Babi na 219-222
***
Sannu a hankali siffar Sarkin-sarki ta bayyana. A ƙafafunta akwai jan takalmi na fata wanda ya rufe har izuwa idan sahu. A karo na fari ta bayyana da wani tufafi bana haske ba. Abin mamaki wannan tufafi anyi shi ne da dusar ƙanƙara mai launin toka. Anyi amfani da fasaha ɓoyayyiya an hana ƙanƙarar narkewa. Idan ka nutsu sosai ka ƙurawa ƙanƙarar ido zaka fuskanci cewa ƙanƙarar [Sanyin-babban-sihiri] ce.
Akwai mamaki yadda akai amfani da ƙanƙara aka samarda doguwar riga har ƙasa, sannan aka samarda kambu na mulki da awarwaron duk na ƙanƙara. Sarki-sarki na da kamala matuƙa da gaske, wataƙila shi yasa da dama suke ganin kyawunta ya haura na sauran matan duniya baki ɗaya idan aka haɗe su a waje ɗaya. Bata ɗauke da makami ko ɗaya amma kuma duk wanda ya kalle ta sai gabansa ya faɗi.
Mataimakin shugaban makarantar Bábila tsoho ne tukuf mai yawan gashin-gira fari. Yana da doguwar haɓa wadda takai kamu huɗu amma babu gemu kwata-kwata a jikinta. Kansa akwai ƴar ƙaramar hula wadda saman kan kawai ta rufe. Yana bayyana dukkan ɗaliban dake iface-iface suka nutsu suka jada baya.
Wannan mutun ya matso gaba a nutse ya fuskanci sarkin-sarki ya ce, "suna na farfesa Ƙyarunu, nine mataimakin shugaban wannan makaranta. Muna farin ciki da wannan ziyara da kika kawo mana kuma da fatan zamu biya miki buƙatunki."
Sarkin-sarki ta kalleshi a hasale amma bata ce komai ba. Bayan yan daƙiƙu ta ɗaga kai ta dubi sauran mutun goma sha dake kewaye dashi wanda duk manyan malamai ne a makarantar. Ta ɗaga ɗan'yatsanta ta nuna mutun na uku daga daman farfesa Ƙyarunu ta ce, "farfesa Kjal, kaine mafi girman izza a wannan makaranta idan aka ɗauke shaihu Babila. Kafi kowa sanin koda zaku haɗu ku kawomin hari a tare a lokaci guda baza kuyi nasara a kaina ba. Bani da matsala da makarantar Babila, hasalima akwai ɗalibanmu da dama aciki saboda haka ina fatan baza ku shiga gaba na ba. Al'amarin tsakani na da Armad Wilbafos ne."
Nan take farfesa Ƙyarunu yai gyaran murya gami da cewa, "maganarki gaskiya ce, mafi yawan Ayrid da muke amfani dashi a wannan makaranta ku kuke kawo mana shi. Bayan Ayrid kun taimakemu da yaƙutun izza da sauran ababen koyon izza da dama. Shugaban wannan makaranta shaihu Babila ya ce a miƙo godiyarsa bazai samu ya iso ba saboda yana tsaka da halwar izza. Ba daban kinzo ana tsaka da wannan gasa ba da ni da kaina zan jagoranci tawaga domin kamo miki wannan yaro Armad Wilbafos, to amma..."
Nan take sarkin-sarki ta katse shi, "wataƙila baka fahimce ni ba, bawai shawara nake nema ba, umarni na baka. Dakai da jama'arka ku matsa gefe."
Farfesa Ƙyarunu ya numfasa ya ce, "matsalar daga sama take, idan ta Babila ne bamu da matsala to amma babban sarki Kuyurussa'ayi nake ji. Wannan gasa shi ne ya ƙirƙiro ta, kuma shi ne ya sakko da ita wannan makaranta. Idan kikai katsalandan ina jiye miki fushinsa. Na taɓa ji Haruta Ururu yana cewa sarki Kuyurussa'ayi zai iya sakkowa ƙasa akan wannan gasa. Idan zaki bi shawara ta ki bari a kammala wannan gasa. Ni da kaina zan dafa miki wajen hukunta wannan yaro."
"Ban yadda ba." Inji sarkin-sarki.
Dukkan wanda ke wajen saida yaji gabansa ya faɗi ganin cewa ana gaya mata kuyurussa'ayi amma taƙi.
Farfesa Ƙyarunu ya jada baya suka ɗan tattauna tsakaninsa da sauran malaman kafin daga bisani su bata hanya, "dani da mutane na baza mu shiga gabanki ba."
Sarki-sarki ta gyaɗa kai ta wuce gaba izuwa ƙofar-asali. Har ta kusa ƙarasawa farfesa Ƙyarunu ya bita ya ce, "kafin ki tafi ko zaki canja yanayin da wannan ɗalibai suka jefa kansu aciki?" Yai nuni izuwa ga ɗaliban da suka makance bayan kallon sarkin-sarki.
Sarkin-sarki tai tsaki ta wuce gaba, wannan tsakin da tayi shi ne ya dawo wa da ɗaliban ganinsu. Amma saboda halin da ake ciki kowa yayi tsit babu mai cewa uffan.
Tana isa ta tsaya a bakin ƙofar tayi tsawa, "[Jaura]!"
Nan take guguwa ta taso ta turnuƙe sama tayi kan ƙofar. Acikin guguwar akwai dusar ƙanƙarar sanyin babban sihiri. Koda guguwar ta haɗu da ƙofar sai ƙofar ta daskare, duk wani abu dake kan hanya shima ya ƙame. Ƙanƙarar tayi kama da ta sanyin babban sihiri amma kuma ƙarfinta yafi gaban hakan. Hatta iskar dake kaɗawa bata kyale ba. Kai har wanda ke nesa da ita, sauran ɗaliban Babila karkarwa suka fara yi.
Guguwa ta shige cikin ƙofar tai sama zuwa matakin da Armad yake.
A gefe guda farfesa Ƙarunu da sauran malaman Babila na tsaye suna kallo. Ɗaya daga cikin farfesoshin wanda ake kira da farfesa Ksalgis wanda ya kasance farfesa ne akan fannin Tsaro ya juya ga ɗaliban dake wajen ya fara yi musu bayani, "yau ga asalin fasahar sanyin-babban-sihiri da kuma ƙololuwar fasahar Tsaro. A ɓangarori huɗu na fagen daga wato Hari, Tsaro, Yanayin-izza da Sauri sarkin-sarki ita take da ƙololuwar Tsaro. Tayi tarayya da Ururu wajen mallakar ƙololuwar yanayin-izza. Asalin ƴan ƙabilar Elbis sune suka fara samarda fasahohin Tsaro, wato fasahohinda zakai amfani dasu wajen kare kanka koda baka da makami, suka kira wannan fasaha da [Tauri]. Masu amfani da ita ana kiransu da ƴan-tauri.
"Ƴan-tauri suna samarda wani sirri ne acikin jikinsu wanda yake hana makami da duk wata fasaha cinsu. Wani taurin yana bayyana kansa yasa fatar mutun ta canja kala zuwa wani launi kamar baƙi, ja ko ruwan-ƙasa. Sarkin-sarki ita ce ta farko data ɗaukaka fasahar [Tauri] ta kaita mataki na gaba, matakin da ɗan tauri zai iya amfani da fasahar sa ta tauri ya kawo maka hari! Ta gano cewa duka da hannun da yasha tauri yafi illa akan duka da hannun da bai sha ba. Hakan ke nuna cewa tauri yaka ƙara ƙarfin hari.
"Daga nan ta shiga bincike har sai da ta samarda fasahar [Kan-kada] wadda zaka iya haɗe taurinka a waje ɗaya ka kai hari. Hakan zai ninninka ƙarfin harinka sau da yawa. Bayan tsahon lokaci aka ƙarawa fasahar ƙarfi ta koma [Kan-gwanki]. Amma asalin sirrin shi ne yin amfani da Tauri wajen aika hari daga jikinka zuwa wani wajen ba tare da ka taɓa wajen ba.
"Daɗin-daɗawa Sarkin ita ce ta ƙirƙiro fasahar sanyin-babban-sihiri a duniya. Ita kaɗai tasan asalin sirrin fasahar da kuma dalilinta. Muda mukai yarinta a doron ƙasa na biyu iyayenmu sunai mana takara da mu gudu indai mukai arba da sarkin-sarki a filin yaƙi. A yanzu nima zanyi muku wannan takara. Da sarkin-sarki da Bihanzin idan kuka haɗu dasu a fagen daga ku gudu. Bihanzin yana da ƙololuwar fasahar Hari wato Dauwamammen sara ita kuma sarkin-sarki tana da ƙololuwar fasahar Tsaro wato [Kan-iska]. Akwai mai tambaya?"
Yana rufe baki wani ɗalibi mai hazaƙa yai tsalle ya ce, "kace ƴan ƙabilar sarkin-sarki wato Elbis sunyi tarayya da Ururu wajen mallakar ƙololuwar fasahar Yanayin-izza, munsan Elbis suna amfani da fasahar [Mutan-ɓoye] ta Yanayin-izza wajen ɓacewa da hana ido ko ruhi ganinsu. Kuma malaman Kalkeci sun bayyana cewa babu wata fasaha data kai wannan a fannin Yanayin-izza. Tambayar anan ita ce wacce fasaha Ururu suke da ita a ɓangaren Yanayin-izza wadda takai fasahar [Mutan-ɓoye]?"
Farfesa Ksalgis ya ɗan yamutsa rai domin baiji daɗin yadda ɗalibin yayi magana ba tare da an bashi dama ba. Amma saboda yasan ɗalibin kuma yasan hazaƙarsa sai ya share. "Fasahar [Saɓani] wadda suke amfani da ita wajen ganin abinda zai faru daga Yanayin-izza suka samar da ita. A ƙarni na uku babban sarki Kuyurussa'ayi ya samar da ita."
Ɗaliban suka nutsu suna saurare.
Farfesan yaci gaba da cewa, "abinda baku gane ba shi ne duk wata fasaha tana ƙarƙashin wannan tsaruka huɗu wato Tsaro, Hari, Sauri da Yanayin-izza. A aji na gaba zamu tattauna akan dordor da aljanu da fasahohinsu."
A dai-dai lokacinda farfesa yake lakca akan Tsaro acikin ƙofar-asali Armad na zaune zaman dirshen akan ruwan cikin Hasanu yana lodarsa ta ko'ina. Fuskar Hasanu tayi luhu-luhu sai kayi da gaske zaka gane shi.
Armad ya ɗaga hannu sama ya daki kumatunsa inda jini yayi feshi sama. A halin da ake ciki Hasanu baya iya kwakkwaran motsi. Armad ya zaro takobinsa da niyyar ƙarasa aikinsa amma anan yaji tsigar jikinsa ta tashi. Yaji wani irin abu ya riƙe masa hannu. Ya waiwayo baiga kowa ba amma kuma yana jin hannunsa a riƙe. Yayi amfani da [Yanayin-izza] amma duk da haka baiga komai ba.
