Babi na 68: Tarihin Nusi
*Yanzu zamu ɗan ajiye Armad a gefe mu leƙa muga halinda Nusi da Ikenga da kuma Miyurar Armad suke ciki*
-------
Garin Khan
Shekarar 1835 Bayan Amri
*
Acikin babbar kasuwar dake wannan gari wata yarinya ce kimanin ƴar shekaru shida sanye da baƙaƙen kaya wanda kana ganinsu kasan sunji jiki. Tana tafiya da kyar tana iya ƙoƙarinta wajen kaucewa mutane. Tana da duhun fata sannan fuskarta nada tsayi madaidaici. Idanunta na cike da yarinta amma kuma haɗe da rashin tsoro. Tasan cewa bata da kowa a dai-dai wannan lokaci, kuma hanya ɗaya da zata rayu shi ne idan tayi juriya da jarumta ta tsaya da ƙafafunta. Domin kuwa wannan gari ba garin su bane, kuma lallai tayi nesa da gida.
Abu ɗaya kacal da wannan yarinya take iya tunowa a game da iyayenta shi ne rabuwarsu ta ƙarshe, da kuma alƙawarin da mahaifin ta yayi mata na cewa bazai huta ba saiya kaita gida wajen mahaifiyarta.
Sai dai kuma kash, wannan yarinya tasan cewa a matsayin ta na ƴar ƙabilar Djinn komawa gida a wajenta abu ne mai wahala. Domin kuwa garinsu mai suna Shaniza an ƙulle ƙofofinsa sama da shekaru ɗari da suka gabata, sannan kuma an katange bangwayensa daga dukkan halittu, mutun ko aljan ko dordor. Amma abin mamaki wannan yarinya tana jin yaƙini zata koma gida watarana. Kuma lallai baza ta mutu ba sai taga mahaifiyarta wadda ke cikin garin Shaniza. Sunan wannan yarinya Nusi, Nusi Djinn.
Wata biyar kenan da babanta ya barta a hannun abokinsa domin ya kula da ita a yayinda shi kuma ya tafi domin gamuwa da wata tawaga, amma ƙaddara ta ratsa, sai gawarsa aka dawo da ita. Koda abokin baban nata ya tabbata a yanzu babu wani abu da zai samu saiya kore ta daga gidansa, lamarinda yasa watanta uku kenan cir tana rayuwa akan titi. Abincin da zata ci ma wahala yake mata. Sauƙi ɗaya kacal da take samu shi ne abokanta guda biyu wato Iliyasis da Cokali, wanda suma yara ne sa'anninta wanda suke bin titi a sakamakon siyar da iyayensu da akai a cinikin bayi na wannan shekara.
Nusi na tafe kanta na nazarin mutanen dake gefenta. Daga ganin yadda take ɓoye fuska kasan akwai wanda take gujewa. Ba jimawa tasha wata kwana inda babu mutane da yawa. Tana shan kwanar ta fara gudu inda ta ƙara shan wata kwanar dai-dai gefen wata bola inda babu mutane da yawa. Da yake magariba ce kuma duhu ƴaɗan fara yi da kyar ta iya hango wasu yara dake laɓe a bayan wani ƙaton kwanon zuba shara dake gaba da ita.
Nan da nan ta isa wajen yaren, inda suka ƙura mata ido cikin tsammani suna jira suji mai zata ce. Ita kuwa Nusi sai ta canja fuska zuwa kalar tausayi, lamarinda yasa nan take jikin waɗannan yara yayi sanyi. Koda taga haka saita fashe da dariya tana cewa, "Wululu... Tsokanarku nake na samo..."
Wannan yara dai ba wasu bane illa Iliyasis da Cokali. Dukkaninsu suna yara, Cokali irin yaran nan me masu ƙiba da kumburarriyar fuska mai ɗauke da kalar tsoro, amma Iliyasis siriri ne mai tsayi kuma yafi Nusi haske sai dai kuma shima Cokali ya fishi haske.
Nusi ta zira hannu acikin tsohuwar rigarta ta futo da ƴar jaka mai ƙunshe da kuɗaɗen Ayrid. Suna ganin haka sukai tsalle suka rungume Nusi cikin farin ciki, haƙarsu ta cimma ruwa. Nusi ta zira hannu a cikin jakar ta lissafa Ayrid ɗai-ɗai har guda ashirin ta miƙawa Iliyasis. Sannan ta ƙara miƙawa na Cokali Ayrid ashirin. Sannan itama ta ɗebi ashirin. Amma duk da haka jakar na nan cike da Ayrid ko rabi basu ɗiba ba.
"Ƴar uwa mai za'ai da ragowar?" Suka tambaye ta cikin mamaki.
"Mayar masa zanyi. Dama aikin da mukai masa na wata biyu akan kuɗi Ayrid ashirin-ashirin ne. Tunda yaƙi biyanmu ba laife bane idan muka kwaci kuɗinmu, amma bai kamata mu ɗebi sama da haka ba."
Daga ganin fuskar Iliyasis da Cokali basu yadda da wannan mataki ba, amma tunda ita ta ɗakko kuɗin babu yadda zasu yi. Iliyasis ya buɗe baki ya ce, "To ta yaya zaki mayar masa? Kinsan za'a iya kama ki fa tunda yanzu na tabbatar yasan kuɗinsa baya nan, kina mayarwa zai gane ke kika ɗauka."
Nusi ta kyaɗa kai, "Eh haka ne, amma dai duk da haka sai an mayar masa. Wataƙila amma sai gobe. Yanzu muje mu ci abinci mu siyi kayan sawa mu kuma nemi wajen kwana. Wataƙila zamu samu ko ɗaki ɗaya ne da kuɗinmu."
Su ukun suka juya suka nufi hanya domin suje su ci abinci. Da wannan kuɗi nasu suka samu suka siyi abinci kuma suka kama wajen kwana.
Sun kwana cikin farin ciki a wannan rana, ko ba komai sun kwana acikin ɗaki sannan kuma cikinsu a cike da abinci.
------
Washe gari bayan isha duhu ya fara yi, ƙasaitaccen ɗan kasuwarnan mai suna Ɗan-darbejiya yana tafe zai koma gida bayan rufe shaguna. A kewaye dashi akwai zaratan samari uku majiya ƙarfi waɗanda aikinsu kawai su kare shi. Fuskar Ɗan-darbejiya na rufe da ƙasumba da gemu amma hakan bai hana baƙin cikin dake lulluɓe da ita bayyana ba. Kuma zaka fuskanci lallai Ɗan-darbejiya yana da dalilin yin baƙin cikin idan ka lura cewa jiyan nan yayi asarar dukkan ribar da ya samu ta gaba ɗaya watan. Babban abinda yake ciwa Ɗan-darbejiya tuwo a kwarya shi ne bai masan yadda akai kuɗin suka ɓace ba. A iya tunaninsa bai taɓa yarda ko da Ayrid ɗaya ba a tsahon rayuwarsa. Hasalima saboda san kuɗi na Ɗan-darbejiya yana da shaguna sama da goma amma yana tafiya yana kallon hanya ko zaiga wani ya yadda kuɗinsa ya tsinta. A cewar Ɗan-darbejiya duk wanda ya yarda kuɗi baya so ne. Abu ne sananne duk wanda yayi wa Ɗan-darbejiya aiki to da wuya kuɗinsa su fito, hakan nema yasa duk ƴan kwadagon kasuwar suke gujewa yin harka dashi. Kuma dalilin da yasa Ɗan-darbejiya yake saka yara ƙananu aiki domin kada ya biya kuɗi da yawa.
Kwanakin baya ya saka Nusi da Iliyasis da Cokali aiki. Kuma daga bisani ya hanasu kuɗin. Su Nusi sukai jele har suka gaji suka daina zuwa. Amma kwanaki huɗu bayan sun ɗauke ƙafa Ɗan-darbejiya ya wayi gari aljihunsa da yake saka kuɗaɗensa ya yage kuma kuɗinsa sun faɗi a tsakiyar kasuwar. Ɗan-darbejiya yai rigimarsa ya gaji, amma babu wanda zai kama a tsakiyar kasuwa. Hasalima da dama suna tunanin Ɗan-darbejiya haɗa labarin kawai yayi domin kada ya biya bashin da ake binsa.
To abinka da yarinta, tunanin yara ƴan shekara shida zuwa takwas bashi da ƙarfi. Kawai Ɗan-darbejiya yana tafiya yana saƙe-saƙe a ransa saiga ƴar sakarsa da yake ajiye kuɗi ta yiwo tsalle daga sama ta faɗi a gabansa. Ai kuwa tunma kafin yayi magana ƙarti biyun dake kewaye dashi suka rankaya a guje zuwa wajen da wannan jaka ta taso.
Su Nusi dai sune suka cilla wannan jaka da danƙo, kuma suna cilla ta suka rankaya a guje suka sha kwana. Amma suna cikin gudu saiga ɗaya daga cikin ƙartin ya bayyana a gabansu, lamarinda yasa suka juya da gudu, amma suna juyawa suka iske ɗaya ƙaton tsaye a bayansu an saka su a tsakiya.
Ƙaton gardin dake gabansu yai dariya gami da kyaɗa, "Hahaha.... Nusi, Iliyasis, Cokali, dama na gayawa oga kune kuka saci kuɗin nan yaƙi yadda."
Na bayan yai wata dariyar mugunta tare da cewa, "Hukuncin sata kisa."
***
Babi na 69: Tarihin Nusi(2)
------
Dukkanin wannan ƙarti biyu dake kewaye dasu Nusi Izzarsu akan shekaru casa'in da tara take. Na gaban ya taka a hankali ya isa gaban su Nusi, a yayinda su kuma suke ta janyewa suna ƙara takurewa a tsakiya cikin tsoro. Gaba zaki baya damisa.
Yana isa saitin Nusi ya zaro wuƙa samfurin zabira, sannan ya finciko Nusi yana cewa, "A fuskarka zan rubuta miki ɓarauniya, kinga daga yau koda oga yaji tausayinku ya ce kada a kasheku nayi miki sheda."
