"Suna na Rafiyan Nazára, manzo ga shugaba Armad na Farkon Lokaci. Daga yau sarki Armad Wilbafos ya haramta cinikin bayi. Zaka fito da duk bayin dake cikin garin ka. Zaka bawa kowanne bawa haƙuri, ka nemi yafiyar sa da ayrid dubu goma."
Kujerar da Sarkin Hanibal yake kai ta juyo a hankali ta fuskanci Nazara, wanda ke zaune kan taga ya juya kai yana nazarin cikin garin Faideba.
"Mutun zaiyi tunanin ɗan Daljari shi Armad zai tura garin Jekis domin ɗaukar fansar tsohonsa. Sai dai kash, kun makaro. Tuni mun karɓi tafarkin Mai Iko Ikenga mamallakin lokaci. Sarkin Jinzidal Deniz Iluru ɗan aƙidar Deniz Ururu ne, wanda shi ma ya karɓi tafarkin Ikenga. Deniz Iluru, Deniz Ururu, B. Ururu, Kána, mai tsaron takobi Daddaru, Ƙaraiƙisu da sarakunan Ikwatora, shugaba Amraikugyu na Hantsi, shugaba Báya Azaba na Farkon Lokaci... Koda kun tsallake wuta ta, mutun zaiyi mamakin yadda zaku iya ji da waɗannan ma'abota izza." Inji Hanibal. Muryarsa na ɗauke da ƙololuwar nutsuwa, kai kace ba yaƙi ake yi.
Nazara ya miƙar da hannayensa a hankali, sannan ya haɗe ƴan'yatsunsa waje guda. "Tsamiya, Kuka, Darbejiya, Kalkeci!" Ya ambata cikin Tsohon Aldurish.
"Babu yafiya ga ɓatattu." Inji Nazara. Kalmomin guda huɗu suka juye izuwa ɗalasimi, kai kace harshensa wani allo ne na babbar izza abar tsayuwa ga Sammai. Ɗalasimin ya juye izuwa zangarniya. Abu kamar wasa zangargani ta zama manyan rassai wanda suka shige cikin ƙasa, suka juye izuwa bishiyu. Bishiyu suka fitar da rassa da ganyayyaki, sannan suka haɗe suka zama ƙatuwar gada wadda ta samarwa rundunar Lamarudu Wilbafos dake ƙasa hanya zuwa cikin garin.
Nazara ya sauke ƙafafunsa ƙasa cikin ɗakin. Ya miƙa hannu kan iska inda wata ƴar taga ta bayyana, ya sa hannu ya tsamo takobi. Taku yake ɗai-ɗai kamar ɗan toron giwa ya nufi sarkin Jinzidal kai tsaye da nufin kisa.
"Armad baiyi dabara ba." Inji Hanibal. Har yanzu bai motsa ba, kamar bai damu da abinda ke faruwa ba.
A dai-dai wannan lokaci Nazara ya iso kansa. Takobin sa ta sauka akan Hanibal kamar saukar aradu daga sama. Sai da ya rage saura taƙi guda takobin ta dirar wa Hanibal sai kawai ta tsaya cak. Bawai dan Nazara yayi niyyar tsayar da ita ba. Ikon Deba ne yai aiki. Shi fa Deba daban ne. Faɗa da deba kamar faɗa da duniya ne. Ita kanta duniyar ita take kare deba. Indai duniya na nan to babu wanda ya isa ya taɓa deba.
Takobin Nazara tai gogayya da duniya. Duniya na ƙoƙarin tura takobin baya, shi kuma yana ƙoƙarin sara duniyar gida biyu ya halaka komai.
"Ko deba baka kai ba, amma ka ɗaga takobin ka akan mutanin Hantsi." Inji Hanibal. Ya ja wani gwauron numfashi tare da girgiza kai. Badan sanin zahirin mai ake ciki ba da sai kace tausayin Nazara yake ji.
"Mutun zaice Armad baiyi dabara ba." sarki Hanibal ya ci gaba da bayani. "Mutun yana ganin da Armad ya tattara ƙarfinsa waje guda ya yaƙi Bihanzin ko shugaba Ikenga da yafi masa sauƙi. Amma mutun yana ganin Armad baiyi dabara ba daya fara da Jinzidal. Mu sarakunan Jinzidal da garuruwan mu da mutanan mu duk suna ƙarƙashin kariyar babban sarki Kuyurussa'ayi. Kada ka manta rukunin Jinzidal rukunin sarki Kuyuru Ururu ne. Mutun yana ganin sarki Kuyuru bazai zauna ya bar Armad ya rusa Jinzidal ba. Koda kuwa sauran mayaƙan Ururu dake doron ƙasashen ƙasa sun yanke shawara su ja baya."
Nazara yai ƙaraji mara sauti ya ƙara kaiwa Hanibal sara. Ga dukkan alamu ba zance yazo ba. Abinda kawai ya kawo shi shi ne sara-da-suka. A wannan lokaci saƙon sarkin yaƙi Ayubu ne ya isarwa Nazara. Zaren izza ya bayyana ya nannaɗe ikon duniyar kanta ya tarwatsa. Takobin Nazara ta sauka akan Hanibal.
