Skip to main content

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad. 


Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje.


"Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?"


Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta. 


Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda Burjan yana tsaye a tsakiya yana goge takobinsa. Babu wanda yaga sanda yazo wajen amma ya tsarge tauraruwar gida biyu kamar wanda yake yanka albasa. 


Wani abin mamaki shi ne Armad da Fatima suna can gefe a ƙasa. Duk yadda akai basu samu sun shiga ta cikin ƙofar ba. Hakan ba abin mamaki bane tunda iskar data tashi kaɗai zata iya cilli dasu. 


Ganin haka Nazára yayi wa Nusi inkiya inda da sauri ta tafi ta ɗauki Armad da Fatima a kafaɗa ta tafi da gudu cikin ƙofar zata shiga. Nazára, Rabi, da Burjan suka shiga gaba da niyyar tare duk wani hari da Binani ko Dul'Ururu zasu kawo. 


Nusi tana zuwa bakin ƙofar ta fara cilla Armad ciki. Kafin ya ƙarasa ta jefa Fatima. Su Nazára suka zagaye ƙofar cikin kariya. Sai dai Binani baiyi wani motsi ba banda kallon-kallo daga nesa. Ganin hakan yasa Nazára yasha jinin jikinsa akwai matsala, amma baice komai ba.


Suna tsaye Armad ya shige ta cikin ƙofar amma abin mamaki maimakon ya ɓace sai kawai ya fito ta baya. Ita ma Fatima ta fito ta baya ta dira akansa. 


Rabi da Burjan suka kalli juna sannan suka yi kokarin taɓa ƙofar domin suga mai ke  faruwa. Ai kuwa suna taɓawa sai hannunsu ya shige ciki. Ƙofar ta juye ta zama haske. 


"Hahaha..." Suka ji dariya daga sama. Suna daga kai suka hangi kwamanda Ki'jinu a tsaye kan iska. 


Daruruwan mayaƙan Ururu wanda tuni hankalinsu ya dawo kan su Nazára suka fara ihun murna. 


"Kwamanda!"


"Kwamanda!"


"Kwamanda!"


Ganin haka zuciyar Nazára ta fara dukan uku-uku. Tabbas duk acikin kwamandun Ururu babu mai sharrin Ki'jinu. Fasaharsa baza ta kashe kaba, amma zata lahanta ka. Za kuma tasa har a gama yaƙin baza ka iya amfani da jikinka ba wanda hakan zai saka ka zama kamar wani hoto kenan. Tunda fari yarima Abba da yarima Umaru sune suka sadaukar da kansu wajen tare Ki'jinu, amma ga dukkan alamu a halin yanzu ya kwace. 


Nazára ya ɗaga kai wajen akwatin ƙanƙarar da aka kulle Ki'jinu. A wajen babu komai sai yarima Umaru da Abba suna tsaye suna lilo akan iska. Idan baka sani ba sai ka rantse lafiyar su kalau amma kuma hoto ne kawai. 


Duk yadda akai a sanda Dul'Ururu ya saukar da harin tauraruwar a lokacin Ki'jinu yazo ya lalata ƙofar. A yanzu babu hanyar tsira kenan. 


Kwamanda Ki'jinu ya fara miƙe-miƙe yana gyara rigarsa. A hankali ya sakko ƙasa wajen Binani. A lokacin suka hango Diwani ya taho daga nesa. Cikin ƴan dakiku ya ƙaraso ya tsaya a kusa da ƴan uwansa biyu. Zaka iya cewa kwamandun uku wanda akafi sani da salsan Dul'Ururu sun hallara.


Shin Diwani ya gama da Najunanu da jan doki kenan? Nazára ya ɗaga kai yana dube-dube. Acan kusa da Zaikid ya hango Najunanu da jan doki suna tsaye. Ga dukkan alamu sadaukan biyu sun yanke shawarar su rabu da Diwani su taimakawa Zaikid wajen yaƙar Dul'Ururu. A halin yanzu mutun takwas ne suke yaƙar Dul'Ururu wanda suka haɗa da Cokali, Giwa, Inyaya, Barilu, sarkin Bai, Najunanu, jan doki, da farfesa Zaikid.