Kafin ya ankare kawai sai ji yayi hannunsa yayi ƙankara, kafin yayi wani abu ƙanƙarar tabi jikinsa. Hasanu ya buɗe ido da kyar ya ga ƙanƙarar data ɗaure Armad. A karo na farko murnushi ya dira a fuskarsa.
Daga inda take tsaye sarkin-sarki ta nuna cikin ƙofar-asali da ɗan'yatsanta ta kira fasaha, "[Kan-iska]!"
Wani haske ya tashi daga tsinin ɗan'yatsanta ya daki ƙofar inda ta tarwatse ya shige ciki yai kan Armad.
Armad yai sauri ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya ya narka ƙanƙarar sannan yai tsalle gefe ya kauce.
Ya kauce ya dira a gefe shi kuma harin sarkin-sarki ya dira akan Hasanu. Amma bisa mamaki kawai sai dukkan ciwukan jikin Hasanu suka ɓace ɓat. Izzarsa ta dawo dai-dai, dukkan lahanin da Armad yai masa ya ɓace, wani sabon ƙarfi ya bayyana a jikinsa kai kace ba'a taɓa yi masa rauni ba. A lokaci guda kuma Armad wanda ya kamata ace ya kaucewa harin sai kawai yaga hannunsa na dama ya fara kumbura, jijiyoyi sun fito burɗun-burɗun.
Ga jikin izza ga jikin walƙiya amma duk da haka tsananin zafi ne yake shigarsa kamar ana soya hannun a tafasasshen mai. Bashi da masaniya akan abinda yake faruwa ko kaɗan.
Abu kamar wasa hannu ya suntume ya rinƙa ƙara girma kamar ana hura masa iska. Abu na farko daya fara ɓacewa daga jikin hannun shi ne izzarsa, sannan jini ya ɗauke, sannan jijiyoyin hannun suka tsintsinke. Armad ya buɗe baki zaiyi ƙara amma koda ya tuna cewa duk duniya tana kallonsa sai kawai ya rufe bakinsa ya ciji harshensa har saida yayi jini.
Babban ɗan yatsansa wanda a yanzu yafi girman kansa shi ne ya fara fashewa yai feshin jini ko'ina. Duk da jijiyoyin hannun sun tsinke amma hakan bai rage zafin da Armad yake ji ba. Bai san mai yake faruwa ba amma yasan wani ne yake taimakawa Hasanu daga waje. Koma waye yasan izzarsa ta haura Jemai kuma tafi ta duk wani mutun dake cikin gasar. Hasalima Armad yana ji a jikinsa tamkar wannan izza ta girmi Deba. Wannan izza bata da zaren izza, idan ya kalleta baya ganin komai sai taurari maɗaukaka wanda basu da adadi. A tsakiyar taurarin akwai wani haske wanda yake ambaliya da ƙarfin iko da isa. Koda Armad ya ƙurawa hasken ido sai yaji idanunsa sun fara zubarda jini kamar hawaye.
Hasanu ya tashi zaune ya dubi Armad ya ce, "na gaya maka kada ka bari mahaifiyata ta zo, babu ruwanta da ƙa'ida ko doka domin ita take yin dokar. Tana kan matakin izzar da babu wanda yasan sunansa, matakin izza na gaban Deba, matakin sarakunan farko. Saboda ta nunawa duniya muhimmanci na shi yasa tazo da kanta amma ina mai tabbatar maka tana daga fadar ta duk abinda ta furta saiya faru.
"Nasan kana mamakin yadda akai harin da aka kawo maka ya warkar dani sannan kuma duk da ka kauce ya cutar dakai, bari nayi maka bayani. Shi ne abinda ake kira da [Kamalar-ruhi], a duk faɗin duniya wanda suke da wannan fasaha basu fi mutun biyar ba. Saboda ƙarfin ruhi da cikar izza idan suka ayyana abu a ransu hatta ƙaddara bata iya canjawa. Harin da aka kawo maka ya same ni to amma niyyar da aka aiko harin da ita shi ne kai saboda haka koda harin bai same kaba a zahiri kamar ya same kane. Ni kuma daya same ni sai ya juye ya koma magani saboda haka aka ayyana. Kamalar-ruhi kenan."
Hasanu ya tako a hankali a hankali ya tsaya a gaban Armad ya ce, "kaga yanzu reshe ya juye, a yanzu zan rama abinda ka ai katamin."
Hasanu ya kawo duka da hannunsa da niyyar kutufar Armad amma Armad ya sa hannunsa kumburarren ya tare. Sannan kafin Hasanu ya ankare yayi amfani da Kaban'shisu ya sa takobi ya tsinke hannun.
"Koda an shigar maka wannan bazai hana ni kashe ka ba..."
Ganin abinda ke faruwa ran sarkin-sarki yai matuƙar ɓaci. Tai tsawa, "KAI MARA KUNYA!" Iskar data fita daga bakinta ta haɗu da niyyar dake zuciyarta ta tarwatsa hannun Armad tun daga kafaɗa har ƙasa.
Maimakon yai ihu Armad ya ciji leɓensa har saida ya rabe gida biyu bai sani ba. Ƙarfin izzar sarkin-sarki ya tsare shi a waje ɗaya tayadda ko motsi baya iyawa sannan kuma ya kasa mayarda kansa walƙiya. Wannan ne karo na farko daya gamu da irin wannan izza mai nauyi wadda ta hanashi numfashi.
Sarkin-sarki ta ɗaga ƙafa zata shiga cikin gasar amma a lokacin ne wani ƙarfin iko wanda ya haura nata ya taso daga doron ƙasa ta farko ya dira a gabanta. Ƙarfin ikon ya juye izuwa idanuwan Ururu guda uku; ɗaya a sama biyu a jere a ƙasa. Guda biyun na ƙasa suna da ɗigon haske guda biyu a tsakiya sannan kuma tsarinsu a kewaye yake kamar bal. Na saman baƙi-ƙirin ne kuma babu komai aciki sai baƙi. Wannan idanu na bayyana dukkan mutanen dake wajen suka zube a ƙas cikin biyayya ba tare da sun sani ba. Sarkin-sarki ita kaɗai ta rage a tsaye amma ita ma ta ja da baya a firgice. Ta zare takobi ta riƙe ta da hannu biyu cikin shiri. A fuskarta akwai wasu-wasi da kokwanto.
Babu wanda yasan mai yake faruwa amma wannan idanu na bayyana shi kansa shugaban makarantar shaihu Babila sai da ya fito daga halwa ya bayyana akan iska. Fuskarsa a rufe take da baƙin kyalle amma duk da haka ana iya hangen idanunsa da zanen takobin dake ciki. Ga dukkan alamu shima shugaban wannan makaranta izzarsa takai domin yana tsaye a nutse yana kallon abinda ke faruwa.
Sarkin-sarki tai kukan kura ta kaiwa idanun sara. Takobin tana dira ta daddare ta tarwatse, wata iska ta ɗebe ta tayi jifa da ita. Tana dirowa ƙasa jini ya fara zuba daga idanunta da bakinta da hancinta. Nan take tufafinta na ƙanƙara suka narke. Ta miƙe tsaye ta fara kiran ɗalasimai manya irin wanda duniya ta daɗe bata ji ba.
Nan take surarta ta rabe gida bakwai, kowacce sura ta zare takobi suka kewaye idanun. Surorin guda bakwai suka tafa hannayensu a wata irin siffa mai ban al'ajabi. Sannan a tare suka ce, "Mutu! Mutu!! Mutu!!!"
Kalmar bakinsu ta haɗu da niyyar zuƙatansu ta hanyar fasahar [Kamalar-ruhi] ta juye izuwa mutuwa ta dira akan idanun guda uku. Sannan sarkin-sarkin ta juyarda ruhinta izuwa sanyin-babban-sihiri ta dira akan idanun.
Gab da afkawa idanun wata murya ta sauka daga sama, "Duk wanda ya kawo naƙasu a gasar nan a wannan rana ya mutu!"
Acikin muryar akwai daɗewa da shekaru irin wanda baza su lissafu ba. Akwai ƙarfin iko irin wanda bazai misaltu ba kawai sai wanda ya gani. Amma mafi muhimmanci shi ne tsantsar fasahar [Kamalar-ruhi] dake cikin wannan murya. Zaka rantse wannan murya idan tace duniya ta tarwatse tarwatsewa zatai a take. Duk wannan ƙarfi an tattareshi waje ɗaya akan sarkin-sarki da niyyar tarwatsa ta.
Muryar na gama magana sai kawai sarkin-sarki ta tsaya cak a inda take. Alamun mutuwa suka fara bayyana a jikinta, gashin kanta yai fari fat, fatar jikinta ta yamutse ta tsofe. Dukkan hare-haren ta da surorinta guda bakwai suka fara ɓacewa.
Ta haɗe waje ɗaya ta fara kira fasahar [Kan-iska] domin kare kanta. Idan mai karatu bai manta ba wannan fasaha ita ce ƙololuwa a fannin Tsaro. Kuma sarkin-sarki ita ce ta ƙirƙiro ta. Amma hakan bai sa ta daina tsofewa ba. Jikinta da ruhinta ya kama da wuta, gashin kanta yana hayaƙi.
Ana cikin haka TASU'A suka bayyana suka tsaya a bayan idanuwan nan guda uku. Haruta da Maruta Ururu da manyan kwamandojin Mayaƙan jinzidal guda huɗu suka bayyana kowanne cikin shirin yaƙi.
Sarkin-sarki ta ɗaga hannunta sama ta kira fasahar [Ikon-tauri] wadda a gaba take da fasahar [Kan-iska]. A sanin duniya babu wanda yasan wannan fasaha domin kuwa babu wanda yake tunani akwai abinda yafi fasahar [Kan-iska] a fannin Tsaro.
Wasu hatimai na asalin tauri suka bayyana a jikin sarkin-sarki suka kewaye ta. Wannan yasa tsufan da take ya ragu amma duk da haka bai tsaya ba.
Magana kawai akai aka ce ta mutu amma ta kasa kare kanta daga Kamalar-ruhin ma'aboci wannan magana. Lallai ko waye ma'aboci wannan magana ya cancanci yabo a fannin iko.
A dai-dai wannan lokaci zaka iya tunanin an gama da sarkin-sarki amma a lokacin ne kawai jikinta ya fara saɓa kamar miciji. A hankali duk fatar data tsufa ta zube a gefe, gashinta ya dawo dai-dai. Kayan haske suka bayyana a jikinta. Kai tsaye ta wuce cikin ƙofar-asali kamar bata ga Tasu'a ba. A lokacin wata muryar ta ƙara sauka daga sama, "Duk taku ɗaya da kika ɗauka zuwa ciki ki MUTU!"
