Skip to main content

375-378

 Ɗakin yayi shiru, maganar Taidara tana kararrawa acikin kansu. Wato ita Fatima ta haƙura da halinsa amma shi bazai iya haƙura da abinda yake yi saboda ita ba. Wata ƙwalla mai zafi ta zubo daga idanun Fatima. Ta sunkui da kai. Maganar Taidara ta tabbatar mata da abinda take tunani. Daman wani dalili ne yasa ya aureta ba soyayya ba. Duk kuwa da shi Taidara yana musun hakan.


Sai da aka kwashe minti guda cir babu wanda yace uffan sannan Alu mai sango yayi gyaran murya. "Ina ganin... Taidara baka shirya yin aure ba saboda haka zaka iya sauwake mata." Ya ja ɗan numfashi tare da shafa fuskarsa, kana gani kasan acikin damuwa yake, watakila yana dana-sanin yiwa Taidara waliyi a wannan lokaci. Abinda ya faru ya riga ya faru sai dai neman mafita. A hankali ya juya inda Fatima take kanta a sunkuye, ya bude baki zaiyi magana amma ya kasa. 


Ya juyo wajen Taidara da murya mai kaushi yace "Taidara, koma jikin bangon can ka tsaya." Babu kunya Taidara ya miƙe ya koma jikin bangon ya tsaya. "Ko ka sauwake mata, ko baka sauwake mata ba, aure na rabashi a matsayina na waliyinka har sai lokacin da kayi hankali. Ƴaƴa guda biyu da kuke dasu na bawa Fatima Armad domin jariri ne. Ba za'a raba shi da uwarsa ba, ita kuma Abijan tunda tana da hankali zan bata dama ta zaɓa da kanta. Idan ta zaɓi ta bika to babu matsala zamu barta, idan kuwa ta zabi ta zauna da mahaifiyarta kamar yadda muke fata zata yi to dole kai kadai zaka tafi, sai dai watakila ƴarka Hidaya wadda dama tare muka gan ku."


Taidara ya buɗe baki zaiyi magana Alu ya tsayar dashi. Ya juya wajen Maikiro'Abbas. "Yi haƙuri fa, nayi gaggawar yanke hukunci da kaina, amma ya kake gani?"


Maikiro'Abbas ya girgiza kai. "A'a, bakai hanzari ba, nima hukuncin da zan yanke kenan. Yanzu kawai zamu saurara muji Abijan wane ɓangare zata zaba."


A wannan lokaci Abijan ta miƙe ta juya inda mahaifiyarta take zaune. "Mama, kiyi haƙuri amma Abba ya fiki gaskiya." 


Da wannan Abijan ta taka ta koma ɓangaren mahaifinta. Wani kallo na jinjina Taidara yayi mata haɗe da murmushin godiya tare da gyaɗa kai. Zaka iya cewa ragowar mutanen da suke cikin ɗakin ba suyi mamakin hakan ba domin duk labaran da suke zuwa sun nuna Abijan halin babanta tayo. Fatima bata ce komai ba. 


Maikiro'Abbas ya nuna Hidaya wadda ke zaune a kusa da Fatima. "Saura ke."


Tun kafin Hidaya ta bada amsa Taidara yayi murmushi ya dubi Maikiro'Abbas yace, "Meye kuma abin zaɓe? Dama Hidaya tare kuka ganmu, tare kuma zaku barmu." Ya juya wajen Hidaya. "Ƴata, taso mu tafi." Kana jin muryarsa kasan ya yarda ɗari-bisa-ɗari Hidaya tana tare dashi. Hakan ba abin mamaki bane tunda tare aka gansu sannan kuma babu wanda yasan tsawon lokacin da suka daɗe suna tare. 


Sai dai kuma har yanzu Hidaya tana zaune bata motsa ba. Mai saurare zai iya tambaya mai take yi har yanzu a zaune bata koma ɓangaren Taidara ba. Ya kamata ace ta riga Abijan komawa. 


Hidaya taja dogon numfashi. "Ina tunanin zan zauna tare da Fatima. Idan na tafi waye zai kula da Armad?"


