Fatima ta cije baki. A duk tsahon rayuwarta babu wani mutum guda daya kyautata mata kamar Maikiro'Abbas. Tun tana jaririya yake riƙe da ita. Yanzu gashi ta girma ta mallaki hankalin kanta amma har yanzu bai daina ba. A dalilinta gashi ya fito yaƙi duk kuwa da ƙinsa da zubar da jini da kuma daɗewar da yayi rabonsa da yaƙi. A lokuta da dama ta kance ko mahaifinta bai nuna mata kaunar da Maikiro'Abbas ya nuna mata ba.
Yanzu haka zata zamo sanadiyyar halakarsa? Ta sani yana da ƙarfi na gaban misali amma tana tsoron Ururu. Yaya zata yi da rayuwarta idan ta tabbata ita ce sanadiyyar mutuwar Maikiro'Abbas?
Wani zazzafan hawaye ya zubo mata.
Ga ƴan'uwanta yarima Najunanu da yarima Umaru da yarima Abba duk sun zo domin su cece ta. Idan wani abu ya sami wani acikinsu baza ta iya rayuwa da hakki ba.
Ga Armad....
Koda tazo kan Armad sai hawaye ya fara gudu akan fuskarta. Yanzu haka ƙaddarar ta zata kasance? Duk ƙoƙarin da tayi dan kare Armad da Abijan baiyi aiki ba, kamar ƙara ingiza wutar tayi.
"Kuka ki keyi?" Maruta wanda ke zaune a gefe ya tambaye ta ba tare da ya juya kai ya kalleta ba.
Fatima ta tsaida hawayenta ta kalli Maruta ta gefen ido.
"Maruta," ta kira sunansa. "Nasan mai kuke yi, amma baza kuyi nasara ba."
Maruta ya juya ya ƙura mata ido na ɗan lokaci kafin yaja numfashi ya girgiza kai.
"Bana farin ciki da mutuwarki. Kai bana farin ciki da mutuwar duk wani abu mai rai komai kankantarsa. Da ace bayi sun san wahalar samar da rai da basu yi gaggawa wajen kashe shi ba."
Yana magana yana jimanta abun a ransa.
"Amma kashe ni ya zama dole, ko?" Inji Fatima.
"Haka ne." Maruta ya gyada kai cikin tunani. "Dole a fitar da shugaba a ƙasashen ƙasa indai ana so a samu zaman lafiya irin na doron ƙasa ta farko. Dole ne ya zamana sarki ɗaya ne yake mulki ba sarakuna da yawa ba. Nayi bincike akan hakan tsahon shekaru kuma na miƙawa babban sarki Kuyurussa'ayi sakamakon dana samu. Hakan shi ne yasa sarkin ya kirawo kamfen domin a rushe duk wani tsari na gamayya a dawo tafiya guda ɗaya - tafiyar Ururu."
"Wato kai ne ka ingiza wannan yaƙi kenan?" inji Fatima. "Kuma koda an kama ni ko ba'a kamani ba sai anyi shi?"
"Eh... to," inji Maruta. "Tunda aka zo maganar kamfen dole wasu zasu yi tawaye. Bamu da dama face muyi musu ladabi ta hanyar kisa. Amma kamar yadda na gaya miki ana bukatar a dawo tafiya guda. Kuma barin mutane irin su Maikiro'Abbas a raye bazai haifarwa da kowa ɗa mai ido ba."
"Hmm.." Fatima tayi murmushi mai ɗaci. "Wato duk akan babana kuke yi kenan?"
Ba kunya Maruta ya gyaɗa mata kai.
"Amma, Fatima, kece tarkon. Idan bamu kawo ki nan ba tayaya zamu tara kowa? Duk da dole ne mutuwarki a yanzu ko dan saboda ƴan jaridu da kuma idon duniya amma bamu damu dake ba. Zarar Maikiro'Abbas ya tafi shikenan kamfen ya cika ko a wajen babban sarki Kuyurussa'ayi."
Ran Fatima tuni ya fara tafasa. Ta buɗe baki zatai magana amma ta kasa. Dole ta ɗauke kai daga Maruta ta dawo kan filin dake gabanta.
Daga can ƙofar shigowa ta hango babanta Maikiro'Abbas. Taku dai-dai ya matso gaba. Kamar sama tana biyayya ga aniyarsa sai ruwa ya fara zuba. A lokacin Armad ya lura sarkin acikin shirin yaƙi yake. Babu sulke, babu kwalkwali, babu takobi, amma kallo guda zaka san acikin shirin yaƙi yake. Gabjeje ne mai tarin damatsa da kauri, sannan kuma ga buwaya. Ga littafi nan a rataye a kafaɗarsa ta dama, da kuma jakar tsafi a rataye a kafaɗarsa ta hagu. Boka yakai boka.
Ya ɗaga hannu sama ya kira babbar izza. Nan take ruwan dake zuba na sama ya ƙaru. Duk wanda ruwan ya taɓa sai kaga ya haɗe gira yana kallon jikinsa.