Babu abinda Nusi take sai karkarwa fuska cike da tsoro, amma wannan sadauki ko a jikinsa, babu ko alamun wasa ko tausayi a tattare dashi. Kana ganin yadda ya ɗaga wuƙar kasan lallai bashi da niyyar tsayawa.
Sai dai kuma a dai-dai wannan lokaci ne komai dake wannan waje ya tsaya cak tamkar wanda aka tsayar da lokaci. Wannan sadaukai biyu dake neman halaka su Nusi suka ƙame ƙam, idan ka kalli wannan sadauki mai wuƙa a hannunsa zaka ganshi tsaye da wuƙa riƙe akan iska tamkar hoto. Na bayan shima ya ƙame a dai-dai inda yake. Da Nusi da Iliyasis da Cokali duk ba wanda yasan inda kansa yake. Ana cikin haka wannan sadaukai biyu tare da shugabansu, Ɗan-darbejiya, suka fara aman jini baƙi-ƙirin. Kan kace meye wannan tuni sun isa lahira.
Duk abinda ke faruwa su Nusi basu san me ake ciki ba. Kuma abu na gaba da suka gani shi ne bayyanarsu acikin wani katafaren gida mai yawan bishiyu da sanyin ni'ima. Kuyangi da sauran bayi suna ta kai-komo acikin hidima. Idan da Armad yana nan da kallo ɗaya kacal zai yiwa wannan gida ya gane cewa wannan shi ne gidan da suka zauna da Nusi watannin baya.
Su kuwa su Nusi da Iliyasis da Cokali tuni sun farfaɗo kuma suna zaune acikin ɗaki mafi alfarma acikin wannan gida. Kewaye dasu abinci ne irin wanda basu taɓa gani ba. Abin ka da yarinta kuma ga yunwa, babu wani tunani haka suka afkawa wannan abinci. Bayan da suka kammala saiga wata farar kuyanga nan tayi sallama a garesu. Kunyangar na shigowa su Nusi sukai tsalle suka jada baya cikin tsoro. Amma kuyangar kawai murmushi tayi, sannan kuma ta tambayesu ko suna buƙatar ƙari.
Nan take duk su ukun suka ƙurawa wannan kuyanga ido cikin tsananin mamaki. "Ƙari??"
Cokali ne ya fara yin magana, "a ƙaro, wallahi ban ƙoshi ba. Rabona da abinci tun ina yaro...."
Wannan kuyanga tayi iya ƙoƙarinta amma ta kasa riƙe dariyar dake wuyanta. Koda ganin wannan kuyanga tayi dariya, sai itama Nusi tayi murmushi. Lallai ga dukkan alamu ba gidan yankan kai suke ba.
Nan take wannan kuyanga ta tafa hannu, inda wasu kuyangin guda uku suka fara safarar kwanuka izuwa wannan ɗaki. Ba jimawa Nusi da Cokali da Iliyasis suka ƙara afkawa waɗannan kwanuka. Lallai baza kaga laifin su Nusi ba a wannan hali, domin kuwa da yunwa ta kashe ka kwanda daɗi ya kasheka. Ko manya sun san haka. Sannan kuma basu da tabbashin daga wannan rana zasu ƙara samun irin wannan abinci. Wataƙila ma shikenan haihata-haihata.
Wannan kuyangar ta ɗanyi kyaran murya, lamarinda ya ja hankalin su Nusi suka ɗaga kai daga wannan kwanuka suka kalleta, "Idan kun gama akwai tafki na wanka mai cike da ruwan zafi. Kuyangi suna ciki suna jira suyi muku wanka."
Cokali ne ya ƙara yin magana da ƴar kumburarriyar fuskarsa cike miya caɓo-caɓo. Lallai kallo ɗaya zakai masa ka fashe da dariya. "Wanka???!!! Iliyasis yaushe rabonka da wanka."
Iliyasis ya harari Cokali, "Kai yaushe rabonka? Nusi ce kaɗai tayi a wannan satin, har gwanda nima nayi wancan satin. Kaifa?"
Duk su ukun suka fashe da dariya. Ko a mafarki basu taɓa tunanin samun irin wannan daula ba, kuma lallai basu da niyyar yin tunanin daga ina wannan daula take har sai sunyi hani'an. Haka kuwa akai, kwata-kwata basu fara tunanin matsaloli ba sai washegari bayan sun tashi daga baccin awa ashirin da sukai akan wani katafaren gado na alfarma. Duk su uku acikin fararen kaya irin na bacci. Iliyasis ne ya fara tashi, sannan Nusi.
Su biyun suka kalli ƙasaita ta cikin wannan ɗaki sannan suka kalli junansu cikin damuwa. Iliyasis ya numfasa ya ce, "ba dai abinda nake tunani kike tunani ba?"
Nusi ta kyaɗa kai, lallai duk abu ɗaya suke tunani. Waye ya kawo su nan? Kuma maiya faru dasu Ɗan-darbejiya? Ina ne wannan gida da suka tsinci kansu?
Ba jimawa suka tashi Cokali, fuskarsa cike da yawun bacci suka labarta masa cewa akwai matsala. Abu kamar wasa Cokali ya buɗe baki ya ce, "amma dai ba'a gidan yankan kai muke ba ko? Ba siyar damu akai ba? Ina ne nan?"
Ba jimawa tsoro ya cika su duk su ukun, inda kafin kace meye wannan tuni sun cure a ƙarshen gadon suna leƙe-leƙe. Kafin wani lokaci tuni sun fara lissafe-lissafen yadda zasu tsere daga wannan gida. Suna cikin haka sai suka ji an buɗe ƙofar ɗakin. Suna tsammanin suga wannan farar kuyanga sai suka ga wani farin saurayi mai yawan gashi. Lallai tsayin gashinsa ya haura na mata da yawa a wannan zamani, domin kuwa yakai har gadon bayansa. Sai dai abin mamakin gashin nasa launin ja ne, jajawur. Yana sanye da baƙar alkyabba. Yana shigowa ya nemi waje ya zauna, sannan yayi murmushi a garesu.
Duk su ukun suka ƙame a waje ɗaya, ko numfashi basa iya yi sosai ballantana magana.
Saurayin ya fara magana cikin lafazi mai ɗauke da tsantsar Izza da kamala, "suna na Yarima Niyashi. Ni ne na ceto ku daga waɗancan mutane dake neman halaka ku. Sannan kuma ni ne na kawo ku wannan gida."
"Y....yarima Niyashi?? Kai.... ne Yarima Niyashi?" Iliyasis ya fara magana cikin ƙinƙina, domin kuwa indai abinda yake tunani haka ne to kuwa lallai suna ganawa da ɗaya daga cikin waɗanda ake yiwa kallon su zasu iya mulkar duniya anan gaba. A duk faɗin ƙasa bakwai mutun ɗaya ne mai suna Yarima Niyashi wanda keda irin wannan jan gashin, saboda haka Iliyasis bai ɓata lokaci ba ya dubi wannan saurayi ya ce, "Yarima Niyashi, ɗan sarkin Jinzidal, Rafiya, na daular Infiriya?"
Saurayin yayi murmushi, tare da kyaɗa kai. Alamun haka ne.
Cokali ya ja rigar Iliyasis cikin tsoro, "Wane ne? Kasan shi?"
Iliyasis bai kula da Cokali ba ya ci gaba da magana, "to amma mai kake yi a daular Maikironomada? Na tabbatar duk wanda ya ganka anan cewa zaiyi leken asiri kazo."
Wannan saurayi ya ɗan numfasa tare da juyawa ya kalli Nusi wadda tai shiru tana tunane-tunane, ga dukkan alamu ita ma ta gane wane ne wanna saurayin.
Kafin daga bisani saurayin yayi mata magana, "Tsahon lokaci ina nemanki, Nusi Djinn."
***
Babi na 70&71: Cokali da Iliyasis sun shiga duniya
Nusi ta ƙara jada baya cikin tsoro, inda ta ɓoye a bayan ƙibar Cokali. A wannan rana ta gane cewa hatta ƙibar Cokali nada ranarta. A ranta tama kasa gane maike faruwa. Ta yaya za'ace wai ɗan sarkin babbar daular Infiriya yana nemanta? Wai tayaya ma akai ya santa? Dududu shekarunta shida kacal a duniya, kuma acikin waɗannan shekaru bata taɓa yin inda hanyar daular Infiriya take ba, ballantana ace ta gamu da ɗan sarkin dake mulkin wannan daula, harma ace wai yana nemanta. Lallai koma wanne laifi ta aikata yana da girman gaske, tunda har za'ace ɗan ɗaya daga cikin sarakuna biyar na Jinzidal ya taso ƙafa-da-ƙafa yana nemanta.
"Kada kiji tsoro." Muryar yarima Niyashi ta shiga kunnenta tamkar ana busa algaita. "Banzo danna cuce kiba. Nazo ne danna taimake ki. Amma kiyi sani cewa a halin yanzu bani da ikon gaya miki tayadda akai na sanki ko kuma mai yasa nake nemanki, duk da kuwa nasan wannan tambayoyi sune suke yawo akanki. A halin yanzu wannan gida da muke ciki naki ne halak-malak. Bama gidan ba kaɗai, tare da duk abinda ke cikinsa. Sannan kuma akwai kuɗin Ayrid kimanin miliyan ɗaya dana bari wanda zaku yi amfani dashi zuwa sanda zan dawo. Na bar umarni mutanen cikin wannan gida zasu yi muku shaidar zama cikakkun ƴan garin nan kuma zasu saka ku a makarantar koyon Izza. Akwai mutanen mu wanda zasu kula dake har zuwa sanda zan dawo."
Koda yarima Niyashi yazo nan a zancensa sai ya miƙe ya gabato izuwa gaban wannan gado dai-dai inda Nusi maƙale a bayan Cokali tayi kalar tausayi. Koda ganin haka sai Iliyasis yai tsalle ya dira a gabanta, wato ya shiga tsakaninta dashi.
