Kalman yana kwance kan kujera yana jinyar ciwon dake ƙafarsa, wanda tuni ya zama gyanbo, ya jiyo an buɗe kofar ƙaton gidan. Banda ciwo akwai gajiya wadda ta samo asali daga korar yara daya wuni yana yi. An wayi gari tun sanda ma'aikatan tsaro suka bayyana iyalan Wilbafos a matsayin ƴan'tawaye shikenan mutanen ƙauyen Kanyu suka takurawa gidan. Yawanci sukan labe suyi jifa wanda ta haka suka fasa tagogin gidan baki ɗaya. Wataran kuma haurowa suke amma iyakacin su farfajiyar gidan inda bishiyoyin ɗorawar suke. Da zarar sun tsinki ɗorawa sai su buɗe ƙofar shiga ta cikin gidan su gudu. To amma yau abin mamaki duk da ba'a iya buɗe ƙofar ta waje (saboda izzar dake jikinta) amma yaran sun buɗe kuma sun shigo.
Ya yunkura zai miƙe domin ya leƙa ya gano su waye amma yana motsawa ƙashin bayansa ya amsa, dama ya daɗe yana ciwo. Dolensa ya koma ya kwanta. A halin da yake ciki koma waye yazo dole haka zai hakura ya kalle su.
Mutun na farko daya fara shigowa falon namiji ne dogo baƙi yana ɗauke da takobi a hannu. Baiyi kama da barayi ba, to amma meye ya kawo shi idan ba sata yazo ba?
Kalman na zaune yana lissafa mai ya kamata yayi sai yaga mutumin ya ɗagawa na bayansa hannu. Ba jimawa suka ƙaraso inda ya iske mutun goma sha huɗu: sha-biyu maza, biyu mata.
Macen ta ƙarasa wajen da yake ta durkusa a gaban sa. Da kyar ya iya muskutawa ya tashi zaune.
"Idan sata kuka zo to ku sani kun makaro... *Tari.*Tari.*" Yana cikin magana tari ya ɗebe shi, sai da ya ɗebi minti guda yana abu ɗaya kafin daga bisani ya tsagaita. Duk tarin da yayi sai kaga ɗiso-ɗison jini yana fita daga bakinsa. Can bayan ya tsagaita ya numfasa ya ce, "wasu sun riga ku." Ya nuna cikin ɗakin da ɗan'yatsa.
A lokacin macen da sauran ƴan'uwanta suka fuskanci an sace komai acikin falon. Ƴan abubuwan da aka bari basu wuce tebura da sauran abubuwan da baza suyi amfani ba irin su ƙarafa da kwanuka da sauransu.
"Kalman?" Macen ta tambaye shi da murya mai taushi.
Ya yamutse fuska yana mamakin yadda wannan ɓarauniya ta san sunansa.
"Suna na Nusi, ƴar'uwar Armad Wilbafos." Inji macen.
Ya yamutse fuska. Wane irin ƴar'uwar Armad kuma? Shin Armad yana da wata ƴar'uwar banda Hidaya?
"Armad yazo gida? Shi muke nema." Inji ta.
Kalman najin haka yayi wani murmushin baƙin ciki. Dama yasan sauran zancen kenan. Irin arnan dajin nan ne masu neman kuɗin da aka saka akan Armad, ko kuma mayaƙan Ururu ko na sarakunan jinzidal wanda aka turo gida su nemi Armad. Abinda basu sani ba shi ne koda Kalman yasan inda Armad yake bashi da niyar gaya musu koda zasu kashe shi.
Ya amsa mata da cewa, "bai zo ba."
Macen mai suna Nusi tayi ajiyar zuciya idanu cike da fargaba. Bayan ɗan lokaci ta saka hannunta akan ciwon dake ƙafarsa. Nan take yaji ciwon ya ɗau ɗumi. Kan kace meye wannan tsoka ta fara fitowa tana haɗewa da juna. Fata ta fito ta rufe ciwon sannan komai ya dawo dai-dai.
Macen ta miƙe ta juya ta fuskanci mutanen dake bayanta tana cewa, "bamu da lokacin ɓatawa amma dole a raya wannan gida. Su waye acikinku zasu zauna su kularmin da wannan gida mai albarka?"
