Skip to main content

Chapter 30-33: Bayyanar Ururu

 Babi na talatin : Manyan gobe guda shida


A haka dai wannan awa ɗayan ta shuɗe ana ta iface-iface da nunen gwanaye!


Kowa yana nuna nasa kuma yana cewa shi zai samu nasara a ƙarshe.


Kai tuni da dama suka fara saka kuɗi ma, akan jaruman nasu. Suna masu imani da cewa lallai Su zasu yi nasara. 


Zuwa wannan lokaci, kusan duk jama'ar wajen sun hallara acikin wajen.


Akwai ƴan kallo da yawa akan waɗannan kujeru na baya wanda suka cikasu maƙil. Duk da kuwa anzo kallo da dama daga sauran nahiyoyin ƙasa bakwai, musamman idan kai duba ga cewa wannan ita ce dama ɗaya kacal da al'ummar wajen keda ita wajen iya shigowa wannan ƙasa ta ƙarƙashin ƙasa. Amma duk da haka kusan kaso sittin na ƴan kallon Denizawa ne!


Sannan kuma daga gaba kaɗan waɗanda zasu fafata acikin gasar sune a tsattsaye acikin waɗannan kewayayyun wajaje.


Kuma idan ka lura zaka ga cewa, a kowanne irin wannan waje akwai allo wanda ke ɗauke da sunaye.


Kuma idan ka duba zaka ga duk wanda ke wajen akwai sunansa akan allon wajen. Sannan kuma a gaban kowanne suna akwai ƙarfin Izzar mutun. Sai dai kuma amma kowa acikin dubun-dubatar masu fafatawar nan, idonsa nakan wasu sunaye ne guda shida kawai. Waɗanda sunfi kowa girman Izza a masu fafatawar. Tunda a bisa dokar Ƙaramar Jinzidal irin ta wannan lokaci da ake gabatarwar shi ne babu wanda zai haura Izza ɗari. Domin acewarsu domin yara masu tasowa (manyan gobe) ake shirya ƙaramar jinzidal ɗin. Indai kana so ka gwada ƙarfin Izzarka to sai dai kazo babbar Jinzidal wadda ake kira da suna Jinzidal Mejo. Sai dai kuma ba ita Jinzidal Mejo ba kamar Jinzidal ƙarama bace da ake yi duk shekara ba, ita sai bayan shekaru biyar akeyi.


To waɗannan suna ye shida dai da suka shigewa kowa ido sune;


1)Ikenga O Bayajidda : Izza Shekaru 100 (Fasahar takobi + Aljanin Hadari)


2)Deniz Bizarre : Izza shekaru 100 (Fasahar Ƙusa + Ruhin mutanen farko)


3)Han Ameer : Izza shekaru 100 (Aljanin Wuta)


4)Yarima Niyashi : Izza Shekaru 100 (Fasahar mashi + Ruhin Dordor)


5)Yarima Kiru : Izza shekaru 100 (Fasahar takobi)


6)Ameey Sadiq : Izza Shekaru 97 


Daga cikin wannan babban fili kuwa bisa mamaki wani abu aka buɗe, wanda cikin ƙiftawar ido da bismillah wannan ƙaton fili na fafatawa ya rabu izuwa adadin waɗannan alluka masu ɗauke da sunayen mutane.


Wato izuwa kaso shida!!


Daga can sama kuma acikin wannan ɗaki da aka katange da gilashi manyan baƙi ne, waɗanda duk da kasancewar wannan gilashi bai hana yanayin Izzarsu fitowa kowa yaji ta ƙarara ba.


Aciki akwai Babban baƙo daga Rafiya, wato Asifu (Ruwan Bala'i)!


Daga Maikironomada kuwa wata budurwa ce kyakkyawa mai duhun fata, wadda ke sanye da jar alkyabba, kuma a goshinta an rubuta lambar sittin, amma da yaren Aldurish!


Daga Infiriya, abin mamaki babu wanda yazo, abinda ya daɗe bai faru ba!!


Daga doron ƙasa ta uku kuwa wani dattijo ne mai yawan farin gashi, sannan kuma a kallon farko zaka gane hannunsa yana karkarwa.


Ɗaya abin mamakin shi ne duk da cewa suma Banfiriya kusan ɗaya daga cikin manyan goben da suka fi ji dashi suka turo, wato Kiru, amma babu wanda yazo daga daular, ko mutun ɗaya.


Amma wani abin mamaki shi ne, duk da cewa babu ko mutun ɗaya daga Namekiya ko kuma doron ƙasa ta biyu, amma duk da haka sun turo ɗaya daga manyan su, abinda bai taɓa faruwa ba a tarihi.


Wannan kuwa ba kowa bane ba illa ɗaya daga cikin shugabannin Ururu, wanda ake kira da 'Uznu'Ururu'!! Idan mai karatu bai manta ba, wannan ma'aboci Izza daga ƙabilar Ururu yana daga cikin waɗanda suka fafata acikin gabatarwar wannan littafi. Wanda kuma yana daga cikin waɗanda suke farautar littafin takobi. Littafinda kuma yanzu yake hannun Armad. 


Yana zaune a kujera daga gefe idanunsa a rufe ruf, kamar wanda baya so wani abu ya fice daga cikin idon nasa!


Yanayin zamansa akan kujerar, da kuma al'amarin yadda jikinsa ya mu'amalanci wajen da yake zaune kai kasan, cewa shi yake da iko akan wajen bawai wajen keda iko akansa ba.


Baya ko motsi, tamkar wanda aka ɗorawa kwanon kwai aka, kuma baya so ya faɗi.


Sai dai kuma idan ka lura zaka ga cewa wajen da yake zaunen shi ne ya nutsu kuma ya daina motsi, tamkar wajen baya so yayi wani abu da zai ɓatawa wannan mutun mai suna Uznu Ururu rai.


Kallo ɗaya ya isa kasan cewa yayi shekaru marasa adadi a duniya, amma abin mamakin shi ne fuskarsa babu ko ɗigon alamun tsufa akanta.


Babu wanda acikin wajen ya isa ya kalleshi, hasalima kowa, tamkar an manne masa kansa ne a gabansa, babu abinda suke iya yi face kawai du kalli gabansu.


Waɗannan abubuwan sun shafi kowa, dake cikin wannan ɗaki, amma banda wani dattijo, wanda bai daɗe da shigowa ba ya ɗauki kujerarsa ya koma kusa da wannan ma'aboci Ururu! Yana zama yai kyaran murya, abinda yasa Uznu Ururu ya juyo da kansa ya kalli ɓangaren da wannan dattijo yake, kana yayi wani ɗan murmushi mai cike da girman kai irin na ma'abota Ururu, sannan kawai ya ɗauke kai!


Wannan dattijo wanda ke sanye da fararen kaya ba wani bane illa Sarki Deniz Iluru. Sarkin wannan gari na ƙarkashin ƙasa. Wanda ya buɗe baki ya ce, ''Uznu'Ururu lallai ban san da zuwanka ba, amma da munyi shiri na musamman.


''Amma dai duk da da haka inai maka, sannu da zuwa!'' Sannan cikin murmushi ya ci gaba da ƙoƙarin jin menene maƙasudin wannan ziyarar bazata da ma'abota Ururu sukai masa, musamman domin yasan cewa indai aka gansu to ba alkhairi aciki;


''Ko menene ya taso, har ya saka ka zuwa wannan ƙauye namu kuwa??''


Wato kallon farko duk da irin ƙarfin Izzar dake tashi daga jikin Sarki Deniz Iluru, baza ka iya cankar wanene ba idan baka taɓa ganinsa ba.


Ba dan komai ba, sai dan cewa kayan jikinsa masu matuƙar araha ne, kuma ba'ai musu wani ɗinki mai kyau ba.


Toh amma bisa mamaki, wannan tsoho dai ba wani bane, illa sarkin wannan daula, wato Sarki Deniz Iluru!


Mahaifin Deniz Bizaya!


Saboda haka wannan mutum mai suna Uznu'Ururu bashi da mafitar data wuce ya amsa masa wannan tamabaya tasa.


