Ganin haka, Binani da matar mai kama da Rabi suka bisu da gudu.
Idan ka lura zaka ga filin yaƙin ya sauya salo. A ɓangare guda Nusi tana ɗauke da Armad da Fatima tana gudu. A ɗaya ɓangaren kuma Nazára ya ɗakko Rabi, Binani da Rabi-mutun-mutumi suna binsa.
A wani wajen kuma Zaikid yana ƙoƙarin tare Dul'Ururu, jan doki da Najunanu suna ƙoƙarin tare Diwani. Maruta kuma yana can gefe yana kula da rundunar Ururu da kuma faɗan Ƙaraiƙisu da Maikiro'Abbas.
"Armad," inji Nusi. "Ka amsa min mana. Kana ji na? Armad?"
Shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Kawai jini ne yake zuba daga bakinsa.
"Ya suma," inji Fatima, cikin alhinin. "Bazan iya amfani da izza ba saboda da wannan ƙarfen." Ta nuna ankwar dake jikinta. "Amma farfesa Zaikid zai iya bashi izza ya farfaɗo dashi."
Nusi najin haka ta waiwaya ta hangi Zaikid tsaye a gaban Dul'Ururu. Ko kokwanto bata yi Dul'Ururu yafi ƙarfinsa.
"Giwa, Cokali, Sarkin Bai, Barilu, Inyaya, Burjan," Nusi ta kira sunayen mutanen dake tare da ita. "Ku taimakawa farfesa."
A tare dukkansu suka juya suka nufi wajen da Zaikid yake faɗa da Dul'Ururu. Sai dai Burjan bai motsa ba.
"Kina da buƙata ta," inji Burjan. "Idan duk muka tafi muka barki ke kaɗai aka kawo miki hari waye zai tare miki? Sannan kuma ni har yanzu banga hanyar guduwa daga filin nan ba. Kada ki manta akan doron ƙasa ta biyu muke. Yanzu da kike tafiya ina zaki?"
Jin haka Fatima ta kalli Nusi domin taji ko akwai shirin da sukai. Tabbas tuntuni ta fuskanci zasu samu matsala koda kuwa sun samu nasarar kwace ta kasancewar dukkan doron ƙasa ta biyu a karkashin Ururu yake. Babu wajen da zasu iya ɓuya. Shin zasu yi ta gudu ne har sai sunje bango sannan su shiga ta ikwatora? Amma kuma Ururu baza su rabu dasu su zuba musu ido har suje bango su shiga ikwatora ba.
"Ni shiri na Armad ya ɗauke mu da fasahar Aiban'shisu ya kai mu bango," inji Nusi. "Daga nan sai mu shiga sashin ikwatora mu gudu. Ururu basu da iko anan. Tabbas zamu samu hanyar guduwa."
Fatima da Burjan suka kalli juna sannan suka juya suka kalli Nusi. Akwai matsala guda biyu da wannan shirin da take yi: na farko, Armad bashi da ikon ɗiban dubunnan mutane a lokaci guda komai ƙarfinsa, kuma tabbas baza su gudu su bar ragowar mutanen da suka zo taimakon su ba; na biyu, Armad a sume yake yanzu kuma babu wanda yasan sanda zai farfaɗo.
"Mai zai hana na buɗe muku ƙofar Eycigan ku gudu ta ciki?" Inji Burjan. "Ina daga cikin kaɗan da baba Abbasu ya bawa wannan fasaha a Non-toch-teka. Zan iya buɗe babbar kofar da zata yi minti goma. Ina ganin da yawa daga cikin mutanen mu zasu tsira. Ya kuke gani?"
"Yayi," inji Fatima. "Amma Armad da mayaƙan mu kaɗai za'a saka. Ni zan tsaya na taimaka."
Burjan ya haɗe gira. "Saboda mai baza ki tafi ba? Sau ɗaya kacal zan iya samar da ƙofar a rana. Ina ganin zai zama asara idan ke baki shiga ba."
Fatima taja dogon numfashi. "Na tabbatar koda minti talatin zaka bamu ko awa guda wasu baza su samu damar shiga ba. Kada ka manta a filin yaƙi muke; abokan gabar mu baza su bari kawai mu gudu suna gani ba. Dole ana buƙatar mayaƙa da zasu tsaya su bada kariya kafin kowa ya tafi." Fatima tayi masa bayanin abinda take tunani.
"Nima zan tsaya," inji Nusi. Dama tun can bata niyyar tafiya sai tare da Armad.
Suna cikin magana suka hango Nazára ya taho da gudu inda suke. Kwamanda Binani yana bayansa suna gudu.
Ganin haka Nusi ta juyo da sauri kan Fatima tana ƙoƙarin tsinke ankwar. Amma tana taɓa ƙarfen taji wata kasala ta shiga jikinta. Tayi ƙasa luu zata fadi. Burjan yayi sauri ya taro ta.