Dukkan wanda ke cikin ɗakin sai da ya zare ido cikin mamaki domin babu wanda yake tunanin zaiji wannan kalmomi daga bakinta. Amma Taidara yafi kowa kaɗuwa. Tafiya yayi da sauri yaje wajen da Hidaya take. "Haba, Hidaya, mai kike cewa ne? Ki daina wasa, ki taso mu tafi."


Hidaya ta girgiza kai. "Nifa na riga na yanke shawarar na zauna kuma bada wasa nake ba."


"Hidaya!" Ya daka mata tsawa. "Wai kin manta da duk shirye-shiryen da muka daɗe muna yi shekara da shekaru? Wane dalili ne zaisa ki bar komai ki juya min baya duk irin abubuwan da muka shiga tare? Idan wasa kike yi to ki daina, ki taso mu tafi kinsan kina buƙatata, nima kuma ina buƙatarki. Mafi muhimmanci kina bukatar ki zama a sahun gaba na waɗanda zasu ɗau fansa akan Ururu. Idan mun ci nasara a yaƙi kece ta farko wadda zaki karya tutar Ururu, ki saka mata wuta. Meye dalilinki na zama anan?" 


"Komai zaka faɗa, Abba, amsata ba baza ta canja ba."


"Hidaya! Bazan yarda da wannan zancen naki ba, dole ki dawo cikin hayyacinki ki taso mu tafi. Wai uban mai yasa kike so ki zauna?"


Ko kaɗan harzukar da Taidara yayi bai daga mata hankali ba. A hankali ta buɗe baki tace, "idan na tafi waye zai kula da kanina Armad?" 


"Wannan wane irin zance ne? Kina tunanin babarsa baza ta iya kula dashi ba? Ko kuma kakansa Zaikid da Maikiro'Abbas baza su iya kula dashi ba? Ki daina wannan zance." Ba tare daya bata dama ta ƙara yin magana ba ya finciki hannunta. "Tashi mutafi." 


Hidaya bata tashi ba kuma bata motsa daga inda take ba, shi kuma Taidara bai daina janta ba har saida ya samu dama ya finciketa. Yana juyowa zai tafi yaga Maikiro'Abbas tsaye a bayansa yasha kansa ya lullubeshi da girman ƙirjinsa. Ga izza mai ban tsoro tana fita daga jikinsa. 


"Tace bata so, ko dole ne?" Inji Maikiro'Abbas.


Taidara ya ƙurawa Abbas ido yana tunanin koda wasa yake, amma kuma babu alamun wasa a fuskarsa. Ya buɗe baki zaiyi magana amma ya rufe. Ya saki hannun Hidaya a hankali sannan ya wuce ya koma jikin bango inda Abijan take. 


Kafin kowa yayi magana Fatima ta miƙe. "Ina son ayi min tsakani dashi domin bana raba-ɗaya-biyu zai dawo wajen Armad anan gaba ya nemi ya kwacemin shi."


Maikiro'Abbas ya ɗan jinjina maganar domin tayi masa nauyi, kamar tana so ya raba uba da ɗa ne wanda kuma yake ganin hakan ba lallai ya haifar da ɗa mai ido ba. Kafin ya bada wata amsa Zaikid ya miƙe. A lokaci na farko tun bayan fara tattaunawar ya shiga maganar. "Taidara, maganganun ka sun shiga zuciyata kuma zan iya cewa burinka na farfaɗo da martabar gidan Wilbafos abu ne mai kyau. Amma kuma ba tsarin rayuwa bane na mutum mai iyali. Ina ganin rabuwarka da Fatima shi ne mafi alheri a gareku. Amma koda kun rabu ka sani Abijan ƴarmu ce kuma kaima ɗanmu ne tunda ka auri ƴarmu. Saboda haka damuwarka damuwarmu ce. Ni, Zaikid Wilbafos, zan zamar maka salsa a ƙoƙarinka na gwagwarmaya amma ina so kai min alƙawari baza ka ƙara shiga rayuwar 'yata ba. Baza kayi wani abu da zaka raba ta da ɗanta Armad ba. Idan son samu ne idan ka tafi ya zamanto ka tafi kenan." 