Ganin salsan sun hallara Burjan ya cije baki yayi kan Fatima da gudu takobi a zare. Ko kaɗan baya goyon bayan Fatima taci gaba da tsayawa a filin yaƙin domin kuwa idon kowa a kanta yake. Kuma Ururu ita suke so su kashe, amma babu yadda zaiyi, dole suna buƙatar fasahar Fatima idan suna so su samu nasara. Sannan kuma a lokacin Fatima ita kaɗai zata iya tashin Armad daga suman da yayi. 


Yana zuwa ya ɗaga takobi ya sari ankwar dake ƙafar Fatima. A take ankwar ta tarwatse. Ya ƙara ɗaga takobi ya nufi ankwar dake hannunta. Amma a lokacin kwamandu ukun sukai kansu da mugun nufi. Diwani ya riƙe hannun Binani, shi kuma Binani ya riƙe hannun Ki'jinu. Wani dankwalelen farin ƙarfe mulmulalle ya fito daga hannun Binani ya haɗu da hasken gemun Ki'jinu inda ya koma jajawur. A lokaci guda al'amudai uku ne suka fito daga hannun Diwani suka shiga jikin ƙarfen a kowace kusurwa. Kai tsaye suka harbo musu ƙarfen. 


Da sauri Nazára ya ɗaga hannu biyu ya samar da ƙatoton faifan ƙarfe da niyyar tare harin nasu, amma abin mamaki sa kawai dunkulallen ƙarfen ya shige ta cikin faifan kamar ma babu shi. A lokacin Nazára ya fuskanci harin nasu na musamman ne domin kuwa kamar yana da fasahar Ki'jinu da kuma ta Diwani da kuma ta Binani duk a waje guda. Tabbas duk abinda harin ya taɓa ya gama dashi. Da sauri Nazára ya miƙa hannu zai ɗauke Nusi amma hannunsa bai ƙarasa ba saboda haka ya samar da hannun ƙarfe ya janyo Nusi da ƙarfin tsiya ya dauke ta daga jikin Armad. Da shi da Rabi sukai tsalle suka kauce. Wanda kawai ya rage a wajen shi ne Burjan wanda yake ƙoƙarin sare ankwar dake hannun Fatima, sai kuma Armad wanda ke ƙasa a sume.


A dai-dai sanda Burjan ya kai sara zai tsinke ankwar dake hannun Fatima, a lokacin harin ƙatoton ƙarfen jajawur ya diro kansa. Al'amudan uku dake kowace kusurwa ta ƙarfen suka yi nakiya a lokaci guda. Ƙarfen yayi bindiga ya tarwatse. Duk abinda ya taɓa sai kaga ya zama haske. Sannan kuma a hankali sai kaga abin yana narkewa kamar ana narka shi da wuta. Nazára ya samar da bangon yashi har uku a jere a gabansu amma duk a banza. Babu wani abu da yake iya tare harin. Daga ƙarshe sai juyawa sukai suka fita da gudu da ƙafafunsu. 


Duk wani mutun ko kuma wani abu dake kewayen wajen sai da harin ya narkashi. Wato wani irin hari ne wanda babu ruwansa da sulke ko kuma wata kariya. Indai yazo to babu abinda yake iya tare shi. Sannan kuma idan ya taɓa mutun maimakon kawai kaga mutun ya koma haske kamar yadda Ki'jinu yayi wa yarima Umaru da Abba, sai kaga mutun ya narke ya zagwanye kamar an narka ƙarfe. Haɗa ƙarfi waje guda da kwamandun sukai ya canja yanayin fasahansu ya ƙara musu ƙarfi sama da lissafi. Da dama suna ganin ƙarshen Fatima da Armad da Burjan yazo. 


Can bayan ƙura ta lafa sai mayaƙan dake wajen suka yamutse fuska.


"Kai... Menene wancan jan abin?" Inji wata mace daga cikin mayaƙan Ururu.


"Ehmm... Watakila jikin abokan gaba ne da suka narke, ko?" Inji na kusa da ita.


"A'a, haba dai, ka duba fa ka gani. Wancan abin hayaki ne ba jini ko tsoka ba."


Sai dai ba kamar sauran mutanen dake nesa ba, idanun kwamandun uku yana kan Armad da Fatima da Burjan. A dai-dai wajen da suke tsammanin suga gawar Armad data Fatima data Burjan, wani jan hayaki ne ya bayyana ya rufe komai tayadda basa iya ganin abinda ke ƙasa. A hankali hayakin ya ringa ƙaruwa har dai duk wani mutun dake filin ya ankara dashi. 