"Bana jin akwai mai amfani da aljani wanda zai iya tsinke wannan ankwa," inji Asifu. "Indai kana da aljani to da zarar ka taɓa ta zata zuƙe maka ƙarfi kamar an saka maka farar laya."
Nazára yana ƙarasowa, Binani ya kawo masa suka da wani irin fafalo. Nazára yayi tsalle sama ya haye fafalon, a lokaci guda ya buɗe Rabi ta tari matar dake kama da ita. Suna haɗuwa suka kaiwa juna sara, amma maimakon Rabi ta tare takobin mutun-mutumin sai ta miƙa mata kafada ta sara sannan a lokaci guda tayi amfani da damar ta zagaya ta baya ta sari Binani a kafaɗa. Shi kuma Nazára maimakon ya kaiwa Binani hari sai yayi amfani da damar ya juya ya kaiwa matar mai kama da Rabi. Wani baƙin yashi ya fita daga hannunsa ya bi jikin matar ya lullube ta. Daga nesa idan ka hange ta sai kace mutun-mutumin ƙarfe ne.
Shi kuwa Binani jada baya yayi da sauri yana kallon kafaɗarsa. Ciwon da Rabi taji masa har ya warke. Amma kuma cikin dakika goma ya ƙara fashewa.
"Takobin waraka, ko?" Inji Binani. "Hmm.. Ina da ƙarfin izzar da zan iya sati guda da wannan ciwon banje ƙasa ba, yarinya."
Rabi ta shafa kafaɗarta inda mutun-mutumin ta sare ta. Nan take ciwon ya ɓace. Ganin matar mai kama da ita bata motsi sai Rabi tayi tsalle ta dawo baya wajen su Nusi. Shima Nazára ya jada baya. A ɓangare ɗaya akwai Nusi da Nazára da Burjan da Rabi. A ɗaya ɓangaren kuma Binani ne shi kaɗai.
"Burjan?" Inji Nazára. "Mai kake jira ne? Bana son ganin Armad da Fatima a filin nan."
Burjan ya yamutse fuska cikin mamaki. A sanda sukai maganar buɗe ƙofar Nazára yana can nesa. Bai kai ace yaji mai suka ce ba. Sannan kuma Burjan yana da yaƙinin Nazára bai san yana da fasahar ba. Hasalima idan ka ɗauke Maikiro'Abbas babu wanda yasan yana da ita, hatta Rabi. Hakan abu ɗaya yake nufi: iska tana ɗaukan zance ta kaiwa Nazára. Burjan yayi murmushi. Wannan tawaga tasu Armad ta fara kayatar dashi.
Ganin yayi shiru bai bashi amsa ba yasa yayi tunanin ko yana kokwanto ne saboda haka yayi masa bayani abinda yake nufi. "Armad dai-dai yake da mutun dubu, amma a haka bashi da amfani. Idan ka bashi dama ya warke zai dawo ya taimaki sauran. Ita kuma Fatima saboda ita ake yaƙin nan. Idan muka cece ta dai-dai yake da mun samu nasara. Sannan kuma cetonta dai-dai yake da mutunta mutanen da suka mutu a yaƙin nan. Saboda haka dole muyi duk wani abu mai yiwuwa mu tseratar dasu biyun nan."
Fatima ta fuskanci mai Nazára yake faɗa, amma ko kaɗan bata so. Bata jin zata iya rayuwa da kanta idan ta gudu ta bar filin bayan wadan suka zo ceton ta suka zo yi.
"Armad ya tafi amma ni ina nan," inji Fatima.
Jin haka Rabi ta juyo a fusace. "Jinjira, filin yaƙi ba wajen tausayi bane, ba kuma wajen yin abinda ya kamata bane. Filin yaƙi waje ne da zaka yi komai dan kayi nasara. Ki tafi, kada kiyi musu. Kuma kada ki damu da dukkan wanda ke filin nan. Munzo ne dan muna so, ba takura mana akai ba."
Jin haka Fatima tayi shiru. Bayan ɗan tunani ta fuskanci baza ta iya musu da Rabi ba saboda haka ta amince, amma ta ƙudure a ranta koda ta tafi to zata dawo da zarar Armad ya samu lafiya.
Ganin an cimma matsaya, Burjan ya haɗa hannu biyu guri guda ya fara kiran ɗalasimai. Wata iska mai ƙarfi ta taso. Bayan ta lafa wata koriyar ƙofa ta bayyana a gabansu.
Da sauri Nusi ta ɗaga Armad zata jefa shi ciki. Ganin haka Binani ya yiwo yunkuri zai tare ta amma Nazára ya shiga gabansa yana dariya.
Comments
Post a Comment