Nan fa mutanan sukai shiru suna kallon-kallo. Ganin babu wanda ya bata amsa sai ta zabura ta zaɓi mutun tara acikinsu sannan ta juya ta dubi Kalman. "Wannan mutun tara mutane na ne na amana. Ina so ka basu haɗin kai su tayaka kula da wannan gidan har zuwa sanda zan dawo da Armad gida. Nasan baka da wata hanya ko kuma wani dalili da zai sa ka yadda dani, to amma a zahiri ni yaya ce a wajen Armad duk kuwa da bamu haɗa jini dashi ba. Kalman, ina fatan ALLAH ya haɗa fuskokin mu a gaba."
Da wannan ta juyo ta fice. Ragowar mutun shidan data ware suka bi bayanta. Su kuma mutun taran data zaba tun farko suka tsaya a falon suna kallon Kalman. Duk abubuwan dake faruwa kamar a mafarki Kalman yake ganinsu. Shi dai bai taɓa gani ko jin labarin wannan mace ba. To amma ga dukkan alamu ba mugunta ce ta kawo taba, duk da zata iya yiwuwa ƴan-leken asiri ta bari. To amma babu yadda zaiyi domin bashi da izzar faɗa da wannan tawaga. Idan idonsa gaskiya yake gani to kowanne ɗaya acikinsu yakai Sammai. Kaga kuwa bashi da yadda zaiyi, dolensa ya zauna dasu a gida ɗaya. Daɗin abin kawai babu wata alama data nuna suna da niyyar cutar dashi.
Bayan fitar macen da sauran mutun shidan sai ragowar mutun taran da aka bari suka fara shara suna ƙoƙarin gyara gidan. Wannan shi ake cewa ikon ALLAH sai kallo.
***
Bari mu koma ƙarƙashin ƙasa, dai-dai gaɓar garin Seerish na sarki Iluru.
Ginad wanda aka fi sani da B. Ururu ya shafa cikinsa inda wani kululu ya fito. Tabbas yana tunanin tsinannan baƙin basamuden nan ya fasa masa wani abu aciki. Ɗan daɗin kawai da yake ji shi ne ba shi kaɗai aka tafka ba. Akwai wani ƙatoton basamude a gefensa mai bakaken idanu wanda shima fuskarsa da jikinsa duk a nade suke da bandeji. Sunansa Deniz Curu-curu. Ga wasu tsoffi guda biyu a gefensa wanda suma duk hakan take. Ɗaya sunansa Kána, ɗaya kuma Daddara.
A dai-dai wannan lokaci dukkaninsu suna tsaye a ƙofar shiga garin.
Babu abinda yake kai-komo a zuciyar dattijo Kána sai wani baƙin basamude mai ƙaho a goshi dake gefensa. Abinda yafi konawa Kána rai shi ne babu ko gwarzane a jikin baƙin basamuden. Fuskarsa kawai sheki take tana bada yanayin izza da kwanciyar hankali. Dama can saida ya gayawa Ikenga cewa ƙaraiƙisu matsala zai zamar musu kada a jawo shi cikin tafiyar. Yanzu gashi daga ɓatan Ikenga ko awa ba'ai ba amma ƙaraiƙisu yayi juyin mulki. Dole yasan yadda zaiyi yayi maganinsa kafin wani abin ya faru wanda zasu yi dana sani.
Kamar ƙaraiƙisu yaji abinda yake tunani ya juya ya harare shi. Kána ya ɗauke kai ya kalli gefe. Wato idan a fafatawarsu ta baya wadda sukai a sashin ikwatora a lokacin gasar cin ruhin deba ance shammatarsu ƙaraiƙisu yayi to a yanzu babu zancen shammata. Ƙarfi kawai aka gwada. Duk su huɗun suka tarar masa amma basu yi masa ko kwarzane ba. Gashi yayi musu jina-jina. A ganin Kána babu wanda yakai ƙaraiƙisu karfi a ban ƙasa indai zancen dantse ake. Sai dai kuma idan fasaha za'ace, amma indai dantse ake zance yafi karfin kowa.
Ƙaraiƙisu yayi gyaran murya ya fara bayani da cewa, "a halin yanzu mun samu fahimtar juna tunda kowa ya yadda ni ne shugaban wannan tafiya. Idan kuma akwai mai magana to yayi kafin lokaci ya ƙure."