Iliyasis yai ta maza ya buɗe baki ya ce, "Bazan bari kayiwa ƙanwata wani abu ba indai inada rai."
Abin mamaki saiga Cokali shima yai tsalle ya dira a gefen Iliyasis, inda gadon yai wata ƙara ƴana neman ɓallewa saboda nauyi. Hannun Cokali na karkarwa, ƙaton cikinsa na sama da ƙasa saboda tsabagen nishi, yana ƙinƙina yana cewa, "ni....ma... b...bazan bari k...ka taɓa taba. Kwandama ka tafi ko kuma ka tafi." Koda Cokali yazo nan a zancensa amma Niyashi bai tsaya, sai nan take haƙoransa suka fara karkarwa tamkar wanda aka tsoma acikin dusar ƙanƙara.
"Baza ka tsaya!!!" Cokali ya kwala ƙara mai kama da kuka. Amma Niyashi yai kamar baiji shi ba yaci gaba da tafiya. Yana ƙarasowa saitin Cokali ya tsaya, inda ya juyo da kansa ya kalli Cokali. Abun mamaki suna yin ido-da-ido Cokali ya faɗi ƙasa sumamme saboda tsananin tsoro. Sannan ya tafi gadan-gadan zai faɗa ƙasan gadon. Haka na faruwa Niyashi yai sauri ya taroshi tare da fashewa da dariya. Yana cewa, "Haha... lallai Nusi kina da wanda zasu kare ki ba saina damuba." Yana rufe baki ya shafa fuskar Cokali ya farfaɗo dashi ta hanyar ɗalasimai. Sannan ya juya ya fice daga ɗakin yana dariya.
---------
Tun daga wannan rana basu ƙara ganin Niyashi ba, tun suna tsoron wannan ƙaton gida har suka saki jiki. Duk abinda suke buƙata akwai aciki, sannan idan zasu fita akwai bayi jarumai dake kula dasu. Ba daɗewa suka zama tamkar wasu ƴaƴan attajirai a wannan gari na Khan. Suka shiga babbar makarantar Izza dake wannan gari na Khan.
Abu kamar wasa suna jira Niyashi yazo amma baizo, bashi ba alamunsa. Rani yazo, kaka tazo, bazara tazo, akai hunturu sannan damuna ta kewayo. Sannu a hankali har sunyi shekara ɗaya a wannan gida. Abin mamaki duk su uku tamkar an haɗa baki suka zamanto masu matuƙar ƙoƙari a makaranta. Sannu a hankali a kwana a tashi wata shekarar ta wuce. Iliyasis ya zaɓi ɓangaren takobi a makaranta, shi kuma Cokali ya zaɓi ɓangaren aljanu da zanunnuka. Nusi kuwa ta zaɓi ɓangaren Izza da dabarun yaƙi na daular Maikironomada.
Sannu a hankali a wannan hali saida sukai shekaru tara cif, harma sun fara mantawa da labarin Niyashi. Ranar nan kwatsam sun dawo daga makaranta su uku sai babbar hadima mai yi musu hidima a gidan tace musu suna da baƙo idan sun shirya.
Dukkaninsu sukai tunanin bazai wuce ɗaya daga cikin masu zuwa gida yanai musu karatu ba, saboda haka ko a jikinsu. Suka shige izuwa sashinsu sukai wanka suka kimtsa a hankali sannan can yamma suka bayyana a falon gidan.
Nusi na sanye da doguwar riga samfurin daular Maikironomada mai ɗauke da bezar gashin zaki. Babu abinda take sai sheƙi. Kyawunta ya bayyana matuƙa a wannan lokaci, domin kuwa tuni Nusi ta cika ƴar shekara sha biyar da haihuwa a duniya. Ga dogon gashinta yana kwanciya akan kyakkyawar fuskarta mai ɗan duhu.
Cokali ya ɗan rage ƙiba, amma duk da haka yana da tumbi da kuma da manyan gaɓɓai. Shi kuwa Iliyasis kamalarsa da nutsuwa ta ƙaru. Yana rataye da takobinsa launin ja.
Abinda suka gani basu yi tsammani ba, domin kuwa ba kowa bane a zaune acikin wannan falo ba illa yarima Niyashi. Hannunsa ɗauke da jaridar kamfanin Maikiro ta wannan sati.
Dukkaninsu suka gabato izuwa gareshi fuskokinsu cike da damuwa, duk da kuwa babu sauran tsoro a tattare dasu. Abu ɗaya da suka sani shi ne idan da Niyashi yaso halaka su da tuni hakan ya ɗaru tun shekaru tara da suka wuce.
Yana ganinsu ya miƙe fuska cike da murmushi yana cewa, "Ahh.. duk kun girma. Nusi... dube ki har kin kamo ni tsayi. Cokali kaima....."
Amma a dai-dai wannan lokaci da Niyashi ya ajiye jaridar data rufe masa fuska suka ga fuskarsa sosai sukai tiris suka cake a inda suke, baki a buɗe. Niyashi yana nan dai-dai da dai-dai yadda suka ganshi shekaru tara da suka wuce. Da daida girma ko kuma canji na kwayar zarra babu a fuskarsa. Hasalima sai kace sa'ansu ne koma sun girme shi. Musamman ma Iliyasis da yake da kamannin manya lallai zaka ce ya girmi Niyashi.
"W...ane ne kai? Maike faruwa?"
Wannan kawai shi ne abinda duk su ukun suka buɗe baki suka cewa Niyashi cikin mamaki da ɗimuwa.
Amma Niyashi yai murmushi tamkar ba wani abu ya ce, "kada ku damu, sannu a hankali zan baku labari na. Amma ba yanzu ba. Kamar dai yadda kuka gani bana tsufa kuma shekaruna sun tsaya cak tun daga ranar da na cika shekara sha shida a duniya. Babu wanda yasan wannan labari daga ƴan gida na saiku. Kuma abinda ya kawo ni nan a wannan lokaci shi ne ina so kuyimin alƙawari cewa baza ku gayawa kowa ba. Baza ku gayawa kowa kun sanni ba, sannan kuma baza ku gayawa kowa wannan labari nawa na rashin tsufa ba. Idan kukai min wannan alƙawari to ni kuma zanyi muku alƙawarin taimakon ku a duk lokacin da kuke buƙatar taimako, sannan kuma zanyi muku bayanin komai akan dalilin da yasa nake neman Nusi da kuma dalilin da yasa bana tsufa idan lokaci yayi."
Duk su ukun suka kalli juna suna mamaki wannan abu. Iliyasis ne ya fara magana, "To mai yasa bazaka gaya mana yanzu ba?"
Niyashi ya amsa yana murmushi, "Saboda bazan iya ba."
Nusi ta tari numfashinsa tace, "Zanyi alƙawari, amma idan kayadda cewa zaka amsa min tambaya ɗaya."
Niyashi ya ce, "Wacce tambaya ce?"
Nusi tace, "Ka gayamin, shin kasan mahaifina?"
Niyashi yaja dogon nimfashi tare da sunkuyar dakai, baya so ya amsa wannan tambaya, amma ga dukkan alamu Nusi ta daɗe tana so tayi masa wannan tambaya, kuma baza ta amince da wannan alƙawari nasa ba idan bai amsa mata ba, saboda haka a ƙarshe ya buɗe baki yace, "Nasan shi. Amma bazan gaya miki komai akansa ba yanzu."
-------
To daga wannan rana Nusi da Cokali da Iliyasis da Niyashi suka ɗaura wannan alƙawari. Niyashi ya daɗe acikin wannan gida suna tare a wannan karan, amma bayan ɗan ƙokaci ya ƙara tafiya ya koma daular Infiriya. Kuma tun daga wannan rana har zuwa sanda Nusi ta zama ɗaya daga cikin manyan ɗalibai masu hazaƙa a daular Maikironomada basu ƙara haɗuwa da Niyashi.
Nusi tana ƴar shekaru sha tara ta shiga takarar jarabawar da zata bata dama ta zamo ɗaya daga cikin waɗanda za'a ɗaukaka matsayinsu a daular Maikironomada. Jarabawar da ta kaita inda suka haɗu da Armad a shekarun baya. Jarabawar da ta canja rayuwarta har abada.
Nusi bata ƙara ganin yarima Niyashi ba sai a gasar Jinzidal. Tayi mamaki sanda ta ganshi yana nan dai-dai yadda ta sanshi shekaru goma sha da duka wuce. Kuma taso su gana dashi amma Niyashin bai amince ba. A cewarsa akwai kunnuwa a binne a ƙarƙashin ƙasa, da kuma idanu a kafe a sararin samaniya wanda baya so suji ko kuma su ganshi tare da ita.
---------
Iliyasis na tsaye rataye da takobinsa yana kallon ƙaton mutun-mutumi na Al-yaya a bakin ƙofar garin Khan. A gefensa Cokali ne tsaye shima yana kallon wannan mutun-mutumin. Abin mamaki basu kaɗai ne tsaye suna kallon wannan mutun-mutumi ba. Mutane sama da ɗari biyar kallonsa kawai suke suna kuma kallon jaridun dake hannunsu. Babu abinda kake ji sai hayaniya. Wataƙila ace ba abin mamaki bane aga mutane suna kallon wannan mutun-mutumi ba, tunda sama da shekara ɗari mutun-mitumin gida shida ne a ƙofar garin na Khan, amma ƴan watannin baya kaɗan na bakwai ya ƙaru. Lallai maza da mata zasu so suje suga wannan sabon mutun-mutumi da ake cewa na wani kyakkyawan saurayi ne.
Sai dai kuma abin aljabin shi ne wannan sabon mutun-mutumi yana tsaye ɗaure a kansa da ɗan kyalle. A saman hannunsa na dama walƙiƴa ce take ta ci tana balbali. A hannunsa na hagu kuwa takobi ce tsirara. Idanun wannan saurayi sunyi kama dana jakadun mutuwar ƙarni na farko. Gashin kansa baƙi ne, wani a kwance wani a tsaye. Idan ka matsa kusa zaka gane cewa wannan yaro ba wani bane illa Armad Wilbafos. Kuma shi ne acikin shafin wannan jarida da mutane suke ta kallo suna hayaniya. A saman wannan hoto nasa ga kuɗi nan ansa har Ayrid sama da miliyan.
