Daga wannan rana Taidara da Hidaya da Abijan suka fara shiri a ɓoye. Fatima ta sani saboda haka ta ɗauki gaɓar janyo Abijan a jikinta. Idan duk sun taɓu to dole a bata 'yarta.
Sai dai kuma a lokacin ta fuskanci Abijan tayi nisa sama da yadda take tunani. Irin yadda Abijan ta tsani Ururu ya wuce lissafi. Wani lokacin tana bacci tana kiran sunayen Ashura. Fatima tayi-tayi, amma kamar hurawa abin wuta take yi.
Wata guda bayan wannan rana aka haifi santalelen saurayi aka saka masa suna Armad. Ko suna ba'ayi ba. Duk mutanen gidan kowa abubuwan gabansa sunyi masa yawa. Hidaya ce kaɗai ta yiwa Armad suna. Ta tara ƴan-ƙauyen ta dafa musu abinci. Duk kayanta na izza dana sawa ta rabar dasu saboda murna.
Abijan sau uku kacal ta ɗauki Armad tun sanda aka haifeshi badan komai ba saboda bata zama ko kaɗan. Taidara baya zama amma a duk sanda yazo gida yana riƙe da Armad.
Fatima ta shiga damuwa sosai. Abinda kurum yake ɗan faranta mata rai shi ne yadda Hidaya take nunawa Armad soyayya.
Watarana dai abin ya dameta ta tara kowa a gidan domin ta amayar da abinda yake ranta.
"Ku dubi ALLAH, ku dubi Annabi, ku daina abinda kuke yi," inji Fatima. "Nabi ku ba sau ɗaya ba, ba sau biyu naga abinda kuke aikatawa. Har Ururu sun fara samun labari. Yanzu ace kamar ke Abijan kin fara haɗa tawagar mutane zaki yaƙi Ururu? To wai tayaya kuke lissafin samun nasara? Eyriyon da kansa ya gwada bai ci nasara ba. Kuma komai akwai lokaci, idan kuka yi hakuri namu lokacin zaizo."
Abijan ta miƙe tsaye. "Wai, mama, mai kike da tsoro ne? A tarihinki da nake ji da yadda mutane suke faɗar faɗanki da Anti Hidaya banyi zaton haka kike ba."
Fatima tayi wani yaƙe. Abijan ta fara bata tsoro. "Ba tsoro bane, ƴata. Idan da rayuwar yaƙi nake so da bazan zo nayi aure na kawo yara duniya ba. Idan ina son rayuwar yaƙi nasan yadda zan shiryata. Amma ki sani, Abijan, a yaƙi ba'a aure, ba'a zama a gida, kuma ba'a noma. Yaƙi yana nufin fyade, yaƙi yana nufin marayu, yaƙi yana nufin fari, yaƙi yana nufin yunwa. Tabbas bamu da ƙarfin yaƙar Ururu a yanzu, kuma idan kuka janyo wannan faɗan sai ya shafi kowa, musamman ƴan-ba-ruwana. Wai yaushe kuka fara shirin ne? Ke yaushe aka haifeki harda zaki ringa kiran yaƙi? Kinsan mai kike cewa kuwa?"
"Mama, tun shekaru da dama kafin Abba ya gamu dake yake shiri fa. A duk sako da loko na ƙasa bakwai babu inda bamu da mayaƙa a ajiye suna jira. Kina tunanin fasahar Hisabi da Abba ya samar ta meye? Ta ajiye mayaƙa ce. Duk wata maƙabarta da kika sani a faɗin ƙasa bakwai, harda doron ƙasa ta farko, akwai mutanenmu aciki. Tawagar matattu gaskiya ce, mama. Abinda kawai ya rage mana shi ne fasahar duniya wadda zata tare Kuyurussa'ayi, kuma yanzu mun samar da ita, dama ita kaɗai Abba yake jira."
Fatima ta yamutse fuska. Duk abubuwan da Abijan take faɗa tasan a bakin Taidara taji. Ina yarinyar da aka haifa shekaru goma-sha da suka wuce tasan irin wannan abubuwa. Abin haushin tun da take da Taidara bai taɓa gayamata yana binne mayaƙa a kabari ba. Tabbas tasan fasahar Hisabi, amma bata san Taidara yana amfani da ita wajen ɓoye mayaƙansa ba. Yaushe ya fara? Mutun nawa ne dashi yanzu? Ga dukkan alamu da gaske Taidara yake. Dole tana buƙatar tasan hakikanin al'amarin kafin su je su aikata wata ta'asar.
"Kika ce dama fasahar duniya kuke nema kuma yanzu kun samu?"
Abijan ta gyaɗa kai. "Ita kaɗai ta rage mana kuma yanzu mun samu. Ni Abijan ina da fasahar da muke buƙata."
