Skip to main content

290

 Ɓangaren Ayúbu


***


A ƙarƙashin ƙasa tuni yaƙi yayi nisa. A halin yanzu Deniz Iluru shi kaɗai ke yaƙar Ayubu, a yayin da Bizaya da Kalhari suka koma gefe suna kallo. Idan ka hangi yaƙin daga nesa zaka iya cewa duk da rayukan mutanen dake zuba a ƙasa daga kowanne ɓangare shugabannin wannan yaƙi basu ɗauki sha'anin yaƙin da muhimmanci ba. 


A ɓangare ɗaya Ayubu ya maida takobin sa cikin kufen ta, ya tsaya cak ya ware hannayen sa. 


A ɗaya ɓangaren kuma Deniz na tsaye zare da takobi. 


Bayan ƴan daƙiƙu ana kallon-kallo sai Deniz yaja da baya kaɗan, sannan a wani salo mai cike da kwarewa ya juya takobin sa ya saukar wa da Ayubu sara mai ɗauke da ƙusoshin Mairakana.


*Ƙal* 


Iluru ya sari kafaɗar Ayubu, sannan manyan ƙusoshin suka caccaki jikin Ayubu ta ko'ina. Maimakon kaga jini sai ƙusoshin suka kakkarye, takobin tai ƙara kamar an sari dutsen wuta, amma kafaɗar Ayubu na nan yadda take ko ƙwarzane babu.


Iluru ya nuna Ayubu da ɗan-yatsa ya ce, "Wannan jiki da ubangidan ka ya haɗa maka yayi. Kana tunamin da wancan zamani kafin kamfen. Kace baka da lokacin jin tarihin kakana Deniz Huhutu, to amma duk da haka zan gaya maka wani abun mamaki wanda babu wanda ya sani a duniyar ƙarƙashin ƙasa sai ƴan kaɗan." 


Ayubu ya girgiza kai tare da zare takobin sa ya ce, "Bari idan akwai sauran rai a jikin ka bayan na gama sai ka gayamin." 


Yarjejeniyar ita ce Ayubu zai tsaya cak Iluru ya sare shi, idan bai mutu ba to shima zai tsaya Ayubu ya sare shi. Kuma akan haka Ayubu ya tsaya Iluru ya sare shi, shima kuma yanzu zai tsaya. Sabida haka Iluru ya maida takobin sa cikin kufen ta ya tsaya cak yana jiran Ayubu.


Ayubu ya sauke masa babbar takobin izza. 


*Ƙal*


Takobin ɓallewa tayi gida biyu ɓaras, lamarin da yayi matuƙar bawa kowa mamaki. Kai bama su Bizaya dake kusa ba, hatta sojojin dake fafatawa a nesa sai da suka juyo suka kalla. Takobin izza ta ɓalle!


"Hahaha..." Iluru ya fashe da dariya. A  wannan lokaci ya yaga rigar sa dai-dai wajen da Ayubu ya sara domin ya nunawa duniya cewa baya sanye da rigar ƙarfe ko kuma wata kariya, hasalima daga shi sai fatar sa ko sulke babu. 


Ayubu yayi mamaki amma ba jimawa ya dawo dai-dai. Ya buɗe ƙirjin sa ya nunawa Iluru.


Amma Iluru ya girgiza kai, ya ce, "Ina ganin babu adalci aci gaba da wannan karawa tunda ka rasa takobin ka, ko ya kake gani?" 


Ayubu yayi murmushi tare da kaɗa kai, ya ce, "Kada ka damu dani, ka fara damuwa da kanka."


Iluru ya ɗanyi shiru yana jimanta maganar a ransa kafin ya gyaɗa kai. "Ina ga baka fuskanci abinda nake nufi ba, Ayubu. Abinda nake cewa shi ne: kai dai baza ka iya cin nasara akai na ba, dole kana buƙatar agajin ubangidan ka. Nima kuma bana tunanin zanci galaba a kan ka ta sauƙi, musamman idan akayi la'akari da wannan zarurrukan dake zagaye da filin nan ta ko'ina. Kai idan ma nayi nasara akan ka to a banza, ko kashe ka nayi Armad zai tashe ka. A taƙaice dai wannan fafatawa tamu bata da amfani: idan nayi nasara a banza, kai kuma baka da ƙarfin yin nasara. Ya kake gani? A haƙura haka, mu haɗu a Jinzidal."