"TSAYA CAK DA IKON IKENGA!!" Inji Hanibal. A wani salo mai ban mamaki gagarumin ikon Kamalar-ruhi yai fitar burtu daga bakin Hanibal ya damƙe takobin.
"IKON ARMAD!" Inji Nazara. A wannan lokaci gabaki ɗayan duniya sai da ta girgiza. Hadarin daya taso a baya wanda saƙo ne daga aljani Gal-iyyu ya baje. Kiɗan babbar izzar K'Narbig ya fara tashi. Hasken rana ya juye izuwa ruwan ƙasa. Nan take duk wani mai tafiya da numfashi aban ƙasa yaji buƙatar ya durƙusa yayi biyayya. Kamalar ruhin da Hanibal yai amfani da ita ta tawartse kamar an fasa kwai a jikin dutsen wuta. Takobin Nazara ta wuce kai tsaye ta dirar wa Hanibal.
A wannan lokaci Hanibal ya san cewa duk wani wasan Iko ya ƙare. Duk wani wasan Kamalar ruhi ya ƙare. Idan bai fito da fasahar sa ba to fa ƙarshensa yazo.
"Wut-Naru!"
Sarkin aljanun wuta da kansa ya bayyana a wannan rana. Bango-bango na wuta sai da bango ɗari bakwai ya bayyana a tsakanin takobin Nazara da Hanibal. Babban abin mamakin shi ne sarkin aljanu Wut-Naru wanda suka haɗu da Armad tare da sauran sarakunan aljanu a baya. Duk wani saƙo da loko na garin sai da ya fuskanci canji.
***
Wata mace budurwa mai ɗan duhun fata na tsaye tare da mutane a tsakiyar kasuwa tana kiransu izuwa sabon tafarkin hana cinikin bayi. Kayan jikinta farare ne marasa nauyi sabida haka a yanayin sanyi da ake ciki zaiyi wuya ace tana gumi. Amma abin mamaki da ita da ƴan tsirarun mutanen dake gabanta duk gumi suke. Idan ka lura sosai wannan mace ba wata bace illa Nusi Kil'zanki. Ko mai yasa take ta tafka gumi.
"Daga yau sarki *Tari* Wilbafos ya haramta cinikin bayi. Zaku fito da *Tari* *Tari*..." Maƙogoron ta ya bushe ƙayau kai kace bata taɓa haɗiyar yawu ba. Tari ya hana ta magana. Shi kansa gumin ya fara bushewa kai kace wuta ake kunna masa. Kuma bawai ita kaɗai bace, duk wani mahaluƙi dake yawo a garin sai da maƙoronsa ya bushe, fatarsa ta fidda gumi.
A dai-dai wannan lokaci su Lamarudu suna ƙoƙarin hawowa cikin garin sai kawai gadar da Nazara yayi musu ta kama da wuta.
Shi dai garin Faideba nada ƙananun hukumomi bakwai. A ƙaramar hukumar Tanja dake gaɓar arewa ta garin akwai wata unguwa mai suna Zinaru. Zaka iya cewa wannan unguwa tafi kowacce fuskantar zafi da gumi a lokacin zafi. Wataƙila sabida ruwan daya zagaye ta.
Mutan wannan unguwa kuwa tuni suka gudu. Dalili na farko akwai tiriri dake tashi daga cikin kudiddifin yana shaƙe musu numfashi. Dalili na biyu kuma akwai wasu mutane guda goma a tsakiyar wannan ruwa suna lilo akan iska. Kowanne acikinsu ya ɗaga hannu sama ɗauke da dunƙulen walƙiya. Idan ka lura sosai zaka ga cewa wannan mutun goma ba wasu bane illa Ƴan-goma da Armad ya bawa kwangilarsa ta walƙiya. Manzo Inara na tsaye a gabansu takobi a zare. Babban abin al'ajabin shi ne jikin Inara baki ɗayansa ya juye izuwa na walƙiya. Tamkar shi ne Armad. Tamkar shi ne Sikai. Sararin samaniya ya cika da walƙiya yana jiran umarnin sa. Dalili na uku da yasa duk mutanen garin suka gujewa wannan unguwa shi ne Ururu.
A dai-dai wannan lokaci wani mutun ne ɗauke da idanun Ururu a tsaye shi kaɗai yana fuskantar su Inara a wani salo na jiran kotakwana. Fuskarsa a rufe take, sabida haka zaiyi wuya a gane ko wane ne. Abu guda ɗaya bayyananne shi ne wannan mutun ma'aboci Ururu ne.
Waye zaiyi nasara?! Ko mai yasa rundunar Ururu suka fasa jira sai ƙarshen yaƙin? Ko mai ya kawo sarkin aljanu Wut-Naru wajen Hanibal.
#
Comments
Post a Comment