Skip to main content

BABI NA 270: An fara

 A littafi na uku mun tsaya a inda Áyúbu yaje garin Kanyú ya haƙa ɗaruruwan ramika ya binne Zaren IZZA. Sannan ya samarda wani zaren wanda yai amfani dashi ya haɗe duk zarurrukan dake cikin ramikan a waje guda. Ya saƙalo wannan zaren ya jashi zuwa doron ƙasa na huɗu daular Sisiyu, garin Bihanzin, yai rami ya binne.


Bayan nan ya sakko doron ƙasa ta uku ya ringa bi gari-gari yana haƙa irin wannan rami yana binne zarurrukan. Kan kace meye wannan ya binne sama da dubu a dukkan faɗin garuruwa ɗari da bakwai dake doron ƙasashe shida. 


Sannan ya saƙala wani zaren a cikin Bangon arewa, ya janyo shi har zuwa garin Jiha, garin su Ikenga, ya ɗaure. Ya ƙara saƙala wani zaren guda ɗaya dogo yayi wa doron ƙasashen ɗankwali. Tayadda a kowanne saƙo da loko akwai zaren sa. 


Bayan wani lokaci Ayubu ya koma can ƙasan doron ƙasa ta bakwai yai rami ya binne kansa. 


A dai-dai wannan lokaci saura daƙiƙa goma kurkukun lokaci ta ƙare, a buɗe filin daga. A baje kolin fasahohi.


Anan muka tsaya, a yanzu zamu ɗora. 


Kwanaki sittin da aka alƙawarta sunzo ƙarshe. A ƙarshen kowacce rana, da asuba, Armad, Ikenga da Bihanzin da dukkan mutanen su suna maimaita wannan rana cikin Kurkukun-lokaci. Akwai daƙiƙa uku dake tsakanin kowacce rana data gabanta. Acikin wannan daƙiƙu uku hatta Armad bashi da masaniya akan abinda ke faruwa. Amma daƙiƙun na wucewa tunanin kowa zai dawo dai-dai. 


A kullum Armad yana ganinsa ɗaure acikin kurkuku tare da Shal. Amma a wannan rana an karya Kurkukun-lokaci. Babu sauran maimaita lokaci. Kuma kamar yadda umarni ya sauka daga Tarifil-fakta da kansa, lokacin fidda gwani yazo. Mutun ɗaya tsakanin Armad da Ikenga da Bihanzin zai rayu, ragowar biyun sun tafi. Babu sauran sulhu. Babu sauran zance. Babu sauran kace-nace. Abinda kawai ya rage shi ne jini da hankakan mutuwa. 


Ranar alhamis sha huɗu ga watan satumba. Da asubahin fari na wannan rana, wani baƙin hadari ya taso daga gabas ya rufe rana da dukkan abinda ke motsi a sararin sama. Al'ummar ƙasashen ƙasa sunyi tunanin ruwa za'a tafka amma nan take hadarin ya juye izuwa jajawur launin azaba. 


A garin Jekis dake daular Sisiya wasu ƴan kasuwa ne guda biyu dake fita sabgar kasuwancin su suka ɗaga kawunansu sama suna hasashen maike faruwa. 


"Za'a sha ruwa da walƙiya." 


Ɗayan ya girgiza kai. "Anya kuwa ruwa ne? Nidai ina ganin mu fake mu saurari mai zaizo."


Bayan kai-komo suka amince su tsaya su jira.


Sannu a hankali wannan hadari ya daidaita a sararin samaniya. Sannan walƙiya ta fara sukuwa tsakanin sama da ƙasa. Acikin wannan walƙiya wasu mutane ne guda hudu suka dira a ƙofar garin Bihanzin - garin Jekis. A wannan gari aka ɗaura auren Armad da Nostaljiya kuma ga dukkan alamu wannan gari shi ne gari na farko da za'a fara tafka yaƙin ruhi. 


