Skip to main content

BABI NA 276: Walkiya daga sama

 Garin Faideba 


***


Nazára yana tsaye yana fuskantar sarkin Jinzidal Hanibal. 


Ko kaɗan Hanibal bai damu da 'Ikon Armad' da Nazara ya kira ba. "Kasan banbancin aljanu da mutane?" Inji Hanibal, sannan ba tare da jiran amsa ba ya ɗora da cewa, "aljanu basa gajiya, basa jin yunwa, basa rashin lafiya, basa mutuwa. Abin daya basu wannan baiwa shi ne jikin su: an ƙirƙire su daga wuta; saɓanin turɓaya. Wuta maɗaukakiya. Wuta abar ruruwa da balbali."


Nazara yai kamar bai ji mai Hanibal ke faɗa ba: ya nuna shi da ɗan'yatsa, lamarin da yasa manyan rassan bishiyar kuka sukai fitar burtu daga ɗan yatsan suka afkawa Hanibal. Kafin Hanibal ya motsa sama da rassa ashirin sun tsire shi. Kowanne reshe ya fara zuƙar jinin sa yana ƙara girma. Cikin ƙanƙanin lokaci jikin Hanibal ya cika da itace. 


Abin mamaki hakan bai hana Hanibal magana ba. Muryar sa na fita da kyar (sabida itacen dake cake a wuyan sa), tana bada wani sauti kamar ana goga tattasai akan dutse niƙa. "Baka gane sirrin ba, yaro. Idan halitttar aljanu daga wuta shi ne ya basu iko, da wanzuwa, da waɗancan baiwarwaki dana lasafta, kana tunanin ni sarkin wuta Hanibal, babban ɗalibi a wajen na Farkon Lokaci, zai tsaya da jikin turɓaya? Jikin wuta, jinin wuta, ruhin wuta, tunanin wuta, ikon wuta... an haifeni acikin wuta, na daɗe acikin ta har sai da na zama ita, ta zama ni. 


"A farkon al'amarin zafin yakan ƙona jiki na da tsoka ta, zafin yakan sani hauka da surutai acikin bacci na, a haka nayi ƙuruciya ta acikin raɗaɗi. An kira ni maye sabida duk abinda na faɗa sai ya lalace. Ban damu ba ko kaɗan." Hanibal yai shiru na ƴan daƙiƙu kafin ya fashe da dariya. "Wataran dana fito waje na bar cikin wutar sai na kasa zama; na riga na saba da zama cikin wuta... na saba da kururuwar da wuta keyi a duk sanda iskar bazara ta kaɗa, da walwali da take yi cikin dare, da ƙarar soyuwar naman bil'adama dana dabba idan sukai arba da ita... Nan da nan na koma cikin wuta na nemi wajen na zauna cikin halwar izza. 


"A kwana a tashi wutar ta karɓeni a matsayi 'ɗa'. Tun daga nan ban ƙara rashin lafiya, ban ƙara jin yunwa, ciwo ko rauni ba... Ni ne mutun na farko dana juye izuwa aljanin gaske tunda aka halicci duniya." Yana rufe baki jikin sa ya zagwanye izuwa wata koriyar dalma mai tiriri. Dalmar ta haɗe izuwa jini da tsoka, wanda suka juye izuwa Hanibal. Ko rigar jikin sa bata ɓaci ba. Kai kace yanzu ya fito daga wanka, sabida kyalli da fatar sa keyi kamar yanzu aka halicce ta, da kuma haske da idanun sa keyi babu alamun gajiya ko kaɗan. "Bana buƙatar izza na rayu. Hasalima na katse duk wata alaƙa da nake da ita da izza, domin na yaƙe ku da zaren izzar ku."


Nazara ya jada baya. Baiyi tsammanin samun nasara fatta-ɗaya ba, to amma bai yi tunanin Hanibal ya girgije kamar babu abinda ya faru ba. Aljanin mutun. Wannan sabon labari ne wanda basu dashi. Idan labarin ya tabbata gaskiya to Hanibal zai zama ɗaya daga cikin mafi hatsari a tawagar Ikenga. To amma bawai Hanibal ne kaɗai yake da ɓoyayyen shiri ba, babu wanda acikin su bai dashi.


Nazara ya turawa Nusi ɓoyayyen saƙo. Sannan ya rufe ido, ya kira wasu ɗalasimai a zuci. Yana buɗe ido wata doguwar bishiya (zira'i maitan) ta bayyana a gefen sa. Jikin ta baƙi ne mai ɗauke da gashi irin na namun dawa. Iska na kaɗawa, gashin jikin bishiyar yana tashi sama kai kace bajimin zaki ne. Daga can saman bishiyar akwai wasu ramika biyu manya baƙaƙe masu jan hankali. Duk wanda ya ƙura musu ido zai ji tamkar za'a zuƙe shi ciki. Su kuwa rassan wannan bishiya basu da kai basu da gindi: wasu gajeru, wasu dogaye, wasu kaurara wasu sirara... Yawan su bazai ƙirgu ta sauƙi ba, sabida yadda suke da yawa kuma a cuccushe a waje guda. 


"Haaa..." Hanibal ya hangame baki cikin mamaki. "Ya sunan wannan aljani naka? Na daɗe banga jinsin su ba."


Nazara yai murmushin ƙasaita, ya ce, "Ka jiƙa idanun ka da aljani Bil'Bishiyaini. Shi ne aljani na ƙarshe da zaka gani a rayuwar ka." 