"Ashe kana ganin zaren." Inji Ayubu. "Hmmm... Duk da haka kana nan tare dani. Kana tunanin zan barka ka samu dama ka shiga kamfen ɗin ne kai ma." 


Iluru yaja dogon tsaki. "Mtswwww..." Ya rasa ta wacce hanya zai ɓullowa Ayubu. Dole aka ci gaba da bata kashin. Duk sanda Ayubu ya sari Iluru sai takobin sa ta ɓalle (lamarinda zai sa ya samar da wata takobin daga zaren izza), shi kuma Iluru ya kasa yiwa Ayubu ko ƙwarzane. 


Bayan tsahon lokaci ana fafatawa sai kawai aka ga Ayubu ya yada takobin sa yaja da baya ya ɗaga hannu sama cikin saranda yana cewa, "Iluru, idan ka gayamin sirrin dake cikin jikin ka wanda yake karya takobi na to zan yadda a tsaya da wannan fafatawa anan." 


Iluru ya kalle shi cikin mamaki. Yasan akwai dalilin da yasa Ayubu ya canja shawara kwatsam. 


Ayubu ya nuna fatar Iluru da hannu. "Baka da Tauri, baka da Fatar Ƙashi, kai ina tunanin ma baka da komai - babu wani abu dake kare ka amma kaƙi saruwa. Meye sirrin? Idan ka gayamin zan yadda a kammala yaƙin nan yanzu."


Abinka da tsoffi a harkar izza. Ba jimawa Iluru ya gane abinda ke afkuwa. Ya dubi Ayubu ya ce, "Duk yadda akai Armad ya turo maka saƙo." 


"Kana da matsala da hakan ne?" Inji Ayubu.


Deniz ya girgiza kai. "A'a. Kai da ubangidan ka wa zai hana ku ganawa. Kawai dai kada ayi gulma ta."


"Meye sirrin ka? Ka gayamin idan kana so na barka kasha iska."


Iluru yai murmushi. "Idan naƙi fa? Dani da kai duk mun san kona gaya maka ko ban gaya maka ba dole tafiya zakai. Kayi addu'a na barka ka tafi da ran ka. Idan ma ka gudu ai akwai waɗancan." Ya nuna sadaukan da Ayubu yazo dasu guda dubu (wanda a yanzu yawan su ya sakko ƴan ɗaruruwa), wanda suke ta fafatawa da denizawa.


A zahiri kamar yadda Iluru ya faɗa haka abin yake. Armad ya haɗu da kwamandun sa, Dul'Ururu da mutanen sa sun tafi, yaƙin da ake a garin Faideba da garin Jekis duk sunzo ƙarshe, kowa ya haɗu babu wanda ya rage sai Ayubu. Hakan yasa Armad ya bashi umarni ya dawo, a dai-dai lokacin da Ayubun yake tsaka da fafatawa da Deniz Iluru.


***


Acan doron ƙasa na biyar, a tsakiyar wani daji wani abin al'ajabi ne ke faruwa. Acikin wannan dajin akwai ɗan tanti madaidaici wanda aka gina da taɓo. A kowacce kusurwa ta tantin akwai aljanu biyu na tsare suna gadi. Idan ka lura sosai zaka fuskanci cewa ta cikin wannan dajin Armad da Nusi suka biyo acan shekarun baya sanda suka fara zuwa garin Khan. Sai dai dajin ya ƙara duhuwa sabida yanayi na damuna. Ciyawa kaɗai tafi tsayin mutun.


A cikin wannan tanti Armad ne tare da kwamandun sa. Wani abin al'ajabi shi ne cikin tantin yafi wajen sa girma nesa ba kusa ba. Misali idan ka kalli tantin ta waje bai fi tsahon zara'i goma ba, amma ta ciki yafi faɗin zira'i ɗari. Akwai ƙatoton falo haɗe da kicin da banɗaki. Ga wani ƙatoton teburi a tsakiyar falon wanda shi kaɗai yakai tsayin zira'i goma. 


Ko wacce sabuwar fasaha ce wannan?


