Amma ina, bashi da izza ko ɗigo a jikinsa, ko walkiya ɗaya bai gani ba.
"Armad!" Fatima ta kwala masa kira tana ƙoƙarin ture shi gefe. Kafin ya fahimci mai take ƙoƙarin gaya masa yaji izzar Dul'Ururu a bayansa.
Da sauri ya dawo da mahaifiyarsa ƙasa ya rufe ta da jikinsa. Sandar Dul'Ururu ta sauka a bayansa. Wata wuta mai haɗe da narkakken dutse tayi sama tana tartsatsi.
"Armad!" Nusi ta kwalla ƙara tare da tafiya da gudu wajen Armad.
Zaikid wanda ke kusa da ita yayi maza ya riƙe ta. "Idan kika shiga faɗan can mutuwa zaki yi," inji Zaikid.
A banza, duk da abinda Zaikid ya faɗa Nusi bata ji ba, kawai ƙoƙarin ƙwacewa take yi domin ta tafi wajen Armad ta ceto shi.
A ɗaya ɓangaren ita ma Fatima hawaye kawai take yi tana ƙoƙarin ture Armad gefe domin harin ya sauka a kanta. Amma Armad ya dake yaƙi matsawa ko'ina.
Dul'Ururu ya ƙara loda masa sandar tsafinsa. Jini ya fara malala daga hanci da bakin Armad yana zuba akan Fatima. Gashi babu izza ko guda a jikinsa balle ya iya wani abu. Duk izzarsa ta ƙare a fasahar da yayi amfani da ita ɗazu.
To a dai-dai wannan lokaci acan baya wajen Maikiro'Abbas wani abun al'ajabi ne yake faruwa. Mayaƙa kowa idonsa nakan Armad da Dul'Ururu suna mamakin abinda ke faruwa. Wai tayaya Armad ya ɗakko Fatima? Wannan ita ce tambayar da suke yiwa kansu domin kuwa babu wanda yaga lokacin da abin ya faru.
"Non-toch-teka?" Inji Maikiro'Abbas, yana murmushi. "Wannan yaron Armad yana da ban mamaki. Ban taɓa tunanin ganin irin wannan fasaha a wajensa ba."
"Nima nayi mamaki," inji wata murya daga ɗan yatsan sarkin. Idan ka lura sosai zaka ga zoben dake hannun sarkin mai ruwan zuma shi ne yayi maganar. "Amma fasahar tana jan izza da yawa. Na tabbatar da ace a doron ƙasa ta uku zuwa ta bakwai yayi amfani da ita da tuni Hajarul Ururu ya taka masa burki tunda ya wuce adadin izzar da aka yadda ayi amfani dashi. Amma dai duk da haka ya cancanci yabo tunda ya kwato Fatima a maimakon ka."
Sarkin yaja dogon numfashi tare da gyaɗa kai. Yaga abinda Armad yayi tun daga sanda ya ƙaddamar da fasahar har zuwa sanda ta ƙare. Baiyi tunanin Armad zai iya hakan ba saboda haka yayi tunanin shi zai kwaci Fatima da kansa. To amma duk da haka akwai sauran aiki a ƙasa. Ururu baza su bawa Armad hanya ta sauki ba.
Maikiro'Abbas ya juya wajen mayaƙansa.
"Mayaƙan Maikironomada," inji Maikiro'Abbas da babbar murya. A take kowa ya juyo kai yana kallonsa. "Masu unguwanni, yan majalisa, dagatai, barada, dama dukkan mayaƙan dake tare damu..." Yaja numfashi ya ɗaga sandarsa ya nuna Ururu. "Ku karɓi ƴar ku Fatima."
Yana rufe baki yayi tsalle sama ya rataya jakar tsafinsa yayi kan Ururu. Dukkan mayaƙan da suka rage sukai kukan kura suka rufa masa baya.
Ganin haka Zaikid, Nusi, Burjan, jan doki, Najunanu, Cokali duk sukai kukan kura suka rufawa sarkin baya. A lokacin Giwa, Barilu, Inyaya, da sarkin Bai suka bayyana a bayansu. Idan ba'a mantaba su aka saka su kula da Suwainah da Ibraham Nil, su kuma tare su idan suka fuskanci zasu shiga yaƙin. Sai dai har yanzu Suwainan da Ibraham Nil Basu da niyyar shiga yaƙin. Ganin hakan yasa sadaukan suka dawo kusa da uwar gidansu - Nusi.
A lokaci na farko sarki Maikiro'Abbas ya shigo yaƙin kai tsaye. Ruwan saman dake zuba a hankali ya tsuge kamar da bakin kwarya, kai kace yana bin umarnin zuciyar sarkin ne.
"Ku kashe su," inji Maruta. Jin haka mayaƙan Ururu sukai ƙaraji suka zare makamansu suka afka kan mayaƙan Maikironomada dake tahowa.
Maikiro'Abbas yana zuwa ya daki ƙasa da ƙafarsa. Ƙarfin dukan yasa ƙasa tayi sama da mutanen Ururu. Sama da mutun ɗari dake gaba sukai sama suka faɗo ƙasa tim. Maikiro'Abbas yasa sandar tsafinsa ya kai duka dama. Wata ƙanƙara ta fita daga tsinin sandar tayi kan Ururu kamar an harba mashi. Duk wanda ta taɓa sai kaga ya daskare ya fashe. Ƙanƙarar bata tsaya ba sai da ta dangane da bangon katangar daya zagaye filin. Daga nan sai kawai ta fara buɗewa tana yin faɗi. Mayaƙan dake kusa sukai sauri suka durkusa suka bata guri. Wanda kuwa basu yi sauri ba suka gamu da fushin ƙanƙarar inda ta daskarar dasu. A haka sai da ƙanƙarar ta cinye sama da mutun ɗari biyar.
Kafin Ururu su farfaɗo Maikiro'Abbas ya daki iska da hannunsa na hagu. Nan take aljanar kada ta bayyana akan iska ta buɗe kakkausan bakinta ta fara feshin ruwan zafi. Duk wanda ruwan ya taɓa sai kaga fatarsa ta salube ya faɗi ƙasa a sume. Kamar abin bai isa haka ba sai Maikiro'Abbas ya riƙe sandarsa da hannu biyu ya daki gabansa da ita. Nan take wasu ƙananun masu na ƙanƙara suka fara fita daga sandar suna yin kan mayaƙan Ururu. Duk wanda mashin ya taɓa sai kaga yayi sama kamar anyi cilli dashi ya faɗo ƙasa tim ya daskare. Cikin dakika kaɗan Maikiro'Abbas ya kashe sama da mutun dubu. Ganin haka mayaƙan Ururu suka fara jada baya. Su kuwa mayaƙan Maikiro'Abbas dama tunda suka ga sarkin ya fara kai hari suka jada baya; sun san idan ransa ya ɓaci ba'a shiga gabansa indai baso kake ya haɗa da kai ba.
Thanks Dr
ReplyDeleteTAiki yayi kyau
ReplyDeleteThanks for reading
Delete