A ɓangare guda rundunar Ururu mamaki suke yadda suka ji ƙarfin su da ƙarfin zukatansu yana raguwa. A ɗaya ɓangaren kuma rundunar Maikiro'Abbas murna suke yi yadda suka ji ƙarfin su yana ƙaruwa. Sai dai ko kaɗan ba haka abinda yake ba. Armad wanda ya shiga gadar zare yasan ainihin abin kawai ikon Kuyurussa'ayi Maikiro'Abbas ya rage. Irin ikon da yake sawa abokan gabar Ururu su karaya tun kafin a fara yaki. Ance kada ka soma faɗa da Ururu idan baka karya wannan iko ba. Kuma Armad yaga hakan a aikace a yayin faɗansa da Haruta. Har sai da yayi amfani da sirrin Negrinkinsa ya rage ƙarfin ikon Ururu sannan yayi nasara.
Babban abinda ya bawa Armad mamaki shi ne yadda Maikiro'Abbas yayi abin a nutse, hankali kwance. Kamar bai san yana yi ba. Bayan Armad sai ya samar da mutun-mutumi sannan yake iya tara Negrinkin da zata ishe shi. Duk da haka girman wajen da Armad yake iya canjawa bashi da yawa, amma Maikiro'Abbas ya canja dukkan filin yaƙin. A halin yanzu ikon Ururu ya kau. Kowa da ƙarfinsa zaiyi amfani.
Armad ya ƙara kallon marubuci a karo na biyu. Irin yanayin yadda yake sakar izzarsa daki-daki kasan akwai kwarewa. Acikin kowanne ɗigon ruwan sama daya zuba akwai sihiri. Abinda yafi bawa Armad mamaki shi ne bai ga sanda Maikiro'Abbas ya saki izzarsa ba. Koda ka ɓoye ɗalasimin da kayi amfani dashi izza baza ta ɓuya ba. A irin kwarewar Armad yaci ace yaga sanda Abbas yayi amfani da izza.
Yana cikin nazari Maikiro'Abbas ya ƙara taku biyu. Nan take ruwan sama ya ƙara tsugewa.
"Hmm... Dul'Ururu!"
Dul'Ururu Wanda ke ɗaya ɓangaren yana kallon Maikiro'Abbas ya matso gaba ya tsaya.
"Maikiro'Abbas!"
Sukai kallon-kallo na ƴan dakiku kafin Maikiro'Abbas ya fashe da dariya.
"Da fatan ƴa ta tana nan kalau."
Dul'Ururu ya kada kafaɗa.
"Ba ƴarka bace. Al'ummar ƙasa bakwai sun shaida an saida ita a matsayin baiwa. Ni Dul'Ururu na sayi Fatima a matsayin baiwa sannan kamar yadda doka ta tanada a yau zan sayar da ita ga mai so. Shin Maikiro'Abbas meye zalunci acikin abinda na aikata? Mai yasa har zaka haɗo runduna kazo doron ƙasa ta biyu bayan kana sarkin jinzidal wanda daku aka kafa wannan dokoki?"
Maikiro'Abbas yayi shiru ya ƙura masa ido baice komai ba. Bayan ɗan lokaci ya jada baya taku ɗaya sannan ya ɗan juya. A wani salo na tsananin kwarewa ya daki iska da bayan hannunsa na hagu. Iska ta fara ƙugi, ƙasa tana girgiza. Wani haske mai kama da walkiya ya bayyana akan iska wanda yasa dole kowa ya rufe ido. A sanda Armad ya buɗe ido abin mamaki ya gani. Tsaye akan iska dai-dai gaban Maikiro'Abbas wani tafkeken gida ne. Fadinsa ya kai kafa dubu. Akwai manyan diraku a kafe a kowace kusurwa ta gidan. Ga wasu katangu masu nuna alamun daɗewa da kwari.
Yanayin fentin da tsarin ginin kamar Armad ya taɓa ganinsu. Kai hatta ƙatuwar ƙofar shigar da tsarin katangar....
Armad ya haɗe gira yana nazari. Ba jimawa ya gano tabbas ya taɓa ganin wannan gini sai dai kuma ya kasa tuna a ina yasan shi.
"Non-toch-teka!"
Wani sadauki a bayansa yace.
Nan take da dama suka ɗauka.
"Ai kuwa Non-toch-teka ce. Kaiii... to mai ya kawo ta nan?"
Wannan ƙananun mayaƙa kenan. A nasu ɓangaren Salsa wanda ke tsaye a bayan Maikiro'Abbas fuska a rufe. Da ya'yan sarki uku (Najunanu, Umaru, da Abba) duk sun san abinda ke faruwa.
Abinda ya bawa Armad mamaki shi ne girman ginin da kuma yadda sarkin ya samar dashi hankali kwance. Gashi yana dauke da izza amma Armad ya kasa gane lokacin da sarkin yake sakar izzar. Hakan yana da muhimmanci sosai a wajen Armad domin kuwa idan baya ganin sanda sarkin yake sakar izzarsa to kaga kenan bazai iya tare izzar ba. Daɗinta kawai a wannan lokaci Armad a ɓangare ɗaya suke da sarkin saboda haka bashi da buƙatar ya damu da hakan. Abinda yafi ɗaukar hankalinsa shi ne mai sarkin yake niyyar aikatawa da ƙatoton gini irin wannan? Shin da gaske Non-toch-teka ya kawo ko kuwa kawai ginin ne?
Da sannu ginin ya fara tafiya yana dosar abokan gaba. Yana tafiya yana ƙara gudu. Kara da rugugi suna tashi. Nan da nan hankalin abokan gaba ya tashi.