To koma dai wacce fasaha ce hakan baya gaban Armad da kwamandun sa wanda ke zaune sun zagaye taburin dake tsakiyar falon. Armad shi ne a gaba, Nostaljiya a ɓangaren sa na dama, Nusi a hagu. Iliyasis, Cokali da Nazara suna ɓangaren Nusi, Babara, Lamarudu da Inara suna ɓangaren Nostaljiya. Daga can ƙarshe Ayubu na zaune ya harɗe ƙafa, ga dukkan alamu ba'a maraba da zuwan sa, idan kayi la'akari da kallon da kowa yake masa.


Armad ya dubi Ayubu, ya ce, "Shi ne ka taho ka bar mayaƙan naka acan?" 


Ayubu ya yamutse fuska ya ce, "to kace na taho baka yimin bayanin dalili ba, ba dole na taho da sauri ba. Na sani ko kana cikin hatsari ne, ko wstaƙila an cika da yaƙi kana neman agaji na. Shi yasa na garzayo na rabu dasu." Kana jin muryar Ayubu kasan baiji daɗin kiran sa da akai ba. Shifa matsalar sa ɗaya baya so a bashi umarni. Shima ji yake 'Armad' ne sabida haka babu umarnin wanda zaibi. Idan ana son zaman lafiya dashi to kada a ringa bashi umarni. Indai har ana so yayi abu to sai dai a nemi shawarar sa kafin a bashi umarni. Ko kaɗan Armad bai yadda da wannan ƙa'idar iskancin ta Ayubu ba. Su kuwa kwamandu abin yafi ƙarfin su, kawai zuba musu ido sukai suna kallo.


"Ko mutun ɗaya idan ya mutu acikin su a wuyan ka. Dolo kawai." Armad yai tsaki ya dawo da hankalin sa kan taswirar dake saman teburin. A jikin taswirar akwai zanen ƙasa bakwai. Ga wasu duwatsu dake gefe an ajiye su sabida lissafi.


Armad ya ɗebi duwatsu huɗu ya ɗora a sassa daban-daban na taswirar. Dutse na farko akan sashin ikwatora yake, na biyu akan garin ƙarƙashin ƙasa Shadeniz, na uku kan doron ƙasa na biyu, na huɗu kuma na kan Duniyar Ɓoye. 


"Wannan sune wajaje huɗu da za'a fafata wannan yaƙi." Inji Armad. "Sarkin-sarki tana ganin ita ce mai mulkin duniyar ɓoye, Ikenga ya nemi ta bashi dukkanin ɓangarorin da kakansa Oduduwa ya gina amma taƙi. Lamarinda yasa ya tura B. Ururu da Deniz Ururu da Amraikugyu domin yaƙar ta. Ko a yanzu da muke wannan magana tuni yaƙi yayi tsamari tsakanin ɓangarorin biyu - sama da mutun dubu hamsin sun halaka daga kowanne ɓangare. A halin yanzu Ikenga da Bihanzin duk sunƙi shiga yaƙin. Tsoron su idan suka yaƙi juna zan laɓe na ƙarasa wanda yayi nasara, sabida haka na tabbatar baza su shiga yaƙin kai tsaye ba. Ya kuke gani?"


Iliyasis ya nuna dutsen dake kan doron ƙasa ta biyu, ya ce, "da Dul'Ururu da mutanen sa suna nan. Anan zamu haɗu dasu a Jinzidal nan da wata ɗaya mai zuwa. Babu makawa yaƙi ne mummuna a tsakanin mu. Meye zai hana Ikenga, wanda ke sashin ikwatora, da kuma Bihanzin, wanda ke Shadeniz, su afka mana ta baya a yayin da muke tsaka da yaƙi da Dul'Ururu?" Iliyasis yayi gyaran murya ya girgiza kai yaci gaba da cewa, "abinda nake nufi shi ne duk a jirgi ɗaya muke. Damu da Bihanzin da Ikenga, kowa taka-tsantsan yake. Kuma na tabbatar kowa acikin su jira zaiyi a gama kamfen yaga mai zai faru tsakanin mu da Dul'Ururu. A taƙaice dai ina so naji, shin zamu iya faɗa da Dul'Ururu da kuma Bihanzin da Ikenga duk a lokaci ɗaya?"


Babara yaja dogon numfashi ya fuskanci Armad ya ce, "ina ganin babbar tambayar anan ita ce: shin Armad zaka iya yaƙar Dul'Ururu, da Bihanzin da Ikenga kai kaɗai a lokaci guda?!"


Nan fa duk suka juyo suka fuskanci Armad suna jiran amsa. 


Armad ya buɗe baki ya ce, "....."


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...