A fusace sarkin-sarki ta ɗaga kanta sama ta ce, "kai Kuyurussa'ayi, idan ka ƙara magana ka MUTU!"
Muryarta ta haɗu da Kamalar-ruhinta tayi sama. Duk abinda ke faruwa da Tasu'a da Haruta da Maruta da shugaban makarantar Babila suna gefe kawai suna kallo babu wanda ya shiga.
Sarkin-sarki na rufe bakinta kowa ya zare ido cikin mamakin rashin tsoronta. Tsarin shi ne indai kana ƙasa da izzar mutun baka isa kayi amfani da Kamalar-ruhi akansa ba idan ba haka ba kuma abin kanka zai dawo.
Cikin rashin tsoro Sarkin-sarki ta ɗaga ƙafa ta ɗauki taku na gaba. Haka na faruwa ƙarfin iko mai ɗauke da nauyin maɗaukakiyar fada da doron ƙasa na farko ya sauka akanta. Ƙasusuwan jikinta suka fara ɓaɓɓallewa. Ta tafi ƙasa zata faɗi amma a lokacin Bihanzin ya bayyana ya tallafeta. Yana bayyana fasahar Kuyurussa'ayi ta Kamalar-ruhi ta ɓace ta dawo kansa. Nauyin ya dannashi ƙasa amma a lokacin hoton takobin dauwamammen sara ya bayyana a bayansa. Takobin tayi kan idanun Ururu inda nauyin dake sauka daga sama ya ɓace. Ciwukan sarkin-sarki suka ɓace ta ƙara dawowa sabuwa.
Bihanzin ya kalli Tasu'a sannan ya juyo kan shugaban makarantar Babila wanda ke gefe. Sannan ya ɗaga kai ya kalli sama yai murmushi ba tare da ya ce komai ba yayiwa Sarkin-sarki inkiya da ido cewa lokacin tafiya yayi. Su biyun suka ɓace kamar dama can basu taɓa zuwa ba. Ɓangaren Tasu'a suma suka ɓace, shima shugaban Babila ya ɓace.
Acikin gasar kuma Armad na zaune ba hannu ɗaya. Sarkin-sarki ta tarwatsa masa hannunsa na dama tun daga kafaɗa har zuwa ƙasa. A lokacin da yake ƙoƙarin tsayarda jinin Hasanu yayi amfani da damar ya tsere zuwa mataki na biyar inda Ƙaizadussa'ayi yake. Har yanzu Ƙaizadu na zaune yana jira, ko buɗe ido ya kalli Hasanu baiyi ba.
Hasanu ya wuce mataki na shida inda ya haɗu da Ikenga.
A cikin duniyar Negrinki kuwa Elbinuil na zaune a tsakiyar wutar amma ko kwarzane babu a jikinsa. Yasha tauri wanda baya gogewa. Hasalima wutar ko kaɗan bata damunsa, abinda kawai yake damunsa shi ne nauyi wanda yake hanashi motsi amma da tuni ya fara neman ƙofar fita.
Bayan Armad ya gama gyara kafaɗarsa ya tashi yabi matattakala zuwa mataki na biyar inda Ƙaizadu yake.
Babbar tambayar anan ita ce meye haƙiƙanin dalilin daya kawo sarkin-sarki da Bihanzin wannan gasa? Shin da gaske sun zo ne dan su ceci Hasanu? Ko Elbinuil? Ko kuma dai akwai wani ɓoyayyen shiri a ƙas. Amsar wannan tambaya tana kwana biyu da suka wuce.
Kwana biyu da suka wuce
Daular Elbis
Fadar sarkin-sarki
Tattaunawa tsakanin Bihanzin da Sarkin-sarki
Sarkin-sarki ta dubi Bihanzin ta ce, "kwana sittin? Kana nufin nan da kwana sittin za'a gama?"
Bihanzin ya gyaɗa kai ya ce, "na gama lissafa komai, nan da kwana sittin zamu mallaki duniya da abinda ke cikinta. Abu na farko ina so nayi miki bayanin sabuwar fasahar Laidan. Tana da ɓangarori guda huɗu: Laidan Gabas, Laidan yamma, Laidan Kudu da Laidan Arewa. Kowanne ɓangare yana ƙarƙashin fanni guda ɗaya daga cikin fannoni huɗu na filin daga wato Tsaro, Hari, Yanayin-izza da kuma Sauri.
"Bari na fara magana akan Laidan Gabas wadda take ƙarƙashin Yanayin-izza. Akwai bayanai kan cewa Kuyurussa'ayi yayi dogon bacci kuma bazai tashi ba har sai ranar da wani yakai matakin izzarsa. Hakan ne yasa wasu daga cikin ƴan leƙen asirinmu na doron ƙasa ta farko suke ganin Kuyurussa'ayi ya daɗe da mutuwa. Kinga akwai abubuwa uku: kodai Kuyurussa'ayi ya mutu, kodai yana da rai amma bacci yake, ko kuma yana da rai kuma idonsa biyu. Shirin mu na kwana sittin masu zuwa ya ta'allaƙa da wanne yanayi Kuyurussa'ayi yake ciki saboda haka dole mu tabbatar da wanne ne ba wanne ne ba."
Sarkin-sarki ta haɗe gira ta ce, "sai dai mu je doron ƙasa ta farko mu shiga maɗaukakiyar fada mu duba idan muna don sanin wannan amsa."
Bihanzin yai murmushi. "Ki kwantar da hankalinki ba sai munje sama ba. Kin tuno wanda ya ƙirƙiro da gasar nan da ake yi ta cin ruhin Deba?"
Sarkin-sarki ta gyaɗa kai. "Kuyuru ne."
"Hakane Kuyurussa'ayi shi ne ya ƙirƙiro ta, idan muka yi mata kutse lallai bazai yi shiru ba. Indai yayi magana ni kuma zanyi amfani fasahar Laidan Gabas na gano halin da ake ciki. Idan ma bacci yake zamu sani, idan ma ya mutu zamu sani, idan yana raye ido biyu zamu sani."
Sarkin-sarki tayi shiru tana jimanta abin a ranta, tasan abinda Bihanzin yake so tayi amma a zahiri bata son bayyana kanta a duniya saboda wasu dalilai. Bayan tsahon lokaci ta numfasa ta ce, "wai ma tsaya, wanne ne acikin ukun zai dace da shirin mu na?"
Bihanzin yai ajiyar zuciya ya ce, "kinga dai idan Kuyurussa'ayi ya mutu to dole akwai wanda ya gaje shi wanda kuma ba yarima Dumaƙisu bane ba kuma waziri Tadiyraini bane. Koma waye yakai matsayin Kuyurussa'ayi shi yasa ya gaje shi. Wannan bazai dace da shirinmu ba domin kuwa da maƙiyin da baka sani ba gwanda wanda ka sani. Na biyu idan Kuyurussa'ayi yana nan amma yana bacci. Hakan yana nuna Kuyurussa'ayi yana iya ganin abinda zai faru shekaru dubu kafin abin ya faru, ya kuma shiryawa faruwar abin tayadda koda yana bacci ruhinsa zaiyi aikin da ake so. Idan haka ne to yana nuna Kuyuru ya wuce inda muke zatonsa. Shima wannan bazai dace da shirinmu ba.
"Na uku idan ya kasance Kuyuru yana nan kuma idonsa biyu. Hakan shima bai dace da shirinmu ba domin kuwa yadda muke shiri shima zai zamo yana shiri."
Sarkin-sarki taja dogon numfashi ta ce, "to meye amfanin sanin idan duk ukun babu wanda ya dace da shirinmu?"
"Babu wanda ya dace da shirin mu to amma sanin dole ne domin musan halinda abokan gaba suke ciki. Ta sama zamu shige su ko kuma ta ƙasa, ko ta gefe?" Inji Bihanzin.
Nan fa suka shiga tattaunawa akan yadda zasu yi kutse cikin gasar. Hakan ne ya jawo bayyanar Sarkin-sarki da kuma Bihanzin a makarantar Babila. Ko wacce amsa suka samu bayan Kuyurussa'ayi yayi magana?!?!
***
Babi na 223-225
***
Armad ya ƙarasa hawa matakkalar a hankali inda ya tarar da baƙar wuta naci tana balbali ta rufe ko'ina. Daga can bayan wutar kuma yana hango matattakalar da zata kaishi mataki na shida. A ƙasa da matattakalar Armad yana jin yanayin-izzar wani abu mai girma wanda ya tokare da sararin samaniya.
Armad ya ƙara ƙura ido amma maimakon ya gane menene wannan abun sai kawai yaga girman abun ya ƙara ƙaruwa ya rufe ko'ina. Wata irin izza mai girma na tashi daga jikin abun tana malala ta cika ko'ina. Can bayan ɗan lokaci Armad ya hango wasu abubuwa guda biyu sun buɗe a jikin wannan abu. Abubuwan sunyi kama da idanu amma idan ka ƙura musu ido zaka ga masu ne masu tsini ababen haske da walwali.
Ba jimawa Armad ya gane abinda ke faruwa, wannan gayyatar yaƙi ce ba komai ba.
Yai tsalle da fasahar kaban'shisu ya dira a bayan wutar inda yai arba da ma'aboci wannan izza. Saurayi ne kamar sa. Fari dogo mai dogon hanci da baƙaƙen idanu. Yana da ƴar doguwar fuska da baƙin gashi dogo wanda ya sakko har wuyansa duk da kuwa an ɗaure shi ta baya. Yana sanye doguwar riga wadda aka ɗinka da wani irin tufafi mai duhu wanda Armad bai taɓa gani ba. Shi dai wannan tufafin yana da duhu amma kuma a lokaci guda walwali yake kamar baƙar fitila. Ƙirjin rigar a buɗe yake wanda ya bayyana murɗaɗɗen ƙirjin wannan saurayi. Sunan wannan saurayi Ƙaizadussa'ayi Ururu.
Koda ganin Armad ba hannu ɗaya sai Ƙaizadu ya canja fuska, canjin fuska irin wanda ke nuna bai ji daɗi ba amma kuma dama can ya riga ya sani. Ya nuna hannun daya cire tare da buɗe baki zaiyi magana amma bayan ɗan taƙi ya fasa ya rufe bakinsa.
"Baka taɓa ganin mai hannu ɗaya ba?" Inji Armad.
"Meye amfanin tambayar da baza a baka amsa ba." Inji Ƙaizadu.
Armad najin haka ya tuna da Uznu Ururu a ransa yana cewa, Fasahar [Saɓani]!