A lokaci guda Dul'Ururu ransa a ɓace yake. Magana yake yiwa Maikiro'Abbas amma maimakon ya bashi amsa da baki sai ya kawo masa hari.
Rundunar sadaukai dake ƙasa suka fara jada baya. Girman ginin Non-toch-teka yakai rabin Filin jiri baki ɗaya. Tabbas idan ya diro musu babu makawa ƙarshensu yazo.
Ana cikin wannan yanayi na firgici sarki ƙaraiƙisu ya tashi kan iska ya tunkari ginin. Baki a buɗe kowa ya bishi da kallo ana jira a ga mai zai aikata. Ko babu komai duk girmansa ginin ya ninka shi girma sau hamsin zuwa sama.
Amma hakan bai tsorata basamuden ba. Suna yin gaba da gaba yasa kai ya tunkuyi ginin da goshi, kai kace rago ne yake tunkuyar rago. Wata ƙara ta tashi sama kamar karfe ya daki karfe. Ginin yana dannowa, shima Ƙaraiƙisu yana dannashi da ƙahonsa. A sama suka ci gaba da gogayya, a ƙasa kuwa mutane sun dafe kayikansu sun kuma toshe kunnuwansu saboda ƙara da kuma tsoron kada gini ya faɗo musu.
Bayan minti guda ana wannan dambarwa ƙahon dake goshin ƙaraiƙisu ya fasa ginin ya shige ciki. Nan take ginin ya tsatstsage. Iska mai ƙarfi ta shiga cikinsa. Shi kuwa ƙaraiƙisu dannawa yayi da dukkan ƙarfinsa ya fasa ginin har ciki. A gaban idon kowa gini ya fara darewa yana fashewa.
Ƙaraiƙisu ya jada baya yana lasar baki. Idanunsa suna kan Maikiro'Abbas, kamar yana gaya masa ya ƙaro wani harin, ko kuma wancan harin yayi kaɗan. Duk wanda yaga Ƙaraiƙisu yasan yana alfahari da ƙarfinsa.
Nan take rundunar Ururu suka fara shewa suna kiraye-kiraye.
"Ururu!"
"Ururu!!"
"Ururu!!!"
Sai dai kuma zaka iya cewa murna ta koma ciki. Ginin yana gama rushewa wata ƙatuwar Ƙawanyar ƙanƙara ta bayyana acikinsa. Wato daman babu komai acikin wannan gini sai wannan ƙawanya.
Jikinta a sumulmule yake. Babu abinda ke tashi sai hayakin sanyi da ƙanƙara. Abin mamaki babu alamun wannan ƙanƙara zata narke domin kuwa ko ɗison ruwa babu a jikinta. Kada dai a manta banda fasahar marubutan farko da sarki Maikiro'Abbas ya kirkira, shi ne ma'aboci kwangilar ruwa da ƙanƙara a ban ƙasa. Kuma lallai yau ya shirya tsaf domin ya baje kolinsa.
Ƙawanyar tana dai-dai saman rundunar Ururu tayadda a tsakiyarsu zata fado. Kafin kowa ya ankare ƙawanyar ta fara faɗowa ƙasa. Sadaukai suka fara ihu neman agaji. Ƙaraiƙisu yayi kururuwa ya tari ƙawanyar ta ƙasa. Hannayensa biyu ya saka ya cafeta sannan yayi sama da ita.
Har sun fara nishin farin ciki sai suka kula hannun ƙaraiƙisu ya fara ƙanƙara. Ba shiri ya saki ƙawanyar taci gaba da faɗowa domin idan baiyi haka ba to dukkansa zai ƙanƙare. Kamar ya haƙura amma abinka da tsohon mayaki. Kawai sai ya tashi sama da sauri ya dawo saman ƙawanyar ya saka ƙahonsa ya dake ta da niyar tarwatsa ta.
Tsananin ƙarfi iko irin na tsoffin samudawa ya fita ta cikin ƙahon ya daki ƙanƙarar. Nan take ta tarwatse tayi daga-daga.
Kamar an gama amma kawai sai jama'a suka tsinkayi ruwan zafi mai tururi a tsakiyar ƙanƙarar. Ko tayaya aka yi ruwan zafi ya haɗu da ƙanƙara amma bai salamce ba? Wannan tambaya ce mai muhimmanci amma a wannan lokaci babu wanda yake da lokacin amsa ta domin kuwa ruwan zafi ne fara zuba yayi akan mutane. Duk wanda ya taɓa sai kaga ya zube yana ihu, fata tana salubewa. Ko ƙasa ya taɓa sai kaga wajen yana hayaki. Kuma idan ka ɗaga kai sama zaka tabbatar yanzu aka fara. Akwai wani babban sihiri wanda ya hana ruwan zafin zuba a lokaci guda. Duk inda mutane suka fi taruwa sai kaga ruwan yafi zuba. A hankali a hankali shirin rundunar Ururu ya fara wargatsewa tun ma kafin a fara yaƙin.
A wannan lokaci kwamanda Yurba ya tashi daga kan kujerar yayi sama kan iska ya tari ruwan. Hannaye ya watsa ya kira ɗalasimi.
"Turɓayar-gini!"