Iliyasis ya dubi Cokali ya ce, "Lallai Ururu sunji labarin wannan mutun-mutumi shi yasa suka zabga wannan kuɗi akan Armad. Amma dai a halin yanzu ya zama dole mu nemeshi a duk inda yake, domin kuwa shi kaɗai ne zai iya gaya mana taƙamaimai inda ƴar uwarmu Nusi take. Amma na yarda da shawararka, mu fara zuwa daular Infiriya mu tuntuɓi yarima Niyashi muji ko yasan inda take."
Cokali ya kyaɗa kai, "To mai muke jira, mu ɗau hanya kawai. Mu da dawowa wannan gari sai sanda muka ganta, ko kuma mu mutu muma nema, domin kuwa ita ma haka zatai mana idan mune muka ɓata."
A wannan shekara Cokali da Iliyasis suka shiga duniya neman ƴar uwarsu Nusi Djinn.
***
Babi na 72: Sarauniya Nusi
----------
Taro yakai taro. Dukkanin wanda ya isa a sashin ikwatora dake bisa doron ƙasa ta shida ya halacci wannan taro. Sahu-sahu na mutane yakai sahu dubu, sannan kuma ga sahu-sahu na Dordor da ƙabilunsu. Dukkanin waɗannan mutane a durƙushe suke bisa gwiwowinsu, kayikansu sun fuskanci ƙasa suna sauraron abinda limamin wannan taro yake faɗa.
Shi kuwa liman yasha doguwar alkyabba samfurin mutanen Ikwatora. A kewaye dashi sarakuna ne guda shida, kowanne na wakiltar ɗaya daga cikin shida na ƙasashen da suka haɗa sashin Ikwatora. Daga tsakiyarsu wata kyakkyawar budurwa ce mai tsananin kyawu irin na mutanen farko. Fatar ta baƙa ce, idanuwanta dara-dara masu kyau da kwarjini. Dogon gashin kanta kuwa anyi masa ado irin na sarakunan Ikwatora. Idan da Armad na wajen zaice wannan budurwa ba wata bace illa Nusi Djinn. Wannan ita ce ranar rantsuwa, ranar da za'a rantsar da Nusi a matsayin ɗaya daga sarakunan shida dake mulkin Ikwatora.
A lokacinda waje yayi tsit tayadda koda kiyashi ne ya gilma za'a ji, sai liman ya kyara murya sannan ya fara karanto ɗalasiman rantsuwa, "A yau ni limamim Baƙar Guguwa na Tsibirin guguwa a doron ƙasa na shida na naɗa Nusi ƴar gidan Djinn a matsayin sarauniyar Ikwatora, mai kare Tsibirin guguwa, mai kula da ƙabilar mutane da Dordor. Ranki ya daɗe, sarauniya. ALLAH yaja kwana."
Koda yazo nan a zancensa sai dukkan dubunnan mutanen nan da Dordor suka haɗa baki suka amsa, "RANKI YA DAƊE SARAUNIYA. ALLAH YAJA KWANA."
A wannan waje a wannan rana ta laraba 1855Bayan Amri aka rantsar da sarauniya Nusi Djinn. Biki ya fara gudana har tsahon kwanaki tara. Sannan aka raka Nusi izuwa fadar ta dake garin Dula dake tsakiyar garuruwan dake doron wanann sashi na Ikwatora.
---------
Kwanaki takwas bayan wannan gagarumin biki Nusi na zaune akan karagarta, kewaye da ita ƴan majalisarta ne guda uku suna tattauna al'amuran mulki.
Ƴan majalisar mata sun haɗa da wazirinta wanda ya fito daga ƙabilar jajayen Dordor masu kai ɗaya. Ana kiransa da suna Saiza. Sai kuma galadima mai suna Naru, wanda dogo ne mai doguwar haɓa da yawan farin gashi. Sai kuma muƙamin da ake kira da Sarkin Bai, wanda shima jinsin mutun ne akai mai suna Rayaya. Rayaya mutun ne gabjeje mai faɗi da manyan kafaɗu. Kana ganinsa kaga sadauki ragowar samudawa.
Rayaya shi ne kamar sarkin yaƙi domin kuwa sarautar sarkin Bai ita ke kula da mayaƙan daular. Rayaya yayi kyaran murya ya fara jawabi, "muna da mayaƙa ma'abota Izza kimanin dubu goma sha tara. Kowanne yana ƙarƙashin ikonki kuma zai bada rayuwarsa a gareki."
Waziri Saiza yai kyaran murya ya ce, "muna da garuruwa biyar a wannan doron Ikwatora wanda kowanne yake da mutane tsakanin dubu ɗari zuwa dubu ɗari biyu, wanda duk suna ƙarƙashin ikonki, sarauniya."
Galadima Naru ya buɗe baki ya ce, "muna da rumbu na abinci da abin sha wanda zai ishemu nan da shekaru uku masu zuwa koda bamu yi noma ba. Sannan kuma ƴan uwanmu Dordor wanda suka fi sha'awar nama ɗanye akwai dazu ka na farautarsu da aka killace na musamman."
Nusi tai kyaran murya duk sukai shiru, sannan ta ɗago kai ta dube su tana mai cewa, "kafin muje ga bayanin mulki akwai abinda nake so kuyimin. Ina so ku samo min wani mutun, sunansa Armad Wilbafos. Ina so nasa kuɗi akansa yadda duk inda yake zamuji labari. Iyakacin nawa ne yawan kuɗin da zan iya amfani dasu a lalitar kwamnati?"
Waziri da galadima da sarkin Bai suka kalli juna tsahon lokaci sannan daga bisani galadima Naru ya amsa da cewa, "Sarauniya zaki iya amfani da kuɗi har Ayrid dubu ɗari tara ba tare da kin tambayemu ba, amma duk abinda yakai miliyan ɗaya zuwa sama sai an tattaunashi a majalisa."
Nusi tayi murmushi, tana ji a ranta ta samu dama da zata kawo dukkanin wanda take so a duniya kusa da ita suci duniya da tsinke. Nan take ta buɗe baki ta fara jawabi, "Armad Wilbafos, ga hotunansa." Ta fito da zanen Armad ta miƙa musu tare da cewa, "ku saka masa Ayrid dubu ɗari tara yadda zamu yi sauri mu gano shi. Ina son duk inda yake a nemo min shi."
"An gama, Sarauniya. Amma muna buƙatar bayani akansa na wajen da kika rabu dashi na ƙarshe, da asalin ƙasarsu da ƴan uwansu da danginsu. Wannan bayanai sune zasu taimaka mana wajen nemoshi."
Nusi taja numfashi amma sai suka ga tayi shiru ta kasa cewa komai.
"Armad... Wilbafos? Hmmm...." Nusi ta ƙara jan dogon numfashi tare da tuna ranar farko da suka haɗu da Armad. Amma daga ƙarshe ta kasa cewa komai. Babu abinda take ji sai ƙunci da ciwo idan ta tuno yanayin yadda suka rabu da Armad. Tana baƙin cikin yadda ta kasa kareshi, sannan kuma tana baƙin cikin yadda tabarshi a wajen Ururu. Lallai tun daga ranar da suka rabu babu wata rana da batai tunanin Armad ba.
Koda ganin halinda sarauniya Nusi ta shiga sai waziri Saiza yai kyaran murya ya ce, "sarauniya ta ba saikin gaya mana wane ne ba, kawai dai ki gaya mana wanne gari ne asalinsa saboda musan ta ina zamu fara dubashi."
Nusi ta amsa da cewa, "Doron ƙasa ta uku sashin arewa."
Suna jin kalmar doron ƙasa ta uku sashin arewa duk su ukun suka zare ido cikin mamaki tare da sakin baki. "Ehmm....? Mai kika ce sarauniya? Doron ƙasa ta uku?"
Nusi ta haɗe gira tana mamakin dalilin daya basu mamaki. "Eh mana doron ƙasa ta uku sashin arewa, akwai matsala ne?"
Koda jin haka waziri Saiza yai sauri ya tambayi Nusi, "Sarauniya, daga wacce ƙasa kika fito?"
"Ƙasar Maikironomada, doron ƙasa na biyar sashin arewa." Nusi ta amsa a nutse.
Amma bisa mamaki kafin ta gama amsawa duk ƴan majalisar ta uku sun rikice sun faɗi ƙasa daga kan kujerunsu. Nusi ta haɗe rai ta daka musu tsawa, "Kai wai mai kuke yi ne, ku gayamin maike faruwa."
Nan take Waziri Saiza ya fara amsawa cikin ƙinƙina, "D....daga ƙ....ƙasa ta biyar kike? Sashin arewa? Nayi tunanin haka da naga na kasa gane daga wacce ƙaɓila kike amma tunda nasan ba abu mai yiwuwa ba saina manta kawai. Sannan kuma a tsarin mulkinmu haramun ne tambayar sarki ko sarauniya asalinsu shi yasa ban tambaya ba. Amma lallai muna cikin garari, akwai abinda kike da buƙatar ki sani cikin gaggawa. Sarkin Bai sanya a naɗa mana sirdi izuwa Bangon arewa."
Galadima ya juyo ya fuskanci Nusi, "Sarauniya ta ina ganin ya kamata mu ɓoye kamannin mu kada wani yasan inda zamu je. Tayadda babu wanda zaisan mai ake ciki sai iyakacin mu."
Sarkin Bai da waziri suka amince amma Nusi har yanzu ta kasa gane mai ake ciki.