Sukai shiru. Ƙaraiƙisu yayi murmushi sannan ya shige gaba zuwa cikin garin suka bishi a baya. Suna isa wajen masu gadin suka nuna katin shiga inda ba tare da wata tangarda ba aka barsu suka wuce.
"Kai tsaye zansa Ayubu ya karya asirin da aka yi muku sannan kuma daga nan zamu wuce sashi na - wato ikwatora - inda zanci gaba da mulki." Inji ƙaraiƙisu.
Ginad yayi farat ya ce, "wai mai kake nufi ne? Kwata-kwata ma baka maganar nemo Ikenga."
Ƙaraiƙisu ya yamutse fuska ya harare shi. "To akan me zamu je nemansa? Sai kace wani jariri? Idan ya mutu shi ya juyo domin kuwa lalacinsa da rashin kwazonsa yasa ya mutu. Kuma abu guda da kuka kasa ganewa shi ne nifa ba bawan Ikenga bane kamar ku, haɗaka mukai dani dashi."
Kána ya kasa daurewa ya dubi ƙaraiƙisu a fusace ya ce, "haɗaka kuma? Sabida kaga bayanan shi yasa kake faɗar haka?"
Ƙaraiƙisu ya girgiza kai. "Ba haka bane. Ranar da naga fasahar Ikenga ta lokaci a ranar na aminta cewa shi ne wanda muke jira, shi ne wanda zai kai mu sama doron ƙasa ta farko. To amma ga dukkan alamu kuskure nayi wajen yin mubaya'a da wuri. A ɗan lokacin da muka zauna dashi na gano cewa bai kai matsayin nayi masa mubaya'a ba, sai dai muyi haɗaka dashi ko kuma yayi min mubaya'a. Kuma wannan faɗan nasa da Armad ya ƙara tabbatar min da haka. Kuna tunanin zanci gaba da bin wanda bazai iya nasara akan yara ba?"
"To idan haka ne mai yasa har yanzu kake tare damu?" Inji dattijo Daddara. "Ai tunda baka tafiyar sai kayi naka waje."
"Akwai abinda nake nema kuma idan kayi shiru kayi haƙuri zaka gani."
Da wannan suka wuce cikin gari wajen Ayubu.
***
Bari mu koma ɓangaren Nostaljiya.
Ɗakin otal ɗin ya ɗau zafi. Babu mai cewa uffan acikinsu. Armad yana zaune akan gado ya tankwashe ƙafarsa, ido a rufe yana tunani. Nostaljiya tana ta kai-komo daga wannan bango zuwa wannan. Inara da Lamarudu sun haɗa kai da gwiwa suna ta jimami. Tabbas tafiyar Nusi da Cokali ba ƙaramar matsala bace. Ka ɗauke ta taimakon ƙarfin yaƙi da zasu iya bayarwa, akwai abota wadda ta juye ta zama ƴan'uwantaka ba tare da ma sun sani ba. Ita ma Nostaljiya da suke cacar baki da Nusi ranta a ɓace yake ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tabbas tasan ita ce akan gaskiya domin ko kokwanto babu a ranta Armad ne a gabanta. Tayi amfani da fasaharta mafi girma wadda kuma ta nuna mata lallai Armad ne. Banda kuma wasu hanyoyi da tayi amfani dasu na dabarun yau da kullum na mata wanda suka ƙara nuna mata hakan. Dole Nusi ce ba akan gaskiya ba, to amma meye yasa take jin nauyi a zuciyarta? Irin nauyin nan na mai laifi wanda mutun yake ji idan ya aikata mummunan zunubi.
Ta ƙara kallon Armad a karo na arba'in ta ƙura masa ido amma duk da haka ita dai har tsakaninta da mahaliccinta tasan Armanos ne a gabanta. ALLAH sarki.
Bayan ɗan lokaci ta ajiye duk wani kewaye-kewaye a gefe ta danna cikin kwakwalwar Armad a wani salo na bazata. Armad ya buɗe ido da sauri tare da cije haƙora saboda zafin da yaji a kansa, amma kuma duk da haka baiyi ƙoƙarin hanata ba. Hasalima komawa yayi ya zauna ya rufe ido, ƙafafunsa a tankwashe.
Babu wani saƙo da loko da bata duba ba amma babu wani alamu dake nuna ba Armad bane a gabanta. To amma kuma duk da haka tana jin wannan nauyi na laifi a ranta. Meye haka? Mai yasa take jin haka? Mai yake faruwa da ita?
