A halin yanzu garin Jékis ya bayyana tsirara babu katanga, babu ƙofa. Iliyasis, Babara, Nostaljiya da Cokali suka fuskanci waɗannan Deba guda huɗu dake tsaye a bakin garin.
Liyurul Linbul shi ne shugaban Deban guda hudu masu tsaron garin. Yana da cikakkiyar masaniya akan cewa wannan yaƙi ne na ko'a mutu ko ai rai. A wannna yaƙi babu fursuna, kowa yaje ƙas ya zama mushe. Sabida matsayinsa a tawagar Sarkin-sarki yana da masaniya kan wasu daga cikin tsare-tsaren tawagar su. Kuma yafi kowa sanin muhimmancin tsare wannan gari na Jekis, wanda anan shugaba Bihanzin ya fara kafa daularsa. Garin Jékis gari ne mai tarihi da yawan kafi. Akwai izza, akwai kaburbura, sannan kuma akwai na cikin kabarin. Idan mai karatu bai manta ba, shekarun baya sanda Armad ya farkar da idanun sa ya samar da sabon farin wata anga ɗaya daga cikin iyalan wannan kaburbura ya motsa. Wannan shi ne yasa ko kaɗan ba abin mamaki bane dan an ajiye Deba ɗai-ɗai har huɗu, domin suyi gadin wannan gari.
"Hussuil, Kanduil, Cunduil, kowa ya kama nasa." Inji Liyurul Linbul. Nan take mutun uku dake bayansa suka rarrabu. Kowa ya kama abokin fafatawarsa. Babu wani dalili dake nuna zaɓin nasu nada alaƙa da yanayin fasaharsu ko kuma ta abokin karawarsu, amma dai Hussuil shi ne ya kama Nostaljiya, Kanduil ya kama Cokali, Cunduil ya kama Iliyasis, sai kuma Liyurul ya boka Babara.
Sai dai kuma kash, wannan tsarin abokan karawarsu ne, suma ƴan aiken Armad suna da nasu tsarin wanda kuma baiyi dai-dai da tsarin abokan karawar tasu ba. A taƙaice dai su Iliyasis basu da niyyar yaƙar abokan karawar tasu ɗaya-da-ɗaya. A wajensu wannan lissafin ƙananun ma'abota izza ne. Abinda suka shirya shi ne mutun ɗaya tak daga cikinssu ya shanye Liyurul LinbuL, Hussuil, Kanduil da Cunduil. Wannan mutun ɗaya shi ne Cokali.
Cokali abin wasan yara. Cokali abin sakacen manya. Cokali gatan mai jin yunwa. Cokali tumbin ka yafi izzar ka girma.
Iliyasis da Babara da Nostaljiya suka koma baya suka bawa manzo Cokali dama yai aikinsa. Shi kuwa Cokali gaba yai ya tari abokan gaba kai kace Ƙassai ne a gabansa ba Deba ba. Ya zaro littafin marubutan farko ya fara aiki. Zaren izza wanda Ayubu sarkin yaƙi ya ajiye a wannan gari ya taso ya ɗaure abokan karawarsa. Sannan ya kwafi yanayin izzarsu ya aikewa Cokali. Tun da an samu yanayin izza rubutu kawai ya rage.
"Liyurul Linbul fari mai dogon kunne. Faɗin fuska taƙi bakwai. Tsayin fuska taƙi sha ɗaya. Idanu sirara a loko. Faɗin baki taƙi biyu.
"Cunduil fari gajere mai dogon kunne. Faɗin fuska taƙi tara. Tsayin fuska taƙi sha biyar. Idanu manya. Faɗin baki taƙi biyar.
"Hussuil fari siriri mai dogon kunne. Faɗin fuska taƙi shida. Tsayin fuska taƙi tara. Idanu koraye. Faɗin baki taƙi huɗu.
"Kanduil fari tittirna mai dogon kunne. Faɗin fuska taƙi goma. Tsayin fuska taƙi tara. Idanu baƙaƙe. Faɗin baki taƙi shida."
Abu kamar wasa Deba suka narke izuwa haske. Aljani A'Barmushe ya haɗiye hasken ya saka a littafin marubutan farko dake hannu ubangidansa Cokali.
"Shoshosho... Deba ko abin sakace?" Inji Cokali. Ya ƙara kyakyatawa cikin farin ciki. Lallai halwar izza ta biya shi.
"Sarauniya Nostaljiya, ai bakya buƙatar ɓata hannunki a wannan..."
Kawai gilmawar babbar izza Cokali yaji ta gefen kunnensa na hagu, lamarinda yasa yai shirun dole. Wannan babbar izza daga takobin Iliyasis take.
Ƙal
Abu na gaba ɗa yaji shi ne ƙarar haɗuwar takobin Iliyasis da Liyurul Linbul. A wani salo mai ban mamaki Liyuru da mutanensa suna tsaye a bayan Cokali kamar basu yanzu aka ɗaure acikin littafin marubutan farko. Kodai fasahar batai ba, ko kuma sunfi ƙarfin littafin, ko kuma suna da tasu fasahar ta kansu. Kai bama anan abin ya tsaya ba, shugabansu Liyuru har yayi amfani da wannan damar ya kaiwa Cokali sara ta baya. Ba daban taimakon Iliyasis ba da tuni kan Cokali ya taɓa ƙasa.
