Skip to main content

BABI NA 100-108: Shawarar Armad

 Babi na 100: Shawarar Armad


Armad da Nostaljiya suka nufi hanya izuwa ɗakin da aka saukeshi. Akan hanyarsu kowa yayi shiru bai ce komai ba. Nostaljiya tana jira Armad ya gaya mata abinda suka tattauna da mahaifinta amma Armad yayi shiru. Ita kuma bata tambaya ba. 


Koda isarsu ƙofar ɗakin sai Armad ya shige ɗakin ba tare da yace uffan ba sannan ya turo ƙofa. Nostaljiya ta buɗe baki zatai magana amma ta fasa. Cikin ɓacin rai ta juya ta tafi. Har ta kusa ƙulewa ta juyo ta dubi kuyangar dake ƙofar ɗakin ta ce, "Ku bashi duk abinda yake buƙata, idan ya nemi ku nuna masa hanyar fita daga fada ku nuna masa." Tana rufe baki ta juya ta tafi. 


Armad ya faɗa kan gado yana jinta harta ƙule. Yai shiru yana tunanin maganarda Bihanzin ya gaya masa. Abu ne mai sauƙi tunda mahaifiƴarsa ta sami sauƙi ya fice daga wannan daula kada ya ƙara waiwayarta. Yaje can wani waje ya tsara sabuwar rayuwarsa cikin kwanciyar hankali. To amma Armad yasan cewa tun daga ranar da yayi rantsuwa zai tarwatsa cinikin bayi rayuwarsa baza ta ƙara kasancewa cikin kwanciyar hankali ba. Irin wannan rayuwa wadda za'ai aure a haihu a sami ƴaƴa biyar ko goma, sannan a zauna cikin kwanciyar rai har a tsufa a mutu ba tasa bace. 


Dama dai tuntuni abinda yasa Armad bai maida hankali ba akan shirinsa na tarwatsa cinikin bayi shi ne halinda mahaifiyarsa ke ciki. Amma ga dukkan alamu wannan ya kau. A yanzu ne lokaci mafi dacewa daya kamata ya fara aiwatar da shirinsa. 


Auren Nostaljiya lallai zai ɗaukaka martabarsa a idon duniya kuma zai saka rundunar sarki Bihanzin ta zama kamar tasa. Daɗin daɗawa daga abinda Nostaljiya ta gaya masa a wancan lokaci da suka haɗu, akwai rigima tsakanin sarakunan Jinzidal tayadda kowannensu zaiso yaga bayan ɗan'uwansa. Duk da cewa manufar Bihanzin ta yaƙi da sauran sarakunan Jinzidal ba lalle bane ta zama ɗaya data Armad ba, amma dukkaninsu suna da abokan gaba iri ɗaya. 


Matsala ɗaya ita ce; shin Bihanzin akan kansa yana so ya tarwatsa cinikin bayi ko kuma kawai yana so ya tarwatsa sarakunan Jinzidal ne? Domin zata iya yiwuwa Bihanzin yana goyon bayan cinikin bayi amma yana rigima da sarakunan Jinzidal. 


Armad na zuwa nan a tunaninsa ya yanke shawara, Idan har Bihanzin ya amince ce zai taimake shi ya rusa gasar Jinzidal to shima zai taimaka masa ya karya sarakunan Jinzidal.


Bayan Armad ya cimma wannan matsaya saiya fito da Maikiro Inara daga cikin zobensa. Har izuwa wannan lokaci Inara bai farfaɗo ba, amma ga dukkan alamu ruwa kawai yake buƙata. 


Ai kuwa Armad yana yayyafa masa ruwa ya farka, inda Armad ya kwashe dukkanin labarin daya afku bayan ya suma ya gaya masa. Inara ya taya Armad murnar samun lafiyar mahaifƴarsa sannan yayi masa fatan alkhairi. 


---------

Armad da Inara suka kwana acikin wannan ɗaki, washe gari da safe Armad ya kaisu wannan tafki sukai wanka sannan suka ci suka sha. Bayan sun dawo ɗaki Armad ya fara jira ko zaiga Nostaljiya amma shiru har yamma ta kawo kai rana ta faɗi ba labari. Da magariba Armad ya tura ɗaya daga kuyangin dake kawo musu abinci ta kira masa Nostaljiya amma bisa mamaki hakan bata samu, Nostaljiya ta amsa amma bata zo ba. Haka ya gaji da jira har dare yayi gari ya waye.


Washe gari Armad ya ƙara tura wata kuyangar, Noltaljiya tace taji amma har dare yayi bata zo. Nan take Armad ya fara shiga damuwa saboda yasan haƙiƙanin dalilin da yasa Nostaljiya bata amsa kiransa ba. 


Washe gari Armad ya yanke shawara ya taka yaje wajenta da kansa. Koda ya fito bakin ƙofa saiya tarar da ɗalibinsa Inara na tsaye yana gadin ƙofar. Murmushi kawai Armad yayi ya bashi umarnin yazo ya rakashi. 


Armad ya dubi ɗaya daga cikin kuyangin dake wajen ya ce, "Muje ki rakamu wajen gimbiya." 


Amma wannan kuyanga ta kada baki ta ce, "Ai ba'a shiga wannan ɓangare daga mu kuyanginta sai ita kanta, gimbiya."


Maganar bata yiwa Armad daɗi ba, ya tsaya yana ta tunani kafin daga bisani ya juya ya koma ɗaki. Har ya isa bakin ƙofa sai wata dabara ta faɗo masa, yaci birki ya tsaya tare da juyowa izuwa wannan kuyanga ya ce, "muje naga wajen saboda tsaro."


Kuyangar fara ce mai tsaho sanye da farar doguwar riga. Tana jin abinda Armad ya ce ta zare ido tana mamaki. Abinda bata gane ba shi ne mai Armad yake nufi da 'saboda tsaro'. To amma ba muhallinta bane a matsayinta na kuyanga ta tsaya tana yiwa Armad tambaya, saboda haka ta shige gaba ta fara tafiya, su Armad suka bi bayanta. 


Abin mamaki sai Armad yaga sun ɓulle ta wata ƙofa wadda ta shigar dasu wani ƙaton fili. Duk kewayen da Armad yayi na kwana biyu bai san da wannan filin ba. Haka suka ci gaba da bin kuyangar har suka ƙarar da wannan fili suka nufi ɓangaren arewa, sannan daga bisani suka iso wata farfajiya mai yawan bishiyun dabino. 


Wannan bishiyun dabino sun kekkewaye wannan sashi ta yadda ba'a iya gano cikinsa sosai. Suna ƙara matsowa sai Armad ya fuskanci cewa wannan ɓangare an raba shi ne izuwa gida uku manya-manya. Abin mamaki shi ne hatta katangar da aka kewaye wannan waje da zinare aka yaɓe ta. Komai kawai walwali yake. Nan take Armad ya fara tunani yana mamakin irin dukiyar dake cikin wannan fada. 


Suna isowa gindin wannan bishiyu sai wannan kuyanga ta tsaya tana nuni da ginin dake tsakiyar gine-ginen guda uku. "Wancan ne na tsakiyar. Na ɓangaren dama kuma na ƴarima Kiru ne, na ɓangaren hagu kuma na yarima Hasanu me. Amma daga nan babu wanda yake da damar haurawa sai su ƴaƴan sarkin uku."


Tuni Armad ya gama lissafa yadda zai biyo dare ya haura wannan katanga sai kawai wani haske mai kashe ido ya haske masa ido. A zuciyar Armad ya gane wannan haske amma yana ji a ransa wataƙila kawai dai idonsa ne. Amma ba jimawa wanda ke ɗauke da hasken ya bayyana daga bayan wannan bishiyun dabino. 


Lallai Armad yayi gaskiya, domin kuwa ba idonsa bane. Wannan haske hasken Farar-takobi ce, wato takobin yarima Kiru Sisiyu ɗan sarki Bihanzin wanda suka fafata da Armad shekaru da dama da suka gabata. 


Kiru ya fashe da dariya tun kafin ya iso. "Ko baka zo nema na ba zan neme ka. Domin kuwa bamu idar da fafatawarmu dakai ba a wancan zamani. Da sannu zaka gane ƙarfin Farar-takobi na."


A zahiri Armad ba wajen Kiru yazo ba, amma babu yadda zaiyi. Wannan fafatawa kamar anyi ta ne an gama.


Armad ya fara magana yana leƙen saman benen ko zai hango Nostaljiya, "K....kiru, lallai naji daɗin ganinka, domin kuwa ina neman wanda zan wasa takobi na dashi."


***

Babi na 101: Armad da Kiru


Cikin murmushi Kiru ya ƙaraso tare da ƙarewa Armad kallo sannan ya miƙa ido izuwa Inara. 


"Kana da ƙani ne dama?"


Armad yai murmushi tare da waiwayawa ya kalli Inara sannan ya ce, "A'a. Aboki na ne."


Kiru ya ɗanyi shiru sannan daga bisani ya gyaɗa kai yana kallon filin nan ya ce, "Nakan yi atisaye a wannan fili, ya kake gani?"


Armad ya miƙa hannu izuwa takobinsa yana cewa, "Eh.. Ina ganin yayi."


Nan take Kiru ya kira bayi suka fara kai-komo suna gƴara filin. Kan kace meye wannan tuni waje ya haɗu, an samarda wata ƙawanya wadda aka zagaye da raga-raga. Sannan kuma ƙasan wajen aka saka wata leda mai tudu da santsi tayadda koda ka faɗi baza kaji ciwo ba. 