Fuska a yamutse ta nemi waje a can ƙuryar ɗakin ta zauna ta rufe ido.
Awa guda bayan zamanta suka ji ana kwankwasa ƙofar ɗakin da suke ciki. Su dai babu wanda suka aika kuma babu wanda yasan suna nan ballantana a kwankwasa musu kofa. Kai tsaye kowa acikinsu ya miƙe ya kai hannunsa kan makaminsa. Abinda ya ƙara sawa suka sha jinin jikinsu shi ne duk cikinsu babu wanda baya amfani da yanayin izza, to amma kuma duk da haka basa iya jin izzar wanda ke bakin ƙofar. Kodai gama-garin mutane ne wanda basu da izza, ko kuma maɗaukaka a fadar izza wanda suke iya ɓoye izzarsu.
Su huɗun suka bi layi suka tsaya a bakin ƙofar. Armad ya shige gaba ya buɗe ƙofar ba tare da tambayar waye ba.
Abin mamaki wasu tsoffi ne guda biyu tsaye suna jira. Akwai alamun ciwuka a jikin su amma babu bandeji wanda hakan ke nuna kodai ciwon ya fara warkewa ko kuma ƙaramin ciwo ne. Idan ka lura sosai zaka hangi wani ɗan yaro a gefensu daga ɓangaren dama. Duk inda ka duba a jikin wannan yaro bandeji ne caɓa-caɓa.
"Suna na Kána Wilbafos." Inji ɗaya daga cikin tsoffin, sannan ya nuna ɗaya tsohon ya ce, "wannan kuma shi ne Dádara Bayajidda. Wancan yaron kuma sunansa Ginad." Daga nan sai yaja bakinsa yayi shiru suka ci gaba da kallon kallo. Kai kace yana tsammanin sunansu daya fada yayi bayanin komai.
Nostaljiya ta yamutse fuska. Zaka iya cewa duk babu wanda bata gani ba a ƴan watannin baya sanda babban sarkin ikwatora yayi jifa dasu zuwa kurkukun bango.
"Kai ne Wilbafos ɗin dake tare da Ikenga?"
Tsohon da yayi magana ya gyaɗa kai. "Ni ne."
Nan take Lamarudu da Inara suka kai hannunsu kan takubbansu. Ita kuma Nostaljiya ta buɗe ƙarfin fasaharta ta tunani baki ɗaya ta miƙa ta kan Kána cikin shirin kota-kwana. Armad kuma ya zare takobin ɗorawa ya nuna su da tsininta ita.
Kána yayi murmushi tare da girgiza kai. Ya buɗe baki zaiyi magana amma kawai sai wani baƙin basamude ya leƙo daga sama. Ga dukkan alamu wannan basamude yana kan soro yana sauraren duk abinda ke faruwa. Abin tambayar anan shi ne: yaushe har ya hau saman basu ji ba? Kuma yaushe har suka zo aka zagaye gidan basu ji alamu ba?
"Muna da abubuwan yi da yawa." Inji baƙin basamuden. Wanda zuwa yanzu duk sun gane waye. Hasalima wannan baƙin basamude mai ƙaho a goshi shi ne wanda yayi cilli dasu Kána cikin kurkukun bango. Idan zata iya tunawa sunansa ƙaraiƙisu.
Ƙaraiƙisu ya yamutse fuska jin basu bashi amsa ba. A fusace ya diro ƙasa. Wajen daya dira yayi ƙara kamar zai dare gida biyu. Ya miƙa hannu ya nuna Armad ya ce, "kai Ayubu, ya kake nema ka mai damu ƙananun mutane ne? Tunda munzo kuma ai sai ka kawo gaisuwa a daina wani ɓoye ɓoye."
"A...Ayubu?"
Nostaljiya taji kamar an zira mata narkakken ƙarfe aciki. Wani gumi mai tsananin zafi ya fara kwaranya daga fuskarta da sauran bangarori na jikinta. Idanunta suka kada sukai jajawur suka fiffito.
Ta buɗe baki zatai magana amma ta kasa. "...."
Ba ita kaɗai ba, hatta su Inara da Lamarudu maganar tayi musu nauyi sama da tunaninsu. Ayubu kuma? Ayubu ba yana can an tura shi kula da doron ƙasa ta biyu ba?
