Skip to main content

BABI NA 148-162: Armad da Uznu

 Babi na 148, 149 &150: Ruhin Armad (1)

***

Armad da Uznu na tsaye suna kallon-kallo. A lokaci guda hankalin sauran mutanen dake filin na kansu. 


Armad ne ya fara magana. "Idan da gaske kasan abinda zai faru mai zai hana ka kashe ni a yanzu? Idan ka kawomin sara kasan wajenda zan kauce kaga sai ka hari wannan waje."


Nan take Uznu ya ƙara murtuke fuska domin yasan wannan magana ba komai bace face izgili. Ya ɗaga takobinsa baƙa-ƙirin ya kawo wa Armad sara daga inda yake tsaye. 


Baƙin hayaƙi ne ya fara fita daga ƙarshen takobin kafin daga bisani hayaƙin ya juye izuwa wuta mai launin baƙi. Wutar ta fara ci tana balbali kafin ta juye izuwa siffar takobi tayi kan Armad. Komai ya faru  ne cikin daƙiƙa ɗaya kacal. Armad na tsaye yana kallon takobin wuta ta yiwo kansa gadan-gadan. Kana gani kasan wannan fasahar tana gaba da fasahar da Uznu yai amfani da ita ya aika Nusi sashin Ikwatora. Ga dukkan alamu bangon duniya yake so ya aika Armad.


Idan ma akwai wanda bai taba ganin fasahar Baƙar-wuta ba to a wannan ya ganta. Shi kansa Armad wannan ne karo na farko daya ganta. 


Masana sunce wannan wuta tana iya ƙona kowanne irin gangar jiki sannan kuma ta ƙona ruhinsa tayadda zai zamo tamkar ba'a taɓa halittar mutun ba. 


Armad yana da zaɓi guda uku. Kodai yai amfani da fasahar Kaban'shisu ya kauce mata ko kuma ya tare da takobinsa ta Wilbafos ko kuma ya tsaya ta same shi tayadda zaiga ko zata iya yiwa jikinsa na walƙiyar wani abu.


Nan take Armad ya yanke shawara. Ya tsaya a inda yake cak bai motsa ba. Meye amfanin gudu idan wutar baza ta iya cutar dashi ba?


Takobin wutar ta sari ƙirjinsa ta wuce. Walƙiyar dake wajen tai tartsatsi tai sama, wajen ya dare gida biyu tayadda idan ka leƙa kana iya ganin abinda ke bayan Armad. Amma duk da haka Armad na tsaye a inda yake bai motsa ba tamkar ganuwa. 


Bayan daƙiƙa biyar ruwan walƙiya ya fara kwaranya daga kwakwalwar Armad yana ɗinke wajen daya yage. Kan kace meye wannan waje ya rufe ruf. Armad yana tsaye a inda yake kamar bango babu wani rauni a jikinsa. Ya dubi Uznu ya ce, "shikenan?"


Armad da gatsali ya faɗa amma abin mamaki Uznu baice komai ba kawai murmushi yake.


"Kayi murmushi yadda kake so..." Armad ya fara magana amma bai ƙarasa ba ya cake. Abin mamaki saiya fara gani dishi-dishi. Sannan a duk sanda ya rufe ido sai yaga Tsarin-ruhinsa naci da wuta. Wutar dai ta fara ne daga ɗan ƙaramin allon dake saƙale cikin Tsarin-ruhinsa kafin ta fara haɗiye sauran abubuwan dake ciki. 


Uznu ya ɗaga hannu sama a wani yanayi na nuna isa da izza yana cewa, "Ita Baƙar-wuta ruhi take ci ba gangar jiki ba. Ko kana da fasahar Sikai baza ka iya kare kanka daga ita ba."


Ɓangarori huɗu na jikin mutun masu tarayya da juna sune RUHI, JIKI, TUNANI da kuma IZZA. 


Sai kuma ɓangarori huɗu na fasaha masu alaƙa da juna: HARI, TSARO, SAURI da kuma YANAYIN-IZZA.


Wannan ɓangarori guda takwas sune duniyar izza. Iyakacin kwarewar ma'aboci izza a kansu iyakacin ɗaukakarsa. 


Kowanne ma'aboci izza ƙoƙari yake yaga ya kware wajen iya kare Izzarsa, da ruhinsa da jikinsa da kuma tunaninsa. Sannan kuma a lokaci guda ƙoƙari yake yaga ya san hare-hare da fasahohi da zasu iya yin aiki akan waɗannan ɓangarori huɗu na jikin mutun. 


Ta hanyar karɓar horon daya kamata mutun zai iya koyon hanyoyin dazai iya kare wannan ɓangarori huɗu (jikinsa da ruhinsa da izzarsa da kuma tunaninsa). Inda lamarin ya banbanta wajen iya hari ne. Da yawan ma'abota izza suna da hari mai aiki akan ɓangaren jiki ne kawai. Hasalima idan kaɗauke wasu ƴan tsirarun ƙabilu babu wanda yake iya amfani da hare-hare masu aiki akan ruhi ko izza ko tunani. 


Wannan dalili ne yasa aka ƙirƙiro Salsa. Zaka samu cewa acikin mutun uku da suka haɗa Salsa kowanne yana da kwarewa akan ɗaya daga wannan ɓangarori huɗu. Idan ka haɗa dana shugaban ƙungiyar kaga an cika kowanne ɓangare. 


Tuni aka bayyana cewa ƙabilar Wilbafos sune masana kan hare-haren izza amma ba'a bayyana wacce ƙabila ce suke da tasiri akan ruhi da kuma tunani ba. 


Ƙabilar Ururu sune masana kan al'amuran ruhi. Hasalima da dama daga cikin hare-harensu suna aiki ne akan ruhi maimakon gangar jiki. 


A wannan lokaci Armad ya gane maike faruwa. Harin Baƙar-wuta yana ƙone ruhinsa maimakon gangar jikinsa. 


Uznu yai dariya sannan ya juya ya dubi macen dake bayansa ya ce, "Yarsaira, kin ga abinda kike so?"


[Kalmar Yarsaira tana nufin masoyiya a yaren Aldurish, saboda haka bawai asalin sunanta bane]


Macen ta gyaɗa kai ta ce, "bashi bane. Ka gayawa yarima dole sai naga Tarifil-fakta zan iya gane abinda ke faruwa. Amma wannan yaron ruhinsa a rabe yake saboda haka wannan bashi ne dukkan ƙarfinsa ba, gwanda ka sare ƙafafunsa da hannayensa da wuri kafin wani tsautsayin yasa ɗaya ɓangaren ruhin ya dawo."


Uznu ya gyalgyale da dariya ya ce, "kinsan ina ɗaya ɓangaren ruhin nasa yake? Yana kame acikin Hajarul-Ururu. Dutsen da ya gagari hatta Amraikugyu. Dutsen da ya gagari Matafiyan-alwashi. Kinsan ko dukkan bil'adama da aljanu da Shishirui zasu taru baza su iya kwato shi daga cikin wannan dutse ba."


Koda jin haka sai macen tai ajiyar zuciya tai murmushi. "Ah, hakane. Indai ba Eyriyon ne zai dawo ba ai ya shiga kenan."


Armad yana jin abinda suke cewa sama-sama. Yana cikin haka jiri ya ɗebeshi ya nufi ƙasa zai faɗi. Amma ya daddagira ya tsaya. Ya ƙara yin ƙasa zai zube akan gwiwowinsa amma a wannan lokaci yaji wata murya acikin kwakwalwarsa tana cewa, "kai sarki ne. Kuma sarki baya durƙusawa. kai sarki ne. Kuma sarki baya durƙusawa."


A zahiri Armad bai san mai muryar take nufi da cewa shi sarki bane amma kawai sai yaji shekarunsa na izza sun kaɗa. Nan take izzarsa ta motsa, yaji a ransa lallai bazai durƙusawa kowa ba. Armad ya cake takobinsa a ƙasa ya hana gwiwowinsa zuwa ƙasa.


Abin mamakin shi ne Armad yana ji lallai ya taɓa jin wannan murya. Amma ya kasa tuna a ina ya santa. Ya nutsa cikin tunani. Can sai ya tuno inda ya taɓa jinta. A lokaci na farko daya fita zai nemowa mahaifiyarsa magani, a lokacinda Babara ya buɗe masa ƙofar Eycigan. A lokacin muryar ta gaya masa ya kula da Ururu. Ya daɗe yana tunanin muryar daga ina take harya gaji ya daina. Kuma tun daga wannan lokaci bai ƙara jinta ba sai a wannan rana.


A wannan lokaci Armad ya kalli zoben dake hannunsa. Ya tuna da cewa mahaifiyarsa da matarsa suna ciki. Idan ya faɗi suma sun faɗi. Idan ya faɗi zai iya rasa su har abada. Nan take Armad yai ƙaraji yai kururuwa. Sararin samaniya ta kaɗa aka fara tsawa da walƙiya. 


Jikinsa na walƙiya ya juye daga kore-kore zuwa jajawur tamkar walƙiyar azaba. A wannan lokaci wannan mutun-mutumi goma dake bayan Armad suka juye izuwa manyan filolin walƙiya jajaye. Kowacce fila ta kafu a bayan Armad sannan suka haɗe da sararin samaniya kamar suna ƙoƙarin haɗe doron ƙasa da sama. 


Waɗannan filoli goma suka zagaye Armad a wani salo na bada kariya. A wannan lokaci iska da tokar da suka ƙone da farko suka ƙara kamawa da wuta suna ƙara ƙonewa. Kamar wannan jar walƙiya tana gaya musu cewa baku ƙone sosai ba. Armad yai kururuwa yai ƙaraji. 


Wannan jar walƙiya tai kan wutar dake ci a cikin ruhinsa. A wani salo mai ban mamaki sai kawai walƙiyar ta hau kan wannan baƙar ta fara ƙona ta. Walƙiya mai ƙona wuta. Kan kace meye wannan walƙiyar ta ƙone wutar zuwa toka. Armad ya girgije ya dawo dai-dai sannan ya fuskanci Uznu Ururu da wani kallo mai ɗauke da raini.


Ana cikin haka wani sadauki daga ɓangaren Uznu yai kururuwa yai kan Armad da sara, amma kafin ya ƙarasa narkakkiyar jar walƙiya ta ɗiso akan takobinsa. Nan take takobin ta juye izuwa toka sannan sadaukin ya narke yabi iska. Nan fa kallo ya koma sama. Ƴan kuci-kubamun ma'abota izza dake filin suka fara guduwa.


Wannan macen dake bayan Uznu ta dubi Armad tai murmushi tana cewa, "ƙarfin dagiya? Kana wahalar da kanka ɗan-uwa. Dama ka haƙura Yarsairi ya kama ka cikin sauƙi. [Yarsairi shi ne kishiyar Yarsaira. Wato kamar namiji da mace] 


"Mijini baya tsufa kuma baya mutuwa. Ko bashi da SIRRIN Ururu da albarkar sarki Kuyurussa'ayi yafi ƙarfinka. Wataƙila da ruhinka yana nan da zaka iya ɗanyin ƙoƙari."


Armad ya fusata ya daki ƙasa da ƙafarsa. Lamarinda yasa walƙiya ta shige ƙarƙashin, tayi tafiya a ƙasa sannan ta ɓullo a dai-dai ƙasan wannan mace. Komai ya faru ne cikin abinda bai wuce rabin daƙiƙa ba. Saboda haka kafin ta ankara walƙiyar ta rufe ta ruf. Amma abin mamakin Uznu ko motsi baiyi ba duk da cewa yaga niyyar Armad kuma yaga abinda zaiyi. 


Macen ta harari walƙiyar da idanuwanta. Abin mamaki sai kawai walƙiƴar ta fara jada baya tana guduwa daga inda take. Kamar tana tsoron taɓa ta. 


Tai dariya tace, "ni ba ruwana da faɗanku, kallo nazo. Amma kai sani cewa a gidan Wilbafos akwai tsari. Iya kusancinka da Aldaima iya ƙarfin jininka, kuma ba'a yadda ƙarami yai amfani da izzarsa akan babba ba. Kayi ƙanƙanta da shekara dubu ɗari kai amfani izzarka akaina."


Uznu ya haɗe gira. Bai taɓa tunanin Armad zai ƙone baƙar wutar ba amma wannan ba wani abu bane tunda ita kanta Baƙar-wuta tana da mataki ɗai-ɗai har bakwai kamar yadda idanuwan Ururu suke. Kuma wadda yai amfani da ita mataki na farko ne kawai. Sannan kuma mafi muhimanci Armad bazai iya taɓa shi ba domin duk harin da Armad zai kawo masa yasan inda zaiyi kuma kafin ma yazo ya kauce masa. 


Armad ya zare takobinsa yai tsalle ya dira kan Uznu. Amma abin mamaki sai Uznu ya kauce hankali a kwance. Ya ƙara kai masa sara amma ya ƙara kaucewa cikin sauƙi. A haka saida Armad yakai sara ashirin a jere amma Uznu yana kaucewa cikin kwanciyar hankali. 


A sara na ashirin da ɗaya bayan Uznu ya kauce saiya kaiwa Armad sara da baƙar takobinsa. Ruhin Armad ya ƙara kamawa da wuta. Armad ya tura walƙiyarsa ta cinye wutar amma abin mamaki sai kawai yaji amai ya taho masa. Nan take aman jini mai kauri baƙi-ƙirin ya futo daga bakinsa. 


Armad ya ƙara kaiwa Uznu sara amma Uznu ya kauce ya ƙara sarar Armad. A haka saida ya sari Armad sau ashirin da bakwai. Duk inda ka duba jinin Armad ne a ƙasa. Da jimawa ya kamata ace Armad yaje ƙasa amma tsananin ƙarfin dagiya da kafiya ta sa yake tsaye. 


Macen nan ta gyaɗa kai cikin mamaki ta ce, "ɗan-uwa daka haƙura mun kama ka da yafi maka sauƙi. Babu wani mahaluƙi dazai iya cin galaba akan #sirrin ururu."


Armad ya miƙe tsaye yana tangaɗi. Sannan ya kirawo wannan filoli goma na walƙiya suka haɗe da jikinsa. Ya tafa hannayensa ya kira wasu ɗalasimai. A lokacin gangar jikinsa ta rabe gida uku. Kowacce ka kalla ta zama Armad. 


Armad uku masu amfani da fasahar Kaban'shisu suka zagaye Uznu Ururu. Kowanne a hannunsa yana riƙe da takobi. A lokaci ɗaya suka kaiwa Uznu sara ta sama ta ƙasa. Uznu yai tsalle sama ya kauce musu. Amma bisa mamaki sai mutun ukun suka ɓace da fasahar Kaban'shísu. Sannan a lokaci guda suka ƙara kaiwa Uznu sara. 


Uznu ya kaucewa na farko. Ya kaucewa na biyun duk da bai ga ta inda ya ɓullo ba, amma na ukun ƴa samu dama ya sari Uznu a kafaɗa. Takobin tai ƙara sannan ta ɓalle gida biyu tai sama kamar an sari dutse. 


Duk da Uznu bai sami rauni ba amma dashi da wannan mace kawai buɗe baki sukai cikin mamaki. Ga dukkan alamu basu taɓa yin tunanin Armad zai gano sirrin fasahar Saɓani ba da wuri haka. 