Ƙaizadu ya miƙe a hankali ya tsaya, surarsa ta bayyana a haske. Yafi Armad tsayi da kai ɗaya. Jikinsa na bada ƙanshin sarauta tsohuwa, izzarsa na bada ƙarfin jini, fuskarsa na bada dabarun yaƙi, ruhinsa na bada girma da ɗaukaka da sarauta da buwaya irin wanda babu a jikin Armad.
[Saɓani]
[Bayani]
[Haƙiƙa]
[Baƙar-wuta]
[Shankil]
Nan take fasahohin Ururu suka fara kwaranya.
Ba tare da alama ba kawai sai gani yayi Ƙaizadu ya bayyana a gabansa. Armad baiyi ƙoƙarin kaucewa gefe ba, ya tsaya cak a inda yake. Ƙaizadu ya kawo duka ya sami Armad a dai-dai dungulmin hannunsa daya cire. Lamarinda yai cilli da Armad gefe guda. Jini ya fara zuba daga hannun da ya cire.
Kafin Armad ya ankara Ƙaizadu ya dira akan ruwan cikinsa lamarinda yasa dukkan kayan cikinsa suka kaɗa, wani ƙaton dunƙulen jini ya futo ta hancinsa. Ruhin Armad yai ƙara ya kamar zai tsage. Jikinsa ya kama da baƙar wuta. Sannu a hankali jikin Armad ya fara ƙonewa yana cinyewa har saida ya ƙone ƙurmus ya ɓace.
Armad ya bayyana a duniyar-kuyurussa'ayi. Haske ya ɗauke, duhu ya yawaita. Wannan shi ne karo na biyu da Armad yazo duniyar Kuyurussa'ayi. A wancan lokaci Uznu ne ya kawo shi kuma yayi amfani da Miyurarsa ya fice. A wancan lokacin bashi da fasahar [waƙar-maƙabarta] kuma bashi da Negrinki. A wancan lokaci da yazo akwai tsoro a ransa, amma a wannan lokaci yana bayyana yai arba da halittun Dordor wanda yawansu ya ninninka wanda ya tarar a baya, wataƙila sabida jinin Ƙaizadu na Ururu yafi na Uznu ƙarfi.
Dukkan wannan halittu sukai kan Armad gadan-gadan da niyyar afka masa. Babu gida gaba babu gida baya, babu wajen guduwa ko ɓuya. Ko'ina baƙi ne cike da baƙar-wuta tana ci tana balbali.
Maimaikon guduwa ko tsoro Armad miƙewa tsaye yayi ya tofar da jinin dake bakinsa. Sannan a nutse ya kira fasaha:
"[Tsallen-Eycigan]"
Nan take iska ta dare gida biyu, hanya ta bayyana. Ya miƙa hannunsa ya kamo zaren izzar Ƙaizadu ya taka ya fito. Yana dira ya ƙara kiran wata fasahar:
"[Telan-ruhi]"
Nan take ruhinsa daya fara tsagewa ya dawo ya haɗe.
"[Sekai]."
Nan take jikinsa ya juye izuwa balbalin walƙiya abar ruruwa tana sama tana ambaliya.
Armad ya dubi Ƙaizadu ya ce, "saura ni."
Yana rufe baki ya kira ɗalasimai, "[Kaban'shísu] [Hannun-Aradu]."
Ya bayyana a gaban Ƙaizadu, hannunsa dunƙule cike da walƙiya. Bai zame ko'ina ba sai ƙirjin Ƙaizadu inda ya dira akan zuciyarsa. Walƙiyar tayi rami ta cinye ƙashin ƙirjin Ƙaizadu sannan ta shige hunhunsa ta fafake komai ta cinye. Armad ya ƙara yawan walƙiyar inda ta shige cikin Ƙaizadu ta rarake komai dake cikin. Sannan daga bisani launin walƙiyar ya juye izuwa jajawur launin Negrinki, wadda ta zuƙe Ƙaizadu zuwa duniyar Armad. Dukkan abinda ya faru Ƙaizadu baiyi ƙoƙarin kare kansa ba kamar yadda a baya shima Armad bai kare kansa daga harin sa ba.
Armad ya koma gefe ya tsaya.
Acikin duniyar Armad Ƙaizadu ya bayyana akan ɗaya daga cikin tsainuka bakwai dake cikin duniyar. Yana dira wutar dake ci a ƙasa tayo kansa. Tsaunin yai sama ya cillo shi cikin wutar, sannan aradu ta sauka daga sama. Dukkan wannan bala'in akwai kuma fasahar Nauyi dake matse shi tana danne shi ta hanashi sakat.
Sannu a hankali ya diro cikin wutar. Daga can gefe ya hangi Elbinuil Randuil zaune cikin wutar. Shi bai ƙone ba amma kuma ya kasa fita. Daga kan ɗaya daga tsibiran ya hangi Hidaya na zaune na kallonsa.
Maimakon damuwa sai kawai murmushi ya ɓarke a fuskar Ƙaizadu. Nan take ya tafa hannunsa cikin kwarewa, wasu hatimai suka bayyana akan iska. Nan take murmushin fuskar Ƙaizadu ya ƙara faɗaɗa. Kafin murmushin ya bar fuskarsa wani hayaƙi ya fara fita daga jikinsa. Abu na gaba daya faru ya bawa kowa mamaki a duniya.
Da tsibiran guda bakwai, da wutar data cika duniyar, da nauyin, da Elbinuil Randuil da Hidaya da komai dake ciki ya juye izuwa ƙanƙara. Ƙaizadu ya ƙanƙare komai cikin daƙiƙa ɗaya. Sai dai da a iya nan abin ya tsaya to da da sauƙi. Amma wannan ƙanƙara ta fito daga duniyar Armad ta fito waje ta shigo cikin makarantar Babila. Wajenda Armad yake tsaye nan ne ya fara ƙanƙarewa, sannan dukkan matakan guda shida dake cikin gasar suka ƙanƙare. Ikenga da Hasanu da Armad duk suka ƙanƙare.
Idan da anan abin ya tsaya to da da sauƙi amma ana haka sai ƙanƙarar ta fara fitowa daga cikin ƙofar asali ta shiga ƙofar gaskiya, sannan daga nan ta fito wajen ƴan-kallo. Kafin shaihu Babila ko wazirinsa ko wani malami yayi wani abu tuni ɗalibai dubu sun ƙanƙare. Duk wanda yayi ƙanƙara sai kaga yayi ya murmushe ya ɓarɓashe a ƙasa. Cikin tsananin zafin nama malamai suka shiga tsakani.
Armad tsaki kawai yayi ƙanƙarar ta narke, kamar Hasanu da Ikenga wanda suma duk da sunyi ƙanƙara amma bata kama su da yawa ba.
Babu wanda yasan yadda akai amma sai ga Ƙaizadu daga duniyar Armad babu ko kwarzane.
***
A doron ƙasa ta farko yarima ne tare da waziri Tadiyraini da mutun uku daga cikin Tasu'a suna kallon wannan gasa.
Waziri ya fashe da dariya ya ce, "yara kenan, duk wannan abun da sukai wai gaisuwa ce. Tunanin su ya zo ɗaya. Muje zuwa."
Yarima bai ce komai ba kawai gyaɗa kai yayi ya ci gaba da kallo. Sauran sarakunan Tasu'a kowa ya jefa albarkacin bakinsa. Kafin daga baya kowa yayi shiru suci gaba da kallo.
Zasu iya kallon wannan gasa ta hanyar fasahar [Shankil] amma yarima ya hana ya ce a saka allo kowa ya gani.
Shaihu Babila da kansa ya tsaya a bakin ƙofar asali domin tare duk wani ɗalasimi ko wata fasaha da tayi ɓatan dabo ta dawo.
Acikin gasar Armad da Ƙaizadu na tsaye suna kallon-kallo. Idan Ururu suna da idanu to ai Wilbafos suna da Miyura.
Nan take Miyurar Armad ta fara haske. Takobin izza ta fito daga cikin Miyurar. Fitowar takobin kaɗai saida yasa rana tayi duhu.
Dukkan wani mahaluƙi dake Babila sai da yaji izzarsa tana rawa. Shi kuwa Ƙaizadu dake kusa da Armad jikinsa karkarwa ya fara yana rawar ɗari, idan ka kalli gefen bakinsa akwai ɗan jini daya fara zuba. Amma ba jimawa jikinsa ya dawo dai-dai, maimakon kaga tsoro a fuskarsa sai kawai wani sabon murmushi ya bayyana. Ya miƙa hannunsa saman kansa inda wani shinge baƙi-ƙirin wanda faɗinsa yakai zira'i biyar ya bayyana. Sunan wannan shinge Taskar-ruhi. Ita ce fasahar da hatta Uznu bashi da ita. Daga Ururu sai Ururu.
Ta hanyar wannan fasaha kana iya kama ruhi kowanne iri ne ka ɗaure kasa ya ringa bauta maka. Iya yawan ruhin daka kama iya yawan ƙarfinka. Sai dai kuma a kullum ya danganta da yanayin ruhin. Misali, ruhin Deba ɗaya yafi ruhin Sammai dubu. Wani sirri da Taskar-ruhi shi ne yadda zaka iya sarrafa ruhin daka ɗaure ka basu fasaha ta musamman, ko kuma ka canja tsarinsu ka basu sabon tunani da addini.
Ƙaizadu ya miƙa hannunsa ciki ya zaro wata fatalwa fara mai dogon gashi. Tana fitowa jikinta ya koma irin na mutane. Sannan Ƙaizadu ya dube ta ya ce, "Jiu 13, kwafar mana yanayin-izzarsa ki rubuta shi a matsayin sabon bincike da zamuyi."
Nan take biro da takarda suka bayyana a hannun fatalwa mai suna Jiu 13. Ta koma gefe ta fara rubuce-rubuce. Ƙaizadu yayi ajiyar zuciya tare da jan dogon numfashi. Sannan ya haɗe hannayensa guda biyu ya rufe ido.
Abin mamaki fatalwi ne suka fara zuba daga cikin baƙin abin dake saman kansa. Duk fatalwar data futo sai kaga ta rikeɗe izuwa siffar mutun, ko mace ko namiji. Sannu a hankali sai da fatalwi dubu suka futo suka taru wata kan wata sukai tsiri. Kowacce fatalwa tana da idanuwan Ururu amma fatarsu baƙa ce mai munin gaske. Suna fitarda wani maiƙo na baƙin sihiri. Abin mamaki kowacce fatalwa tana da jela doguwa wadda ta haɗu data ƴar uwarta, ta haka dukkaninsu a haɗe suke da juna.
Wani irin sauti mai razani na fita daga bakinsu. Sautin yayi kama da nishi to amma kuma ta hanci yake fita kamar gurnani. A duk sanda sukai nishin sai kaga baƙin hayaƙi ya fito daga bakinsu lamarinda yasa hazo ya fara taruwa.
