Littafi na Uku : Babi na 172&173 (Tarihin Hidaya)
***
Katafaren gidan Wilbafos yakai zara'i dubu a tsaye. Yana da ɓangare-ɓangare da lambu kala-kala wanda ƙoramu ke gudana ta cikinsu. Kallo ɗaya tak zakaiwa gidan kasan na manya ne. A ƙuryar arewa anan ɓangaren Hidaya yake. A dai-dai wannan lokaci wani dattijo ne ke kwala mata magiya.
"H...hidaya... Ki yafemin amma SARKI BISA BAKWAI ya ce idan ban gayyatoki ba yau ruhina zai ƙare. Ki taimakeni ƴar'uwa."
[Sarki Bisa Bakwai sarautace a zamaninda wadda ke mulkar sarakuna bakwai]
Bayan ɗan lokaci Hidaya ta fito daga ɗaki tana sanye da riga mara nauyi ruwan madara. Kyakkyawar surarta ta bayyana sosai. Dattijon na ganinta ya fara kyarma.
"Kai Ƙáyusu Wilbafos, ba daban sunanka na Wilbafos ba da tuni na zuƙe maka izza. Ka dame ni. Kaje ka gayawa shi wannan mutun da kuke cewa sarki bisa bakwai idan yana so ya ganni sai dai ya taso da kansa."
Tana gama magana ta kaɗa ɗan yatsanta lamarinda yasa iska ta ɗebe Ƙáyusu tayi cilli dashi waje.
Bayan kwana biyu ƙayusu ya dawo amma tare da wasu mutun uku.
Bayan sun wuni suna neman iso Hidaya ta fito ta dube su ta ce, "Waye acikinku sarki bisa bakwai?"
Mutun ukun suka dubeta cikin girman kai suka ce, "Mune sarakuna uku daga cikin sarakuna bakwai dake bautawa sarki bisa bakwai. Muna umartarki daki taho cikin lumana domin sarki bisa bakwai ya bamu damar mu ɗaukeki aka mu kaiki."
Hidaya najin haka fuskarta ta canja. Hadari ya haɗo cikin daƙiƙa guda sannan fuskarta ta bayyana a samaniya. Kowanne acikin sarakunan yakai matakin Sammai amma take shekarun izzarsu ta ɓace ɓat. Sarakunan suka zube ƙasa a sume. Bayan sun suma ruwan jikinsu ya fara ƙonewa har saida gangar jikin ta kama da wuta suka ƙone ƙurmus.
Sannan Hidaya ta kaɗe jikinta ta juya gida tana cewa. "har waye ya isa ya ɗauki ƴar sarki Aldaima aka."
Washegari mutun shida suka dawo. Abin mamaki uku daga cikinsu sune mutun ukun data ƙone jiya.
Hankali kwance a nutse ta dube su ta ce, "abinda mutane suke cewa akan wannan mutun wanda kuke kira da sarki bisa bakwai gaskiya ne kenan. Yana iya dawo da matattu. Zan kashe ku sannan naje na kashe shi sai naga waye zai dawo daku."
Hidaya ta ƙone su ƙurmus sannan ta ɓace daga harabar gidan wilbafos ta bayyana a bakin wata katafariyar fada. Hasalima duk girman wannan fada ba'a kan ƙasa take ba. Tana kan iska tana lilo kamar fadar doron ƙasa na farko. A ƙasan fadar akwai wani bakan gizo wanda abin mamaki mutane ne ke yawo akai suna harkokinsu na yau da kullum.
Abin mamakin shi ne bayan fadar akwai gine-gine na mutanen gari akan bakan gizon suka shaƙatawarsu. Ƙatoton gari akan iska sannan kuma ga wani garin a ƙasa. Sarakuna bakwai dake ƙasan wannan sarki sune suke mulki acikin garin ƙasan, shi kuma sarki bisa bakwai yana kan bakan kizo yana mulki.
