Idan ba abin al'ajabi ba, wace takobi ce take hayaƙi kamar an kunna itace?!
A dai-dai wannan lokaci wani baƙin hayaƙi ne ya taru a kaifin takobin Maruta yayi kan su Iliyasis kamar an saki kura. Ƙasa da iska suka fara girgiza kamar zasu fashe.
Iliyasis ya ɗaga takobin sa da hannu biyu ya tare takobin Maruta, shima Babara cilla sandar sa ta tsafi yayi ya tare silin takobin. A gefe guda kuma Inara ƙoƙari yake ya tare hayaƙin takobin da ƙarfin walƙiya, shi kuma Cokali ƙoƙarin zuƙe hayaƙin yake zuwa cikin littafin marutan farko.
Amma duk da haka takobin Maruta bata girgiza ba. Cikin kwarewa tayi Rawa akan takobin Iliyasis da sandan Babara ta zille musu ta bar su suna dukan iska. Hayaƙin takobin ya fashe ya fara ambaliya yana cin ƙasa da iska. Duk abinda ya taɓa sai kaga ya dare. Kafin kace meye wannan tuni hayaƙin ya haɗiye su baki ɗaya.
Nusi, Nostaljiya, Nazara da Lamarudu na gefe basu motsa ba. Suma su Dul'Ururu basu motsa ba. Tsahon lokaci ana kallon-kallo a tsakanin su har saida hayaƙin takobin Maruta ya lafa su Iliyasis suka bayyana.
Wata ƙawanyar shuɗin haske ta zagaye su Iliyasis ta rufe su kamar ƙwarya. Hayaƙin takobin bai samu damar ratsa wannan shuɗin haske ba, amma duk da haka rigunan su sunyi daga-daga kamar an fizgo su daga bakin kura. Jikin Inara ya juye ya koma walƙiya, amma hakan bai hana wani baƙin jini ɗisa daga bakin sa ba.
Maruta ya nuna Inara da ɗan'yatsa, sannan a wata murya mai cike da mamaki ya ce, "Kai ne na farko daka taɓa tare saukar takobi na."
Inara yayi murmushi tare da goge jinin dake bakin sa, ya ce, "haha.. nima wannan shi ne karo na farko dana taɓa yin arba da kaifin takobi mai aiki akan ruhi."
Shuɗin hasken ya yaye a hankali suka fito fili. Idan ka dube su sosai zaka ga cewa bawai Inara kaɗai ba, har su Babara da Iliyasis da Cokali sunyi faca-faca da jini. Faɗa da ifritun aljani ba riba.
Nostaljiya taja ɗan numfashi tare da girgiza kai, ta ce, "ga dukkan alamu sai na saka hannu a faɗan nan." Ta shige gaba, shi kuma Lamarudu ya taka mata baya.
Sai dai kuma a lokacin Nusi da Nazara suka shiga gaban su. Nusi ta dubi Nostaljiya ta ce, "ni Armad ya bawa alhakin kawo garin Faideba, sabida haka koma mai ya faru ni ce. Wannan aiki na ne, indai ba neman suna ba ki matsa."
Nan take aka hau kallon-kallo tsakanin Nusi da Nostaljiya. Kowacce na cije baki kamar zata ci babu. Bayan ɗan lokaci Nostaljiya ta gyaɗa kafaɗa tare da turo baki ta koma baya ta bar Nusi.
A ɗaya ɓangaren Hanibal ne ya matso gaba domin tarar su Nusi (wanda daman abokan karawar sa ne) amma a lokacin Dul'Ururu ya taka masa birki. "Muna da abin yi a wajen kamfen, bamu da lokacin ɓatawa anan." Inji Dul'Ururu.
A wannan lokaci Dul'Ururu ya shige ya tsaya a gaban Hanibal da Maruta. Da ganin haka kowa ya gyara tsaiwar sa. Haruta da Ibraham Nil (mai farin ido) da Suwainah suka matso kusa suka jeru a bayan sa a bayan Dul'Ururu - wazirin kamfen.