Ta cikin kowane ɗan'yatsansa wata jikakkiyar ƙasa mai kauri ta fara fita tana rufe ruwan. Cikin dakiku ƙalilan ƙasa mai tarin yawa ta fita daga hannunsa. Kafin kace kwabo ta rufe ruwan baki ɗaya. Idan ka hangi abun daga nesa kace tsauni ne akan iska.
A hankali tsaunin ya fara faɗowa ƙasa kan mutane. Yurba ya samar da durkokin ƙasa ya tare tsaunin ta ƙasa. Abin ya zama kamar wata rumfa.
Bayan kimanin minti guda abubuwa suka lafa kowa ya dawo hayyacinsa sai aka fuskanci duk abinda ya faru hari ne guda kurum. Lallai yau za'a sha kallo.
Filin yaki ya canja kama. A halin yanzu akwai ƙatotowar rumfa ta ƙasa a saman rundunar Ururu wadda a kowanne lokaci zata iya faɗowa kansu.
Maikiro'Abbas yayi gyaran murya. A yanzu ya shirya ya bawa Dul'Ururu amsar tambayarsa.
"Babban kuskurenku shi ne girman kai," inji Abbas yana nuna dai-dai inda Yurba ya rufe ruwan zafin. "Kana rufe ruwana yana ƙara zafi. Idan yayi zafi da yawa sai ya fashe. Buuummm!"
A lokacin Yurba ya fuskanci mai Maikiro'Abbas yake nufi. Da sauri ya ɗaga hannu yana ƙoƙarin narka ƙasar data rufe ruwan amma ya makaro. Kafin yayi wani abu abin ya tarwatse. Ruwan zafi mai tsananin tururi yayi feshi ko'ina. Manyan tubali suka faɗo kan rundunarsu. Hankali ya tashi. Masu gudu nayi, masu kuka nayi, masu burgima a ƙasa domin su rage zafin ƙunar dake jikinsu nayi. Wasu kuwa tuni tubali ya danne su a ƙasa sun riga mu gidan gaskiya.
Kallo ya koma kan Maikiro'Abbas wanda yake tsaye yayi tamasi yana kallon abokan gaba cikin isa.
"Hari ɗaya ne fa?" Inji wani sadauki daga cikin mayaƙan Ururu. "Amma ya halaka mutane daruruwa."
Wani sadaukin dake gefensa ya gyaɗa kai cikin amincewa.
"Sai da kwamanda Yurba da mutanen ikwatora suka saka hannu amma duk da haka basu tare shi ba. Wai waye Maikiro'Abbas?"
Nan fa hankali ya dugunzuma. Mayaƙan Ururu suna ƙara kallon Maikiro'Abbas hankalinsu yana ƙara tashi. Ba tare da sani ba suka fara jada baya cikin tsoro.
Kamar Dul'Ururu ya kula ya daka musu tsawa. A wani salo na maida martani ya tashi sama akan iska. Doguwar sandar tsafi ta bayyana a hannunsa. Kamar wasa ya ɗaga sandar ya nuna sama. Nan take sai sandar ta fara tsayi tana dosar sararin sama. Tana tafiya tana haska hanya. Komai nisan mutun a faɗin duniya idan ya ɗaga kansa zai hango ta. Ba jimawa ta isa cikin gajimare. Abin mamaki sai kawai gajimaren ya fara darewa yana bata hanya. Taci gaba da tafiya tana shiga samaniya har sai da aka daina ganin komai sai duhu. A wannan lokaci masu kallo suka fuskanci cewa an fita daga filin wannan duniya an shiga ta taurari. A duniyar babu komai sai taurari ababen haske da buwaya. Suna tafiya a hankali suna haske gwargwadon hasken ruhin mai su. Yawansu bazai kirgu ba kamar yadda yawan bil'adama bazai kirgu ba. A hakan Dul'Ururu ya fara farauta. Sandar tsafin tana lalube tana rangaji tana rawa a tsakanin taurari. A wasu lokutan sai kaga ta kama tauraruwa ta fasa. A wasu lokutan kuma sai kaga ta hurawa tauraruwa haske tana sheki. Sannu a hankali yawan taurarin da sandar ta fasa suka fara yawa.
Dul'Ururu ko a jikinsa. Haka yaci gaba da aikinsa. Kowa yana gani amma babu mai iya tunkararsa. Shi ne bajimi uban mafarauta.
Bayan kimanin minti guda sai sadaukai daga cikin rundunar Maikiro'Abbas suka fara faduwa a ƙasa suna mutuwa. Babu ciwo, babu rauni, amma kawai sai kaga mutum ya zube a ƙasa ya mutu. Sannu a hankali mutane suka fuskanci cewa ruhinsu mafarauci yake kashewa a duk sanda ya fasa tauraruwa. Dole suna buƙatar su taka masa burki domin idan ba haka ba zai iya ƙarar dasu baki ɗaya.
Maikiro'Abbas ya daki iska da bayan hannunsa. A lokacin Armad ya fuskanci a duk sanda sarkin zai daki iska yana yin zane da ƴan'yatsun hannun da yake amfani dashi a wani salo mai kama da rubutu.
Kada dai ace zanen da Maikiro'Abbas yake yi da yan'yatsunsa rubutu yake yi. Ance shi ne marubucin farko. Ba abin mamaki bane dan yayi rubutu akan iska da yan-yatsu. To amma mai yake rubutawa?