Zaka iya cewa tunda aka fara wannan tattaunawa sai yanzu Taidara yayi murmushi. Murmushi ne irin na girmamawa da jinjina. Da farko yayi tunanin Zaikid haushinsa yake ji saboda abinda yayiwa 'yarsa, amma kuma a yanzu ya fuskanci ba haka bane. Hasalima duk cikin ɗakin babu wanda ya fuskance shi kamar Zaikid. Da sauri ya tafi wajen da Zaikid yake tsaye ya durkusa akan gwiwowinsa. "Ni, Taidara Wilbafos, nayi alƙawari bazan yi duk wani abu da zai raba Fatima da Armad ba, sannan kuma ba zanyi ƙoƙarin janyo shi ɓangarena ba. Duk wata ziyara da zata jawo hankalinsa ba zanyi ta ba."


"Ka samu salsa," Inji Zaikid. Ya ɗora hannunsa akan kafaɗar Taidara. 


"Nagode, nagode, ban taɓa tunanin mutun kamar ka zai yarda ya zama salsa na ba." 


Da wannan aka zo ƙarshen wannan tattaunawa. Taidara ya tattara kayansa da Abijan sukai sallama da Hidaya da Zaikid suka kama hanya. Fatima ko sallama bata yi musu ba. 


Zaikid yaja dogon numfashi yace, "to kaji abinda ya faru, Armad. Wannan shi ne abinda yasa ka taso baka san mahaifinka ba. Kuma wannan shi ne dalilin da yasa kaga Fatima bata son zancensa. Duk lokacin da ka kawo mata zancensa ranta yana ɓaci."


Armad bai ce komai ba, yayi shiru yana kallon ƙasa, a zuciyarsa ya rasa wa zai ji haushi. Fatima ko Taidara? A ganinsa duk su biyun suna da laifi. Ta wani ɓangaren Taidara yafi laifi, amma kuma ita ma Fatima da nata. 


"Yanzu ina Abijan? Kuma mai ya faru bayan Taidara ya tafi?" Armad ya tambaya.


"Shekara ɗaya bayan rabuwar iyayenka," Zaikid ya fara bayani. "Taidara da Abijan suka jagoranci runduna guda suka kai farmaki doron ƙasa ta biyu. Al'umma suka sawa yaƙin suna yaƙin maƙabarta saboda yawan gawarwakin da Taidara ya tasa. Duk wata gawa ma'abociyar izza ce wanda suka juye izuwa jarumai. Yaƙi ne mummuna wanda aka shafe sama da kwana bakwai anayi. Daga ƙarshe hatta Ashura sai da suka shigo ciki. Zaka iya cewa Taidara yayi nasara kuma bai yi nasara ba. A dalilin yaƙin Taidara ya cinma burinsa na kafa majalisin sulhu tsakaninsa da Ururu wanda ya haɗa da duk wasu manya a ƙasashen ƙasa. Dama shi ne shirinsa - ya nunawa Ururu ƙarfinsa yasa dole su amince a zauna a teburin sulhu. Amma kuma akwai sharadi, kafin Ururu su yarda sai da aka basu fursunan yaƙi a matsayin garkuwa. Suna tsoron Taidara zai sake kai musu wani harin." 


"Farfesa," Armad ya tari numfashinsa. "Kada dai kace Abijan aka bayar a matsayin fursunan saboda a kafa majalisin?"


Zaikid ya gyaɗa kai. "Ita Taidara ya bayar. Hakan shi ne babban abinda ya ƙara lalata alaƙa tsakanin Fatima da mahaifinka, kuma har yau bata yafe masa abinda yayi ba. Har yanzu da muke magana dakai ƴar-uwarka Abijan tana doron ƙasa na farko. Akwai lokacin da Taidara ya kai ni na ganta muka gana. Sun bata gida da 'tsaro' amma kuma bata da damar zuwa ko'ina. Kullum a inda ta tashi anan zata wuni, kuma anan zata wayi gari. Ururu sunyi hakan ne domin su takawa Taidara birki. A halin yanzu duk wani motsi da Taidara yayi suna da damar da zasu kashe Abijan. Tun daga lokacin Taidara bai ƙara fito-na-fito da Ururu ba.


