Skip to main content

422-427

 Ganin cewa har yanzu su Armad basu tsaya ba ya ɓatawa Diwani rai. Al'amudinsa ya kumbura. Cikin fushi ya dira akan Armad ya riƙe hannayensa da al'amudin ya jashi baya. 


"Ƙaraiƙisu, tarwatsa su."


Ƙaraiƙisu ya juyo a fusace ya dubi Diwani. 


"Wai ba nace ka daina bani umarni ba? Anƙi a tarwatsa sun."


Kwamanda Diwani ya cije baki. Babbar matsalar data saka ya tsani haɗa ƙarfi da wani kenan a yayin faɗa musamman idan wanin ba ahlin Ururu ba ne. 


Armad yayi amfani da damarsa ya samar da Negrinki. Hannunsa ya koma jajawur lamarinda ya rikida al'amudin ya koma ja. 


Cikin sauri ya motsa zai ɓace amma sai yaji shi har yanzu a riƙe. Yana dubawa sai yaga hannunsa ya shige duniyar Negrinki ba tare da ya kula ba. Al'amudin daya tura cikin duniyar Negrinki ya ja hannunsa ciki sannan kuma har yanzu bai sake shi ba. 


"Kada ka damu," inji Diwani. "Al'amudina dauwamamme ne. Koma ina ka tura shi zai dawo. Kuma tunda ya riƙe hannunka bazai saka ba sai idan nace ya saka."


Armad ya cije baki. Bai taɓa ganin shegen al'amudi kamar wannan ba. Hatta walkiya ta kasa narkashi sannan kuma idan ya riƙe ka to ya riƙe kenan. Gashi ya zuƙe shi cikin duniyar Negrinki amma duk da haka bai sake shi ba. Dole ya janyo al'amudin waje inda suka fito tare da hannunsa. A lokaci guda ya shiga lissafin yadda zaiyi yaci galaba akan al'amudin. 


Yana cikin tunani yaji Ƙaraiƙisu a bayansa. Kafin ya waiwayo basamuden ya daki ƙirjinsa ta baya. Armad yaji wani tari a wuyansa. Yana yin tarin yaga dunkulen jini aciki. 


"Gidan gizo-gizo!"


Zarurrukan izza suka bayyana a saman Armad kamar rumfa. Kowanne ya zama ja, launin Negrinki. Armad ya dunkule hannunsa na dama ya ɗaga shi sama. Hakan yasa rumfar zaren ta sakko ƙasa ta rufe su duk su uku. Cikin sauri ya ƙara dunkule hannunsa na hagu. Gidan gizo-gizon ya zama kamar wata ƙawanya ya kewayesu sannan ya fara motsewa yana ƙoƙarin haɗe su a tsakiya. 


Ƙaraiƙisu bai damu ba. Amma Diwani kawai kallon Armad yake yi yana lissafi da Saɓani. Idan ya bari gidan gizo-gizon ya rufe shi to Armad zai zuƙe shi cikin duniyar Negrinki. Idan kuma ya fita to zai saki Armad daga kamun al'amudinsa kenan. Yayi amfani da idanunsa bakake yaga abinda zai faru. Tabbas idan bai fice ba akwai matsala. Ya hangi wata duniya ja wadda bashi da iko acikinta.


Gidan yana ƙara matsowa Armad yana ƙara famfa Negrinki. Ƙaraiƙisu ya fuskanci abinda ke faruwa amma maimakon ya kawowa Diwani ɗauki sai kawai ya fashe da dariya. 


"Haha... Wato ma'abota izza kuna da rauni matuƙa."


Diwani yaji kamar ya lodawa ƙaraiƙisu al'amudin dake hannunsa. Da kyar ya danne zuciyarsa ya rabu dashi yaci gaba da lissafi. Saura ɗan taƙi gidan gizo-gizon ya haɗe dashi ya saki Armad ya gudu. Jikinsa ya ɓace ya bayyana a wajen gidan gizo-gizon a wani salo mai kama dana fasahar Kaban'shisu.


Dama abinda Armad yake jira kenan. Yana sakarsa ya juya kan Ƙaraiƙisu. Saura su biyu acikin gidan gizo-gizon. Tunda fasaha baza tayi aiki akan Ƙaraiƙisu ba sai Armad ya saki hannunsa na dama. Gidan gizo-gizon ya daina motsewa ya buɗe ya basu fili su buga. Ya ƙara sakin hannunsa na hagu sai kofofin gizo-gizon suka ƙara faɗi yadda zai iya hango abinda ke faruwa a waje. Diwani yana tsaye a bakin gidan gizo-gizon yana kallon Armad amma shigowa ta gagareshi. Tunda babu wanda zai shigo daga waje kaga kenan daga Armad sai Ƙaraiƙisu. Babu wanda zai kawowa basamuden agaji. 


Su Nusi tuni sun ci gaba da tafiya akan tsarin da Armad ya bar musu. Duk wani hari daya zo daga gaba sai kaga Shísu da sarkin Bai sun tare. Idan kuma ta baya ne Barilu da Inyaya suna nan. Ta sama kuma Nazára ne da Asifu da jan doki. Nusi kuma tana ƙasa cikin kariyar Cokali da Giwa. 


Maruta yana ganin duk abinda ke faruwa daga inda yake. Ya dubi Fatima wadda idonta ke kan Armad, ya ce, "ɗan nan naki akwai dabara. Wato waccan yarinyar Nusi ita ya bawa ragamar. Ita yake so ta kwace ki. Yasan dole manyan ma'abota izza zasu yi ƙoƙarin tare su kuma duk cikin tawagar tasa babu wanda zai iya ja dasu sai shi. Saboda haka maimakon ya dage shi ne zai kwace ki daga hannun mu sai ya naɗa Nusi. Kinga ita Nusi tana tsakiya suna kare ta. Sannan kuma suna matsowa a hankali." Yaja numfashi a hankali. "Amma duk da haka mune da nasara."


"Akwai abinda ka manta," inji Fatima. A karo na farko tayi masa magana. "Armad baya buƙatar ya yaƙe ku har ƙasa. Abinda kawai yake buƙata ya tare ku har Nusi ta samu dama tazo nan." Fatima ta juyo ta kalleshi. "Duk da haka kana ganin bamu da nasara?"


"Na gaya miki," inji Maruta. "A tafe muka kwana."