Armad yai murmushi ya ce, "ya kake zare ido, ai ba wani babban abu bane. Tunda na riga na gano cewa kana iya ganin abinda zai faru da daƙiƙa biyu ne kawai na gama dakai. Mutun-mutumi na uku, na farko zai shirya abinda zai yi maka daƙiƙa biyu masu zuwa. Na biyu zai shirya abinda zai yi daƙiƙa huɗu masu zuwa. Na uku kuma daƙiƙa shida masu zuwa. Kaga zaka ga abinda na farko zai aikata ka kauce masa. Na biyu ma haka amma sai dai kawai kaga na uku. Abin kawai da nake buƙata shi ne fasahar haɗa mutun-mutumi wadda na haɗa da fasahar Sikai sannan da fasahar sauri wadda zata sa mutun-mutumin su ɓace maka. Kuma ina da Kaban'shìsu. Ko kana ganin abinda zai faru baza ka iya nasara akaina ba."


Sannan Armad ya dubi macen ya ce, "kika ce nayi ƙanƙanta da shekara dubu ɗari kafin na yaƙeƙi? Bari kiji, ina mai rantsuwa da mahaliccin izzar ƴar'uwata Hidaya ko Eyriyon ne ya taɓa mahaifiyata ko matata sai na yaƙe shi."


Macen ta haɗe gira tana kallon Armad cikin al'ajabi. Shi kuwa Uznu fara ɓalle maɓallin rigarsa yayi yana cewa, "nayi zaton yaron dana gamu dashi ne shekaru biyu da suka wuce. Amma ka fara girma, a yanzu kaima za'a iya kiranka ma'aboci izza. Amma bari na nuna maka #sirrin Ururu. Bari na nuna maka sirrin da muka halaka Eyriyon dashi" 


Uznu ya cire rigarsa zuwa ƙugu. Sannan ya fara kiran wasu ɗalasimai marasa daɗin ji. Wani ƙatoton gunki mai manya-manyan baƙaƙen idanuwa guda biyu ya bayyana a bayan Uznu. Nan take sararin samaniya ta rabe gida biyu. Rabi yana ɗauke da jar walƙiya rabi kuma baƙin hayaƙi. A wannan lokaci wata waƙa mai kama da ƙasidar baƙaƙen aljanun ta fara tashi.


[SARKI MAI URURU]


[A TUN FARKON URURU]


[A HAR ƘARSHEN URURU]


Abin mamakin shi ne ba'a ganin mai yin wannan waƙar. Da dama mutane ɗaga kansu sama sukai suna tunanin daga sama ake yin waƙar amma abin al'jabi ba daga nan bane. Suka kalli sama suka kalli ƙasa amma duk babu mai waƙar. Can sai suka gane cewa ashe waƙar sune da kansu suke rerata. Abin mamaki shi ne basu da masaniya akan yaushe suka fara reta waƙar kuma basu da masaniya akan yaushe suka iya waƙar. Hasalima basu suke motsa bakinsu ba. Kai koda sunyi ƙoƙarin tsayawa baza su iya ba. Ance duk wanda kakanninsa suka risunawa sarki Kuyurussa'ayi a lokacin yaƙin Rukunan Ururu indai yaga wannan mutun-mutumi saiya rera wannan waƙa. Kuma abin yana bin jini ne, koda kakan kane yabi kaima saika rera.


Ƙololuwar izzar baƙaƙen idanu. Ƙololuwar buwaya irinta sarakunan farko. 


Ana haka sai wasu manyan baƙaƙen idanuwa suka ƙara bayyana a saman Uznu. Ɗaya na kama da wata daren sha takwas, ɗaya kuma na kama da rana lokacin azahar. Wannan mace na ganinsu ta ɗaga hannu ta fara addu'a. Idan da Armad zaiji mai take cewa da yayi mamaki. Domin kuwa nemarwa ruhinsa gafara take idan yaje lahira. 


A wannan lokacin sarki Daljari da Bihanzin suka bawa rundunarsu unarnin su nisanta kansu daga kusa da su Armad koda kuwa hakan na nunfin guduwa daga filin.


Nan take Armad ya tafa hannayensa wasu mutun-mutumin bakwai suka bayyana suka haɗu da ukun farko suka kewaye Uznu. 


Amma a lokacin Armad ya fara ganin baƙi-baƙi, tamkar dukkan duniya ta juye izuwa baƙin hayaƙi. Acikin baƙin hayaƙin akwai wani sanyi mai ratsa jiki. Kamar wasa walƙiyar Armad ta fara yin ƙanƙara. 


Armad yaja da baya yai kururuwa. Ya ɗaga takobinsa sama ya caki tafin hannunsa. Sannan ya shafa jinin daya fito a jikinsa. Sannan ya kewaye kansa da jinin. Haka na faruwa mutun-mutumin Al'yaya ya bayyana a bayan Armad. 


Acan ƙofar garin Khan na Maikironomada Al'yayan Armad ya fara haske yana walƙiya. 


Jikin Armad ya juye daga jar walƙiya zuwa baƙa-ƙirin.


Ƙanƙarar data fara cin jikin Armad ta narke amma kuma zoben dake hannunsa ya fara narkewa saboda tsananin zafin walƙiyar dake kewaye dashi. Dukkan abinda ke cikin zoben ya fara narkewa. 


Kowa ya tsaya cak yana kallon ikon ALLAH. 


A wannan lokaci Armad ya rasa mai zaiyi: idan ya bar walƙiyar, matarsa da mahaifiyarsa zasu iya narkewa, idan kuma ya kashe jikinsa ya ƙanƙare. Ga kuma Uznu a gabansa riƙe da al'amudin Baƙar-wuta.


***

Babi na 151: Armad vs Uznu

***

Armad na tsaka mai wuya, ƙarfin walƙiyarsa ya bashi damar narka ƙanƙarar Sanyin-babban-sihirin Uznu to amma a lokaci guda yana taɓa zoben dake hannunsa. Sai dai kuma fasahar Sikai aba ce mai girma. Nan take Armad ya ɗauke walƙiyar ɗan-yatsan mai ɗauke da zoben inda hannun ya koma dai-dai. Fasahar Sikai ta bashi dama ya juya duk wani ɓangare na jikinsa izuwa walƙiya sannan kuma ya dawo dashi a duk sanda yaga dama. 


Uznu Ururu ya dube shi ya ce, "idan kasan akwai wata fasaha da kake ɓoyewa to ka bayyanata tunda ragowar numfashinka domin daga yanzu lokacin motsa-jiki ya wuce."


Armad ya ɗaga kafada a hasale yana cewa, "har yanzu baka yadda anfi ƙarfinka ba kenan?"


Uznu najin wannan magana ya fusata ya ɗaga ƙatoton al'amudin dake hannunsa na dama da takobin dake hannunsa na hagu ya afka kan Armad. Saboda tsananin saurin da yai tafiya dashi kai kace ɓacewa yayi ya bayyana a gaban Armad. Duk inda Uznu ya gilma sai kaga wajen ya juye izuwa ƙanƙarar Sanyin-babban-sihiri.


Uznu na bayyana ya kawowa Armad sara da takobinsa ta hagu sannan ya kawo masa duka da al'amudin dake hannunsa ta sama. 


Armad ya sa takobinsa ya kare, ko kuma nace yai ƙoƙarin karewa amma kawai sai jin sara yai ya same shi. Tuni Uznu yaga abinda Armad zai aikata saboda haka ya canja hanya. 


Al'amudin ya saukarwa Armad kamar luguden azaba sannan takobin ta sare shi ta hagu. Uznu na tsaye ya rufewa Armad dukkan wata ƙofar tsira. 


Armad na ganin haka ya ƙara samarda mutun-mutumi guda uku. Kowanne mutun-mutumi yana ɗauke da fasahar Sekai da kuma Kaban'shìsu. Suka kewaye Uznu suna zagayashi. Sannan daga bisani suka ɓace suka ƙara aiwatar da fasahar da sukai a sahun farko wadda ta basu dama shatale fasahar Uznu ta Saɓani. 


Mutun-mutumi na farko ya kawo sara, Uznu ya kauce, na biyu ma ya kawo, Uznu ya ƙara kaucewa, na uku ma ya kawo, Unzu ya kauce. Nan take mamaki ya bayyana a fuskar Armad badan komai ba sai dan cewa indai har daƙiƙa biyu ne ratar fasahar Saɓani to ya kamata ace ya sami Uznu koda sau daya. Amma bisa mamaki Uznu ya kauce cikin sauƙi.


Kamar Uznu ya fuskanci halin mamakin da Armad yake ciki saiya nuna wannan baƙaƙen idanu masu kama da wata da rana dake samansa ya ce, "kana tunanin a banza na kirawo waɗannan? A yanzu ina ganin abinda zai faru da daƙiƙa shida kafin ya faru. Kuma kada manta nace zan nuna maka abinda yasa Ururu suka fi ƙarfin kowa a duniya, duba ka gani!"


A wannan lokaci Uznu ya maida takobinsa cikin kufenta sannan ya rataye al'amudinsa a kafaɗa. Ya tafa hannayensa ya kirawo ɗalasimai irin wanda ya kirawo a farko.


Cikin ƙiftawar ido da bismilla idanuwan Ururu suka dulmiye suka ƙara baƙi. Kan kace meye wannan baƙinsu yakai wani mataki wanda zaka iya cewa a da farare ne. Nan take baƙin idanuwan nasa ya fara zuƙe hasken dake filin. Duk da rana na tsakiyar sama, kewayen da Armad da Uznu suke tsaye ya juye izuwa la'asar sakaliya. 


Bayan daƙiƙa goma ya juye izuwa magariba. Bayan daƙiƙa ashirin ya koma isha. Bayan minti ɗaya ya koma duhu dunɗum tayadda ba'a iya ganin komai. 


Kamar hakan bai isa bala'i ba sai duhun-daren ya fara zuƙe takubba da makamai da aka yar a filin yaƙin. Wani irin sirrin sihiri ya fara fita daga cikin idanun Uznu yana shiga cikin duhun yana zuƙe komai da komai. Kan kace meye wannan hatta gawarwakin da suka je ƙas sun fara ɓacewa. Jim kaɗan sai duhun ya fara zuƙo masu rai yana shanyewa. Nanfa aka fara kudu ana ihu. Babu wanda yasan inda zaije idan ya ɓace cikin wannan duhu. 


Bayan kimanin mintuna biyar aka dainajin ihun komai, ko motsi baka ji. Sannan duhun ya fara raguwa haske yana bayyana. 


Armad bai fuskanci abinda ke faruwa ba amma baya son yaga mai zai faru bayan duhun ya ɗauke saboda haka ya tafa hannayensa ya kirawo mafi girman fasaha da ya ɓoye saboda irin wannan rana. 


Fasahar HISABI. 


Takobinsa ta juye izuwa ƙarfe maimakon walƙiya. Sannan wani ratsi-ratsin ja-da-baƙi ya bayyana a jikinta. Armad ya ɓace daga inda yake, sannan bayan rabin daƙiƙa ya ƙara bayyana a dai-dai wajen. A gefe guda babu wanda yaga abinda ya faru sai Uznu domin kuwa koda ƙifta ido kayi baza kaga ɓacewar Armad da bayyanarsa ba. Amma tuni Armad ya aiwatar da fasahar Hisabi. 


A wannan lokaci Armad ya maida takobinsa cikin kufenta ya koma gefe yana kallo. 


Bayan duhun gari ya lafa sai aka iske wani abun mamaki. Wani wawakeken rami ne ya bayyana a tsakiyar filin dagar. Duk wani abu dake kewayen wajen ya ɓace ɓat. Ga dukkan alamu duhun idanun Uznu yana iya zuƙe komai izuwa cikinsa. 


Fili yayi tsit kowa idonsa ya koma kan Armad da Uznu.


Uznu ya dubi Armad irin kallon da akewa gawa. Sannan a daƙiƙa ta gaba wani baƙin haske yai fitar burtu daga cikin idanun Uznu kamar an jefa mashi yai kan Armad. 


A lokacin da baƙin hasken ya fita daga idanun Uznu yana da kauri wanda baifi ɗan-yatsa ba amma yana dosar Armad yana ƙara faɗi da kauri har saida yakai zira'i ɗaya. 


Kewayen hasken ya rikiɗe ya kama da wuta. Sannan wani hayaƙi mai ban al'ajabi ya kewaye hasken. Wata murya mai kama data matattu ta fara tashi daga cikin hasken. Duk da ba'a iya jin abinda muryar take cewa amma kasan masifa take ambato. Yanayin filin yaƙin ya canja, mutane suka fara rawar ɗari. 


Armad yasan bazai iya kaucewa hasken ba domin komai yai Uznu ya sani. Idan ya kauce dama ya sani, idan ya kauce hagu ya sani. Ƙarfin gwiwar Armad kawai yana kan harinsa daya aiwatar na fasahar Hisabi. 


Wannan baƙin haske ya caki Armad, ɗaya ta dama ɗaya ta hagu.


A wannan lokaci Armad yaji kansa ya fara juyawa kamar an dannashi acikin teku. Kan ya ankara ganinsa ya koma dishi-dishi. A dai-dai wannan lokaci Armad ya yanke shawara, inda ya cire zoben dake hannunsa yai cilli dashi sama. Zoben na fita ya buɗe idonsa yaga ganshi a wani tafkeken fili mara iyaka. Tsahon lokaci baya ganin komai sai duhu. Daga bisani saiya fara ganin wasu surori manya-manya wanda girmansu ya wuce duk wani basamude daya taɓa gani. Wannan manyan samudawa su goma ne sannan a kewaye dasu akwai ƙananun halittu masu kama dasu. 


Da farko Armad yayi tunanin haske wajen ya fara yi shi yasa yake ganin wannan halittu amma daga baya ya gane cewa ba haka bane. Dalilin da yasa yake ganinsu shi ne baƙinsu ne ya ninninka na wajen saboda haka idan ka kallesu za kaga kamar sune baƙaƙe wajen kuma fari.


Sai dai kuma abinda ke faruwa a waje ya saɓa da abinda Armad ke gani. Domin bai jima da cilla zoben dake hannunsa ba jikinsa ya ɓace ɓat kamar ba'a taɓa yinsa ba.


Fili yayi tsit babu mai cewa uffan. Armad ya bace babu alamunsa. Kaɗan ne daga wajen suke da ilmi akan maike faruwa.


A dai-dai wannan lokaci Iliyasis wanda basu daɗe da bayyana ba yai tsalle ya cafe zoben da Armad ya cilla.


***

Babi na 152: Shirin Bihanzin 

***

A wannan lokaci Armad ya ƙurawa wannan halittu dake gabansa ido yaga ba wani abu bane illa Dordor. Ya ɗaga takobinsa ya aika musu sara inda jan haske ya fice daga jikin takobin yai kansu. 


Sama da Dordor ɗari suka tare saran amma duk da haka ya ratsa ta cikinsu ya wuce suka faɗi matattu. Cikin rashin tsoro wasu suka ƙara shiga gaban saran suma suka mutu amma wasu suka ƙara shiga. A haka har saida suka zuƙe ƙarfin saran. Armad ya ɗaga takobinsa yana niyyar aika musu da wani saran sai kawai yaga dukkanin halittun da suka mutu a baya sun miƙe. Sannan daɗin daɗawa kowanne ɗaya daga cikinsu ya rabe izuwa gida uku, kowanne ɗaya ya ƙara girma izuwa Dordor. Kan kace meye wannan yawan Dordor da suke gaban Armad sun ninka kansu sau uku.


