juya zahiri zuwa rubutu. Zaka iya cewa kamar sakandire ce da jami'a: za'a koya maka juya rubutu zuwa zahiri a sakandire, a jami'a kuma a koya maka juya zahiri zuwa rubutu domin kuwa yafi wahala. Kai hasalima Cokali bai taɓa tunanin zai kai matakin juya zahiri zuwa rubutu ba a rayuwarsa. Al'amarine da yake buƙatar a kwafi izzar abinda ake so a mayar rubutu. Cokali bashi da iko ko kuma fasahar da zai iya yin hakan. Kuma hakan ne yasa ya kakare a iyakacin sakandire - wato juya rubutu zuwa fasaha. 


Wani zai iya cewa juya rubutu zuwa zahiri yafi wuya akan juya zahiri zuwa rubutu. To amma juya rubutu zuwa zahiri abu ne da baya buƙatar kwafar yanayin-izzar abinda kake so ka samar. Abinda kawai kake buƙata shi ne fasahar marubutan farko da kuma littafin marubutan farko. Saɓanin juya zahiri zuwa rubutu. Misali kana so ka samarda takobi. Rubuta sunan takobin da bayanin ta acikin littafin shi ne kawai abinda kake buƙata. Saɓanin idan akwai takobi kuma kana so ka mayar da ita rubutu. Anan dole sai ka kwafi yanayin-izzar wannan takobi ka sakawa littafin kafin abin ya yiwu. Wanda kuma hakan shi ne abu mafi wahala wanda zaka iya cewa hatta marubutan farko sai da taimakon iyalan Wilbafos suka cimma burinsu.


Ko Cokali ya samu ƙarin matsayi bayan fitowa daga halwar da yayi ta kwana sittin?


A dai-dai wannan lokaci wani sihirtacce zaren izza wanda aka binne a ƙasan katangar garin ya bayyana. Yana bayyana ya kwafi izzar katangar garin sannan ya miƙawa Cokali ita. Cokali ya amsa ya miƙawa littafin dake hannunsa. Wato idan ka lura akwai wasu zarurrukan da suka taso daga cikin garin suka kawo wa Cokali samfurin izzar wasu manya-manyan gine-gine dake cikin garin. Nan take littafin marubutan farko dake hannun Cokali ya fara haske. Acikin hasken akwai alamu na godiya da jin daɗi, kai kace mai jin yunwa ne aka bawa furar izza da soyayyiyar jimina. 


Hohoho... Nan fa Cokali ya ajiye kasala a gefe ya fara rubutu. Alƙalamin hannunsa na ayrid ne (fari, siriri, mai cike da izza), littafin ma na ayrid ne, sannan kuma ga zaren izza taimako daga Ayúbu sarkin yaƙi. 


Katangar garin Jekis wadda aka gina a shekarar 1133 bayan Amri, wato shekaru 722 da suka wuce. Katangar tana da tsayi ƙafa ɗari uku da biyar a tsaye, a kwance kuma ta zagaye garin baki ɗaya a samfuri irin na badala.


Cokali na gama rubutu katangar ta fara girgiza. A zahiri fasahar marubutan farko bata buƙatar ka rubutu haƙiƙanin abinda kake ɓuƙata. Idan ka kwakwanta, ita fasahar da kanta zata ƙarasa maka. Wani fanni ne na izza wanda yake da ruhi nasa na kansa. Zaka iya cewa alamu-alamu ne na Deba.


Daga girgiɗi sai kawai katagar ta fara juyewa izuwa haske. Hasken ya dunƙule waje guda inda ya haskewa kowa ido. Cokali ya nuna hasken da ɗan'yatsa ya kira ɗalasimai. Ya haɗa ɗan'yatsansa na tsakiya na dama da kuma ƙaramin ɗan'yatsansa na hagu. Ya juya ƙafafunsa a wani salo na rawar aljanu, sannan ya ɗaga littafin sama yana ambaton ƙolumbotai.


Abin fa ba anan ya tsaya ba. Take Cokali ya kira aljanin sa. 


"A'Barbushe!"


A wannan lokaci aljanin ne da kansa ya bayyana a filin yaƙin. Basamuden ifritu wanda ya kai zira'i maitan a tsaye. Jikinsa akwai tsoka amma a saman tsokar wata koriyar wuta ce ke ci. A'Barbushe yana da jela tafkekiya wadda kaurinta yakai kamu hamsin. Akwai ƙahunhuna barkatai a goshinsa. Amma duk da wannan abinda yafi jan hankalin kowa shi ne idanun wannan aljani. Kwayar baƙin idon guda biyu ne acikin kowanne ido. Duk wanda ya kwana ya tashi a wannan duniya yasan wannan alamu ne na shaiɗanci. A taƙaice wannan aljani yana da jinin shaiɗanun aljanu a jikinsa. Aljanu mafi ƙarfi a ban ƙasa. 