Fatima ta riga ta yanke shawara lokaci yayi da zata daina kuka. Yaƙi ne an riga an fara. Kafin a fara shi ne ake gudunsa amma tunda an fara babban abinda zata yi shi ne ta nemi hanyar da zata taimaka. Tunda ga Maruta a kusa da ita kuma yana so suyi magana to bari tayi amfani da damar ta bugi cikinsa ko zata samu bayani. 


Acikin gidan gizo-gizon, Armad da Ƙaraiƙisu suna tsaye suna fuskantar juna. 


"Lokaci yayi," inji Armad. 


"Lokacin mutuwarka ba," inji Ƙaraiƙisu yana dariya. 


Armad ya girgiza kai ya ɗora hannu akan idanunsa. 


"Saif-Al-Barzak!"


Wata iska mai zafi ta kaɗa. Kafin iskar ta wuce jinin Ƙaraiƙisu ya zuba ƙasa. 


Diwani na ganin haka ya juya da sauri yayi kan su Nusi. Armad ya buɗe gidan ya bishi da gudu amma ina, tuni yayi masa nisa. 


Sai dai duk da gaba su Nazára suke kallo amma suna lura da abinda yake faruwa da Armad. 


"Jan doki," inji Nazára. "Tare Diwani."


"An gama, yarima."


Jan doki ya fito ya tari Diwani. Katoton doki wanda aka sarrafa daga Negrinki ya bayyana a gabansa ya hau. Takobi jajawur ta Negrinki ta bayyana a hannunsa. 


Diwani yaja tunga suka fuskanci juna. 


"Jan doki," inji Diwani. "Matsa zan wuce."


Jin haka kwamanda jan doki yayi dariya ya ce, "to ka wuce mana, ko na rufe maka hanya ne?"


Diwani ya juya al'amudinsa ya kawowa jan doki duka ta sama. Jan doki ya karkace al'amudin ya wuce sannan yayi amfani da damar ya kai masa sara a kafaɗa. Amma sai wani abin al'ajabi ya faru. Al'amudin Diwani ya tsaya cak akan iska dai-dai wajen da jan doki ya kauce. Sannan dakika guda bayan ya tsaya sai kawai yayi bindiga. Wuta ta dunkule ta fashe tayi fancakali da duk abinda ke kusa da ita. Jan doki ya tsinci kansa anyi cilli dashi can gefe. Wato sharrin al'amudin Diwani koda ka kauce baka tsira ba. Kuma abin haushin da yayi bindiga sai kaga ya dawo ya haɗe ya zama sabo yana sheki kamar ba shi ne ya fashe ba. 


Diwani ya rabu da jan doki ya wuce da sauri yayi kansu Nusi. Asifu yana ganin haka yayi sauri ya tare shi.


"Asifu Ruwan Bala'i," inji Diwani. "Kai dama wajen mu ka dawo muka baka muƙamin kyaftin bayan mutuwar Daljari. Amma yanzu gashi kana bin yaro zai kai ka ga halaka."


"Rayuwata, zaɓi na," inji Asifu. "Kuma wane dalili ne zai sa wani ya shiga cikinku idan ba tsautsayi da asara ba?"


Diwani ya haɗe gira. 


"Haka ma kace? To ai shikenan."


Kai tsaye ya kawo masa duka da al'amudin. Asifu ya tafa hannayensa. Baƙin hadari ya bayyana a gabansa sannan da sauri ya fara cika ko'ina. Kafin kace kwabo ko wanda ke kusa dakai baka iya gani. Asifu yayi amfani da wannan damar ya kaucewa al'amudin. Diwani bai sa al'amudin yayi bindiga ba saboda baya ganin Asifu. Amma kawai sai al'amudin da kansa ya kumbura ya samar da ƙofa ta gabansa, Diwani ya shige ciki kamar ɗaki. Yana shiga al'amudin ya dawo ya rufe sannan ya tashi sama akan iska yayi kan su Nusi. Asifu, fuska cike da mamaki, ya bishi da gudu, hadari yana binsa a baya. 


Ganin Diwani yafi Asifu gudu sai Nazára ya taso da sauri ya haɗe tafin hannayensa guri guda. Yashi mai ɗauke da garin ƙarfe ya bayyana a gabansa. Nazára ya ƙara ɗaure yan-yatsunsa guri guda inda yashin ya zama katanga. Al'amudin da Diwani ke ciki ya daki katangar ya koma baya. Tartsatsin wuta yayi sama. 


A dai-dai lokacin Armad ya ƙaraso. Yana zuwa yasa takobinsa ya sari al'amudin. 


"Ɗorawa Abada."


Takobin ta ratsa ciki tana neman yanka al'amudin gida biyu. Koda Diwani ya tabbatar bazai tsira ba sai ya fice ta baya ya bar al'amudin shi kaɗai. Shi kuma Al'amudin yayi kansu Armad ya fashe. Armad yasa Negrinki ya rufe wutar harta gama ci. 


A lokacin Asifu da Jan doki sun dawo. 


"Mu koma formation C," Inji Armad. Nan take Asifu, jan doki, da Nazára suka yi ƙasa. Armad ya tsaya a sama wajen Diwani. Nusi taci gaba da tafiya tana tunkarar Fatima. 


Diwani ya juya baya wajen da ya baro Ƙaraiƙisu dan yaga mai ke faruwa.


"Ya mutu ne?" Ya tambayi Armad.


Armad ya juya ya kalli Ƙaraiƙisu a tsaye kan iska, jini yana ɗisa ƙasa daga jikinsa. 


"Watakila," inji Armad. 


"Ka auri takobi," inji Diwani. "Kafin ma'aboci izza ya auri takobi dole ana buƙatar iko. Iko irin na matakin wa'adin Deba."


Yayi shiru yana kallon Armad cikin tunani. 


"Idan hakane ka haura muƙamin kyaftin kenan," inji Diwani. "Idan kuwa ka haura muƙamin kyaftin kaga kazo muƙamin kwamanda kenan. Ka cancanci kaga Rawar Al'amudi."


Cikin sauri Diwani yayi wasa da yan'yatsunsa a wani salo na sihiri. Idanunsa suka ƙara baƙi. Rigar jikinsa tayi duhu. Wasu sabbin al'amudai guda uku suka bayyana a saman kansa. Al'amudin farko kuma da yake amfani dashi ya canja daga shuɗi ya koma baƙi. 