Ana haka sai kawai tsinin jelar wannan fatalwi da ta haɗe waje guda ta tafi taje ta shige cikin cibiyar Ƙaizadu. Haka na faruwa sai kawai fatalwin suka fara shigewa cikin cibiyar Ƙaizadu. Duk sanda fatalwa ɗaya ta shiga sai kaga jikinsa ya ƙara haske ya ƙara kyau. Daga bisani sai jikinsa ya fara girma yana kumbura. Cikin ƴan daƙiƙu ya zuƙe dukkan fatalwin cikin jikinsa.
Idan ka kalleshi kasan shi ne dai Ƙaizadu amma kuma ya ƙara tsayi zira'i biyu, sannan kuma gaɓɓansa da tsokar jikinsa ta ƙara girma. Dukkan abinda ya faru ya faru ne cikin daƙiƙa biyar kacal.
Bayan komai ya kammala Ƙaizadu ya dubi Armad ya ce, "idan gidan Wilbafos kuna da izza to gidan Ururu muna da ruhi. Kana tunanin bayan shekaru dubu da yaƙin rukunai biyu har yanzu bamu da maganin takobin izza?"
Armad ya buɗe baki zaiyi magana amma Ƙaizadu ya riga shi, "akwai dai masu tsoron Hidaya amma banda ni. Domin ni..."
Armad ya katse shi da cewa, "amma a haka kuke tsoron Hidaya sama da shekaru da dama." Yana rufe baki ya gano cewa tuni Ƙaizadu ya bashi amsarsa. Sabida haka ya rabuda shi ya ƙarasa.
"Domin ni fatalwi na basa amfani da izza. Ni ne mutun na uku a duk faɗin duniya wanda na samarda abin ruhi wanda baya buƙatar izza. Idan kana tunani zaka yi nasara a wannan yaƙi saboda fasahar izza to ka canja shawara."
Armad ya juye izuwa walƙiya sannan ya jawo duk wani ɗalasimi daya sani a waƙar-maƙabarta kusa. Tunda hannu ɗaya ne dashi babu damar amfani da takobi da kuma hannun-aradu saboda haka ya zaɓi takobi.
Dunƙulen walƙiya ya fara ci a ɓangaren Armad, kafin kace meye wannan ya kai girman rana. Baka ganin komai, baka ganin Armad domin kuwa yana tsakiyar ranar.
A ɗaya ɓangaren kuma dusar ƙanƙara ce ta fara zuba kamar da bakin kwarya. Cikin rabin daƙiƙa duniya ta rabu gida biyu, rabi ƙanƙara rabi walƙiya. Ƙaizadu yai ƙaraji ya afkawa Armad, shima ya afka masa sukai arangama irin wadda aka daɗe ba'a gani ba.
Koda haɗuwarsu sai filin ya fara girgiza yana rawa. Walƙiyar Armad tana ƙoƙarin cinye Ƙaizadu shima ƙanƙararsa na neman ƙanƙare Armad. Tsahon lokaci ana wannan fafatawa kafin daga bisani abubuwa su fara canjawa. Abu kamar wasa sai ƙanƙarar Ƙaizadu ta fara cin walƙiyar Armad, cikin ƴan daƙiƙu komai ya ƙanƙare. Armad yai tsalle ya koma gefe.
Ƙaizadu ya tsaya a gefe yana kallonsa.
Kowanne ruhi acikin wannan fatalwi yakai Deba! Ruhin Deba dubu a jikinsa shi kaɗai?
Wannan tunani na zuwa ran Armad fuskarsa ta canja. Ƙaizadu a matakin Sammai yake, mataki ɗaya da Uznu, amma yafi ƙarfin Uznu nesa ba kusa ba. Hasalima a iya tunanin Armad bai taɓa gaba da gaba da kamar Ƙaizadu. Kuma babban abin tashin hankalin shi ne har yanzu yana ji a ransa akwai wasu sirrika da Ƙaizadu yake ɓoyewa wanda zai iya fito dasu a kowanne lokaci.
Negrinkin Armad baiyi aiki ba, walƙiya batai ba...
Nan take Armad ya juye izuwa mutun sannan ya nuna Ƙaizadu da hannu. Ƙaizadu yayi murmushi sannan shima ya ɗauke ƙanƙararsa.
Faɗan hannu da hannu za'ai.
Samarin biyu suka afkawa juna da dantsensu. Armad ya kai wa Ƙaizadu duka a fuska amma maimakon Ƙaizadu ya kauce sai ya ƙara matso masa da fuskarsa. A lokaci guda shima Ƙaizadu ya kawo masa duka da ɗaya hannunsa. Shima Armad bai kauce ba. Kowa ya daki kowa a fuska. Armad yana da jikin izza shi kuma Ƙaizadu yana da jikin ruhi.
Armad yaji ƙararrawa a kunnensa, ƙarfin dukan yai jifa dashi gefe guda. Shima Ƙaizadu haka. Sai dai idan ka duba zaka ga Ƙaizadu bai ƙarasa ƙasa ba ya tashi. Dukan yafi shigar Armad. Idan da ace wani mahaluƙin Armad yayi wa wannan dukan da tuni ya daɗe a lahira to amma Ƙaizadu a halin yanzu jikinsa baya amfani da izza. Saboda haka duk wani harin Armad baya zuwa ko'ina. Shi kuma a ɓangare guda harin Ƙaizadu har cikin ruhinsa yake shiga, banda tsagoran ƙarfi da yake dashi akwai sirrin cutar da ruhi.
Armad ya miƙe suka ƙara garƙamewa cikin fafatawa. Duka da hannu da ƙafa. Kowa acikinsu baya ƙoƙarin karewa kawai ƙoƙarin kai duka suke, a saboda haka yawan raunikan dake jikinsu ya ƙaru. Lallai ba'ai ƙarya ba da aka ce Ƙaizadu ya kware a kowacce fasaha tun yana ɗan shekara bakwai. Domin kuwa a halin yanzu baje kolin fasaha ake.
Armad ya kira fasaha: "[Inkil Dantse]."
Ƙaizadu ya kira ta sa fasahar, "[Ƙashin Samudu]."
Armad, "[Tsaiwar-wata]."
Ƙaizadu, "[Zagayen-rana]."
Nan fa aka ƙara rincaɓewa. Kayan jikinsu suka yayyage suka radaddage. Wannan faɗan hannu da ake bawai karazuben kokawa bace. Akwai RAWA irin ta izza data ruhi aciki. Ƙaizadu ko kaɗan baya amfani da fasahar Saɓani wajen kaucewa harin Armad. Hasalima kai kansa yake. Shima Armad baya ƙoƙarin kaucewa harinsa. Kowa acikinsu ya yadda da jikinsa. A duk sanda jikinsu ya haɗu sai kaga iska ta tashi, ƙura ta turnuƙe. Sirrin izza da na ruhi sunyi sama.
A hankali a hankali Armad ya fara gane yadda harin ruhi yake aiki. Bashi da banbanci sosai da harin izza sai dai shi ruhi yake duka. A duk sanda aka sami ruhinsa ƙarfin jikinsa da izzarsa da fasahohinsa ƙasa yake. Sai dai kuma Armad yana da Miyura da yake kare kansa da ita yana ƙarawa kansa ƙarfin izza.
Bayan tsahon lokaci suka ɗauki takobi. Ƙaizadu ya juyarda taskar-ruhinsa izuwa takobi, shi kuma Armad ya zaro takobi daga cikin Miyurarsa.
Nan fa aka koma rawar takobi. Kowa acikinsu yana ƙoƙarin nuna fasaha daban-daban. Abin mamaki duk da yawan fasahan dake kan Armad acikin waƙar-maƙabarta saida Ƙaizadu ya kamo shi. Duk wata fasaha da zai futo da ita Ƙaizadu zai futo da makamanciyarta. Wannan zai nuna maka girman al'amarin Ƙaizadu da ƙarfin kwakwalwarsa. A ƴan shekarunsa yasan yawan fasahohin da zasu jera kafaɗa da waƙar-maƙabarta. Lallai Tadiyraini baiyi ƙarya ba, Ƙaizadu sirri ne ɓoyayye, takobi ce sihirtacciya wadda aka zare a yau.
A wannan rana tamkar tsohuwar daular Wilbafos ce da kuma daular Ururu suke fafatawa. Idan ka kalli faɗan tun farko kowa acikinsu yasan duniya tana kallo, saboda haka kowa yana yi dan gidansu. Rashin kare harin ɗan'uwasa na nuna cewa babu sauran tsoro. Rana ce ta baje-kolin fasaha. Idan gidan Wilbafos sun sa Armad a gaba to gidan Ururu sun sa Ƙaizadu a gaba.
Bayan takubban sun kakkarye aka futo da wasu aka ɗora daga inda aka tsaya. Sai da aka shafe sa'a uku ana wannan fafatawa sannan kowa ya jada baya suna haki. Idan ka dubi Ƙaizadu zaka ga ko kwarzane babu a jikinsa ballantana jini. Shi kuwa Armad duk da taimakon jikin izzarsa a jiƙe yake da jini faca-faca. Yafi Ƙaizadu gajiya kuma yafi Ƙaizadu nishi.
Armad ya nutsu ya ƙara karanta yanayin da ake ciki. Negrinki da Izza duk basa aiki akan Ƙaizadu. Walƙiya ma bata yi. Waƙar-maƙabarta bata yi. A zahiri babu wani abu da yake aiki a kan Ƙaizadu. Yana tsaye ƙiƙam cikin isa da kamala, kai kace wani ƙasurgumin tsauni ne mara ƙarshe mara iyaka. Idanu baƙaƙe, farar-fata, jikin ruhi.
Wai duk wannan abin dan ma Ƙaizadu baya amfani da fasahar Saɓani da ko sau ɗaya Armad bazai samu damar kai masa hari ba, domin kuwa ƙarfin fasahar da zai samar sai tafi ta Uznu.
Armad ya ƙara nutsuwa ya ƙara karanta yanayin. Babban matsalarsa shi ne gaba ɗaya fasahohin Ƙaizadu sunfi nasa ƙarfi, misali ƙanƙara ace tana aiki akan walƙiya ai akwai damuwa. Kamata yayi ace walƙiya ce take narka ƙanƙara. Amma a wannan lokaci ne murmushi yazo fuskar Armad, wannan ne karo na farko daya samu wani mahaluƙi wanda yake tsaransa amma kuma yafi shi. Wanda hakan ke nuna duk yanda yakai akwai wanda zai fishi. Sai dai ba'a wannan rana ba, a yau lallai sai yayi nasara. Dukkan ƙimarsa da ƙimar gidan Wilbafos tana ƙasa. Idan ya faɗi a yayin wannan fafatawa da saurayi kamarsa ɗan shekarunsa to ta yaya zai iya tunkarar Bihanzin da sarakunan Jinzidal, ballantana babban sarki Kuyurussa'ayi wanda idan aka kwatanta shi da Ƙaizadu zaka iya cewa kamar mutun ne da kiyashi. Sannan kuma meye amfanin sadaukar da rayuwarta da Hidaya tayi?