Yana bayyana yai ƙaraji sannan ya risuna a gaban Cokali. A lokaci na farko halittar da tafi Cokali ƙaton ciki ta bayyana. 


A wannan lokaci tuni katangar garin ta gama juyewa izuwa dunƙulen haske. Aljani A'Barbushe ya buɗe hangama'un bakinsa ya haɗiye hasken. Ya juyo amayar da hasken cikin littafin ubangidansa.


Bayan komai ya lafa, haske ya ɗauke, ƙura ta lafa, sai akai arba da garin Jekis tsirara. Babu katanga babu alamunta. Acikin littafin Cokali zanen katangar ya bayyana. 


A dai-dai wannan lokaci tuni Babara ya gama shanye katangar guguwar da Deban nan huɗu samar. Sabida haka babu wani abu dake tsakaninsu da garin sai waɗannan Deba guda huɗu. 


Nostaljiya na gefe har yanzu bata motsa ba. 


Iliyasis ya taka izuwa gaban wannan Deba guda huɗu ya tsaya. 


"Suna na Iliyasis. Manzo ga sarki Armad Wilbafos." Ya nuna Nostaljiya. "Wannan ita ce sarauniya Nostaljiya mai ɗakin sarki Wilbafos ta farko. Waɗannan kuma sune Cokali da Babara, duk manzon ni ne iri na. An aiko mu da saƙo. Daga yau sarki Wilbafos, halattacen sarkin doron ƙasa ta farko, ya haramta cinikin bayi. Zaku fito da duk bayin dake cikin garuruwan ku. Zaku bawa kowanne bawa haƙuri ku nemi yafiyar sa da ayrid dubu goma. Idan baku yi gaggawar aikata hakan ba hukunincin sarki ya tabbata a kanku."


Ɗaya daga cikin Deban nan guda huɗu ya matso gaba. Yana da farar fata mai haske irin ta Elbinuil. Ga kunnuwa dogaye wanda Iliyasis yake hangowa tun daga inda yake. Wannan Deba yafi Iliyasis faɗi da cika ido da komai. Gashin kansa ya ɗan fara komawa fari-fari alamun girma. Yana sanye da kayan yaƙin rundunar Bihanzin kamar sauran dake bayansa.


"Suna na Liyurul Linbul, kwamanda na tara a rundunar mai iko, mai haske, sarauniya tun a farkon lokaci, hadari malafar duniya, SARKI-SARKI jinin Randuil Elbinuil, malama a fannin tauri." Ya nuna ragowar dake bayansa. "Wannan dake baya na duk manyan ma'abota izza ne wanda suka shiga wadin Deba shekaru hamsin da suka gabata. Saƙon mu guda a gare ku da sauran mutanen duniya shi ne SABUWAR ZURI'A."




Comments

Most Popular

297-300

 Armad da Nostaljiya na tsaye a gefen titi. Wata budurwa ƴar kimanin shekaru bakwai na tsaye a gaban su tana kallon ƙasa. Armad dai na sanye da jar riga yar-shara da baƙin wando. Tambarin Miyura na ɗamfare a goshin sa, sannan kuma, kamar kullum, idanun sa na hagu a rufe da audugar jamsiƙa. Ita kuwa Nostaljiya na sanye farar riga doguwa. Kanta babu ɗan-kwali tayadda gashin kan nata ya kwanto gadon bayanta. Duk inda ta motsa sai kaga gashin yana yalali yana haske abin sha'awa da ƙawa. Fatar jikin ta, kamar kullum, haske take bayarwa a duk sanda rana ta haska.  Amma duk wanda ya lura sosai zai gane cewa babban abin jan hankali shi ne wannan budurwa dake gaban su Armad tana kallon ƙasa. Rigar jikin ta baƙa ce dunɗum. Fatar ta ja ce jajawur kamar gashin kanta. Idanun ta kuwa wasu iri ne, maimakon alamar baƙin ido dake tsakiyar idon kowa ita takobin ce a tsakiyar idon ta. Kai hatta idon nata samfurin takobi ne - a fiƙe yake yake kallon doron ƙasa ta farko yanai mata izgili. Wani abi...