Armad ya tafa hannayensa ya ce, "HISABI!!"


A dai-dai wannan lokaci Uznu ya goge jikinsa ya maida rigarsa yana nufin barin filin. Macen dake tare dashi ta tambayeshi, "har an gama?"


Ya amsa da cewa, "tunda ya shiga duniyar Kuyurussa'ayi ai kema kinsan ya gama. Ba daban yarima ya ce akai masa shi zai zaƙulo Littafin-takobi daga jikinsa ba da tuni na aikata shi."


Macen tai ajiyar zuciya ta ce, "magadan Wilbafos duk sun zama malalata. Babu wani mai dama-dama acikinsu. Shi wannan ina ganin kamar zai taɓuka amma kaga shima ya halaka da wuri. Ba'a ma yi masa amfani da asalin Fasahar Baƙar-wuta ba. Kash!"


A gefe ɗaya kuwa Bihanzin ne ya dubi sarki Daljari ya ce, "Baba Dalja bari murna karenka ya kama zomo. Bawai da Armad na dogara ba."


Daljari yai murmushi a nutse ya ce, "kai da kana tunanin surukinka zai iya samun nasara akan Ururu ne? Yadda kaga an murƙushe shi kaima haka zanyi maka." Yana rufe baki wasu masu wanda aka yisu da ƙonanniyar ƙasa suka fito daga ƙarƙashin ƙasa sukai kan Bihanzin da mugun nufi.


Bihanzin ya fara kaucewa yana kare wasu da takobinsa, amma abu kamar wasa sai yawansu ya fara ƙaruwa kamar ana ruwan sama. Bihanzin yai tsalle sama ya juya akan iska yana goce musu cikin kwarewa. 


Suna cikin wannan hali suka ji ihu. Suna waiwayawa suka ga macen dake tare da Uznu ta rike shi zai faɗi ƙasa jini na fita daga bakinsa. 


Ta kirawo wasu ɗalasimai ta danna a ƙirjinsa lamarinda yasa ya farfaɗo. Amma duk da haka yana zaune yana haki ya kasa tashi. 


Duk filin anyi tsit babu wanda ya fahimci abinda ke faruwa sai ƴan kaɗan. Daga cikinsu akwai Bihanzin wanda ya dubi Daljari ya ce, "kasan labarin ƙauyen Dare-ɗaya?"


Daljari yai tsaki yaci gaba da aikawa Daljari masu ba tare da ya bashi amsa ba. Amma Bihanzin bai damu ba kawai yaci gaba da bayani. "Mutanen ƙauyen su dubu shida ne da ɗoriya a lokacin da abin ya faru. Ance a dare ɗaya mutun dubu uku suka mutu suna aman jini idanunsu cike da mamaki. Babu wanda yasan dalilin mutuwarsu amma har yau idan kaje ƙauyen gawarwakinsu suna nan basu lalace ba. Idanunsu suna buɗe sunƙi rufewa. Babban abin mamakin shi ne tsananin mamaki da yake cikin idanun wannan gawarwaki wanda zai nuna maka suna mamakin dalilin mutuwarsu. Fasahar data kashe mutan wannan kauye ita ce fasahar Hisabi wadda Armad yai amfani da ita akan Uznu yanzu.


"Nima ban tabbatar ba amma naji ance kabilar wilbafos sun gina fasahar ne akan tsohuwar fasaharsu ta Wasu-wasi. Sai dai a maimakon mutun yaga raunin da akai masa a lokacin a wannan karon alƙawari ake ɗaukarwa ruhinsa a bashi iya adadin kwanakin da suka rage masa a doron ƙasa. Saran takobin zai shiga cikin ruhin ya buya, duk sanda wannan kwanakin suka cika saran zai tarwatsa ruhin. Wannan dalili shi yasa suke ce mata Hisabi wato kamar an yankewa mutun hukuncin ranar dazai mutu."


Daljari yai tsaki ya ce, "to ai wannan fasaha tana amfani ne da yarjejeniya tsakanin ruhi da takobi, kuma kaima kasan ruhin Ururu bazai hallaka ta cikin sauƙi ba. Saboda haka idan ma kana tunanin surukinka ya kwaci kansa ta wannan fasaha to ka daina."


Bihanzin yai dariya ya aikawa da Daljari dauwamammen sara yana cewa, "eh kayi gaskiya Baba. Shi yasa yanzu zan daina ɓata maka lokaci nayi amfani da shirina na gaba."


Bihanzin na faɗar haka ya juya ya kalli sarki Deniz Iluru sannan ya gyaɗa masa kai. Shi kuma Deniz ya dubi Bizaya da sarkin yaƙi Kalhari ya gyaɗa musu kai. 


Haka na faruwa wani abin al'ajabi ya afku. Dukkan mayaƙan sarki Deniz suka ɗaga makamansu suka afkawa rundunar sarki Daljari wanda da suke tare. Sannan Bizaya da Kalhari suka dawo ɓangaren su Hasanu. 


Sarki Deniz ya dawo bayan Bihanzin. 


Nan take aka saka sarki Daljari a tsakiya. Waje yai tsit kowa ya buɗe baki ya ware ido an rasa mai za'a ce saboda tsananin al'ajabi.


Bihanzin yai dariya ya ce, "Baba Dalja, idan kana tunanin ka fara shiri da wuri, toni a tafe na kwana. Zan kashe ka da sauri ba tare da kasha wahala ba saboda darajar marigayiya Hilhusa."


***

~Bangon duniya

~Ƙofar aljanu

***


Hidaya da Taidara da Zaikid na tafe suna hira suka iso ƙofar aljanu inda Ranbirshishirui da Dandirshishirui suke gadi.


Suna ganinsu suka juyo da hankalinsu kansu. Idanun Ranbirshishirui na cike da murna, shi kuwa Dandirshishirui idanunsa cike suke da al'ajabi a yayinda yake kallon izzar Hidaya. 


Ranbir yai tsalle ya dira a gaban Hidaya ya ce, "ina alƙawari na?"


Hidaya ta ɗaga kai ta kalle shi tana girgiza kai ta ce, "baka mantuwa. Ungo." Ta cilla masa wata Farar-laya mai ƙafa-uku. 


Ranbirshishirui ya cafe ya ƙurawa layar ido tsahon daƙiƙu. Har saida Hidaya ta ce, "kana tunanin zan baka jabu ne?"


Ranbir ya girgiza kai cikin risunawa ya ce, "ah haba nina isa. Ina mamakin girman kwarewarki ne kawai a harkar." Amma duk da ya faɗi haka ya ci gaba da kallon layar kamar bai yadda da ita ba. Can bayan ƴan daƙiƙu ya ja dogon numfashi sannan ya fara tsalle yana murna yana gyaɗa kayikansa guda bakwai. Wasu suyi gabas, wasu yamma, wasu gudu, wasu arewa. Hidaya tayi murmushi ta shige gaba tare da su Taidara wanda basu ce uffan ba. 


Sarki Han'ibal da Salsa ɗinsa suna kallon abinda ke faruwa cikin shiri. Kowa acikinsu ya zare takobinsa. 


Han'ibal ya dubi Hidaya ya ce, "Baƙar wuta, ko ke kaɗai na kama yaci ace Ururu sun ɗaga daraja ta zuwa doron ƙasa na farko ballantana kuma ga shugaban masu yiwa Jinzidal da Amri taway.e Taidara Wilbafos." Sannan ya dubi Zaikid a nutse ya ce, "Wannan ɗan tsohon shi kaɗai ne ban sani ba amma shima tunda yana tare dake nasan kansa zaiyi tsada."


Abin mamaki Hidaya kamar bata ga Han'ibal ba ta juya ta dubi Zaikid ta ce, "dattijo kai zaka gyara mana gida ka dafa mana abincin dare."


Zaikid ya zare ido hade da ajiyar zuciya ya ce, "a'a fa, wannan lokaci girkin ki ne. Kin manta kowa yayi saura ke?"


Hidaya ta ɗora ɗan'yatsa a hanci ta karkata kai tana tunani. Bayan ƴan daƙiƙu ta fara magana cikin nutsuwa. "Au hakane fa. Amma ai.. Nifa kasan ban iya girki ba, ƙonewa yake. Kayi na yau da daddare, gobe da safe zan gwada yin shayi."


Zaikid zai ƙara cewa wani abu amma Taidara ya tari numfashinsa ya ce, "kaga ni zanje na duba mayaƙanmu na ƙasashe naga halinda rundunoninmu suke ciki. Ita kuma Heeda zata ɗakko Armad da Fatima ta taho dasu gida. Kaga kai kaɗai ne baka da aikinyi a yau saboda haka girki ya faɗo kanka."


[Heeda shi ne lakaninda Taidara yake gayawa Hidaya]


Taidara ya risuna ya gaisheda Zaikid sannan ya ɗora hannu a kafaɗar Hidaya kafin ya tafa hannu ya ɓace. Ɗaya daga cikin mutun uku dake bayan Han'ibal yai tsalle zaibi Taidara amma Han'ibal yai sauri ya tsayar dashi.


Zaikid ya ja numfashi a hasale sannan ya ce, "to kiyi sauri ki ɗakko jikana da ƴata ku dawo kafin magariba. Babu abinda na tsana sama da na dafa abinci yayi sanyi ba'a ci ba." Yana gamawa shima ya tafa hannu ya ɓace.


Hidaya tai ajiyar zuciya ta juyo ta kalli Ranbirshishirui ta ce, "to Ranbir saina dawo." 


Ranbir ya ɗaga mata hannu yana murmushi.


Hidaya tai ajiyar zuciya, kana ganinta kasan akwai gajiya a tare da ita. A wannan lokaci ta dubi Han'ibal kamar wannan ne lokaci na farko data ganshi a wajan ta ce, "Han'ibal! Mai kake anan?" 


Han'ibal ya buɗe baki zaiyi bayani amma Hidaya ta katse shi taci gaba da magana kamar bata buƙatar amsarsa. "Ah.. Hanani zuwa filin yaƙi kazo yi?"


Han'ibal ya bawa na bayansa umarni a fusace suka kewaye Hidaya. Sannan dashi dasu suka afka mata. Amma abin mamaki ko motsi Hidaya bata yiba. Kafin su ƙarasa kanta suka fara tafa hannu suna kiran dalasimai zasu kira wuta amma abin mamaki sai suka ga komai ya kame. Wuta taki fitowa. Nan take suka tsaya cak suna kallon kallo. 


A lokacin Hidaya ta gyara alkyabbatta sannan ta gyara gashin kanta ya koma baya ta ce, "ah.. sai yanzu kuka gane kenan? Ai na ɗaure aljanunku sama da dakika dari da suka wuce. Idan kuna da wata fasaha wadda bata amfani da aljanu ku fito da ita."


***

Babi na 153&154: Shirin Bihanzin (2)

***

Han'ibal yai yai murmushi a nutse sannan ya doka ƙafarsa a ƙasa lamarinda yasa ƙasa ta fara girgiza. Kan kace meye wannan ƙasar da suke kai ta fara tafasha kamar ana babbakata da wuta. Lallai da gama-garin mutane ne da tuni naman jikinsu ya fara zagwanyewa saboda zafin. Tiriri ya ci gaba da fita daga ƙasa kamar ana tafasa ruwan zafi. Ana cikin haka wata ƙara mai haɗe da rugugin aradu ta tashi kamar ana fasa duwatsu.


Sai da wannan ƙara ta ɗauki sama da daƙiƙa goma kafin ta lafa. 


Abin mamaki tana lafawa saiga wata ƙatuwar laya mai samfurin mutun da zanen ja ta bayyana a hannun Han'ibal. Ya dunƙule hannunsa ya murmushe layar kamar yana murmushe gyaɗa marau. Sannan ya watsar da ɓurɓushin yana duban Hidaya cikin tunƙaho da turo ƙirji.


Hidaya ta numfasa ta ce, "eh lallai da gaske aljaninka shi ne Ifiritu mafi girma dana taɓa gamuwa dashi. SARKI IFIRITU"


Han'ibal yai murmushi ya ce, "Heeda,  koda sama da ƙasa zata haɗe bazan bari kije filin yaƙin nan ba."


Hidaya taja dogon numfashi kamar bata ji abinda yace ba ta ci gaba da magana. "idan zan iya tunawa sunansa NI-MAGME."


Han'ibal najin haka ya haɗe gira yana cewa, "kina magana kamar kin manta, sau nawa yayi ya yage miki aiki?"


Hidaya ta maida takobinta cikin kufenta sannan ta amsa da cewa, "wannan tsohon labari kake, shekarun baya mun haɗu dashi a filin daga. Amma ka manta da wannan, akwai abinda nake so na gaya maka." 


Han'ibal yai ajiyar zuciya ya maida takobinsa yana kallon Hidaya idanu a ware yana jiran mai zata ce.


"ZAN GAYA MAKA SIRRIN DAZAI RIKITA DUNIYA. Bayan kaji abinda zan gaya maka saika yanke shawarar mai zaka yi da kanka. Zaka tare ni ka hanani zuwa filin yakin ko kuwa."


A wannan lokaci Hidaya ta tafa hannunta inda ta saka hijabi ya kewayesu. Duk abinda zata faɗa babu wanda zaiji sai Han'ibal. Sannan ta kwashe duk abinda take so ta gaya masa. Kafin ta gama Han'ibal ya fara nishi yana gumi. Kayan jikinsa sun jiƙe sannan idanunsa sunyi jajawur. Ba shiri saiga sarki Han'ibal ya nemi waje ya zauna yana ƙoƙarin kama numfashinsa. 


Har Hidaya ta juya zata tafi amma Han'ibal ya numfasa ya ce, "da gaske ne abinda kika gayamin?"


Hidaya ta amsa da cewa, "Na taɓa yi maka ƙarya?"


"Baki taɓa ba. Amma banda ke waye yasan wannan magana?"


"Maulana Amraikugyu, Maikiro'Abbas da Tarifil-fakta."


Han'ibal najin sunan Tarifil-fakta ya yamutsa fuska. "Hmmm.. Kina magana kamar kinsan waye Tarifil-fakta."


"NASAN WAYE TARIFIL-FAKTA."


Han'ibal ya zare ido cikin firgici. Bawai kaɗai sanin da Hidaya tayi bane ya tsorata shi, sai yadda take faɗa hankali kwance kuma a nutse kamar ba wani abu.


Hidaya tayi kamar bata ga halin mamaki da Han'ibal yake ciki ba taci gaba da magana. "Kafin Ururu su ƙulle Amraikugyu ya ɓoye wannan sirri acikin wani allon tsafi. Nima bansan yadda akai Bihanzin ya mallaki wannan allo ba. Kuma yasa ƙani na Armad ya fassara masa abinda ke ciki. Kaga kenan banda wannan mutun uku dana lissafa maka akwai karin Bihanzin da ƴaƴansa guda uku da kuma ƙanina Armad. Suma duk sun san wannan sirri.


Han'ibal ya ƙara tambaya, "idan Bihanzin ya sani ta hanyar maulana Amraikugyu dake da Maikiro tayaya kuka sani?"


"Dani da Maikiro'Abbas mun karanta Littafin-takobi."


"Hmmm... Amma mai yasa kike gayamin wannan sirrika wanda zan iya amfani dasu akanki? Ko kin canja shawara akan soyayyata ne?"