A fusace ya ɓace daga inda yake ya bayyana a saman Armad. Al'amudinsa ya daki kan Armad. A zahiri kawai dukan Armad yaji amma bai kula da sanda akai dukan ba. Abin haushin har yanzu Diwani yana samansa riƙe da baƙin al'amudin a hannu. Ƙarfin dukan ya danna Armad ƙasa kan gwiwowinsa. Tunda babu ƙasa a wajen sai yayi ƙasa zai danne su Nazára. 


Cikin kwarewa ya samar da tabarmar zaren izza ya faɗa kanta. Diwani ya motsa kafaɗa. Kawai sai Armad yaji saukar wani al'amudin a bayansa. Abin haushi ko kaɗan bai ga lokacin da akai dukan ba. Sai dai ya kula cewa al'amudi uku yake gani, idan ka haɗa dana hannun Diwani huɗu kenan, amma kuma al'amudin sunfi haka yawa a zahiri domin dai wanda suke dukansa basa cikin huɗun da yake gani. Dole akwai wasu ɓoyayyu da baya gani. Sannan kuma Diwani yana iya sarrafa wannan al'amudi ba tare da ya taɓa su ba.


"Babbar fasaha," inji Armad yana jinjinawa abokin faɗansa. A irin matakin da Armad yakai duk wanda zai iya taɓa shi ma ba ƙaramin ma'aboci izza bane. Hakan yasa Armad yake ganin Diwani ya ciri lambar yabo. "Amma a yanzu bani da lokacin tsayawa muyi wasa. Watakila ka samu dama idan mun ƙara haɗuwa."


"Saif-Al-Barzak!"


Budurwar mai kama da takobi ta bayyana a bayan Diwani zata aikata shi.


"Ka lura," inji Diwani. "Na riga na jera al'amudi na a jikin kowane ɗayanku. Idan jini na ya zuba to duk al'amudin sai sunyi nakiya. Da fatan baka manta nakiya ta ba?"


Armad ya ɗagawa Saif-Al-Barzak hannu ta tsaya. 


"Mai zai hana ka tashi nakiyar koda na rabu dakai?" Armad ya tambaye shi. 


Diwani ya fashe da dariya. 


"Baka fahimta ba, Armad. Ina so ne na gaya maka ko ka sare ni, ko kada ka sare ni ƙarshen ka dana mutanenka yazo. Kunzo in-taha. Daga nan bazan barku ku ƙara matsawa ba."


Armad ya juya wajen su Nusi. Dukkansu suna jin abinda kwamandan yake faɗa. Kuma kawo yanzu sun tsaya tsam suna lissafin abinda ya kamata suyi. Watakila mai karatu zai iya cewa sai a yanzu Diwani ya cimma burinsa na tsayar dasu. 


Acan baya kuma Ƙaraiƙisu yana tsaye akan iska. Har yanzu jini yana zuba daga kafaɗarsa amma ciwon ya kusa warkewa, saura baifi kamu ɗaya ba. Ko mai yasa har yanzu sarkin yake tsaye bai motsa ba? 


Can dai ya buɗe baki ya lashi leɓensa. A hankali ya juya wajen da Saif-Al-Barzak take tsaye ya kalleta. 


"Na daɗe banji daɗi irin na yau ba," inji Ƙaraiƙisu. "Na daɗe ban samu jarumi kamar ki ba. Naji sara ya ratsa ni har ciki irin naki ban taɓa ba. Amma yau kika bani wannan daɗin. Tabbas na aminta dake."


Ƙaraiƙisu ya fashe da dariyar farin ciki yayi kan Saif-Al-Barzak. 


Takobin ta kalleshi fuska a yamutse. Ta kasa gane mai yake faɗa. Yawanci bil'adama ƙinta suke yi. Musamman idan suka dandani kaifinta. Amma yau ga jarumi ta samu. Tabbas Ƙaraiƙisu ya bata mamaki. Ko kaɗan baza taƙi ba idan Armad ya bata dama ta auri wannan jarumi. Matsalar kawai aure guda zata iya yi a duniya.


"Ƴar budurwa, yaya sunan ki?" ƙaraiƙisu ya tambayi takobin. 


Saif-Al-Barzak ta zaro ido cikin mamaki. Wannan ne karo na farko da wani mahaluki ya tambaye ta sunanta. 


"Sunana Saif-Al-Barzak. Sunana Saif-Al-Barzak."


Kafin Armad ya bata umarni ta bar kan Diwani ta taho kan Ƙaraiƙisu tana buɗe hannu kamar zata rungume shi. 


"Saif?" Armad ya kwala mata kira amma ina, ko kaɗan bata ji shi ba. "Saif?"


A banza. Takobin taje ta haɗu da Ƙaraiƙisu cikin nishadi. 


Ta sareshi a hannu har sai da ta taɓo ƙashi. Shi kuma ya nausheta a ciki har sai da cikin ya loma ya koma baya. 


"Ina sonka saboda ALLAH," inji Saif-Al-Barzak. 


"Nima ina sonki," inji Ƙaraiƙisu. 


Armad da Diwani suka tsaya suna kallon ikon ALLAH. Jinin ƙaraiƙisu yana zuba amma ƙara nishadi yake yi. Ita ma takobin har bashi jiki take yi ya daka. A wasu lokutan sai kaga tayi aman jini idan ya dake ta amma ko a jikinta. Haka suka ci gaba da sharafinsu. 


Kkkkk


A yayinda hankalin Diwani yayi kan Ƙaraiƙisu da Saif-Al-Barzak, Armad neman ɓoyayyun al'amudan ya shiga yi da yanayin izzarsa. Har yanzu baiji komai ba. Sai dai hakan ba abin mamaki bane tunda al'amudin ba lallai akwai izza a jikinsa ba. Amma kuma akwai yiwuwar ƙarya Diwani yayi, akwai yiwuwar babu wani al'amudi daya ɓoye. Watakila ya faɗa ne kurum saboda ya janye hankalinsu su tsaya. Sai dai Armad bai yadda ya bar rayuwar mutanensa akan hasashe ba. Domin dai nakiyar Diwani ba kamar kowacce nakiya bace. Ya jita a jikinsa kuma ya tabbatar zata iya halaka wasu daga mutanensa, ko kuma tayi musu mugun rauni. 