Kuma duk da ya ɗauki lokaci mai tsaho bai ce komai ba daga ƙarshe saida ya buɗe baki ya ce, "ina tafe da saƙo daga Sarki acikin fadar Namekiya, Sarkin Ururu, Sarki bisa Maɗaukakiyar Masarauta, Sarki bisa Doron ƙasa ta farko!!"


Tunda Uznu ya faɗi wannan maganganu, wanda a zahiri basu amsa asalin tambayar da Deniz Iluru yayi masa ba. Amma bai ƙara cewa komai ba, kawai yaja bakinsa yai shiru.


Yana gama faɗar haka ya juyarda da kai, ba tare jin mai Deniz Iluru zai faɗa ba, inda ya ci gaba da fuskantar cikin wannan fili da idanunsa a rufe!


Shi kuwa sarki Deniz kawai ajiyar zuciya yayi, shima ya ɗauke kai, gami faɗawa cikin kogon tunani.


Kafin bayan ɗan lokaci ya dawo hayyacinsa kuma ya bada umarnin a fara wannan gasa.


Sarki Deniz Iluru ya kasance yana da siffar jikin da ta daɗe tana bawa ma'abota nazari mamaki. Badan komai ba kuwa saidan cewa shi ɗin ya kasance Basamude ne. A tsaye yakai kimanin zira'I talatin da ɗoriya. A ƙa'idar yadda duniya ke tafiya, mutun shi ya kamata ya haifi mutun, sannan kuma Basamude ya haifi basamude. To amma a dukkanin ilahirin alummar Denizawa, Deniz Iluru shi kaɗai ne yake da ƙirar Samudawa. Domin hatta ɗansa Deniz Bizaya shima siffar mutane ce dashi. To ko mai yasa? A hankali zaku ji dalili.


Tunda ƙarfin Izzar Deniz Iluru ya haura shekaru ɗari biyar, hakan na nuna cewa zai iya yin magana ba tare ya buɗe bakinsa ba kenan. Irin wannan magana wanda kayiwa shi kaɗai zaiji, kuma shima ɗin kawai acikin zuciyarsa zaiji bawai ta kunnensa ba. To a irin hakane sarkin ya isar da wannan maganar izuwa zuciyar wani saurayi fari mai dogon gashi, dake tsaye akan wani ɗan ginannen waje, kuma rabi a kewaye.


Wannan waje bashi da nisa da filayen da za'a fafata guda shida, domin yana gaba da waɗannan wajaje masu allunan nan.


Daga gani kasan wannan mutun shi ne alƙalin wasa na wannan gasa. Domin a hannunsa harda bututun magana.


Jama'a suna ta hayaniya kuma, kowa na faɗin albarkacin bakinsa, amma a dai-dai lokacin da wannan mutun ya fara jawabi kowa yai shiru kamar mutuwa ta gifta!!


''Yauwa... da farko dai muna yiwa kowa barka da zuwa wannan gasa ta Deniziyya Kuronikil a karo na ɗari biyu da arba'in da uku.


''Kuma fatan kowa ya koma gida lafiya, harda....masu fafatawa.


''To a gurguje ba tara da ɓata lokaci ba zan bi takan ƙa'idojin wannan gasa, sannan kuma zan bayyana kyaututtukan wannan shekara!


''To ƙa'idoji dai basu canjaba; kamar kullum acikin wannan gasa zamu fitarda, mataki guda biyu;


"Matakin da ake kira da Janareshin Béligi, wanda za'a samu har mutun shida daga cikin masu fafatawa.


"Sai kuma mataki na biyu, wato Shugaban ƙarnin gobe (Béligi lee), wanda kuma mutun ɗaya ne kawai zai iya ci.


"Kuma kamar yadda kuka sani, muƙamin Beligi Lee, yau shekaru sama da hamsin kenan babu wanda yaci shi, hasalima a gabaki ɗayan tarihi, mutun biyar ne kawai suka taɓa cin wannan muƙamin." Yana faɗar haka ya ɗaga kai izuwa ƙaton allon dake manne a saman wannan filin, inda aka rubuta sunaye biyar da manyan baƙi akai;


Deniz Ururu


Maikiro Abbas


Han'Ibal


Sarki Rafiya


Bihanzin Mai dauwamammen sara


Ya ja dogon numfashi, sannan yaci gaba da cewa, "Ba komai bane yasa hakan ba, sai cewar, bawai kawai buƙata ake ka zama na farko ba a wannan gasar ba, a'a, sai ka haye Siriɗin Jinzidal," yana faɗar haka ya ɗaga wani ɗan sanda a hannunsa ya nuna shi izuwa wannan allon dake ɗauke da sunayen nan biyar, lamarinda yasa nan take wani jan ƙarfe ya bayyana. 


Wanda ya haɗe gefen zagayen wajen fafatawar da kuma wannan allon dake sama.


Babu abinda ke tashi, sai kyalli daga tsinin wannan jan ƙarfe, wanda yafi reza kaifi, amma kuma yafi dinare tauri. Lallai ko iska idan ta gilma takan wannan tsini saita rabe gida biyu ballantana ma kuma mutun.


Abinda kuma ake so, shi ne, abi ta kansa a je harkan wannan allo, sannan sunanka ya bayyana. A kusan kowacce shekara za'a samu mutun ɗaya wanda zaije zagayen ƙarshe, ya cinye kowa, amma sai a shekara hamsin, ba'a samu wanda zai haye wannan Siraɗi ba. Hasalima a dukkanin tarihi waɗannan ma'abota Izza guda biyar su kaɗai suka taɓa haye wannan siraɗi. Wanda kuma hakanne ya kaisu matsayin da ake kira da SARAKUNAN JINZIDAL GUDA BIYAR.


Wannan alƙalin wasa yaci gaba da bayani, "kamar kullum mun raba kowa da kowa zuwa gida-gida, kuma la'akari da yawan mutanen wannan karan mun samu kaso shida!


''Kowanne kaso idan akai busa ta farko, zasu hau ɓangaren da harafinsu yai dai-dai da.


''Sannan kuma idan akai busa ta biyu kuma, zaku fara gwabzawa!


''Zaku fafata har sai ya kai saura mutun ɗaya da zai iya tsayawa, acikin kowanne zagayen wasannin nan guda shida, wato mutun shida kenan! Wanda kuma waɗannan mutane su ne sukai nasara a wannan zagaye, na farko, kuma sune sukaci matsayin, Janareshin Beligi!


''Sai dai kuma kamar yadda kuka sani, gasar Deniziyya kuronikil, fitattu huɗu kawai take so, wanda zasu wuce zagaye na gaba.


''Saboda haka kamar yadda doka tace mutanen da zasu zamo fitattu huɗu, daga cikin Janareshin Beligi shidannan su ne mutane huɗun da suka gama wannan zagaye na farko cikin mafi ƙanƙantar lokaci!!


''Bayan an gama wannan zagaye, za kuma a kaɗa ƙugen yaƙin tsakanin waɗannan mutane huɗu, wanda daga ƙarshe ya danganta da abinda amsa ta bayar, za'ayi zaɓen zagayen kusa dana ƙarshe tsakanin su huɗun.


''Sannan kuma a ƙarshe, za'a fafata tsakanin mutun biyu da sukayi nasara a zagayen!


"Shi kuma, wanda yai nasara a ƙarshe, yana da zaɓi, kodai ya hau siraɗin Jinzidal, ya ƙarasa ladansa, idan yaci sunansa ya shiga cikin waɗannan sunayen manya biyar. Shima ya zama Sarkin Jinzidal, Ko kuma ya haƙura ya tafi, kasancewar acikin ɗaruruwan mutanen da suka taɓa hawa wannan siraɗi, tara ne kaɗai suka sha da ransu! Biyar daga ciki sune suka rayu kuma suka zamo Sarakunan Jinzidal, huɗu kuma daga ƙarshe suka mutu a kan gadon asibiti saboda jikinsu bazai iya ɗaukan dafin dake kan wannan tsibiri ba. Kuyi sani cewa lallai dafin dake kan wannan siraɗi tun farkon duniya aka haɗashi, kuma indai ya taɓa jikinka to lallai kwananka yazo ƙarshe.