Armad yai tsalle ya dira a tsakiyar filin wanda daman tuni Kiru yake jiransa akai. Ana cikin haka sai ga yarima Hasanu ya bayyana daga cikin wannan gidaje uku yana murmushi. Ko ba'a tambaya ba kasan yana tuno abinda ya faru ne a shekarun baya tsakanin Armad da Kiru. A wancan lokaci da sukai niyyar halaka Armad amma saboda bayyanar wani Dordor a yayinda Kiru yake fafatawa da Armad basu samu dama ba. Yau gashi Armad ya dira a daularsu amma a matsayin aboki. Duniya juyi juyi.


Armad ya dubi Kiru yana goge takobinsa ya ce, "rabo na da amfani da takobi tun a gasar Jinzidal. Ina ganin zaka iya yin galaba akaina."


Kiru ya fashe da dariya yana cewa, "Saboda kai baƙo na ne zanyi faɗa dakai ido na a rufe. Indai kayi nasara to zan baka doki na."


"Hmm.." Armad yayi ajiyar zuciya. Indai doki ne ai bazai samu wanda yafi Ubbaru ba amma kawai yayi murmushi tare da mayarda takobinsa ciki kufenta yana cewa. "Na yadda ka rufe ido amma ni kuma bazan yi amfani da takobi ba. Indai kaci galaba akaina ko kuma kasa na fita daga cikin iyakar nan koda sau ɗaya na yadda kayi nasara."


Kana jin maganganunsu kasan kowa yana taƙama da ƙarfin izza. Amma ko waye zaiyi nasara? Nan take Kiru ya rufe idonsa, shi kuma Armad ya maida takobinsa. 


Kiru ya tunkaro Armad gadan-gadan yana sassarfa takobi a zare. Yana zuwa ya kawowa Armad sara ta ɓangaren dama amma Armad ya kauce cikin kwanciyar hankali. Kiru ya ƙara kawo masa sara ta sama, Armad ya ƙara kaucewa. Kan kace meye wannan Kiru ya aikawa da Armad sara sama da goma yana kaucewa. 


A wannan lokaci ne Farar-takobi ta fara haske tana ɗaukan zafi kamar yadda ta saba. Tun a wancan Armad yasan sirrin wannan takobi kuma yasan zarar ta fara wannan haske abubuwa sun rikice. Idan zai iya tunawa sunanta guda uku ne; WALƘIYA, FASHE-FASHE, ƘURA. Ana kiranta da walƙiya saboda tsananin haske mai kama da walƙiya da take bayarwa wanda yake haske idanun abokan gaba. Sannan kuma ana kiranta da 'Fashe-fashe' saboda duk abinda ta sara bindiga yake ya tarwatse tamkar an saka masa bom. Sunanta na ƙarshe kuwa wato Ƙura ba komai ya sa ake gaya mata shi ba sai yawan ƙura da take jawowa idan ta tarwatsa waje. Lallai akwai sirrika da dama acikin wannan Farar-takobi, musamman duba da cewa duk wannan abubuwa da Aramd ya sani a shekara uku ne da suka gabata. Kaga dole daga wannan lokaci zuwa yanzu shima Kiru ya ƙara gogewa ya ƙara ƙarfin takobinsa. 


Abin mamaki Armad na cikin tunani sai wannna Farar-takobi ta Kiru ta fara bayarda wata farar iska. Iskar nada haske kamar na farin gajimare. Nan take ta fara juyawa cikin sauri tana zagaya takobin ta Kiru. 


Cikin murmushi Armad ya kalli takobin ya ce, "Ah.. Lallai ka ƙarawa Farar-takobi ƙarfi. A sani na da ita bata da wannan fasahar iskar."


Kiru yai murmushi tare da ƙara juya takobin tasa yana cewa, "Ai baka ga komai ba." 


***

Wato wani abu da Armad bai sani ba shi ne a dai-dai wannan lokaci bawai Hasanu da Inara ne kaɗai ke kallonsu ba. Hatta sarki Bihanzin da kansa na wani waje zaune akan karagarsa yana nazarin wannan wasa ta wani sihirtaccen mudubi. Ya riga yasan ƙarfin takobin ɗansa, kuma idan akwai wanda zai gaji fasaharsa ta Dauwamammen Sara wato Bankái Bihanzin yana ganin Kiru ne. Domin tuni yayansa Hasanu ya yarda hanyar takobi ya ɗauki hanyar fasahar aljanu. Idan mai karatu bai manta ba Hasanu yana sarrafa jar iska wadda tafi wuta zafi. 


Daɗin daɗawa bawai Bihanzin ne kaɗai ba hatta Nostaljiya na kallon wannan fafatawa ta cikin gidanta.

***


Wannan Farar-iska dake kewaye da takobin Kiru ta fara tsiri tana yin sama. Kan kace meye wannan ta cika filin. A wannan lokaci Kiru ya ɗaga takobinsa ya kawo wa Armad sara. Abin mamaki sai kawai wannan farar iska ta juye izuwa wasu mutun-mutumi guda bakwai wanda kowanne su na riƙe da takobi irin ta Kiru, suka yiwo kan Armad gadan-gadan. Abin mamakin shi ne wannan mutun-mutumi na iska basa bada yanayin-izza ko kaɗan tayadda baka isa kaji su ba idan idonka a rufe yake. 


Armad ya tsaya yana nazarin yadda zai kaucewa wannan mutun-mutumi guda bakwai musamman ganin yadda suke mugun gudu. Kafin yayi wani abu sun saka shi a tsakiya, babu wata mafita data wuce banda sabuwar fasahar Kaban'shísu. 


Nan take Armad yaci gaba da jira har saida suka zo dab da inda yake sannan ya ɓace ɓat suka nemeshi suka rasa. Bai tashi bayyana ba sai a bayan Kiru wanda idonsa a rufe yake yana jiran sakamakon da mutun-mutuminsa zasu samo masa. 


Amma abin mamaki ko kaɗan Kiru bai nuna mamaki ba da ganin ɓacewar Armad duk da kuwa bawai abu bane daya taɓa gani ba. Sannan kuma yana jin bayyanar Armad a bayansa amma ko jiyo wa baiyi ba. 


Armad ya ɗora hannunsa a wuyan Kiru yana cewa, "kaga da a filin daga ne da tuni kaje ƙasa."


Sai dai kuma ko rufe baki Armad bai yiba ya gane cewa da matsala. Motsi kawai yaji a bayansa mai kama da ƙaɗawar iska, yana jin haka ya duba yaga wannan mutun-mutumi guda bakwai basa wajen daya baro su. Nan take ya gane mai yake faruwa. 


Ya ƙara ɓacewa ya bayyana acan nesa. Takobinansu suka sauka a ƙasa inda nan take suka tarwatsa dukkan ƙasar wajen dake ƙarƙashi. Lallai wannan mutun-mutumi suna da matuƙar mahaukacin sauri tunda har zasu iya bin bayan Armad a halin yanayin ɗalasiminsa. Amma babban abinda ya firgita Armad shi ne rashin jin yanayin-izzarsu da ba'ayi. 


Nanfa aka fara ƴar zille-zille tsakanin Armad da waɗannan mutun-mutumi. Yana amfani da Kaban'shìsu amma duk da haka da kyar yake iya guje musu. Duk inda ya bayyana saiya gansu. Da ace da takobinsa da tuni ya gama dasu, to amma ga rashin takobin kuma baya so yayi amfani da walƙiyarsa. Ana cikin haka kawai sai gani yayi wannan mutun-mutumi sun fara haske. Kafin Armad yayi wani motsi dukakaninsu bakwai ɗin sunyi bindiga dashi a tsakiya. Ƙari akan haka Kiru a karo na farko ya saka hannu a wannan fafatawa inda ya kawowa Armad sara da zahirin Farar-takobin dake hannunsa bawai mutun-mutumi ba.


***

Babi na 102: Kwamanda Damjinu Djinn


A dai-dai wannan lokaci yarima Hasanu yai tsalle ya faɗa tsakiyar filin nan da niyyar tsayarda harin Kiru domin ba kamalarsa bace ya bari yana wajen a jiwa Armad ciwo a matsayinsa na baƙonsu. Amma lamarin shi ne ba shi da cikakkiyar masaniyar zai iya isa wajen akan lokaci.


Shi kuwa Bihanzin kawai murmushi yayi. Yasan cewa Kiru bawai ƙoƙarin jiwa Armad ciwo yake ba kawai dai yana so ya kaishi bango ne tayadda zai matsa shi yayi amfani da takobi. 


Nostaljiya kuwa zuciyar ta ce ta fara bugawa amma jikinta ya kasa motsi. Kallon filin kawai take daga ɗakinta baki a buɗe.


Shima Inara ba'a barshi a baya ba wajen tsalle da ƙarasawa wajen Armad.


Ƙura ta turnuƙe ko'ina ba'a ganin komai. Amma Kiru tuni ya saukar da takobinsa kafin kowa ya ƙaraso. Abin mamakin Kiru yasan lallai Armad bai kaucewa takobinsa ba. Kuma hanya ɗaya da Armad zai iya kuɓuta daga wannan hari shi ne yayi amfani da takobinsa wadda yace bazai yi amfani da ita ba. To amma abin mamakin shi ne duk da Kiru baya ganin Armad saboda ƙura dake wajen amma yasan lallai takobinsa bata haɗu da takobin Armad ba. Hasalima yana ji a jikinsa kamar ya sami Armad. To amma lokaci ne kaɗai zai nuna bayan wannan ƙura ta lafa. Abu ɗaya dai da kowa ya sani shi ne ba'a ji ihu ko kuma ƙarar Armad ba. Lallai da an same shi akwai yiwuwar zafi yasa yayi ƙara ko kuma aga fallatsar jini. 


Da Hasanu da Inara kawai kasaƙe sukai suna jira ƙura ta lafa suyi ido biyu da sakamakon wannan wasa. 