Ita dai Nostaljiya tana tsaye tsam ta kasa motsawa. Ta kasa juyawa ta kalli Ayubu. Jikinta ya ƙame ƙam ya kasa motsi.
Ƙaraiƙisu ya daka masa tsawa. "Kai, Ayubu, wai ba magana ake maka ba?"
Ayubu yayi tsaki ƙasa-ƙasa amma baice komai ba. Kawai tsalle yayi ya dawo ɓangaren su ƙaraiƙisu.
"To tunda yanzu mun fuskanci juna sai mu ƙarasa wajen asirin da akai mu karya shi domin kowa ya koma harkokin gabansa. Koya kuka ce?" Inji ƙaraiƙisu yana shafa dogon ƙahon dake goshin sa.
Nostaljiya na tsaye ta kasa motsi. Wai mai yake faruwa ne? Shin ana so ace mata ba Armad bane? To idan ba Armad bane dawa ta kwanta kenan...? Wani tari ya taso mata ba shiri, yana fitowa sai ga wani baƙin jini daga cikinta. Baƙin ciki yasa wani abin ya fashe acikinta.
Da kyar ta ɗaga hannunta ta nuna shi da wani irin kallo na tsana wanda aka daɗe ba'a yiwa wani mahaluki shi ba a ban ƙasa. Zaka iya cewa ko iyayenka mutun ya kashe a gabanka iyakacin tsanar da zaka iya yi masa kenan.
Kafin tayi magana Ayubu yayi farat ya ce, "kada ki zarge ni. Zaɓi aka bani: dana zauna Armad ya kashe ni ya dawo da Hidaya ina ji ina gani, da kuma na bi Ikenga nayi amfani dake na rayu a matsayin Sarki tsahon shekaru dubu masu zuwa. Idan kece wanne zaki zaba? Ina son Armad amma kuma nafi son kaina sama da shi. Kada kiga laifina?"
Nostaljiya ta rufe bakinta ta fasa maganar domin a halin yanzu babu abinda zata ce. Kawai dama so take taji daga bakinsa. Ragowar hukunci ne kawai zai biyo baya.
Ƙaraiƙisu ya kalli Ayubu ta gefen ido amma baice komai ba. Ya juya wajen su Kána ya ce, "ku daure mana su muyi sauri mu ƙarasa, babu lokacin ɓatawa."
Ayubu da Kána da Ginad da Dádara suka afkawa su Nostaljiya.
***
Awa guda bayan wannan al'amari ya faru, a dajin ramuka wanda ke doron ƙasa ta huɗu dai-dai inda ake shiga garin Seerish na daular denizawa, wasu mutune ne kimanin dubu da doriya suna zauna akan wani faifan haske. Idan ka lura zaka ga kowanne faifai a dai-dai saitin saman rami ɗaya yake. Banda waɗannan akwai wasu mutun tara a gefe: uku a ɗaure, shida a sake. Na ɗauren suna ganin duk abinda ke faruwa amma ankokin baƙin ƙarfen da akai wa ado da farar-laya sun hanasu motsi. Daga cikin mutun shidan ɗaya a kwance yake a sume, ɗaya kuma yana kula dashi, sai kuma ragowar huɗun suna gefe a gaban wani rami mai lamba ta 1000 suna zana wasu alkaluma akan wani hatimi dake zagaye da ramin. Idan ka lura zaka ga ba wasu bane illa su ƙaraiƙisu. Shi kuma mutumin dake kwance a sume sarki Iluru ne da ɗansa Bizaya yana kula dashi (ga dukkan alamu har yanzu bai farfaɗo daga aikin da Armad yayi masa ba). Su kuma na ɗauren su Nostaljiya ne.
Bayan tsahon lokaci su ƙaraiƙisu suka kammala zanen dalasimin, sannan kowanne ɗaya daga cikinsu ya hau kan kusurwa ɗaya ta hatimin (tunda daman kusurwa huɗu ce dashi), suka fara kiran manyan ɗalasimai. Sai da suka shafe awa biyu suna yi sannan suka sakko suka dawo wajen Iluru.
Ginad ya nuna Iluru da ɗan'yatsa ya ce, "wai mai zamu yi dashi idan bai farka ba?"
Bizaya ya harareshi.