"Kasan yadda akai mahaifiyarka ta samu ciwon izza wanda har yasa ka fita neman mata magani? Nasan tunaninka yaƙi ta fita yi da Ururu aka ji mata rauni, amma kuma ba haka bane. Maimakon yaƙi ita sulhu taje. A ƙoƙarinta na hana yaƙin shi ne yasa taje filin yaƙin. Kaga dai Shísu Bayajidda, baban Ikenga Bayajidda, abokin Taidara ne. Suna zama a lokuta da dama su tattauna al'amuran izza. Mahaifinka ya koyi fasaha daga Shísu kamar yadda Shísu ya koyi fasaha daga gare shi. Wasu daga cikin fasahohinsu suna kama, wasu kuma iri ɗaya ne sak. Wannan dalili yasa a lokacin da Shísu ya haɗa rundunarsa ta tawaye ya kuma fara kamfen a doron ƙasashe sai Ururu sukai tunanin tare suke da mahaifinka. Hakan yasa suka fara ikirarin kashe Abijan wadda take hannunsu. 


"Hankalin mahaifiyarka ya tashi, ta fara hawa da sauka tsakanin doron ƙasa ta biyu zuwa ta bakwai. Da farko tayi ƙoƙarin sulhuntawa, amma hakan bai yiwu ba, saboda haka sai ta koma ƙoƙarin bayyanawa Ururu babu hannun Taidara acikin abun. Ba wai dan ta damu da Taidara ba, amma duk abinda Taidara yayi zai shafi ƴarta kai tsaye. 


"Daga baya Ururu sun yarda babu hannun Taidara a cikin tawayen amma kuma duk da haka suna zarginsa da koyawa Shísu fasaha. Wannan shi ne dalilin daya sa Ururu suka tilastawa mahaifiyarka shiga wannan yaƙi; a cewarsu tunda Taidara ya koyawa Shísu fasaha to dole tazo ta shiga yaƙin ta taimaka musu. Hakan kaɗai zai tabbatar da babu hannun Taidara aciki. Idan kuma ba haka ba da zarar an gama yaƙin zasu lissafa iyakacin mutanensu da aka kashe su ɗauki fansa akan Abijan. Dole mahaifiyarka tayi shiri ta shigarwa Ururu yaƙin da akai. Bansan takamaimai wanda ya jiwa mahaifiyarka ciwo a yaƙin ba, amma mutane da dama suna tunanin shugaban ƴan-tawayen ne da kansa - Shísu Bayajidda. 


"Koma dai yaya abin yake mahaifiyarka ta shiga yaƙin ne saboda Abijan, kuma hakan yasa Ururu basu taɓa yar-uwarka ba. Tana nan cikin koshin lafiya. Kusan gaba ɗaya rayuwar Fatima tun daga lokacin da Abijan ta bi mahaifinka take cikin damuwa, bata da wani aiki sai ƙoƙarin ta tabbatar Taidara bai yi wani abu da zai jawo Ururu sun kashe Abijan ba. Amma kuma duk da haka zaka iya cewa matsalar Taidara mai sauki ce akan matsalar ka. 