Armad ya gyara tsaiwa ya shiga lissafi. A dai-dai lokacin yaji muryar Ƙaizadu na cewa, "lokacin wasa yazo ƙarshe. Idan kana da wata fasaha ka fito da ita."
Yana rufe baki ya nuna Armad da ɗan'yatsa, lamarinda yasa hayaƙin Negrinki ya fara zuba daga jikinsa. A lokaci na farko tsoro ya bayyana a fuskar Armad domin wannan ba irin Negrinkin daya saba gani bace. Ba irin ta Uznu bace kuma ba irin ta Hidaya bace.
***
Babi na 226-.229
***
Wai daman bai ma yi amfani da Negrinkinsa ba?
Wannan shi ne tunanin da ya cika zuƙatan duk wani mai kallon wannan gasa. Ƙaizadu abin tsoro, Ururu abin tsoro.
Sannu a hankali baƙin hayaƙi mai rawaya-rawaya ya kewaye Ƙaizadu. Akwai wasu irin halittu wanda basu da jiki acikin hayaƙi suna bada ihu mara sauti. Ɗaya daga cikinsu yana da ƙaho wanda yakai zira'i biyu, ɗaya kuma yana da ido ɗaya a tsakiyar kansa. Armad ya fuskanci cewa wannan abubuwan guda biyu aljanu ne, amma ragowar Dordor ne.
Ƙaizadu ya daki ƙasa. Lamarinda yasa Negrinkinsa ya tashi sama ya tokare sararin samaniya. Manyan baƙaƙen idanuwa guda biyu biyu suka bayyana a sama suka ƙurawa Armad ido. Kiɗan babbar izza ya fara tashi. Hankula suka ɗugunzuma, ruhina suka razana, rana ta risuna.
"Ni ne Ƙaizadu ɗan yarima Dumaƙisu ɗan babban sarki Kuyurussa'ayi. Na sakko kasa dan hukunta Armad Wilbafos ɗan Eyriyon Wilbafos." Muryar Ƙaizadu ta zaga ko'ina a faɗin duniya kai kace yana ko'ina. Kowa ya nutsu, tsoffi suka shiga taitayinsu, yara suka fara rawar ɗari. Ace Ƙaizadu a matakin Sammai yake akwai kuskure, domin kuwa a wannan rana babu wani Deba da ya isa ya tanka masa.
Ƙaizadu ya ɗaga ƙafarsa ya yi taku ɗaya, nan take ƙasar gurin daya taka ta canja tayi baƙi-ƙirin ta bushe. Abin mamaki Armad na tsaye ya kasa motsi kamar ya suma. Kan kace meye wannan Ƙaizadu ya iso gabansa. A lokacin Armad ya ɗaga hannu ya samarda Negrinki, tunda hannunsa guda ɗaya ne ya samarda takobi guda ɗaya ƙatotuwa, sannan ya kewaye jikinsa da Negrinki. Idan ka kwatanta girma da yawan Negrinkin Armad data Ƙaizadu za kaga kamar allura ce ta faɗa cikin teku.
Ƙaizadu ya dunƙulen hannunsa, inda hannun gaba ɗaya ya juye izuwa Negrinki. Ya kawo wa Armad duka, Armad yakai masa sara ta ɗaya ɓangaren. Kowa acikinsu baiyi ƙokarin kaucewa ko kare kansa ba. Tsagoran yadda da Negrinki.
Koda takobin Ƙaizadu ta sauka akan Armad sai fatar Armad tayi baƙi, ruhinsa yayi baƙi sannan tufafinsa ma yayi baƙi. Armad bai san sanda yayi ƙoƙarin komawa walƙiya ba saboda tsananin zafi, ihu ya nemi kwace masa amma ya cije.
A ɗaya ɓangaren kuma Negrinkin Armad ta sauka akan Ƙaizadu. Ta ratsa jikinsa tun daga kafaɗar dama har zuwa ƙugun hagu, jini yayi feshi amma kafin jinin yaje ƙasa ƙanƙara ta bayyana ta haɗe jikinsa. Komai ya haɗe ya dawo dai-dai.
Ƙaizadu ya nuna Armad ya ce, "kana tunanin Negrinkin da ko suna bata dashi ita ce zatai aiki a kaina? Sunan Negrinki na DIL'INDIR, yunwa mai cin ruhi."
Yana magana manyan aljanun nan masu ƙaho da mai ido a tsakiyar ka suka dira kan Armad. Jikin Armad ya koma walƙiya amma suna taɓa shi ya dawo dai-dai, walƙiyar ta ɗauke. Lokaci ya daina gudu.
Ma'aboci ƙahon ya kafa ƙahonsa a cikin Armad, shi kuma ɗayan ya kafa bakinsa a wuyan Armad kamar Banfaya (vampire). Tunda Armad yazo duniya bai taɓa jin zafi irin na wannan rana ba, sauran ƙiris ihu ya kufce masa amma ya ciji harshensa da ƙarfi har saida jini ya fara kwaranya ta gefen bakinsa. Zafi da jini da raɗaɗi ya cika kwakwalwarsa. Jini ya haɗu da ƙasa suka fara bada ƙarni mai ratsa zuciya. Idan akwai wata fasaha ko kuma wani shiri da Armad yake dashi to yanzu ne lokaci. Shima yasan haka.
Armad yakai sara da takobin Negrinki amma bisa mamaki sai kawai ta shige ta cikin aljanun. Yakai sara da walƙiya, yasa hannu amma duk a banza.
A duk sanda wannan aljanu biyu suka zuƙi ruhinsa sai kaga gashinsa yayi fari, fatarsa ta tsofe ta yamushe. Hankakan mutuwa ya fara yawo a kansa yana sanar masa lokaci yayi. A hankali a hankali saida suka zuƙe dukkan ruhin Armad ya rage saura ɗan ɗigo.
Tun Armad na iya buɗe ido har ya kasa. Negrinkinsa ya ƙare, duniya tayi duhu. Babu komai daya rage a idanunsa sai halaka.
Ƙaizadu ya taho a hankali ya tsaya a gaban yana cewa, "kayi ƙoƙari daka kawo wannan mataki a rayuwarka, amma ka gane banbanci na dakai asali ne. Jini da tsarin halitta. Ba laifin ka bane, ba kuma rashin ƙoƙarin ka bane, komai yadda zakai ƙoƙari kayi nasara baza ka iya ba. Asali. Jini. Tsarin-ruhi. An fika waɗannan. Fasaha ɗaya ce ta rage maka a yanzu, [Fasahar-Mutuwa]. Kai kanka ba lallai kasan da wannan fasaha acikin jinin kaba amma kana da ita."
A zahiri shi kansa Armad yasan lokaci yayi. Babu wata fasaha data rage masa, kuma babu wani tsimi ko dabara. Ita kanta wannan [Fasahar-mutuwa]r da Ƙaizadu yake magana a kanta Armad bai taɓa jinta ba. Kuma babu ita acikin [waƙar-makabarta].
Idan kayi zancen Negrinki to Armad yana da duniyar Negrinki, idan kace Walƙiya to yana da jikin walƙiya, idan kace fasaha to yana da waƙar-maƙabarta, idan kace izza to yana da Miyura. Amma babu wani abu da baiyi amfani dashi ba amma Ƙaizadu ya wuce nan, Ƙaizadu shi ne ƙololuwar misali na doron ƙasa ta farko da kuma ɗalibansu. Duk wani matashi yana bayansa. A yau idan Armad yayi nasara akansa to zaka iya cewa yafi ƙarfin duk wani matashi a doron ƙasa ta farko.
Armad zai iya bugar ƙirji ya ce a ƙasashen ƙasa indai basu Bihanzin ba da sarakunan Jinzidal da irinsu Ikenga to sai dai sashin Ikwatora amma babu wani ɗa. Amma a yau ya ƙara fahimtar yadda duniya take: duk inda ka kai da kwarewa to wani ya fika. Kuma akwai irin ɗaliban nan da zaka haɗu dasu a aji komai zakai sai sun fika cin jarabawa, ko zaka daina bacci ka shiga halwa su kuma suna fati (party) to fa indai sakamako zai fito sai sun fika ci.
Jinin Kuyurussa'ayi!
Sarki mai dauwamammen sara na zaune kan wani tsibiri dake can ƙarshen duniya suna shan shayi da masoyiya. Kamar kullum idanunsu na kan wannan fafatawa musamman yadda al'amura sukai zafi.
"Indai dan wannan ne Hidaya baza ta sadaukar da ranta akansa ba." Inji Bihanzin.
Sarkin-sarki tayi tsaki. "Wai kai meye naka ne da wannan Hidaya. Kullum HIDAYA HIDAYA HIDAYA, da ƙafarta ta gudu da tuni na kashe ta. Ni banga wani abu na musamman ba a kanta."
Maimakon Bihanzin ya ɗauki abin wasa sai ya ƙara haɗe rai cikin damuwa ya ce, "wannan yarinyar Hidaya tana sane ta bari ta mutu, har ta mutu ba tayi amfani da Miyurarta ba. Badan komai ba saboda bata so a gane wace ce ita. Bata so a gane meye asalin ta. Tana da fasahohi da dama wanda na daɗe da sani amma bata yi amfani da su ba har ta mutu. Duk ɗan Wilbafos yana da [fasahar-mutuwa], dan me yasa Hidaya ba tayi amfani da ita ba a lokacin da zata mutu? Daɗin-daɗawa a sanda zata mutu taƙi saka Armad cikin jakar tsafinta ko kuma zoben sihiri, hakan na da alaƙa da sirrin [Fasahar-mutuwa]. Tana sane ta mutu. Na rantse da takobin kaka na tana sane ta mutu. Kina tunanin zata mutu a banza. Nayi faɗa da ita nasan yadda take tunani, nasan yadda take lissafi. Eh, naji daɗi data mutu amma akwai abinda ta shirya kuma yana da alaƙa da Armad, yana ƙona min rai idan na tuna ban san meye shirinta taba har yanzu."
Sarkin-sarki ta ja dogon nunfashi sannan ta tashi tsaye ta je ƙarshen tsaunin ta tsaya. Bayan ɗan lokaci tana tunani ta dawo ta zauna ta ce, "za'a iya cewa wataƙila jinin Hidaya na Wilbafos bashi da ƙarfi shi yasa batai amfani da [Fasahar-mutuwa] ba a sanda zata mutu, to amma hakan ba abin yadda bane. Indai ƴar gidan Wilbafos ce to lallai ya kamata tana da ita, sai dai ace taƙi amfani da ita."