Hidaya ta girgiza kai a nutse ta ce, "A'a, ina nan akan batu na. Nayi bincike a duk faɗin duniyar aljanu babu wani aljani da yakai naka hatsabibanci da ƙarfin izza. Aljaninka NI-MAGME SARKI IFIRITU ne. Kuma shi ne mafi girma a dukkan wannan sahu. Sannan kuma dani dakai tare muka koyi haɗa Farar-laya shekaru da dama da suka wuce a wajen Amraikugyu. Duk da baka da ƙoƙari sosai amma kana da naci da dagiya. Idan ka dage zaka iya kamoni a wajen fasahar ɗaure aljanu kaga koda bana nan akwai wanda zai kare duniyar aljanu."


Han'ibal najin haka ya tari numfashinta da sauri ya ce, "Kullum ƙara lalacewa kike, banda jiji dakai yanzu kuma kin ƙaro raina na gaba dake. Shekara nawa na baki amma kina cewa bani da ƙoƙari."


Hidaya ta karkata kai kamar tana mamakin maganar da yayi ta ce, "ba raini bane gaskiya na faɗa. A duk faɗin duniya Yarima Dumaƙìsu ne kaɗai ya fini ƙarfin kwakwalwa. Amma kayi haƙuri na kwatanta kane da kaina shi yasa nace baka da ƙoƙari amma idan na haɗa ka da sauran gama-garin ma'abota izza kaima sarki ne."  


Han'ibal yai ajiyar zuciya sannan ya buɗe baki kamar zai maida raddi amma saiya fasa ya canja magana. "Mai kike nufi da idan bakya nan? Ba dai nufinki kije ki mutu ba ko? Daga nan ina zaki?" Han'ibal na magana sautinsa na nuna kulawa, kana ji kasan akwai sanayya a tsakaninsu. 


"Kada ka damu. Ina tabbatar maka idan son samu nane naci abincin dare da ƙanina a gidanmu. Ina so naga yadda idonsa zaiyi mamaki idan yaga mahaifinmu a karo na farko a rayuwarsa. Ina son naga dimfil ɗinsa idan yana dariya. Amma abu mafi muhimmanci shi ne a fitarda ruhinsa daga cikin Hajarul'Ururu kafin sarki Kuyurussa'ayi ya gane waye shi."


Han'ibal yai ajiyar zuciya ya ce, "Ah... Na tuno fa. Har yau baki gayamin maiya faru da Armad yana shekara uku ba. Kinsan har yau ina so naji."


"Bazan gaya maka ba." 


"Hmm.. Daman nasan haka zaki ce. Amma ina ganin kece wadda Amraikugyu yake zance domin a iya hange na babu wani mahaluƙi dazai iya jada Ururu sama dake. A yau idan kika kira yaƙi a fito a yaƙi Ururu futowa za'ai. Saboda haka kada ki jefa kanki cikin halaka akan ƙaninki nasan yadda kike sonsa amma ki tuna mutanenda suka dogara dake ki ɗan rage son kai."


Hidaya tai shiru tana kallon ƙasa kafin daga baya ta ɗago tace, "ko ni bani da ikon jada Ururu. Armad shi ne wanda zan zuba dukkan jari na akansa. Akansa bazanyi kokwanton saka raina a layi ba." Hidaya ta juya zata tafi amma Han'ibal ya ƙara tsayar da ita.


"Ururu sun san kin san wannan sirri?"


"Waya sani."


"Kibi a hankali kada ki..."


Amma kafin ya ƙarasa Hidaya tayi masa murmushi ta ɓace. Yai ajiyar zuciya ya dubi Salsa dinsa ya ce, "akalar wannan yaki ta canja. Muje filin daga."


***

A can ƙofar garin Khan Hidaya ce ta bayyana a gaban mutun-mutumin dake jere a kofar garin. Wannan mutun-mutumi su ake kira da Al'yaya. 


Tana tsaye a dai-dai saitin Al'yayan Armad tana nazarinsa cikin tsanaki. Abin mamaki shi ne ƙofar garin cike take da ƴan kasuwa masu shige-da-fice dama waɗanda suka zo domin yawon buɗe ido amma babu wanda yake ganin Hidaya. Kai kace wata mashahuriyar aljana ce wadda idanuwa basa iya gani. Idan mutun yayiwo inda take da kansa sai kaga ya canja hanya ba tare da yasan mai yasa ba. 


Can bayan ɗan lokaci ta matsa gaba ta ɗora hannunta akan kafaɗun Al'yayan Armad sannan ta fara angiza masa shekarun izza. Idanuwanta suka kaɗa sukai ruwan ƙasa. Babbar izza ta fara kwaranya daga jininta zuwa cikin Al'yayan. Kan kace meye wannan ya fara haske kamar wata daren sha takwas. 


Mutanen dake wajen suka waiwayo kansa cikin mamaki. Kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa. 


Amma a dai-dai wannan lokaci acikin fadar babban birnin daular Maikironomada wato Sháldin sarki Maikiro'Abbas ne ke zaune a kan karagarsa. Ƴaƴansa guda tara wanda kuma sune manyan kwamandu ma'abota izza a wannan daula suna durƙushe a gabansa. 


Babban nasu ya fara magana kansa a sunkuye. "Naje na tabbatar da kaina, Baƙar Wuta ce."


Koda jin wannan batu sai sarki Maikiro'Abbas ya mike ya ce, "kuje kuci gaba da harkokinku ba ruwanku da ita."


Babban ɗan nasa ya zabura haɗe da ajiyar zuciya ya buɗe baki zaiyi amma ya fasa. Yasan bashi damar tankawa mahaifin nasu amma duk da haka suka ƙi tashi su tafi kamar suna buƙatar ƙarin bayani. Can mai biye masa yai shahada ya ce, "Baba idan muka barta zata tozarta darajar Al'yaya. Komai ƙarfinta ina ganin mu tara mun ishe ta ba saika je ba." 


Maikiro'Abbas yai shiru baice komai ba. Can bayan ƴan daƙiƙu ya dube su ransa a ɓace sannan ya rufe ido. Suna ganin haka kowa acikinsu ya tashi ya ɓace. 


Suna tafiya Maikiro'Abbas ya tafa hannayensa ya ɓace daga kan karagarsa ya bayyana a gefen Hidaya.


Hidaya ta juyo tayi murmushi sannan ba tare da tace komai ba ta juya taci gaba da abinda take. 


Maikiro'Abbas ne ya fara magana. "Shekara goma sha uku tun bayan haɗuwarmu. Ah.. Kina nan dai da rashin maganarki."


Hidaya tai ajiyar zuciya ta ce, "a lokacin kaga sunana ya bayyana acikin waɗanda suka karanta Littafin-takobi ka takura saika ganni."


Maikiro'Abbas ya fashe da dariya yana tuna irin yadda yayi ta neman Hidaya da tura mata wasiƙu amma taƙi yadda su haɗu. A wancan lokaci Abbas yayi ƙoƙarin janyo Hidaya daularsa yayi mata sarkin yaƙi saboda wasu aƙidunsu da suka zo ɗaya amma taƙi. Wani abin mamaki shi ne duk da ƙarfin dariyar Abbas amma babu wanda yake jinta a wajen sai Hidaya. Hasalima babu wanda yake iya ganinsu.


Maikiro'Abbas ya numfasa ya ce, "bansan yaya wannan yaƙi zai wakana ba kuma a zahiri bansan wane ne zaiyi nasara ba. Amma nasan bakya tare da Bihanzin tun bayan abinda ya aikata a yaƙin ɗalasimai. Wai yaya kika ji da akace ƙaninki ya auri ƴarsa?"


Hidaya ta ɓata rai ta ce, "kaima kasan bazan bari ƙanina ya haɗa jini da Bihanzin ba, da da yadda zanyi da tuni na aika shi lahira dashi da tsinannan baƙin hankakansa."


Abbas ya zare ido cikin mamaki ya ce, "Ban taɓa jin kinyi amfani da irin wannan lafazi akan wani ba sai yau. Amma banga laifinki ba duk da kuwa ni ban tsani Bihanzin ba. Mutane da dama suna ɗauka kawai kowanne karabutun ɗalasimai Ururu suka hana Daljari siyarwa basu san ɗalasiman ƙara yawan izza suka hana ba. Kaga ta wannan hanya babu wanda yake da wannan ɗalasimai sai su kaɗai. Kuma su kaɗai zasu rinƙa ƙara izzarsu. To amma mai za kiyi akan wannan yaƙi?"


"ƙani na zan ɗauke da mahaifiya ta. Koma wa yayi nasara bai shafeni ba."


Abbas ya numfasa ya ce, "Amma kuma Daljari ya taimaki gidan Wilbafos a baya. Hasalima ɗalasiman da yake siyarwa wanda Ururu suka hana har abin ya jawo yaƙin ɗalasimai mahaifinki ne ya siyar masa dasu. Kema da hannunki aciki."


Hidaya ta gƴaɗa kafaɗa a hasale ta ce, "nima na taimakeshi a lokacinda babu wanda zai iya taimakonsa. Kasan ɗansa Niyashi ai? Mahaifiyar yaron ƴar ƙabilar Uzzus ce kuma yaron baya tsufa. Ina mai tabbatar maka cewa na kusa mutuwa a karo da dama wajen hana Kuyurussa'ayi gano ta. Kasan komai fa, ka daina nuna kamar baka sani ba."


Abbas yayi murmushi ya ce, "eh hakane, kin biyashi. Amma har yanzu abu ɗaya ne ban sani ba akanki, waishin shekararki nawa a duniya?"


Hidaya ta ɗauke kai tayi kamar bata ji abinda ya ce ba. Lamarinda yasa ya gyalgyale da dariya ya ce, "ah.. na manta fa ba'a tambayar mace shekarunta amma shekarun ƙaninki Armad nawa?"


"Ka tambayi taurari nima ban sani ba."


Maikiro ya numfasa a nutse ya ce, "mai ya kawo ki daulata? Nasan idan kawai zuwa kikai ki bawa Armad izza ta hanyar Al'yayansa zaki iya yi a boye ba tare da na sani ba. Meye hakikanin dalilin zuwanki?"


Koda jin haka sai annurin fuskarta ya dauke. Ta juyo ta fuskance shi tsattsauran kallo ta ce, "akwai abinda nazo rokonka."


***

~Watanni kafin fara yaƙi 

~Daular Sisiya

~Garin Jekis

~Fadar Bihanzin

***


Abinda mutane suka san ya faru a wannan rana shi ne sarki Deniz Iluru yazo nemawa ɗansa Bizaya auren ƴar sarki Bihaninzin. Abinda daga ƙarshe bai yiwuwa ba saboda Zahra taƙi amincewa. Amma a zahiri wannan kawai shiri ne domin a yaudari idon duniya. Hasalima a dai-dai lokacin da Bizaya yake hira da Zahra Bihanzin da Iluru suna sihirtaccen waje suna tattauna yadda zasu yaudari duniya. 


Bihanzin ya zaro ƊALASIMAN ƘURU na duniyar ƙarƙashin ƙasa wanda ya karɓa a wajen Ikenga bayan ya bashi takobin Yùra-shira. 


Idanun Iluru suka kaɗa sukai jajawur. Akan wannan ɗalasimai babu abinda bazai iya yiba a duniya. "Bihanzin baka tunanin idan na karɓi wannan ɗalasimai zan yaudareka a filin daga?"


Bihanzin ya gyaɗa kafaɗa ya ce, "shi cikakken mutun a har kullum sai yayi imani da abinda yasa a gaba idan ba haka ba kuwa bazai taɓa cin nasara ba. Na baka wannan ɗalasimai halak-malak indai ka taimake ni a filin daga a lokacinda nake buƙatar taimako. Kada ka manta ni nafi kowa sanin ƙarfin sarakunan Jinzidal, kuma nasan komai ƙarfina bazan iya jada sarakuna uku ba ni kaɗai."


Iluru ya fashe da dariya ya ce, "Bihanzin kana bani tsoro wataran. A zahiri ƙarfin izzarka ba wani babba bane amma tsananin lissafinka yana da yawa. Sama da shekara ɗari biyu ka sace takobin Yura-shira, mutane suna ta lissafin mai zaka yi da ita amma bakai komai ba kawai ka ajiye ta tana ƙura. Kasan cewa baka isa ka sato ɗalasiman Ƙuru ba saboda haka ka ajiye takobin kasan komai daren-daɗewa ɗan ƙabilar Bayajidda zaizo neman takobin. A lokacin kai kuma sai kayi musayar takobin da ɗalasiman. 


"To amma kasan ɗalasiman kai baza suyi maka amfani ba saboda ba'a ƙarƙashin ƙasa kake ba, saboda haka saika ajiye su domin rana irin ta yau...."


Koda Iluru yazo nan a zancensa saiya cake ya tsaya kawai yana kallon Bihanzin da ido a ware kamar zai fito. Can ya numfasa muryarsa na rawa ya ce, "wato a zahiri kana sane kasa aka saka maka Baƙin-maraya! Kana sane ka tsaya a inda Daljari zai tsince ka!! Kana sane ka...." 


A wannan lokaci Iluru ya kasa ƙarasa maganarsa, jikinsa ya hau tsima. Abu na farko daya gane shi ne kwata-kwata bai san waye Bihanzin ba. Ƙololuwar shiri wanda aka fi shekaru ɗari biyar ana yinsa.


Bihanzin yai dariya ya ce, "Kamar yadda ka gani shekaru na ɗari tara ina wannan shiri, kuma duk da ka sani a yanzu baza ka iya tsayarda shiri na ba. Na riga na kwanto kurar."


Iluru ya tashi ya fice. Yana fita bai zame ko'ina ba sai kurkukun da aka ƙulle Deniz Ururu.


***

~Titin Bayajidda

~Filin yaƙi

***


Yaƙi ya sauya salo. Amma har a wannan lokaci Armad na cikin duniyar kuyurussa'ayi.


***

Babi na 155: Ruhin Armad


***

Bayan ɗan lokaci Hidaya ta gama zuba shekarun izza acikin Al'yayan Armad sannan ta juya a nutse ta kalli sarki Maikiro'Abbas kallo mai cike da ma'ana kafin ta ɓace. 


Bayan ɗan lokaci ta bayyana akan tsibirin Sido-Ururu. Wanda a wannan lokaci babu kowa sai masu gadi. Tun bayan lokacin da Ikenga ya wargaza tsibirin duk ɗaliban dake koyon al'amuran izza akai suka gudu suka koma doron ƙasa na farko. Aciki hadda Suwainah Ururu wadda ta yaudari ruhin Armad tasa aka kamashi acikin dutsen Hajarul-Ururu. 


Hidaya na bayyana ta tashi sama kanta tsaye ta nufi doron ƙasa ta farko. Babu wani mahaluƙi mutun ko aljan dake iya ganinta, kai kace jikinta haske ne kawai. 


Saboda tsananin gudu da take har ƙugi ne ke tashi wanda ke rikita iskar dake kewaye da ita. Bayan ɗan lokaci ta fara hango babban dutsen Hajarul-Ururu wanda ya raba doron ƙasa na farko da ƙasashen ƙasa. A lokacin ta tsaya ta fito da wani ƙatoton allo daga jakar tsafinta sannan ta yanka tafin hannunta na dama ta ɗisa jinin akai. 


Jininta na taɓa allon wani haske ya fara tashi daga jiki. Hasken ya dunƙule ya shige ƙirjinta sannan daga bisani ya fara fitowa yana dawowa jikin allon. Amma a wannan karon ya koma launin ja kamar jini ya gauraya dashi. 