Hidaya na bayyana ta ɗaure komai dake kan wannan bakan-gizo sannan ta zare takobinta ruwan ɗorawa. Ƙatotuwar fuskarta ta bayyana a sararin samaniya.
Hidaya ta ɗaga murya ta ce, "sarki bisa bakwai, koma waye kai ina gargaɗinka da kada ka ƙara damuna."
A dai-dai wannan lokaci dariya ta taso daga cikin fadar. Sannan abin mamaki sai waɗannan sarakuna shida data kashe suka ƙara bayyana. Sannan sarki na bakwai shima ya bayyana a bayansu. Bayan kowa ya hallara sai ƙofar fadar ta buɗe.
"Wani saurayi wanda shekarunsa baza su wuce na Hidaya ba ya fito daga cikin fadar. Yana sanye da jar alkyabba da hirami. Fuskarsa bata da kuzari sosai amma kana ganinsa zaka ji tsoro ya rufeka ka fara karkarwa. Iskar izza wadda ta haura matakin Sammai na tashi daga jikinsa.
"Hidaya Wilbafos. Ni shehu Amraikugyu Bayajidda inai miki barka da zuwa."
Hidaya ta kalleshi tsahon lokaci kafin daga bisani ta amsa da cewa, "kaine Amraikugyun da su Haruta da Maruta Ururu suke zance?"
Amraikugyu ya gyaɗa kai alamun eh.
Hidaya ta fashe da dariya sannan ta ce, "zaka je ka yaƙi Kuyurussa'ayi gaba-da-gaba?"
Ganin dariyar Hidaya yasa Amraikugyu ya canja fuska ya tafa hannunsa. Haka na faruwa wani saurayi ya bayyana a gefensa. Ya zare takobinsa ya afkawa Hidaya. Nan take ƙazamin yaƙi ya kaure. Cikin ƙanƙanin lokaci takubbansu suka tarwatse suka canja wasu. Saurayin ya kware matuƙa akan sarrafa takobin amma babban abinda yafi cima Hidaya tuwo a kwarya shi ne Balbalin wuta da jikinsa yake ya ɓata mata kaya.
Idan ka dubi wannan saurayi ba wani bane illa Han'ibal sarkin Jinzidal.
Saida suka kwana suka wuni suna fafatawa sannan Hidaya ta kashe Han'ibal amma abin mamaki tafa hannu kawai Amraikugyu yayi ya dawo dashi kamar ma bai taba jin ciwo ba.
Har yanzu Hidaya na tsaye ko gezau bata yi ba.
Amraikugyu ya dube ta ya ce, "Ƙaninki Armad bashi da lafiya tsahon lokaci. Kuma nasan maganin cutarsa. Idan kin yarda zaki yimin abu ɗaya ni kuma zan bashi magani. Wannan shi ne dalilin kiran ki."
Shekara bakwai bayan haihuwarsa ya fara wata rashin lafiya wadda tasa jikinsa ya daina girma kwata-kwata. Baya ramewa baya rage nauyi amma kuma sama da shekara goma bai ƙara nauyi ba. Kuma babu wani abu a jikinsa daya canja. Da farko anyi tunanin sirri ne na rashin tsufa irin na gidan Uzzus amma daga baya aka gano wani Dafi ne acikin ƙahon zuciyarsa wanda yake hanashi girma.
Wannan Dafi shi ne yake zuƙe izzarsa da ƙarfin jikinsa lamarinda yasa Armad ya daina girma.
Babu wani abu da gidan Wilbafos basu yi ba amma a banza. Daga ƙarshe sai Heeda ce ta sadaukarda izzarta take ciyarda wannan Dafi daga ƙarfin izzarta da shekarunta. Ta haka Dafin ya daina cin jikin Armad har Armad ya samu ya girma.
Tambaya ɗaya wadda hatta Heeda bata san amsar taba ita ce wanene ya saka wannan Dafi a jikin Armad?