Fatima tayi shiru tana tunani. A hankali ta dubi Taidara.
"Dama kasan ina da Negrinki mai fasahar duniya tun kafin kazo maikironomada, ko?" Inji Fatima.
Tana sane da tsarin gado na izza da Negrinki. Wato akwai fasahohi na gado irin su miyura waɗanda kai tsaye ake gadonsu. Sannan kuma akwai na caca. Wato zaka iya gada idan iyayenka suna dasu, kuma zaka iya rasawa - basu da tabbas. Duk wata fasaha da take da tsananin ƙarfi kowacce iri ce tana daga cikin irin waɗannan fasahohi. Wato kamar fasahar tayi ƙarfin da ita akan kanta take so ta yaɗa kanta. Bata so ta ɓace a ban ƙasa saboda haka take shiga jini ta yaɗa kanta. Ɗa zai iya gada idan uwa ko uba suna da ita. Fasahar Negrinkin Fatima ta kai wannan mataki saboda haka ba abin mamaki bane idan ƴar data haifa ta gada. Abinda take so taji shi ne: shin wannan shi ne dalilin da yasa Taidara ya aureta? Shin daman ba sonta yake ba?
"Na sani," inji Taidara. "A gaskiya zuwanmu daular maikironomada ba saɓani bane. Dama mun shirya zuwa saboda ke."
"Mayaudari!" Inji Fatima. Kwalla ta zubo mata. "Dama saboda haka ka aureni. Ban yafe maka ba. Dana san haka ne da babu yadda za'ai na aure ka. Baka so na. Dama duk ƙarya ne abinda ka faɗa."
Taidara ya miƙe da sauri ya zagaya wajenda take. "Wallahi ba haka bane... Eh, da farko abinda ya kawo ni kenan, amma bayan na ganki na canja shawara. Ina sonki. Mai zai saka na zauna har yanzu idan ba haka ba? Tunda muke zaga duniya bamu taɓa zama a guri ɗaya mun daɗe haka ba."
"Bazan saurareka ba," inji Fatima. Ta juya tana huci ta fice daga ɗakin.
Hidaya ta tashi ta bita da sauri suka shiga cikin gida tana bata hakuri amma ko kaɗan Fatima bata jita ba.
Kwana kaɗan da faruwar abin Fatima ta kira waliyan da suka daura auren. Suka zo aka zauna domin samo bakin zaren.
"Taidara, mai ke faruwa ne?" Inji Maikiro'Abbas. "Matarka tana zarginka da abubuwa da dama wanda hakan yake neman cutar da zamantakewarku ta aure. Mai kake so ka cimma da Abijan? Na fuskanci a kullum idan anzo irin wannan tattaunawa baka samun dama kayi magana sosai. Amma yau na baka dama ka faɗi duk abinda kake so."
Taidara ya miƙe tsaye domin yin bayani.
"Ina son na dawo da martabar gidan Wilbafos a idon duniya. Tsahon shekaru muna tafiya da Hidaya kafin muzo wannan gari naku. Munyi bincike na hanyoyi da zamu dawo da martabar gidan Wilbafos. Idan sarki ya bani dama zan fadi wannan shiri namu."
Taidara ya dubi Maikiro'Abbas yana jira ya bashi umarni yaci gaba da bayani. Abbas ya kalli Alu wanda ya gyaɗa kai sannan ya juyo ya dagawa Taidara kai.
"Nagode," inji Taidara. Daga nan ya fara bayani. "Ina da mayaƙa a maƙabartu daban-daban wanda na haɗe da zaren izzata. A kowanne lokaci zan iya tashinsu. Shiri na mataki-mataki ne bawai lokaci ɗaya zai jawo yaƙi da daular Ururu kamar yadda Fatima take tunani ba. Mataki na farko ya ƙunshi nunawa Ururu muna da ƙarfin da dole a zauna sulhu da mu. Ta hanyar wannan ina so a kafa wani majalisi wanda damu da Ururu zamu zamanto muna aiki kafaɗa da kafaɗa: baza su kawo mana hari ba, baza mu kai musu ba. Hakan zai samar da zaman lafiya mai dorewa saɓanin a yanzu da suke bin mutane suna kamawa babu ka'ida.
"Sai dai Ururu baza su taɓa zama damu ba matuƙar bamu nuna musu ƙarfi ba. Dole sai sun yarda muna da hatsari sannan zasu yarda su zauna a teburin sulhu. Tuntuni muke ta ƙoƙarin muyi wani gagarumin abu da zai saka Ururu su yarda su zauna a teburin sulhu, sai dai bamu da ƙarfin yin hakan. Mun rasa irin fasahar da muka daɗe muna nema.