Tuni duhu ya fara yi sanda suka suka fito. Suna fitowa suka haye dawakin da aka ajiye musu suka rankaya izuwa Bangon arewa domin nunawa Nusi abinda ya firgita su. Ita kuwa Nusi tama rasa mai zata ce. Amma ta ƙudure a ranta lallai idan abinda zasu gaya mata ba wani babba bane saita hukunta su.
Kwanansu uku suna sukuwa kafin su isa izuwa wannan Bango. Nusi taga irin girman wannan ganga ta ruwa tana ta ambaliya tana zuba izuwa ƙasa. Lallai duk wanda ya kalli wannan gangar ruwa zaisan girman ubangiji.
Suna isowa waziri yai kyaran murya ya fara jawabi, "wannan bango na arewa shi ne abinda ya raba sashin arewa da sashin Ikwatora na wannan doron ƙasa. Kuma kamar yadda kika ga wannan Bango akwai ɗaya bangon ta ɗaya ɓangaren wanda ake ce masa bangon kudu.
"Babban abinda mutane basu da masaniya akan wannan bango shi ne bawai kawai bangon ruwa bane. A'a acikinsa akwai waje wanda yake yakai girman manyan garuruwa goma wanda kuma ba ruwa a wajen. Wannan waje kurkuku ne da ƙabiƙar Ururu suka gina tun a shekarar da sukai yaƙi da ƙabilar Wilbafos. Kuma acikin wannan kurkuku ake saka dukkan wanda laifinsa ya wuce iyaka ko kuma wanda ya gagari hukuma, ko kuma wanda yai fito-na-fito da Ururu.
"Dukkanin wannan ma'abota Izza dake cikin wannan kurkuku sama da shekaru dubu sun kasa fitowa daga ciki badan komai ba saidan baƙaƙen idanu dake kare wannan bango na ruwa.
"A shekarar 127 Bayan Amri sarakunan ikwatora shida suka saka hannun a yarjejeniya da ƙaɓilar Ururu cewa babu wanda zai ƙara shiga ko kuma fita daga sashin Ikwatora, sannan su kuma Ururu zasu rabu da sashin Ikwatora suyi mulkinsu yadda suke so ba tare da Jinzidal ba. Tun daga wannan rana babu wani mahaluƙi daya ƙara shigowa wannan sashi na Ikwatora daga sauran ƙasashe na duniya, sannan kuma muma bama fita. Kinga ba ƙaramin tashin hankali zaki jawo ba idan aka ji kin shigo daga waje, ballantana ma aji bayan kin shigo kuma kin zama sarauniya. Sannan kuma wai kina so ki ƙara shigo da wani.
"To amma daga yadda kika gayamin kema baki san yadda akai kika zo nan ba, saboda haka hanya ɗaya da zaki iya kare kanki daga sharrin sauran sarakunan Ikwatora da kuma sharrin Ururu shi ne idan basu san daga ina kike ba. Lallai indai sunsan daga inda kike to zasu ce kin karya wancan doka kuma lallai sai sun miƙa ki ga ƙaɓilar Ururu. Amma indai mu ukun nan ne muka sani to babu wanda zaiji, tunda tuni muka riga mukai alƙawari cewa zamu kare duk wanda Tsibirin guguwa ya zaɓa. Amma lallai indai sauran sarakuna suka ji to kuwa babu yadda zamu yi. Saboda haka kinga baza mu iya saka kuɗi ba akan wannan yaro ba, domin kuwa kowa zai gane. Shawarata yake sarauniyarmu a manta da wannan mutun. Domin kuwa baza su iya zuwa sashin Ikwatora ba, ke kuma baza ki iya fita ba. Kinga har duniya ta naɗe baza ku haɗu ba."
Nusi ta daki ƙasa da ƙafarta tai tsawa, "kai waziri, lallai bazan mutu ba saina haɗu da Armad. Idan ni na kasa nemo shi shi zai nemo ni. Kuma lallai bazan huta ba saina nemo yadda zan fita daga wannan sashi na Ikwatora koda kuwa zan rasa raina. Yafi ace na ganshi sau ɗaya na mutu dana rayu shekaru dubu ban san a halin da yake ciki ba."
***
Babi na 73: Ikenga
Ran Nusi a ɓace haka suka rankaya tare da Waziri, Saiza, da Galadima, Náru, da Sarkin Bai, Rayaya, izuwa garin Dula. Akan hanyarsu ne Nusi ta waiwayo izuwa waziri tana mai cewa, "amma nasan dole akwai mutanen da suke da damar keta wannan bango a sashin Ikwatora, ko kasan su?"
Waziri Saiza ya ja dogon numfashi tare da kyaɗa kai yana cewa, "Eh, lallai akwai mutun ɗaya, babban sarkin Ikwatora, sarki Rainay Guguwa. Shi ne kaɗai sarki a ikwatora wanda tun shekarar da aka saukarda al'ummar biladama izuwa ƙasashen ƙasa yake mulki a sashin Ikwatora. Duk shekara tsibirin guguwa shi yake zaɓa a sashin Ikwatora dake doron ƙasa ta biyu. Ko a wannan shekara ma shi aka zaɓa. Wasu daga cikin mutane suna ganin cewa acikin baƙar guguwa aka haifeshi. To koma dai menene shi ne sarkin da yafi kowanne ƙarfin iko a sashin Ikwatora, kuma shi ne ya saka hannu a dokar hana ratsa wannan bango shekaru dubu da suka wuce, kuma shi kaɗai yake da ikon sauya wannan doka."
Nusi taji daɗin wannan labari na waziri, inda ta juyo izuwa gareshi cikin jin iko da ƙarfin mulki tana cewa, "mene ne matakin da ake bi wajen zama babban sarkin Ikwatora? Ko zaɓe ake yi? Domin koma me akeyi saina hau wannan kujera na kuma karya wannan doka. Babu ruwana da a ina aka haifi sarki Rainay Guguwa, ko kuma ƙarfinsa ko kuma alaƙarsa da Ururu. Abinda na sani kawai shi ne saina nemo abokina Armad da ƴan uwana Iliyasis da Cokali.
Koda jin wanann magana sai duk su ukun suka ja linzami cikin firgici suna duban Nusi wadda ko a jikinta. Baki a buɗe sun kasa cewa komai, haka suka rankaya har zuwa fada ba tare da kowa yace uffan ba.
***
A shekarar da aka gama Jinzidal abubuwa da dama sun afku. An siyarda Armad a matsayin bawa, Nusi ta ɓata sannan kuma Ikenga ya gudu bayanda yayi arba da Uznu Ururu.
Armad ya rayu a hannun Ururu duk da kuwa uƙubar da suka gana masa, sannan ya farkar da babbar Izza a jininsa.
Nusi ta rayu duk da raunin da Uznu yaji mata, sannan kuma ta tsinci kanta a sashin Ikwatora ba tare da tasan yadda akai taje ba.
Shi kuwa Ikenga yana ɓacewa daga wannan fili ya bayyana a tsakiyar saharar dajin Ƙairus dake doron ƙasa ta biyar. Babu gida gaba babu gida baya, hasalima Ikenga shi kaɗai ne a tsakiyar wannan dokar dajin. Ƙuwwar iska da zafin rana da yashi yasa gumi ya fara karyo masa. Gashi tuni ya ƙarar da ƙarfin Izzarsa a fafatawarsa da Armad. Saboda haka dakyar yake tafiya. Sai dai kuma ana cikin haka yaji wata ƙara a bayansa. Yana waiwayawa yai arba da wasu manyan-manyan sadaukai guda biyu. Wanda kana ganinsu zaka tuna da tarihin daular samudawa. Saboda nauyinsu ƙafafunsu sun nutse acikin ƙasar da suka dira. Suna sanye da baƙaƙen kaya masu ratsin ɗorawa daga sama. Kowanne ɗaya acikinsu Izzarsa ta haura dubu ɗaya.
Ikenga yana ganinsu ya gane su. Ba wasu bane illa biyu daga cikin kwamandu biyar dake aiki a ƙarƙashin Uznu Ururu. Ikenga yayi murmushi yana mai cewa, "dama nasan baza ku kyale ni haka ba."
Ɗaya daga cikin kwamandun guda biyu ya miƙa hannunsa kan takobinsa yana mai cewa, "ka miƙa kanka salin-alin babu gardama. Dukkanmu izzarmu ta haura dubu, kana da ɗari kacal. Mai zaka iya yi face miƙa wuya."
Ɗaya kwamandan wanda keda baƙar fuska da manyan ƙasusuwa masu kama da duwatsu ya ƙara da cewa, "kada ka zargi kowa ka zargi rauninka da lalacinka dana zuri'ar ka."
"Hmmm....." Ikenga yaja dogon numfashi tare da murmushi yana cewa, "Idan zaku iya kama ni to ku gwada." Yana rufe baki ya tafa hannayensa guda biyu yana kiran waɗansu ɗalasimai da harshen Wilburish. Lamarinda yasa wani shinge na koren haske ya bayyana ya kewaye shi. Abin mamaki daga cikin wannan haske saiga wasu mutane uku sun bayyana. Babban abin mamakin shi ne biyu daga cikinsu kamarsu ɗaya sak da Ikenga, kai hasalima Ikenga ne kawai. Babu maraba koda kuwa ta kwayar zarra. Ɗaya mutumin kuwa wannan tsohon ne mai suna Kána, wanda aka gansu tare da Ikenga watanni kaɗan kafin Jinzidal, a lokacin da Ikenga ya jawo salwantar ruhin Armad.
Waɗannan mutane biyu masu kama da Ikenga suka rikiɗe izuwa iska sannan suka shige jikin Ikenga. Haka na faruwa wannan da'irar haske ta ɗauke, amma Izzar Ikenga nan take ta canja daga ɗari zuwa duba ɗaya, sannan ta ƙara rikiɗewa daga dubu ɗaya zuwa dubu goma. Gashin kan Ikenga ya rikiɗe izuwa fari fat, sannan kuma ya ƙara tsayi har zuwa gadon bayansa. Fatarsa jikinsa tai fari fat tamkar an zuƙe jinin dake jikinsa. Wata sabuwar nutsuwa ta bayyana a tattare dashi. A wannan lokaci idan baka sanshi sosai ba baza ka gane shi ba.