Dul'Ururu ya ɗaga hannun sa sama ya fara karatun yanka. "Da sunan sarki Kuyurussa'ayi ɗan Kalbukussa'ayi ɗan Biyákúyassa'ayi ɗan Urúrú na Farkon-farkon Lokaci, da sunan mai Babban Kabari, da sunan Yardaddun Idanu, da sunan Babbar Siffa, da sunan Babban Allo, ni Dul'Ururu - wakilin babba ɗan babba; wakilin kamfen a ƙasashen ƙasa - na yanke wa waɗannan kafirai takwas hukuncin kisa."
Nan take kamar daga sama taurari takwas suka bayyana a gaban Dul'Ururu. Girman kowacce tauraruwa baifi faɗin hannu ba, amma ko kurma zaiji irin tiririn izza da girman iko dake tashi daga cikin wannan taurari. Kowacce tauraruwa tana haske kamar rana. Idan ka lura sosai zaka ga sunaye akan kowacce tauraruwa. Wannan suna ye bawai ɗalasimai bane, ba kuma wani ƙulumboto bane, a'a, suna yen su Nusi ne akai. Su takwas kowa da tasa tauraruwar.
A karo na farko gumi ya ketowa Nusi da Nostaljiya. A fuskar su akwai alamun firgici dangane da wannan taurari. Gashi dai taurarin basu motsa ba, to amma kasancewar su a wajen kaɗai ta isa razani. Zaka iya cewar kamar abin nan ne da masana suke faɗa: mai izza da wuri yake gane babbar izza. Su Nusi tuni suka ankare da taurarin.
"KU JERU A BAYANA." Inji Nostaljiya, muryar ta na rawa.
"Ehh..."
Sauran kwamandun suka buɗe baki suna kallon Nostaljiya. Babu shirin hakan. Hasalima wani babu lokaci a baya da Nostaljiya ta taɓa yin wani abu irin hakan. Amma acikin muryar ta babu wasa ko kaɗan, dukkanin su sun san cewa da gasken-gaske take.
Lamarudu bai tanka ba ya koma bayan Nostaljiya ya tsaya.
Shi kuma Babara ganin sauran sunƙi bin umarnin Nostaljiya yasa ya yanke shawara ya hau layi. Na ukun shi ne Inara. Amma kana ganin idanun Inara kasan akwai damuwa aciki. Bawai tsoro bane, kuma bawai kunyar tsayawa a bayan mace yake ba, to amma kana ganin sa zaka fuskanci cewa akwai damuwa a tattare dashi. Koma mai Nostaljiya take niyyar yi bai aminta dashi ba, to amma dole yayi biyayya sabida koba komai ai 'matar sarki sarauniya ce'.
A ɗaya ɓangaren kuma Nusi ce taja tunga a gefen Nostaljiya ta ɗora hannayen ta biyu akan ƙasa.
Iliyasisi ya dubi Nusi jikin sa na rawa, ya ce, "Ƴar'uwa... kar dai... fasahar nan zaki yi amfani da ita?!"
Wani murmushi mai cike da ɓacin rai ne yazo gefen bakin Nusi ya tsaya. "Buri na naga Armad a kan kujerar doron ƙasa na farko, duk abinda na mallaka (da ruhi na da izza ta) duk nasa ne."
Iliyasis yayi mata wani kallo mai cike da mamaki da ɗimuwa haɗe da tausayi, amma bai ce komai ba kawai yabi layi a bayan ta. Cokali yabi bayan sa.
Nazara kawai murmushi yayi sannan ya ƙara sa kusa da Nusi ya ɗora hannun sa akan kafaɗar ta. Nan take sinadarin Negrinkin sa da izzar sa suka fara fita daga jikin sa suna shiga jikin ta.
Nusi ta kalle shi tai ajiyar zuciya. Ta buɗe baki zatai magana amma ya riga ta. "Indai kina so na bari sai dai kema ki bari. Kada ki manta nazo wannan tafiya ne domin ke badan kowa ba."