Bihanzin yai farat ya ce, "Babban abin kenan da wannan fasaha, baka da zaɓi, indai ka tunkari mutuwa gadan-gadan ƙafarka ɗaya ta taɓa siraɗin barzahu to da kanta take aiwatar da kanta. Idan da Hidaya ƴar Wilbafos ce da da kanta fasahar zata bayyana."
Duk su biyun suka ja dogon numfashi. Bayan ɗan lokaci Sarkin-sarki ta ce, "ƙarshen ƙarya yau zamu ga meye sirrin. Meye abinda Ururu da Taidara da Hidayan suke ɓoyewa akan wannan yaro Armad. Koma meye Tarifil-fakta shi ne wanda ya haddasa, naso na kashe shi sanda na samu dama."
Acan daular Maikironomada sarki Maikiro'Abbas ne zaune kan kujera yana fuskantar Taidara da Fatima da farfesa Zaikid.
"Alƙawarin mu da Hidaya yana nan baku da damuwa a wannan ɓangaren." Inji Maikiro'Abbas. Fuskarsa akwai damuwa akai amma idanunsa akwai nutsuwa wadda ta saɓa da yanayin fuskar tasa. Dogon sagensa ya ƙara yin fari, kansa ya cika da furfura.
Taidara na sanye da tufafin alharini da alkyabba ƙarama. Zaikid da Fatima suna sanye da kayan da suka saba sawa wato ƴar'ciki doguwa mara faɗi. Akwai rawaya-rawaya da ɗori-ɗori akan na fatima wanda ya banban ta ta dana Zaikid. A hannayensu akwai ɗan tulu wanda ke ɗauke da wani sihirtaccen tsimin izza wanda babu wanda yasan meye. Fatima ta ƙarasa ta ajiye masa akan teburin.
Maikiro'Abbas ya ɗauka ya dudduba. Nan take fuskarsa ta cika da farin-ciki amma baice komai ba.
Bayan ɗan lokaci Taidara ya ce, "to mu zamu tafi, amma kayi sani buƙatar mu zata iya zuwa kusa da lokacin da aka tsara. Bihanzin bai gaya maka ba amma akwai matuƙar yiwuwar yaƙin-duniya-na-uku nan da kwana sittin."
Maikiro'Abbas ya ɗaga ido ya dubi Taidara a firgice amma baice komai ba har suka ɓace.
A bakin babban birnin Maikironomada akwai mutun-mutumin Al'yaya guda tara. Kowannensu tsohon sarki ne a garin banda mutun ɗaya. Wannan mutun ɗaya ba wani bane illa Taidara.
Zaikid da Fatima da Taidara suka dira a bakin wannan gari. Komai dake wajen yayi kama da wanda ke bakin garin Khan sai dai banbanci girma da ƙawa da kuma nauyin izza daya cika wajen.
Zaikid ya ɗauki tsimin dake hannunsa ya juye akan mutun-mutumin Zaikid sannan suka juya suka ɓace.
A filin gasa tuni ruhin Armad ya kai kan gaɓa. Ransa na gabda fita. Ana haka sai wani haske ya fara ɓulɓula ya rufe jikin Armad. Hasken fari ne ruwan ƙasa amma kuma yana rufe Armad yana ƙara duhu. A wannan lokaci mutanen duniya masu kallo basu san meye asalin hasken ba: yana kare Armad ne ko kuma wani hari ne daga Ƙaizadu?
Ana haka sai Kaizadu yayi tsalle ya koma baya. Yana barin wajen hasken daya kewaye Armad ya dira a wajen. Tuni yaga dirarsa da fasahar Saɓani daƙiƙa uku kafin ya dira.
"Hmmm... Da gaske kai ɗan Wilbafos ne ba kamar Hidaya ba. Amma kada ka taɓa tunanin zanzo nan ba'a shirye ba, nasan abubuwa akanka wanda kai kanka baka sani ba. Ina nan zanga wanda zai cece ka."
Sannu a hankali hasken ya gama kewaye Armad kafin daga bisani ya ɓace ɓat. Yana ɓacewa Armad ya bayyana dukkan ciwukan jikansa sun ɓace ɓat.
Abu na farko daya fara bayyana ga Armad shi ne hannunsa na hagu wanda da babu shi. A yanzu ya dawo babu ciwo babu tabo babu alamun rauni. Sannu a hankali ya duba izzarsa yaga tana nan yadda ya santa, jikin izzarsa ma yana nan sannan walƙiyarsa da Negrinkinsa suna nan. Kai kace a yanzu ya fito daga gida, babu ko kwarzane a jikinsa. Kai hatta kayan jikinsa sun dawo dai-dai, duk wajenda ya yage ya dawo ya haɗe.
A cikin idanun Armad na dama wani mutun-mutumi ya bayyana a dai-dai wajen da da kwayar idanu ce. Idonsa na hagu ya koma fari fat babu ko kwayar ido.
Wannan shi ne canjin daya bayyana a jikin Armad bayan da ya leƙa lahira ya dawo. Sai dai kuma canje-canjen sun shafi cikin jikinsa da ruhinsa. A tsakiyar tsarin-ruhinsa wani mutun-mutumin Al'yaya ne ya bayyana a ciki.
A dai-dai wannan lokaci aka ji muryar Ƙaizadu yana ceww, "sirrin Alyaya... Kuna tunanin har izuwa wannan lokaci babu wanda zai gano alaƙar gidan wilbafos da Al'yaya? Al'yaya da [Fasahar Mutuwa]? Ni ne Ƙaizadu jikan Kuyurussa'ayi, ni ne na farko da nayi duba izuwa allon dake cikin tsarin ruhi na karanta abinda ke ciki.
"Kàha'abal riyena dalo'aghâr, Káha'abal riyena diney'aghâr !! Idan zan mutu ka tashi sirri na, idan na mutu ka ɓoye sirri na? Haka rubutun yake akan allon dake cikin tsarin ruhi. A duk sanda Wilbafos ya tashi daga mutuwa zai tashi da Al'yaya dazai ninka ƙarfin tsarin-ruhinsa kuma ya warka masa da dukkan abin ƙi. Idan kana tunanin wannan zai baka nasara to..."
Kafin ya rufe baki yaga hasken walƙiya ya gifta ta gefen wuyansa ta hanyar fasahar Saɓani, sabida haka yai sauri ya kauce ɗaya ɓangaren. Amma bisa mamaki kafin ya ƙarasa kaucewa walƙiyar ta karce shi. Ba daban saurin da yayi ba da tuni kan sa yana ƙasa.
Armad ya kalli ɗan'yatsansa wanda ya harba walƙiyar, har yanzu akwai hayaƙi a jiki amma saurin da walƙiyar ta fita da kuma ƙarfinta ya haura tunaninsa shi kansa.
Nan take Ƙaizadu ya gyara tsaiwa ya ƙara shirin yaƙi. Ya shafa wuyansa inda ciwon yake, nan take wajen ya warke.
Armad ya tsaya a inda yake ya buɗa hannunsa yana gayyatar Ƙaizadu.
Ƙaizadu ya ɗaga hannunsa sama Taskar-ruhi ta bayyana, ya kira ɗalasimai taskar ta juye izuwa ƙatotuwar baƙar takobi. Ya ɓace daga inda da wata fssaha kwatankwacin Kaban'shisu ya dira akan Armad da sara. Nan take ya raba Armad gida biyu, jini yayi feshi sama, Armad ya faɗi ƙasa yana shure-shuren mutuwa.
Yana gab da mutuwa ruhinsa ya ƙara kaɗawa, guguwa ta kewayeshi, sannan tsawa ta sakko. Irin hasken ɗazu ya kewaye shi. Nan take jikinsa ya ƙara haɗewa ya dawo dai-dai. Hasken daya kewaye shi ya haɗe guri guda ya shige cikin idonsa na hagu lamarinda ya sa mutun-mutumin Al'yaya ya ƙara bayyana acikin idon suka zama biyu.
A dai-dai wannan lokaci dukkan wani Al'yaya dake daular Maikironimada sai da yayi durƙuso ya kawo gaisuwa banda Al'yaya guda ɗaya; Al'yayan Bihanzin. Hakan yasa wani nauyi ya sauka akan Al'yayan Bihanzin, yai bindiga ya tarwarse. Mai waje yazo, idan baza ka risuna ba ka bar wajen.
Duniya ta tsaya cak tana kallo cikin ruɗani. Zaka iya cewa babu wanda yasan abinda yake faruwa sai ƴan tsiraru irinsu Taidara.
Bayan Armad ya dawo dai-dai ya ƙara miƙewa tsaye ya kirawo Ƙaizadu.
Koda Ƙaizadu ya sare shi sai takobin ruhin ta karye. Rabi yai tsalle sama sannan ɗaya rabin daya cake a jikin Armad ya narke.
Ƙaizadu ya kawo duka da hannu, gabda hannunsa zai daki Armad ya ga abinda zai faru amma yaƙi yadda ya ƙarasa. Ai kuwa yana taɓa Armad hannun ya karye ya lanƙwashe kamar narkakkiyar dalma.
Yai tsalle baya ya kira wasu ɗalasimai wanda suka gyara masa hannun cikin ƴan daƙiƙu kaɗan.
Ya miƙe tsaye ya kalli Armad ya ce, "Al'yaya ko? A lokacin yaƙin rukunai biyu bamu san meye sirrin Al'yaya ba, a haka mukai nasara. Ana tsaka da yaƙi ake gane sirrin abokan gaba domin baza su taɓa bayyana sirrin su kafin ranar ba. A kan haka aka raine mu, akan haka muka taso, a kan haka nazo nan. Nasan kana da Al'yaya tun kafin nazo amma ban san wanne iri bane, nazo da shirin gano sirrin Al'yayan ka na kuma tarwatsa alkadarin sa."
Ya juya gefensa na dama yayi wa wannan fatalwar mai rubutu magana, "Jiu 13, ina abin yake?"
Nan take fatalwar ta miƙa hannu kan iska ta janyo wani abu, tana sauke hannunta sai Armad yaga salka aciki.
Ƙaizadu ya karɓi salkar ya zuba ruwan ciki akan takobinsa. Ruwan fari ne fat garai-garai babu wata alamar cuta acikinsa. Amma yana sauka kan takobin ƙarfen takobin ya koma ja. Sannan hoton wasu mutun-mutumi guda ashirin ya bayyana.
Armad na tsaye a gefe yana kallo bai motsa.
Ƙaizadu ya afka masa da takobin ya sare shi a ka. Maimakon ɗazu da takobin taƙi shiga a wannan karan kan Armad rabewa biyu, kwakwalwar ciki tai feshi waje, gangar jikinsa ta faɗi ƙasa matacce. Dukkan Al'yayan dake cikin kwayar idon Armad guda biyu suka ɗauke, jikinsa ya koma yadda yake kafin Al'yaya su bayyana. Ba hannu ɗaya sannan kuma ga tulin raunika.