Armad ya tuno abinda Maikiro'Abbas ya rubuta a lokaci na farko, wanda kuma ya bambanta da abinda ya rubuta a yanzu da zai ƙara kai hari. Shin hakan yana nufin kowane hari akwai rubutunsa?
Kafin ya rufe baki wata ƙatuwar kawanyar ƙanƙara ta bayyana a kan iska, dai-dai inda Maikiro'Abbas ya daka. Ganga-ganga tayi kan abokan gaba zata cinye su.
Dul'Ururu na ganin haka ya jada baya ya janyo sandarsa daga sama. Hakan yasa duk wata tauraruwa daya fasa ta fara faɗowa ƙasa. Sama tayi duhu. A hankali duhun ya fara komawa ja. Kada a manta taurari manyan duwatsu ne masu ci da wuta wadda bata mutuwa. Lallai idan suka faɗo kan mutanen Maikiro'Abbas to yaki ya ƙare. Domin kuwa aƙalla akwai taurari sama da ɗari, wato adadin mutanen da suka mutu, wanda zasu iya murkushe su baki ɗaya.
Sarki Maikiro'Abbas ya fuskanci haka. Da sauri ya ƙara dukan iska a jere har sau bakwai. Manya-manyan guma-guman ƙanƙara suka fice daga hannunsa sukai kan abokan gaba. Kowacce ƙanƙara cike take da ruwan zafi tana jira ta fashe.
Hakan yasa sadaukan kowane ɓangare tsorata. Waɗannan suna ganin taurari na zuba daga sama, waɗannan kuma suna ganin ruwan zafi da ƙanƙara.
A lokaci na farko Armad ya shigo filin daga. Ba tare da jiran umarni ba ya tashi sama ya kira ɗalasimi.
"Gidan gizo-gizo!"
Nan take saka ta bayyana akan iska. Fararen zarurruka ababen haske suka cika sama. Kafin taurarin su ƙaraso zaren yayi musu rumfa. Sannan jan Negrinki ta hau kansa ta rufe.
A ɗaya ɓangaren daga cikin kwamandun Ururu biyar ɗaya ne ya tashi. Kada a manta idan ka ɗauke Yurba da Dul'Ururu, dukkanin ragowar ukun samudawa ne. An bayyana mana cewa karfinsu yakai suyi jayayya da sauran kwamandu kamar Yurba da Uznu Ururu, amma kuma a lokaci guda salsan Dul'Ururu ne. Ɗaya acikinsu yana amfani da al'amudi duk da bamu taɓa ganin yadda yake amfani dashi ba sai dai kawai yana rataye dashi, biyu kuma babu makami a hannunsu. A wannan lokaci ɗaya daga cikin marasa makamin ne ya miƙe. Yana da sanko da ɗan gajeren gemu fari. Ana kiransa da kwamanda Binani. Yana miƙewa suka haɗa ido dana kusa dashi mai ƙunshi a gemu wanda ake kira da kwamanda Ki'jini suka gyaɗa kai.
A lokacin jikinsa ya fara haske. Farin sulke ya bayyana a jikinsa. Ya miƙa hannu gaba inda nan take sulken ya fara narkewa yana bin hannunsa. Kafin kace kwabo dunkulen farin karfe ya taru a hannunsa. Hakan bai ragewa sulken dake jikinsa yawa ba. A wani salo mai ban al'ajabi sai farin ƙarfen ya fara miƙewa yana fita daga hannunsa har sai da yakai gaban rundunar Ururu sannan ya buɗe ya fara samarda katanga. Kafin harin Maikiro'Abbas ya ƙaraso tuni wata mashahuriyar katanga ta bayyana ta rufe rundunar Ururu a wani salo na bada kariya.
Ƙawanya ta farko data daki katangar sai da ƙasa tayi girgiza. Katangar duk da karfe ce sai da ta tsage. Wato ba iyakacin sanyi da zafi harin Maikiro'Abbas yake dasu ba, akwai ƙarfin dantse da gudu da kuma kwari.
Kwamanda Binani ya haɗa ɗan'yatsansa babba da yatsa na biyu guri guda. Nan da nan yawan ƙarfen dake fita daga hannunsa ya ƙaru. Tsagewar da katangar tayi ta rufe. Katangar ta fara ƙara kauri. Duk wata ƙawanya data iso sai dai kaga ta doki katangar ta zube. Idan ta fashe ruwan zafin ya zuba akan katangar sai kaga hayaki yana tashi. Amma dai duk da haka babu alamun katangar zata fadi. A haka harin Maikiro'Abbas ya ƙare bai taɓa rundunar Ururu ba.
Idan muka dawo ɓangaren Maikiro'Abbas kuwa zamu ga daruruwan taurari suna zuba akan rumfar da Armad ya haɗa ta zare. A zahiri babu wata rumfa komai kwarin ta da zata iya tare tauraruwa, amma Armad yana da Negrinki, kuma bai damu da abinda zai faru ba dan ya zuba taurari cikin Negrinkinsa. Yadda jan Negrinkin ta shafe zaren haka kowace tauraruwa take ɓacewa da zarar ta taɓa zaren. A haka sai da Armad ya shanye dukkan taurarin cikin duniyar Negrinkinsa. Yana sane da ajiyarsa aciki. Yana kuma sane da ƴan-ruwan daya jefa. Amma yanzu ba lokacin jimami bane.