Duk wannan abubuwa na faruwa Inara na gefe yana tunani a cikin ran sa. Wai shin ya cika alƙawarin daya ɗaukar wa Armad na kasancewa tare dashi da kare shi da iyalan sa? Ya dubi Nusi da Nostaljiya ya girgiza kai. Shima yasan bai cika wannan alƙawari ba. A yadda abin yake tafiya shi ake karewa bawai shi yake karewa ba.
Dul'Ururu ya miƙa hannun sa kan taurarin dake gaban sa cikin kwanciyar hankali. "Ina miƙa rayukan wannan kafirai takwas izuwa gare ka." Inji Dul'Ururu. Ga dukkan duk wani shiri da Nusi da Nostaljiya ke yi bai dame shi ba. Ya yadda ya aminta da ƙarfin ikon fasahar sa.
Tauraruwa ta farko da Dul'Ururu ya fara kai hannun sa kai ita ce tauraruwar Nusi. Hannun sa na shirin murƙushe tauraruwar Inara yai kukan kura yai tsalle sama ya kira ɗalasimi. "Kaban'shisu!"
Nan take ya ɓace daga inda yake ya bayyana a gaban Dul'Ururu. Hannun sa na hagu yana ɗauke da Hannun-Aradu, na dama kuma yana ɗauke da babbar takobi. A ransa yana cewa, *zan sadaukar da rai na indai zan kare iyalan shugaba Armad.*
Abin ya bawa Dul'Ururu da kowa a wajen mamaki. Ratar dake tsakanin su ba ƙarama bace, tayadda Iliyasis yana ganin Inara kawai jefar da rayuwar sa yake niyyar yi a banza, domin kuwa babu wata hanya dazai iya cin galaba akan sarki Dul'Ururu - sarki bisa doron ƙasa ta biyu.
Dul'Ururu ya saki tauraruwar Nusi ya cafi ta Inara, sannan ya shaƙi wuyan Inara da ɗaya hannunsa yai walanƙeluwa dashi ya buga shi da ƙasa. Sai da ƙasar wajen ta dare gida biyu sabida tsabagen ƙarfin harin. Ba daban Inara yayi sauri ya juye jikin sa izuwa walƙiya ba da tuni ƙasusuwan jikin sa da kayan cikin sa sun ruɓurɓushe. Dul'Ururu ya miƙa hannun sa zai tatsile tauraruwar Inara amma kawai sai aka ga ya canja shawara ya saki tauraruwar ya danna kan Inara a ƙasa da hannu biyu. Sannan ya dunƙule hannun sa ya fara dukan fuskar Inara. Gashi dai jikin Inara na walƙiya ne amma duk sanda hannun Dul'Ururu ya haɗu da fuskar sa sai kaga jini yai feshi.
"Kamar kai, ɗan tsatsitsin kiyashi kace zaka tare ni?! Wannan cin mutunci ne a rayuwa ta. Ni, Dul'Ururu, ɗa ne a wajen BABBA ɗan BABBA. Kana tunanin zaka iya tarar yarima Dumaƙisu kai tsaye? Baka isa ba, to amma ni ka tare ni sabida raini. Kana tunanin zan yafe maka kawai sabida raunin ka. Bari kaji na gaya maka, ko a doron ƙasa ta farko bana yadda da raini. Duk wanda ya nuna Dumaƙisu ya fini sai naga bayan sa ba kai ba wani ɗan tatsitsi." Yana magana yana dukan fuskar Inara. Tun Inara na ihu har sai da ya daina magana. Jikin sa ya canja daga walƙiya zuwa jini da tsoka.
Kwamandun Armad suka rankayo da gudu domin ceto Inara amma su Suwainha suka shiga gaban su.
Ana cikin wannan hali, Inara ya ɗebe haso daga rayuwa, wani saurayi sanye da ƴar shara ya bayyana a bayan Dul'Ururu. Yana bayyana ya riƙe hannun Dul'Ururu, ya ce, "Baka ganin ya ishe ka haka, yaro?"
***
Ko waye wannan saurayi?!
Comments
Post a Comment