''Abu ɗaya dai, daya kamata kowa ya sani shi ne, a wannan gasar ko ka mutu ko kayi rai, ya rage ya naka da kuma wanda yai nasara, ƙasar Sirish ta Deniz Iluru baza su ɗauki nauyin komai ba.


''Mu dai kawai abinda muke so mu gani shi ne, wane ne na ƙarshe dake tsaye!!


''Idan kowa ya gane kuma ba mai tambaya, to zamu fara.


An dai ɗau lokaci babu wanda yace uffan, sauran ƙiris ayi busa ta farko, kawai sai wani saurayi mai ɗaure da baƙin kyalle a goshinsa ya samawa kansa hanya ta cikin mutane, inda ya ɗaga hannu ya tambaya, ''idan mutun ya fita daga cikin zagayen wasa fa?''


Wannan alƙalin wasa bawai mantawa yayi da wannnan ƙa'ida ba, hasalima gani yake abu ne da kowa ya riga ya sani, cewa kana fita an cire ka kawai, saboda haka baiji daɗin wannan tambaya sosai ba.


Amma dai saboda jama'a ya bawa wannan saurayi amsa a hasale, "ya fita!"


Tuni sauran jama'a suka fara maganganu suna nuno wannan saurayi, amma ba'a ɗauki lokaci ba akai busa ta farko kowa hankalinsa ya dawo kan waɗannan filayen wasa shida, dake tsakiyar fili!!


Wannan saurayi mai baƙin kyalle ba wani bane illa Armad Wilbafos. Duk da cewa Miyurarsa ta ɓace, amma ya riga ya saba da ɗaura kyalle a goshinsa, saboda haka yake ɗaure da wannan kyalle. 


Kafin kace meye wannan tuni kowa ya hau kan filinsa kuma waje ya hargitse babu abinda kake ji sai ƙarar sara da suka ko'ina.


Fafatawa kawai ake akan waɗannan filaye shida, babu wani nutsuwa ko kuma wata fasaha ta musamman.


Abinda kawai kowa acikin wannan turnuƙu ke so shi ne ya zamanto ya gama da ragowar, kuma ya zama na ƙarshe a tsaye cikin ƙanƙanin lokaci. Ƙarar takubba da masu ne kawai ke tashi daga cikin ƙurar data turnuƙe tasa ko gano masu fafatawar ba'ayi.


Ana cikin wannan hali akan tawaga da aka sawa rukunin B, Armad na tsaye, baya ko motsi, idan dai ba zuwa kansa kayi ba, to bazai nufe kaba.


Tuni Armad ɗin ya daɗe da gano wani abu acikin ransa; cewa a irin wannan faɗa da akeyi lallai bazai taɓa samun nasarar da yake nema ba.


Hakan nema kuma yasa ya tsaya cak yana tunani akan wacce fasaha ya sani guda ɗaya wadda zata share duk waɗannan karen-kuci-kubamun ma'abota Izzar dake cikin rukuninsa a cikin ƙiftawar ido.


Tayadda zai zamo shishi kaɗai ne a tsaye ba tare da ɓata lokaci ba!


To amma abinda bai sani ba shi ne, tuni wasu mutane biyar ɗaya daga cikin kowanne rukuni suma sukai wannan tunani irin nasa.


Sabida haka, a dai-dai lokacin daya ɗaga takobinsa da niyyar aiwatar da abinda yai niyya, a rukunin C wani saurayi shima acikin ƙurar dake tashi ya ɗaga mashinsa sama da irin niyya ɗaya da Armad.


A rukunin D kuwa wani ma'abocin Izza shima yana nan ya ɗaga Fafalonsa-mai-lanƙwasa, a rukunin E kuwa babu abinda wannan saurayi yayi face tafa hannunsa kawai, abinda yasa wata lamba mai alamu da lamba tara ta bayyana a goshinsa.


A rukunin A kuwa wani saurayi a tsaye. Babu abinda yayi sai kawai mayarda takobinsa cikin gidanta, wanda a dai-dai lokacin kuma wani jibgegen mutun yana nufoshi, amma babu abinda yayi sai kawai ya ƙara taku ɗaya zuwa kusa da wannan mutumi wanda gatarinsa yake neman sara kan wannan saurayi biyu. 


Amma ina, rashin sani yafi dare duhu, da ace sauran masu fafatawa acikin wannan waje sunsan irin tsafin da waɗannan ma'abota Izza shida suka shirya, lalllai da basu tunkaro su ba.


***

Babi na talatin da ɗaya : Na ɗaya dana ƙarshe


Koda waɗannan ma'abota Izza guda shida suka tsaya, sai kowa acikinsu ya buɗe baki tare da furta waɗansu ɗalasimai waɗanda suka shafi al'amarin Izzarsa. Dukkaninsu nada cikakkiyar amanna cewa lallai waɗannan ɗalasimai nasu sunfi ƙarfin kowa dake cikin zagayen karawarsu. Badan komai ba saidan cewa a wannan gasa zance ne na waye ya riga gamawa. Domin suna da cikakkiyar masaniyar cewa acikin waɗanda sukai nasara guda shida daga kowanne zagaye, guda huɗu kaɗai za'a ɗauka suje zagaye na gaba. Waɗannan kuma sune wanda suka riga sauran gamawa.


Musamman duba ga cewa da dama daga cikin waɗanda suke kwabzawa dasu a rukunin nasu basu kaisu ƙarfin Izzarsu ba. Saboda haka mutun shidan nan suna da amanna sai sunyi nasara a rukuninsu, kawai dai kowa yana ƙoƙari ne ya riga sauran ƴan uwansa gamawa.


Saboda ƙarar karan batta dake faruwa da ihun mazaje suna fafatawa a cikin dukkanin wajajen shida, babu wanda ya kula da abinda suke aiwatarwa, kusan kowa ya takansa yake. Kowa so yake ya samu nasara ko ya samu ya tseratsarda ƙannensa da ƴaƴansa da abokansa da iyayensa daga zama bayi. Domin rashin yin nasararsu tana nuna kason mutanen da suka kawo sun zama bayi kenan a wajen wanda yayi nasara. 


A dai-dai lokacin da waɗanann samari shida ke ƙoƙarin aiwatar da munanan hare-hare akan ƴan uwan fafatawarsu, kowa ka gani idonsa a rufe yake. Babu abinda nakan filin dagar nan suke sai saran junansu, jini na malala, kayika na tsalle sama. Amma tamkar ba ɗan adam ake kashewa ba, ma'abota kallon fafatawar nan kawai sai ihu da jin daɗi da shewa suke daga kan kujerunsu da suka zagaye filin wasan. Kai daka gani kasan sun saba gani kuma wannan ba wani sabon abu bane. 


Ana cikin haka saurayin dake rukunin E, wanda babu makami a hannunsa, ya tafa hannayensa guda biyu! Suma sauran samarin kawai sai wani shuɗin haske ya fara tashi daga jikinsu, lamarinda ta fara jan hankalin wasu daga cikin masu fafatawar da kuma da yawa daga cikin ƴan kallo.


Abu na gaba kuwa da aka gani a kowanne rukuni ya bada matuƙar mamaki, wanda saida yasa dukkanin wanda ke kallon wannan gasa acikin wajen ko kuma a waje ta hanyar Ayrid mai nuna hoton bidiyo, buɗe baki da shiga mamaki mai haɗe da firgici.


Bayanin dalla-dalla abinda ya faru ba abu bane mai yiwuwa ba, domin komai ya faru ne cikin rabin ƙiftawar ido kuma a tare. Sannan kuma ga wannan shuɗin haske ya ƙaru matuƙa tayadda ya haskewa mutane da dama idanu.


Ga kuma wani wuta jajawur datai ƙuwa tare da tsalle sama ta kuma haske ilahirin filayen fafatawar nan guda shida. Lallai akwai ma'abocin aljanin wuta a ɗaya daga cikin waɗananan filaye.