"Shin ko kasan cewa a wancan lokacin bayar da Abijan da akai a matsayin garkuwa shi ne ya hana Ururu yin kamfen? Yaƙin maƙabarta yakai matakin da Ururu suka kira kamfen, ba daban an basu Abijan ba da tun a wancan lokacin sun ƙaddamar da kamfen na biyu. A wannan lokaci rugujewar sarakunan jinzidal da abubuwan da kayi sune suka jawo kamfen. Kamar abin a jinin ku yake, duk yadda Fatima tayi ƙoƙarin kada ka shiga faɗa da Ururu sai da ka shiga. Idan baka mantaba wannan shi ne dalilin da yasa mahaifiyarka bata son ta koya maka fasaha har sai ka gama duk littattafan data sa maka. Tana fatan ilmin cikin littatafan zai nuna maka hanya sannan kuma zai hanaka bin layin da mahaifinka ya bi. Amma kuma duk da ƙoƙarin data yi hakan bai hana ƙaddara tayi halinta ba. Rashin lafiyarta ce tasa ka fita nemo mata magani, kuma a dalilin haka komai ya faru. An kai wata gaɓa da Ururu suka riga suka saka ido a kanka. Duk doron ƙasashen ƙasa babu wanda bai sanka ba. Idan mahaifiyarka ko Taidara suka shigar maka hakan zai jawo a kashe yar-uwarka, idan kuma basu shigar maka ba akwai yiyuwar kai ɗin a kashe ka. Ganin haka yasa Fatima tayi abinda ta saba. Tana ji ance Ashura zasu sakko taje ta tare su. Kafin hakan ta faru Taidara yazo da sauri ya fadamin abinda take ƙoƙarin yi. Yana so naje na hanata. Nayi shiri na fita, amma kafin na isa tuni da ita da Shata sun haɗu da Ashura. Bari na nuna maka yadda abin ya faru."


Zaikid yasa hannu yayi gaba da faifan bidiyo zuwa ƙarshe, daidai inda Fatima da Shata suka tari Ashura a yayinda suke sakkowa ƙasa domin ƙaddamar da kamfen. 


Zai yi wahala kaga Ashura a ƙasashen ƙasa. Watakila zaka iya ganin mutun ɗaya ko biyu, amma ganinsu gaba ɗaya a tare a lokaci guda abu ne mai wahalar gaske. Duk da haka dabi'a ce a duk sanda za'a fara kamfen su sakko domin share hanya. Haka akai a kamfen na farko. Haka akayi a lokacin wancan kamfen ɗin da Taidara ya janyo. Dalilin da yasa aka fasa wancan kamfen ɗin shi ne Taidara ya tari Ashura ya basu Abijan a matsayin garkuwa. A wannan zamani Ashura sun sakko domin share hanya a fara kamfen. Fatima ta tare su da bayani a ƙoƙarinta na dakatar da kamfen din.


***


Suna tafe akan iska kamar tsuntsaye. Idan ka hangesu daga nesa zaka ga mutum tara a jere, ɗaya a bayan ɗaya, sanye da bakaken kaya da bakaken idanu. Mun daɗe da sanin idanunsu ne suke juyar da kamannin kayan da suka saka izuwa baƙi saboda haka ba lalle bakaken kaya suka saka ba. Akwai yiwuwar farare ne amma ikon idon ya juyar da launin zuwa baƙi.


Iskar dake kewaye dasu tana kaɗawa da ƙarfin gaske, kai kace wata guguwa ce wadda ake rurawa. Babu wata fargaba a tare dasu. Suna tafe akan iska domin sunfi ƙarfin taka ƙasa. Suna jin sunfi duk wata halitta iko. Suna jin idan banda babban sarki Kuyurussa'ayi to babu wani mahaluki daya isa ya shiga gabansu. Kololuwar girman kai da isa da iko. 


A tsakanin doron ƙasa ta farko data biyu akwai wani tsibiri mai suna Sido-Ururu. A duk sanda zasu sakko ƙasa sukan tsaya a wannan tsibiri suyi addu'oinsu samfurin Ururu. A wannan lokaci ma haka akai. Sun kammala addu'a kenan suna niyyar tafiya sai sukai bakuwa. Farar mace mai cikar kamala da wani mutun mai ɗauke da garaya. 


Mutun takwas daga cikin mutun taran basu juyo sun kalli wannan bakuwa ba suka ci gaba da kallon wajen ibadar dake gabansu. Wasu daga cikinsu ƙara matsawa sukai kusa da dutsen suka ɗora hannu akansa. Wasu kuma durkusawa sukai a wani yanayi mai kama dana addu'a. Mutun ɗayan daya tsaya ya kalli wannan bakuwa a nutse. Wannan mutun ba wani bane illa yarima mai jiran gado - yarima Dumakisu Kuyurussa'ayi. Yana nan da dakakkiyar fuska kamar yadda muka saba ganinsa. Akwai wani ɗan gajeren gemu ruwa toka daya fito masa wanda wannan bakuwa bata san dashi ba. Idanunsa sun ƙara baƙi akan yadda ta sansu, abinda a da take ganin bamai yiwuwa bane. Gashin girarsa yayi ruwan toka alamun daɗewa a duniya. Tunda yawan shekaru baya sa Ururu furfura sai dai gashin yayi ruwan toka.