Yana cikin tunani Diwani ya murza al'amudin dake hannunsa. Dai-dai gaban Nusi ya fara yin ja kafin nakiya ta fashe a dai-dai fuskar Nusi. 


Diwani ya fuskanci Nusi tana da muhimmanci a shirin Armad saboda haka yake ƙoƙarin halaka ta. Armad zai iya zuwa ya shiga gaban nakiyar ya ture Nusi to amma sauran ragowar mutanensa kuma fa? Idan shi yana da jikin izza da zai iya shanye nakiyar to su kuma fa?


Babu lokacin tunani da yawa saboda haka Armad yayi abinda yake ganin shi ne dai-dai. Ya kira Kaban'shisu ya shiga gaban nakiyar sannan yasa Armad 3 da Armad 4 suka samar da bukkokin Negrinki guda biyu suka rufe kowa aciki. 


Diwani ya kira ɗalasimi a ɓoye lamarinda yasa ragowar ɓoyayyun al'amudan suka fashe. Wata wuta tayi sama sannan ta faɗo ƙasa ta fara cin mutane. Babu ruwanta da Ururu ko Maikiro. Duk wanda ya tsaya akan hanyarta sai ta ƙone. 


"Kwamanda," kyaftin Tangile ya kwalawa kwamandan kira. "Kana ƙone mutanenka anan." Ya nuna wasu sadaukai durkushe akan gwiwowinsu sunyi baƙi kamar gawayi.


Wato a hankali Armad yake fuskantar ƙarfin kwamanda. Yana sane Diwani bai gama ware ƙarfinsa ba, amma duk da haka ya ɗauki hankalin kowa a filin. Dole Armad ya gama dashi kafin wani kwamandan ya shigo cikin faɗan. 


"Aiban'shisu."


Yana rufe baki ƙasar da take ƙasan ƙafarsa ta ɓace ta bayyana a saman Diwani. Kafin kwamandan ya ankara Armad ya hura masa Negrinki a fuska. A ƙoƙarin ya kaucewa Negrinkin bai lura da takobin Armad ta bayansa ba. 


"Ɗorawa Abada."


Sauran kiris takobin ta yanka cikinsa ya juya a sama kamar babu ƙashi a jikinsa ya goce


Armad yana tafiya da saurin Kaban'Zhisu amma kuma kwamandan ya gocewa harinsa har guda biyu. Lallai kwamanda ba wasa ba. Sai dai kuma Armad abinda yake nema kenan: kwamandan ya ɗan juya baya. Ai kuwa kafin ya juyo hannun Armad yayi baƙi. Baƙar walkiya irin wadda ta hallaka Uznu Ururu ta sauka akan Diwani. 


"Hannun Aradu!"


Asalin ƙarfin izzar Armad ya shiga cikin walkiyar ya daki Diwani. Iska mai zafi haɗe da walkiya dunkule guri guda sukai jifa da kwamandan can ƙarshen filin. Yana zuwa ya daki wani gini ya rusa katangar ya shige ciki. 


"Kwamanda!"


Kyaftin Tangile da sauran mayaƙan Ururu dake wajen suna kallon faɗan suka kwalla ihu. 


Armad ko a jikinsa. Tabbas da yaga dama a wannan lokaci zai iya zuƙe kwamandan cikin duniyar Negrinki sai dai yin hakan bashi da amfani a yanzu. Na farko dai zai nunawa Diwani inda Haruta yake. Tabbas kwamandan zaiyi ƙoƙarin kubutar dashi. Watakila yayi nasara. Na biyu kuma koda ya jefa shi ciki tabbas zai iya fitowa tunda Deniz Iluru ma ya fito. A kullum irin wannan lokuta suna ƙara nunawa Armad buƙatar ya gyara Negrinkinsa. Dole yana buƙatar yayi mata aiki ta yadda duk abinda yasa aciki ya zauna kenan. 


Armad ya sallami Armad 3 da 4 suka koma filin yaƙin domin su ci gaba da aikinsu.


"Akwai wanda yaji ciwo acikin ku?" Armad ya tambaye su.


Suka girgiza kai. Fuskar Giwa da sauran mutanen ikwatora ta cika da mamaki. Mai yasa Armad ya damu dasu haka? Shin haka kowane sarki a wajen ikwatora yake son mutanensa, ko kuwa dai Armad ne kaɗai haka?


"Muje," inji Armad. "Har yanzu dai muna kan Formation C."


Nan take kowa ya kama guri suka tunkari Fatima. 


Acan gefe kuma Diwani ya fito daga cikin ginin da Armad ya cillashi. Yana zaune a ƙasa ya ajiye al'amudinsa a gefe yana goge ƙurar dake jikinsa.


"Hmmmm..." 


Ya ja numfashi.


"Armad Wilbafos, yanzu mai kake so nayi dakai?" 


Kwamandan yayi shiru yana tunani. Bayan ɗan lokaci ya miƙe tsaye ya ɗauki al'amudinsa yayi kan Maikiro'Abbas. 


Zaikid da Shata suna tsaye har yanzu basu shiga faɗan ba. Ganin Diwani yana matsowa suka kalli juna. Ba tare da cewa komai ba suka tashi sama kan iska sukai kudu. Sukai ta tafiya a saman filin yaƙin babu ruwansu dana ƙasa. Duk kibiya ko mashin da aka harbo musu sai kaga ya kauce musu da kansa. A haka har sai da suka kai ƙarshen filin. Daga nan suka juyo sukai gabas suka tunkari inda Fatima take.


Koda abokan gaba suka ga haka sai suka yi azama wajen harbinsu da kibbau da masu. Sai dai a banza. Farfesa da Shata ko ƙoƙarin tarewa basa yi. Ta saman Diwani suka wuce. Kwamandan ya ɗaga kai ya kallesu amma baiyi ƙoƙarin tare su ba, maimakon hakan sai ya rabu dasu yaci gaba da tunkarar Maikiro'Abbas. Su kuwa suka ci gaba da tunkarar Fatima. Sai da suka kusa zuwa, ratar dake tsakaninsu da ita bata fi taku ɗari uku ba, sai kurum suka daki wani ɓoyayyen bango. 