Ana haka saiga aljani Gal-iyyu ya bayyana ya fito daga jikin Ikenga ya zube a ƙas cikin biyayya. Shima wannan tsoho Kána a ƙas ya zube yana mai cewa, "barka da dawo wa, sarkin duniya."
Su kuwa waɗannan kwamandu guda biyu buɗe baki sukai cikin firgici suka fara jada baya, amma ina tuni sanyin babban sihiri ya sauka a garesu. Wannan ƙanƙara ruwan toka mai ɗauke da ƙarfin Izzar Ikenga ta ratsa ƙashinsu, sannan ta rusa ruhinsu. Kan kace meye wannan waɗannan kwamandu masu Izza sama da dubu sunyi bindiga sun faɗi ƙasa matattu.
Ikenga ya juyo izuwa Aljani Gal-iyyu da tsoho Kana yana magana a nutse tamkar ba shi ne ya halaka ma'abota Izza sama da dubu ba. "Kunga yanzu duniya zatai tunanin ƙarfinmu bai wuce na Izza ɗari ba. Za suyi tunanin cewa ƙarfin Izzarmu bai wuce na mu kara da wannan yaro ɗan zuri'ar Wilbafos ba. Hakan zaisa baza a saka mana ido ba a lokacin da muke gudanar shirye-shiryenmu ba."
Ɗan tsoho Kána ya amsa da cewa, "wannan haka yake ya shugaban mu. Zanso naga fuskar yaron nan Armad a sanda zai gane cewa da ɗaya bisa ukun ka ya fafata amma ya kasa samun nasara. Hasalima saida ka raba izzarka gida ɗari sannan kai amfani da kaso ɗaya."
"Armad?" Ikenga ya tambaya cikin girman kai da jin Izza tamkar bai taɓa jin sunan Armad ba, sannan ya ɗora da cewa, "Ah... sunan sa kenan."
***
Babi na 74: Miyura (1)
A wani gari nisan kimanin shekaru hamsin daga inda Armad tsaye, a wani tsiburi dake tsakanin doron ƙasa ta farko data biyu, wasu yara ne ƴammata guda biyu ke wasa a gefen wani kogi. Kana ganin ƙirar yaran da kayan jikinsu zaka san cewa lallai ƴaƴan sarauta ne. Dukkan idanunsu farare ne fat babu ko kwayar baƙin dake cikin ido. Kai ka rantse makafi ne.
Amma zaka gane cewa suna gani tar-tar kamar kowanne ɗan adam a yayinda ɗaya daga cikinsu wadda ta kasance fara mai gashi roɗi-roɗi ta ga wani mutun a kwance a gabanta ruwa ya koroshi. Ba shiri taja rigarta sama, ta kuma fara kiran ƴar uwar ta, "Suwee! Suwee!! Suwee!!!"
Ƴar-uwar tata ta juyo izuwa gareta. Asalin sunan ƴar uwar shi ne Suwainah, amma ƙanwar tata mai suna Zeera ta fiso ta ringa kiranta da Suwee.
Zeera ta nuna mutunin dake gabanta tana cewa, "Kizo kinga wani ma, ina ragowar ukun?"
Suwee ta zare ido cikin firgici tana cewa, "Wani ne ya ƙara bayyana? Waɗancan baba ya tafi dasu wajen sarki."
Zeera ta buɗe baki cikin mamaki,"Baba kuma? kina nufin baba da kansa! To gaskiya ne kenan abinda ake faɗa cewa daga wata duniyar aka jefosu!"
Tun kafin ta rufe baki yayar tata mai kimanin shekaru sha shida wadda kuma ta bata shekaru uku, ta taho wajen da take da gudu domin taga wannan mutun da ƙanwarta take nuna mata. Tana zuwa ta rufe ƙanwar tata da faɗa, "ba baba yace mu daina faɗa ba, so kice wasu suji. Yana ina?"
Zeera ta nuna mata wani yaro kwance a gefen kogin, duk taɓo ya shafe masa jiki da fuska. Amma duk da haka idan kalura sosai zaka ga cewa akwai ɗaurin jan kyalle a gaban goshinsa. Kuma lallai idan kasan Armad Wilbafos mamallakin tambarin Miyura zaka gane cewa shi ne ba wani.
Suna tsaye suna tunanin ya zasu yi kawai sai suka ji hayaniyar sauran ƴan matan daga nesa suma suna kusanto wannan kogi.
Zeera ta dubi ƴar uwar tata cikin sauri tana cewa, "Yaya to ya zamuyi dashi, ga mutane nan!"
Nan take Suwainah ta fito da wata ƴar ƙaramar jakar tsafi a cikin rigarta ruwan hoda, inda ta bawa ƴar uwarta ta. Suka kuma fara tala wannan jaka har saida takai dai-dai tsayin yadda zasu iya zira Armad aciki.
Ƙanwar ta miƙa hannunta domin ta fara saka kan Armad aciki, amma a lokacin al'amari ya canja.
Domin kuwa tana taɓa jikin Armad hannunta ya shige cikin kansa tamkar babu komai a wajen. Cikin sauri ta zaro hannunta ta kuma ƙara taɓawa dan ta tabbatar, amma hakan dai ta ƙara faruwa a karo na biyu.
Nan da nan ita ma Suwainah ta miƙa nata hannun ta taɓa ƙafarsa, amma taga itama hannunta ya shige tamkar babu komai a wajen. Cikin tsananin mamaki suka fara tunanin ko mafarki suke. Amma maganar ƴan uwansu matan dake ƙara matsowa ita ce ta tabbatar musu cewa ba mafarki suke ba. Nan take suka fara bin duk wata hanya domin zira jikin Armad acikin wannan jaka, amma ina.
Kuma suna cikin haka ne ɗaya daga cikin matannan masu ƙarasowa ta hango su, ai kuwa nan take ta fara kwala musu kira, tare da tahowa inda suke.
Nan take Suwainah ta yanke hukunci tana mai cewa, "Zeera jeki ki gano inda baba yake. Idan da dama ki gaya masa abinda ke faruwa a ɓoye ba'a cikin mutane ba. Zanyi maganin abubuwa anan."
Tana faɗar haka ƴar uwar tata Zeera ta rankaya a guje ta nufi gabas.
Suwainah tayi duk wata dabara da zatai ta ɓoye ruhin Armad amma abin ya gagara. Tana cikin wannan hali wannan ƴammata huɗu suka iso wajenda take tsaye. Tai kasaƙe tana jira su tambaye ta wane ne wannan mutun dake kwance a bayanta amma ba suce komai ba. Hasalima tamkar basa ganinsa. Wanda hakan yasa Suwainah waiwayawa cikin zafin nama tayi duba izuwa inda tabar Armad amma babu shi babu alamunsa.
Tana cikin diri-diri taji muryar ɗaya daga cikin wannan mata dake gabanta. "Suwainah me kike anan ke kaɗai? Saura kwanaki bakwai a rantsar da ma'abota Ururu na wannan shekarar, kije ki rubuta sunanki ki hau layi."
Suwainah ta kyaɗa kai tana cewa, "Eh hakane. Dama nazo wanka ne kuma bansan an fara rubuta suna ba. Yaya tsarin yake?"
Ɗaya daga cikin ƴan matan taja dogon numfashi kafin daga bisani ta kyaɗa kai tana cewa, "fafatawa za'ai kawai. Duk wanda ya farkar da Ururun dake idanunsa zai shiga cikin ma'abota Ururu. Ragowar kuma zasu ci gaba da zama anan sai wata shekarar. Sannan kuma acikin waɗanda suka farkar da Ururunsu za'a raba su izuwa mataki-mataki. Muje mu rakaki ki saka sunanki."
Suwainah tana so taje ta saka sunanta to amma bata so tabar wajen ba tare da taga Armad ba. Domin kuwa tuntuni take ta zulumin ina Armad ya shiga. To amma babu yadda zatai, tunda babu wani uzuri da zata iya gayawa ƴan matan saboda haka suka rankaya tare izuwa cikin wannan gari.
Wannan tsibiri dai waje ne na musamman wanda yake da tarihi na sama da shekaru dubu. Ya kasance akan iska a tsakanin doron ƙasa ta farko da kuma doron ƙasa ta biyu. Sunan wannan tsibiri Tsibirin Sido-Ururu.
Akan tsibirin Sido-Ururu anan ƙabilar Ururu take bawa ma'abota Ururu horo akan yadda zasu farkar da Ururun dake idanunsu. Asali dai ana haifar ƴan ƙabilar Ururu ne da baƙaƙen idanuwa to amma wannan idanu na farko basa aiki da Izza. Duk wanda yake so ya farkar da Ururunsa izuwa matakin Izza saiya fara juyarda idanunsa izuwa fari fat kamar irinna waɗannan ƴammata. Irin wannan fararen idanu su ake kira da Sido-Ururu. Daga matakin Sido-Ururu akwai horo kala-kala da ake bayarwa kafin mutun ya ƙara juyarda idanunsa izuwa baƙaƙe. Duk wanda yabi wannan matakai ya zama ma'aboci Ururu.
A ƙarƙashin ƙabilar Ururu mai mulkin doron-ƙasa ta farko akwai aƙalla manyan gidaje guda goma. Kowanne gida yana da matuƙar girman da shi kansa zaka iyai masa kallon ƙabila mai zaman kanta. Wannan gidaje guda goma sune kamar haka:
1)Gidan Kuyurussa'ayi Ururu: Ɗa ɗaya
2)Gidan Dumaƙisu Ururu: ƴaƴa ashirin.
3)Gidan Uznu Ururu: ƴaƴa sha takwas
4)Gidan Dul'Ururu Ururu: ƴaƴa tara.
5)Gidan Jushai Ururu: ƴaƴa talatin da uku.
6)Gidan Ƙilbaru Ururu: ƴaƴa sha tara.