A haka Armad ya tare harin Dul'Ururu akan rundunar Maikiro'Abbas. Shima kwamanda Binan haka ya tare harin Maikiro'Abbas. Bayan Binan ya cire katangar ƙarfen da yayi amfani da ita sai shima Armad ya cire gidan gizo-gizon dake samansu. Kowane ɓangare ya tsaya yana kallon ɗayan a wani salo na auni. Ko babu komai sun fahimci cewa hari daga nesa bazai bawa kowa nasara ba.
"Dul'Ururu," inji Maikiro'Abbas da babbar murya. "Kana tunani zaka fake da siyasa ka halaka ahlin gida na? Ko ka bani Fatima, ko kuma na kwata da ƙarfin tsiya."
Dul'Ururu ya dunkule hannu tsahon dakiku suna kallon-kallo.
"To shikenan," inji Dul'Ururu. "Tunda abinda ka zaɓa kenan, kada kayi kuka da kowa duk abinda ya same ka. Daga yau na sauke ka daga muƙamin ka na sarkin jinzidal" Ya juya ɓarin rundunarsa. "Ni sarki Dul'Ururu na baku umarni ku kama duk wanda yayi ƙoƙarin karɓar Fatima. Sannan ku kashe duk wanda yayi tawaye kamar yadda doka ta tanada."
Watakila saboda duniya tana kallon wannan yaƙi ta hanyar kwallon ayrid da faifan bidiyo shi yasa Ururu suke so a gane sune masu gaskiya. Ko kuma dai kawai ki-fadi ne na ururu basa so a ga kamar yaƙin neman waje suke. Koma dai meye dalili a yanzu babu ja baya. An fito fili kuma dole a fafata.
Armad wanda yake tsaye a bayan Maikiro'Abbas tare da su Nusi ya taka wajen da sarki Abbas yake ya tsaya.
Kafin Armad yayi magana sarkin ya riga shi.
"Ka shirya mutuwa saboda ita?"
Armad ya kalli sarkin cikin mamakin tambayar. Bayan ɗan lokaci yaja numfashi sannan ya wuce gaba ya tsaya.
"Bana nufin izgili ko raini, amma Ni ita ta haifeni, kai kuma riƙe ta kayi. A iyakacin sani na alaƙar ka da ita dai-dai take da alaƙar ɗa da ubangidansa."
Maikiro'Abbas ya kalli Zaikid ta gefen ido. Ko babu komai ya fuskanci cewa Zaikid ya bayyanawa Armad abinda yake faruwa.
"Kai ka shirya mutuwa saboda ita?" Armad ya tambaye shi.
Maikiro'Abbas yayi murmushi tare da jan dogon numfashi. A idanunsa Armad jikansa ne saboda haka duk wata magana ɗaya faɗa gani yake kamar bai kai ba.
Maimakon Maikiro'Abbas ya bashi amsa sai ya ƙara yi masa wata tambayar. "Meye hasashen samun nasarar mu a wannan yaƙi?"
Armad ya fuskanci sarkin yana ƙoƙarin gwada kaifin basirarsa ne da kuma iya lissafinsa na yaƙi. Watakila hakan shi ne zai saka ya bashi ragamar yaƙin a matsayin babban kwamanda. Ko babu komai Maikiro'Abbas bai shirya ganin Armad a wajen ba saboda haka yazo da shirinsa. A yanzu Armad yana buƙata ya nuna kansa kafin Maikiro'Abbas ya shigo dashi cikin lissafi ya kuma bashi matsayi. Armad yasan hakan yana da muhimmanci domin kuwa idan zasu yi nasara to suna buƙatar haɗin kai.
"Sunfi mu yawa, sunfi mu mutane masu ƙarfin izza, kuma suna da abun da muke nema. Ta kowane ɓangare sun wuce mu musamman idan muka yi duba da cewa gidansu muka zo. Babu shakka sun shiryi zuwan mu. Babu wanda yasan sharrin da suka shirya. Hanya guda da nake hango nasara shi ne..."
Armad ya ɗanyi shiru yana tunani. Ganin haka ya saka Maikiro'Abbas yayi murmushi.
"Da kyau," inji Maikiro'Abbas. "Kada ka faɗi shirin mu iska ta ɗiba ta kai musu."
Armad ya gyaɗa kai. Tabbas ya fahimci abinda sarkin yake nufi. Yaƙi ɗan zamba ne. A sau da dama nasarar ka bata da alaƙa da ƙarfin ka.
"Mun kama Haruta," inji Armad. "Yana cikin wani shinge dana haɗa da Negrinki. Kamar duniya wajen yake amma kuma..."
Maikiro'Abbas ya katse shi ta hanyar ɗaga masa hannu.
"Nasan duniyar Negrinki, Armad. Ina ganin Fatima da Hidaya suna da irinta. Amma tayaya kuka kama Haruta..."
Sarkin ya ɗanyi shiru tare da juyowa ya kalli Zaikid da Shata. Bayan ɗan lokaci ya gyaɗa kai alamun ya fuskanci abinda ke faruwa.
"Baku da hanyar ajiye shi a waje ku hana shi guduwa, ko?"
Armad ya gyaɗa kai. Sarkin yayi ajiyar zuciya.