To amma idan ba Cokali akwai Iliyasis. Wato idan Cokali ya kasa Iliyasis zai shige gaba. Kuma shi Iliyasis yana da sirri. Aljaninsa tsuntsu ne mai ɗaukar siffar tsuntsaye. Yana bawa Iliyasis damar juyewa izuwa duk irin tsuntsun da yake so. Kuma tuni Iliyasis ya yanke shawarar tsuntsun da yake so ya koma. Sabida haka ya kira aljaninsa.
"Abu-Nizuru!"
Kan Iliyasis ne ya fara zagwanyewa izuwa haske, sannan ragowar jikinsa. Hasken ya juye izuwa rin tsuntsun nan da akan gani acan doron ƙasa ta bakwai kusa da Babila wanda ake kira da Jurnutu. Shi wannan tsuntsu idanunsa manya ne kamar na mutane. Hasalima yana da fuka-fuki masu ƴan'yatsu wanda suna iya riƙe takobi sukai hari da ita.
Tsuntsu Jurnutu ya juye izuwa tsuntsaye huɗu. Kowanne tsuntsu riƙe da doguwar takobi a fuka-fukansa. Nan take wannan tsuntsaye sukai kan su Liyuru. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci mummunan yaƙi ya kaure. Ƙura ta turnuƙe ba'a hango komai.
Bayan abubuwa sun lafa. Tsuntsu Jurnutu yayi daga-daga da naman su Liyuru. Babu abinda kake gani sai jini yana malala da tsoka gunduwa-gunduwa a ƙasa. Saɓanin Cokali, shi Iliyasis tsayawa yayi ya ƙura musu ido yaga ko zasu sake dawowa. Ai kuwa akan idonsa tsoka ta haɗe da jini. Ɓargo ya tashi ya koma ƙashi, sannan ƙashi ya miƙe izuwa mutun. Liyurul Linbul, Hussuil, Kanduil da Cunduil suka ƙara samuwa. Kayan jikinsu suka koma suka haɗe guri guda. Kai kace dama can babu abinda ya afku. Hasalima izzarsu ta koma dai-dai yadda take ada, wato ko kaɗan bata ragu ba, tamkar yanzu aka fara. A ɓangare guda kuma Iliyasis da Cokali sun fara gajiya sabida amfani da fasahansu.
"SHI FA ZAREN LAIDÁN ZAREN HALITTA NE." Inji Liyurul. Muryarsa a nutse yana shafa dogon kunnensa kai kace kwance yake cikin dakinsa. "Kuna tunanin a banza akai yaƙin sarakunan Jinzidal? Kuna tunanin fasahar jini uku wasa ce? Kuna tunanin shirin shugaba Bihanzin na wasa ne? Ku canja shiri. Ana sane aka bani tsaron wannan gari. Kada ku taɓa tunanin sa'a ko ƙaddara zata sa kuyi nasara akaina."
Garin Faideba
Babban birnin doron ƙasa ta uku
Watanni kaɗan bayan kammala yaƙin sarakunan jinzidal, sarki Hanibal ya canja babban birnin ƙasarsa zuwa garin Faideba, wanda akafi sani da garin farar wuta. Badan komai ba sabida kasancewar garin a tsakiyar ƙasar, sannan kuma a saman tsauni. Zaka iya cewa zaiyi wuyar gaske a kaiwa wannan gari hari ayi nasara. Badan komai ba sabida shiga garin ma matsala ne. Sai ka ɗaga kai sosai zaka hango garin a can ƙololuwar saman tsaunin. Akwai ma'abota izza na musamman wanda aka tanada domin hawa da saukar ƴan kasuwa da sauran mutanen gari cikin garin.
Abin mamakin a dai-dai wannan lokaci wata runduna ce ta mutun dubu goma ke tsaye a ƙasan wannan dutse. Kowannensu zare da takobi suna jiran umarni. Suna sanye da kayan yaƙi: sulke ruwan ɗorawa mai ratsin fari-fari wanda ya rufe dukkan jikinsu daga wuya har ƙasa. Abinda kawai ake gani shi ne fuskokinsu. A gaban wannan runduna Lamarudu Wilbafos shugaban iyalan Wilbafos wanda aka daure a kurkukun bango ne tsaye cikin shiri. Ƙatotuwar Miyura ɗamfare a goshinsa.
A dai-dai wannan lokaci abubuwa ne da dama ke faruwa acikin wannan gari. Mafi muhimmancinsu na cikin ɗakin sarki Hanibal. Manzo Rafiyan Nazára, ɗan tsohon sarkin Jinzidal baba Daljari na zaune akan tagar ɗakin sarki Hanibal hankalinsa a kwance. Kada mai karatu ya manta wannan lokaci dare ne, amma duk da haka akwai kakkauran tsaro a fadar. Sa'annan kuma ɗakin sarkin yana can cikin tsakiyar fadar. Lallai za'ai mamakin yadda Nazara ya isa wannan waje, harma yake zaune abinsa hankali a kwance.
A ɗaya ɓangaren sarki Hanibal na zaune kan kujera yana duban mudubi. Yasan da zuwan Nazara amma tsahon lokaci babu wanda ya ce uffan acikinsu.
To ko mai ya kawo Nazára? Ko yaya lamarin zai ƙarke.
Comments
Post a Comment