Bayan wani ɗan lokaci ƙura ta fara lafawa. Wani farin haske ne mai tartsatsi ya fara yi musu sallama daga bayan wannan ƙura. Kafin daga bisani surar Armad ta bayyana amma ba Armad ɗin da suka sani ba. Wannan Armad ɗin na walƙiya ne. Jikinsa ya juya ga baki ɗaya izuwa walƙiya yana ƙuwwa yana bada ƙara irinta saukar Aradu. Takobin Kiru na cikin kafaɗarsa ta shige amma babu alamun jini.


Cikin firgici Kiru ya cire kyallen daya rufe idonsa tare da yin tsalle baya yana haki. Shi kuwa Hasanu kawai ɗaga hannu yayi yana nuna Armad ya rasa mai zaice. Amma Inara kawai zubewa yayi a ƙasa yana mubayi'a ga sarki Wilbafos. Babban abinda Armad bai sani ba shi ne duk wanda ya taɓa karanta tarihi yasan wannan sihirtacciyar fasaha ta walƙiya wadda a tarihin duniya sarki Eyriyon ne kaɗai ya taɓa mallakar ta.


Nostaljiya kanta idanunta a zare suke tana al'ajabin wannan abu. Tun a farkon haɗuwarsu tasan Armad zai iya farkarda babbar fasaha daga gidan Wilbafos amma ko'a mafarki bata taɓa tunanin wannan ba. Hasalima ko'a ƴaƴan Ururu babu wanda bazai so ya sami wannan fasaha ba. 


A can cikin fada kuwa, uwa uba sarki mai dauwamammen sara sakar mudubin tsafin dake hannunsa yayi ya miƙe yana al'ajabi. Domin idan wasu a tarihi suka karanta, shi Bihanzin yasan wannan fasaha kamar yadda yasan idan baici abinci ba zaiji yunwa. Lallai wannan ita ce fasahar nan ta sarki Eyriyon ɗan sarki Aldaima Wilbafos. 


Acikin filin wasa kuwa Armad gano wa yayi ya jawo wa kansa tambayoyi da bayane-bayane. Domin ko ba'a faɗa ba wannan gasa tazo ƙarshe, dan tuni Kiru yaja baya da takobinsa. 


Armad ya juya ya kalli Inara yaga halinda yake ciki na durƙushe yana mubayi'a. Sannan ya kalli Hasanu yaga mamakin dake cikin idanunsa. Nan take ya gane cewa indai har ƴaƴan sarakuna zasu yi wannan bayan sunga wannan fasaha to yaya sauran mutane gama-gari zasu yi. Idan ya bari aka ga wannan fasaha tasa to lallai ba jimawa duniya zata ɗau labari, kuma komai zai koma kunnen Ururu. A take Armad ya yanke shawarar indai bawai babu yadda zaiyi ba dole ya ringa ɓoye wannan fasaha.


Cikin murmushi Armad ya dubi Kiru ya ce, " ni naci wannan gasa tunda gashi ka buɗe idonka." 


Ajiyar zuciya kawai Kiru yai tare da girgiza kai ya ce, "eh.. kayi nasara amma ka shammace ni ne kawai da mamakin wannan fasaha taka da babu shakka baza kayi nasara ba. Sannan kuma ni fasahar takobinka naso na gani amma kaƙi amfani da takobi saboda haka lallai zamu ci gaba da wannan gasa anan gaba. Yanzu kaje ka huta."


Armad yai murmushi yana gyaɗa kai yasan cewa dama Kiru bazai ɗauki rashin nasara ba cikin sauƙi. 


Koda ganin haka sai Hasanu ya fashe da dariya yana cewa, "ai ƙa'ida ƙa'ida ce. Lallai tunda aka saka ƙa'ida cewa indai ka buɗe ido ka faɗi to ka faɗi."


Haka dai aka tashi daga wannan fafatawa ana ta tsokanar Kiru.


Daga bisani Armad da Inara suka nufi ɗaki. A hanyarsu Armad ya dubi Inara ya ce, "kada ka damu ina sane dakai kuma wannan satin zan fara horar dakai."


"Babu komai sarki Wilbafos, a kullum da nake tare dakai ina koyar abubuwa masu amfani."


Armad yaji daɗin amsar da Inara ya bashi kuma bai sani ba kodan saboda irin wannna ɗabi'a ta Inara yasa yake jin daɗin zama dashi.


Koda suka iso bakin ƙofar ɗakin sai Inara ya kewaya yabar Armad ya shiga shi kaɗai. A zuciyar Armad yana ta lissafin yadda za'ai ya gamu da Nostaljiya, dan babu alamun jan ajinta zai ƙare nan kusa idan baije ƴa bada haƙuri ba. Yana ƙarasawa kan gado ya cire takalminsa ya ɗare sannan ya faɗa cikin kogon tunani yana kallon wannan kifaye dake cikin gilas suna iyo. A haka har sa'a guda ta wuce, a lokacin bacci na niyyar ɗauke shi yaji an turo ƙofar ɗakin. Zuciya ɗaya Armad yai zaton Inara ne ya dawo amma kawai sai wani zabgegen mutun mai irin ƙirar Bihanzin ya shigo cikin ɗakin.


Mutumin yana sanye da baƙar ƴar shara wadda takai har idon sahunsa, yana tafe a hankali cikin limana amma kana ganinsa kasan ba ƙaranin barde bane. Fatarsa fara ce fat kamar ta sauran mutanen wannan daula, gashin kansa kuwa fari-fari ne mai ruwan ƙasa.


Mutumin ya ce, "kada ka tsorata suna na Damjinu Djinn, kuma ni ne kwamandan runduna ta farko a dukkan wannan daula. Nazo ne nayi maka tambaya a bisa umarnin sarki Bihanzin."


Armad har yakai hannunsa kan takobinsa yayi shiri ya tsaya cikin ajiƴar zuciya yana mamakin wanne dalili ne zaisa a turo masa babban kwamanda tsakar dare. 


Damjinu yaci gaba da cewa, "banda waɗanda suka ganka a yau akwai wanda suka san kana da wannan fasaha ta Eyriyon?"


Armad najin tambayar ya haɗe gira domin kuwa shima abinda yake tunani kenan. Ya dubi kwamandan ya ce, "akwai, amma duk suna cikin kurkukun Bango."


Kwamandan najin haka yai shiru yana nazari. Armad ya lura cewa idanuwan kwamandan sun ƙara ƙanƙacewa duk da ƙasa yake kallo. Can daga bisani kwamandan yaja dogon numfashi ya dubi Armad ya ce, "to shikenan, amma a shawarce kada ka bari kowa ya ƙara ganin wannan fasaha. Sannan kuma ka yiwa wannan ɗalibi naka kashedi domin a halin yanzu baka da fasaha da tafi ta ƙarfi, zaka iya amfani da ita kaci galaba akan mutun ko min ƙarfinsa indai bai san da ita ba. Amma zarar kowa ya sani idan zaiyi faɗa dakai zai shigo cikin shiri."


Kwamandan na gama faɗar haka ya juya ya nufi ƙofa, Armad yai masa shiru baice komai ba amma har yakai baƙin ƙofa ya juyo ya ce, "haka ma baƙin hankaka daka gani, shima dan mun yadda dakai ne muka nuna maka amma babu wanda ya san dashi. Haka ma sunan Nostaljiya Nára, shima babu wanda yasan shi acikin wannan daula, kowa Zahra Sisiyu ya sani. Idan zaka kira ta kayi amfani da Zahra musamman idan acikin mutane ne." 


Yana gama faɗar haka ya buɗe ƙofar ya fice.


Armad ya ajiye takobinsa gami da yin ajiyar zuciya ya ƙara faɗawa kogon tunani.


***

Babi na 103&104: Ƙabilar Nára


Iliyasis da Cokali da Inara ne ke tsaye akan Armad wanda ke zaune akan kujera acikin babban ɗakin karatu na daular Sisiya. Girman wannan ɗakin karatu ya wuce duk inda mai karatu zai hango, domin kuwa idan ka ɗaga kai zaka ga rufinsa tamkar ya haɗe da samaniya. Duk inda ka waiga manya-manyan malamai ne da ɗalibai cikin babbar riga da rawani suna nazari akan kujeru. Babu ruwan kowa da kowa babu wanda ma yasan Armad na wajen ballantana ya damu. Abu ɗaya kaɗai da aka hana shi ne surutu, wanda kuma Armad da mutanensa sun kiyaye.


Abin mamakin shi ne gumi kawai suke haɗawa kamar sun dawo daga filin yaƙi. Hasalima su Iliyasis da Cokali haki suke. Idan ka kalli cikin Cokali zaka ga yana sama yana ƙasa kamar ana cilla tulu saboda tsabagen nishi. Ko meye yasa su acikin wannan hali?


Armad yai ajiyar zuciya ya goge gumin dake fuskarsa tare da maida littafin dake hannunsa kan kanta yana cewa, "wannan ma babu." 


Dukkaninsu sukai nishi mai haɗe da doguwar ajiyar zuciya suka ƙara nausawa cikin ɗakin karatun. Babu abinda suke sai wuce kantoci masu ɗauke da tsofaffin littattafai wanda ke bada wani irin yanayi na da wanda yasa dukkan yanayin ɗakin karatun canjawa. Amma Arnad da mutanensa ko'a jikinsu kawai nausawa suke. Suna isa matattakala suka hau suka fara yin sama izuwa sauran ɗakunan dake sama.


A hankali a hankali tun suna sassarfa har suka fara gudu amma wannan matattakala taƙi ƙarewa. Abin mamaki babu wanda ya damu acikinsu ko magana basa yi kowa dai kawai yana ta zulumi da alhinin abinda ke ransa.