Fuskar Hidaya tai duhu sannan ta taufa da shekara hamsin. Kafin tayi wani abu tayi wani aman jini wanda ke nuna hatta kayan cikinta sun taɓu saboda tsananin ƙarfin fasahar da take amfani da ita. 


Bayan ƴan daƙiƙu sai wannan haske ya fara juyawa da ƙarfin gaske yana kewaya jikina har saida ya haɗa da gajimare. Idanunta suka fara gani dishi-dishi. Sai da aka shafe awa guda hakan na faruwa kafin daga bisani hasken ya tsaya. Abin mamaki bayan komai ya lafa sai ihun yara da maganganu suka cika wajan. Kana ji kasan akwai tsoro aciki. Can sai ƙara taci gaba da tashi kamar ana tashin bom. Sannan kuma guje-guje da tsoro suka cika wajen. 


Hidaya tana tsaye tana kallon komai dake faruwa. Can bayan ɗan lokaci sai  taga an buɗe ƙoɗar dake jikin Hajarul-ururu an fara ɗebe mutanen dake wajen ana tafiya dasu doron ƙasa ta farko. Sannan bayan ɗan lokaci sai wata yarinya ta gabato ana caje ta kafin ta shiga. Duk da ƙarfin izzar masu gadin amma basu ga komai a tare da ita ba amma yarinyar da kanta ta buɗe baki ta gaya musu cewa akwai baƙon ruhi a tare da ita. 


Hidaya na ganin haka ta ɓace daga inda take ta bayyana gefen wannan yarinya. Kafin mai tsaron ƙofar ya duba yarinyar Hidaya tasa hannu ta kama ruhin ta mayar jefa shi cikin jakar tsafinta. Sannan cikin ƙiftawar ido da bismilla ta ɓace. Tana ɓacewa komai a wajen yayi dishi-dishi sannan ya ɓace kamar ma ba'a taɓa yinsa ba. 


Hidaya ta ƙara bayyana a kan dai-dai inda take ada. Ta ƙara yin aman jini sannan gashin kanta yai fari saboda wahala. Ta ɗebo wasu kwayoyi daga jakarta ta jefa a baki sannan ta ɓace. Tana ƙara bayyana ta a bakin garin Khan kusa da Al'yayan Armad. 


Maikiro'Abbas yana tsaye yana kallon Al'yaya kamar wanda yake nazarin wani abu. Hidaya na bayyana ta zaro ruhin Armad ta danna shi acikin Al'yayan lamarinda yasa wajen ya cika da haske. A karo na farko wannan Al'yaya ya motsa lamarinda ya girgiza ƙassai. Hidaya na ganin haka tai ajiyar zuciya cikin farin ciki sannan ta kirawo wasu ɗalasimai ta tofa a jikin Al'yayan lamarinda yasa ya daina motsi sannan hasken dake jikinsa ya ɗauke.


Maikiro'Abbas ya girgiza kai ya ce, "tafiya acikin lokaci abu ne mai matuƙar hatsari da rikitarwa. A dk sanda aka yishi mutun yakan gamu da hatsarurruka masu yawa waɗanda zasu iya tarwatsa ƙashin izzarsa. Hakan nema yasa waɗanda suke gwada wannan fasaha basu fi a irge su da ɗan'yatsa ba a duk faɗin duniya. Amma ke gashi kinyi ta kamar ba komai ba. Lallai har yanzu ban gama sanin iyakacinki ba."


Hidaya najin haka taja dogon numfashi ta girgiza kai ta ce, "shekara biyu kenan ina tara izzar dazan aiwatar da wannan fasaha amma duk da haka saida ta cutar da Tsarin-ruhi na. Badan Armad bane babu wanda zanyi wa."


Hidaya na faɗar haka tai murmushi mai cike da ƙarfin izza sannan ta ɓace. 


***

~Titin Bayajidda

~Filin Yaƙi

***


Armad na tsaye yana fuskantar tsananin duhu na duniyar Kuyurussa'ayi. Yayi duk abinda zaiyi amma babu mafita. Duk da babu lokaci a tare dashi amma yasan cewa yayi awanni yana abu ɗaya. Duk Dordor daya kashe sai yaga goma sun bayyana. A haka sun cika duniyar baka ganin komai saisu. Sannan kuma  duk bayan daƙiƙa ji yake ƙarfinsa yana raguwa kamar ana zuƙe masa izza. 


A filin yaƙin kuwa Bihanzin na tsaye tare da Deniz Iluru sun kewaye sarki Daljari. Tuni yaƙi ya sauya akala. Tsananin tsana da baƙin-ciki sun cika idanun Daljari ya rasa abinda zaice. 


Uznu na gefe a zaune ya gama aman jini. Bai taɓa tunanin Armad yana da fasaha irin Hisabi ba. Fasahar da take haɗa kwantiragi da ruhi mutun ta ƙayyade masa ranakun da zaiyi kafin ya mutu. Badan Uznu tsohon hannu bane da tuni ruhinsa ya tarwatse ya faɗu matacce. Bayan ɗan lokaci wannan mace mai idanuwan Wilbafos tai murmushi ta ce, "ba laifi yana da fasaha iya tasa amma tunda ya riga ya shiga duniyar Kuyurussa'ayi kwanansa ya ƙare."


Uznu ya kalleta ya gyaɗa kai ga dukkan alamu shima yayi amanna babu yadda za'ai Armad ya taɓa fitowa daga cikin wannan duniya. Yai ajiyar zuciya ya miƙe yana cewa, "akwai sauran rikici a wannan yaƙin amma mu mun gama abinda ya kawo mu."


Ya tafi zai fita daga filin fuska a hasale kamar bashi da sauran buƙata a yaƙin. Ita ma macen ta mara masa baya. 


A farkon wannan yaƙi Daljari shike da rinjaye da Uznu da Deniz duk suna bayansa. Amma a yanzu Deniz ya yaudare shi, Uznu kuma ya cimma burinsa na kama Armad ya tafi. Duniya taiwa Daljari duhu. Ya waiwayo bayansa ya dubi Yarima Niyashi da kwamanda Asifu ruwan bala'i da kwamanda Jan-doki ya ce, "Ga dukkan alamu baza a gama yaƙin nan ba sai ɗaya daga cikin sarakunan Jinzidal ya mutu. Daga yanzu na baku dama kowa yai amfani da duk wata izza da fasaha daya tara kada ku rage komai."


Yana rufe baki fuskokinsu suka canja aka ƙara jan tunga za'a ware raini.


Acan gefe guda kuwa wani haskene ruwan ƙasa ya fara tasowa daga sararin samaniya. Da farko hasken ya dunƙule kamar rana amma daga bisani ya buɗe ya fara haɗe ko'ina a sama. Kafin daga bisani ya fara sakkowa ƙasa yana nufo filin wannan yaƙi.


Ko menene wannan haske?


***

Babi na 156: Deniz Ururu

***

A dai-dai wannan lokaci Hidaya na cikin gajimare tana tafka gudu. Abin mamaki a yau tana kan takobinta tsaye tana kallon sama. Kai kace takobin wata tsuntsuwa ce mai fuka-fuki. 


A wannan lokaci babu inda Hidaya ta dosa sai titin Bayajidda, filin yaƙi. 


Babu jimawa ta ƙaraso. Inda ta sakko ƙasa tana ratsa hazo bata zame ko'ina ba sai tsakiyar filin yaƙin. Ta dira a wani ɗan fili wanda ba mutane sosai. Daga inda take zaka iya hango mutane sun ɗaga kansu sama suna kallon wani haske wanda ya ɗunƙule kamar rana. Abin mamaki dukkan yawan mutanen dake filin babu wanda yake iya ganinta hatta sarakunan Jinzidal da Uznu.


Hidaya tayi ajiyar zuciya tana kallon filin yaƙin da mutanen da suke kwance ƙasa matattu da kuma jinin daya rina ƙasa. Acikin idanunta babu fushi babu baƙin ciki. Kai kace duk abinda ke faruwa a wajen bai ishe ta kallo ba. 


A wannan lokaci ta kaɗa alkyabbata inda wani ɗan wadan aljani yawan fuka-fuki ya bayyana a gefenta ɗauke da karagar mulki. Yana bayyana ya saka mata kujerar ta zauna sannan ya sunkui da kai cikin biyayya tamkar bai isa yace ƙala ba. 


"Toh.. Bari naga ɗan ƙaramin ƙanina."


Koda aljanin yaji abinda Hidaya ta faɗa saiya juya kai ya kalli hasken dake sauka daga sama sannan ya kalli Uznu dake tsaye a gefe. Nan take ya gane abinda ke faruwa. Maimakon Hidaya ta shiga faɗan ta zaɓi ta bar Armad ya nuna kansa. Idan taga baxai iya ba saita sa hannu. 


Hasken yaci gaba da sauka kamar buɗewar rana har saida ya dallewa kowa ido. 


Acikin duniyar Kuyurussa'ayi Armad na cikin wani halin sai yaji wani jikinsa ya fara karkarwa. Da farko yayi zaton wata masifar Uznu yake aikowa amma daga bisani sai yaga haske ya fara fita daga goshinsa. Haɗe da wani zazzafan ciwon kai irin wanda bai taɓa ji ba. 


Kafin yai wani abu hasken yai fitar burtu kamar an kefa mashi ya fice daga goshinsa ya keta duniyar gida biyu. 


A dai-dai wannan lokaci Uznu ya duba gefensa yaga wani iskar dake gabansa ta rikice ta wargatse kamar wani abu na neman fitowa daga ciki. Kanya ankara baƙar ƙofa ta bayyana sannan wani haske ya fasa ta cikinta ya fito ya nufi samaniya kamar an jefa mashi. 


Uznu ya zare idanu cikin mamaki a lokacin da yaha hasken ya haɗe da dunƙulallen hasken dake sama.


Sannan wata ƙara da ƙuwwa mai kama da zikirin aljanu ta fara tashi. Sanyin babbar izza ya game filin yaƙi. 


Kowa ya zare idanu yana ƙoƙarin ganin abinda ke shirin afkuwa. Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne hasken da ƙofar da komai suka ɓace ɓat kamar ba'ai ba. 


Kowa ya wangale baki cikin al'ajabi yana na mamakin abinda ke faruwa sun kasa cewa komai. Ana cikin haka sai mutane suka fuskanci wani abu ya canja a filin yaƙin, wani mutun ya bayyana a filin wanda da babu shi. Wani saurayi wanda shekarunsa basu da yawa amma idan ka kalleshi zaka ji yana bada yanayi na dattijantaka da buwaya. Wannan saurayi yana tsaye a ɗan nesa kaɗan da Uznu tayadda su biyun suna tsaye suna kallon juna ido cikin ido. 


A tsakiyar goshin wannan yaro akwai wani tambari wanda aka ɗamfara da wasu rubucu-rubuce na tsohon yaren Wilburish wanda aka manta dashi. A tsakiyar wannan tambari akwai mutun-mutumi riƙe da wani al'amudi. Ga wata takobi mai fuska uku na kewaya mutun-mutumin. 


Wannan saurayi ba wani bane illa Armad Wilbafos.


***

Awa biyu kafin dawowar ruhin Armad, akan wani sihirtaccen tsibiri wanda ke ɗauke da wata ɓoyayyiyar kurkuke dake doron ƙasa na biyu sarki Dul'Ururu wanda akafi sani mafarauci shi ne ke tsaye a bakin wani ɗaki dake ciki can ƙasan kurkukun. 


Babu abinda kake gani acikin kurkukun sai duhu. Amma a haka mafarauci yana tsaye a bakin ɗakin yana yiwa na ciki magana. 


"Deniz Ururu, kada kaji dawai idan ta nine baza mu sake ka ba amma babu yadda zanyi Yarima yace a sake ka."


A dai-dai wannan lokaci zaka iya jin wata kakkausar murya daga cikin ɗaƙin mai kama da ana goga ƙashi da ƙashi. "Hmmm.."


Dul'Ururu yai kamar baiji ba yaci da cewa, "mun yadda dakai amma ka yaudare mu ka ɗauke yaron da ya kamata ka kashe ka tafi dashi."


Muryar ta tari numfashin mafarauci ta ce, "koda ban ɗauke shi ba baza ku iya kashe shi ba a lokacin. Ikenga shi ne jinin Bayajidda mafi ƙarfi. Kuma bana danasanin cetarsa."


Mafarauci ya fusata ya ce, "ɗan aro baya rufe katara. Mahafinka Deniz Yaƙútu shi ne ya aikata laifi mafi girma a tarihi tun bayan Amri. Ya sace mahaifiyarka jinin Ururu ta haka aka haifeka da idanuwan Ururu duk kuwa da cewa kaiba jinin Ururu bane. Tun a lokacin da anbi ta tawa da tuni mun kashe ka amma waziri ya hana."


Muryar ta ƙara fusata ta ce, "to mai zai hana ka gwada kashe ni yanzu?"


Mafarauci yai shiru yana kallon cikin kurkukun kamar zaice wani abu amma ya fasa sai kawai ya jefa mukullin kurkukun cikin ya juya ya fice a fusace. Ga dukkan alamu baya tare da hukuncin da yarima ya yanke na sakin Deniz Ururu. 

***


A filin yaƙi kuwa wani abin mamaki ne yake ƙara faruwa. Babu wanda yasan meye dalili amma sarki ya janye dukkan sadaukansa daga filin yaƙin tun daga kan wazirinsa Dandil da manyan kwamandu wanda ake kira da Tagwayen-auni har zuwa kan sadaukai masu ƙaramar izza. Lamarinda ya ƙara rikita filin yaƙin. 


Waje yai shiru kamar mutuwa ta gifta.


Sai dai kuma kash, abin mamaki bai ƙare ba. Ana cikin haka wani basamuden mutun ya bayyanawanda saboda tsabagen girmansa ba'a ganin kansa. Tafin hannunsa kaɗai kamar tsauni yake. Idan ka ɗaga ido abinda kawai zaka iya gani shi ne baƙaƙen idanuwa guda biyu wanda ke haske suna walƙiya tamkar dunƙulen wuta. Wannan ba wani bane illa Deniz Ururu. 


Wannan mutun na bayyana ya dubi Deniz Iluru yayi masa magana da wani wanda ba wanda ya gane. Abin mamaki sai kawai Deniz Iluru ya ɗurƙusa ƙasa yai mubaya'a ga wannan basamude. 


A wannan lokaci basamuden ya kece da dariya da wata murya kamar ana feshin wuta. Bayan ɗan lokaci ya ƙara yiwa Deniz Iluru magana da irin wannan yare. Lamarinda yasa take Deniz Iluru ya bada umarnin duk wani badenize ya haɗa kayansa su bar filin yaƙin. 


Ana cikin haka sai Ikenga da muƙarrabansa suka bayyana a gaban wannan basamude. Dukkansu suka zube ƙasa sukai gaisuwa. Ikenga bai taɓa tunanin zaiga Deniz Ururu a wannan waje ba kuma abinda ya kawoshi kallo ne kawai. Basamuden ya dubi Ikenga kallo mai cike da yadda da jinjina irin kallonda uba yake wa ɗansa. 


Kafin kace meye wannan sama da rabin mutanen dake filin sun daɗe sun koma bayan wannan basamude.