Babu zato, babu tsammani sai kawai hayakin ya fashe ya bazu ko'ina. Ganin haka kwamandun suka yi sauri suka jada baya. 


Daga inda yake, Dul'Ururu ya hango hayakin amma ko a jikinsa. Ci gaba yayi da ƙoƙarin murkushe abokan faɗansa.


"Ku matsa nace," inji Dul'Ururu a fusace. "Fatima baiwa ce. Bazan bari ku karya doka ba."


"Wilbafos ba bawa ba," inji Zaikid. 


Dul'Ururu ya kawo duka da sandarsa. Zaikid yasa takobi ya kare. Sai dai akan idon kowa Dul'Ururu ya ringa tura Zaikid baya. Zaikid yasa hannu biyu ya danna takobinsa amma duk da haka Dul'Ururu bai daina tura shi ba. 


Inyaya ya bayyana a bayan Dul'Ururu da wani mutum a hannunsa jini yana malala daga wuyansa. Cikin kwarewa yasa ɓarin takobinsa ya mari jinin. Jinin dake malala ya juye izuwa kwayoyin jini wanda sukai kan Dul'Ururu. A lokaci guda sarkin Bai da sarkin yaƙi Barilu suka bayyana a kusa da Inyaya. Da sauri suka harbawa Dul'Ururu kibiya saitin ƙashin bayansa inda lakarsa take. Kibiyoyin biyu suna tafiya akan iska suna ƙara gudu. 


Mutun na ƙarshe daya bayyana a bayan Dul'Ururu shi ne Cokali. Yana bayyana ya buɗe littafinsa yayi rubutu. A take aljanun zakuna uku suka yi fitar burtu daga cikin littafin suka tunkari Dul'Ururu. 


Ta gaba kuma Najunanu ne ya bayyana ya haɗe hannu guri guda ya samar da ƙatotuwar ƙawanyar ruwa ya harba masa a ƙirji. Jan doki ya sauka a kusa da Zaikid ya saka takobinsa ya danna sandar tsafin Dul'Ururu dake tura Zaikid. 


Kafin Dul'Ururu yayi wani abu kibban da sarkin Bai da sarkin yaƙi Barilu suka harbo sun dira a bayansa sun cake shi. Kwayoyin jinin Inyaya suka feshe masa baya. Duk inda suka taɓa sai kaga yana zubar jini. Zakunan Cokali uku suka sauka ƙasa suka kama agara ƙafa suka hana shi motsi. Ƙawanyar ruwan Najunanu ta daki fuskarsa amma maimakon ta zube ƙasa sai ta rufe kan sarkin baki ɗaya. Idan ka duba zaka ga ƙawanyar ruwa ta rufe kansa tun daga gashin kansa har wuya ta yadda ko numfashi bazai iya ba. 

Comments

Most Popular

461

Rai a ɓace, Dul'Ururu ya saka hannu biyu akan sandarsa ya ture takobin Zaikid data jan doki gefe. Sannan da sauri ya juyo ya take zakunan dake riƙe da ƙafarsa ya kuma kawowa Cokali sura. Abin mamaki kafin hannunsa ya ƙaraso sai Cokali ya ɓace ɓat. Sarkin ya juyo kan sarkin Bai da Inyaya, amma kafin ya ƙaraso duk sun ɓace. Ya ƙara juyawa kan Barilu, amma kafin yayi wani abu shima ya ɓace. "Hmm.. wannan sihirin da kuka zo dashi bazai yi aiki ba," Inji Dul'Ururu. To a yayinda Dul'Ururu yake fama dasu Zaikid, acan gefe kuma Maikiro'Abbas ne suke kai-komo da Ƙaraiƙisu. "Haha... Maikiro'Abbas, Maikiro'Abbas," Inji Ƙaraiƙisu. "Kada ka bani kunya mana. Na saka rai zan samu jarumi barde wanda zan kara dashi amma har yanzu banga komai ba." Ya ƙara kawowa Maikiro'Abbas duka da ƙafa. Maikiro'Abbas bai motsa ba har ƙafar basamuden tazo ta same shi. Zaka yi tunanin saboda girman ƙafar zata yi cilli da Maikiro'Abbas, amma sarkin...