Bayan rabin sa'a suka iso ƙarshen wannan matattakala inda suka tararda ƙofa a rufe. Armad ya kwankwasa lamarinda yasa bayan ƴan daƙiƙu aka buɗe wata ƴar taga a tsakiyar ƙofar. Wani tsohon mutun mai yawan tamusasshiyar fata da farin gashi ya leko yana magana cikin ƙinƙina ya ce, "Wannan sihirtaccen waje ne, indai ba sheda ba'a shiga."


Armad ya ɗakko wani kati daga aljihunsa ya nunawa dattijon. Cikin mamaki dattijon ya kalli katin sannan ya kalli Armad kamar yana mamakim yadda akai Armad ya sami katin. Sannan daga bisani ya ɗakko wani ƙaton tabarau ya saka a ido, sannan ya karɓi katin dake hannun Armad ya fara haskawa da fitila yana duba saka-hannun dake kan katin dalla-dalla. 


Saida ya ɗauki sama da minti goma yana haka har saida su Armad suka fara gajiya sauran ƙiris Cokali ya bada shawarar a tura ƙofar sannan suka ji dattijon yayi ajiyar zuciya ya buɗe ƙofar a hankali. Amma duk da haka bai buɗe ta gaba ɗaya ba, hasalima ɗan kaɗan ya buɗe tayadda ko mutun ɗaya idan zai wuce saiya karkata.


Amma Armad bai damu ba, cikin sauri ya karkata ya shige. Inara ya bi bayansa amma cikin sauri wannan dattijo ya turo ƙofa ya rufe yana cewa, "ai mai katin sheda shi kaɗai ke shiga wannan waje."


Cokali najin haka ya cije baki yana niyyar dannawa ya shiga ta ƙarfi amma Iliyasis ya riƙe shi. Inara shima baya ya dawo ya tsaya cikin ɓacin. Armad kuwa wucewa kawai yayi tunda daman ba'a son ransa suka biyo shi ba. 


Tsohon na rufe ƙofa Armad ya tsinci kansa a wani waje mai tsananin duhu ko tafin hannunsa baya gani. Nan take ya dunƙule hannunsa ya mai dashi walƙiya ya fara amfani da hasken a matsayin fitila. Wasu manya-manyan kantoci ne wanda aƙalla sunyi ashirin ɗin wanda ya gani a ƙasa girma, kowacce na ɗauke da littafai iƴakacin ganinsa. Wasu da dama daga cikinsu tuni sun fara yana saboda rashin taɓawa. Har yanzu Armad bai tararda kowa acikin wajen ba, yana tafiya yana karanta rubutun dake kan kowacce kanta, wanda ke nuni da littattafan dake saman kantar.


ASALIN ALJANU


ALAƘAR ALJANU DA DORDOR


ƘASA BAKWAI


IZZAR TAKOBIN GIDAN SISIYA


IYAKAR ƘASA BAKWAI


ASALIN URURU


ASALIN IZZA


TARIFIL FAKTA DA AMRAIKUGYU


SHAIƊANUN FARKO DANA ƘARSHE


FARAREN ALJANU DA MAIKIRO ABBAS BABAN DAIKIRIN


DANGIN KABILAR NARA DA WILBAFOS!!


Armad na zuwa kan wannan kanta mai magana akan dangin ƙabilar Nara da Wilbafos saiya tsaya, domin kuwa ya samu dai-dai abinda yake nema. Nan take ya jawo littafin farko ya nemi kujera ya zauna. Abin mamaki yana zama sai yaga wajen yayi haske, tamkar an ɗakkoshi daga cikin ɗakin an kaishi wani waje na musamman.


Daga can nesa yaga wasu malamai wanda aikinsu kawai haɗa tarihi suna ƙara rubuta shi. Amma wannan malamai ko kaɗan basu nuna sunga shigowar Armad ba.


Armad yai ajiyar zuciya ya nemi waje ya zauna ya fara nazarin mene ne dalilin da yasa rayuwarsa zata shiga ƙunci duk da yana ganin mahaifiyarsa zata samu sauƙi kuma ya samu Nostaljiya saboda haka ya samu komai. 


Armad ya gama karanta wannan littafin amma baiga komai ba. Ya ƙara duba na gabansa shima haka. Har saida yakai littafi na tara sannan ya tararda abinda yake nema.


Rubutun littafin manya-manya ne kuma anyi sune da hannu da tawada. 

***

A ɓangaren yamma da ruwan maliya ƙabilar Nára su suka fara ƙirƙiro abinda aka sani da IZZA. Su kuma ƙabilar Wilbafos su suka fara bautarda aljanu. Sarki Aldaima mai Hannun Aradu, mai zuciyar zaki, ya auri ƴar uwarsa daga ƙabilar Nara mai suna Jinaina Nara wanda suka kasance jikokin mutun ɗaya. 


Sarki Aldaima da Jinaina sun haifi ƴaƴa huɗu, ƴan biyu sau biyu, amma duk Jinaina ta kashe su da hannunta saboda an haifosu da baƙaƙen idanuwa. Kuma tun daga wannan basu ƙara haihuwa ba. Wanda hakan ke nuni da cewa ko ɗa ɗaya acikin ƴaƴaƴen sarki Aldaima bai rayu ba. Kuma lallai sarki Eyriyon ba halattaccen ɗan sarki Aldaima bane. Da dama daga cikin malamai sunce sarki Eƴriyon ƙanin sarki Aldaima ne. Babu wanda yasan gaskiyar wannan sai sarki Aldaima da sarki Eyriyon. Kuma hatta wannan sirri babu wanda ya sani sai Ururu da kuma wasu ƴan tsirari aban ƙasa.


Sarki Aldaima ya barwa sarki Eyriyon wasiyar kada ya auri ƴar ƙabilar Nara amma ƙaddara ta riga fata, shima saida ya aura daga ƙabilar Nara wata mace wadda aka bada labarin tafi kowa kyawun sura da ƙarfin izza aban ƙasa. Ana ce mata Madariyya Nara. 


Amma abin mamaki shi ma sarki Eyriyon ya fara haifar ƴaƴa masu baƙaƙen idanuwa. Madariyya da kanta ta ringa kashe su duk da kuwa sarki Eyriyon bai so hakan ba. 


Bayan an yanka ɗa na bakwai sai sarki Eyriyon ya daina haihuwa sannan kuma wani abin mamaki aka daina haifar maza a ƙabilar Nara. Lamarinda yasa dole sai matan ƙabilar sun fita wata ƙabilar sunyi aure. Amma kuma sarki Eyriyon da yawun sarauniya Madariyya suka hana duk wani aure tsakanin matan ƙabilar Nara da kowa a duniya.


A haka zamani bayan zamani ƴan wannan ƙabila mai Nára suka fara ƙarewa saboda rashin auratayya. Bayan shekaru dubu huɗu na mulkin Eyriyon saida ya rage babu kowa sai ƴan kaɗan. To amma kuma wani abin mamaki sai wannan kaɗan ɗin suka daina tsufa kwata-kwata. Babu wanda yasan mai yasa amma dai har ila yau wannan ƴan ƙabilar basa tsufa wanda hakan yasa basa mutuwa kamar sauran mutane. 


Amma bayan mutuwar Eyriyon sai ƙabilar Ururu suka ringa tursasawa matan ƙabilar Nara su aure su. Amma bisa mamaki duk auren da akai sai kaga an haifo wanda ba Ururu ba. Lamarinda yasa nan take Ururu suka daina airensu suka fara kashe su. Ƴan kaɗan ne daga cikin wannan ƙabila suka gudu suka ɓuya a ƙasashen ƙasa har Ururu suka gaji nema. 


Amma daga baya sai mutanen ƙasashen ƙasa suka fara farautar ragowar matan ƙabilar Nara, suna yi musu auran dole suna kashe su bayan sun haifi ƴaƴa. A cewar masu wannan mummunan abu wai indai ka auri ƴan ƙabilar to baza ka mutu ba. Wanda a zahiri ƙarya ne tunda ga Eyriyon ya mutu, Aldaima ma ya mutu.


Kaɗan ne suka tsira daga cikinsu, wanda suka ɓuya har yau babu wanda yasan inda suke.

*** 


Koda Armad yazo nan a karatunsa saiya gane haƙiƙanin abubuwan da suke faruwa. Lallai Nostaljiya Nára nada duk wani dalili da zaisa tayi masa abinda tayi masa. Jikinsa a sanyaye ya fito daga cikin ɗakin karatun ya samu su Iliyasis ya kwashe duk abinda ya faru ya gaya musu. Kuma ya nemi shawararsu akan abinda ya kamata ya aikata.

***


KWANA ƊAYA KAFIN WANNAN RANA

------

Da kyar bacci ya ɗauke Armad bayan fitar kwamanda Damjinu Djinn. Har Inara ya dawo bai sani ba saboda haka Inara ya yanke shawarar tsayawa a kansa gadi har ya tashi.


Sannu a hankali gari ya waye, Armad yayi niyyar fara koyawa Inara al'amuran Izza daga wannan rana. Amma wani mugun labari wanda bai taɓa tsammani ba ya iske shi.


Wata kuyanga ce mai yawan jan gashi kamar na Rafiyawa ta leƙo ɗakin bayan rana ta ɗaga ta ce, "shugaba Armad, Nostaljiya tace a gaya maka zata iso nan bada daɗewa ba."


Armad najin haka ya fashe da murmushi ya nufi bakin ƙofar domin ya ƙara jin abinda wannan kuyanga ta faɗa saboda farin ciki. Nan take ya ƙara yin wanka ya canja kaya ya fesa turare. Shi kansa bai taɓa tunanin zaiyi farin ciki irin wannan ba dan ance Nostaljiya tana nemansa. Amma gashi har ya wuce iyaka. 


Inara kawai murmushi yayi ya bawa Armad waje. 