Bayanda wannan wuta da wannan shuɗin hasken suka gauraye suka bada wata irin kala mai ban tsoro, suka lafa, sai mutane sukai arba da filaye guda shida. Kowanne babu kowa a tsaye sai mutun ɗaya; A rukunin A, wani saurayi ne riƙe da wata doguwar takobi da tama fishi tsayi. Yana sanye da kaya masu zanen ɗorawa da baƙi. Fari ne mai yawan baƙin gashi. Idanunsa a tsaye suke, sannan kuma idan kayi duba cikinsu babu abinda zaka gani sai azabar tsana da kafiya, kai kace duk wata tsana da fushi da baƙin cikin duniya daga cikin waɗannan idanu suka samo asali.


Fatar fuskarsa kuwa a ɗame take, kana gani kasan yayi shekaru da dama baiyi dariya ba.


Kallon ɗaya zakai masa ka gane cewa a lokacin yana yaro kyakkyawa ne, kuma kuma har a wannan lokacin idan ka kalli yanayin zubin hancinsa da fuskarsa kasan irin kyan nan ne da baƙin ciki da ɓacin rai yake lalatawa.


Kaf tsokar jikin wannan saurayi a murɗe take, kai kace basu taɓa motsi ba.


Irin waɗannan mutananne da idan aka ce kayi bayaninsu a kalma ɗaya zuwa biyu, zaka ce, 'rashin imani', kawai ka rufe baki!


Idan kuma ka kalli mutanen dake kwance a ƙasa acikin rukunin zaka tabbatar da haka.


Domin kuwa dukkaninsu ƙirjinsu a cake yake da makamai, kuma abin mamakin shi ne, makamansu ne kuma hannayensu ne suka daɓa musu su a ƙirji.


Kaf ɗinsu sama da mutun talatin gasu nan a kwance a ƙasa matattu!


Wannan saurayi ba wani bane illa Ikenga O. Bayajidda!


Ba jimawa ƙasar filin rukunin na A ya fara haske, kafin daga ƙarshe ya nuna alamun daƙiƙa ashirin da tara.


Wato alamun cewa Ikenga ya gama a tsahon daƙiƙa ashirin da tara kenan. Koda wannan haske ya ɗauke sai Ikenga ya ɗaga ya ɗanyi  wani murmushi mai cike da nufaƙa. Ɗaga kan nasa kuma ya ƙara bayyanarda wani ƙaton tabo a wuyansa.


A rukunin B kuwa wannan saurayi mai riƙe da takobi wadda bata fi tsayin hannunsa ba, da kyalle a goshinsa shi-shi kaɗai ne a tsaye.


Kuma idan ka kalleshi sosai zaka ga ba wani bane illa Armad Wilbafos. Wanda bai samu hankalinsa ya kwanta ba saida yasa kyalle ya rufe goshinsa duk da kuwa Miyurar tasa ta ɓace kuma baisan inda tayi ba. Amma kasancewar kyallen a goshinsa yana ɗan sawa yaɗan manta na ɗan lokaci. Tuni Armad ya yanke acikin ransa cewa duk ma inda wannan Miyura ta tafi lallai saiya nemo ta. Domin yafi kowa sanin amfanin ta. Koba komai tana ƙara masa ƙarfin Izzza, kuma da dama daga cikin fasahar walƙiyarsa suna buƙatar babbar Izza, wadda kuma bashi da ita. Amma ta dalilin wannnan Miyura bashi da matsala.


A kwance a ƙasansa ragowar ƴan rukuninsa ne suke ta murƙususu amma babu wanda ke iya tashi, saboda haka bayan ƴan daƙiƙu shi ma wannan haske ya bayyana, wanda ya sa masa alamun daƙiƙa talatin da biyu, wato ƙarin daƙiƙa uku kenan akan na Ikenga.


A rukunin C kuwa babu kowa akan gaba ki ɗayan filin. Dukkansu kamar ansa tsintsiya an sharesu zuwa ƙasa.


Babu kowa sai wani saurayi mai yawan gashin fuska, riƙe da fafalo mai lanƙwasa.


Sannan hasken dake tashi na nuna daƙiƙa talatin dai-dai.


Saurayin nada faɗi da yawan gaske, hakan nema yasa duk da cewa bawai gajere bane kuma ba dogo bane, amma da dama sai a ringa yi masa kallon gajere. Lamarinda bai masa dadi Ko Kadan! 


Amma kuma wani abu dashi shi ne, fuskarsa bata da faɗi sosai, sannan kuma baka buƙatar a gaya maka cewa tsatson wannan saurayi ma'abota sarauta ne.


Domin a duk cikin waɗannan samari, da wuya ka samu mai yawan kyawunsa da kuma fitarda kamalar sarauta.

Wani ƙarin abu ga fuskarsa shi ne, saboda yawan gashin dake fuskarsa sa, gashin girarsa ma a haɗe suke, wanda hakan ya bashi kamanni na daban, kuma da dama suna ganin abinda ke rage masa kyau kenan!


Amma duk da wannan, babban abinda zaisa idan ka kalli wannan saurayi baza ka taɓa mantawa dashi ba shi ne idanunsa.


Babu komai acikinsu face tsananin azabar masifar marmarin yaƙi!! Irin soyayyar nan da baza ka iya rabuwa da abu ba, irin ta sak zaka gani acikin idonsa, amma ba soyayyar komai bace ba illa yaƙi.


Wannan saurayi ba wani bane illa Deniz Bizaya! Ɗan sarki Deniz Iluru.


Saboda tsananin sansa da yaƙi, ance kullum yana cikin gwabzawa, har nemo abokan fafatawa yake a kullum ƙasa zuwa ƙasa, kuma hakan nema yasa suka saba da Ikenga! Idan mai Karatu bai mantaba an gano su suna fafatawa kwanaki kaɗan kafin a fara wannan gasa. Koya waɗannan giwaye suka ji, domin dai ga dukkan alamu basu samu damar haɗiye su ba. Tunda gasu acikin filin daga.


A rukunin D kuwa, saurayi ne riƙe da mashi a hannunsa, kuma kana ganinsa, zaka san cewa ransa ɓace yake kuma acikin zuciyarsa akwai ɓacin rai na rashi!


Amma kuma idan ka lura zaka ga wannan ɓacin ran baishiga cikin ƙashinsa ba kuma baikai irin ƙiyayyar dake zuciyar Ikenga ba!


Fuskarsa babu gashi ko guda, kuma kyakkyawa ne, fari fat dashi kamar fulanin farko!


Idan ka duba ƙasansa zakai arba da yuyar mutane kwance fululu!


Amma abin mamakin da wannan rukuni shi ne, dukkanin waɗannan mutane dake kwance, idan ka lura zaka ga cewa da dama daga cikin waɗannan mutane waɗanda da suka kasance farare, amma a wannan lokaci suna ƙasa fatar jikinsu ta sauwa izuwa shuɗiya!!


Sannan ragowar kuma waɗanda suke baƙaƙe, su kuma sun ƙara baƙi sosai matuƙa, tayadda kana ganinsu zaka gane cewa sun canja.


Amma bisa mamaki, duk wannan abin hasken dake tashi daƙiƙa talatin da biyu shima yake nunawa, wato kamar na Armad.


Babban wajan al'ajabin shi ne rukunin E, inda babu abinda kake ji sai ihun mutane waɗanda rashin sa'a ya tadda su, domin kuwa a wannan lokaci idan ka kallesu zakai arba da cewa acikin wata jar wuta suke muraran suna soyuwa!!


Duk inda ka kalla sai kaga wannan wuta ce a jikin mutanen, sannan kuma sun kasa motsawa a wani yanayi na kamar ta ɗaure su da ƙasar wajen, ta yadda ko motsi basa iyayi.


Kuma abin mamaki shi ne, hasken dake tashi yana nuna masa daƙiƙa ashirin da takwas ne, wato ƙasa dana Ikenga ma.


Kuma duk da abinda ke faruwa, murmushi ne kawai a fuskar wannan yaro.