A gefe guda kuma Ƙaraiƙisu murmushi yayi, sannan kafin kowa ya ankara ya ɓace daga inda yake ya bayyana a gaban Iluru. Kafin Bizaya yayi wani abu dunkulallen hannun ƙaraiƙisu ya sauka akan fuskar Iluru. Wata iska mai ƙarfin gaske ta tashi tayi jifa da Bizaya gefe. Suma su Nostaljiya dake ɗaure bata barsu a baya ba sai da tayi cilli dasu can nesa. Kai hatta su Kána da Dádara da Ginad sai da suka kare fuskokinsu da hannayensu. Duk wannan kawai naushi ɗaya ne kurum. Idan ka lura zaka ga fuskar Iluru ta koma ciki. Baka iya banbance hanci ko ido ko baki, komai ya haɗe guri guda. Wata muguwar atishawa ta kwace masa. Ai kuwa yana yin atishawar ya mike yana muzurai.
Ƙaraiƙisu ya gyada kafaɗa ya ce, "kun gani? Dama na gaya muku zai farka."
Kafin Iluru ya gama fahimtar halin da ake ciki ƙaraiƙisu ya cafi kwalarsa. "Yaro, ina ragowar ɗalasiman dake wajenka?"
Iluru zai fara kinkina ya daka masa tsawa. Nan take ya wartsake ya fara laluba jakar tsafinsa sai ga layoyi nan sama da ɗari ya fito dasu.
Ƙaraiƙisu yayi murmushi. "Da wannan komai ya haɗu." Sannan ya juya wajen Ayubu ya ce, "saura kai Ayubu."
Ayubu ya ƙaraso ya ɗora hannunsa akan ramin dake tsakiyar hatimin ya fara kiran nasa ɗalasiman. Ba jimawa jikinsa ya fara haske da wani irin farin haske mai kashe ido. Bayan ɗan lokaci haske ya fara taruwa a saman kansa yana samar da wata irin rana dabbare-dabbare.
Awa guda da farawa jikin Ayubu ya fara tsofewa, amma ranar ko rabi batai ba. Zaka iya cewa har yanzu a ɗaya bisa huɗu ake.
Ayubu ya miƙe yana nishi ya juya ya nuna Nostaljiya ya ce, "bazai yi ba dole sai ta taimaka."
Kána ya kaɗa kai ya ce, "ai wannan mai sauki ne." Ya juya wajen Nostaljiya, "Nostaljiya, muna so ki bawa Ayubu ƙarfinki domin ya ƙarasa karya asirin dake jikin ramukan nan."
Nostaljiya ko kallonsa batai ba. Idonta ya cika da jini sabida kuka.
Ƙaraiƙisu ya daka mata tsawa. "Ke! Dake ake magana kinyiwa mutane shiru."
Tana jinsa amma bata ce uffan. Tsana ce kawai take ƙara bulbula daga zuciyarta tana cika ruhinta. Lallai ta samu wanda take so ta kashe sama da Bihanzin. Kuma tabbas ita ce zata kashe Ayubu da hannunta koda kuwa shi ne abu na ƙarshe da zata yi.
"Wai ba magana ake yi miki?"
"KE!"
"KE!"
Bata ce musu komai ba kuma bata ɗago ta kalle su ba. Su kai tsawa suka gaji. Abinda kawai yake ranta shi ne hanyoyin da zata kashe Ayubu. Ko ta shake shi ta sakale shi har sai ya daina motsi. Ko kuma ta ringa yankar naman jikinsa da wuka kullum-kullum, ɗan'yatsa zuwa ɗan'yatsa har sai ta ƙarar dashi. Ko kuma ta danna kan shege a ruwa har sa ya daina motsi. Ko kuma ta kwakule masa idanu ta tsikaresu har cikin kwakwalwar sa. Ko kuma ta dafa dutse ta dama da karfe tasa a buɗe bakinsa ta zuba masa. Ko kuma tasa karnuka su cinye shi da ransa. Hanyoyi da dama, waɗansu ma sai ta zauna tayi tunani zata samo su. Abu ɗaya dai data sani shi ne ita ce zata kashe Ayubu.
Tana cikin wannan tunane-tunane sai gani tayi ƙaraiƙisu ya damƙi Lamarudu.