"Idan baza mu iya fitowa dashi ba kowa ya gani kaga baza mu iyayin barazana dashi ba kenan. Amma Dul'Ururu da Maruta dole sun sani tunda su suka turo shi. Abin tambayar anan shi ne: meye matsayinsa a gurinsu?"
Armad ya jinjina tambayar. Shin kama Haruta zai hana Dul'Ururu kashe Fatima? Shin yin barazana da rayuwar Haruta zai saka Dul'Ururu ya canja ra'ayi? Idan bazai canjawa Dul'Ururu ra'ayi ba to wace hanya ce mafi dacewa da zasu yi amfani da Haruta? Musamman duba ga cewa baza su iya fito dashi su durkusar dashi a gaban idon duniya ba. Watakila da zasu iya yin hakan da sun karya gwiwar mayaƙan Ururu.
"Yanzu ka bar zancen a zuciya," inji Maikiro'Abbas. "Idan ban da Zaikid da Shata ai babu wanda yasan yana gurin ka, ko?"
Armad ya gyaɗa kai.
"To ka barshi a haka. Ana cikin yaƙi zaka samu damar da zaka yi amfani dashi."
Armad ya ƙara jinjina maganar. Tabbas akwai hangen nesa aciki. Maimakon su faɗawa kowa sun kama Haruta sannan idan aka nemi su nuna shi su kasa, gwanda su ajiye shi a matsayin shirin ɓoye. Shi kansa Dul'Ururu a yanzu bai san inda Haruta yake ba. Zasu barshi cikin kokwanto. Amma watakila da zai san inda yake ya kafawa Armad ƙahon-zuƙa ya kwace shi. Amma yanzu basu da masaniya ko Haruta yana raye ko ya mutu, sannan kuma idan yana da rai basu san a ina yake ba. Fatan dai kawai ya zama Haruta bashi da dama wata hanya da zai yi musu magana ta cikin duniyar Armad. Koda yake babu tabbas amma da zaiyi da tuni yayi.
"Zan shiga gaba," inji Armad.
Maikiro'Abbas ya gyaɗa kai.
A dai-dai lokacin da Armad yake ƙoƙarin kai hari, a nasu ɓangaren kwamandun Ururu lissafi suke yi. Kwamanda Kijin ya dubi sarki Dul'Ururu.
"Mai zai hana mu kashe shugabansu shikenan kowa ya huta?" Inji Ki'jinu. "Na tabbatar zasu karaya su gudu idan hakan ta faru. Maimakon muyi fito-na-fito dasu wanda zai jawo asarar rayuka ai gwanda kurum mu sare kan micijin. Jelar baza tayi wahala ba."
Ki'jinu ya miƙe tsaye. Sauran kwamandun suka bishi da kallo babu wanda yace uffan. Shima Dul'Ururu shiru yayi yana kallo.
Kwatsam Armad yaga mutun a gabansu.
"Maikiro'Abbas," inji Ki'jinu. "Idan na kashe ka shikenan kowa ya huta."
Bayyanar kwamandan yaja hankali. Ƙananun mayaƙa daga ƙasa suka fara kiran sunansa.
"Ki'jinu ne. Ki'jinu ne!!"
Jerin kibbau sama da goma suka tunkaro shi ta ƙasa. Kwamandan ya saka hannu akan gemunsa mai ƙunshi ya fizgo silin gashi guda ya jefi kibban. Gashin yayi fitar burtu kamar an jefa kibiya. Yana tafiya yana ƙara girma. Kafin ya isa ya zama ƴar ƙaramar kibiya. Suna haɗuwa da kibiyoyin ya fashe ya koma haske. Hasken ya dunkule ya samar da wata katanga ta haske wadda ta shiga tsakanin kwamandan da kibiyun a wani yanayi me kama da na kariya.
Kowacce kibiya idan tazo wajen hasken sai kaga ta shige zuruf ta tunkari kwamandan ba tare da wata tangarda ba. Abin mamaki hasken ko kaɗan bai iya tare su.
Shi kuwa a nasa ɓangaren kwamanda Ki'jinu juyowa yayi kan Maikiro'Abbas kamar bai san kibiyoyin suna tunkaro shi ta ƙasa ba. Yana kallon sarkin yan murmushi.
A hakan kibban suka same shi. Ta farko ta shige kirjinsa ta sama sannan ragowar suka tsire shi ta sassa daban-daban na jikinsa. Suka fasa ƙashi suka fice ta baya.
Armad ya haɗe gira. Babu ko ɗigon jini a jikin kibban sannan kuma babu ciwo a jikin Ki'jinu. Kamar kawai kibiyoyin wucewa sukai ta jikinsa amma basu taɓa shi ba. Kamar yadda Armad yake buɗe taga izuwa duniyar Negrinki. To amma idan Armad ne kibiyoyin ɓacewa zasu yi, saɓanin kwamanda Ki'jinu wanda kibiyoyin suka ɓulle ta bayansa. To ɗayan biyu: kodai jikinsa ya koma haske ko kuma kibiyar.
Kwamanda Ki'jinu ya fara fizgo gashin gemunsa yana jifan Maikiro'Abbas. Kowane silin gashi sai kaga ya kumbura yana haske.
Harin yana gabda samun Maikiro'Abbas wani sadauki ya shiga tsakani. Idan mu kayi duban tsanaki zamu fuskanci ba wani bane illa yarima Abba - kanin yarima Umaru, kuma ƙarami acikin ya'yan Maikiro'Abbas.