Suka kalli juna suka gyaɗa kai, sannan ba tare da cewa komai ba suka ja da baya suka dawo a guje suka ƙara dukan bangon da kafaɗa. Wata ƙara tayi sama kamar sun daki bangon ƙarfe. Amma a banza. Suka ƙara ja da baya suka daki bangon. Wata ƙara sama da ta baya ta tashi sama. Zaikid yasa hannu ya shafa wajen da katangar take. Yana taɓa ta ya girgiza kai. Har yanzu tana nan. 


"Farfesa," inji Shata. "Ga dukkan alamu sun saka kafi wanda yake hana tashi sama anan."


Zaikid ya gyaɗa masa kai. "To ai sai mu ƙarasa da ƙafa ko?"


Daga nan suka sakko ƙasa tsakiyar mayaƙan Ururu. Da farko mayaƙan sun fara jada baya amma daga bisani wani ƙatoton mutun ya bayyana.


"Zaikid Wilbafos da Shata Kil'zanki," inji mutumin yana dariyar mugunta. "Ku bani dama na gabatar da kaina. Ni ne kyaftin Ubandi na rundunar kwamanda Binani. Nazo domin na halaka kaku."


Ya juya wajen dubban mayaƙan Ururu dake gurin. 


"Ku halaka su."


Mayaƙan sukai kukan kura suka afka kan su Zaikid.


Shata ya ciro garaya ya ɗan karkata kai sannan ya fara kaɗawa. Kafin mayaƙan su ƙaraso sai kwatsam suka tsaya cak. 


Shata yaci gaba da kida. A wasu lokutan sai kaji sautin yayi sama, a wasu kuma kaji yayi ƙasa. 


Idan sautin yayi sama sai kaga abokan gaba sun fara jada baya a hankali a hankali. Idan kuma yayi ƙasa sai kaga sun ɗan tsaya. Idan ya ƙara yin sama sai kaga sun yadda takubbansu. 


"Uban mai kuke yi haka?" Kyaftin Ubandi ya daka musu tsawa. "Kuna so na kashe kune?"


"Kyaftin, sunyi mana girma. Sunfi ƙarfin mu, kyaftin."


"Mahaukatan banza," inji Ubandi. "Su biyu ne fa?"


A fusace ya janyo kwalar wani sadauki dake kusa dashi. 


"Zaka koma ko sai na kashe ka?"


Sadaukin ya fashe da kuka yana girgiza kai cikin tsoro. Ubandi yasa takobi ya sare shi sannan ya jefar dashi ƙasa. 


Koda ragowar suka tabbatar babu yadda zasu yi sai suka juya suka fuskanci su Zaikid. Amma kana gani kasan babu kwari a jikinsu. Hatta riƙon takubbansu babu ƙarfi aciki. 


Zaikid ya dubi Shata cikin mamaki. 


"Wai yaushe zaka koyamin wannan kiɗa?"


Shata yayi murmushi. 


"A haba, farfesa, ai baka buƙatar ka ɓata lokaci akan wannan fasaha tamu. Sunan kiɗan Kiɗan Tsoro. Bari kaga na basu Kiɗan Bacci."


Shata ya canja salon waƙar. Yanayin garayar ya canja. Salon sautin ya canja. Duk wanda yaji sautin sai kaga ya zube a ƙasa yana minshari. Kafin su ƙaraso sama da rabin sun faɗi. 


Ganin abinda ya faru da mutanensa, kyaftin Ubandi yasa dutse ya toshe kunnensa. A fusace yayi tsalle ya kawowa Shata sara da takobinsa. Kafin ya ƙaraso Zaikid ya tare shi. 


Ƴar ƙaramar wuƙa Zaikid yasa ya tare ƙatotuwar takobin dake hannun Ubandi. 


Ubandi ya danno takobin amma taki motsi kamar ya daki dutse. Dole ya ɗago kai ya kalli Zaikid ido cike da mamaki. Kafin yayi wani abu Zaikid ya ture takobinsa gefe da wuƙar. Takobin tayi tsalle can gefe guda. A ƙoƙarin Ubandi na ya riƙe ta shima ya bita kamar anyi cilli dashi. Da sauri ya tashi zaune yana sosa ido. 


Shi kuwa Zaikid wajen Shata ya juyo. 


"Shatan waƙa," inji Zaikid. "Wato idan gaskiya zan faɗa to lalle na fara jin bacci. Wannan kiɗa naka yana da armashi. Tabbas yana tunamin da labarim sarki Aldaima. Yazo a littafan mu cewa ya taɓa samun matsalar bacci saboda rashin haihuwa. Akwai sanda ya shekara biyu bai runtsa ba. Ance bai samu waraka ba har sai da wani mawaki daga ƙabilar Kil'zanki yazo yayi masa waka. Tabbas bazan yi mamaki ba idan aka ce wancan mawakin jinin kane."


Kil'zanki ya tsaya da kiɗan yana murmushi. 


"Farfesa, kana fasa min kai, har ni na isa nayi jayayya da mutanen Farkon Lokaci."


Su biyun sukai dariya. 


A lokacin kyaftin Ubandi ya taso kansu a fusace. Takubba biyu a hannu yana ihu da karaji. Mutanen dake gefe suna ihu, suna zigashi.


Zaikid ya ja numfashi. A ransa yana cewa yara sun fiya garaje da saurin zuwa halaka. Har wani kyaftin ne zaiyi jayayya da farfesa?


Kafin Ubandi ya ƙaraso, Zaikid ya bayyana a bayansa. Kyaftin ɗin ya waiwayo yana mamakin sanda Zaikid ya wuce bai gani ba. A lokacin ya lura da jini a cikinsa. Tuni Zaikid ya cake shi bai sani ba. 


"Mayaƙan Ururu," inji Zaikid cikin babbar murya. "Idan akwai mai son mutuwa ya matso kusa."


Fatima ta dubi idanun mahaifinta. Babban jarumi ne. Bata taɓa tunanin zata sashi cikin halin yaƙi ba a rayuwarta amma yau gashi ƙaddara ta riga fata. Kwalla ta ƙara cikowa a idanunta. 


"Kinsan hawayenki zai iya ƙarewa kafin yaƙin nan ya kammala ko?" Inji Maruta. 


Acan gefe kuma Dul'Ururu ne ya dubi Iluru da Ayubu. Ba tare da cewa komai ba sadaukan biyu suka tashi sama sukai kan su Zaikid.