Can bayan wasu daƙiƙu sai Armad yaji ana kwankwasa masa inda ya taso da sauri ya buɗe ƙofa. Amma maimakon yaga Nostaljiya sai yaga Hasanu. Armad ya haɗe gira yana mamakin abinda ya kawo Hasanu ɗakinsa a wannan lokaci. Amma kafin yai magana kawai sai yaga wasu mutun biyu a bayan Hasanu; ɗaya ƙatoto ɗaya kuma siriri rataye da takobi. 


Armad ya ƙara cika da murna. "Cokali, Iliyasis? Dama yau nake niyyar idan mun haɗu da Nostaljiya na nemi izininta na shigo daku fada."


Cokali yana yaƙe ya ce, "malan kawai ka shigo daula ka manta damu. Yau kwana nawa? Kazo kaga Nostaljiya ka..."


Armad yayi gyaran yanawa Cokali inkiya cewa Hasanu wan Nostaljiya ne. 


Hasanu yai murmushi ya juya yana cewa, "Kwamanda Damjinu ne ya ce na kawo maka su. An kama su suna ƙoƙarin haurowa fada."


"H..haurowa??" Iliyasis yai sauri ya tari numfashin Hasanu. "Kace dai munzo ƙofar fada muna tambaya ina Armad?"


Hasanu dai baice komai ba kawai ya wuce yana murmushi. Armad dasu Iliyasis suka rankaya izuwa cikin ɗakin. Armad ya kwashe duk abinda ya afku tun bayan zuwansa fada ya gaya musu. Sannan kuma ya gaya musu Nostaljiya na gabda ƙarasowa ɗakin.


Cokali ya zare ido cikin mamaki yana cewa, "Lallai kuwa zanso naga wannan halitta da ake iƙirarin tafi kowa kyawun sura a duniya ido da ido."


Iliyasis ya fashe da dariya yana cewa, "ai duk zana tan da kake yi a baya da sunan soyayya kuke dama baka taɓa ganinta ba?!"


Armad najin haka ya tuno da haɗuwarsu ta farko da Cokali yana zana surar Nostaljiya yana mata waƙa. Wai itace wadda yake so zai aura. A cewarsa Nostaljiya tafi son ɗan ƙaton yaro kamarsa kuma mai zatai da siririn mutun kamar Armad. 


Duk su ukun suka fashe da dariya inda Cokali ya zaro ɗaya daga cikin hotunan Nostaljiya da yake zanawa ya bawa Armad a matsayin kyauta. Nan take suka ci gaba da tattauna akan hanyoyin da zasu bi su nemo Nusi. Har Armad ya fara basu labarin abinda Ikenga ya gaya masa akan Nusi da kuma inda take sai suka ji an kwankwasa ƙofa. Sannan daga bisani wata sanyayyar murya mai ɗauke da nutsuwa ta biyo baya.


"Ni ce."


Armad ya gane muryar, nan take ya sanar dasu Cokali cewa Nostaljiya ce, kafin ya nufi ƙofa ya buɗe mata. Armad ya ɓoye zanen da Cokali ya bashi a bayansa yana jiran lokaci yayi ya bata amma a karo na farko yaga fuskar Nostaljiya babu annuri kwata-kwata. 


Koda Cokali da Iliyasis suka ga haka sai suka fasa gaisawa suka nufi ƙofa. Amma kafin su ƙarasa suka ji muryar ta a kunnensu.


"Na amince zan auri yarima Deniz Bizáya. Dani dakai labarinmu ya ƙare tunma kafin ya fara. Ina fata ka samu wadda... ta fini." 


Tun a farko muryarta take rawa amma tana zuwa ƙarshe saida kyar ta ƙarasa. Tana gamawa ta juya ta nufi ƙofa idanunta cike da kwalla. Zanen dake hannun Armad yayi masa nauyi, kowa kawai shiru yayi yana kallonta baki a buɗe sun rasa mai zasu ce.


Tsahon lokaci suna wannan hali har saida Nostaljiya ta ƙule sannan suka dawo hankalinsu. Amma kafin su fara cewa komai saiga kwamanda Damjinu ya shigo ɗakin. Inda ya miƙawa Armad katin shedar ɗakin karatu na daular baki ɗaya wanda ke zaune a tsakiyar birni. 


"Idan kana so kasan dalilin da yasa Nostaljiya ta yanke wannan shawara to kaje babban ɗakin karatu da wannan kati kayi bincike. Wataƙila ganin fasaharka ta sarki Eyriyon ce tasa ta canja shawara, duk da kuwa dama tasan kai ɗan ƙabilar Wilbafos ne. Amma kayi sani cewa duk abinda zaka gano sirri ne wanda kai kaɗai aka yadda ka sani."


Yana gama faɗar haka ya juya ya fice. Su kuwa nan take suka yanke shawarar su nufi babban ɗakin karatu domin ganewa idonsu maike faruwa. 


Wannan shi ne dalilin da yakai Armad da Inara dasu Iliyasis wannan ɗakin karatu.


***

Babi na 105: Shawarar Armad


Da Armad da Inara dasu Iliyasis suna tafe akan hanyarsu ta komawa fada kowa yayi shiru ba'a cewa komai. Dukkaninsu tausayin Armad kawai suke ji da kuma taya shi baƙin ciki amma shi kaɗai yasan mai yake ji. 


Koda suka iso bakin ƙofar ɗakin sai Iliyasis ya nemi zai fita daga fadar ya shiga gari domin yayi bincike akan abinda Armad ya gaya musu akan Nusi da kuma inda Ikenga ya ce take. Amma da farko ya nemi da Cokali ya zauna tare da Armad. Sai dai Armad ya nuna cewar hakan ba lallai bane. Saboda haka suka bar Inara da Armad suka shiga gari domin dama dai su abinda ya fito dasu daga gida kenan.


Armad ya shiga ɗaki ya kwanta akan gado ya rufe ido kamar yana bacci amma baccin yaƙi zuwa. Babu abinda yake sai tunanin shawarar da zai yanke. Dukkanin abokansa sun ƴadda cewa babu wanda zai iya yanke masa wannan hukunci sai shi kansa. Kuma duk hukuncin daya ɗauka zasu goya masa baya.


Sannu a hankali Armad yana ta kai-komo acikin kogon tunani sai kwatsam hasken alfijir yaga ya keto ta tagar dakin, gari ya fara wayewa. 


A wannan lokaci Armad ya tashi ya nufi wannan tafki dake bayan dakinsa yayi wanka sannan ya dawo ya canja kayan ya fice ya bar Inara yana bacci. Duk da dare ne amma tsaron cikin wannan fada yana nan kamar yadda yake. Fitilu na alfarma sun haskake duk inda ka hanga. Amma wannan ba matsala ba ce a wajen Armad Wilbafos, domin kuwa da sabuwar fasaharsa ta Kaban'shísu kawai ɓacewa zaiyi daga inda yake ya bayyana acan nesa ba tare da bayarda wani sauti ba. Lallai koda kyamera mai motsi aka saka baza ta iya hana Armad motsi ba. 


Kan kace meye wannan Armad da taimakon Kaban'shìsu ya bayyana a wannan fili da suka fafata da Kiru. Daga nan ya nufi katangar data kewaye gidajen ƴaƴan sarkin guda uku. Nan take ya ƙara amfani da Kaban'shísu ya bayyana a bayan katangar gidajen. 


Ya ƙara ɓacewa ya bayyana a kusa da gida na farko. Tuni Armad ya haddace yanayin-izzar jikin Nostaljiya. Saboda haka yasan indai tana ɗaya daga cikin gidajen uku yana matsawa zaiji ta. Ai kuwa haka akai, gida na farko babu kowa aciki, na biyu ma haka sai na uku yaji alamun yanayin izza aciki. Nan take Armad ya buɗe ƙofa ƴa shiga. 


Hatta ƙofar gidan da dinare da lu'u-lu'u aka gina ta. Cikin gidan kuwa duk da ragowar duhun dare amma sheƙi yake yana ƙanshi yana walwali irin na kyauwun yaƙutu da murjani. Nan take Armad ya raina kyawun gidan da aka kaishi.


Sai dai amma ba wannan ne a gaban Armad ba, duba wa kawai yayi ya gano ɗakin dake da ragowar fitila a kunne ya danna kai. 


Yana shiga ya iske Nostaljiya zaune a kan gado tana kallon ƙofar. Kafin yai magana ta buɗe baki ta ce, "amma dai kasan mahaifina yasan ka shigo nan ko. Koda ka kai nisan tafiyar shekara guda yakan iya jin yanayin-izzar mutun kuma ya gane waye ballantana daga nan zuwa inda yake tafiyar mintina ce."


Shiru kawai Armad yayi saboda duk da maganar da take bai hana kwalla zarya a idanunta ba. Hatta rigar jikinta ta jiƙe, lamarinda zai nuna maka ta ɗau lokaci tana wannan kuka. 


Armad yayi kamar baiji kashedin da tayi masa ba akan Bihanzin ya taka ya zauna a gefen gadon yana kallonta. Tsahon lokaci babu wanda ya ce wani abu acikinsu, kafin daga bisani Armad ya numfasa ya ce, "Bihanzin ba shi ne mahaifinki na haihuwa ba?"


Nostaljiya ta ɗago kai ta kalle shi ta gyaɗa kai a hankali tana kwalla. Nan take Armad ya gane haƙiƙanin dalilin da yasa babu wanda yasan ta da sunan Nostaljiya Nára sai ƴan uwanta. Kuma lallai akwai ƙololuwar yadda a tsakaninta dashi tunda ta gaya masa wannan suna tun a farkon haɗuwarsu. 