7)Gidan Jidda Ururu: ƴaƴa bakwai
8)Gidan Nasára Ururu: Ƴaƴa huɗu
9)Gidan Shiysui Ururu: ƴaƴa shida
10)Gidan Fayziy Ururu: ƴaƴa sha ɗaya.
Kowanne ɗaya daga cikin gidajen nan yana da jikoki barkatai, waɗanda sune wanda ake turowa wannan tsibiri domin samun horo su farkar da Ururunsu. Sauran ragowar ma'abota Ururu dake doron ƙasa ta farko idan suna buƙatar tayarda Ururunsu sai dai suyi shi a sauran wajaje da aka tanada a bisa doron ƙasa ta farko.
A saboda haka Armad bai sani ba, amma a dai-dai lokacinda ruhinsa ya ɓalle ya bayyane akan wannan tsibiri inda yayi arba da Suwainah Ururu da Zeera Ururu jikokin gidan Ƙilbaru Ururu.
Akwai jarabawowi da dama da ake gudanarwa kafin a zama Ma'aboci Ururu, kuma waɗannan ƴan mata, Suwainah da ƙanwarta, abinda ya kawo su wannan tsibiri kenan.
Kwana ɗaya kafin baiyanar ruhin Armad a wannan tsibiri, ruhin mutanen nan uku dake muradin mallakar littafin, wanda Ikenga yayi musu haramiya ya kuma yi cilli dasu izuwa Tsibirin-Sido-Ururu suka bayyana. Suna bayyana mahaifinsu Suwainah wanda shima jikane a gidan Ƙilbaru Ururu ya ɗebe su ya nufi dasu wajen sarkin wannan tsibiri mai Shadi Ururu, wanda jikan gidan Fayziy Ururu ne.
Babu wani ɓata lokaci, Shadi Ururu yana ganin ba suda Ururu yasa aka sare musu kai sannan aka binne gawarwakinsu ba tare da kowa ya sani ba. Domin a wajen ma'abota Ururu indai ba kada Ururu to kai ba mutun bane. A wannan lokaci hatta su Suwainah basu san halinda ake ciki ba, sudai kawai mahaifinsu yace kada su faɗawa kowa labarin waɗannan mutane da suka tsinta, sannan kuma ya gaya musu idan sunga wasu su kira shi. Saboda haka Suwainah ta tura ƙanwarta Zeera domin ta nemo mahaifin nasu, amma bisa mamaki ruhin Armad ya ɓace ɓat babu shi babu alamunsa.
***
Baba na 75: Miyura (2)
Yara ma'abota Sido-Ururu guda dubu goma ne akan wannan tsibiri suna karɓar horo. Suwainah da Zeera biyu ne kacal daga cikin wannan adadi. Kowanne babu abinda yake so illa ya farkar da Ururun da tafi ta sauran ƴan uwansa girma.
Abu ne sananne akwai Ururu mataki-mataki ɗai-ɗai har mataki bakwai. Mataki na bakwai shi ne mataki da yafi kowanne ɗaukaka da buwaya da girman Izza. Kaɗan ne daga cikin ma'abota Ururu tun daga farko duniya har izuwa wannan lokaci suka taɓa mallakar mataki na bakwai na Ururu. Hasalima mutun uku ne kacal. Ɗaya shi ne sarkin Ururu wanda ya ture Eyriyon Wilbafos daga kan kujera a lokacin juyin-mulkin Amri, sai kuma yarima mai jiran gado na Ururu wanda aka fi sani da Dúmaƙisu Kuyúrussa'ayi Ururu, sai mutun na ƙarshe wanda shi ne babban wazirin sarki Kuyurussa'ayi Ururu.
Mataki na shida na Ururu shima abu ne mara yawa, kuma waɗanda aka sani dashi basu da yawa. Akwai sarakuna goma dake jagorantar gida je goma na Ururu wanda muka labarta a babi na baya, sarakunan da ake kira da ASHURA. Sannan bayansu akwai wasu ƴan tsirarin sadaukai wanda sukai shura a gidan Ururu.
Mataki na biyar shi ne iyaka da aka sani, wanda duk wanda yaje shi ana ganin yakai ƙololuwar Izza a gidan Ururu. Mataki na huɗu dana uku dukkansu suna da ƙarfin izzarda zasu iya tarwatsa rundunar mutane da aljanu komai girmanta ba tare da wahala ba. Mataki na biyu akan yi musu laƙabi da Matasan-Ururu, wanda su ake bawa muƙamin kyaftin-kyaftin na runduna. Mataki na farko kuwa sune mayaƙan Ururu mafi ƙanƙanta. Amma a hakan kowanne ɗaya daga cikinsu idan har ya kware akan sarrafa Ururun sa shi kaɗai dai-dai yake da runduna guda.
Abin mamaki ruhin Armad na laɓe akan wannan tsibiri yana kallon duk abinda ke faruwa tamkar mutun mai rai. Jiki ne kawai babu. Ba jimawa yana cikin wannan hali ya yanke shawarar abinda zaiyi. Saboda haka ya ci gaba da laɓewa yana nazarin wannan yara tsahon wata da watanni. Inda ALLAH ya taimaki wannan ruhi baya buƙatar ci ko sha, sannan kuma saboda rashin gangar jiki yana iya shigewa ta jikin kowanne abu. Hasalima a waɗannan watanni wannan ruhi na Armad ya gano cewa yana iya shiga jikin mutun ko dabba harma su gana da wannan mutun ba tare da kowa ya sani ba. A saboda hakan ɓuya ba abu bane mai wahala ba.
A wata na goma wannan ruhi yabi wannan yarinya mai suna Suwainah cikin wani daji inda take keɓe wa tana koyon sarrafa al'amuran Izza.
Suwainah na tsaye a tsakankanin bishiyu masu kama dana darɓejiya sai dai sun fisu tsayi da kauri, sannan kuma rassansu suna da kaifi da tsini tamkar masu. Kana ganin idanun Suwainah kasan tana da kafiya irin ta ma'bota Ururu.
A waɗannan watanni da ruhin Armad yayi yana nazarin waɗannan yara ya gano cewa Suwainah irin mutanan nance da zasu iya aikata koma meye akan su sami ƙarfin Izza. Kuma wannan shi ne dalilin da yasa ruhin Armad ya zaɓe ta.
Idanun Suwainah suna nan a farare fat sanfurin Sido-Ururu, amma takobin ta tuni ta juye izuwa baƙa-ƙirin samfurin Ururu. Lallai Suwainah tayi rantsuwa saita zamanto ɗaya daga cikin matasan Ururu da ake kwatance dasu. Musamman duba ga yadda sama da shekaru ɗari biyar babu wanda aka samu ya fito daga gidansu wanda ƙarfin Ururunsa yakai mataki na biyar. Wanda hakan yasa ake ganin gidan nasu ya fara rushewa. Amma Suwainah tayi rantsuwa lallai saita ɗago da wancan martaba a matsayinta na ɗaya daga cikin ƴan gidan.
Hannunta a miƙe, tana riƙe da doguwar takobin. Idanunta a rufe tana fuskantar yamma. Saboda yadda ta tsaya a ƙame tare da miƙe ƙafa ɗaya da kuma ɗage ɗayar ƙafar, lallai zaka ce mutun-mutumi ne wanda bai taɓa motsi ba.
Ruhi da Izza na Ururu na kewaye da jikinta. Hatta wannan bishiyu idan ka lura zaka ga suna tsoron suyi wani abu da zai dame ta.
Acikin wannan hali Suwee ta ci gaba da tsayuwa tana nazari da lazimin al'amuran Izza dake cikin idanunta har saida asubahi ta gabato. Sannan ta buɗe idanunta, inda wani baƙi mai ɗauke da Izzar gidan Ururu ya bayyana a idanun nata tsahon daƙiƙa biyar kafin daga bisani ya ɗauke idon ya koma fari.
Suwainah ta nufi gindin bishiyar dake kusa da ita inda ta ajiye kayanta, ta ɗauki robar ruwa tasha. Sannan daga bisani ta juyo ta fara wasa da takobin dake hannunta. Kai kace wannan takobi bata da nauyin komai, domin kuwa yadda take sarrafa ta tana juyata tamkar kawai takobin wani ƙari ne na hannunta.
Haka dai taci gaba da rawa da wannan takobi har saida rana ta ɗaga, sannan ta fara shirin komawa cikin ƴan-uwanta domin karɓar horon safe. A dai-dai wannan lokaci ne ruhin Armad ya bayyana a gabanta, cikin tsananin zafin nama, Suwainah ta kawo sara da takobin dake hannunta. Amma ruhin Armad ko motsi baiyi ba. Ya bari takobin ta ƙaraso, sannan ta sari wuyansa, amma bisa mamaki sai takobin ta shige ta cikin wuyan tamkar babu kamai a wajen. Ruhin yayi murmushi tare da girgiza kai yana mai cewa, "takobinki baza ta iyayin aiki akaina ba."
Suwainah ta ja da baya tare da fara kiran ɗalasimai. Amma a dai-dai wannan lokaci ne ruhin Armad ya ɓace daga inda yake sannan ya shige jikinta. Yana shiga taji tamkar zatai atishawa amma bata zo ba. Ta tsaya tana tunanin mai zatai amma a lokacin ne taji muryar ruhin yana mata magana.
"Dani dake zamu iya taimakon juna. Ki taimake ni na taimake ki."
Suwainah ta haɗe rai tana cewa, "Mai zaka iya taimako na dashi? Na gane ka, ba kaine wanda kuka zo tare da waɗannan mutane ba ƴan watannin baya. Dama sarki yana nemanka."
Ruhin Armad yai kyaran murya sannan yaci gaba da magana tamkar baiji mai take cewa ba. "Zan iya baki ƙarfin Izzar da kike buƙata ki farkar da Ururu mafi girma a tarihi. Idan baki yadda ba tsaya na gwada miki."