Sai kuma wani abin al'ajabi idan ka kalli idanun wannan yaro mai suna Han Amuru wanda bai wuce shekaru sha shida ba, zaka alamun aljanin wuta yana balbali da wuta. Kai kace idanun sun ƙone gaba ɗaya. Sai dai kuma amma saboda wannan aljani nasa ma'aboci wuta, shi baya jin zafin wutar ko kaɗan. Ko kuma ace shi bata aiki a kansa. Wannan saurayi shi ne yazo daga ƙasa ta uku. Wato mahaifar Armad kenan. Kuma daga ƙabilar Han, wato ƙabilar babban sarkin ƙasa ta uku kenan.


A rukunin F kuwa wani saurayi ne tsaye da takobi mai hasken gaske, kai kace walƙiya ce saboda yadda take haskawa.


Yana tsaye, kuma duk inda ka duba, idan banda wajen da yake tsaye akai, zaka ga ya rududduge ya zama gari, duk sauran abokan karawar tasa na ƙas.


Wato dai a taƙaice shi kaɗai ne akan wajen da aka ƙaiyaje!


Ya riga ya gama fashe ko'ina, kuma sauran abokan fafatawar tasa suna tsaye a zagaye dashi a ƙasa, amma haka zasu haƙura, babu abinda suka iya saidai kallo. Domin an riga an cire su saboda sun fita daga kan kewayen.


Idan ka dubi wannan saurayi sosai zaka ga ashe ba wani bane illa Kiru Sisiyu, yayan Zahra! Kuma duk yadda akai yayi amfani da farar takobi. Wadda idan mai karatu bai manta ba ta kusa halaka Armad a baya.


Amma fuskar Kiru bata nuna alamun komai, ko kaɗan.


Wato dai bata nuna farin ciki, ba kuma ta nuna baƙin ciki, tamkar babu wani abu da yake tunani acikin zuciyarsa!


Idan da Armad zai ganshi a wannan lokaci kuma ya tuna da yadda ya sanshi, to da lallai saiya sha mamaki.


Hasken dake tashi daga ƙasansa na nuna daƙiƙa talatin da biyar.


Bakin ƴan kallo a buɗe yaƙi rufuwa. Kai hatta shi kansa alƙalin wasan bakinsa a buɗe yake, idanunsa na cike firgici.


Can bayan wasu ƴan daƙiƙu ya dawo hayyacinsa inda ya bayyana cewa, da Ikenga mai ashirin da tara, da Hán-Amuru mai ashirin da takwas, da kuma Deniz Bizaya mai talatin da ɗaya duk sun wuce zuwa zagayen kusa dana ƙarshe.


Amma Armad da Kiru da Niyashi duk sun sami maki iri ɗaya wato talatin da biyar, saboda haka, abisa dokar Deniziyya za'a kawo musu Alkadar domin fitar da gwani.


To a wannan lokaci ne aka tafi hutun lokaci, kafin a dawo a fitarda gwani a tsakaninsu Armad, sannan kuma a wuce izuwa gasar kusa dana ƙarshe.


Kuma a lokacin aka bawa sauran manyan baƙi damar zasu iya zuwa su tattauna da waɗanda suka zo dasu.


Kuma a wani lamari mai ban mamaki kawai saiga tawagar Banfiriya nan sun danno kai!!!


***


Babi na 32 : Alkadar 


Wani abin mamaki, wannan tawaga ta Banfiriya suna zuwa suka nufi inda Kiru yake, kuma suka jashi gefe suna ƙus-ƙus. Babu wanda yasan mai suka tattauna, amma dai daga baya sun nemi waje sun tsaya a kewayen wajen da ake fafatawar, wato dai basu shiga wajen manyan baƙi ba.


Ragowar sauran manyan baƙin kuwa irin su Asifu (wanda akafi sani da RUWAN BALA'IN), baima nuna alamun yaga shigowarsu ba, kawai hira yake. Suna tattaunawa akan Izza da ɗaya daga cikin mutanen da suka rako sarki Deniz. Wani Badenize da ake kira da Deniz Kalhari.


To da yake idan ka duba gefen Armad zaka ga Nusi a gefensa. Kuma tunda ta fito daga cikin wajan manyan baƙi take yi masa bayani akan Alkadar.


Ji take kamar wani babban jafa'i na dab da saukarwa Armad, saboda haka kwata-kwata bata saki jiki ba.


Kuma tunda daman su Maikironomada gaba ɗaya basu fiya damuwa da tura wani babba zuwa wannan gasar ba, shi yasa da tace zata zo, da wuri ta zama shugabar tafiyar, tunda babu wanda yakaita matsayi acikin tawagar.


Hasalima wannan shi ne babban dalilin da yasa Denizawa basu kula dasu ba a baya, saboda a matsayinsu na babbar daular tsohuwa, bai kamata ace basa taɓa turo wani babba ba, kai koda matsayin ɗan majalisa kawai. Wanda hakan yasa Denizawa suke ganin raini ne yasa.


Nusi ta gama yiwa Armad bayani kenan tana niyyar komawa wajen manyan baƙin, kawai taga ƴan Banfiriya sun tsaya saboda haka ita ma ta tsaya.


Acikin wajen manyan baƙin nan kuwa tuni sarki yasa aka wadatashi da kayan ci da sha, sannan bayan wani lokaci ya ƙara komawa gefen Uznu'Ururu, wanda har wannan lokaci idanunsa a rufe suke, yana isa ya dubi Uznu tare da cewa, ''ina fatan yaran suna ƙayatar dakai!


''Kaga yanzu duk wanda suka futo matakin zagayen kusa da ƙarshe kyautar da zan basu ita ce Ayrid mai mataki na ɗaya guda hamsin hamsin sannan kuma da ƙusar yaƙi guda ɗaya ga kowannensu.


"Wanda yazo na biyu kuwa, Ayrid guda ɗari da kuma ƙusar yaƙi guda biyar.


"Amma ga wanda yazo na ɗaya kuwa kyautarsa ita Ƙusar yaƙi guda goma da kuma Ayrid mai mataki na goma."


"Wato ni da kaina zan basu wannan kyauta, saboda haka ya zamo zai iya yin nutso a wannan fage na Izza kamar yadda kowanne Badenize zaiyi. Duk wannan kyauta kawai zan bada ita ne a matsayin nuna jin daɗi ga ƙasashen da suka taka rawa a wannan gasa acikin ƙasa ta. Kaga idan aka haɗa da kyautar bayi ga waɗanda  sukai nasara ɗin, to kaga gobe kowacce ƙaramar ƙasa babba ko ƙarama zata so ta taka rawa a Jinzidal idan za'ai a gari na na Seerisha." Sarki Deniz Iluru ya ƙarasa bayanin sa da kurɓar wani ƙayataccen fari lemo dake hannunsa.


Sai dai kuma Uznu Ururu shiru kawai yai masa baice masa komai ba, sai can wani lokaci, tuni Armad da Niyashi da Kiru sun hau kan ɗaya daga cikin sababbin filayen da akasa domin gudanar gasar mutun-mutumin Alkadar, sannan acikin wata murya ƙasa-ƙasa ya ce, "Abubuwa masu muhimmanci sun taso, na farko bayyanar Magajin Wilbafos, wanda kasan ba batu bane da Ururu take ɗauka da wasa ba.


"Na biyu, muna da isassun hujjoji dake nuna mana cewa akwai masu san tada ƙayar baya akan Rukunin Jinzidal, nan bada daɗewa ba!!"


"Na uku, akwai ƴan ƙabilar Djinn, waɗanda suma suke ƙoƙarin komawa garin Shaedníza da kuma ƙara yaɗa abubuwan da suka afku a wannan shekara, domin mutane suji. Kaga ta haka, tunda abin ya haɗa da Tirifil-fakta, mutane zasuyi ca akai, kaga tashin hankali zai afku." Wannan mutun mai suna Uznu'Ururu yaci gaba da bayani cikin mulki da isa da ƙarfin Izza. "Amma mafi muhimmanci akwai abinda nayi shekaru sama da ɗari tara ina nema. Kuma nayi duba izuwa taurari bakwai dake saman ƙasa ta farko. Wanda suka tabbarmin da cewa wannan abu da nake nemo zai bayyana a wajen wani yaro dazai taka rawa a wannnan gasa.