Wannan mutane hudu na sanye da kayan yaƙi: sulke ruwan ɗorawa mai ratsin fari-fari wanda ya rufe dukkan jikinsu daga wuya har ƙasa. Abinda kawai ake gani shi ne fuskokinsu. 


Na farko shi ne Babara. Yana tsaye fuska babu alamun murmushi. A yayinda sauran mutun ukun suke tsaye bayansa. 


Daga ɓangaren dama Iliyasis ne zare da takobi. A kafaɗarsa ta dama akwai wata angulu wadda a idanunta babu alamun imani. A kusa dashi Cokali ne riƙe da littafin marubutan farko. Sai kuma Nostaljiya wadda ke sanye da kayan asibitin da kuma allon tsafi rataye a ƙirjinta.


Armad, Nusi, Nazara, Ayubu, da Lamarudu basa tare dasu, ko ina sukai?


Manyan mayaƙa matakin Deba guda hudu suka bayyana akan katangar garin. Idan ka lura sosai zaka fuskanci cewa wannan mayaƙa suna sanye baƙaƙen kaya ne. Babu sulke a jikinsu. Fuskokinsu na fitar da haske irin wanda ba'a saba gani a jikin bil-adama ba. Kunnuwansu a fiƙe suke kamar na zomo, sun kalli sama suna izgili ga halittu doron ƙasa ta farko. Ba tare da cewa komai ba, wannan mayaƙa suka haɗe ƴan'yatsunsu waje guda sannan suka buɗe baki suka fara kiran ɗalasimai. 


"Tsohon Zaki, Farar Damisa, Aljanar Mesa, Zakanyar Laidán!"


Suna rufe baki waɗannan halittu guda huɗu suka bayyana, kowacce ɗaya ta kama kusurwa ɗaya ta garin. Katangar guguwa ta bayyana ta kewaye garin; babu shiga babu fita. 


Iliyasis ya kalli su Babara suka gyaɗa kai kafin su afkawa garin da azababben yaƙi.


***


A can wani ɓangaren duniya, B. Ururu ne tare da basamude Deniz Ururu tsaye a ƙofar wani tsohon gari dake tsakanin doron ƙasa ta uku da kuma doron ƙasa ta huɗu. Dukkansu na sanye da koren sulke mai ratsin jini a kafaɗa. B. Ururu na haye bisa ingarman koren zaki, shi kuma Deniz Ururu na haye bisa koriyar giwa mai basamuden hanci. A duk sanda wannan giwa ta cilla hancinta sama sai kaga tana neman tsaga samaniya ta jefo da nakai. 


A bayansu akwai wani baƙin kogi launin idanun B. Ururu yana take musu baya. A gefe kuma akwai korayen namun dawa wanda yawansu bazai ƙirgu ba. 


Ƙofar wannan gari a kewaye take da yana amma kuma ƙofar a buɗe take. 


B. Ururu ya nuna ƙofar da ɗan'yatsa. Izza maɗaukakiya mai cike da mugun nufi da nufaƙa da azabar yaƙi ta fita daga jikinsa ta daki ƙofar garin. Nan take ƙofar ta narke tabi iska. 


B. Ururu da Deniz Ururu suka ƙarasa cikin garin cikin ƙasaita akan korayen ababen hawansu. 


Suna shiga suka iske rundunar samudawa dubu, kowanne sanye da korayen kayan yaƙi suna jiransu. Wata murya mai cike da tsana tana tasowa daga can cikin fadar wannan garin. 


"NI BAYAJIDDA ƊAN ALMA'ATA ƊAN DJINN ƊAN ODUDUWA ƊAN IKENGA DA HÁRÚNU ƊAN MASARAYÚLÚ, INA MAI RANTSUWA DA MAHALICCIN SARKI WILBERIYA, BAZAN TAƁA DENA YAƘAR KUBA, KU MA'ABOTA BAƘAƘEN IDANUWA (URÚRU).


"KODA KUNYI AMFANI DA WANNAN LA'ANANNIYAR IZZAR DA KUKA GADA ACIKIN WAƊANNAN BAƘAƘEN IDANUWA NAKU, KUN HANANI TAKA DORON ƘASA, TO NI KUMA ZAN YAƘE KU A TSAYE A INDA NAKE.