***
A dai-dai wannan lokaci Amraikugyu yana iƙirarin zai samarwa Armad lafiya.
Hidaya ta numfasa ta dubi Amraikugyu ta ce, "Na baka daƙiƙa sittin."
Sarki Amraikugyu ya tafa hannu sandar tsafinsa ta bayyana akan iska. Yai nuni izuwa Hidaya da ita lamarinda yasa wani haske yai fitar burtu daga tsinin sandar ya shige jikin Hidaya. Hidaya bata motsa ba kuma ko kaɗan batai ƙoƙarin kaucewa ba domin tasan babu abinda wannan haske zai mata.
Hasken na taɓa ta sai surarta ta fara rabuwa gida biyu. Cikin daƙiƙa kaɗan sai Heeda ta rabe gida biyu. Ɓangare ɗaya ya rikiɗe ya koma siffar.... Armad Wilbafos ɗan shekara bakwai. Ɗaya ɓangaren kuma ya zauna a Heeda.
Sarki Amraikugyu yaci gaba da cewa, "kece halitta ta farko data fara gano sirrin wadin Déba meye yasa har yanzu baki haura wannan mataki ba? Ba wani dalili bane illa rashin lafiyar ƙaninki Armad Wilbafos. Taurari sun nuna mana cewa a kullum kina ɗura sinadarin Negrinki wanda yawansa yakai kimanin shekarun izza dubu talatin a jikinsa. Hakan nema yasa kika haɗa jikinki da nasa. Idan kika taimakeni na samo abinda nake nema zan warkar dashi."
Hidaya ta taɓa surar Armad wanda ke tsaye idanu a rufe lamarinda yasa surar ta narke ta koma jikinta. Sannan ta dubi Amraikugyu ta ce, "mai kake so?"
Amrikugyu najin haka ya bushe da dariyar murna sannan ya ce, "ai zaifi kyau na nuna miki. Muje zuwa."
Yana faɗar haka ya kirawo iska ta ɗaukesu dashi da Hidaya da Han'ibal tai sama dasu suka ɓace.
***
Tun bayyanar Hidaya, Han'ibal yake kallonta baice komai ba. Yau kwana uku da fara tafiyarsu acikin gajimare amma Han'ibal bai daina kallonta ba.
Hidaya ta fusata ta dubi Amraikugyu ta ce, "idan bai daina kallona ba zan cire masa idanuwa na kunna masa wuta wadda kai kanka baza ka iya dawo dashi ba."
Amraikugyu ya fashe da dariya ya ce, "shi ne babban hadimi na kuma zan ɗaga matsayinsa zuwa sarkin Jinzidal kafin na fita yaƙi da doron ƙasa na farko. Kuma..."
Hidaya bata jira ya gama ba ta juyo a fusace ta dubi Han'ibal wanda yayi tagumi yana kallonta. Tana kallonsa wata baƙar wuta ta tashi daga cikin idanunta ta sauka akan Han'ibal. Han'ibal ya fara ihu yana ƙoƙarin kaucewa amma cikin daƙiƙa ɗaya kacal baƙar wutar ta ƙone shi ƙurmus.
Ta dubi Amraikugyu ta ce, "bana son kallo."
Amraikugyu ya fashe da dariya ya girgiza kai ya ce, "Lallai kamar yadda ake faɗa zazzafar zuciyarki bata jira. Amma kiyi sani cewa lokacin mutuwar Han'ibal baiyi ba."
Amraikugyu ya tafa hannu lamarinda yasa tokar Han'ibal ta haɗe ta dawo jiki da tsoka da jini. Han'ibal ya dawo kamar yadda yake a baya.