A ɓangaren Ƙaizadu kuma zanen mutun-mutumin dake jikin takobinsa guda ashirin ya dawo sha takwas, biyu sun ɓace tare da Al'yayan Armad.
A wannan karan sai da aka shafe rabin sa'a sannan hasken ya dawo jikin Armad ya kewaye shi. Sannu a hankali raunikan jikinsa suka warke, hannunsa ya dawo. Rayuwa ta dawo jikinsa, ya miƙe daga mutuwa. Acikin idonsa na hagu akwai Al'yaya amma guda ɗaya tak.
Tun kafin ya gama haɗewa Ƙaizadu ya ƙara rabashi biyu da takobin sa. Armad ya faɗi ƙasa matacce tare da Al'yayan sa amma shima Ƙaizadu zanen jikin takobin sa ya dawo sha bakwai, ɗaya ya ƙara raguwa.
Bayan tsahon lokaci Armad ya ƙara miƙewa daga mutuwa, Ƙaizadu ya ƙara aika shi. Haka abin yaci gaba, a duk sanda Armad zai farka zaka ga sabon Al'yaya a idanunsa, idan Ƙaizadu ya aika shi lahira sai kaga zanen jikin takobinsa ya ragu. Sai da akai haka sau goma sha biyar sannan Ƙaizadu ya tsaya, ya kalli Armad cikin mamaki da firgici. Ka mutu sau goma sha bakwai amma ka dawo? Babu wani mahaluƙi daya kamata ace yana da wannan baiwa."
Armad yayi murmushi, shi kansa bai gama waye wa da sabuwar fasahar sa ba, ko sunanta bai sani ba. A duk sanda zai mutu zai tsinci kansa a cikin shinge mai duhu. Jiki shi ke fara mutuwa kafin ruhi, a sanda jikin Armad ya mutu a sannan yake bayyana a cikin wannan ɗaki, idan ruhinsa ya mutu daga nan zai tafi lahirar gaske. To amma akwai wani sirri a jikin ruhinsa wanda yake hanashi mutuwa, ya gujewa mutuwa, ya gagari mutuwa. Komin rauni komin wahala sai kaga ruhin sa ya samar da Al'yaya da kansa ya warkar da kansa ya kuma warkar da jikin. Asalin abin daga ruhin ne, kai kace ruhin ya girmi mutuwa ya fita izza. A duk sanda ya dawo Al'yayan daya dawo dashi zai ɗamfaru a idanunsa na hagu, ya ƙara masa ƙarfi ninkin nasa na da.
A jikin takobin Ƙaizadu akwai wani sirri dake cinye Al'yaya, abin mamakin baya aiki akan Armad. Idan an cinye wannan saiya samarda wani. Duk iyakacin ƙoƙarin mutuwa na ta ɗauki ransa amma abin yaci tura. Sai goma sha takwas kenan mutuwa tana kawo farmaki amma ruhin ya gagara. Al'amarin ya wuce ƙaramin zance.
Ƙaizadu yai tsalle gefe ya na haki yana cewa, "babu wani ruhi da yake da damar samarda Al'yaya sama da biyar. Tun da aka halicci duniya da izza, mafi girman abinda aka taɓa gani shi ne Al'yaya uku. Rayuwa uku. Meye sirrin ka, dole akwai abinda kake amfani dashi kana yaudarar idanu na. Bazai yiwu ace kana da rayuwa goma sha takwas ba, Alyaya goma sha takwas wannan ya saɓa da ƙa'idar halitta."
Armad yayi murmushi ya ce, "matsalar mutane kenan tun daga farkon lokaci, indai baza su iya abu ba ko kuma basu taɓa gani ba sai kaji sunce bazai yiwu ba. Da sannu zaka ga yiwuwar hakan akanka. Mai kake nufi da abinda ka faɗa akan Hidaya?"
"Haha... Zancen Hidaya sai dai ka matsa ka ji. Ƙar ya kake, kana nufin baza ka mutu ba kenan?"
"Ka zan mutu ba'a hannunka ba, yaro."
Ƙaizadu ya fusata da jin wannan magana, yai tsalle ya ƙara sara Armad. A haka har sai da zanen dake jikin takobinsa ya ƙare.
Armad ya ƙara tashi daga mutuwa. Zanen dake jikin takobin Ƙaizadu ya ƙare saboda haka bashi da sirrin kashe Al'yaya. Idan ka kwatanta Armad ɗin yanzu da sanda suka fara yaƙi da Ƙaizadu izzarsa da ƙarfin duk wata fasaharsa ya ninku. Yana da Alyaya guda ɗaya acikin tsarin ruhinsa. Shi kuma Ƙaizadu yana nan a yadda yake sai ma gajiya da ya ƙara.
A haka suka rincaɓe da faɗa. Sara suka da duka. A karo na farko Ƙaizadu ya fara amfani da fasahar [Saɓani] yana kaucewa hare-haren Armad saboda karfin da suka ƙara.
Bayan sa'a guda ana kai-komo al'amari ya nuna duk da haka an fi ƙarfin Armad. Zuwa yanzu ya sami munanan raunika guda bakwai shi kuma Ƙaizadu yana da guda ɗaya. Duk da a halin yanzu walƙiyar Armad na iya narka ƙanƙarar Ƙaizadu amma ba ko'ina ba. A wasu lokutan sai ya ɗau mintuna.
Ana cikin haka Ƙaizadu yai amfani da [Saɓani] ya cakewa Armad mashin ƙanƙara a zuci. Armad yai sauri ya koma walƙiya anma kafin yaym gama kayan cikinsa sunyi ƙanƙara. Ƙanƙarar ta shige ruhinsa ta fara daskara shi. Ƙaizadu ya kirawo Negrinkin sa yasa aljanun nan guda biyu suka zuƙe ruhin Armad. A karo na ashirin da biyu Ƙaizadu ya kashe Armad.
Babu ɓata lokaci [fasahar-mutuwa] ta fara aiki. Al'yaya ya ƙara bayyana.
Faɗa ya koma sabo. Aka ƙara komawa tun daga farko har zuwa ƙarshe. Ƙaizadu ya kashe Armad bayan ya sami raunika da dama.
Armad ya ƙara amfani da [Fasahar-mutuwa] ya dawo sabo fil.
A wannan karo Al'yayan Armad ya dawo guda biyu, dukkansu a idon hagu. Badan komai ba sabo da wancan kisa da Ƙaizadu yayi masa na ƙarshe bai kashe Al'yayansa ba. A saboda haka ƙarfin izzar sa da dukkanin fasahohinsa da Negrinkinsa suka ninka kansu sau huɗu maimakon sau biyu.
Dai-dai yake ace Ƙaizadu a yanzu yana faɗa da Armad guda huɗu ne a haɗe waje guda.
Armad ya dunƙule hannu ya saukarwa da Ƙaizadu Hannun-aradu. Al'yaya guda biyu dake cikin idanunsa sukai haske kamar an kunna fitila.
Ƙaizadu ya rufe kansa da ƙanƙara,m sannan yayi tsalle ya koma gefe. Dukkan abinda ke wajen daya bari ya ɓace izuwa duniyar Armad. Nan fa aka fara ƴar zagaye-zagaye, babu yadda Ƙaizadu ya iya, duk da fasahohinsa amma ya kasa tsare kansa daga ƙaruwar ƙarfin Armad. Gashi ya fara gajiya. Babban abin haushin shi ne ya gano sirrin yadda zaiyi yaci galaba akan Armad amma bashi da ƙarfin yin hakan.
Ana haka yai ƙifta ido saboda hayaƙi da toka data rufe masa ido. Dama can abinda Armad yake nema kenan, daya ƙifta ido babu damar yin amfani da [Saɓani].
A ɗan wannan taƙi na ƙiftawar ido anan Armad ya tara dukkan ƙarfinsa waje ɗaya ya saukarwa da Ƙaizadu Negrinkin sa gari guda. Kafin ya buɗe ido an zuƙe shi cikin duniyar.
Armad yai maza ya tura sabbin Al'yayansa guda biyu su tsare masa shi.
Sannan yasa suka miƙo masa Hidaya. Yana buƙatar yasan labarin wannan fasaha tasa da kuma zancen da Ƙaizadu ya fara. Shin hakan yana nufin da gaske bazai mutu ba ko kuma akwai wani sirri a ƙasa? Shin mai yasa Hidaya bata yi amfani da irin wannan fasaha ba kan ta mutu?
Bihanzin yana kwance a inda yake ya linƙaya cikin tunani. Babu wanda yasan mai yake tunani sai sarkin-sarki wadda ke gefensa.
Ta ɓuɗe baki ta ce, "Al'yayansa yana da makasa guda biyu, a haka kake tunani zai iya tsayawa a gaba na ni da bani da makasa, bana mutuwa? Ko kuma kai da kake da dauwamammen sara da fasahar data tsorata Kuyurussa'ayi."
Bihanzin ya amsa da cewa, "darajarsa ta ƙaru a filin daga amma duk da haka bai kai ba. A haka ko Hidaya zata iya halaka shi kafin ta mutu, lallai ina ganin har yanzu bamu gano haƙiƙanin shirin Hidaya ba. Kar ki manta akwai alaƙar su da Maikiro'Abbas. Taidara da Fatima da Zaikid sun kai masa ziyara yau ɗin nan."
A lokaci na farko sarkin-sarki ta ɓata rai. Sama tai duhu, iska ta rusuna mata. Ta miƙe ta kalli sama ta ce, "a kullum kana maganar baka san shirin Hidaya ba, kai tasan shirinka? A duk faɗin duniyar nan waye ya san haƙiƙanin waye kai inba ni ba?! Kana tunanin da fasahar ka da fasaha ta ko Kuyurussa'ayi ne zai sakko akwai abinda zai ɓata mana shiri? Na saka iri a jikin Armad, daga yau har ranar da zamu haɗu duk abinda zaiyi kamar a gaban mu yake."
Bihanzin yai tsalle ya miƙe tsaye cike da mamaki ya ce, "Kin sa iri? Yaushe? Wanne irin iri?"
"Kana tunanin idan umarnin kisa na bawa Elbinuil Randuil tuni Armad baya lahira? Kada fa ka manta yana da jinin Randuil, kuma shi ne ƙani na, ciki ɗaya."
Idanun Bihanzin suka zaƙulo cike da al'ajabi. A karon farko yayi murmushi ya ce, "Rinuil'Abigail Ji-Dandil Yima'Randuil. Shekaru da yawa da naji wannan suna na zata sabon ɗalasimi ne aka ƙirƙiro. Ashe ke ce..."
Kafin ya ƙarasa ta kai masa duka.
Comments
Post a Comment