Ta ɓarin dama Armad da ayarinsa wanda har kawo wannan lokaci suke fama da Diwani. Ta ɓarin hagu kuma Zaikid da Shata sun dira. A yayinda Najunanu da Rabi da sauran rundunar Maikiro'Abbas suka taho ta tsakiya. Duk inda suka ratsa sai dai kaga rundunar Ururu sun dare. 


Jerin kyaftin biyar suka shiga gaban Najunanu da niyyar su tare shi. Sai dai kafin su ƙaraso wasu mutun goma sha biyu dake bayan Najunanu sun shiga gaban sun tare su.


"Mu ne majalisar garin Khan," inji mayaƙan. Da Nusi tana kusa da zata gane wasu daga cikinsu. "Kuma lallai yau zaku fuskanci kaifin takobin mu."


Suka zare takubbansu sukai kan jerin kyaftin ɗin. Lamarinda ya bawa Najunanu da tawagarsa damar wucewa. 


Ga dukkan alamu shiri ya fara cika. Maikiro'Abbas ya shirya tsaf domin karɓar Fatima. 


A ɓangaren Ururu akwai ragowar Ibraham Nil, Suwainah, da Han'ibal a ɓarin hagu. A ɓarin dama kuma akwai Dul'Ururu, Binani, da kuma Yurba. Sai Maruta a tare da Fatima. Kowa za'a turowa su Armad?


"Kowa ya zama cikin shiri," inji Armad. "Har yanzu bamu san fasahar Ibraham Nil da Suwainah ba. Akwai yiwuwar ɗaya daga cikinsu za'a turo."


Ai kuwa kafin ya rufe baki wani gungumen dutsen wuta ya sauka a gabansu. Irin dutsen wutan nan ne amma kuma ya fara narkewa yana tartsatsin wuta saboda wutar dake ci a kewayensa. 


Wuta tayi sama ta tare musu hanya. Dole suka tsaya cak a inda suke.


Sarkin Bai yayi tsalle sama ya zare takobi yayi kan wutar. Kafin ya ƙarasa sai bangon wuta ya bayyana a gabansa. Ya saka takobi ya yanka bangon biyu ya shige ciki. Yana wucewa bangon ya dawo ya haɗe. A bayan bangon yayi arba da wani dogon mutun mara kauri sosai. 


"Suna na Han'ibal," inji mutumin. Sarkin Bai ya lura mutumin shi ne yake tsaye a kusa da gadon da aka ajiye Fatima. Idan zai iya tunawa dai-dai sunansa Han'ibal. Kuma shi ne sarkin jinzidal a doron ƙasa ta uku.


"Suna na Rayaya amma suna cemin sarkin Bai."


Su biyun suka kalli juna kafin sarkin Bai ya kawo masa sara. Han'ibal ya saka hannu ya riƙe takobin kamar wasa. Yana taɓa ta sai hannunsa ya koma dutsen wuta. Nan take ta fara narkewa. Ya miƙa ɗayan hannunsa ya cafi wuyan sarkin Bai ya ɗaga shi sama ya cillashi cikin bangon wutar dake gabansa. 


Sarkin Bai yaje ya daki katangar ya shige ciki ya faɗi a gaban Armad. 


Shísu ya taho da gudu kansa. Yana taɓa shi ya janye hannu amma tuni ya ƙone saboda zafi. Nusi da sauran mutanen ikwatora suka kewaye Sarkin Bai wanda ke kwance rai a hannun ALLAH. 


A lokacin Han'ibal ya sauke bangon wutar suka fuskanci juna dashi da Armad. 


"Bazan bari ku wuce ba," inji Han'ibal. 


Su Armad idanunsu na kan sarkin Bai. Ya kamata a fitar dashi wajen filin ayi masa magani to amma waye zaiyi hakan? Fitar sarkin Bai ta lalata musu shiri. Idan Armad ya tura wani ya kai sarkin Bai waje hakan zai ƙara rage musu yawa da ƙarfi. Sannan kuma babu lalle su samu damar fita daga cikin filin saboda mayaƙan Ururu. Sai dai kuma duk da haka Armad bashi da niyyar barin sarkin Bai a waje ya mutu. 


"Armad 3," inji Armad. Yana rufe baki mutum-mutuminsa ya bayyana. 


"Akwai likita a rundunar bayan mu. Ina so ka ɗauki sarkin Bai ka kaishi can."


"An gama, shugaba," inji Armad 3. Ya duƙa ya taɓa sarkin Bai wanda yake kwance yana numfarfashi suka ɓace. 


Nusi ta ɗago a fusace tayi kan Han'ibal. Kafin ta isa Nazára ya mara mata baya. Asifu da jan doki da dukkan mutanen ikwatora suka shigo ciki. Kafin kace kwabo dukkan tawagar sun rufu akan Han'ibal. Nusi ta saka rassan bishiya ta riƙe Han'ibal a guri guda. Jan doki ya saka jar takobinsa ya sari cikinsa. Asifu ya samar da hadari a hannunsa ya jefe shi dashi. Koda hadarin ya haɗu da Han'ibal sai ya narke ya zama ruwan guba inda ya wanke Han'ibal tun daga sama har ƙasa. 


Nazára ya samar da duwatsun ƙarfe ya fara jifan Han'ibal dasu. Duk sanda dutsen ya daki Han'ibal sai kaga ƙasa tayi sama, ƙura ta rufe ko'ina. Kafin su ƙarasa duwatsun sun rufe Han'ibal a ƙasa. 


Shísu da Inyaya da Barilu suka hau haƙar rami. Cikin ƴan dakiku sun samar da wawakeken rami. Giwa ta ciccubi Han'ibal ta jefa cikin ramin sannan suka dawo da ƙasar suka rufe. 


Duk abin bai wuce dakika talatin ba. Kafin wani ya kawowa Han'ibal ɗauki sun rufe shi a ƙasa. 


"Da sauri haka," inji Armad cikin jinjina. "Ko ku ɗan bani dama na saka hannu."


Nusi da Nazára sukai dariya. A lokacin suka ƙara shiga layi suka ci gaba da tafiya. Nusi tana tsakiya suna kare ta. 


A ɗaya ɓangaren kuma Zaikid da Shata sunyi ido da ido da Ayubu da Iluru. 