Ana cikin haka Bihanzin ya zare takobinsa ya ce, "kai Deniz Ururu, munyi alƙawari da yaron ka Iluru akan wannan yaƙi, idan baza ku shiga to sai dai ku ajiye ɗalasimin Ƙuru dana baku."


Koda jin haka sai wannan basamude ya juyo ya dubi Bihanzin ya fara magana da yaren Aldurish yana cewa, "ƘARFI SAI MAISHI. KOMAI NA DUNIYA NA MAI ƘARFI NE, IDAN KANA DA ƘARFI KA ƘWATA."


Abin mamaki ko tsayawa baiyi ba kawai ya juya suka nufi hanyar fita daga filin dashi da jama'arsa. 


Kan kace meye wannan sarakunan Jinzidal biyu ne kacal suka rage a filin. Bihanzin da Daljari. 


A gefe guda kuma ga Armad da Uznu. Sai kuma sarauniya Baƙar-wuta na zaune tana kallo. 


***

Babi na 157&8: Miyurar Armad

***

Filin yaƙi yayi tsit kamar mutuwa ta gifta. Abu na farko bayyanar Armad wanda ya yaga duniyar Kuyurussa'ayi ya keto waje. Ga wani haske mai ɗaukan hankali dake fita daga tambarin dake goshinsa. Idanunsa na cike da wani kallo mai ratsa jiki. Kana gani kasan wannan sabon Armad ne ba irin na da ba. Yana tsaye yana kallon Uznu Ururu ido cikin ido. Shima Uznu Ururu yana kallonsa. 


A gefe guda kuma ga ga rundunar sarki Daljari data Bihanzin na tsaye ana kallon-kallo. Yarima Niyashi, Asifu da Jan-doki na tsaye a bayan sarki Daljari suna kallon abokan karawarsu dake bayan Bihanzin wanda suka haɗa da yarima Hasanu da Kiru da kuma kwamanda Damjinu da Naƙata.


A duk cikinsu zaka iya cewa babu wanda yake cikin ɗimuwa kamar Bihanzin domin kuwa a tsaye yake bakinsa a buɗe yana kallon sama da rabin rundunarsa sunbi bayan Deniz Ururu. Sannan kuma ga maganar izgili da Deniz Ururu ya gaya masa. "Ƙarfi sai mai shi, komai na duniya na mai ƙarfine, idan kana da ƙarfi ka ƙwata."


Bihanzin na tsaye yana kai-komo da abubuwan acikin ransa. Har yanzu shirinsa yana kan hanya to amma akwai cikas aciki. Bai taɓa tsammanin bayyanar Deniz Ururu ba. 


Nan take ya lissafa mayaƙansa yaga tuni sama da kaso ɗaya cikin uku sunje ƙas, kodai sun riga sun halaka ko kuma suna da rauni. Ya ciji harshe ya kalli takobinsa yana lissafin wacce hanya zai ɓullowa abubuwan. 


A gefe guda shima Armad nazari yake. Dawowar ɓarin ruhinsa abu ne daya bashi matuƙar mamaki domin yasan dole da saka hannun wani aciki. To amma wa? Yayarsa Hidaya? Kakansa Zaikid? Abul Babara? Nusi? Sunaye da dama suka bujuro kansa. 


Tunda ruhinsa ya dawo ilmin duk abubuwan da suka faru da ruhin ya shiga kwakwalwarsa kamar yana wajen suka faru. Ya ga yadda ya tsinci kansa a tsibirin Sido-Ururu. Da yadda suka haɗu da Suwainah Ururu da yadda ya taimaka mata amma a ƙarshe ta yaudare shi tasa aka ƙulleshi cikin dutsen Hajarul-Ururu. 


Koda yazo nan a tunaninsa saiya tuna abin daya gani a lokacinda yake cikin dutsen. Abin mamaki irin yanayi ɗaya ne sak da abinda ya gani acikin duniyar Kuyurussa'ayi wadda Uznu ya ƙulleshi. Banbancin kawai shi ne duniyar cikin dutsen Hajarul-ururu ta ninka wadda Uznu ya sashi sau dubu ɗari. Amma da yanayin launin duniyar da halittun ciki masu rabi kama da aljanu rabi kama da dordor duk iri ɗaya ne sak. 


A wannan lokaci abu ɗaya ne kaɗai ya faɗo wa Armad zuciya. Wato SIRRIN DAZAI RIKITA DUNIYA. Sirrin da yaji a lokacin haɗuwarsa ta farko Nostaljiya. 


Armad yai ajiyar zuciya ya ɗaga kai sama ya kalli Bihanzin. Har yau bai gayawa kowa wannan sirri ba amma a har kullum abin yana damunsa. Sannan kuma ya kasa gane manufar Bihanzin ta ɓoye wannan sirri. 


Abubuwa da dama sun faru wanda kuma Armad yana ganin duk suna da alaƙa da wannan sirri. Saboda haka Armad ya yanke shawara ana kammala wannan yaƙi zai samu Bihanzin ya tambayeshi akai. To amma a halin yanzu abu mafi muhimmanci shi ne yaƙin dake gabansa. 


Wannan yaƙi ne wanda kusan ta dalilin Armad aka fara shi. Tun farko dai Uznu Ururu shi ne wanda ya sa aka siyarda Armad a matsayin bawa bayan ya gama gana masa azaba. A sakamakon haka Nostaljiya ta bugi ƙirji ta manta da matsayinta da komai a duniya ta ceto shi. Kasancewar hakan sauran sarakunan Jinzidal wanda daman suna da ƙullalliya tsakaninsu da mahaifinta sukai amfani da wannan dama wajen haɗa kai domin su tarwatsa shi. 


A ƙa'ida yaƙin bazai afku ba idan da Nostaljiya ta amsa cewa Armad ne ya tursasa mata yasa ta kawo hargitsi a yayin cinikin bayin. To amma taƙi. Wanda hakan yasa laifin ya dawo kanta, dama kuma ƙiris sauran sarakunan suke jira. 


Armad ya dubi Uznu da wani irin kallo mai cike da tsana. Komai ya fara dashi. Da ace Uznu bai siyar dashi ba a matsayin bawa ba da duk haka bata faru ba. Hasalima da Uznu baizo ya ƙara sace Nostaljiya a garin Jekis ba da abubuwan basu ƙara lalacewa ba. Lallai Uznu ya cancanci fushin Armad. 


Nan take zuciyar Armad ta fara tafasa. Amma abu na farko daya fara yi shi ne amfani da fasahar yanayin-izza ya nemo inda zobensa yake. Nan take ya waiwaya baya inda ya tararda Iliyasis da Cokali da Inara haɗe da wasu mutun goma sun nufo inda yake. Suna ƙarasowa ya gane cewa wannan sune mutun goma na farko wanda suka karɓi fasaharsa ta kwangila daga matarsa Nostaljiya.


Armad ya buɗe baki zaiyi magana amma kan yace wani abu Iliyasis ya shige gaba ya miƙa masa zoben. 


Abin mamaki a dai-dai wannan lokaci sai zoben ya fara haske. Da Armad da Iliyasis duk suka buɗe baki cikin mamaki domin duk basu da masaniyar abinda ke faruwa. 


Ana haka sai ƴar ƙaramar ƙofa ta buɗe a saman zoben. Nan take Armad ya gane maike faruwa domin kuwa duk duniya babu wanda ya isa ya buɗe wannan zobe daga shi sai Nostaljiya. Kafin yace wani abu farin haske ya fito daga ciki wanda ya juye izuwa Nostaljiya. Fuskarta da fatar ta cike da ƙoshin lafiya. Kana gani kasan ta farfaɗo. Kuma a yadda take bata ƙi ta afka cikin wannan yaƙi ba domin kuwa hadda takobi a kafaɗarta. 


Bayan ta fito sai ƙofar zoben ta fara rufewa, amma a lokacin wani abun mamaki ya afku wanda ba wanda ya lura a kaf filin sai Bihanzin. Hidaya ta ɓace daga inda take ta shige cikin zoben sannan cikin ƙiftawar ido kafin ƙofar ta rufe ta fito daga ciki ta koma inda take kan karagarta. A hannunta tana riƙe da mahaifiyarsu wato Fatima. Shi kansa Bihanzin sai a lokacin ya fuskanci ƙarasowar Baƙar wuta filin. 


Har yanzu Armad baiga Hidaya ba. Hankalinsa na kan matarsa ya haɗe gira cikin mamaki yana kallonta gefe-da-gefe. 


Nostaljiya ta karkata kai ta mayar masa da kallo irin na miji da mata sannan ta turo baki ta shige gaba tana cewa, "kaje ka huta na karɓeka."


Armad yai ajiyar zuciya sannan ya bita da kallo cikin mamaki kamar yadda su Iliyasis suma suke kallon ikon ALLAH.


Bayan daƙiƙa ɗaya Armad yai ajiyar zuciya ya janyo hannunta yana cewa, "wai mai zakiyi? Kinga wajen yaƙi ba wajen kyawawa bane. Kawai ki koma ciki kiyi bacci."


Nostaljiya ta juyo tana kallon fuskar Armad gefe da gefe kamar a ranar ta taɓa ganinsa har saida Armad ya fara jin kunya saboda irin kallon da take masa. A lokacin ta buɗe baki tace, "idan wajen yaƙi ba wajen kyawawa bane mai kake anan?"


Armad ya buɗe baki zaice wani abu amma ya rasa mai zaice. Da kyar bayan ya ɗau lokaci yana lallashi ya samu ya shawo kanta ta fasa shiga yaƙin akan yarjejeniyar cewa baza ta shiga ba amma babu inda zata je tana bayansa a tsaye. Armad yai ajiyar zuciya ya girgiza kai babu yadda zaiyi. Ada yana yaƙi babu ruwansa da wanda ke kusa ko nesa amma yanzu dole ya kiyaye kada wani abu ya same ta. Bayan ɗan lokaci ya shige gaba izuwa Uznu. 


A gefe guda Hidaya ce take nazarin Nostaljiya da wani irin haske a idanunta mai ban mamaki. 


***

Armad ya wuce Nostaljiya ya nufi Uznu gadan-gadan a wani yanayi mai cike da isa da iko. Nan take tambarin Miyurar dake goshinsa ya fara haske. Tun bayan sanda Miyurar Armad ta ɓace Armad bai taɓa jin dai-dai ba sai wannan rana. Duk wata gajiya da wani tsoro da rashin tabbas ya kau daga idanunsa. Ɓarin jikinsa ɗaya na ɗauke da izza dubu ta musamman, ɗaya kuma na ɗauke tambarin Miyura. Tambarin da yake iya ƙara ƙarfin izza a kowanne. A da can farkon fitowar Armad daga gida a lokacinda ya fafata da mai tsaron ƙofa Han'Diyuza, Armad yayi amfani da tambarin ya ƙara yawan izzarsa daga hamsin da ɗaya zuwa ɗari da huɗu. A lokacin iyakarsa kenan domin iya abinda jikinsa zai iya ɗauka kenan.


To amma a yanzu abin ba haka bane. A yanzu Armad yana da jikin walƙiya wanda bazai taba mutuwa ba. Komai yadda ya tarwatse ya rududduge zai ƙara haɗewa ya koma yadda yake. Saboda haka shi kansa Armad bai san iyakacin izzar dazai iya zuƙa daga cikin wannan tambari ba. Abu ɗaya daya sani shi ne a yau saiya hukunta Uznu Ururu. 


Miyurar na fara haske izzar Armad ta fara yin sama. Daga 1000 zuwa 1100 zuwa 1200 zuwa 1300..... 


Kafin ya ƙarasa takai shekaru 2400. A lokacin Armad ya tafa hannayensa ya kirawo wasu ɗalasimai. Lamarinda yasa sama tayi duhu. Sannan cikin ƙasaita Armad  ya ce, "Aradu!"


Yana rufe baki dunƙulen walƙiya ya bayyana a sararin samaniya wanda girmansa yakai girman dutsen dala. Sannan a wani yanayi mai ban mamaki ta fara sakkowa cikin rugugi ya dosa filin yaƙin. 


Idan da shikenan da da sauƙi, to amma a wannan lokaci wani dunƙulen na biyu ya bayyana. Sai na uku dana huɗu. Kan kace meye wannan sama da dunƙule dubu sun biyo baya. Suna sakkowa suna ƙara yawa sannan kuma suna haɗewa izuwa siffar wani basamuden Hannun-aradu. 


Amma duk da haka Armad bau gama ba. A lokacin ya ƙara tafa hannayensa ya kirawo ɗaƙasimai sannan ya ce, "Wilbafos!"


Idanunsa suka juye izuwa ruwan ƙasa. Idanun gidan Wilbafos. Armad ya ɗora idanunsa a kan walƙiyar daie sakkowa lamarinda yasa wani haske ya fice daga cikin idanun ya shige jikin walƙiyar inda wasu layi-layi ruwan ƙasa suka bayyana a jiki. Duk wanda ya rayu a wannan zamani yasan mai Armad yake niyyar yi. 


FASAHAR LINZAMI!


Gidan Ururu suna da fasahar Saɓani wadda ta basu damar ganin abinda zai faru kafin ya faru. Su kuma gidan Wilbafos suna da fasahar Linzami. 


Kan kace meye wannan Hannun-aradun ya sakko dai-dai ƙasan duniya. Inda ya shafe ko'ina ba'a iya ganin komai saboda tsananin girmansa. A kewaye da walƙiyar akwai manyan layika ruwan ƙasa sun zagaye. 


A wannan lokaci Hannun-aradun ya fara dunƙulewa yana motsewa izuwa ƙaramar ƙawanya. Idan ka kalla sosai zaka ga wannan layika ruwan ƙasa sune suke matse walƙiyar suna ƙara dunƙule ta waje ɗaya. Cikin ƙaramin lokaci duk girman walƙiyar ta dawo ƴar ƙaramar ƙawanya wadda bata fi girman mutun ba. 


Saboda tsananin yawan walƙiyar da aka matse a waje ɗaya wani irin rugugi ne ke tashi mai firgitarwa. Duk wani abu daya kusanci wajen narkewa yake. Kai kace wannan ƙawanta ita kaɗai zata iya halaka dukkan duniya. 


Amma duk da haka Armad bai gamsu ba. Nan take ya ƙara ɗaga hannunsa sama ya ce, "Walƙiya!"


Yana rufe baki ruwan walƙiya ya fara zuba daga sama yana shigewa cikin ƙawanyar yana ƙara mata ƙarfi. Nan take launin walƙiyar ya juye izuwa baƙi-ƙirin. Baka ganin komai sai baƙin walƙiya da hayaƙi. Sai kuma huci da rugugi. 


Armad ya ɗaga ɗanyatsansa yai nuni da Uznu. Nan take ƙawanyar ta yiwo kansa gadan-gadan kamar Armad yana sarrafa ta da "linzami". 


Uznu na ganin haka fuskarsa ta canja. Maimakon yai ƙoƙarin kauce mata da fasahar saɓani sai ya fara tafa hannaye yana kiran wasu baƙaƙen ɗalasimai. "SAMMAI! NEGRINKI!!"


Sannan cikin zafin nama ya danna hannayensa acikin ƙirjinsa. Nan take wani jan hayaƙi ya fara futowa daga cikin shekarun izzarsa. Kafin ƙawanyar walƙiyar ta cimmasa jan hasken ya dunƙule izuwa ƙatoton al'amudi na haske. Uznu ya riƙe al'amudin yana jiran isowar ƙawanyar walƙiyar.