Hanibal yai ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya girgiza kai. Yaro sai ya taka garwashi yake gane zafin wuta. 


Nazara ya ga kallon rainin da Hanibal ke masa, amma hakan bai sa ya saduda ba, azama ya ƙara wajen kiran ɗalasimai. Yana gamawa aljanin mai kama da bishiya ya ɓace daga inda yake, bai bayyana a ko'ina ba sai tsakiyar ruwan kan Hanibal. Aljanin ya danne Hanibal ya murƙushe shi kamar ya murƙushe kiyashi. Tun daga inda Nazara yake yana jin ƙarar ɓallewar ƙasusuwan gadon bayan Hanibal. Ko shurawa bai yi ba, ajanin (bishiyar) ta tatsile shi. Jini yai tsartuwa ko'ina, amma asalin gangar jikin Hanibal na ƙasan bishiyar an binne ta. 


Kafin Hanibal ya samu damar aiwatar da wani abu, Nusi ta dira a gefen Nazada. Su biyun suka haɗa hannayen su waje guda suka kira wani sabon ɗalasimi wanda suka ƙirƙira da kansu a lokacin halwar da sukai a duniyar aljanu. Bishiyu huɗu baƙaƙe suka tsattsafo daga ƙarƙashin ƙasa suka saka aljani Bil'Bishiyaini (wanda shi kuma yake danne da Hanibal) a tsakiya, kowacce a kusurwa ɗaya. Wani dattijo ya bayyana a gefe ya nuna bishiyun, nan take ƙasar wajen ta juye izuwa farin yashi ta binne komai. 


"Farin yashi baya jin wuta. Dama can wuta ce ta mayar dashi fari." Inji dattijon. Idan ka dube shi sosai zaka iske ba wani bane illa ɗaya daga cikin Salsan baba Dalja, wanda aka fi sani da Farin Yashi. Nazara ya gyaɗa masa kai alamun jinjinawa, kafin ya juyo izuwa Nusi.


Wataƙila ba abin mamaki bane, amma fasahar Nazara data Nusi suna da matuƙar kamanceceniya da juna. A duk sanda su biyun suka haɗa ƙarfin fasahar su waje guda, girman izzar su yana ninkuwa sau adadi da dama. Wannan abu ne da suka gano a lokacin halwar su a duniyar aljanu.


Kamar yadda aka bayyana a baya Nusi tana amfani da Fasahar Noma. Shi kuma Nazara Fasahar turɓaya. Dukkanin fasahan guda biyu suna amfani da ƙasa a matsayin ginshiƙi. Fasahar Noma inganta sinadarin dake cikin ƙasa take ta samarda tsirrai cikin sauri. Ta hanyar wannan fasaha Nusi tana iya saka ƙananun tsirrai irin su bishiyar masara ko gero ko dawa, da ma manyan tsirrai irin su kuka, tsamiya, darbejiya, dabino, su fito su girma cikin daƙiƙu. Tana kuma iya saka ƙasa ta zuƙe duk wani abu dake jikin shuka cikin ƙanƙanin lokaci. Ta haka Nusi zata iya busar da kowacce irin bishiya, zata iya ƙarar da daji ta mayar dashi fili cikin ƙanƙanin lokaci. Asali Nusi haɗa magani ta kware, a lokacin da suka haɗu da Armad a garin Khan, kafin daga bisani ta sami Fasahar Noma a sashin ikwatora, lokacin data shiga gasar Baƙar Guguwa. 


Nazara kuma aljanin turɓaya ne dashi, wanda ta haka yake sarrafa ƙasa ya fitar da tsirrai da bishiyu a duk sanda yaga dama. Wannan fasaha ta Nazara a iyakacin tsirrai ta tsaya, saɓanin Fasahar Noma wadda ta shafi duk wani abu dake cin abinci (wataƙila shi yasa suka kira ta da fasahar Noma), domin Nusi tana iya zuƙe abinci daga jikin dukkan wata halitta. Idan su biyun suka haɗa hannu waje guda, aljani Bil'Bishiyaini yana amfani da Fasahar Noma wajen faɗaɗa ikon sa da ƙarfin sa. Abinda ada bazai iya ba sai ya zama kamar yara.


"Aljani na ya riƙe shi tamau, fasahar ki ta zuƙe duk wata laka dake jikin sa, sannan kuma yashin nan bazai bari ya narke ba. Idan ma ya narke yashin zuƙe shi zaiyi. Ko zaren Laidan yake amfani dashi ya ƙullu kenan; bazai iya fitowa daga kabarin nan ba." Inji Nazara. 


Nusi tayi ajiyar zuciya. Saɓanin Nazara har yanzu bata samu nutsuwa ba. Ta san Hanibal yana ƙasa sun binne shi, tana jin sa da yanayin izzar ta a ƙarƙashin ƙasa yana wutsil-wutsil, to amma tasan baka raba sarkin Jinzidal da wani shirin.


Suna cikin wannan hali suka ji wata gagarumar tsawa daga sama, hasken walƙiya ya haske ko'ina a faɗin duniya. Tsahon daƙiƙu biyar kowa yai shiru yana jira yaga mai zai faru. A hankali jama'a suka ɗaga kai sama. Zuƙatan su na dukan uku-uku, fuskokin su ɗauke da rashin tabbas ɗin mai zasu gani. 


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...