"Duk waɗannan dalilai, su ne suka taso ni nazo wannan gasa. Da fatan kuma Denizawa zaku bamu haɗin kai domin kautarda asarar rayukan da ba dole ba."


Yana gama jawabinsa, bai jira wata amsa daga sarki Deniz Iluru ba, kawai ya juya kai, idanunsa a rufe, ya kuma ci gaba da fuskantar filin fafatawar nan. Wato dai zaka iya cewa, koma sarkin ya yarda koma bai yarda ba, wannan shi ta shafa, domin a iya saninsa, su ma'abota Ururu, su na da ikon aikata duk abinda suka ga dama, kuma a duk lokacin da suka ga dama.


Dama dai taƙarƙashin ƙasa, shima sarki Deniz yaji waɗannan abubuwa, cewa wani daga cikin manyan-manyan ƙusoshin duniyar ƙasa bakwai, yana so ya tada zaune tsaye akan Rukunin Jinzidal (wato cinikin bayi da ake.) 


Sannan kuma bayyanar Magajin Wilbafos, abu ne da kowa ya sani, amma ba'asan ko waye ba, duk da kuwa kusan kowa farautarsa yake.


Sai kuma batun ƴan ƙabilar Djinn, wanda shi ne kaɗai sabon abu, a abubuwan da yaji.


Sai dai kuma babban abinda ya ɗagawa wannan sarki hankali shi ne, da abu na ƙarshe da Uznu Ururu ya faɗa akan abinda yake nema. Wanda nan take Deniz Iluru ya shuga tunani akan ko menene.


Hakan nema yasa tunda Sarki Deniz yaji wannan batu, ilahirin annurin dake fuskarsa ya ɗauke, kuma bai ƙara cewa komai ba.


Hasalima daka ganshi zaka san idanunsa ne kawai acikin filin gasar, amma tunaninsa yana wata duniyar. Lallai yasan wani bala'I yana kan hanya. Badan komai ba sai dan girman ikon Uznu Ururu da ya sani. Koda kuwa acikin ma'abota Ururu yasan shi ɗin mutun ne mai darajar gaske.


Tun bayan sanda ya zamanto mutun ɗaya daya dawo daga wancan fafatawa data faru a shekaru da dama da suka wuce. Wadda tayi sanadiyyar samun shi kansa Littafin-Takobin.


Saboda haka zai iya turo wasu ma'abota Ururun ma dake ƙarƙashin ikonsa.


To amma mai yasa yazo da kansa??


Kusan tunda manyan baƙi daga Banfiriya suka tsaya a kusa da Kiru, kuma suka ƙi tafiya, itama Nusi ta dawo, dukkanin ragowar waɗanda ke tafe da waɗannan mazaje ma'abota Izza guda huɗu suma sun sauko ƙasan.


Wato idan ka duba zaka ga mutanen Maikironomada tare da Armad, mutanen Banfiriya da Kiru, Mutanen Infiriya da Niyashi, mutanen Hán, daga ƙasa ta uku tare da Hán-Amuru, sai kuma Denizawa waɗanda suka fi kowa yawa, dan sunkai kusan su goma sha biyu, a tattare da Deniz Bizaya.


Saurayi ɗaya wanda babu kowa a tare dashi shi ne Ikenga!


Kuma idan ka dube zaka san cewa kwata-kwata hakan bai dame shiba, hasalima ko a jikinsa, kawai kansa ne a ɗage yana kallon sama acikin matuƙar nutsuwa, tamkar wanda yake kallo wani abu da baya so ya wuceshi, ko kuma wanda yake karanta tafiyar taurari!!


Ana cikin wannan yanayi ne, wanda kowa ke ƙoƙarin gayawa nasa abinda ya kamata yayi da kuma ƙara nuna musu muhimancin samun nasara, kawai alƙalin wasa ya sanar cewa, sarki Deniz Iluru ya bada damar a sanar da kowa kyaututtukan wannan shekara, abinda ya ƙara rikita wajen! Domin kowa yayi tunanin kawai kyautar bayi za'a samu kawai kamar yadda aka saba. To amma ga dukkan alamu gashi sarki Deniz Iluru ya ƙara wasu kyaututtukan.


Amma wannan alƙalin wasa bai tsaya ɓata lokaci ba ya zayyana dukkanin kyaututtukan da suke akwai, kamar yadda sarki Deniz ya gayawa Uznu'Ururu.


Jin waɗannan kyaututtuka yayi matuƙar hargitsa ƴan kallon gaba ɗayansu, kai bama su ba kaɗai, hatta waɗannan manyan baƙi dake tare da waɗannan samari shida saida alamun mamaki suka bayyana ƙarara a fuskarsu.


Kai hatta Asifu dake cikin wannan waje yana tattauna al'amuran Izza da wannan Badenize, saida ya juya ya kalli Sarki Deniz cikin mamaki.


Kai gaba ɗaya wannan taro, wanda idan ka lissafa, sama mutun dubu ɗari suna cikin wajen, amma saida aka shiga shiru na ƴan daƙiƙu kamar mutuwa ta gifta.


Kai hatta masu kallo wannan gasa a sauran garuruwan Denizawa, suma saida suka shiga mamaki!


Wataƙila mai karatu yana buƙatar ɗan ƙarin bayani kaɗan akan darajar Ayrid. Shi dai Ayrid kamar yadda aka labarta a baya kwaya ce ƴar ƙarama kamar masara ko kuma dawa. Wasu su na zuwa manyan wasu ƙanana. Kowanne yana da launinsa na daban. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, akwai busasshen Ayrid, akwai kuma ɗanye. Dukkaninsu daga irin bishiya (zangarniya) ɗaya suke. Shi busasshe, shi ake sarrafawa izuwa sisi da kwandala domin kashewa. Akwai ma'aikatu na musamman dake shalkwatar Ururu wanda ke sarrafa irin wannan Ayrid. Shi kuwa ɗanyen Ayrid shi ne wanda keda mataki-mataki kamar yadda aka gani a baya. 


Kamar wanda Nusi tayi amfani dashi (mai keken doki). Akwai wasu da dama irinsa. Ana iya amfani dasu wajen ajiya na kayan abinci ga matafiya ko kuma kayan yaƙi. Akwai na magani, akwai na sihiri, akwai masu ƙara ƙarfin Izza. Kai dama dai sauransu. Kuma iya matakin Ayrid ɗin, iya darajar abubuwan da zai iya yi.


Idan ka duba zaka ga sama da kaso casa'in da tara na al'umma iyakacin wanda suke iya mallaka, shi ne mai daraja ta uku, wanda dashi zaka ga suna tura saƙo komai nisan waje, kuma su karɓa. Sannan kuma su iya ajiye kayansu a yayin tafiya.


Amma Ayrid masu daraja sama da uku amfaninsu bazai lisaafu ba anan, domin kuwa idan muka fara za'aci shafuka da dama anayi, saboda haka ku biyu mu a gaba zakuga irin al'ajabin dake ƙunshe cikin wannan ɗan iri da akewa laƙabi da Ayrid!


Bayan kimanin mintuna sha biyar, alƙalin wasa ya bada umarnin su Armad su shiga cikin filin su uku.


Inda bayan sun shiga suka tararda wannan abu da ake cewa Alkadar!


Wannan dai ba wani abu bane illa wani mutun-mutumi da akai da jan dutse. Komai kamar na jikin mutun ne, amma a wajenda ya kamata ace fuska ce, sai ya zamana kamar gilas ne kawai, daya rufe kaf wajen.


Aciki akwai hoton lambobi guda uku a jere, wanda ba wani abu bane illa sikelin wannan abu mai suna Alkadar.


Kuma kamar yadda Nusi ta bayyanawa Armad cewa abinda kawai yake da buƙata yayi shi ne, yayi amfani da sak irin Izza da yai amfani da ita ya wuce mataki na farko, ya tattare ta ya kuma daki cikin wannan mutumi da ita.


Ta kuma gaya masa cewa wannan sikeli ɗaya zuwa ɗari ne, kuma duk wanda ya fi kowa lamba shi ne zai wuce zagayen gaba!


Saboda haka a lokacin Niyashi shi ne a gaba, Kiru na biyu, sannan kuma Armad na ƙarshe.