"Fatima?" inji Dumakisu, muryarsa tana bada wani irin kaushi mai sa ƙasa karkarwa. 


"Dumakisu?" inji Fatima. 


"Kin zo ki hana kamfen amma hakan bazai faru ba," inji Dumakisu. "Idan kina tunanin Abijan to ki kwantar da hankalinki, bama saɓa alƙawari, indai Taidara bai saɓa alƙawarinsa ba to baza mu taɓa ta ba. Zaki iya tafiya."


"Ba Abijan ce ta kawo ni ba," inji Fatima da sauri. 


Dumakisu ya haɗe gira amma kuma babu alamun ɓacin rai a fuskarsa. Kamar zaka iya cewa mamaki yake maimakon ɓacin rai. "Idan ba Abijan ce ta kawo ki ba to Armad ne ya kawo ki kenan?"


Fatima ta gyaɗa kai.


"Hmm.." Ya kalli sama a hankali yana tunani. "Hakane."


Fatima ta ɓata rai. "Hakane me? Zaku yadda na baku kaina a matsayin fansa ku tafi dani doron ƙasa ta farko amma ku rabu da ɗana Armad?"


"Um-um.. baki kai darajar Abijan ba saboda haka baza mu karɓe ki ba. Amma idan zaki bamu Armad mu haɗa shi da Abijan to zamu fasa wannan kamfen."


"Kun karɓi waccan kuma yanzu ɗan nawa namiji guda ɗaya shima so kuke na baku shi? Ahir ɗin ku!"


Dumakisu yayi ɗan murmushi kaɗan wanda maimakon ya faranta sai kawai yasa wajen ya ƙara duhu. 


"Shi ne yasa tun farko na gaya miki abinda kike nema bazai samu ba," inji Dumakisu. "Ko Armad ko kamfen. Idan ba haka ba ki koma inda kika fito."


Fatima tayi shiru tana kallonsa. Shi kuwa juyawa yayi ya tafi wajen dutsen da yan-uwansa suka zagaye. 


Fatima ta kalli Shata wanda ya girgiza kai. Taja dogon numfashi ta tsaya tana jiran Ashura su kammala abinda suke yi. 


Minti ashirin suka ɗauka kafin su kammala su juyo wajen da take. Ba tare da ƙara kallonta ba suka tashi sama suka nufi hanyar gadar zare domin su fara aikinsu. Fatima ta tashi sama ta shiga gabansu. Shata yana take mata baya. 


"Kin tabbata da abinda kike ƙoƙarin yi?" Dumakisu ya tambaye ta. 


"Idan ban tabbata ba baza ka ganni a anan ba," inji Fatima. Ta zare takobin ta.


Yarima ya shiga gaba ya zare tasa takobin. Suka ɓace daga inda suke suka bayyana a tsakiya inda suka kaiwa juna sara. Walkiya tayi tartsatsi tayi sama kan Hajarul Ururu daya raba doron ƙasa ta biyu data farko. Koda wannan walkiya ta daki Hajarul Ururu sai ta juyo ta dawo ƙasa. Babu saƙo da loko da ba'a ga hasken walkiyar ba. Bayan komai ya lafa Fatima tana ƙasa cikin ankwar Bilak-siton. Babu wanda yasan yadda akai ko kuma mai ya faru, kawai anga sun haɗa takobi sannan kuma an ga Fatima a ƙasa. Ita kanta Fatima idanunta akwai mamaki aciki domin bata yi tsammanin zuwa ƙasa da wuri haka ba. Kai idan ka tambayeta ba lalle tasan yadda akai taje ƙasa ba. 