Da kyar Nostaljiya ta buɗe baki tace, "amma har kullum kuma har koda yaushe sarki Bihanzin shi ne mahaifina, a wannan rayuwar da kuma ta gaba. Tun ana farautar yan kabilar Nâra kamar namun daji Bihanzin ya ɗakko ni ya mai dani ƴarsa kuma ya bani sunan kabilarsa ya mai dani Zahra Sisiyu. Kaga babu abinda mahaifi zai yiwa ƴar wanda bai yimin ba. Hasalima nafi ƴaƴansa, Kiru da Hasanu, jin daɗi a masarautar nan tun muna yara bama yanzu ba."


Shiru kawai Armad yayi yana sauraro kafin daga bisani yai ajiyar zuciya ya ce, "ƴan ƙabilar Nára da ƴan ƙabilar Wilbafos sun kasance suna da kaka ɗaya kuma ina ganin hakan nema yasa a farkon haduwarmu dake idan jikinmu ya haɗu muke ji tamkar mun taɓa ganin juna. Musamman tunda akwai dogon tarihi a tsakanin mu."


Nostaljiya ta ɗanyi shiru tana tunanin lokacin da ta riƙe Armad zai faɗa rami. Da irin yanayin da taji na tamkar sun riga sun san juna. Gyaɗa kai kawai tayi tana mai yadda da abinda Armad ya faɗa. Musamman duba da cewa daga ƴan ƙabilar Wilbafos ɗin har ƴan ƙabilar Náran duk sun kusa ƙarewa a duniya.


Armad ya miƙe tsaye ya zagayo ya fuskanci Nostaljiya, idanunsa a cike da tsananin kafiya. Zuciyarsa a dake. 


"Ni Armad ina so zan aureki idan kin amince domin kuwa bazan yi miki dole ba. Amma kiyi sani cewa kakanni na, sarki Aldaima da sarki Eyriyon, sunyi mulki irin nasu. Kuma sun yanke hukunci irin nasu. Babu wanda yasan haƙiƙanin dalilin da yasa suka yanke hukuncin da suka yanke. Kuma koda ansan dalilin da yasa suka yanke hukuncin da suka yanke, wannan bai kai ya hana ni auranki ba. Hasalima tunda na riga na ɗarsa a ziciyata ina son zan aureki to lallai koda dukkan kabilun duniya zasu taru, matattunsu da rayayyunsu, ba zasu iya hanani auranki ba. Haihuwar yaro mai baƙin ido ko kuma mai ido ruwan ƙasa duk wannan wani abu ne daga baya, wanda kuma bazai hanani tarwatsa cinikin bayi ba aban ƙasa. 


"Ni Armad Wilbafos ɗan Taidara Wilbafos ɗan Zaikid Wilbafos nayi alƙwarin zan kawo kai da gangar jikin mafi girman abokin gabar mahaifinki Bihanzin a matsayin sadaki, koda kuwa sarkin Jinzidal ne. Sannan kuma zan tsaya na kare ki daga dukkan wani sharri da zai yiwo kanki har ranar da zanyi numfashina na karshe. Amma kiyi sani ke kaɗai ce zaki iya amincewa da wannan batu nawa na aure. Saboda haka zan jira amsarki nan da sati ɗaya. Naji labari ance nanda sati ɗayan yarima Bizaya zai kawo miki ziyara. Kiyi sani cewa koda baki zaɓe ni ba, ni zan ɗauki laifin abinda ya faru a wajen cinikin bayi a waccan shekara, sannan kuma bazan taɓa daina sonki ba da kuma yi miki fatan alkhairi."


Armad na zuwa nan a zancensa ya juya ya fice, Nostaljiya na kallonsa baki a buɗe tana mamaki. Lallai bata taɓa tsammanin Armad zai ɗau irin wannan alwashi ba.


***

Babi na 106: Itacen Aljanu


Bayan Armad ya dawo ɗaki ya jira Inara ya tashi daga bacci, sannan suka ci abinci suka rankaya izuwa kasuwar izza ta daular Sisiya. Armad yayi amfani da ƙaton hirami ya rufe fuskarsa tunda tuni sirrin daya canja masa kamanni ya daina aiki. Kuma duk da cewar acikin fada bashi matsala a waje duk wanda ya gane shi sai yayi ƙoƙarin miƙa shi.


Dama dai a wannan rana Armad ya shirya zai fara koyawa Inara al'amuran Izza. Suna isa suka tararda wani mai gadi sanye da fararen kaya wanda ya basu hanya ba tare da tangarɗa ba. Suka wuce can ciki izuwa wajenda ake siye da siyarwa na kayan izza na musamman.


Mutumin dake kan kantar gajere ne, fari mai yawan gashin gira. Yana ganinsu Armad ya leƙo ya ce, "me kuke so? Muna da kowanne irin kaya wanda suka haɗa da Alƙalamin aljanu, da hotar shaiɗanu, da farcen dordor da tamatirin Ururu, da itacen aljanu, da kashin aljanun-jemagu."


Armad ya amsa da cewa, "itacen-aljanu muke so guda biyu; na aljanin wuta dana aljanin walƙiya."


Mutumin ya duba cikin shagon domin ya tabbata yana dasu sannan ya waigo ya ce, "Ayrid ɗari-ɗari." 


Mutumin yana magana yana kallon hiramin Armad, a jikinsa yana ji kamar ya sanshi. Koda Armad yaga haka saiya juya da baya ya ƙara rufe fuskarsa musamman tunda daman bashi zai biya ba. Har izuwa wannan lokaci Armad baida ko sisi, a ransa yana ji lallai ya kamata ya fara tara kuɗi kodan biyan buƙatunsa.


Bayan sun sayi wannan itace na aljanu sai suka fice daga kasuwar suka koma fada. Suna zuwa basu zarce ko'ina ba sai filin horon dake cikin fadar. Tuni dai kwamanda Damjinu ya bada umarnin a bar Armad ya shiga kowanne ɓangare na wannan fada. Saboda haka basu da matsala.


Suna isa aka buɗe musu wajen suka shiga. Cikinsa ba wani mugun shiri akai masa ba, filaye ne kawai kala-kala kowanne a kewaye yake da dogon bango mai kaurin gaske. Sannan an kewaye wannan bangwaye da ɗalasimai wanda zasu ringa shanye ƙara da sauti suna hana su fita waje. Wannan dalili shi yasa duk girman fafatawar da za'ayi acikin waɗannan filaye ba lalle bane na waje yasan anayi ba.


Suna shiga Armad ya miƙawa Inara ɗaya daga cikin itacen aljanun dake hannunsa. Shi dai wannan ice ɗan ƙarami ne baifi girman ɗanyatsa ba. Jikinsa a sumulmule yake kamar an kankare. Amfaninsa shi ne gano girman aljanin da mutun ke dashi. Kamar yadda aka sani iya girman aljaninka iya girman izzar da zaka iya kaiwa. 


Dama Inara yasan sarai yadda zaiyi amfani da wannan itace, saboda haka yana karɓa ya samarda wata ƴar ƙaramar ƙawanya ta wuta a hannunsa sannan ya jefawa wannan itace ita. Suna haɗuwa itacen ya zuƙe wutar kamar babu ita, amma Inara baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙara cilla masa wata ƙawanyar. Yana zuƙewa sai Inara ya ƙara cilla masa wata. A haka har saida ɗan itacen ya zuƙe sama da ƙawanya talatin kafin daga bisani ya canja kala daga fari zuwa ja. A wannan lokaci Inara ya daina sawa itacen wutar ya tsaya kawai yana kallon itacen, shima Armad matsowa kusa yayi yana jira yaga mai zai faru.


Bayan ƴan daƙiƙu saiga lamba huɗu nan ta bayyana a jikin itacen da yaren Aldurish. Wanda hakan ke nuni da cewa iyakacin ƙarfin da aljanin Inara zai iya kaiwa shi ne mataki na huɗu daga cikin matakai shida na sarrafa wuta. Tsalle Inara yayi yana murna tamkar an masa bushara da aljanna, shi kuwa Armad kawai haɗe rai yayi babu ko alamun murmushi a fuskarsa. 


Bayan Inara ya gama murnarsa saiya fuskanci Armad bai aminta da wannan sakamako ba. Sabida haka nan take ya dube shi ya ce, "ya shugabana akwai matsala ne?"


Armad bai ɓoye wa Inara komai ba, kai tsaye ya ce, "kasan dai akwai matakai shida na alaƙa tsakanin aljanu da mutane. Mataki na shida shi ne yafi kowanne ƙarfi, amma kai kana mataki na huɗu kana murna. Kana tunanin zaka taɓa iya fafatawa da ma'aboci mataki na biyar ko shida? Koda yake kai burinka ka koyi al'amuran izza ka koma ka ci gaba da sana'arka ta tuƙa jirgi, banga laifinka ba. Amma kayi sani indai kana ɗalibi na to a kullum saiya zamana burinka ka taɓo ƙololuwa. Da haka ne kaɗai zanyi alfahari da kiranka ɗalibi na."


Armad na gama jawabi ya fito da takobinsa ya umarci Inara daya zare takobinsa su fara tun daga mataki na farko. Haka kuwa akai, a wannan rana ba'ai amfani da fasahar aljanu ba ko kaɗan. Zallar takobi ce kawai akai ta wasa da ita tsakanin Armad da Inara. Saida yamma tayi liƙis sannan Armad ya sallami Inara. Bayan ya tafi sai Armad ya fito da ragowar ɗaya itacen aljanun dake aljihunsa. Sannan ya fara zuba walƙiyar dake jikinsa aciki. 


Bayan ɗan lokaci sai itacen ya juye izuwa kore-kore. Sannan daga bisani lambar Armad ta fito a jiki. Amma maimakon Armad yaga lamba guda ɗaya sai yaga lamba shida-shida guda biyu. 