Cikin sauri, fuska a murtuke, Niyashi ya isa kusa da wannan mutun-mutumi, inda ya ɗaga hannu ya daki cikin wannan mutun-mutumi.


Hakan na faruwa lambobin dake fuskarsa suka fara bada haske, sannan suka fara motsi.


Kan kace meye wannan tuni sun wuce hamsin... sittin..saba'in, inda suka fara rage sauri.


Amma dukda haka saida suka kai tamanin da tara, sannan suka tsaya.


Kan kace meye wannan shewa ta ɓarke, tuni har an fara taya ƴan Infiriya murna.


Kasancewar dama abinda su Armad basu sani ba, shi ne, mafi girman makin da aka taɓa samu a gasar Jinzidal ƙarama shi ne casa'in da ɗaya, saboda haka samun tamanin da tara a wajen Niyashi lallai abin yabo ne.


Ana cikin haka ne Kiru ya isa gaban Alkadar, inda ya ɗaga takobinsa da niyyar ya caki cikin Alkadar ɗin dashi, amma a wani salo mai ban mamaki wata murya ta fara magana acikin kunnensa, wadda kuma shi kaɗai ke iya jinta, duk da kuwa ba'a hankali take maganar ba!!


Nan take hannunsa ya tsaya cak a sama, abinda yasa ƴan kallon buɗe baki.


Wannan murya cike da wata irin Izza mai ban mamaki ta ci gaba da raɗa masa, ''kada kayi amfani da sama da kaso tamanin na Izzarka!''


Wannan murya na gama faɗa ta ɗauke, inda takobin Kiru ta ci gaba da tafiya daga inda ta tsaya.


Ta kuma ƙarasa ta daki cikin Alkadar ɗin, lamarinda yasa wata ƙara tayi sama sannan lambobin suka motsa kuma basu tsaya ba har saida suka je sittin!!


Shiru kamar mutuwa ta gifta, haka mutane suka kwalalo masa ido yayinda ya juyo kansa a sunkuye cikin ƴan tawagarsa.


Kai hatta alƙalin bai iya cewa komai ba har Armad ya tashi ya isa gaban Alkadar ɗin! Domin babu wanda zaiyi tunanin ɗan Behanzin guda zai tsaya a sittin kawai.


Armad na isa yasa hannu ya zare takobinsa dake rataye a kafaɗarsa ta hagu, wato takobin mahaifiyar tasa wadda tun a farkon fitowarsa daga gida yake tare da ita.


Ya kuma ɗagata sama, inda iya ƙarfinsa ya sari Alkadar ɗin a ciki!


Wanda hakan na faruwa lambobin nan suka fara motsawa cikin sauri.


Basu fara rage gudu ba, har saida suka kai sittin da biyar, inda suka fara juyawa a hankali a hankali har suka isa tamanin da takwas dai-dai!!!


Inda suka tsaya cak!


Armad ya tsaya kurum yana kallon waɗannan lambobi, kamar wanda bai yadda da abinda yake gani ba.


"Lamba ta bata kai ta Niyashi da ɗaya ba kenan?" cikin mamaki Armad ya girgiza kai. Domin ya fuskanci mai hakan yake nufi. Wato dai dashi da Kiru sun fita kenan, shi kuma Niyashi yayi nasara.

***


Babi na 33 : Bayyanar Ururu


Armad saida ya ware dukkan ƙarfin dake dantsensa sannan ya afkawa wannan Alkadar da sara. Amma bisa mamaki gashi akan idonsa yana gani cewa ƙarfin wannan fasaha bata kai ƙarfin fasahar da Niyashi ma'abocin mashi yayi amfani da ita ba!


Koda yake Armad kusan yayi tunanin hakan zai iya faruwa, tunda dukkanin waɗannan samari da yake karawa dasu yara ne waɗanda suke karɓar kulawa ta musamman daga manyam ƙabilu.


Wanda ma zaka iya cewa acikin ƙabilunsu anai musu kallon waɗanda zasu jagoranci ƙabilun ne a gobe.


Saboda haka Armad yayi tunani cewa lallai dukkaninsu baza suyi amfani da ƙananun fasahohi ba ko kaɗan, kuma su ɗin ba ababen da Armad zaiyi wasa da su bane! Musamman duba ga cewa ya rasa Miyurarsa.


Kuma hakan ya ƙara tabbata acikin ransa, a lokacin da yaga makin da Niyashi ya samu.


Kamar yadda ta gaya masa, amfanin Alkadar ɗin shi ne, a tantance tsakanin waɗanda suka samu maki ɗaya, wane ne Izzar da yayi amfani da ita tafi ƙarfi.


Hakan zai iya kawo adalci, domin tunanin cewa wani lokacin Izzar ka zata fi ƙarfi, amma ka gamu da abokan gabar da zasu fi na ɗan uwanka.


Saboda haka shi Alkadar abu ne da zai banbance tsakanin dukkan Izzan da akai amfani dasu domin fitarda wanda yake gwani na gaskiya acikin wanda suka sami maki iri ɗaya.


Saboda duk waɗannan abubuwa, duk da tunanin dake ran Armad ya daure bai ƙara ko kuma canja Izzar tasa ba, amma kuma bisa takaici gashi makinsa bai kai ba.


Abu na farko daya fara zuwa ransa shi ne, irin imanin da Nusi tayi cewa shi zai ci, amma gashi ya faɗi. Saboda haka da wace fuska zai kalle ta ma!! Shi ne kawai tambayar da yakewa zuciyarsa.


Acikin wannan waje na manyan baƙi kuwa, tun kusan sanda Uznu ya gayawa sarki Deniz abinda ke tafe dashi, sarkin ya shiga wani yanayi, bai kuma ƙara cewa komai ba sai a wannan lokaci, inda ya motsa domin bada umarnin a kaɗa wasa domin zuwa zagaye na gaba.


Sai dai kuma a wannan lokaci ne, mutumin dake zaune a gefensa, wato Uznu'Ururu, wanda tunda yazo bai buɗe idanunsa ba, kai kace dama can a haka aka yisu, ba'a taɓa buɗe suba. Amma a wannan lokaci ya buɗe idanun nasa!!


Yana buɗewa sarki Deniz duk da ba kallonsa yake ba, yaji wani gumi ya keto masa, gami da rawar ɗari.


Nan take ya gane maike faruwa!!! 


Saboda haka ya fasa abinda yake niyyar yi na bada umarnin a fara zagaye na gaba. Kawai ya tsaya cak, a inda yake.


Duk da cewa sarki Deniz shi ya tsayar da kansa yana sane, amma al'amarin ba haka yake ba, ga ragowar sauran duk mutanen dake wajen, idan ka ɗauke Asifu, wanda shi ma ya nutsu, kuma kamar wata ibada ya daina motsi kwata-kwata gami da kallon gabansa kamar yadda Deniz Iluru yayi!


Amma kama daga kan wanda suke hira da Asifu, zuwa kan dukkanin ragowar mutanen da ke cikin wajen manyan baƙin, zuwa kan waɗannan samari guda shida da masu kula dasu, harda su Armad da Nusi. 


Zuwa ga dukkanin ƴan kallon dake wajen da dukkanin waɗanda ke bibiyar abubuwan dake faruwa acikin wannan fili saida suka shiga cikin wani yanayi mai ban mamaki.


Abinda kuwa ya faru shi ne, kowa daga cikinsu ya tsaya cak a dai-dai inda yake, kuma acikin abinda yake yi.


Misali idan ka kalli Armad zaka ganshi a tsaye a gaban Alkadar ɗin, kuma yana ƙoƙarin juyawa, amma daga ganin cikin idanunsa kasan akwai wani dalili da yasa baya son juyawa.


Idan kuma ka kalli Nusi zaka ganta a tsaye cak, hannunta yana rufe da fuskarta kamar wadda ke ɓoye wani abu.


Wani daga gefenta kuwa magana yake mata a kunnenta na dama.


Haka dai kowa ka kalla zaka ganshi a ƙame cak baya ko motsi.