"IDAN MA KUKA YI AMFANI DA WANNAN TSINANNIYAR IZZA DAKE CIKIN BAƘAƘEN IDANUWAN KU, KU KA HANANI MOTSI, TO NI KUMA ZANYI AMFANI DA BAKI NA NA YAƘE KU.


"KAI KODA KUNYI AMFANI DA WANNNAN KORARRIYAR IZZAR DAKE CIKIN BAƘAƘEN IDANUWAN KU, KUN HANANI MAGANA, TO NI KUMA ZANYI AMFANI DA ZUCIYA TA NACI GABA DA YAƘARKU.


"KAI KODA KUNYI AMFANI DA BAƘAƘEN IDANUWAN KU, KUN KASHE RUHI NA, BAZAN DAINA YAƘARKU BA, BAYAN NA MUTU!!!" Bayanda muryar tazo nan a zancenta saita ɗanyi shiru, kafin daga ƙarshe ta rufe da jimla guda ɗaya!


"Ni AMRAIKUGYU BAYAJIDDA YAU RANA TA CE!"


B. Ururu da Deniz Ururu da rundunar mutun dubu ta samudawa suka zube ƙas sukai sujjada ga babbar izza. 


***


A can ƙarƙashin ƙasa, manya-manyan baƙaƙen hankakai ne keta yawo sun cika ko'ina. Idan ka ƙura ido sosai a ƙasan waɗannan baƙaƙen abubuwa akwai wasu mutane huɗu: maza uku mace ɗaya. Abin mamakin shi ne macen kamar su ɗaya sak da Nusin Armad. Idan ka lura duk su huɗun sun taɓa arba da Armad a tsibirin kaɗaici. 


Suna sanye da kayan yaƙi irin na rundunar Bihanzin wato baƙaƙe masu ratsin fari a wuya. Amma kamar wanda aka gani a saman katangar Jekis suma basu da sulke.


Su huɗun suka haɗa hannayensu suka daki iska. Babbar izza ta fita daga jikinsu ta farka iska ta tarwatsa ta. Tsarin halitta da yanayin shirin gaskiya ya tarwatse. A bayan iskar wani ƙasaitaccen gari ya bayyana. Garin a ƙulle yake amma a saman katangar an saka 'DAULAR SHADENIZA'.


Wannan mutane huɗu suka kwankwasa ƙofar sannan suka koma gefe suka tsaya. Bayan tsahon lokaci aka buɗe ƙofar. Wanda suka buɗe ƙofar wasu mata ne guda uku wanda dukkansu kamar su ɗaya sak da Nusin Armad. Acikin wannan gari jerin sojojin yaƙi ne iya ganinka sun jeru izuwa sahu uku. Sahu na farko mutane ne ƴan asalin ƙabilar Shishirui. Suna da kawu na daban-daban. Kowanne kai anyi masa kwalliya da ɗalasimai da hatimai kala-kala. Banbancin kawunan ƴan ƙabilar shishirui da na Dordor shi ne wuya da kuma ƙaho. Shishirui kowanne kai wuyansa daban, saɓanin Dordor dake amfani da wuya ɗaya. Sannan kuma shishirui suna da ƙahunhuna yawanci a goshi ko kuma a ƙeya saɓanin Dordor. 


Sahu na biyu mutane ne ƴan asalin garin Shadeniza, garin da aka ƙulleshi daga sauran alummatai tun bayan zuwan matafiyan alwashi. Sai kuma sahu na uku ƴan ƙabilar Elbinuil - zuri'ar sarkin-sarki. Halittu kyawawa masu dogon kunne. 


Runduna takai runduna amma babu Bihanzin babu alamunsa. Babu sarkin-sarki babu alamunta. Babu Armad, babu Áyúbu, babu Ikenga. Dukkan wannan jarumai dama ragowar masu mara musu baya babu alamunsu. 

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...