Ruhin Armad dai daya ɓalle yazo wannan tsibiri shi ne ruhin dake cikin Miyurar dake goshinsa. Hasali idan mai karatu bai mantaba wannan Miyura tana iya ƙarawa Armad Izza, kuma tunda Armad ya rasa ta ya daina samun wannan ƙarin Izza.
A dai-dai wannan lokaci, tun kafin Suwainah ta amince, taji ruhinta ya girgiza, sannan izzarta ta fara juyawa.
***
Chapter 76: Alƙawarin Urúrú da Wilbafos
A dai-dai wannan lokaci, idanun Suwainah suka kaɗa sukai baƙi-ƙirin, ta fara ƙoƙarin fitarda da ruhin Armad daga jikinta.
Amma ana cikin haka taji izzarta ta fara girgiza tana juyawa. Jikinta ya fara ɗaukan zafi, kafin daga bisani taji wani tsananin ƙarfi irin wanda bata taɓa jinsa ba. Nan take taji a ranta cewa indai za'a zo yin jarabawar rantsar da Ururu a wannan hali sai tayi nasara.
Tana cikin haka taji muryar ruhin Armad na cewa, "zan iya baki izza sama da haka. Amma kiyi min alƙawarin zaki yimin abu ɗaya."
Suwainah ta ɗanyi shiru na ɗan taƙi kafin ta yanke shawara. "Mai kake so?"
Ruhi ya kada baki ya ce, "Fasahar sarrafa lokaci ta ƙabilar Ururu."
Suwainah tai murmushi tare da cewa, "Babu wanda ya isa ya mallaki wannan fasaha idan ba manya goma na Ururu ba wato Ashura. Kuma mai kake so kayi da ita?"
"Abinda zanyi da ita ni ya shafa. Kamar ƴadda abinda zaki yi Ururun ki ke ya shafa. Kuma nasan kowanne ɗaya daga cikin gidaje goma na Ururu suna da wannan fasaha guda ɗaya a rubuce a ajiye. Idan kina son Izza to ki samo min wannan fasaha."
Bayan tsahon lokaci tana tunani ta kada baki tace, "Ba zanyi alƙawari ba har sai naga girman izzar da zaka bani. Zuwa ƙarshen shekarar nan za'ayi jarabawar rantsar da Ururu a doron-ƙasa ta farko. In har ka taimake ni na samu matakin Ururu na biyar zuwa sama to nayi alƙawarin samo maka wannan fasaha."
Ruhi ya kada baki ya ce, "Na amince."
Idan mai karatu bai manta ba, Uznu Ururu yayi amfani da irin wannan fasaha ya canja sakamakon Jinzidal wanda hakan ya bawa Armad damar wuce matakin Alkadar. Da irin wannan fasaha abu ne mai matuƙar sauƙi ruhin Armad ya koma jikin Armad ya kuma haɗe da gangar jikinsa. Amma a duk faɗin duniya ƙabilar Ururu su kaɗai keda wannan fasaha. Hasalima hatta acikin Ururu, manyan nan guda goma wanda ake kira da ASHURA su kaɗai keda iko su mallaki wannan fasaha.
Ruhin Armad yana da tunani nasa daban dana Armad, sannan kuma abin mamaki kowanne yana zaman kansa ne a matsayi ruhi guda bawai rabin ruhi ba. A taƙaice madai abin ya saɓawa al'ada baki ɗaya. Domin kuwa tunda ake rayuwa a duniyar ƙasa bakwai ba'a taɓa samun wanda ruhinsa ya rabe gida biyu ba sannan kuma ya rayu, to amma wani sirri wanda har ƴanzu ba'a san menene ya saka Armad ya zamo mutun na farko da ya iya rayuwa duk da kuwa ruhinsa ya rabe gida biyu.
Wani abun mamakin shi ne yadda kowanne acikin ruhin guda biyu keda tunani nasa na musamman. Misali, ruhi mai ɗauke da Miyura yana da wasu ilmummuka wanda ke ƙunshe acikin Miyura wanda shi Armad baima san dasu ba. Musamman tunda dama Armad bai gama kwarewa wajen sarrafa Miyurar ba. Ta haka nema ruhin yake da masaniyar wannan fasaha ta Ururu da kuma yadda zaiyi amfani da ita wajen komawa jikin ɗan'uwansa.
To a wannan rana ruhin Armad da Suwainah Ururu suka ɗaura alƙawari zasu taimaki juna domin cimma burinsu. Duk da kuwa ruhin Armad baisan cewa burin Suwainah guda ɗaya ne kacal a duniya, wanda shi ne ta ƙarar da dukkan ƴan ƙabilar Wilbafos da Bayajidda da suka rage. Sannan kuma ita ma Suwainah Ururu bata da masaniyar cewa wanda zai taimake ta burinsa ya ruguza gidan Ururu da Rukunan su ba guda biyu na Amri da Jinzidal.
Suwainah da ruhin Armad haka suka ci gaba da kasancewa a wannan hali tsahon wannan shekara. Ruhin yana ƙara mata ƙarfin Izza, ita kuma tana ƙara dagewa wajen samun horo domin cimma burinta.
----------
A can duniyar ƙasashen-ƙasa kuwa, Armad ne tare da sarkin duba Babara ke ketawa ta cikin Bangon arewa domin zuwa wajenda za'a fara horar da Armad.
Bayan kimanin daƙiƙa ɗari suna tafiya sai kwale-kwalen ya fara gudu, lamarinda yasa Armad yin sauri ya zauna ya riƙe kefensa ƙam, ya kuma rufe idonsa. Kwatsam ana cikin haka sai jiyayi tamkar sun faɗa cikin wani ƙaton rami, lamarinda yasa ba shiri ya buɗe idonsa. Ai kuwa yai arba da kwale-kwalensu yana faɗowa ƙasa. Ya waiwaya bayansa yaga wannan Bango da kuma wannan ƴar ƙofa da suka shigo ta ciki. Nan take ya gane cewa lallai kodai cikin tsakiyar wannan Bangon ruwa suka shigo ko kuma bayansa.
Bayan sun shafe sama da daƙiƙa hamsin suna faɗowa Armad ya tafa hannunsa ya kirawo duk wata fasaha da yake da ita domin kare kansa, domin yasan koma ina zasu faɗo to lallai yana da nisan gaske kuma jikinsu zai iya tarwatsewa. Banda kuma cewa bai masan mai zasu tarar ba.
Iska mai ƙarfin gaske ta cikawa Armad ido da hanci. Amma ana cikin haka ya fuskanci cewa Babara ko a jikinsa. Hasalima nishaɗi yake yana murmushi ganin halinda Armad ke ciki.
Babara ya tafa hannayensa ya fito da wata ƴar tasa mai launin ja. Acikin ta akwai wani ruwa mai ɗauke da ɗalasimai na musamman. Kafin Armad ya farga, Babara ya watsa masa wannan ruwa. Ai kuwa ruwan na taɓa jikinsa yaji tamkar an zare masa rai, nan take Armad ya sume.
Armad bai tashi farfaɗowa ba sai bayan kwanaki uku. Yana farkawa ƴa tsinci kansa acikin wani ɗan tanti mai duhu-duhu. Abu na farko da Armad ya fara fuskanta shi ne wani tsananin sanyi mai ratsa ƙashi, tamkar an sashi a tsakiyar tekun ƙanƙara.
Ana haka ya miƙa kansa ya kalli wajen tantin ta wata ƴar taga, inda ya fuskanci cewa ƙanƙarar ce kuwa ke zuba da gaske. A sashin arewa doron-ƙasa ta uku, akanyi sanyi amma bai taɓa kaiwa inda ƙanƙara zata zuba ba. Saboda haka nan take Armad ya fara karkarwa, domin kuwa wannan shi ne karo na farko daya taɓa fuskantar irin wannan sanyi.
Ba shiri ya fara tunanin a ina yake. Bayanda ya duba ya tabbatar jikinsa ba ciwo saiya miƙe ya futo waje. Wata iska mai ɗauke bushin farar ƙanƙara ta daki fuskarsa. Yai duba izuwa ƙafarsa ta hagu yaga inda ya taka ya nutse acikin ƙanƙara. Dukkan wajen yayi duhu tamkar lokacin isha saboda tsananin ruri da rugugin iska da ƙanƙara dake kaɗawa.
Yayi haka zai juya ya koma tantin sai yaji an dafa kafaɗarsa. Inda ya jiyo amma baiga kowa ba. Nan take Armad ya zare takobinsa ta Wilbafos sannan kuma ya ɗaga hannunsa na hagu inda wata ƙatuwar ƙawanyar aradu ta bayyana.
Wannan aradu ta haske wajen amma duk da haka Armad baiga kowa ba. Can yaji an ƙara taɓa shi, amma ta ɓangaren dama. Nan take yakai wawan sara wajen, amma kamar yadda yai tsammani bai samu komai ba.
Armad na shirin ƙara kai wani saran yaji muryar Babara a kunnensa. "Baza ka iya gani na ba, saboda da idon ka kaɗai kake gani. Cikakkun ma'abota Izza suna gani kuma suna ji koda sun makance kuma sun kurumce. Lallai idan kana so ka rayu a wannan kurkuku na tsahon kwana ɗaya to lallai saika fara gani izzarka bada idonka ba. Kuma wannan shi ne mataki na farko na horonka."
Armad yaji duk bayanin da Babara yayi, kuma dama Armad baiyi tsammanin zai samu horo ta sauƙi ba. Amma abu ɗaya ne bai gane.
"Sarkin duba kurkukun gaske ko kuma salon-magana kake?"
Babara yai murmushi tare da girgiza kai yana cewa, "lallai ba salon-magana nake gaya maka ba. Wannan ita ce kurkuku mafi girma da tsaro a duk faɗin duniyar ƙasa bakwai. Yau sama da shekaru dubu da ɗari biyar kenan da gina ta, amma tunda aka halicce ta ba'a taɓa samun wani ya fita daga cikinta taba ko sau ɗaya. Duk wanda ya shigo, ya shigo kenan har abada. Koda gawarsa baza ta fita ba."
Comments
Post a Comment