Uznu yasan cewa zai iya amfani da fasahar hisabi yaga ta inda harin zaizo ya kauce masa to amma saboda fasahar Linzami yin haka bazai haifarda ɗa mai ido ba. Ta hanyar wannan fasaha zuri'ar wilbafos suna iya samarda makami mai linzami wanda yake bin izzar abokin gaba. Misali yanzu Armad yayi amfani da wannan fasaha ya haɗa ƙawanyar walƙiyarsa da izzar Uznu Ururu. Indai wannan ƙawanya bata haɗu da izzar Uznu Ururu ba to baza ta taɓa rushewa ba. Wato dai kamar makami mai linzami.


A dai-dai wannan lokaci ƙawanyar Armad ta haɗu da al'amudin Uznu Ururu.


***

Babi na 159: Negrinki

***

A lokacinda wannan jan haske na hannun Uznu ya juye izuwa al'amudi ya haɗu da ƙawanyar Armad wani rugugi mai girgiza duniya ya tashi. Tsananin ƙarfin harin guda biyu yasa ƙasa ta fara tsagewa, sama tai duhu. Al'ummar dake filin kowa yaja baya. Ƙarfin harin yai cilli da Armad da Uznu baya. Sannan bayan sun tsaya jini yai ambaliya daga bakinsu duk su biyun.


Bayan komai ya lafa, ƙawanyar Armad ta ɓace amma al'amudin Uznu na nan a hannunsa babu abinda ya same shi. Kana gani kasan wannan al'amudi na musamman ne. Abin mamaki sai kawai al'amudin ya fara haɗe jikinsa yana komawa na jan ƙarfe maimakon na haske. Kana gani kasan ƙara ƙarfi yake.  


Duk da wannan ne karo na farko da Armad ya fara yin arba da wannan fasaha a filin yaƙi yasanta. Hasken da Uznu Ururu ya zuƙo acikin ƙirjinsa shi ake kira da NEGRINKI. Armad ya taɓa ganin Negrinki acikin ɗan-itacen Mangwaron-Negrinki da Nusi ta bashi a farkon haɗuwarsu. Bayan wannan lokaci yayi ƙoƙarin siyan ɗan itacen ya shuka amma ya gano cewa akwai wani sirri aciki. Tayadda babu wanda zai iya samarda wannan ɗan itace sai ma'abota izza da ake cewa SAMMAI. 


SAMMAI sune a saman JEMAI kuma sune a saman ƘASSAI. 


Armad yasan a lokacin matakin izzarsa bai wuce matakin ƙassai ba saboda haka yayi niyyar amfani da Miyurarsa ya gina Negrinkinsa amma kafin ya fara ruhinsa ya ɓace. A dole ya cire tunanin shuka mangwaron-negrinki daga cikin ransa a lokacin.


Amma a bincikensa ya gano cewa Matakin Ƙassai da Jemai mataki ne wanda ma'aboci izza yake amfani da yawan izzarsa wajen ƙarfafa harinsa. Abu ne sananne ƙawanyar walƙiyarda aka ƙirƙira da izza biyu ta ninka wadda aka ƙirƙira da izza ɗaya ƙarfi. Haka ma wadda aka sakawa izza goma ta ninka wadda aka sakawa izza biyar. Wannan dalili ne yasa iya yawan izzar mutun iyakacin ƙarfin harinsa. 


To amma wannan ilmi ya taƙaita ne kawai ga matakin Ƙassai da Jemai. Matakin Sammai wani mataki ne na musamman wanda baya amfani da waccan ƙa'ida. Maimakon amfani da yawan shekaru yana amfani da sinadarin da yake cikin wannan shekaru wanda ake kira da NEGRINKI. 


A zahiri Negrinki shi ne asalin sinadarin dake cikin izza. Asalinsa launin baƙin hayaƙi ne dashi to amma kowanne ɗan'adam yakan iya canjawa nasa launi kamar yadda Uznu ya maida nasa ja. 


Babu wanda yasan iyakacin adadin Negrinkin dake cikin kowacce shekara ta izza. Abu ɗaya da aka sani shi ne iya yawan sinadarin iya ƙarfin izzar mutun. Ta haka aka ce yawan shekaru basu ne ƙarfi ba. Zaka iya samun mai izza dubu yafi mai izza dubu da ɗari biyar ƙarfi. Duk ya ta'allaƙa da Negrinki. 


Banbancin Sammai da sauran ma'abota izza shi ne suna iya zuƙo sinadarin Negrinki suyi amfani dashi wajen hare-harensu. Kamar yadda mai gwangwani-ɗaya zai gamsarda miya amma gyaɗa buhu ɗaya baza ta iya ba, haka banbancin yake. Ka ɗauka duk gyaɗa ɗaya izza ce, kuma man dake ciki shi ne Negrinki. Komai yawan gƴaɗar da zaka zuba a miya baza kaga mai ba. Amma kana matse gyaɗar zaka ga mai.


Ta haka ne zaka ga wanda yakai matakin Sammai yana samarda mahaukatan hare-hare wanda hankali bazai ɗauka ba saboda suna amfani da Negrinki ne maimakon izza. 


Kuma idan Sammai suka riƙa sukan iya zuƙo wannan sinadari suyi makami dashi. Makami mai firgici. Kamar yadda Uznu ya zuƙo Negrinkinsa yai al'amudi dashi. Badan haka ba da tuni ƙawanyar Armad ta mai dashi toka.


Duk da Armad yasan nanda lokaci kaɗan zai samarda tasa Negrinkin amma a halin yanzu buƙatarsa ya samu nasara akan ma'aboci Sammai duk da kuwa yana matakin Jemai. Abin mamaki Armad yana da yaƙinin zai samu nasara akan Uznu. 


Nan take Armad ya ci gaba da saukarwa da Uznu irin wannan ƙawanya va sassautawa. Daga ɗaya zuwa biyu daga biyu zuwa uku.... Kan kace meye wannan ƙawanya ashirin sun rufarwa Uznu ta ko'ina. 


Sai dai shima Uznu baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen aikowa Armad nasa harin ba. Ya dunƙuƙe hannunsa na dama wanda baya riƙe da al'amudin ya daki iskar dake gabansa. Lamarinda yasa iskar ta dunƙuƙe kamar bal tayi kan Armad. Kafin ta ƙarasa jan hayaƙi mai ɗauke da Negrinki ya kewaye ta. Kafin Armad ya gama nazarin abinda ke faruwa Uznu ya ƙara dukan iskar ya aika masa da wani harin. Sannan ya ƙara aika wani. Kan kace meye wannan shima ya aika sama da goma. 


Nan fa yaƙi ya koma sabo. A wannan lokaci zaka iya cewa ƙarfin Armad da Uznu yazo ɗaya. Shi Uznu yana taƙa.a da Negrinki, shi kuma Armad duk da bashi da Negrinki amma yana da Miyura wadda take bashi izza ba adadi. Sannan kuma yana da fasahar Sikai ta Eyriyon wadda take bashi ikon samarda walƙiya ba adadi a duk lokacin da yake so.


Duk da armashin yaƙin dake afkuwa a ɓangaren su Armad zaka iya cewa bashi kaɗai ne abin kallo ba. A gefe guda sarki Daljari ya kirawo wasu sabbin fuska guda uku wanda suka bayyana a filin a karo na farko. Wannan mutun uku ba kowa bane illa Salsa ɗinsa.


Na farkonsu yana sanye da riga ruwan ƙasa mai tambarin tsaunika. Jikinsa bashi da girma sosai amma idan ka kalleshi zaka ji kamar yafi badala girma. Fuskarsa cike take da gashi launin ja kai kace bai taɓa aski ba. A saman kansa akwai ƙawanyar farin yashi na kewayawa kamar a sahara. Wannan shi ake cewa FARIN YASHI. Kuma yana tsaye a bayan sarki Daljari.


A gefensa wani ɗan yaro ne ko kuma kace mai fuskar yara wanda kansa babu gashi ko kwalli. Idanunsa na cike da baƙi mai nuna alamun kisa. Kana gani kasan wannan yaro ya kashe jama'a da yawa. Wannan yaro shi ake cewa KASHIN-SHANU.


A kusa dashi na wani siriri ne mai dogon gemu wanda saboda tsayin gemunsa har ƙasa yake taɓawa. Kuma ya ɗaure shi kamar bulala. Amma abin mamakin shi ne hasken da wannan gemu yake fitarwa. Kana gani kasan na musamman ne. Laƙabinsa ISKAR SAHARA.


Babu wanda yasan yaushe wannan mutane suka bayyana kawai ganinsu akai. Hasalima babu wanda yasan ko dama can suna wajen ko kuma yanzu suka zo.


***

.Babi na 160&1: Shirin Sarki Daljari 

***

Koda bayyanar Salsan sarki Daljari sai waje yayi tsit kai kace mutuwa ta gifta kowa ya riƙe numfashinsa. Sai da aka shafe sama da daƙiƙa bakwai sannan mutane suka samu damar ƙara yin numfashi. Yarima Kiru shi ne mutun na farko daya fara yin gwauron numfashi yana ƙinƙina ya ce, "Sadauki F...fa...farin Yashi.... " Yana magana yana nuna ɗaya daga cikin mutun ukun da suka bayyana. Kowa yasan wannan mutun a doron ƙasashen ƙasa sama da shekaru ɗari biyu da suka wuce. 


Asalinsa ance ɗan fashin kan ruwa ne a kan Bango amma mutane da dama suna ganin wannan labarin haɗa shi kawai akai domin babu sheda akan cewa ya taɓa yiwa wani fashi. Amma a shekarar 1577BA jaridar aminiya ta taɓa ɗakko hotonsa acikin ƙaton jirgin ruwa wanda aka gina da farin yashi. Bayan jaridar sunyi ta bibiya sama da shekara ɗari ance daga baya sun samu dama sun gana da wannan hatsabibi. A hirar sun samu sa'ar jiyo izzarsa wadda suka ce shekara aƙalla dubu arba'in. 


Amma duk wannan ba shi ne dalilin da yasa kowa yasan Farin-yashi ba. Dalilin shi ne kuɗin da Ururu suka saka akansa. 


A dai-dai wannan lokaci sadaukan dake ƙasa suka ankare da abinda ke faruwa. Nan take kowa ya fara ƙoƙarin gane waɗannan mutun ukun. Da dama daga cikinsu wanda suka fara ganewa shi ne Farin-yashi.


"Farin-yashi ne? Kuɗin Ayrid naira miliyan ɗari bakwai da ɗoriya."


"Naji ance izzar Farin-yashi takai dubu arba'in."


"Ban dashi akwai Iskar-sahara da Sadauki Kashin-shanu. Dukkansu sarakuna ne a ƙarni na biyar bayan Amri. Dama sarki Daljari yana da waɗannan ya ajiye su."


"Gaskiya wannnan yaƙin yafi ƙarfinmu."


"Ba wani yafi karfinmu.. Ni ina ganin yanzu ne mu Rafiyawa zamu fara azama."


Nan take irin waɗannan maganganu suka ɓalle tsakanin dubunnan sadaukan dake ƙasa. Kan kace meye wannan shewa da ƙuwwar yaƙi mai cike da farin ciki ta fara tashi daga ɓangaren rundunar sarki Daljari. 


A wannan lokaci sarki Daljari yai gyaran murya lamarinda yasa filin tai tsit. Sannan ya dubi Bihanzin ya ce, "wannan yaƙi yazo ƙarshe. Idan kana da wani shiri toka fito dashi a yanzu."


Yana rufe baki ya dubi Asifu RUWAN BALA'I da kwamanda JAN DOKI kallo mai cike da ma'ana. Sannan ya tafa hannayensa ya ce, "ƘASA-BAKWAI!!"


Abin mamaki yana faɗar haka wani haske ya fara bayyana a bayansa. Cikin ƙanƙanin lokaci hasken ya juye izuwa hoton doron ƙasa bakwai tun daga ƙasa ta farko har zuwa ta bakwai. A hankali hoton ya fara haske yana ƙara futowa. Idan ka lura ajikin hoton zaka ga titin Bayajidda, zaka ga doron ƙasashe bakwai sannan kuma zaka ga Bangon arewa dana kudu. Ga sashin Ikwatora a tsakani. Wannan hoton yana futowa wata katanga ta bayyana a bayansa. A saman katangar akwai muridan aljanu guda bakwai suna riƙe da al'amudin azaba. Dukkan jikinsa shafe yake da ƙasar kabari. Babu abinda ke tashi daga jikinsu sai ƙanshin mutuwa. 


Nan take iskar dake filin yaƙin ta cika da sanyi mai ratsa ƙashi. Sannan wata iska mai ɗauke da wani irin sauti ta fara tashi daga jikin katangar. 


Hatta Bihanzin sai da idanuwansa suka zaro. Baice komai ba amma lallai kana ganin fuskarsa kasan al'amarin ya girmama.


To amma idan da shikenan da abin da sauƙi. Ana cikin haka haka wannan aljanu bakwai dake kan katangar suka fara rera waƙa mai ban al'ajabi. Waƙar kawai sauti ake ji amma babu kalma. Komai sauraron mai sauraro bazai iya jin abinda ake cewa ba. Ga wanda suka rayu a zamanin sarki Amraikugyu sun san wannan waƙa ita ake kira da WAƘAR-IZZA. Sautin waƙar yare ne wanda aka daɗe da shafewa daga doron ƙasa.


Asifu da Jan-doki sun fuskanci ma'anar kallon da Daljari yayi musu saboda haka nan take suka tafa hannayensu suka fara kiran ɗalasimai. Dukkan wasa ya ɓace daga fuskarsu. Wani jan doki wanda aka gina da Negrinki ya bayyana a gaban kwamanda Jan-doki ya durƙusa inda Jan-doki ya haye. 


Shi kuwa Asifu ɗaga hannayensa biyu yai sama ya zana wasu ɗalasimai akan iska. Yana gamawa dai-dai samansa wani baƙin hijabi ya bayyana wanda ya fara buɗewa yana ƙara girma cikin ƙanƙanin lokaci ya rufe filin yaƙin baka ganin komai idan ka ɗaga kai sama sai shi. Sannan yai ƙaraji ya ce, "RUWAN-BALA'I!"


Nan take hadari ya haɗo a ƙasan hijabin, kafin a ankare an fara ruwan sama. Launin ruwan kalar ɗorawa ne kuma tun daga nesa yake fitarda tiriri. 


Koda ganin haka sai Naƙata da kwamanda Damjinu sukai tsalle suka nufi filin yaƙin da niyyar kare sadaukansu daga bakin ruwan amma a lokacin ne Farin-yashi ya ɓace daga inda yake ya bayyana a gabansu. Dole suka tsaya cak babu wanda ya isa wuce. 


Yarima Hasanu da Kiru suka yanki wata hanyar zasu wuce amma Kashin-shanu ya sha gabansu. 


Haka na faruwa Iskar-sahara ya ɓace daga inda yake ya tare ɗaya hanyar. Cikin ƙanƙanin lokaci aka saka su Bihanzin a tsakiya.


Bihanzin na tsaye suna kallon-kallo da Daljari. Yasan cewa bai isa ya motsa ba. Shima sarki Daljari yana tsaye yana kallon Bihanzin. 


Bayan ɗan lokaci ya dubi Bihanzin ya ce, "nasan wannan takobin taka ba ita ce asalin Dauwamammen-sara ba saboda haka zan baka daƙiƙa goma ka fito da haƙiƙanin takobinka idan ba haka ba kada ka zargeni duk abinda ya faru dakai."


