"Wacce rawar kake so na nuna maka, Iliyasis? Akwai rawar amare, akwai ta angwaye."
"Hmm. Mai zai hana a nuna min duk biyun?" Inji Iliyasis.
"Bakai haɗama ba?"
Iliyasis ya girgiza kai. "Ko kaɗan. Shi ma'aboci takobi a har kullum buɗe ido yake domin ya hango Rawar da tafi tasa ko zai iya koya ya ƙara ilmi."
Maruta ya ɗanyi shiru yana jiman ta abin acikin ran sa kafin daga bisani yayi gwauron numfashi ya ce, "toh, idan ka shirya ka taho."
Iliyasis ya girgiza takobin sa, ya ce, "ai kullum a shirye nake." Da wannan yai azama ya afkawa Maruta.
Dukkan ɓangarorin biyu suna tsaye gefe guda suna kallo babu wanda yace uffan. A ɓangare guda su Nusi sun aminta da Iliyasis, ba dan komai ba sabida sun ga fasahar sa ido-da-ido a lokacin suna halwa. A ɗaya ɓangaren kuma Maruta ba ɓoyayye bane; babu wanda bai san shi ba tun daga saman ƙasa ta ɗaya har zuwa ƙasan ƙasa ta bakwai. Indai su Nusi basu shigar wa Iliyasis ba, to kuwa zai zamo abin kunya a gare su su shigar wa Maruta. Hasalima Haruta, wanda shi ne yafi kowa sanin Maruta, yana ganin abin dariya ne ace wai za'a shigar wa Maruta faɗan takobi.
Iliyasis bai damu da abinda na gefe suke tunani ba. Abinda ke ran sa shi ne yadda zai sare kan Maruta da takobin sa. Yasan abokin karawar sa bajimi ne, ƙanin Kuyurussa'ayi, to amma duk wannan baya gaban sa ko kaɗan. A wannan lokaci kaifin takobin sa da kuma yadda zai sarrafa ta shi ne kaɗai a gaban sa. Yana tafiya yana sassarfa kamar wani ingarman doki. Yana kaɗa takobin sa.
Shi kuwa Maruta a tsaye yake cak. Ko ɗaga takobin sa baiyi ba. Kai kace bashi Iliyasis yake hari ba.
Koda ya rage saura taku huɗu a tsakanin su sai Iliyasis yai tsalle sama ya kawo wa Maruta sara. A wannan lokaci wani baƙin hayaƙi na Negrinki ya fito daga hannun sa ya shiga jikin takobin sa. Nan take takobin tai baƙi-baƙin kamar idanun Ururu. Wani tiriri ya fara tashi daga jikin ta.
Maruta ya kawo wa Iliyasisi sara da tasa takobin. Acikin saran babu wani alamun dagewa. Zaka iya cewa takobin Maruta tafiyar wahainiya take idan ka kwatantata da takobin Iliyasis. Sannan, saɓanin takobin Iliyasis wadda ke tiriri, takobin Maruta babu ko alamar ɗumi a jikin ta. Da dama zasu bawa Iliyasis nasara ko dan sabida girman takobin sa.
Takubban biyu suka haɗu a sama - ko kuma ince haka Iliyasis yayi tunani - sai dai kuma kash, ko kaɗan takubban basu haɗu ba. Abinda ya faru shi ne: takobin Maruta Rawa tayi (irin Rawar amare a ranar bikin su) akan kaifin takobin Iliyasis, sannan tayi juyi ta wuce ta gefen takobin ta sari hannun Iliyasis. A lokaci guda shi kuma Maruta taku ɗaya yayi izuwa gefe ya bawa takobin Iliyasis dama ta wuce ta sari iska.
Tun daga farko har ƙarshe Maruta motsi biyu yayi kawai: na farko sanda ya miƙa takobin sa ya kai sara; na biyu kuma sanda ya matsa gefe ya bawa takobin Iliyasis hanya. Babu maguɗi babu rufa ido, kawai Rawa ce, Rawa irin ta takobi.