Armad bashi da aljani, kuma walƙiyarsa daga cikin jikinsa take fitowa sabida haka ba abin mamaki bane ya samu ƙololuwar mataki, wato mataki na shida. Amma abin mamakin shi ne lambobi guda biyu daya gani ajikin itacen. A iya saninsa bai taɓa jin faruwar hakan ba.


Yana cikin tunani ne sai ga Iliyasis da Cokali da Inara sun danno wajen. 


Cokali ne ya fara magana, "albishirinka. Akwai hanyarda zamu gano indai da gaske Nusi tana cikin sashin Ikwatora."


Armad ya zare ido cikin mamaki tare da yin sauri ya mayarda itacen dake hannunsa aljihu. "Mai kuke nufi? Yimin bayani."


Iliyasis yayi ajiyar numfashi sannan ya fara jawabi. "Akwai shalkwatar Ururu dake doron ƙasa na bakwai inda ake ajiye sunayen duk wanda suke sashin Ikwatora da kuma kurkukun dake cikin bango. Indai muka samu wannan suna ye to zamu gane ko da gaske Nusi tana cikin Ikwatora. Za kuma mu gane haƙiƙanin inda take da kuma mai take yi. Idan zaka je to saika ɗaura ɗamara domin kuwa gobe da asuba zamu bazama."


Armad yayi murmushin farin ciki sannan ya ce, "kuna tunanin akwai abinda zai hana ni nemo Nusi indai ina numfashi? Kada fa ku manta a dalili na ta ɓata. Gobe dani za'ai ɗamara zuwa doron ƙasa ta bakwai shalkawatar Ururu. Kawai dai dole sai mun gama samo wannan sunaye a cikin kwana shida. Domin kuwa inada alkawari da gimbiya Zahra nan da kwana bakwai. Kuma lallai koda matattu da rayayyu zasu haɗu baza su hanani dawo wa izuwa gare ta ba."


Cokali najin haka ya fashe da dariya. "Ah.. Lallai wani ya kamu."


Haka suka rankaya suna dariya izuwa ɗaki domin fara shirye-shirye. Idan suka isheshi da surutu sai Armad ya waiwayo ya dube su ya ce, "Duk wanda ya ƙara kiran sunan Nostaljiya bazai saka kayansa acikin zobe na ba. Sai dai ya riƙe a hannu!"


***

Babi na 107: Sabuwar Fasaha


Da safe Armad ne ya fara tashi. Kai tsaye ya fice daga ɗakin ya nufi sashin gimbiya Nostaljiya. Yana isowa yai amfani da Kaban'shísu ya bayyana acikin gidan. 


Dama dai tuni Nostaljiya taji tahowar Armad ta yanayin-izzarsa saboda haka tana tsaye a bakin ƙofa tana jiransa. 


"Sannu. Ka tashi lafiya." 


"Lafiya ƙalau. Ke fa?"


Nostaljiya ta ɗanyi shiru bata amsa ba, kafin daga bisani ta gƴaɗa kai alamun itama lafiya. Murmushi kawai Armad yayi yana gayawa kansa cewa yau da jan aji ta tashi bata son magana. Sannan ya ci gaba da cewa, "nazo na sanar dake zanyi tafiya amma zan dawo nanda kwana shida."


Nostaljiya ta dubi Armad cikin mamaki. "Tafiya? Lafiya?"


Ganin yadda hankalinta ke neman tashi Armad yai sauri ya bayyana mata duk abubuwan dake faruwa da kuma tsakaninsa da Nusi da kuma abinda Ikenga ya gaya masa akan Nusi.


Koda jin yadda tsakanin Armad da Nusi yake sai Nostaljiya tasan lallai babu yadda zata iya hana Armad. Saboda haka ta buɗe baki tace, "kwana shida, kada ka wuce haka. Sannan kuma kayi sani wajen da zaku je yana da matuƙar tsaro, shi ne muhallin da Ururu suke ajiye duk wani sirri na ƙasashen ƙasa. Shekarar data gabata aka naɗa Uznu Ururu a matsayin shugaban masu tsare wannan waje. Dole ne kuyi abinda zaku yi a nutse ba tare da kun ƙara tsokano Ururu ba."


Armad yayi murmushi ganin kulawar da ake masa. Kamar yayi godiya ko kuma yace wani abu dazai nuna soyayyarsa amma ya kasa cewa komai saboda haka kawai ya juya ya nufi ƙofa. Harya kusa ƙarasawa ya ƙara waiwayowa suka haɗa ido da Nostaljiya. Baice komai ba, ita ma bata ce komai ba ya juya ya tafi zuciyarsa tana dukan tara-tara. 


Yana komawa ɗaki Inara da Cokali da Iliyasis sun gama shiryawa shi kawai suke jira saboda haka suka ɗau hanya izuwa shalkwatar tafiye-tafiye ta Sisiya. Hanya ɗaya da zata kaisu doron ƙasa ta bakwai cikin ƙanƙanin lokaci ita ce ƙofar Eycigan. Saboda haka duk tsadarta haka zasu biya. Suna isa Iliyasis ya zaro Ayrid dubu sittin ya yankar musu tikiti, kowanne

ɗaya dubu sha biyar. 


Sannan aka shigar dasu wajenda matafiyan suke jira a layi. Saboda safiya da kuma cewar ba kowa ne ke iya amfani da Eycigan ɗin ba, babu mutane da yawa a wajen. Daga wani dattijo da iyalansa sai wasu maza huɗu da mata uku. 


Suna zama Cokali ya fara zancen yunwa yake ji, saboda haka Armad ya buɗe zobensa ya ɗebo masa ƴaƴan itatuwa. Har zuwa yanzu Iliyasis da Cokali basu yiwa Armad cikakken bayani akan wajenda zasu je ba. Amma wannan ba matsalar Armad bace. Yasan cewa komai wahala komai daɗi indai ya shafi Nusi to kamar yaje ya gama. Babban abinda yake ta kai-komo yana cimasa tuwo a kwarya shi ne wannan lambobi guda biyu daya gani a jikin itacen aljaninsa. Har izuwa wannan lokaci Armad bai san ma'anar hakan ba. Kuma yana ta kokwanton ya tambayi wani. 


Can dai suna zaune suna jira Armad ya kasa daurewa ya dube su ya ce, "shin kuwa akan samu wanda yake da lamba sama da ɗaya a jikin itacen aljaninsa?" 


Armad yayi iya ƙoƙarinsa ya saita muryarsa yayi tambayar azuwan kawai dai tambaya yake bawai dan yana da ita ba. Cokali da Inara kawai girgiza kai sukai alamar basu sani ba. Amma Iliyasis shiru yai tsahon lokaci yana tunani kafin daga bisani ya gyaɗa kai, "eh.. to. A mutane dai babu. Amma aljanu dama lamba biyu ce dasu."


Armad yai maza ya juya ɓangaren da Iliyasis yake ido a zare ya ce, "Aljanu kuma? Saboda me suke da lamba biyu?"


Iliyasis ya amsa da cewa, "saboda aljanu suna iya bawa wani fasaharsu kamar yadda suke bawa mutanenda suka bautarda su. Kaga lamba ɗaya tana nuni da shi aljanin, ɗaya kuma dashi mutumin."


Armad yaja wani dogon numfashi sannan yayi ajiyar zuciya ya ce, "ah to nagode da wannan bayani naka."


Acikin ran Armad tuni wata sabuwar fasaha dazai girgiza duniya da ita ta bayyana. Lallai idan har haka ne to kuwa shima zai iya arawa mutane fasaharsa ta walƙiya kamar yadda aljanu suke iya bayarda tasu. To amma babbar matsalarsa yaya zaiyi damai fasahar Kwangila ta walƙiya, wato sarki Deniz Iluru. Ko shi kaɗai da yake amfani da walƙiya ba tare da Kwangila ba idan sarki Deniz yaji labari bazai aminta ba, domin kuwa kamar ana nuna masa bai isa bane kuma ana rage masa ƙarfin mulki, to amma idan Armad ya fara bawa mutane fasaharsa ta walƙiya suna amfani da ita ba tare da Kwangila ba lallai sarki Deniz bazai yadda ba. 


To amma idan Armad ya cimma wannan manufa tasa lallai zai zama gagara badau, domin kuwa zai haɗa runduna tasa ta musamman wanda shi kaɗai sukewa biyayya.


Yana cikin tunani yaji muryar Iliyasis yana tambayarsa, "amma mai yasa kake tambaya? Ko ka fara bincike a fannin aljanu ne?"


Armad ya fara dubi-dubi yana neman amsar data fi dacewa sai aka kira sunansu suka rankaya izuwa ƙofar shiga. 


Shigarsu keda wuya suka tararda ƙofofi a jere har guda bakwai. Kowacce nada lamba akanta daga ɗaya zuwa bakwai. Cikin ƙofar ba'a hango komai sai duhu. Dama dai wannan ba shi ne karo na farko ba da Armad ya fara ganin wannan ƙofa ta Eycigan ba, suma kuma duk sun santa. Saboda haka kawai ƙarasawa sukai kai tsaye suka karɓi ɗalasiman daya kamata su karanta a hannun mai gadin dake tsaye a bakin ƙofar.


Kowa ya karanta saiya shige, har duk su huɗu suka shiga. 


Yana faɗawa ciki Armad yaji wani yanayi kamar ana hajijiya dashi. Lamarinda yasa saida ya rufe idonsa. Ana haka sai yaji wata iska mai ƙarfin gaske ta zuƙe shi ciki. Abu na gaba daya sani shi ne farkawa da yayi ya ganshi a bakin wata ƙofa irin wadda ya shiga sak. Ba daban sauyin yanayin da yake ji ba da ya ce ƙofar daya shiga ya dawo. To amma wani zafi ne ya daki fatarsa wanda lallai yasan babu shi a inda ya baro. 