Kafin Ururu su ɗauke ta zaikid ya bayyana. 


"Wilbafosiyan Siwod Dans!"


Tartsatsin baƙi ya haɗu da takobi. Bayan komai ya lafa aka ga yarima ya riƙe takobin Zaikid da hannu ɗaya kamar wanda ya riƙe alkalami. Kafin Zaikid ya ankare wata takobin ta bayyana a ɗayan hannun Dumakisu ya kawo masa suka da ita. Zaikid ya kauce amma kawai sai yaji takobin acikinsa. A wani lokaci dake tsakanin samuwa da rashi, a wani lokaci dake tsakanin zamani da zamani, a wani lokaci dake tsakanin duniya da duniya, Zaikid yaji takobin ta ƙara saransa. Wato bawai sukan farko ba kaɗai, a'a, tuni yarima ya ƙara saukar masa da wani saran a wani lokaci dashi kansa bai sani ba. Kai kace Dumakisu yana tare lokaci ya tsayar dashi yayi abinda yake so sannan ya sake shi ya tafi. Zallar iko irin na fasahar Saɓani mafi girma.


Zaikid ya riga Shata zuwa ƙasa wanda ke ƙoƙarin kaɗa garaya amma yaji ruhinsa ya kama da wuta irin ta Ururu. 


Daga bidiyon yazo ƙarshe. Zaikid yayi ajiyar zuciya.


"Da ni da Fatima kawai buɗe ido mukai muka gan mu a fadar Dul'Ururu. Bamu da masaniya akan inda Ashura suka tafi, ko kuma inda Shata yake. Shi kuwa shata kawai buɗe ido yayi ya ganshi a gadar zare a ɗaure. 


"Kaji yadda abubuwa suka kasance. Wannan shi ne dalilin da yasa mahaifiyarka ta tari Ashura. Taje ne domin ta hana su kama ka. Kuma ina ganin duk da bata samu damar hana kamfen ɗin ba, amma sanadiyyar zuwanta ne yasa Ashura basu zo wajenka kai tsaye ba. Sai dai kuma a sakamakon haka yanzu tana hannun Ururu. Dul'Ururu zai yi amfani da wannan dama wajen tattara kan duk wani ɗan-tawaye waje guda ya yanke musu hukunci. Tunda sun gama kamfen lafiya har sun gudanar da jinzidal zasu yi amfani da wannan dama wajen ƙara ƙarfin rundunarsu a doron ƙasashen ƙasa."


A yanzu ya gane abinda ke faruwa. Dama dai dalili bai damu Armad ba, ko meye dalilin mahaifiyarsa na tarar Ashura dole zai je ya taimaka mata, amma kuma yanzu ya ƙara gamsuwa da abinda yake yi. Ya fuskanci bashi kaɗai bane acikin jirgin. Banda Nusi da kwamandunsa akwai Zaikid da Shata. Watakila idan sunci sa'a Maikiro'Abbas ya kawo musu agaji. Amma abin zaiyi wuya tunda Abbas sarkin jinzidal ne kuma bai taɓa nuna wata sanayya ta musamman ga Armad ba. 


"Farfesa, kana ganin Maikiro'Abbas zai zo kuwa?"


"Eh... to!" Zaikid yaja dogon nishi. "Maikiro'Abbas yana da hali irin na Fatima. Zaka iya cewa shi ne ya saka mata rashin son tashin hankali. A kullum yana ganin duk wani amfani da yaƙi zai jawo bai kai rayukan da za'a rasa ta dalilinsa ba. Yaga yaƙuka da dama a tsahon rayuwarsa kuma yaga yadda mutane suke wahala. Watakila shi ne yasa ya samu wannan hali. Amma kuma Abbas ya ɗauki Fatima kamar ƴarsa daya haifa acikinsa. Ina ganin yadda Ururu suka tallata kashe Fatima kamar takalarsa suke yi. Kasan daman zaman doya-da-manja ake yi. Kawai da dan babu yadda Ururu zasu yi dashi ne amma duk wannan shekarun shi ne wanda yafi ci musu tuwo a kwarya. Ururu suna ganin wannan wata dama ce da suka samu wadda zasu nunawa duniya waye yake da mulkin doron ƙasashen ƙasa. Domin kuwa ba daban Abbas ba da tuni Ururu sun daɗe da kafa hadaddiyar daular Ururu a ƙasashen ƙasa wadda take amfani da yare daya - yaren Ururu."