"Badai ana yi miki magana kinƙi bada amsa ba," Ƙaraiƙisu ya ɗaga Lamarudu sama ya nunawa ALLAH sannan ya tsire kansa akan tsinin baƙin ƙahonsa, "ga sakamakon masu taurin kai nan." Yayi cilli da gangar jikin Lamarudu gefe jini yana malala, "na kashe shi na kashe banza. Cire mata ankwa Ginad, sannan ka miko min Inara. Kina da dakika goma. Ko ki shiga cikin hatimin nan ki ɗora hannunki akan ramin can, ko kuma," ya nuna Inara, "na tsire shi kamar yadda na tsire ɗayan. Na kashe ku na kashe banza."
A lokaci na farko Nostaljiya ta muskuta ta kalli gangar jikin Lamarudu ko motsi baya yi. Ga wani mummunan rami a tsakiyar kansa wanda ta cikinsa kana ganin waje. Ko shakka babu Lamarudu ya isa lahira.
A dai-dai wannan lokaci B. Ururu ya ƙaraso ya kwance ta. "Tashi muje." Ya daka mata tsawa tare da fincikarta. A wannan lokaci idanun Nostaljiya suka kada, jini ya fara zuba daga ciki.
A wannan lokacin ƙaraiƙisu ya ɗaga Inara sama ya saita shi saman ƙahonsa. "Gani kike da wasa nake, ko?"
"Gudu, sarauniya. Kada ki damu dani. Yi sauri ki gudu. Ki gudu dan ALLAH ko dan saboda abin dake cikinki." Inji Inara. Babu alamun fushi ko tsoro a fuskarsa. Shi dai burinsa sarauniya ta tsira.
Yana cikin magana ƙaraiƙisu ya dodana kirjinsa akan tsinin ƙahonsa ya ce, "ka ci gaba da magana ka ziyarci lahira kamar ɗan'uwanka."
A lokaci na farko Nostaljiya ta zauce. Idanunta suka juye.
Tayi shiru tana tunani yadda zatai. Wato a wannan lokaci ta gano cewa duk tsahon rayuwar ta bata taɓa shiga tsaka mai wuya irin wannan ba. Zaka iya cewa tunda ta taso akwai majibincin al'amarinta a kowanne lokaci, waɗanda suka haɗa da masu amana irin su Armad da kuma maha'inta irin su Bihanzin, amma dai a kullum wani yana gefe yana kula da ita wanda hakan yasa bata taɓa shiga irin wannan hali ba. A yanzu babu kowa sai ita kaɗai. An tozartata, an wulakantata, anci mata mutunci. Sannan kuma wanda zai tare mata baya nan. Daɗin daɗawa rayuwar abokan tafiyarta tana hannunta. Mai zata yi? Wata kwalla ta zubo mata, zuciyarta tayi ɗaci irin wanda bata taba yi ba. Shin Armad zai ƙara kallonta kuwa? Shin zata iya ƙara haɗa ido dashi? Ace Nusi ta gane mai yake faruwa kuma ta gaya mata amma duk da haka bata ankare ba. Wannan shi ne mafi girman abin kunya da zai faru da ita a ban ƙasa.
Wayyo ALLAH, yau yaya zata yi da kanta?
"Aaarghh..." Inara yayi ihu sabida shigar ƙahon ƙaraiƙisu kirjinsa.
A wannan lokaci Nostaljiya ta ɗimauce. Wani abu acikin kanta ya buga. Babu wanda yasan ya akai kawai sai gani akai ta bayyana a gefen Ayubu ta cafi wuyansa. Ta caka ƴan'yatsunta na hagu a idonsa na dama har saida ya shige ciki. Jini yayi feshi. Su Kána sukai sauri suka shiga tsakani suna ƙoƙarin janyeta daga jikin Ayubu wanda ke ta ihu. Amma a lokacin hankalin Nostaljiya ya gushe. Idanunta sun daɗe da rufewa. Nan take ta fara wani ihu mara daɗin ji mai cike da kuka da ɓacin rai da baƙin ciki.
Ƙaraiƙisu yai sauri yai tsalle baya ya rufe kunnensa. Su Kána kuwa da basu yi sauri ba sai da suka zube ƙasa akan gwiwowinsu saboda ƙarfin ƙarar. Suna ji tamkar guduma ake bugawa acikin kansu.
Ayubu ya riƙe kansa yana birgima a ƙasa. Zaka iya cewa zafin dake cikin kwakwalwarsa yafi na idon dake zubar da jini.
***
Comments
Post a Comment