"Wata rana muna cikin tafiya sai muka zo wucewa ta garin Bilda. Sai muka ji wani matafiyi yana bada labarin wata jaruma. Gata ƴar sarki gata ma'abociyar izza. Matafiyin yake cewa duk abinda wannan ƴar sarki ta sara yana ɓacewa a nemeshi a rasa baza a ƙara ganinsa ba har abada. Jin wannan yaja hankalin mu. Muna jin akwai yiwuwar wannan fasaha ita ce wadda muke nema. Saboda haka muka garzayo domin ganin wannan gimbiya.
"Munyi ƙoƙarin ganin Fatima ta hanyar fada amma hakan bai yiyu ba. Waye zai bar fatake wanda ko kaya masu kyau basu dasu suga ƴar sarki? Hmm. Daga baya muka je muka yi kwadago muka sayi kaya masu kyau muka saka sannan muka dawo. Abin mamaki duk da haka ganin Fatima bai samu ba. Dole babu yadda zamu yi muka tafi ƙauyen Nafada muka yi amfani da fasahar Hisabi muka ja hankalin sarki har ya turo mana Fatima.
"Faɗan Hidaya da Fatima abu ne wanda muka riga muka lissafa shi da daɗewa. Munyi amfani dashi domin muga yadda fasahar Fatima take aiki. Bayan ɗan bincike muka gano fasahar bata da karfin da muke nema amma kuma akwai yiyuwar wasu daga cikin 'ya'yan Fatima su samu abinda muke nema. Tsakani da ALLAH wannan shi ne dalilin da yasa a lokacin nayi niyyar auren Fatima. Amma kuma bayan na zauna da ita naga halayenta sai naji duk duniya babu wadda nake so sama da ita. Hakan ne yasa tsawon lokaci na manta da wancan shiri na samar da fasaha, na tattara hankali na akan faranta mata rai.
"Ban ƙara tunanin wani abu ba har sai lokacin dana ga Abijan. Duk da ina son Fatima kuma bana son abinda zai ɓata mata rai amma dole ina da nauyi daya kamata na sauke na al'ummata. Iyayena da 'yan-uwana da matata da aka kashe ina buƙatar nabi musu hakkinsu. Dole na ajiye son zuciyata nayi abinda ya kamata.
"Kada ku manta aure tsakanin Wilbafos da Wilbafos abu ne wanda yake wahalar samar da haihuwa. Wani lokacin akan yi shekaru hamsin da aure ba tare da an samu haihuwa ba. Amma muka ci sa'a muka samu Abijan acikin shekara biyu kacal da yin aure. Ba dabarata bace. Koda na auri Fatima bani da ikon kawo haihuwa. Amma duk da haka ina roƙon Fatima data yafe min akan abinda na aikata."
Jin wannan labari da Taidara ya bayar kowa yayi shiru aka rasa mai yin magana. Ta bayyana ƙarara ga dalilin da yasa Taidara ya auri Fatima. Duk da yace daga baya ya fara sonta. Ko hakane ko ba haka bane amsar sai dai mu tambayi Fatima tunda ita ce ta zauna dashi.
A wannan lokacin idanun Fatima sunyi jajawur kamar garwashi. Babu abinda take sai huci. Babban abinda ya ƙara ɓata mata rai shi ne a gaban waliyinta da babanta Taidara ya bayyana cewa ba soyayya bace ta kawo shi wajen ta. Ga kuma wani zance da Taidara ya faɗa na ɗaukar fansar matarsa da aka kashe wanda bai taɓa yi mata shi ba. Nan take wani kishi mai zafi ya taso mata. Wato ya aureta ne saboda ya samu damar ɗaukan fansar matarsa.
"Ka sake ni, na gama auren. Bazan iya ba."
Alu mai sango ya miƙe da sauri. "A'a, Fatima, baza ai haka ba. Dama a kowanne aure ana samun saɓani, tunda dai Taidara ya karɓi kuskurensa kuma ya nemi a yafe masa ai ina ganin sai ayi haƙuri. Zaman aure komai rashin daɗinsa yafi rabuwa musamman tunda har an samu yara biyu." Alu ya juya wajen Maikiro'Abbas. "Amma, kai Abbas, mai kake gani?"
Maikiro'Abbas yayi shiru tare da runtse ido yana tunani. A matsayinsa na waliyin Fatima kuma wanda ya riƙeta an ɓata masa rai. Domin dai babu wanda zai so yaji an auri 'yarsa ba dan ana sonta ba, ko wane irin dalili ne kuwa. Zaka iya cewa a wannan lokaci shi kansa Abbas yaji haushin Taidara. To amma kuma kamar yadda Alu ya faɗa an riga an haɗu an kuma samu yara a tsakani saboda haka idan ma an rabu to ba a rabu ba. Yana ganin idan Fatima zata iya haƙuri to sai ya bata hakuri a ci gaba da zama. Sai dai kuma shi kansa baya so ya bata haƙurin badan komai ba saboda yana jin kamar Taidara ba zai daina abinda yake ba, musamman al'amuran Abijan. Taidara bazai daina janta cikin al'amuransa na tada-zaune-tsaye ba. Ita kuma Fatima ba zatai shiru ba. Saboda haka yana ganin zaman zaici gaba cikin ɗaci.