Armad na cikin haka yaji muryar wani mutun a gefensa. "Barka da isowa doron ƙasa na bakwai, matafiyi."


Mutumin ba kowa bane illa ma'aikacin mai tsaron wannan ƙofa. Nan take ya miƙawa Armad ruwan sanyi da dabino sannan ya nuna masa wajen zama. Da farko Armad baiyi niyyar zama ba amma saiya hango abokan tafiyarsa akan kujeru suna cin dabino suna korawa da ruwa. Ga dukkan alamu sun rigashi zuwa.


Armad ya ƙarasa ya zauna. Sai bayan ya zauna yasha ruwa sannan ya lura cewa acikin ƙatoton waje suke wanda aka kewaye da gilashi kuma aka ƙawata domin saukar baƙi. 


Duk wanan bashi ne ya damu Armad ba. Can dai Armad yayi niyyar tambaya amma Iliyasis ya rigashi da fara jawabi. "Tunda mun ƙaraso bari na fara gaya muku abubuwanda muke buƙata da kuma hatsarin wannan aiki namu. Amma mubar nan wajen saboda tsaro."


***

Babi na 108: Ƴantattun-mutane


Duniya nada girman gaske. Banda ɓangarori da sarakunan Jinzidal ke mulka a ƙasashen kasa akwai da dama na garuruwa da ƙasashe wanda basa ƙarƙashin mulkin kowa. Irin wannan garuruwa su ake kira da Ƴantattun-dauloli. Mutanen cikinsu kuma Ƴantattun-mutane.


A sau da dama zaka samu kowanne gari yana da shugabanninsa wanda su kaɗai keda cewa a garin. Amma duk da haka irin waɗannan shugabanni kawai suna hana tarzoma ne da kuma zalinci a tsakanin ƴan ƙasar amma babu wata ƙa'ida ko kuma wani ƙarfin mulki. Kowa yana da damar yayi mubayi'a ga duk wanda yaso. A saboda haka zaka samu wasu daga Ƴantattun-mutane suna biyayya ga gidan Ururu wasu kuma sauran gidaje. Kowa dai yana da damar yayi abinda yaga dana.


A ɗaya daga cikin irin wannan dauloli dake kudu da Ikwatora a doron ƙasa na uku wani taro ne ke kasancewa tsakanin wasu mutane a cikin wani ɗaki.


Mutane ne da dama dukkaninsu suna zaune akan tebura su na fuskantar wasu mutane guda biyu dake tsaye a gabansu fuskoki a rufe da hirami. Kayan jikinsu daban-daban ne wanda hakan zai nuna maka kowa daga gari daban yake. Bayan mutanen dake zaune akan tebura akwai wasu a tsattsaye riƙe da makamai su na gadin wannan mutane. 


Ɗaya daga cikin mutanen dake zaune ya ja dogon gemunsa rai a ɓace ya fara jawabi, "har yanzu baka bamu dalili guda ɗaya da zaisa mu bika ba. Sama da shekaru dubu mu ƴantattun mutane mun zaɓi muyi rayuwa ba'a ƙarƙashin kowa. Kuma muna jin daɗin rayuwarmu a haka babu ruwanmu da yaƙin kowacce ƙabila. Abinda ya shafemu shi ne namu, wanda bai shafemu ba babu ruwanmu. A wanne dalili zaka zo rana tsaka ka nemi muyi maka mubayi'a. Bamu kwakkwaran dalili ɗaya wanda zaisa karmu yanke maka hukunci saboda ka taso mu daga garuruwan mu ka hana mu harkokin mu akan wannan maganar banzar."


Mutumin na rufe baki yakai hannunsa kan takobinsa, su kuwa sauran mutanen dake kewaye dashi suka fara ƙus-ƙus cikin murya mai kaushi wadda koda baka ji mai suke cewa ba kasan sun amince da abinda mai gemun ya faɗa kuma zasu yankewa wannan mutun dake nema suyi masa mubayi'a hukunci indai bai basu wani kwakkwaran dalili ba.


Ana cikin haka sai wannan mutane guda biyu suka cire hular fulanin dake kansu sannan suka kwance hiramin da suka naɗe fuskarsu dashi. Na daman ba wani bane illa Ikenga O Bayajidda wanda aka fi sani da ɗan-baiwa. Na hagun kuma babban hadiminsa ne wanda aka fi sani da Kána.


"K...kai ne..." Muryar mutanen dake zaune ce ta fara tashi cikin ƙinƙina suna mamakin ganin Ikenga. Kowa dai yasan wani abu daga cikin tarihin Ikenga da yadda aka halaka garinsu tun yana ƙarami. Amma da dama basu taɓa ganin Ikenga ba sai a hoton jarida. Shima hakan ya faru ne sakamakon kasancewar Ikenga mutun na biyu da aka sakawa kuɗi bayan Armad. 


Dama dai al'umma an daɗe ana mamakin dalilin da yasa ba'a sakawa Ikenga kuɗi ba. Musamman duba ga cewa iyayensa da dukkan mutanen garinsu ƴan tawaye ne, kuma dalilin tawayensu ga rukunan Ururu shi ne yasa Ashuran Ururu da kansu suka sakko ƙasa suka dulmiyar dasu. To amma bisa mamaki bayan Ikenga yaƙi mutuwa duk da kibbau da masu da aka harbe shi dasu basu saka masa kuɗi ba a lokacin. Kowa yayi tunanin tun Ikenga yana yaro Ururu zasu fara farautarsa amma bisa mamaki akai shiru da maganar. Har yau babu wanda yasan yadda Ikenga ya rayu, kuma babu wanda yasan dalilin da yasa Ururu basu sanya kuɗi akansa ba tun a wannan lokaci. 


Akwai dalilai da dama da suka jawo wancan yaƙi daya haɗiye garin su Ikenga. Wanda kuma shi ne yaƙin daya jawo rashin lafiyar mahaifiyar Armad. To amma wannan dalilai kaɗai Ururu da kuma wanda suka fafata a wannan yaƙi ne suka sansu. Abinda kawai ake gayawa mutane shi ne ƴan tawaye ne suka nemi su kawo wa zaman lafiya tangarɗa shi yasa Ururu suka sakko suka halaka su. Amma da dama sun san akwai wata maganar a ƙasa, dole akwai wani sirri wanda ba'a so mutane su sani wanda girmansa har yasa Ashuran Ururu da kansu su sauka.


Shi kansa Ikenga bai san wannan sirri ba. Abu ɗaya dai daya sani shi ne Ururu sune suka kashe mahaifansa da kuma mutanen garinsu. Saboda haka saiya ɗau fansa akan Ururu. Koma dai meye dalilin da yasa Ururu suka aikata abinda suka aikata Ikenga yasan cewa saboda su kare ƙalfin mulkinsu ne. Saboda haka ya ɗau alƙawarin sai ya hau har sama doron ƙasa ta farko inda suke ya tumɓuke su daga kan karagoginsu da suke mulki. Sannan ya kashe su da hannunsa ya ɗau fansar abinda sukai masa. To amma shima yasan yaƙar Ururu babban al'amari ne wanda yake buƙatar shiri. Wannan shi ne yasa a kullum kuma a kodayaushe ɗan-baiwa acikin shiri yake.


Gyaran murya kawai Ikenga yayi sannan yayi murmushi ya fara jawabi. "Shekaru dubunnai kafin a gina ƙasashen ƙasa ai kuma ƴantattun mutane ba haka kuke rayuwa ba. Tarihi ya nuna cewa kun kasance a ƙarƙashin daulolin sarakunan Wilbafos. To amma sarakunan Wilbafos basuda ƙarfin da za su kare ku, hakan nema yasa Ururu suka ci galaba akansu suka watso ku ƙasashen ƙasa. Wanda daga nan ne iyayenku da kakanninku suka yanke shawarar daina biyayya. Harma kuka kafa garuruwanku na Ƴantattu-mutane. 


"Bayan ƙarewar wancan yaƙi wasu daga cikin iyalan gidan Wilbafos basu mutu ba, kuma sun ci gaba da rayuwa daku a ƙasashen ƙasa a lokacin da kuke shan wahala amma a matsayinsu na shugabanninku basu fito sun cece kuba. Mahaifina shi ne mutun na farko daya fara haɗa kan Ƴantattu yana so ya dawo da martabar tsohuwar daular da zata yaƙi rukunan Ururu, kuma wasu daga cikinku sunyi masa mubayi'a. To amma duk da haka wannan iyalai na gidan Wilbafos da suka rage suka ƙi bayyana kansu su taimake ku. Kuma a ƙarshe ma abin kunya dasu aka haɗa baki aka halakar da al'umma ta. 


"Ko a watan daya gabata saida na nemi ɗaya daga cikin irin wannan ragowar ƴaƴan gidan Wilbafos da suka rage yazo ayi wanann tafiya dashi amma yaƙi. Har yanzu zuciyoyinsu suna cike da tsoron Ururu, hatta sunan ƙabilarsu ma ɓoye shi suke. Ɗan ƙabilar Wilbafos yana tsoro ya bayyana sunansa na Wilbafos saboda tsoron Ururu. 


"Ni Ikenga Bayajidda ƙabila ta tsohuwa ce tun kafin daular Ururu. Kuma tunda muke bamu taɓa biyayya ga Ururu ba kuma bamu taɓa tsoronsu ba. Tuni na gano hanyar dazan mallaki dukkan sashin Ikwatora da kuma kurkukun dake cikin bango. Daga nan kuma zan haɗa runduna irin wacca ba'a taɓa gani ba a duniya kuma da ita ne zan yaƙi Ururu. 


"A taƙaice ina nuna muku ni Bayajidda ni ne wanda ya kamata kuyi wa mubayi'a ba Wilbafos ba."

Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...