Yarima ya daki iska da tafin hannunsa na dama. A lokaci guda kuma yayi rubutu da yan'yatsunsa na hagu. Sai dai rubutun kana gani kasan bai kai na Maikiro'Abbas ba. Tun daga saurin har zuwa yawansa. Kuma abin mamaki Armad baiji fitar izza daga jikin yariman ba. Lamarin da yasa Armad ya fuskanci lallai akwai wata sabuwar hanyar sarrafa fasaha da al'ummar Maikironomada suke amfani da ita. Watakila maimakon amfani da aljanu da izza suna amfani da littafin marubutan farko ne.
Armad bashi da lokacin tsayawa yayi tunani akan abin yanzu domin kuwa yarima Abba yana gama rubutu ruwaya fara ambaliya daga hannunsa na dama. Harin Ki'jinu ya daki ruwan.
Sai dai kuma kash, ruwan bai iya tare harin ba, yadda Ki'jinu ya harbo su haka suka fice suka tunkari fuskar yarima Abba suna ƙoƙarin halaka shi. Ruwan ya ƙara ambaliya ya tare su amma a banza. Idan ka lura wannan ruwa ba kowanne irin ruwa bane. Yana da danko kamar zuma sannan kuma yana da sihiri domin kuwa ko zuba ƙasa baya yi. Akwai hannaye acikinsa da igiyoyin ruwa wanda suke ƙoƙarin tare harin. Sai dai kuma a banza, duk sanda gashin gemun Ki'jinu ya taɓa igiyar ruwa sai kaga ya fashe ya zama haske. Duk abinda hasken ya taɓa ya gama dashi. Koda wani gashin yazo wucewa sai dai kaga ya wuce ba tare da tangarda ba. Tabbas sirrin fasahar Ki'jinu yana cikin gashin gemunsa da yayi wa ƙunshi. Duk abinda gashin (ko kuma haskensa) ya taɓa sai kaga ya ɓace. Gashi kana ganin abin da ido amma kuma haske ne kawai baza ka iya taɓa shi ba. Kamar irin yadda kibiyoyin can da aka harbi kwamandan dasu suka zama haske suka shige ta jikinsa. Tambayar anan ita ce: shin duk abinda gashin gemun kwamandan ya taɓa haka zai kasance, koda jikin mutum ne?
Armad yaci gaba da kallon faɗan daga nesa. Yarima Abba ya ƙara yin rubutu akan iska lamarinda yasa ruwan dake fita daga hannunsa ya fara ƙugi yana kaɗawa. Kan kace kwabo ya rufe gaba ɗayan hasken da gashin a guri guda. Yarima Abba ya tashi sama inda ruwan (ɗauke da gashin) ya bishi sukai sama.
Kwamanda Ki'jinu ya kaɗa kafaɗa. Ya ɗora hannu kan gemunsa ya fara zarar wasu yana jefawa. Dole yarima Abba ya rabu da igiyar ruwan taci gaba da yin sama ya dawo domin ya tare harin. Kamar Ki'jinu yaga abinda zai faru sai ya bayyana a gabansa da silin gashi guda a hannunsa ya dannashi a ƙirjinsa. Gashin ya fashe, haske ya rufe yarima Abba. Shi kuwa Ki'jinu gaba ya wuce ya nufi inda Maikiro'Abbas yake.
A fusace yarima Abba ya kawo masa wafta da hannu. Hannunsa ya daki ƙirjin kwamandan ya shige ciki. Maimakon aji ƙara ko a ga jini sai kawai hannun ya ratsa ta ciki ya wuce ba tare da ya taɓa Ki'jinu ba.
Kai tsaye Ki'jinu ya afka kan Maikiro'Abbas. Kafin ya ƙarasa bangon ƙanƙara ya tare shi. A bayan bangon yarima Umaru ne.
Ki'jinu ya zari gashin gemunsa ya cilla. Koda suka haɗu da ƙanƙarar sai ya fashe ya zama haske. Yarima Umaru ya samarda da yar bukka ta ƙanƙara ya rufe hasken.
Ki'jinu ya ƙara harbo wani gashin. Shi kuwa yarima ya tare da ƙanƙarar sannan ya saka wani rumbun ya rufe hasken.
Ki'jinu ya zari gashi goma a lokaci guda ya harba masa. Cikin kwarewa da tsananin zafin nama yarima Umaru ya samarda bukka har guda goma ya tare gashin ya kuma rufe hasken. Dole aka tsaya ana kallon kallo tsakaninsa da kwamandan.
"Hmm.." yarima Umaru yayi dariya. "Ba dai sai hasien ya fita kake da sharri ba? Muje zuwa."
"Amma ina da hanyoyi da yawa na kama bera," inji Ki'jinu. Nan take ya zaro gashi da yawa daga gemunsa ya murmushesu a hannu. Haske ya zagaye shi. Ya ƙara zaro wasu ya murmushe inda hasken ya ƙaru. Ya ɗaga hannu sama tsahon dakiku sannan a hankali ya fara haɗe hannayen guri guda. Kamar hasken yana biyayya ga ikonsa sai ya ringa bin hannayen yana taruwa a tsakiya.
Comments
Post a Comment