"Aaargh..." Iliyasis yai ƙara jin takobin ta ratsa jikin sa. Yai sauri ya kira aljanin sa tare da juyewa izuwa tsuntsu. Kowanne tsuntsu da tasa takobin. Tsuntsu sama da ɗari suka kewaye Maruta, kowanne yana kawo masa hari ta ɓangare daban. Idan a baya ya kare takobi ɗaya to yanzu ga takobi ɗari nan.
"Idan baza ka nutsu ka gane matsayin ka ba, to ya zama wajibi na fahimtar dakai." Inji Maruta. Yana rufe baki yakai sara kan iska da takobin sa. Wani bakin layi ya bayyana akan iska. Nan take iska ta dare gida biyu ta tarwatse, wani wawakeken rami ya bayyana akan iska tare da iska mai ƙarfin gaske wadda ta zuƙe tsuntsayen Iliyasis cikin ramin.
Iliyasis yai sauri ya fice daga jikin tsuntsayen ya tsallake gefe yana haki. Har yanzu ko gumi Maruta baiyi ba, idan ka lura zaka fuskanci cewa babu alamun gajiya a tattare dashi ko kaɗan, kai kace kawai ɗan motsa jiki yake. A gefe guda Iliyasis yayi wujiga-wujiga, haki kawai yake. Taƙamar sa tana kan Negrinkin sa, to amma a yadda abubuwa suke tafiya babu alamun za'a bashi dama yayi amfani da ita. Yana cikin tunani yaga gilmawar takobi ta gefen idon sa, kafin ya ankara maɗaukakin sara ya dira a kafaɗar sa. Takobin ta ratsa ta shige ciki. Jini yai feshi kamar ana ruwan sama.
Ba tare da tausayi ba takobin ta ƙara ɓacewa, inda ta bayyana a saitin wuyan sa tana nufin tsinke masa kai. A wannan lokaci Babara yasa sandar sa ya tare takobin. A ganin Babara bashi da amfani su ci gaba da tsayawa a gefe tunda alamu sun bayyana anfi ƙarfin ɗan'uwan su. Ba wai shi kaɗai ba, Inara ma tsalle yayi ya saukar wa da Maruta Hannun Aradu. A can gefe kuma zaren izza ne ya sauka ya kwafi yanayin izzar Maruta ya saka acikin littafin marubutan farko dake hannun Cokali.
Cokali ya fara rubutu.
*
Suna: Maruta Ururu - ƙani a wajen sarki bisa doron ƙasa ta farko; yaya a wajen Haruta Ururu.
Siffa: tsayi zira'i shida, gashi baƙi, ido baƙi, fata fara, gemu baƙi gajere, kakkaura mai doguwar haɓa.
Mataki: deba
*
Koda ya kammala rubutun sa sai ya tattara izzar sa waje guda, sannan ya himmatu wajen ƙoƙarin zuƙe Maruta cikin littafin.
Amma abin al'ajabi Maruta ko gezau baiyi ba. Yana tsaye Hannun Aradun Inara ya dira a kan sa amma ko gwarzane. Kai ko motsi baiyi ba, yana tsaye ƙiƙam, tsohon tsauni mahadi ka ture.
Iliyasisi, Babara da Cokali suka haɗa hannu waje guda suka ƙara afka masa. Da taɓon Babara, da aljanin Cokali A'Barmushe, dana Iliyasisi Jurnutu da kuma walƙiyar Inara - wadda gado ce a wurin Armad - suka haɗu suka daki Maruta. Ƙura tai sama. Babu abinda kake gani ko ji face tiriri da rugugin fasahai.
Amma bayan komai ya lafa Maruta yana nan ƙikam baiyi ko gezau ba. Kai kayan jikin sa ma babu ko ƙwarzane a jikin su. Nan fa kallo ya koma sama. Sukai zuru suka zuba masa ido. Wannan shi ake cewa gaba da gaban ta; aljani ya taka wuta. Kuma komai asubancin ka akwai wanda a tafe ya kwana.
"Idan kun gama to ni zan fara." Inji Maruta. Ya ɗaga baƙar takobin sa sama, sannan ya saukar musu da ita, sauka ta musamman.
Comments
Post a Comment