Bihanzin ya haɗe gira amma duk da haka baice komai ba. 


A gefe guda ruwan sama launin ɗorawa ya fara zuba acikin filin yaƙin. Nan take ihu mai cike da firgici ya fara tashi daga bakin sadaukan dake cikin filin. Duk abinda ruwan ya taɓa nan take yake narkewa. Ko ƙarfe, ko riga, ko jikin mutun, ko ƙasa komai narkewa yake. Nan take filin yaƙin ya ruɗe ya rikice da kuka da ihu. Idanuwan sadaukai ya raina fata. 


"Wayyo!"


"Wayyo! Kwamanda! Kwamanda!!"


"Wayyo!!!"


Amma abin mamaki ruwan baya zuwa wajen sadaukan rundunar sarki Daljari. Koda ganin haka sai ragowar sadaukan suka rufe ido suka nufi ɓangaren suna ihu suna neman agaji.


Kan kace meye wannan sun kusa ƙarasawa. Har sun fara jin alamun rahama a ransu amma a lokacin suka ga wani ƙaton tsauni ya bayyana a gabansu. A gaban tsaunin akwai wani jan-mahayi kan jan-doki riƙe da jan mashi yana haske. 


Kwamanda Jan-doki. 


Ya dube su yayi murmushi. Dama can kwamanda jan-doki kyakkyawa ne amma da yayi murmushi sai kyawunsa ya ƙara fitowa. Sai dai kuma a lokacin duk wanda ya kalleshi zaiga idanuwa cike azabar yaƙi wanda har tiriri suke. Ya buɗe baki ya ce, "Ina baku shawara kada ku haura wannan layin."


Nan take sadaukan suka dubi inda hannunsa yake nunawa suka iske wani ɗan ƙaramin layi wanda sai kayi da gaske zaka ganshi. Babu wanda ya san yadda akai layin yazo wajen; zana shi Jan-doki yayi da kansa ko kuma wani ne yayi shi a yayin yaƙin. Amma dai akwai layi a wajen.


Ba shiri suka ja tunga suka tirje babu wanda ya isa ya haura. Gaba kura, baya damisa, tsakiya mutuwa. Suna tsayawa ruwan ya ƙara tsugewa. Tuni gashin kansu ya fara narkewa yana bada wani irin wari mara daɗin ji. Tun suna ihu muryarsu ta fara dashewa, hawayen idanuwansu ya ƙafe.


Ana haka wani sadauki yai kururuwa yai ta maza yai kan layin ya tsallaka yayi kan Jan-doki. Amma kafin ƙafarsa ta dira ƙasa wani irin nauyi kamar ana matse shi da tsaunika ya bayyana a jikinsa. Nan take yayi dana sanin tsallaka layin. Ya ɗauke ƙafa da niyyar komawa amma kafin ya koma jikinsa yayi bindiga, jini da rududdugaggen nama ya fallatsu ko'ina.


Jan-doki yai murmushi amma bai ce komai ba. 


Da farko sadaukan suna tsoron kiran sunan Bihanzin saboda haka kwamandun kawai suke kira amma da suka ga mutuwa nan take suka fara kwalawa Bihanzin kira ya kawo musu agaji. 


"Sarki! Ka taimakemu kai mukewa wannan yaƙi. Ka kawo mana agaji."


"Bihanzin!"


"Bihanzin!!"


"Bihanzin!!!"


Daljari yai ajiyar zuciya ya dubi Bihanzin. A zahiri tun farkon yaƙin zai iya sawa Asifu da Jan-doki suyi wannan kisan gilla amma baya son kashe mutane haka saboda haka ya tsagaita. Amma a halin da yake ciki yasan lalle akwai abinda Bihanzin yake ƙullawa kuma akwai abinda yake jira shi yasa yaƙi fito da haƙiƙanin Dauwamammen saransa. Saboda haka ya bawa su Asifu umarni domin ko hakan zaisa Bihanzin ya saduda. 


"Baƙin-maraya kai suke kira."


Amma Bihanzin yai shiru kamar baiji mai Daljari yace ba. Hasalima rufe ido yayi ya fara magana aciki kamar yana yiwa kansa raɗa. Koda ganin haka sai hankalin kwamandunsa da ƴaƴansa ya dawo kansa suka kasa kunne suna jin mai yake cewa. 


Bayan ɗan lokaci maganarsa ta fara yin sama inda suka ji mai yake cewa.


"BAUTAR TAKOBI! RAYUWA DAN TAKOBI!! MUTUWA DAN TAKOBI!!!"


Nan take suma suka ɗauka suna cewa, "Rayuwa dan takobi, mutuwa dan takobi, bautar takobi."


Nan take sautin muryarsu ya haɗu ya fara yin sama inda ya fara shiga kunnuwan wanda ke nesa. Nostaljiya na bayan Armad na ganin abinda ke faruwa. Tuni jininta ya hau tana ta ƙokarin yadda zatai ta taimaki mutanenta da ƴan'uwanta da mahaifinta. Koda taji abinda suke cewa sai hawaye ya fara kwaranya daga idanuwanta badan komai ba saboda abinda suke faɗa shi ne wurindin da ake faɗa a garin Jekis idan anzo mutuwa. Nan take ta kalli Armad sannan ta juya ta kalli Bihanzin tana tunanin abinda zatai. Hankalin ta yai mummunan tashi.


Armad tuni idanuwansa sujai jajawur kai kace jini aka zuba musu. Jijiyoyin jikinsa sunyi burɗun-burɗun. Sama da mintuna ashirin kenan suna fafatawa da Uznu. Tunda suka fara yake zuƙar izza daga Miyurarsa yana ƙarawa kansa izza wanda haka yake ƙara masa ƙarfi amma a duk lokacin daya samu damar tarwatsa al'amudin Uznu sai ya ƙara haɗa wani.


Uznu yai kururuwa ya dubi Armad ya ce, "Kai yaro! Tun kafin a haifi kakanka nake yawo a duniyar izza, kana tunanin zaka iya cin galaba akaina. Ka daina mafarki. Bari kaji na baka wani sirri wanda baka sani ba. Sinadarin Negrinki na bashi da ƙarfi idan ka kwatantashi da sauran ƴan'uwa na da suke cikin Ashura amma ni kuma saboda jinina na Uzzu ina da wani sirri. Kasan wane sirri ne?" 


Uznu ya fashe da dariya sannan ya ɗora da cewa, "ni kaɗai nake da Negrinki wadda bata tsufa kuma bata ƙarewa kamar yadda jikina yake baya tsufa kuma baya mutuwa. Abin kunya ne a gareni a ce wani ɗan tatsitsi kamar ka wai zai ja dani. Da sannu zaka gane kuskurenka."


Armad ya girgiza kai tare da nuna Uznu da dan-yatsa. "ka siyar dani a matsayin bawa, ka ɓatarda Nusi, ka sace mata ta, kana tunanin hukunci bazai biyo ta kanka ba? Ka manta da abinda na faɗa a baya, na riga na yanke shawara kashe ka zanyi."  


Armad na faɗar haka ya ɗaga hannayensa ya danna akan Miyurarsa. Nan take bakan-gizo ya keto ta cikin hijabin da Asifu yasa ya rufe sama ya bayyana a saman Armad. Yana bayyana izzar Armad ta fara ƙara yin sama.


Daga izza 10,000 zuwa 15,000 zuwa 20,000, har zuwa izza 30,000.


Nan take bakan-gizon ya tarwatsa hijabin sannan ya rufe sararin samaniya. Duk inda mutun yake a doron ƙasa yana ganin wannan bakan-gizo. Babu abinda kake ji sai ajiyar zuciya.


***

Babi na 162: Uznu vs Armad

***

Bakan-gizo mai haskaka duniya. A sanda ya bayyana yana da launin ja. Amma koda izzar Armad ta ci gaba da ƙaruwa tana sama sai launinsa ya ci gaba da canjawa. A halin yanzu izzar Armad takai shekaru dubu talatin sannan kuma kala ta uku ta bayyana a cikin bakan-gizon. Ja. Baƙi. Ɗorawa. 


Armad ya ƙara kururuwa ya danna hannunsa acikin Miyurar. Wani hayaƙi kamar ana tafasa ruwa ya fara tashi daga jikinsa. Nan take izzarsa taci gaba da yin sama. 31,000, 32,000.


Nan take wata kalar ta ƙara bayyana acikin bakan gizon. Launin Fari. Sannan a yayinda izzar Armad takai 35,000 launin shuɗi ya bayyana. Wanda ya haɗa launi ɗai-ɗai biyar acikin wannan bakan-gizo.


Amma ina, har yanzu Armad bai ƙoshi ba. Izzarsa taci gaba da yin sama tana ƙaruwa. 36,000, 37,000, 38,000, 39,000, 40,000.


Har said ta dangane da izza shekaru dubu arbain dai-dai. A lokaci sanyin-babban-sihiri ya bayyana. Ƙanƙara mai ruwan toka ta fara zuba daga cikin bakan-gizon kamar ana ruwan. Sannan kuma launi na shida ya bayyana acikin bakan gizon. Launin kore.


Launika shida sun bayyana. Ga sanyin babban sihiri yana bayyana. 


A lokacin ankoki na baƙin ƙarfe suka zubo daga cikin dutsen Hajarul-ururu suka rufe sama. Armad na ganinsu yaji kamar an ɗaure jikinsa tayadda koda yana so bazai iya ƙara yawan izzarsa ba. Yakai ƙololuwar matakin dazai iya zuwa a doron ƙasashen ƙasa. Dama can wannan abu ne sananne cewa shekaru dubu arba'in sune ƙololuwar abinda sarki Kuyurusaa'ayi ya yadda al'ummar dake rayuwa a doron ƙasashen ƙasa su samu. Babu wani wanda ke rayuwa akan doron ƙasa ta biyu zuwa ta bakwai daya wuce wannan mataki. Duk wanda yazo wannan mataki yakai intaha.


Koda ya fuskanci abinda ke faruwa saiya manta da ƙara yawan izzarsa ya dawo da hankalinsa kan Uznu. A halin yanzu Armad yana ji kamar zai iya halaka ƙasa guda da ɗan'yatsa kaɗai. Hatta ƙasa baza ta iya ɗaukansa ba. A ƙalla ya ninka ƙarfinsa na da sau hamsin. Saboda haka babu buƙatar ya damu da wannan iyaka. Burinsa kawai a wannan lokaci Uznu ya karɓi hukunci.


Armad ya haɗa hannayensa wajen ɗaya ya rufe ido sannan ya ce, "WALƘIYA!"


Kalma ɗaya ce amma yana fafarta duniya tai duhu. Komai dake duniya ya fara juyewa izuwa sinadarin walƙiya. Sama ta juye izuwa walƙiya ƙasa ma ta juye. Kai hatta makaman yaƙin da aka jefar a ƙasa juyewa sukai izuwa sinadarin walƙiya. Kai hatta mutanen da basu yi saurin guduwa ba tuni sun juye sun narke izuwa walƙiya. Amad ya ƙara cewa. "SIKAI!"


Dukkan wannan walƙiya ta haɗe waje ɗaya sannan launika suka fara bayyana a jikinta sai da launi ɗai-ɗai har bakwai ya haɗu ajikinta kamar na bakan-gizon. Abin mamaki sai dukkan wannan walƙiya ta fara tunkaro inda Armad yake sannan kan kace meye wannan walƙiyar ta fara shigewa hannun Armad na hagu tana haɗewa izuwa sabon Hannun-aradu wanda ba'a taɓa gani ba. A karo na farko tun bayyanar Uznu tsoro ya bayyana ƙarara akan fuskarsa. Wannan walƙiyar ba irin ta baya bace. Lalle idan ya bari ta dake shi kai tsaye ko gawarsa baza a gani ba. 


Nan take ya danna hannunsa a ƙirjinsa lamarinda yasa wata ƙatuwar takarda mai zanen ɗalasimai ta bayyana ajikin ƙirjinsa. Uznu ya yage takarda, nan take izzarsa ta fara yin sama wani baƙin abu yana fita daga jikinsa. Idanunwansa sukai jajawur. Wannan ita ce fasaharda yayi amfani da ita ya rayu a lokaci yaƙin littafi-takobi. Saboda haka yana da nutsuwar cewa babu wani hari dazai iya halaka shi indai yana da wannan fasaha wadda ya gada daga jininsa na Uzzu. 


A dai-dai wannan lokaci hannun Armad na hagu ya juye izuwa gidan walƙiya. Tuni ya zuƙe dukkan walƙiyar kawai haske yake.


Armad bai wata-wata ba ya afkawa Uznu. Yana dira ya aika masa da hannun-aradu. Nan take iska ta dare gida biyu wata ƙofa ta bayyana wadda ta tunkari Uznu gadan-gadan. Kafin ya ankare ta cimmasa. Yayi ƙoƙari yasa takobinsa ya kare amma duk da haka walƙiyar ta haɗiye takobin sannan ta haɗiye. Nan take jikin Uznu ya fara narkewa. Cikin ƙiftawar ido da bismilla babu komai daya rage sai zuciyarsa kawai akan iska. Shima hannun-aradun Armad ya ƙare. 


Sai dai kuma kash a dai-dai wannan lokaci zuciyar Uznu ta fara fitarda haske. Nan take jini da tsoka suka fara haɗewa suna dawowa yadda suke da. Kafin Armad ya ankare Uznu Ururu ya haɗe jikinsa izuwa guda. Amma kana ganinsa kasan ya galabaita kuma amfani da wannan fasaha tana da tukuici mai girma. Babu abinda yake sai nishi. A lokacin wannan mace dake kusa dashi ta matsa ta dafa ƙirjinsa. Nan take izza ta fara kwaranya daga jikinta zuwa nasa. Cikin ƙanƙanin lokaci Uznu ya farfaɗo. Amma kana ganin matar kasan ta tsofe akan da. Ga dukkan alamu idan taci gaba da bawa Uznu izzarta tsaf zata halaka.


Uznu yai dariya ya ce, "shikenan abinda zaka iya? To bari kaji na ƙara gaya maka wani sirrin. Nine mafi rauni acikin Ashura amma kayi sani cewa hatta ƙololuwar izzar da ake da ita a ƙasashen ƙasa wato shekaru dubu arba'in basu isa su kashe ni ba."


Armad ya haɗe gira ransa a ɓace. Shima wannna hari da yayi ya zuƙe masa izza. Musamman duba da cewa dama izzar aro ta yayi daga Miyurarsa kuma kowanne lokaci zata iya komawa. Zai iya ƙara wani harin irin wannan amma koda ya ƙara aikata Uznu ƙara haɗewa zaiyi. Indai yana so ya hukunta Uznu to saiya fasa wannan ankoki dake sararin samaniya ya ƙara yawan izzarsa. To amma ba'a banza akai shekaru dubu babu wanda ya cire wannan ankoki ba akwai dalili. Dalilin kuwa shi ne babu wanda zai iya. Kusan duk wani wanda ya isa ya gwada sa'arsa, misali kamar sarakunan Jinzidal, amma babu labari. 


Armad ya ƙurawa macen dake kusa da Uznu ido sannan bayan ɗan lokaci ya dawo da hankalinsa Uznu. 


"Uznu, na riga na ce yau zaka baƙunci lahira wai danme baza ka manta da ƴar tatsitsiyar rayuwarka ba."  

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...