Armad yayi shiru yana tunani. Can dai ya ƙara tambaya. 


"Zai zo ko bazai zo ba?"


Zaikid ya girgiza kai. "Ban sani ba. Komai zai iya faruwa ba. Sai dai muyi fatan alkhairi. Abbas shi ne mafi girman izza sama da duk wani mutum dama taɓa gani. Tabbas idan yazo yiwuwar samun nasarar mu ya ƙaru sosai da sosai."


Armad ya runtse ido yana lissafi. Asalin Nusi a daular maikironomada ta taso. Ba suyi maganar ba amma baza ta rasa wata alaƙa tsakaninta da fadar Maikironomada ba tunda har muƙami ne da ita a garin Khan. Watakila a wata gudan da bayanan Nusi ta samu dama ta haɗa kai da Abbas domin su ceto Fatima. Duk su biyun suna da alaƙa da Fatima ta wani ɓangaren. Nusi saboda Armad, shi kuma saboda tarihin dake tsakaninsu. Yasan zaiyi wuya Nusi takai hari doron ƙasa ta biyu ba tare da wani shiri ba. Ba mace mai garaje bace, tasan abinda zata iya kuma tasan wanda baza ta iya ba.


"Abijan," inji Zaikid ya katse masa tunaninsa. "Mai kake tunani game da ita? Kasan dai yar-uwarka ce, uwa ɗaya uba ɗaya."


Tambaya mai kyau. Amma zai yi wuya Armad ya iya bada amsar ta. Duk yadda akai bai san Abijan ba. Ɗan abinda ya gani a yanzu bai kai ya yanke hukunci ba. Yana buƙata ya santa kafin ya nemi wajen da zai ajiye ta. Abu guda ɗaya dai bata kai hidaya a zuciyarsa ba. Tana kusa da Taidara.


"Zan so na ganta," inji Armad. "Na ga yadda kamanninta suke a zahiri. Zan so naga irin fasahohinta da murmushinta."


Wannan ita ce amsar da Armad ya bashi kafin ya ƙara rufe ido ya shiga tunanin yaƙin dake gabansa. Ururu sun gama shiri amma shiri ba shi ne nasara ba. Kuma idanun duniya suna kan wannan yaki musamman idan ta tabbata Maikiro'Abbas zai shiga yaƙin. 


Comments

Most Popular

460

 Dul'Ururu ya hango abinda yake faruwa saboda haka ya ɗaga hannu sama ya daki iska. Yana sauke hannu sai kawai aka ga sama tayi jajawur sannan aka fara jiyo rugugi da ƙara. Daga sama inda rugugin yake tasowa wata ƙatuwar tauraruwa ta fara faɗowa ƙasa dai-dai kan su Armad.  Filin yaƙin ya ɗau wani zafi na musamman. Iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa. Ƙofar da Burjan ya samar ta fara rawa zata ruguje. "Nusi," Nazára ya kwala mata kira ganin ta tsaya tana kallon sama. "Mai kike yi ne?" Yana rufe baki Nusi tayi firgigit ta farka. Ta ɗaga Armad da Fatima ta cilla cikin ƙofar. A dai-dai lokacin tauraruwar ta sauka a kansu. Tartsatsin wuta da feshin narkakken dutse yayi sama. Duk da azabar yaƙin dake faruwa sai da kowa ya dakata yana kallon inda tauraruwar ta faɗo. Wani wawakeken rami ne a wajen wanda babu abinda ke tashi daga cikinsa sai tururi da tartsatsin wuta.  Idan ka lura zaka ga tauraruwar ta rabe gida biyu: ɓari ɗaya ya faɗa dama, ɗaya kuma ya faɗa hagu. Kwamanda B...