"Kai ne butulin da ake faɗa ko?" Inji Zaikid yana kallon Ayubu cikin tsana. 


Ayubu yayi murmushi, ya ce, "na tabbatar kana so ka kashe ni saboda na guji Armad." 


"Zan tabbatar baka bar filin nan a raye ba," inji Zaikid. Bakin dattijon har kumfa yake yi. Kana gani kasan ya gama rantsewa sai yaga bayan Ayubu. 


"To, ɗan tsoho, ka gwada mu gani idan zaka iya."


"Wilbafosiyan Siwod Dans!" Inji Zaikid. Takobinsa ta cika da taurari. A kallon farko zaka yi tunanin taurarin basu fi bakwai ba, amma kana matsawa kusa sai kaga sun haura hakan, idan kuma ka fara lissafi sai kaga ka kasa kayyade adadinsu. Lallai yau Zaikid ya shirya tsaf domin ɗaukar fansa. 


A ɗaya ɓangaren Ayubu takobi ya zare ya girgiza ta a sama sannan ya kira ɗalasimi. 


"Wilbafosiyan Siwod Dans!"


Zaikid ya tsaya cak tare da haɗe gira. Fasaharsa ma ya kira? Dole ya ɗauki mataki. Amma abin tambayar shi ne: zuwa wane mataki Ayubu ya kware akan fasahar. Idan kamar Armad ne to akwai yiwuwar ya ɓace ɓat daga zarar yayi amfani da ita. Kuma idan Zaikid ya bari ta ritsa dashi to har dashi za'a tafi. Bai manta da labarin da Armad ya bashi akan ɓatan Ikenga ba. Watakila Ayubu yasan haka shi yasa ya ɗakko fasahar. To amma mai ya kamata yayi? Tabbas bazai kyale Ayubu ba, kuma wannan fasaha ita ce mafi ƙarfin fasaharsa. 


Kai tsaye Zaikid ya afka kan Ayubu. Yana da yaƙinin Ayubu bazai bari ya ɓace daga filin yaƙin ba domin dai tunda har yazo to akwai abinda yake nema. Tunda Ayubu ya kira fasahar Wilbafosiyan Siwod Dans to lalle yasan akwai yadda zaiyi ya riƙe ta ya hanata jifa dashi. To amma hakan kuma zai nuna cewa Ayubu yafi Armad kwarewa akan fasahar kenan. Anya kuwa? 


Zaikid ya ture duk wannan tunane-tunane daga ransa ya afka kan Ayubu. Ɗauka ɗaya yake so yayi masa tayadda baza a ƙara zancen Ayubu ba.


Shima Ayubu ya jada baya suka taho suka haɗu. Kafin su haɗu takobin Ayubu ta rinƙa canja launi. Daga fari zuwa baƙi, daga baƙi zuwa rawaya. Taurarin suka ɗauke. Wani ɗan duhu mai kama da inuwa ya bayyana a saman Ayubu. Tsoro wanda ba'a san daga inda ya taho ba ya cika zukatan mutane. Kafin su haɗu sai da kowa ya dare ya basu guri. 


Zaikid ya sari gefen takobin Ayubu. Ayubu kuma ya tari Zaikid kai tsaye da kaifin takobinsa. Suna haɗuwa wuta tayi sama. Tartsatsin haske ya cika ko'ina kafin ya dunkule yayi sama. Dukkan filin yaƙin aka waiwayo ana kallonsu. 


Zaikid yaja da baya cikin kokwanto. Mai yake faruwa? Tayaya Ayubu ya iya tare saran takobin Wilbafosiyan Siwod Dans?


A hankali ƙurar da ta haɗe ta lafa, Ayubu ya fito fili. Tabbas fasahar Wilbafosiyan Siwod Dans sak Ayubu yayi amfani da ita. Shin hakan yana nuna Ayubu yafi Armad kwarewa a wajen amfani da fasahar ne ko kuwa?


"Na samu ci gaba," inji Ayubu. "Tun bayan rabuwa ta da Armad na fuskanci yadda al'amuran izza suke. A lokacin na fuskanci cewa Armad kawai dakile ni yake yi. Duk wata fasaha da nake so zan iya koya. Har ma da fasahohin da Armad ya kasa koya. Shin, ɗan tsoho, baka ganin cewa dama can ni ya kamata na zama Armad, shi kuma Armad ya zama Ayubu? Ka faɗa min gaskiya watakila na barka ka rayu."


Zaikid ya cije haƙora. Yana da wuya ya iya yadda Ayubu ya koyi fasahar Wilbafosiyan Siwod Dans ba tare da an koya masa ba. Hatta Armad da Zaikid ya koya masa da kansa bai iya ba sosai amma ace Ayubu ya koya. To amma kuma ga zahiri ya bayyana. Mai ya kamata Zaikid yayi?


"Kana tunanin dan ka iya Wilbafosiyan Siwod Dans shikenan ka tsira? Hmm.. da sannu zaka gane kuskurenka."


Zaikid ya ƙara afkawa Ayubu. A wannan lokaci wasu sabbin fasahan takobin ya buɗe. Wato ka bar mutumin da yake koyarda fasahar takobi a jami'ar Babila. Duk wani salo da tsari ya sani.


Suna fara fafatawa da Ayubu ya nuna masa bambancin kwarewa. Wato Ayubu ya iya Wilbafosiyan Siwod Dans kuma yana iya tare takobin Zaikid. Amma matsalar ita ce yanayin wasan takobin ya bambanta. Yadda Zaikid yake juya takobinsa akan iska yana rawa yana juyi yana saran takobin Ayubu dai-dai gwargwado kasan ya kware. Idan Ayubu ya tare takobin sai kurum kaga Zaikid ya zame ta ƙasa ya tunkari hannunsa zai sara. Tun Ayubu yana amfani da Kaban'shisu yana guduwa har hakan ta fara gagara. Ya zamanto indai zasu haɗa takobi da Zaikid sai Zaikid ya zame ya sare shi a hannu ko jiki. Ba jimawa ya fuskanci tabbas an fishi kwarewa a fasahar wasan takobin koda kuwa yayi ƙoƙari ya iya Wilbafosiyan Siwod Dans. 