Yaja dogon numfashi tare da juyawa wajen da Zaikid yake zaune yayi tagumi. "Abokina, ina ganin wannan hukuncin kai zaka yanke shi."
Zaikid ya girgiza kai. "Wannan yarinya dai 'yarka ce kuma zan iya cewa kafini saninta domin kai ne ka taso da ita. Kasan mai zata iya haƙuri dashi, kasan meye ba zata iya hakuri dashi ba. Yaya kake gani?"
Abbas yayi wani murmushi mai ɗaci. Dama yasan haka Zaikid zai ce saboda sanin kawaicin abokin nasa.
Taidara da Fatima da Abijan da Hidaya da Alu kowa idanunsa na kan Maikiro'Abbas ana jira aji hukuncin da zai yanke. Abijan tana sauraro taji ko zai raba auren iyayenta. Shi kuma Taidara yana jira yaji ko za'a rabashi da matarsa. Ita kuma Fatima tana so abi mata hakkinta.
"To, ina ganin abinda Alu ya faɗa yana kan layi sai dai ɗan gyara kaɗan da zanyi. Aure dai shi ne ginshikin rayuwa kuma babu abinda yakai rabuwa ta aure matsala musamman idan an samu yara a tsakani. Saboda haka ke Fatima ina so kiyi hakuri ki ajiye zancen saki a gefe, ki manta da duk wasu abubuwa da suka faru a baya da kuma duk wani dalili da yasa Taidara yazo wajen ki. Duk wannan ya wuce, zancen gaba ake."
Fatima tayi zumbur ta miƙe tare da buɗe baki za tayi magana amma Maikiro'Abbas ya daga mata hannu. Dole ta rufe baki ta koma ta zauna jiki a sanyaye.
Maikiro'Abbas ya juya wajen Taidara. "Taidara, ina so kasan cewa rayuwarka ta yanzu da kake yi da matarka da yaranka guda biyu tafi duk wata rayuwar ɗaukan fansa da zaka yi saboda wani dalili daya faru a can baya a rayuwarka. Abinda nake so dakai ka ajiye zancen tada-zaune-tsaye, kazo ka zauna da iyalinka. Idan duk ku biyun nan za kuyi wannan to ina ganin zaku samu kwanciyar hankali. Ni dai wannan ita ce shawara ta. Alu, ya kake gani?"
"Wannan yayi," Inji Alu. "Kuma ina ganin da shi mijin da matar duk zasu amince da wannan shawara taka mai tarin hikima." Cikin murmushi Alu ya juyo wajen Fatima yana ganin cewa an samo bakin zaren. "Ƴata Fatima, kin amince zaki ci gaba da zama da mijinki idan har ya amince ya daina tada-zaune-tsaye?"
Har Fatima ta fara girgiza kai zata ce bata amince ba amma Abbas da Zaikid sukai mata wani kallo wanda yasa nan take ta canja shawara ta gyada kai. "Na amince."
Alu yaji daɗin amsar domin yasan bata so amma kuma ta amince saboda ta faranta musu. Ya gyaɗa mata kai na jinjina sannan ya juyo wajen Taidara.
"Taidara, ka amince zaka ajiye makamanka ka daina tada-zaune-tsaye kazo ka kula da iyalanka?"
Taidara ya ɗago kai a hankali ya kalli Hidaya sannan ya juyo ya kalli Fatima sannan ya juyo ya kalli Alu.
"Shin bazan iya zama da iyalina sannan kuma a lokaci guda na cika burina na farfaɗo da gidan Wilbafos ba?"
A fusace Alu ya dube shi. "Kaga, Taidara, dukkan nin mu nan babu ƙaramin yaro, babu wanda zaka yiwa wasa da kalmomi. Idan zaka ɓoye wani abu a matsayina na waliyinka bai dace ka ɓoye min ba. Ka gayamana magana ɗaya; zaka daina ko ba zaka daina ba?"
Taidara yaja numfashi a hankali.
"Gaskiya bazan iya rabuwa da gidan Wilbafos ba. Abinda nasa a gaba abu ne wanda zai taimaki 'ya'yanmu da jikokinmu saboda haka ina ganin ban yiwa kaina adalci ba saboda jin daɗi na ni kaɗai na daina wannan gwagwarmaya."
Comments
Post a Comment