Maimakon Hidaya ta ɓata rai sai kawai ta fashe da dariya ta ce, "lallai Amraikugyu kana da dabara a fannin izza, har ace zaka iya samarda fasahar da zata tserewa idanuwana. Wato ba dawo da wanda ya mutu kakeyi ba, lokacinda abin ya faru kake juyawa. Sai ka mayarda lokacin baya ya koma kafin abin ya faru amma a zahiri bawai matacce kake tayarwa ba. Haha.."
Amraikugyu ya zare idanu cikin mamaki ya ce, "lallai kin cika sarauniyar izza. Hatta Tarifil-fakta saida ya ɗauki kwanaki kafin ya gano wannan sirri amma ke kin gano shi cikin wuni ɗaya."
"Ka zigani yadda kake so amma idan baka ce ya daina kallona ba idan na ƙara kashe shi baza ka iya dawo dashi ba domin ZAN ƊAURE LOKACI DA ZAMANI. Mutun ɗaya daya isa ya kalleni shi ne WILBAFOS."
Amraikugyu ya numfasa ya ce, "tauraruwar Han'ibal ta riga ta ɗamfaru da soyayyarki amma bari na ɗaure idanuwansa dan idan kika kashe shi kinyiwa duniya asara."
Ya nuna Han'ibal da sandarsa ta tsafi lamarinda yasa idanuwan Han'ibal suka rufe ruf.
Sannan Han'ibal yaci gaba da cewa, "Da naji kince babu wanda ya isa ya kalleki sai Wilbafos sai na tuna da tarihin sarki Eyriyon. Kafin sarki Aldaima ƙabilar Wilbafos basa auren kowa sai ɗan cikin ƙabilar. Wato Wilbafos da Wilbafos. Badan komai ba sai dan kada wani bare ya sirka musu jini. A lokacin da Aldaima ya kawo ƴar ƙabilar Nara zai aura majalisar dattijai ta Wilbafos tayi ALLAH wadai da aniyarsa. Bayan Aldaima ya ƙeƙasa ƙasa ya aureta saiya fara haifo masu baƙaƙen idanuwa. Ban sani ba koda gaske ne amma naji ance ɗan Aldaima wato Eyriyon ya haɗa kai da ƴan majalisar dattijan Wilbafos sunyiwa babansa juyin mulki. Kuma daga nan aka saka doka duk ɗan ƙabilar Wilbafos bazai ƙara auren wanda baɗan ƙabilar ba."
Hidaya ta tari numfashinsa da cewa, "gidan Bayajidda kuna ganin kamar ku kaɗai kuka san sirrikan duniya ko? Bari na baka labari. Nasan waye Tarifil-fakta da alaƙarsa da gidan Bayajidda. Na kuma san sirrin fasahar SHAIBAL-SHÍSU da kuma Dafin da kuka saka a gidan Ururu. Ina mai tabbatar maka a duk sanda kai gangancin furtawa wata rai sirrin gidan Wilbafos sai na gayawa kowa wannan abubuwa."
Amraikugyu kyakyace da dariya. Bayan tsahon lokaci ya numfasa ya ce, "ina bada haƙuri. Da gidana da gidan Wilbafos in sunyi rigima babu wanda zaiyi nasara saboda haka babu amfani mu rusa kanmu Ururu suna kallo.
"Abinda nake so kiyimin shi ne ki samarmin hanya na wuce ta titin Bayajidda na shiga duniyar dake bayan duniyar ƙasa bakwai. Akwai al'ummatai masu bautar rana da wata wanda suka tare hanya suka hana ni wucewa. Indai kika samarmin hanya take zan warkar da Armad."
Hidaya ta haɗe gira ta ce, "Kai mai yasa baza ka samarwa kanka hanyaba?"
Amraikugyu yai murmushi ya ce, "fasahata sirri ce. Kuma ina ɓoye tane domin fafatawa ta da Kuyurussa'ayi. Idan da inada ƙarfinda zan iya buɗewa kaina hanya ba tare da nayi amfani da wannan fasaha tawa ba da bazan neme kiba."
Comments
Post a Comment