Wani abin haushi shi ne yadda duk inda Zaikid ya sara yake zubar da jini. Kada dai a manta Ayubu ba jikin izza bane dashi kamar Armad. Saboda haka jikinsa bai kai kwarin na Armad ba. 


Dole ya juye izuwa walkiya ya jada baya yana kallon Zaikid. Zaikid murmushi kawai yayi masa, irin murmushin nan na zaki kafin ya tafi wuyan abinda ya kama. 


A gefe guda kuma Iluru da Shata sun fuskanci juna. Tun a baya mun kula cewa Shata ba gwanin faɗa gaba-da-gaba bane. Yafi kwarewa a wajen kiɗa da kuma hari daga nesa. Zaka iya cewa Iluru shi ne mafi munin abokin faɗa da Shata zai samu. Domin kuwa Iluru gwarzo ne a gurin faɗa gaba-da-gaba musamman idan ya saki jikinsa na samudawa. Hatta Armad sai da taimakon Saif-Al-Barzak ya halaka shi.


Shata ya jada baya yana lissafi.


Iluru yayi tunanin hakan tsoro ne saboda haka ya fashe da dariya.


"Haha... har zaka gudu?" Ya ƙara fashewa da dariya. "Bari na nuna maka ƙarfin dantse."


Shata ya zare ƴar sandar da yake kiɗa da ita ya nuna Iluru. 


"Taho mu gani."


Iluru ya ɓace daga inda yake ya bayyana a saman Shata ya kawo masa duka da hannu. Shata yayi ƙoƙarin tarewa amma kafin ya ankara hannun Iluru ya tarwatsa sandar kiɗan ya wuce ya daki fuskarsa. Kamar anyi jifa da Shata yayi sama ya faɗo ƙasa tim. Yana taɓa ƙasa ƙusoshin mairakana suka dira a kansa suka cake hannayensa da ƙafafunsa a cikin ƙasa. Shata yayi ƙara mai ɗaukan hankali. 


"Shata!" Fatima ta kira sunansa lamarinda yaja hankalin kowa a filin. 


Abinda kawai kowa yake faɗa a ransa shi ne sarkin jinzidal ba wasa ba. 


Iluru ya taho a hankali kan Shata. Zaikid ya kalli Ayubu ya kalli Shata. Taimakon Shata zaiyi ya rabu da Ayubu ya farfaɗo, ko kuma ya ƙarasa Ayubu? Dole ya bar Ayubu yayi kan Shata. Yana zuwa ya tari Iluru. Kaifin takobin Wilbafosiyan Siwod Dans ta sauka akan kafaɗar basamuden ta sare hannun. Guntulen hannun yayi sama kan iska.


Iluru yayi ƙara ji sama. Mayaƙan dake kusa suka jada baya saboda tsoro. Sarkin ya ƙara ɗaga kai yayi kuka. Gajimare ya fara juyawa. Daga nan sai dukkan jikin Iluru ya ɗau haske. A hankali ya fara girma yana kumbura yana buɗewa. Kafin kace kwabo Iluru ya ninka girmansa sau uku. Nan take hannun da Zaikid ya yanke ya fito. 


Ganin haka Zaikid yayi maza ya koma kan Shata yasa takobi ya yanke ƙusoshin da aka manneshi dasu. Sai dai kuma ƙusoshin suna fita jini ya fara malala daga inda suka fita. A lokacin Zaikid ya lura an fitar da Shata daga yaƙin. Dole yana bukatar likita. Amma kuma tuni Ayubu da basamuden sarki Iluru sun zagaye shi. Bashi da wata hanyar guduwa balle ya kai Shata wajen likita. Zai ajiye Shata ya tare su shi kaɗai to amma kuma hakan zai iya yin sanadiyyar mutuwar Shata. 


Yana cikin wannan tunani ne Armad 3 ya bayyana a gabansa. Yana zuwa ya ɗauki Shata ya ɓace.


Zaikid ya ɗaga ido ya hango tawagar Armad. Daga inda yake baya gano Armad sosai amma yana jin yanayin izzarsa. Ya jinjina masa sannan ya juyo kan su Iluru da Ayubu.


"Saura kai kaɗai," Iluru ya gayawa Zaikid. "Zaka iya ji damu kai kaɗai."


Zaikid yayi murmushi. "Har nayi muku yawa."


Har yanzu Ayubu yana kallon inda Armad 3 ya ɓace. Shi kaɗai yasan mai yake tunani. 


Zaikid ya kira ɗalasimi, "Kaban'shisu!"


Take ya ɓace ya bayyana a bayan su. Kafin su juyo ya ƙara kiran wani ɗalasimin ya wuce gaba ya bar su anan. Baizo filin yaƙin domin yayi faɗa dasu ba, yazo ne domin ya kwaci Fatima. Wannan ita ce babbar damar da suke da ita a yaƙin. Idan basu yi amfani da ita ba sunyi asara. 


Iluru da Ayubu suka kalli juna sannan suka juya da gudu suka bi bayansa. Sai dai anan Iluru yaga rashin amfanin girmansa. Duk inda yayi sai kaga ya take mayaƙan Ururu. Dole ya tashi sama a yayinda Ayubu ya tsaya a ƙasa yana bin Zaikid. 


Kafin su cimmasa ya kai inda Fatima take. Yaje ya daki kafin da aka tsare ta dashi. Suna haɗuwa wata iska ta ɗebe shi tayi jifa dashi baya. Bai faɗo ko'ina ba sai gaban gadon da aka ajiye Fatima. Gefensa na dama su Dul'Ururu ne, gefen hagu kuma su Ibraham Nil ne. 


Ana cikin haka sai Ayubu da Iluru suka ƙaraso. Saboda haka suka saka Zaikid a tsakiya. 


A gefe kuma Armad da tawagarsa sunci galaba akan Han'ibal kuma tuni suka ci gaba da tafiya akan Formation C. Sai dai basu yi nisa ba Han'ibal ya fasa ƙasa ya fito. Abu na farko da yayi bayan ya fito shi ne samar da ƙawanyar wuta guda ɗaya ƙatuwa a hannunsa. Sannan ya fara jifansu da ita ta baya yana kuma binsu da gudu. 


Ƙawanya ta farko Nazára ya tare da bangon ƙasa. Ƙawanya ta biyu ta biyu Armad ya tare da gidan gizo-gizo. Ƙawanya ta uku Nusi ta tare da bishiya. 

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...