Dukkanin abubuwan dake faruwa, ba wani abu bane ya jawo su ba, illa buɗe wasu idanu guda biyu rak.


Idan da waɗannan mutanen na cikin hankalinsu da sun lura da cewa wajen da suke kwatsam ba dalili ya fara yin duhu. Duk da kuwa ba yamma bace, ba kuma dare bane! Rana ce tsaka, sannan kuma ga futulu ko'ina a wajen!


Tamkar kawai wani abu ne yake zuƙe dukkanin hasken wajen baki ɗaya.


Sai dai kash! Da ace wani daga cikin mutanen nan dake wajen yana cikin wajen manyan baƙin nan, kuma hankalinsa na jikinsa kamar Deniz Iluru da Asifu, da yaga cewa haka abin yake!


Wato waɗansu idanu ne guda biyu, dukkanin cikinsu gaba ɗaya baƙi ne kurum.


Baƙi-ƙirin, babu zancen wani farin ido, babu komai sai baƙi. Irin baƙin nan da idan ka kalla zakaji tamkar ana jan ka ciki saboda tsabagen duhu.


To idan da iyakacin abubuwan da suke faruwa kenan to da da sauƙi, amma ina! 


Idan ka kalli waɗannan idanu zaka ga cewa a zahiri dukkanin hasken wannan waje cikinsu yake shigewa, tamkar dai wani abu ne acikin idon wanda yake zuƙe hasken. Ko kuma shi kansa hasken ne da kansa yake ji cewa bai kamace shiba ya kasance a waje ɗaya da waɗannan idanuwa guda biyu a waje ɗaya ba, wato yana ji cewa yayi rashin kyautawa!


Kafin kace meye wannan komai dake wannan waje ya koma duhu, duhu dun ɗum!


Amma abin mamakin a dai-dai lokacin kuma kowa ya dawo hayyacinsa, kowa ya ci gaba da abinda da yake yi, tamkar wani abu bai faru ba.


Amma a wannan lokaci ne kowa ya kula da duhun dake wajen, wanda da ba haka yake ba!


Kafin kace meye wannan idanun kowa sun koma kan abu guda ɗaya rak dake da ragowar haske a wajen.


Wannan abu ba komai bane ba illa wannan Alkadar dake gaban Armad, saboda haka kan kace meye wannan hankalin kowa ya dawo kansa.


Wani abin mamakin shi ne, akan idon kowa lambar da da take kan tamanin da takwas ta juya ta dawo tamanin da tara, wato dai-dai da Niyashi.


Hakan na faruwa waɗannan idanu wanda idan ka kula zaka ga ba na kowa bane illa, Uznu'Ururu suka rufe ruf.


Wanda tamkar an kawo wuta dukkanin wannan duhun ya ɗauke ɗif, wajen ya dawo kamar yadda yake a da.


Kuma komai ya ci gaba da yadda yake. Tamkar babu abinda ya faru.


Amma banda abu ɗaya; wannan kuwa shi ne makin Armad, wanda ya ƙaru da ɗaya.


Kuma babban abin mamakin shi ne, abinda kowa kawai yake iya tunawa shi ne Armad ya samu maki ɗaya da Niyashi.


Hasalima idan ka matsa kusa da jama'a, zaka ji maganar abinda zai faru a gaba kawai suke; wanda kowa ya riga ya sani, cewa fafatawa ce gaba da gaba taakanin Armad da Niyashi, wanda yaci nasara kuma shi ne zaije kewaye na gaba!


Babu wani abu da zai iya yin bayanin haƙiƙanin abinda ya afku, wanda yasa dukkanin mutanen dake wajen duk da sun gani da idanunsu cewa makin nan ƙaruwa yayi da baya, amma kowa acikinsu, hatta Armad ɗin abinda ke ransa shi ne ya sami maki iri ɗaya da Niyashi, kuma bisa ƙa'idar gasar kamar yadda Nusi ta gaya masa abu na gaba shi ne su biyu su kece raini!


Saboda haka abinda ke ransa kenan kawai.  Wato dai a taƙaice kowa ya manta duk abinda ya faru.


Amma kuma wata tambaya da Deniz Iluru yayiwa Uznu'Ururu ita ce ta nuna cewa shi ɗin lallai yasan mai ke faruwa a wajen ba kamar sauran mutanen wajen ba, ''Uznu, mai yasa ka taimake shi?'' 


Uznu Ururu ya amsa masa da cewa, ''Wancan yaron mai suna Armad ya nada abinda nake buƙata, amma ina so na tabbatar kafin nayi wani abu. Kuma lallai indai ya fita daga gasar a wannan mataki, tabbatarwar zata yi wuya.!


''Saboda haka ina son naga fafatawarsa, domin na tabbatar da abinda nake tunani!


Shi kuwa Asifu na gefe sun ci gaba da tattaunawa akan Izza da wannan Badenize, wanda yai matuƙar nutsuwa, kai a sunkuye yana sauraron wani bayani daga Asifu, ''Deniz Kalhari, girma da faɗin al'amuran Izza sun wuce yadda kake faɗa!


''kasan kuwa hatta kwakwalwa tana riƙe abubuwan da suke faruwa na yau da gobe, a mataki-mataki ne kuwa.


''Wanda kuma gaba ɗayan waɗannan matakai sun ta'allaƙa da Izza ne!


''Misali, zaka iya raba abubuwa zuwa gida uku; na farko abinda kwakwalwarka zata iya riƙewa, wanda kamar kace Izzar ka zata iya kusantar wannan abu ne harta iya riƙeshi acikin kwakwalwarka.


''Na biyu abinda baza ka iya riƙewa ba, wanda wannan kuma shi yake nuna cewa Izzarka baza ta iya kusantar wannan abu ba, wanda kuma idan tayi to tarwatsewa zatai, shi yasa kawai saita haƙura, tayadda kai kuma bazaka iya taɓa tuna wannan abin ba, har sai sanda Izzarka takai wannan mataki!!


''Sai kuma mataki na ƙarshe wanda ke tsakatsakiya, wato zaka tunowa amma rabi da rabi!!''


Asifu yai shiru kamar wanda yake tunani, sai daga ƙarshe ya ɗago kai ya ƙara duban Deniz Kalhari, ya ce, ''Deniz, kasan a wanne mataki kake idan aka kwatanta ka da wancan mutumin dake zaune idonsa a rufe?''


Cikin sauri Deniz Kalhari ya miƙa ido ya hangi Uznu'Ururu, sannan ya dawo da kansa izuwa Asifu, gami da cewa, ''nasan yafi ni ƙarfin Izza, amma dole ma a mataki na farko nake dashi.


''Domin a irin ƙarfin Izza ta, dole komai ƙarfinsa bazai yimin nisan da zan shiga kashi na uku dashi ba, idan aka dubi wannan labari naka. Wato dai ina nufin duk abinda Izzarsa zatai, to inada ƙarfin Izzar da kwakwalwata zata iya riƙewa!!''


"Hmmm!!!" Asifu yaja wani kwauron numfashi. "Hakane!" Wannan kawai shi ne abinda Asifu ya bashi amsa dashi gami da murmushi, sannan ya bayyana masa cewa tattaunawar su akan Izza tazo ƙarshe a wannan lokaci, sai dai ko wataranar.


Domin yana so ya kalli ragowar wasannin da zasu kasance!


Haka Asifu yace, amma a zahiri abu ɗaya ne kawai a ransa. Yana tunanin cewa wannan Badenize mai suna Deniz Kalhari bai masan matsayinsa ba a harkar Izza. Saboda haka babu amfanin yaci gaba da bayani akan Izza dashi.


Sannan kuma ya maida idanunsa izuwa cikin filin da ake shirye-shiryen fafatawa tsakanin Armad da Niyashi. Idan ka lura sosai zaka idanunsa na kan Armad Wilbafos!!! Babu abinda yake kewayawa acikin ransa sai tunanin mai yasa Uznu Ururu ya taimaki wannan yaro. Sannan kuma menene tsakaninsu. Lallai zaiso yaji tsakaninsu da kuma dalilin da yasa Ururu yake taimakon wani mahaluƙi wanda ba Ururu ba.

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...